Showing 105001 words to 108000 words out of 278032 words

Chapter 36 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1101

mufeeda ta fada musu, suka Bashi wurin xama saman kujera,ya girgixa kai ya Dan zauna Dan nesa da mamah Asaman carpet yace nan ma yayi masa,....



Ya shiga gaida mutanan falon,duk suka ansa masa da kulawa, sannan ya gaidi mamah cikin girmamawa mamah ta ansa kanta aqasa,yay mata Jaje tareda, kwantar mata da hankali, da cewa in Sha Allah suna iya bakin kokarinsu in Sha Allah xa'a samu Rukayya,su cigaba da addu'a,kowa ya ansa da Allah yasa,kafin daga bisani ya tashi yay musu sallama, Hanan tabi bayansa sukai sallama,AA Arab Yana shiga mota sun dau hanyar xuwa gidansu ,ya jinginar da kansa a kujerar motar kira ya shigo wayarsa,ya duba yaga Mai Kiran yay picking,Yana picking aka sanar masa da ankai hari Wani qauye,take ya bawa driver sa oder su juya su nufi hanyar qauyen, Kuma yay waya da jami'an tsaron Dake heardquater,dasu taho ta mota biyu ta police, sannan yay Kiran police din Dake yankin qauyen akan suyi Maza su qarasa wurin gashi nan xuwa,ya aje wayar hannunsa gefensa,ya bawa driver umarnin inda xasu Babu musu ya ansa masa, dama shima police ne,AA Arab ya fesar da huci me xafi ya fara har gitsa gashin kansa, lallai dole yay bincike ta qarqashin qasa Dan Wannan mutanan dole akwai abinda suka taka,wlh muddun suka shigo hannunsa saiya sauya musu kamanni.....








07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t





*____JAMI'AR TSARO ____*




*_____THE WOMEN POLICE _____*




*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*




*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION(QOWA) =?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



________season one ep 4?? 5??



___________?&


Alhamdulillah anyi nasarar kama mutum daya cikin Yan ta'addar nan,Wanda AA Arab ne da kansa ya samu nasarar kamashi alokacin da motarsu ke kokarin shiga qauyan alokacin shikuma Wanda ya rage din ya fito cikin maboyarsa, fuskarsa a rufe Yana waige waige kwata kwata ya sha'afa Bai kula da motarsu AA Arab Dake shigowa kauyan ba,Dan gabadaya Hankalinsa atashe yake,Ashe baisaniba har Yan uwansa suka tafi suka barshi sbd shi yabi wani yaro xai kamo Wanda ya zille ahannunsa Ashe su sunji shigowar motar yansanda qauyan,tuni suka gudu,shikuma kwata kwata baijiba, ganin sun gudu sun barshi yasashi buya inyaso idan yan sandan suka shiga cikin qauyan sayya fito,ya tafi,Aiko AA Arab idansa ya sauka akansa Yana kokarin tsallaka titi, tuni AA Arab ya Gane shima Yana Daya daga cikin Yan ta'addar,babu Bata lokaci yace driver ya tsaya yana tsayawa ya balle murfin motar ya fito, ya nufo shi cikin sauri,take Dan ta'addar nan ya tsargu,ya fara kokarin guduwa,in a seconds AA Arab ya xaro bindigarsa daga cikin aljihun Wandansa na suits,ya harbeshi a kafadarsa take ya rintse ido ya dafe kafadar ya saki ihun azaba,Yana durqushewa awajan,....



AA Arab ya qarasa wajensa ya zaro wayarsa yay qira take wasu police su biyu suka fito daga cikin qauyan Dan babu nisa da titin yay umarni dasu kamashi su sakashi a motar da sukaxo da ita, suka kamashi suka nufi cikin qauyan Dan motar tana ciki,yace su kaishi heardquater a tsareshi,kafin yazo suka ansa Mai da girmamawa,AA Arab ya koma cikin motar driver yaja suka qarasa Shiga cikin qauyan, suna xuwa suka tadda su cikin Wani yanayi wasu anharbesu jikinsu duk jini,wasu Kuma anji musu rauni, suna kwance a qasa,AA Arab take ya Bada umarnin Akira ambulance adaukesu akaisu asibiti mafi kusa Dan Basu taimakon gaggawa,babu dadewa ambulance ta qaraso cikin qauyan take akai komai bisa umarnin sa, wannan karanma sun sace yara saidai Bada yawa ba sbd xuwan da jami'an tsaro sukai akan lokaci,....



Haka suka shiga bincike cikin qauyan lungu da Sako Amma Basu Samu ya ta'addar nan ba sunriga da sun tafi,anbi bayansu Amma shiru ba'a samesu ba, AA Arab yace su dawo tunda ankama mutum daya,ai dole xaiyi bayanin inda sauran suke,haka suka hkr suka dawo, bayan AA Arab dasu CP da DCP sun kwantar wa da mutanan kauyan Hankali, suka tabbatar musu da in Sha Allah komai ya kusan xuwa qarshe tunda yanxu sun samu nasarar kama mutum daya, sbd haka kama sauran ma baxai musu wahala ba,haka suka baro qauyan wajen karfe shabiyun dare,AA Arab Bai koma gida ba saida ya biya ta hospital din da aka kai mutanan ganin jikinsu da sauki ZA'A iya sallamarsu xuwa wayewar gari yasa wucewa gida,Bai je gidan ba sai wajen karfe biyun Saura na dare,.....


Yana xuwa ya tadda ummi a falor tana xaman jiransa,ya Dan waro ido waje yace tace ummi Baki kwanta ba,ummi ta nufoshi ta kamo hannunsa tace,Ina xan kwanta, Ahmad Bai dawo gida ba, kullum cikin Fargaba nake indai ka wuce karfe 9 baka dawo ba, yay murmushi yace ummi kidaina Damuwa kidaina Hana idanki bacci akaina,in Sha Allah I'm okay at always, tunda kina min addu'a , addu'ar ki Batada hijab atare Dani,ya qarasa fada da murmushi a fuskarsa, ummi itama murmushin tace dole ba damu Ahmad ta Kamo hannunsa tace muje kasha ko tea ne,na kula baka San cin abinci, yaudai baxaka kwanta haka ba,ya shafa kansa yace bari nai wanka ummi gabadaya jikina ya Baci da datti, ummi tace ok bari na kawo Maka har bedroom,ya sumbaci hannun ta,yace shukran ya ummi ,ummi tai murmushi ta lakuce masa fuska,tace oya Maza jeka ya nufi sama xuwa bedroom dinsa ummi Kuma ta wuce dining Dan hada masa coffee,.....



Bayan ya fito daga wanka Yana goge jikinsa da towel,ya tadda har ummi ta kawo masa ta ajiye kan table din Dake dakin, ya saki murmushi Yana maijin qara qaunar mahaifiyar tasa aransa,bayan ya shirya cikin pajamas,ya feshe jikinsa da turaruka sannan ya xauna kan sofan Dake dakin,ya dauki mug din ya fara sipping coffee din,bayan ya kammala ya goge bakinsa da tissue, sannan ya shiga toilet yay brush sannan ya dawo ya haye kan gado Yana tunanin yadda komai ya cukur kude masa,ga case din Yan ta'addar nan ga Kuma Batan JAMI'AR su, haka dai ya dinga tunanin yadda zai fuskanci case's din.,Dan yanxu bashida lokacin wannan Dan ta'addar sai gobe tunda ya tabbatar yanxu Yana tsare tunda sunyi waya da wadanda yasa su tsareshi....



___________?&


Yau kwana biyu kenan da batan Rukayya Kuma har yau babu Wani lvr akan inda take kowa ya dauketa,mamah harta gaji da Kukan ta fauwalawa Allah dukkan lamarunta, kullum tana kan sallaya tana addu'oi,idan kika ga tabar kan sallayan nan to alwala ko xatayi ko Kuma wanka, maman Hanan kullum saita xo gidan da safe,maman Shareef ma haka, Kuma Suma su ya hanaf da ya Tahir kullum sai sun fita yawan Neman ta Amma haka suke Dawo wa Babu labarin ta,....



Ta bangaren Hanan kullum cikin xullumi take shin ta fadawa mamah ko AA Arab cewar tana zargin Alhaji sunusi ko yaya, haryanxu ta kasa yanke hukuncin ta fada musu kokar ta fada musu,ita abinda yasa taki fada na farko kartaje ta fada Kuma bincike ya nuna ba Alhaji sunusi bane ya dauke suba, na biyu Kuma Batasan ta fada Kuma ya xamto dole saita fada musu gskyr abinda ya jefa Rukayya cikin wannan halin,Kuma alhalin ruky ta gargadeta cewar bataso mamah tasan da maganar, maganar gsky koda yaushe idan ta kalli mamah cikin damuwa sai taji kamar kaw????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ai ta fada mata gskyr,Amma xata jira idan taga har lokacin ba'a San inda ruky take ba,kawai xata fada musu Wanda take zargi da Kuma yadda sukai da ruky ranar da xa'a sacetan,...



Abangaren gidansu Khalil har lokacin Suma basuda lvrin inda Khalil yake sunyi binciken sunyi Neman Amma Allah baisa sun Sami Khalil ba, addu'a kuwa Babu Irin wacce basuyi ba,kawai Suma sun fawwalawa Allah komai,...



Alhaji sunusi ne tsaye awani gida ga guards dinsa na sirri suna biye dashi,haka suka Bude dakin da Khalil yake ciki bayan sunxo bakin kofar dakin suka Bude masa kofar dakin Wanda yake bakikkirin,guards din suka bashi hanya ya shiga, suka tsaya abakin kofar, Daya ya shiga yay saurin ajiye masa kujera,ya fito Yabar Alhaji sunusi kadai adakin, Alhaji sunusi ya xauna yana karewa dakin Kallo ganin an hasko Wani Abu daga waje take dakin ya gauraye da hsk, Alhaji sunusi ya xubawa Khalil ido kamar yadda shima yake kallansa cikin Mamaki, Alhaji sunusi ya dubi Khalil Wanda ke takure waje Daya akwana biyunnan har Khalil ya fada yay Baki sbd tashin hankali, Alhaji sunusi yace Ina fatan ka ganeni basai na maka bayani va ya qarasa fada yana xuba masa ido, Khalil baiyi magana iyaka kawai idon Daya xuba masa, Alhaji sunusi ya cigaba da fadin , karka wahalar da kanka Abu Daya nakeso awurinka shine ka bani, duk Wani recording da evidence da Kuka gabatar agaban kotu, sannan kuje ku janye qarar da kukayi,ku qaryata kanku cewar qaxafi kukayiwa lateef Dan kawai kunaso ku batamin Siyasa ta,sannan muyi arubuce cewar ka janye kanka daga cikin Wannan case din ,Kuma Babu Wanda xaka fadawa cewar Nina sa asamacemin kai ciki kuwa harda iyayan da suka haifeka,idan kaimun haka shikenan xansa asake ka,akomar dakai har Inda aka daukoka, idanko kaki wlh saina kasheka,nasa abunneka Babu Wanda ya sani , sannan na kashe iyayenka,ya fada Yana Wani cije lebe.....



Khalil da tunda yaga Alhaji sunusi abun ya bashi mamaki matuka, Bai taba dauka Rashin imaninsa yakai har hakaba, nasa adauko shi kawai sbd San xuciyarsa,Alhaji sunusi yace kayi shiru baka bani ansa ba,kainake sauraro akwai inda xani, ya fada Yana kallan agogon hannunsa,Khalil ya kauda kai , sannan ya juyo ya fuskanci Alhaji sunusi ido cikin ido yay karfin halin cewa Aiko da ace suna guna baxan taba baka ba, ballantana basa guna, Alhaji kaji tsoron Allah yarinyar nan marainiya ce yanxu laifine Dan mutsaya mata mun kwato mata hakkinta, Alhaji sunusi yay murmushi yace oh Allah yaro wato Naji tsaron Allah gsky ne,to idan anji tsoron Allah ba, tsoranka kakeso naji, Kodaya ke ,jikinka ne baiyi laushi ba shiyasa har ka samu damar fadamin magana,yace nasan suna gunka taurin kai ne kawai Irin naku na Yan jarida,yasa baxa ka baniba,sbd da haka Idan jikinka yay laushi kaida kanka xaka fada min inda suke nasa adauko,ko Kuma Wanda ka bawa ajiya ,yace banda lokacin batawa akanka daga nan wajen ita shugabar taka xani daga haka ya mike, bayan ya fito ya dubi yaransa Dake bakin kofar suna gadinsa yace kuyi ta dukansa har saiya Fadi inda ya boye su ko Kuma ya bawa ajiya,karku saurara masa,idan ya fada muku saiku kyale shi,Idanko Bai fada ba, karku saurara masa daga haka ya yay gava yaransa biyu suka shiga dakin suka hau laftar Khalil da gora kamar Allah ne ya Aiko su,..wasu Kuma suka mara masa baya......




Alhaji sunusi Yana fita direct inda aka aje Rukayya ya tafi Dan awaje Daya yasa aka ajiyesu, Saidai wuri daban daban, Yana Isa aka Bude masa kofar dakin ya shiga, Ruky tana ciki atakure ta kifa kanta cikin kafafuwanta,kukun ma tayi harta gaji,ganin anshigo dakin da mutane dayawa yasata,xabura tareda xuba musu ido harsuka qarasa shigowa,aka hasko hsk daga waje Wanda ya haske dakin gabadaya,aka zaunar wa da Alhaji sunusi kujera,sannan suka juya suka fita akabar iya Alhaji sunusi,ya xauna nesa da Rukayya ya Dora kafa Daya kan Daya, ruky ta xuba masa ido kirjinta na bugawa Yana dukan uku uku, acikin ranta ta Ambata uncle sunusi fa, uncle sunusi kanin mahaifin ta uwa daya uba Daya, yanxu shine yay mata wannan aikin, shine ya sato ta ,ya hana mahaifiyar ta bacci da Yan uwanta,da duk Wani masoyanta,ya sakasu acikin damuwa sbd xalinci da San xuciyarsa, Kodai mafarki take,idan mafarki take ya kamata farka daga wannan mummunan mafarkin,saidai kash azahirine tunda har mintsinar Kanta tayi danta tabbatar,Alhaji sunusi yay murmushi yace Rukayya umar MaiTama,ya fada Yana kallanta,da Wani shu'umin murmushi ,kinyi mamakin ganina koh,kinyi mamakin cewa ninasa aka kawo ki wurin nan koh,....



Sai Kuma ya qara sakin Wani Dan iskan murmushi cikin nishadi,Yace Nima haka kika bani mamaki lokacin da kikai kararmu nida lateef,ni amatsayin nayi belin lateef ba bisa qa Ida ba, sbd kinfini sanin iya aiki,shi Kuma lateef amatsayin Mai laifi,duk kece kika jefa kanki cikin wannan halin da kike ciki sbd taurin kai Irin naki na JAMI'AR TSARO,abu Daya xakiyi kawai na fitar Dake daga cikin Wannan ukubar na sakeki shine ki janye qarar lateef da kikai sannan ku qaryata kanku, kice qaxafi kukayiwa lateef Dan kawai ki batamin Siyasa ta Amma kina Mai bamu hkr ,nabiyu Kuma shine karki bari Wani yaji labarin cewar Nina sace ci,ciki kuwa harda mahaifiyarki da Kuma Yan uwanki, sannan ki bani duk Wani evidence da kike dashi,sannan kisa ahannu atakarda Dan yarjejeniya xamuyi idan kikai haka , nikuma na miki ALKawari ayau ba gove ba,xansa amaida ke har gida batareda kowa ya saniba ba, ....



Ruky da tunda ya fara magana take Harar sa, takejin tsanarsa na qaruwa aranta,kamar ta tashi ta shake shi haka take ji,ta dubeshi cikin takaici tace, nayi bakin cikin xamantowarka qanin mahaifina, Kuma kasani,wlh baxan tava Aikata Daya daga cikin abubuwan daka lissafoba,wlh saidai kai duk abinda xakayi, ka bani mamaki Irin Wanda Babu Wanda ya taba bani, kawai sbd San duniya kasa nai karya,sbd kawai siyasar ka,naji kai siyasar ka kake dubawa,ita Kuma yarinyar fa da rayuwar ta aka Bata mata gabadaya fa,ita Kuma meye makomarta,mezan fadawa Allah agobe kiyama,idan aka tsaida mu ranar shaida,bayan nasan gsky ,Amma na take ta,nabi ra'ayinka kawai danna faranta Maka, sannan ka kubutar ni daga ukubarka,wlh gara na dauwama cikin ukubar taka da kake fada dadai naje lahira na fuskanci na ubangiji,Dan shine guarantee,ni ba irin jami'an tsaron nan bane masu San duniya da abinda ke cikin ta,ni bisa gsky da Amana nake aikina ,na kare Wanda aka xalinta,na gurfanar da Wanda yay xalinci,dan na koma wajen ubangiji nah Ina Mai alfahari da aikina,Alhaji sunusi yay murmushi yace yaro yarone kinsan Allah Rukayya idan bakiyi abinda nace miki ba,wlh saina kashe yarinyar da kike wannan kumfar Bakin akanta,da uwarta, sannan kema na kasheki,babu wanda xaisan Nina aikata kema kinsani, ruky tace cikin Kuka uncle kenan baxanyi mamakin duk abinda kace xaka aikata ba, sbd tunda ka sato yar Yayanka uwa daya uba dayaba babu abinda baxaka iya aikatawa ba, Alhaji sunusi yay murmushi yace kina burgeni yadda kike da confidence haka,naji dadi da kikasan koni wanene,a badini, Rukayya xahirina kika sani , banida imani ni da kike ganina xan iya aikata komai akan siyasa ta da Kuma mutunci na wlh Rukayya kinsan kashe Rai baxai taba bani wahala ba,idan Baki saniba bari na fada miki Dan kamar kisan kiyashi haka nakeyi duk Wanda ya shigo gonata sbd haka tun wuri,kiyi abinda nace tun kafin lokaci ya kure miki,....



Ruky tai Wani murmushi me ciwo tace, wlh uncle baxan tava janyewa ba, Alhaji sunusi ya mike afusace yace ni Kuma Rukayya wlh saina kasheki ,Kinga inna kasheki babu wanda xai xargi cewar Nina kashe ki, kamar yadda har yanxu babu Wanda yasan nina sace ki, saikuma ya fara xagaye dakin yace jiya naje yiwa babarki jaje tana can kamar xatai huska,sbd damuwa,idan kinasan babarki cikin koshin lpy kiyi abinda nace,idan Kuma kinfiso ta mutu sbd damuwa karkiyi abunda nace, ruky ta goge hawayen fuskarta Jin abinda Alhaji sunusi ya fada lallai mutuminan bashida imani,tace meyasa xanjanye bayan Kasan danka shiya aikata laifin ,Kuma Babu Mai kashewa da rayawa,sai ubangiji giji, yayi yadda yaso akuma lokacin Daya so,Alhaji sunusi ya tsaya tareda juyowa yace sbd siyasa ta, banasan na rasa kujera ta mutane suki xabata idan suka San Dana shiya aikata wannan laifin, sannan banasan naji kunyar duniya....



Ruky tana qara goge hawayen idonta tace iya kunyar duniya kake tunanin ji ko Kuma nace tsaron ji ,ta lahirar kafa, wacce babu wani cin hanci ,bare Kuma dukiya sai a abinda ka aikata shi xaka girba,Alhaji sunusi ya daka mata tsawa yace kin fini sanin da lahiranne, yaushe aka haifeki nidai xabi na Baku daga nan xuwa gobe idan kika yanke xabin Dana Baki xan dawo sannan ki fadawa shima wannan Dan jaridan cewa kinjanye, shima nasan idan Yaga kin janye shima xai bani recording din da yay da Kuma duk wasu evidence da Kuka gabatar akotu, daga haka ya fita daga dakin,Jin ana Kiran wayar sa,yay picking ganin goga ne bayan ya gama sauraransa yace what ankama zailani,goga yace cikin yanayin muryarsa wlh mundawo kawai mukaga bayanan nazy yace tabbas yaga ankama xailani, Alhaji sunusi ya cire hular kansa sankonsa ya fito sosai, sannan yace Ina xuwa ya kashe wayar,bayan fitar Alhaji sunusi ruky ta kifa kanta da bangon dakin ta fara rera kuka Jin mamah tana cikin damuwa,ita babbar damuwar ta dama mamah tafiji sbd ba lallai ta iya daukar Rashin ta a kusa da itaba, wlh Alhaji sunusi saidai ya kashe tan Dadai tayi abinda yace din,.....






07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*




*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*



*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1? QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA) =?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season one ep 4?? 6??



___________?&


AA Arab ne tsaye ata bangaren inda ake aje Irin masu aikata manya manyan laifukan nan,ga CP agefensa da DCP da alama xance Mai muhimmanci suke,bayan sun gama sauraran AA Arab, suka ansa umarninsa cikin girmamawa sannan suka juya suka koma office dinsu a dai dai lokacin da Wani police ya qaraso wajen da AA Arab ke tsaye Yana waya,AA Arab ya sauke wayar sa bayan sun qare maganar da sukeyi police din da AA Arab yasa tun jiya su kula da zailani ya Sara masa, AA Arab ya ansa masa,ya sanar masa cewa xai iya shiga anfito da shi ,AA Arab ya jinjina masa kai sannan yay gaba police din yabi bayansa ya tsaya abakin kofar ganin AA Arab ya shiga ciki,bayan shigar AA Arab wurin ya tadda zailani anfito dashi daga cikin Dan akurkin wurin da suke Saka masu Irin laifukan nan awurin ,xaune yake a qasa cikin fitar hayyaci ,Hannunsa da kafa fuwansa duk ankawa ne Yana xaune ya kifar da kansa,AA Arab ya xauna kan kujeran da aka ajiye masa,ya dubi zailani Wanda ya dago da kansa ya dubi AA Arab saikuma yay saurin Maida kansa qasa,sbd kwarjinin da AA Arab yay Masa,.....



AA Arab in a serious note yace cikin cool voice dinsa, ba westing time naxo gunka nayi ba,inada aikinyi so inaso duk tambayar da xan Maka yaxamto ka bani ansa nan take,I hope u getted so lets go, saikuma ya fesar da numfashi yace inaso


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login