Showing 264001 words to 267000 words out of 278032 words

Chapter 89 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1033

fad'a tana tura Baki gaba.

Ya sauke numfashi kafin yace .

"Ok"daga haka tai gaba shi kuma yabi bayanta har suka shiga cikin falon lokacin ya hanaf ya sauko k'asa yana zaune a kan kujera.suka shigo bakinsu d'auke da sallama.

Hanan da ya hanaf har suna had'a baki wajen ansa musu sallamar su ,suna musu barka da zuwa lokaci D'aya da fara'a a fuskokinsu.har suka k'araso shigowa cikin falon,ya hanaf Dake kan 3 seater ya mik'e Yana bawa AA Arab wajen zaman akan ya zauna,Baiyi musu ba ya k'araso Yana zama akan kujerar ya hanaf ya koma ya zauna a kusa da shi Yana murmushi ,ruky Kuma ta zauna a kujerar da Hanan take kai da yake two seater ce ,ya hanaf ya Mik'awa AA Arab hannu sukai musuba kafin su gaisa cikin girmamawa.hanan ta gaida AA Arab da fara'arta, ya ansa mata da kulawa da tambayarta aiki Dan ita ta koma tun wancen satin,Hanan ta gabatar musu ruwa da drink's da abinda ta girka musu anan kan center table d'in Dake falon k'asa ta Kalli AA Arab tace.


"Sir bari mu baka waje kasha ruwa zamuje sama itama ruky taci nata.ta fad'a tana kama hannuna ruky.

AA Arab yay murmushi yace.

" Alhamdulillah".

Hanan tace .

"Please sir! Dan Allah kasha ruwa ",ya hanaf ya kalleta kafin yace.

" kuje zaisha". daga haka Hanan taja hannun ruky suka haye sama cikin farin cikin ganin ta.A falon Dake sama suka yada zango, bayan sun zauna ta kalli ruky tana Murmushi har lokacin tace.

"Sannu da zuwa sis! Kisha ruwa Dan Allah ,wallahi nayi farin cikin Ganin ki sosai".ta fad'a tana kallan Ruky.


Ruky ta kalleta itama tana murmushi Kafin tace .

"To amaryar Yaya! Wani delicious d'in aka mana haka ne".ta fad'a tana bubbud'e warmers d'in da Hanan ta jera akan table d'in Dake gabansu. take Hanan ta D'an yamutsa fuska tana toshe hanci alamar batason k'amshin.da mamaki ruky ke kallan ta ganin yadda take da fuska da Kuma hanci.ganin Irin kallon da ruky ke ma Hanan yasa tai saurin sakin Hannunta Dake kan hancinta tana kallan Ruky da san kawar da tunanin ruky dake kallanta da mamaki abinda tayi d'in tayi k'arfin halin cewa.

"Ke! in-law Kinga yadda kikai Wani fresh kuwa? kodai har kin harbu ne",ta fad'a tana kallan Ruky da murmushi Dan wallahi ba batun wasa ba ruky ta k'ara Wani Irin kyau na musamman.

Ruky ta Sauke numfashi kafin ta harareta tace .

"Sai dai abinda yafi harbuwa ba harbuwa ba. tsakanin nida ke waya riga Wani auran da har zaki Fad'i haka ,aike yakamata naiwa tambayar nan tunda gashi daga Bud'e wannan warmer d'in na kayan cikin nan kika Wani toshe hanci kina Wani ya Mutsa fuska alamar bakyason aroma d'in".

Hanan tai saurin cewa.

"A'a ni asuwa ai mu kan da saura ". ruky tace .

"Hmm k'arya kike wallahi Dan bakiga yadda kika sauya Bane shiyasa zakice haka,wai kuwa kina kallan kanki a mudubi kuwa?".

Hanan ta Bud'e ido kafin tace."ban Gane ba Mai kike nufi ba ?".

Ruky ta sauke numfashi tace .

"Hmm wallahi kinsauya ba kad'an kinyi Wani irin haske kamar Me Anya ko banyi d'a ba ". Ta fad'a tana murmushi.

Hanan tace.


"Babu Wani d'a da kikayi kawai dai kibar dai nayi da hasken ba Wani abun ba.

Ruky ta harareta tace .


"Hmm muna fuka kinsan i kawai fad'amin ne baza kiyi ba Kinga fa yadda kike Wani toshe hanci alamar bakyason aroma d'in kinga ko ai kin harbu ne,sai dai ko idan b'oyemin kikeyi".ta fad'a tana mata murmushin mugunta.


Hanan tai murmushi tace.


"Haba ruky kema kinsan babu abinda zan b'oye miki idan akwai Mai zai Hana,ni ba Wani jinya nai ba ko Kuma Wani sauyi da zan tabbatar da haka, kawai dai iya yanzunne naji banasan k'amshin kayan cikin Kuma fa wallahi lafiya lau nai girkin kawai yanzunne dai da kika Bud'e warmer d'in naji k'amshin ya hau kaina da yawa". ta fada tana ya Mutsa fuska".

Ruky ta tab'e Baki kafin tace.


"Aishikenan idan tai tsami zamuji ai ".

Hanan ta D'aka mata duka acinyarta tana dariya tace .


"Ke wallahi kema ban yarda dake ba".

Ruky ta Bud'e ido kafin tace .

"Kamar ya"?.

Hanan tace."kema kinsan ba ke kad'ai bace .

Ruky tana 'yar dariya tace.

"iKon Allah to nida waye?".

Hanan tace.

"Hmmm muje dai zuwa ai lokaci na nan zuwa shi zai fayyace mana komai". ta fad'a tana murmushi ita dai ruky Dariya tai kawai Amma batace Komai ba .


Ruky ta sauya zancen da cewa .

"To ya za'ayi?ke bakyason k'amshin ni Kuma zanci ya za'ayi".Ta fad'a tana murmushi..

Hanan ta Bud'e ido kafin tace .


"Meye aciki kici kayanki mana Ina ruwana".


Ruky tace .

"A'a kinga fa my son baya so".karya saki kiyi vomiting". Ta fad'a tana murmushi.


Hanan ta harareta kafin tace.


"Kinga malama banason iya shege idan zakici gara kici babu Wani abinda zai faru".

Ruky tai murmushi ganin Hanan tak'i yarda da abinda ta fad'a mata ta Bud'e ta d'ibi dai dai cikinta tana kallan yadda Hanan ta K'ara ya Mutsa fuska, Amma ta Maze ita ala dole Babu Wani Abu ajikinta .haka dai suna Yi suna hira sun dad'e agidan ashe har su ya hanaf da AA Arab sun fita Basu sani ba su suna can sama suna Shagalinsu Dan sunma manta da su dama Kuma kunsan halin k'awaye biyun nan indai suka had'u to tamkar karsu rabu haka sukeji.sai bayan Magrib sannan su AA Arab suka dawo nan sukai sallama tamkar karsu rabu har Hanan ta K'ara bawa ruky wasu kayayyakin na kayan mata suka rabu.jibi ranar Monday Kuma zasu koma aiki duk gabakid'ayansu.


__________?&


A Ranar Monday suka koma aiki kuwa.suna shiga cikin heardquater bayan sunyi parking a parking lot suka fito daga cikin motar ,nan fa kallo ya koma kansau Dan ma aikatan su sai kallansu suke gwanin ban sha'awa da burgewa,haka suka jero ana ta kallansu ita ruky abun ma kunya ya Bata.AA Arab na rik'e da handbag d'in ruky,haka suka jero duk inda suka gifta sawa musu Kawai ake bayama AA Arab dayake duk a k'ark'ashinsa suke sai Wani bangirma suke bashi na musamman.yanzu kan a cikin office d'insa ma ruky take ta baro falon, Dan Karan Kata kaf desk d'inta da komai yasa aka dawo mata dasu cikin office d'in sa Dan ko kad'an yace bazai barta ita kad'ai ba duk Wasu kayan aikinta yasa anshigo mata dasu cikin office d'in nasa da yake office d'in Yana da girma shiyasa,Dan k'aton gaske ne akwai tazara tsananinsu Amma kuma duk office D'aya ne..


Haka ruky da AA Arab suke more soyayyar cikin farin ciki da annashuwa Kamar babu gobe Dan ji suke tamkar su kad'ai ne acikin duniyar masoya , haka suke nunawa junansu tausayi da kulawa da Kuma k'auna Mai tsafa .....



___________?&

*ZARI'A*


A b'angaren gidan Malam Auwalu kuwa abubuwa K'ara gaba kawai suke Dan babu Wani sauyi sai a iya b'angaren su ummah.dan yanzu har barrister shamsu ya Aiko da wakilinsa Wanda suka zo suka nemar masa AURAN Ameenah, Babu Bat'a lokaci aka bashi tunda sun riga da sun dai dai ta ,aka sa ranar biki nan da wata D'aya gefe D'aya Kuma tana zuwa ABU abinta.


Bayan Byaki sun tafi Malam Auwalu ya shigo da goro da sweet kayan Saka Rana zuwa d'akin ummah. ummah ta d'ibarwa baba asabe da iyalanta, lokacin Nana sunzo hutu tace ta kaiwa baba asabe.babu musu Nana ta karb'a ta tafi har cikin falon Baba asabe tai sallama Baba asabe ta ansa Nana ta shiga ta sameta tana tsaye tana gyara d'aurin zaninta Dan fitowarta kenan zata fita tsakar gidan, Nana tace .


"baba! gashi inji ummah kayan Saka Ranar Yaya Ameenah ne".ta fad'a tana kallan fuskar Baba asabe ganin yadda ta sauya lokaci D'aya tunda ta ambaci wannan kalmar.baba asabe ta mik'a hannunta Dake kar karwa ta karb'i ledar hannun Nana Dake Mik'a mata kafin tace cikin rawar Baki.


"Waye wai Wanda zata aura d'in?".Ta fad'a tana tsoron ansar da Nana zata Bata.


Nana tai Wani murmushi kafin tai fari da ido tace.


"Tsohon saurayin ta Wanda aka tab'a Sa Musu Ranar AURE mana ,Kuma a lokacin Allah baiyi ba ko kin Man tane".ta fad'a tana kallan irin shock d'in da baba asabe ta shiga lokaci D'aya.

Baba asabe ta zaro ido waje kafin tace.


"Na shiga uku ni asabe! wai kina nufin wannan yaron dama Yana nan to Taya ma suka hadu?ta fad'a gaban ta na fad'uwa.

Nana tai Wani murmushi tace .


"k'warai kuwa shidai Ashe dai kin Gane shi ko kina Bak'in ciki ne?"ta fad'a tana kallan Baba asabe Dan ita Kanta Batasan ta fad'i haka ba saboda wallahi Wani Irin haushin baba asabe take ji.

Baba asabe batason lokacin data kai zaune jagwab K'asa ba tana cire D'an kwalin kanta tana Fifi ta jikinta dashi Dan jitai gabad'aya Wani Irin zafi ya shigeta lokaci D'aya.


Ganin haka yasa Nana ta fita daga cikin d'akin. zaliha tana uwar d'akin baba asabe tana fama da kanta da cikinta Wanda yake cikin wata na takwas.tana jin duk abinda ya faru tananin baba asabe da Nana.

take ta fashe da Wani Irin kuka da ya zo mata lokaci D'aya tana Jin duk baba hasiya ce ta jawo mata wannan halin da take ciki tana jin Inama ummah ce ta haifeta ba baba asabe ba da Bata shiga cikin wannan halin da take cikiba,ita gashi ummah da 'ya'yanta kullum cigaba suke samu Amma su gashi daga zaurawa sai ita Mai cikin shige Wanda ya tsufa haihuwa nan da wata D'aya take Wani kuka ya kufce mata ta dinga rerawa Babu Mai lallashinta.


Baba asabe kuwa ta-da zube a k'asa take Wani mummunan zazzab'in ya saukarwa mata lokaci D'aya,kafin ta fara k'ok'arin tashi daga zaunan da take Amma kuma taji ta kasa,tai tai ta tashi daga inda take zaune Amma Abu ya gagara Dan jitai tamkar babu Wani Abu Dake motsi a jikinta sai iya Numfashin da take Hakan yasa ta fara hawaye daga zaunan da take Dan tama kasa yin magana bare tai magana akawo mata d'auki..


Har su mardiya suka dawo gidan suka tadda baba asabe tana kwance ta lullub'e duka jikin ta da bargo nan suka tambayeta ko jikinne , Ganin tak'i magana yasa suka tambayi zaliha meke furuwa.


zaliha tace "ai tun d'azu da aka kawo mata kayan tambayar Yaya Ameenah data zube awajen bata k'ara tashi ba saima nice da nai mata magana najita shiru na fito naga ta kasa Motsi shine na d'auko bargo na lullub'e ta d'auka ta ko jikin nata ne ya tashi".ta fad'a cikin damuwa.


Sukai kan baba asabe suna mata magana Amma shiru kakeji ta kasa furta Komai da gudu mardiya ta fita zuwa d'akin Malam Auwalu ta sameshi ta fad'a masa bud'ar bakinsa sai cewa yayi Allah ya sawak'e ganin haka yasa mardiya rugawa da gudu zuwa d'akin ummah ta fad'a mata halin da baba asabe take ciki.

Ummah ta mik'e cikin damuwa kafin tace.

"Mardiya kin fad'awa malam kuwa?".ta fad'a tana kallan ta .

Cikin damuwa mardiya tace.

"Eh ummah na fad'a masa Amma cewa yay Allah ya sawake".

Ummah tace .

"Muje naga jikin nata" tafad'a tana yin gaba mardiya tabi bayanta .halin da ummah ta tarar da baba asabe aciki abun yayi matuk'ar girgizata Ganin Yadda baba asabe ta koma lokaci D'aya.take ta fito daga d'akin ta tafi zuwa d'akin Malam Auwalu cikin sauri.ta sameshi ya kwanta ya k'urawa kwanan d'akin ido Yana tunani.ummah tashi d'akin bayan tai sallama tace .

"Malam Dan Allah kayi hak'uri kataso kaga halin da asabe take ciki".ta fad'a cikin damuwa.Malam Auwalu yay banza ya k'yaleta ta k'ara Mai Mai ta masa yay tsaki yace.

"Dan Allah maimuna ki K'yaleni Mai kikeso nai matane?". ummah ta Kwantar da murya tace.

" asibiti nakeso a kaita".

Malam Auwalu yay tsaki yace .

"ni bani da kud'in kaita asibiti".

Ummah tace.

"ni zan biya".ya kalleta da mamakin zancen ta fad'a kafin ya mik'e Yana zura rigarsa ummah ta fita daga d'akin ta koma d'akin baba asabe Dan shiryata su kaita asibitin.

Suna zaune bakin emergency kusan mintuna 30 kafin Wani doc ya fito suna ganinsa ummah ta mik'e da sauri ta nufeshi ita da lawisa dama iya su biyu ne suka kawo baba asabe sai Malam Auwalu.ummah tace .

"Likita tayi magana kuwa?".

Doc ya numfasa kafin yace.

"Kubiyoni office Ina son magana daku",daga haka yay gaba abinsa.

Ummah ta koma ta t fad'awa Malam Auwalu abinda likita ya fad'a baiyi musu ba ya mik'e zuwa office d'in likita.

Malam Auwalu ya sauke numfashi cikin damuwa Jin abinda doc ya fad'a yace.

"shanyewar b'arin jiki Kuma likita?".ya fad'a cikin damuwa.

Doc ya Jin Jina kai Kafin yace .

"Eh hakane Dan ma kunyi gaggawar kawota asibiti da gaskiya abun sai yafi haka Muni, Kuma ba kamai ne ya jawowa ba illah tana Saka damuwa ne sosai aranta shiyasa Yanzu ma abin yazo mata farat D'aya,Dan jinin tane ma yayi mugun hawa sosai shiyasa ta fad'i d'in".


Ummah da hawaye har ya zubo mata saboda tausayi wai yau asabe ce da shanyewar b'arin jiki,kai duniya abar tsoro ce take taji tsoron Allah ya Kara shigar ta .lawisa itama hawayenne ya zubo mata ta fara sharewa ,nan doc yace anyi admitting baba asabe .haka suka fito daga office d'in.

lawisa tace zata zauna agunta ummah tace a'a ta bari zata zauna agunta ita tafi gida ta kula da Yara take lawisa taji wata kunya ta lullub'e ta yau ga ummah da baba asabe tai musu hud'ubar tsiya da suke wulak'an tawa da Bata ishesu kallo ba ada Amma yau itace take musu Rana Hakan yasa ta K'ara sautin kukunta ummah tana Bata Baki da haka suka koma gida ita da Malam Auwalu da zumar shima gobe sa safe zai dawo.....



*Bayan sati D'aya*


A Yau za'ayi zaman shari'ar su Alhaji sunusi,kotun nan ta cika mak'il da dan dazon al'umma kowa yazo Dan sauraran wannan shariar ta k'arshe ruky Bata samu damar halartar ba sakamakon kanta da yake mata ciwo a ranar Dan ko office Bata jeba ,AA Arab ne kad'ai ya samu fita office shima daga can ya wuce court d'in tunda k'arfe shad'aya za'ayi shari'ar .An gabatar da dukiyoyin su Alhaji sunusi shida babajo Ali Wanda suka Tara Wanda duk Rabi da kwata Bata hanyar halak suka samesu ba kwatane kawai suka samu ta hanyar halak shima dan suna a Matsayin 'yan siyasa ne tunda suna da albashi.iyalansu duk sunzo Hajiya SA'A abin tausayi kamar wata mahaukaciya haka ta koma jiki duk babu gyara kodan Bata da nutsuwa ne oho.haka Suma Matan su babajo Ali abin tausayi.ya hanaf yazo shari'ar Suna tare da AA Arab Dan waje D'aya suka zauna.bayan ankarantowa su Alhaji sunusi dukoyinsu da adadinsu da Kuma duk wata kadara da suka Tara an Zak'ulo su ansiyar dasu da yadda aka kasaftasu alk'ali ya kalli su Alhaji sunusi yace.

"To kunji dai yadda akai da dukiyarka da kuka Tara da Kuma ta hanyar da Kuka Tara d'in,shin Abinda aka fad'a gaskiya ne ko Kuna da jaa?". ya fad'a Yana kallan su

Abin mamaki sai Suka ansa masa da hakane babu Wani jaa da suke dashi

Alk'ali ya sauke numfashi yace .


"To za'a rarraba dukiyar ku ga k'auyukan da duk kuka kaiwa hari aka kwashe musu Yara,sauran dukiyar data kasance halak d'inku itama Kuma za'a bawa yaranku da Kuma matanku ,sannan Kuma daga k'arshe kotu tana umartar ku daku saki matanku yanzu yanzu tunda ku taku ta k'are".ya fad'a Yana kallan su take awajen Suka saki matan nasu ,Jin ance Kuma rataye su za'a Yi nan fa hankalinsu ya K'ara tashi take kotun nan ta hargitse da koke koke, Alhaji sunusi yasa Wani Irin kuka ya zube awajen Yana ya shiga uku ya lalace Dan Allah ai masa Rai duk Wanda ya zalinta ya yafe masa haka ya dinga kuka yana K'iran sunan Baban su ruky akan ya yafe masa dasu kansu 'yayansa Yana ta sum batu kamar Wanda ya samu tab'in k'wak'walwa Abun abun tausayi.shi kan ya hanaf haushine ma yasa ya tashi ya fita daga kotun bayan alk'ali ya buga guduwamarsa akan kowa zai iya tashi Hajiya za'a take ta yanke jiki tai fad'i awarin sai 'yan uwan tane sukaiyo kanta suka kinkimet suka fita da ita daga cikin kotun bayan Jin abinda aka fad'a akan za'a rataye su Alhaji sunusi ga Kuma sakin da yay mata, haka suma matan babajo Ali dashi kansa da yaran sa kuka kawai suke gwanin ban tausayi suna K'iran sun shiga uku ahaka aka fitar dasu daga cikin kotun akai prison dasu kafin ranar ratayewar Tasu tazo ta.......
Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 1?? 0?? 5??



___________?&


Haka rayuwa ta cigaba da gurgurawa har bayan sati biyu.hasashen ruky dai ya zama gaskiya akan Hanan,Dan Hanan sai cikine da ita bata saniba har na tsawan sati biyar Dan bayan tafiyar su ruky da kwana biyu ta fara jinya babu Bat'a lokaci ya hanaf ya d'auke ta ya kaita asibiti anayin test kuwa gwajin farko ciki ya bayyana farin ciki agurin ya hanaf ai ba'a magana.haka suka tarkata suka dawo gida bayan anrubuta mata magun guna, tsabar kunya Hanan kasa fad'awa ruky tai sai awajen anty mufeeda take ji itama ya hanaf ne yake fad'a mata jinyar da Hanan tai da Kuma zuwansu asibitin abinda doc ya fad'a Aiko ruky ta d'auki waya ta K'irata tai mata tas daga k'arshe Hanan ta Bata hak'uri akan cewa ita kunya take ji shiyasa Bata fad'a mata ba, ruky tai murmushi tai mata fatan sauka lafiya......


Yau dai Ruky suka shirya zasu je su gaida baba lami ,tun safe take jinta Wani iri gabad'aya jikinta yayi so week kawai dai daurewa take tana Kuma San fitar shiyasa bataso AA Arab ya sani Dan indai ya sani zai iya cewa a fasa zuwan ita Kuma Allah Yana Gani tana son fita tunda ba samun lokaci suke ba daga ita harshi sai dai da weekend d'in , Dan weekend ne kad'ai basa fita suna gida suna hutun k'arshen mako abinsu sannan su more soyayyar su.hakanan dai daure ta gama shiryawa tsaf.Bud'e k'ofar d'akin da akayi aka shigo lokaci D'aya yasa ta lumshe idonta Dan tana gaban mirror tana rolling mayafin abayar Dake jikinta ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login