Showing 27001 words to 30000 words out of 278032 words

Chapter 10 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1082

har ya dawo gida yanxun shine suke maganar da mamah ganin su ruky ne yasa sukai shiru Dan basa so taji,abinda Basu saniba ba ita ruky ta sani Amma Batasan babansa yaxo Dan da tasani da anan ne xata tabbatar ta managar da lateef ya fada gsky ne,,....



Hmmmm akwai fa drama>??


Hanan da ruky ne suka fara saukowa bayan sunyi sallahn isha'i Dan ita Hanan ta fitoma cikin shirin tafiya Dan tace tafiya xatai ruky tace Saita ci abinci ita Kuma tace ta koshi, suna wannan gaddamar mamah ta sauko,tace A'A Hanan dole saikinci abinci xaki tafi Babu yadda ta iya tunda Mamah ta riga da ta-da Baki,cikin Jin kunya Hanan ta wuce dining baba hasiya Kuma tana kitchen tana dafawa hanaf green tea,bayan sunci Hanan ta mike tace da Mamah tafiya xatai mamah tace tana xuwa ta wuce dakinta Dake qasa Dan tana da dakima a qasa,ta kawo mata ture da humra,masu bala'in kanshi, Hanan tai godiya, Ruky ta Rakata har bakin mota Dan drivern mamah ne xai kaita har gida,sannan ta dawo ciki ta tadda hanaf xaune a dining Dan haka ta Samu wuri ta xauna a falor, Ganin yadda yau baya cikin mood Mai kyau Dan tana tunanin kila akwai abinda ke damunsa shiyasa ta kyaleshi xata jira har ya sauko daga yanayin Daya shiga,Dan da ace babu abinda ke damunsa dashi zai fara janta da hira ,sbd sanin halinsa da tai ,haka ta tana xaune ta faralatsa wayar ta,...


________?&

Yau da daddare Alhaji sunusi yana xaune da jallabiya a jikinsa, lateef yace,Daddy kaje gidansu Rukyn kuwa, Alhaji sunusi MaiTama Dake xauna bisa Daya daga cikin kujerun tangameman falonsa,Wanda yaji kayan more rayuwa kamar baza'a mutuba,Yana shan fruits matarsa Kuma Hajiya SA'A tana daga gefensa,sai lateef Dake kujerar Dake kallansa,ya gama tauna Wanda yake cin ya Kalli lateef yace my son, lateef ya ansa yana Wani Dan cin magani yanajin yaji wacce ansa dadyn nasa zai Bada, yace naje daxu da safe kafinma na wuce offishin jam'iya na shaidawa Hajiya halima lallai nan da Wata Daya xa'a daura muku aure kaida Rukayya,shine Wani ta kawomin uxurin wai atsaya aji ta bakin ita yarinyar Niko nace sai munjira Ma ta bamu umarni Kome,nace nidai na yanke hukunci ,yadda xa'ayi,
Tunda indai lokaci ne ai munriga da mun Basu ,saunawa muna Basu lokaci, Hajiya SA'A tace yo inbanda abin Hajiya Halima tun yaushe ake basu lokacin, yarinya sai kace yar gwal sai abinda tace xa'a Yi ,ni Gani nake Hajiya Halima kamar bataso ta aurawa lateef yarinyar nan ne,Amma inba haka ba aita Abu Daya,babu ji babu Gani,sai kace cin Kwan makauniya ,ko kunyar kama bataji Alhaji, aida ace yarinyar Bata San lateef dinne ma dashi ne..


Alhaji sunusi yace ai ko bataso saita aureshi tunda Dana Yana Santa nifa farincikin Dana shine gava da komai xan iyayin komai akan Dana wlh,ita din Banxa itadin wofi,me akai akayisu ,Wanda suke takama da shidin ya bar duniyar sai muga abinda xasuyi ,Basu isa su hana abinda Dana yakeso ba, lateef da Saiyanxu yayi magana yaji Wani sanyi aransa Jin xa'a aura masa Ruky nan da one month yace thanks daddy, shiyasa nake Sanka,ni bari naje mom good night, Ina zakaje lateef,yace mom xan fitama saikin tambayeni Ina xani , Alhaji sunusi yace haba SA'A yaran saurayi dashi Amma zai fitama saikin tambayeshi Ina xashi, tace to laifine Alhaji ,danna tambaya,yace eh laifine tace to Allah ya baku hkr daga haka taja Bakin ta ta tsuke, lateef har ya kai bakin kofa Kuma ya dawo yace Dad please kabani cash xanyi anfani dasu, Alhaji sunusi ya kalleshi yace ba jiya na tura ma kudi ba, yace eh dad but ni cash nakeso, gsky bansan xuwa bank, Alhaji sunusi Yace ok kaje ka Bude drawer ka dauka yace yes Dad sannan ya fita, Alhaji sunusi ya bishi da kallo Yana murmushi yanajin Kara kaunar Dan nasa tana qaruwa,...


Bayan fitar lateef Hajiya SA'A ta dubi Alhaji sunusi tace a gsky Alhaji bana San wannan kudin da kake bawa lateef ai yayi yawa,yay aiki mana tunda ya gama karatun,kaga Koba komai idan Yana aikin ai da sauki tunda kaga AURE xaiyi ,zai aje iyali,baxai Yiwu ace ajikinka zai laruba,nifa Alhaji nafiso lateef yay aurannan kona samu ya nutsuwa ya shiryu Amma wannan rayuwar dayake kwata kwata Bata dace dashi ba, Alhaji sunusi ya sauke numfashi yace batun na daina bashi kudi Bata taso ba,tunda shine dai nake tarawa kudin Kuma shine magajina,batun AURE Kuma tunda ya samu wacce yakeso ai zance ya kare, Hajiya SA'A ta sauke numfashi tace aishikenan ,....


Lateef Bai xarce ko Inaba sai gidansa inda yake aje mata yake sheke ayar su dasu Dan tun magrib yake Kiran wayar ruky Amma Bata picking, yaso yaxo gidansu bayan sallan isha'i sai Kuma wata budurwasa tai. Kiransa akan tana jiransa a Inda suke haduwa ya dauketa,shine Yaxo gida Dan ya karbi kudi awajen dadynsa sannan ya tambayeshi ya sukai ta bavar ruky mamah kenan,Kuma tunda yaji abinda dadyn nasa ya yanke saiyaji sanyi aransa domin koba komai babansa baya magana biyu idan yace yes ,to yes dinne idon ko yace no to no dince, shiyasa Bai damu ba xai jira gobe Friday saiyaje Koda daddare ne gidansu Rukyn daga haka ya kure volume din wakar dayakeji a motar yay hanyar inda xai dauki budurwar tasa ya wuce gidansa da ita....




_______*?&GIDAN AMEENAH*


Saude ce ta shigo,Dan tayi ta sallama Basu jiba,inda ta qara sallama bayan ta shigo dakin da kwanan abinci a hannun ta, Ameenah tace a'a saude kece tace eh anty Ameenah Ina wuni , Ameenah tace lpy lau saude ya antyn ( haka take cewa babar saude) tace lpy lau gashi tace nakawo miki Ameenah ta karba tace nagode ki gaida ta saude tace zataji,saude ta fita bayan ta gaida Nana itama Nana ta ansa mata,...


Nana tace wannan fa , AMEENAH ta Bata lvrn yadda take taimaka mata,har kaita chemist da tai, Nana ta jinjina kai tace Allah ya Bata lada in Sha Allah xan fadawa ummah, ta mata godiya,Ameenah ta tura mata kwanan abincin gabanta tace Nana gashi kici, Nana tace a'a na koshi dannaci abinci a gida kila kece Baki civa,ta mike tace bari na gyara miki gidan kici abincin,Ina kayan wankinki na wanke miki kafin na tafi, Ameenah tai murmushi tace nagode sosai yar uwa, ta nuna mata,dama ta Tara wankin tana tunanin ya xa'ayi tayi,haka Nana ta kama share gidannan tas ta wanke mata kwanikan kitchen din nan tas ta hado kayan wankin ganin Babu sabulu ta fita ta Siyo batama fada mata ba,ta gama wankin nan tas ta Shanya,kafin?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? kice me gidan yayi kyau,taxo ta tadda har Ameenah tai bacci ta samu wuri ta xauna tana kare mata kallo tana tausayin yayar tata,tana ayyanawa aranta Sauta fadawa ummah komai na halin da Ameenah ke ciki,tana nan xaune har wankin ya bushe ta kwaso su ta linkemata su ta sakasu a sif sannan itama ta kwanta,....


Da yamma Nana taiwa Ameenah sallama cewa xata tafi, Ameenah kamar tai Kuka dan wlh bataso su rabu,tace Nana Dan Allah karki fadawa ummah abinda xai ta-da mata da hankali nana dai kawai ta ansa mata ne, Amma babu abinda xai hanata ta fadawa ummah,haka suka rabu suna kewar junansu,.....




07066508376_______
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD

*____JAMI'AR TSARO____*


*____THE WOMEN POLICE____*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*NA*


*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*


*____(MRS SARAKIES)____*


*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA) =?1?*


*Bismillahirrahmanirrahim*


____season one ep 1?? 4??


________
'?
'?

Washegari Friday da tai makon Hanan ruky ta samu kwarin gwaiwar xuwa wajen DCP, karfe 11 Hanan ta baro government house xuwa headwater Dan samun DCP akan case din shafa ,bayan sun baro office din Ruky, office din DCP Suka nufa sunxo dai dai bakin kofar shiga Ruky ta kalli Hanan tareda rike hannunta,tace wlh Gani nake kamar baxamu samu yadda mukeso ba, Hanan ta juyo tace don't be scared ruky, karki saurin sarewa haka ,in Sha Allah xa'a dace,kinsan DCP Yana sanki Kodan san dayake miki Ina kyauta xaton in Sha Allah xai goya mana baya,badan ruky ta yadda ba,haka suka qarasa shiga inda sukai sallama suka shiga first falo, ganin baya nan sai wasu police Dake xaune yasa su qarasawa cikin seconds , falon inda sukai sallama, DCP ya ansa musu suka shiga,Yana xaune gaban table dinsa da takardu a gabansa ga computers ga files, yanxu ma Wani file yake dubawa,ya dago ya dubi masu sallaman Ganin ruky ce yasa shi sakin murmushin Jin dadin ganinta,yace barkanku da xuwa Hanan tai murmushi ta Sara masa ya jingina kai Yana nuna musu wurin xama itama ruky ta risina ta gaida shi ya ansa Yana murmushi ,....


Ya rufe file din gaban nasa ya Kalli Hanan da tsokana yace yau Kuma an kawo min xiyara kenan har office Batare da na rokaba hanan Tai murmushi tace ai xiyarar baxata ta bi lada yayi murmushi tareda Kallan Ruky wacce ke wasa da fingers dinta sannan ya dubi Hanan har sannan murmushi ne shimfide a fuskarsa yace ASP Hanan kwana biyu bakya shigo mana tunda kika bar headwater Kuma, shiru saidai idan general meeting xa'ayi,shima Kuma wannan Baki xo ba ko kunyi tafiya ne keda her Excellency, Hanan tai murmushi tace wlh munje jigawa ne,yace ok Masha Allah to ya government house din,tace da Dadi babu Dadi yay murmushi yace haba,tace ni wlh wannan tafiye tafiyen ne banaso ta fada tana Mai batarai bil hakki da GSK take, DCP yay murmushi yace dan babu kawarki ba, Hanan tace ai wlh sir naso da ita dandai kawai ,anriga da anyi posting ne,Kuma Dan tace bataso kai Kuma ka biye mata, ta fada tana hararar ruky,yay murmushi yace CP ne kema ya hana a sake canzawa shiyasa,....


Ya Kalli Ruky yace ranki dade sannu da xuwa, ruky tai murmushi kawai,Jin Hanan tai mgn yasashi juyawa ga kallansa kanta , Hanan tai murmushi tace sir wurinka mukaxo magana ce me mahimmanci ta kawo mu,ya gyara xama ya kalleta on a serious note yace ok ,go a heads Ina jinki,Hanan ta sauke numfashi tace sir case ne na fyade akama wata yarinya Dake hayin rigasa,ta mika masa File din Dake hannunta,Wanda ruky ta dauki statement din komai Amma Basu karbo na wajen Ibrahim Khalil ba,ya karva tace sir fara karantawa tukunna ya karba ya karanta sosai ,bayan kamar mintuna ya dago ya duvi Hanan wacce ke kallansa itama har sannan,tace bari ruky ta baka lvrin komai yadda abin ya faru domin itace tabi diddigin case din,ya Kalli Ruky wacce ta sunkuyar da kai sbd Irin kallan Dayake mata,ta sauke numfashi ta bashi lvrin komai yadda akai har yadda ta kaisu asibiti da komai, ya jinjina kai yace my lallai ke police ce wacce ya kamata ai Koyi da ita Allah ya miki albarka yanxu in Sha Allah xamuje asibitin naga komai Sannan sai muje gidan da kuke suspecting din,in Sha Allah wannan case din xan shigar dashi office Dina zamu bincike Sosai Dan Gano Wanda yay wannan aikin,..


Ruky ta sauke numfashi Jin ya dauki maganar da mahimman ci sosai,tace thanks alot sir for taking this case seriously,yay murmushi yace never mind dear in Sha Allah ranar Monday xamuje asibitin Nima na gani da ido na,tace ok sir Hanan ma tai masa godiya sosai yace Babu komai,ya mike ya kawo musu ruwa da lemo sukai godiya haka suka cigaba da tattaunawa dan shima DCP ransa ya Baci Daya Karanta wannan case din Kuma yace zaije har division din hayin rigasan yaji meyasa suka banzantar da case din,....


Ganin 12 :15pm yasa suka mike suka masa sallama inda ya ansa musu , Yana qara musu godiya Sannan suka fita,bayan sun Koma office din Ruky, Shareef suka Tarar shima Yana shirin fita sbd lokacin sallah yayi , yace twin daga Ina haka , ruky tace daga inda ka aikemu ,hanan tai murmushi tace Dan fita mukai musha iska , Shareef yay murmushi yace lallai ko dafatan kunsha ta da kyau , Hanan tace sosai ma, ruky ta gama tattare ta kardun kan table din ta Sannan ta dubi Hanan tace mutafi,sai Kuma ta kalli Shareef tace mu muntafi,yace kaji Yan gata mudai muna nan Allah dai muma ya kawo ranan hutawarmu, Hanan tace Ameen,tai gaba ganin Ruky harta kai bakin kofa,...


_________?&


Da daddare ruky suna xaune a falor wurin karfe takwas da Rabi Dan har sunyi dinner itada Mamah suna hira da baba hasiya, ya Hanaf Kuma yaje duba abokinsa a hospital ne,baidawoba, ruky tana xaune Kiran lateef ya shigo wayarta,Wanda tun safe yake Kiranta batai picking ba,daxu bayan magrib ma yay ta Kiran nata tana kallo amma batai picking ba,da xata lissafa miss call din nasa sunfi Ashirin,kawai ganin mutum sukai akansu a bakin kofar falon, kamar Wanda aka jefo ,Saida yashigo ma sannan yay sallama mamah ta ansa masa ya samu wuri ya xauna, yana kan kujerar ya gaida mamah, mamah ta ansa masa still kallonsa take, ruky ta saci kallansa taga ita yake kallo ,tace Ina yini yaki ansawa itako tai Banxa ta kyaleshi ta cigaba da kallanta,....


Saida ya gama isarsa da takamarsa sannan,batare da ambaci sunan taba,yace Ina ta Kiran wayarki bakya picking koh ,Kuma nasan kina Gani , meyasa kodan Kinga Ina lallabaki ,kodan lallabawa ma ai ta kare tunda nan da one month iyanxu kina gidana ,ya dubi mamah wace har lokacin idon ta yana kansa, yace mamah Baki fada mata cewa nan one month ne ta xama mallakina ba, ZA'A AURAmin ita ba,ai Babu shiri ruky ta juyo Jin abinda lateef ya fada taga hankalinsa kwance ma yake maganar da ta kalli mamah wacce itama ta xubawa lateef ido tana ganin Rashin kunyarsa da fitsara da Rashin tarbiyar da be samuba,tun asali,ya qara gyara xamansa yace da dukan alamu mamah Bata fada miki ba, Amma nasan Kinsa ni saidai na qara tuna miki domin shekaran jiya da muna waya ainace miki xan fadawa dady Azo ayi managar AURANMU,....


jiya Dady yaxo nan gidan ya samu Mamah,ya fada mata cewa nan da Wata Daya xa'a daura mana AURE ,Kuma anriga da an tsaida magana,tunda har dady yay magana , ruky hawaye ya xubo idanta ta mike jikinta na rawa tace ya lateef bana fada Maka cewa kayi hkr ba,,wlh baxan tava auranka ba Aina fada Maka tun asali nace ka Ravu Dani wlh Allah baxan tava auran kaba,har lokacin hawaye ne kwance saman kyakkyawar fuskarta,wacce take qara jefa lateef a duniyar Santa, lateef ya lumshe ido tareda da Bude su lokaci Daya ,yana Jin kalamanta suna dagar Gaza masa xuciya,yace kina nufin duk jiran da xaman da nai da baki lokacin da nai duk abanxa ne, mamah ce ta katseta ta dubi lateef tace ban fada mata ba domin ni nasan auran baxai taba yiwuwa ba,shi Baban naka Bai fada Maka daidai ba,domin shi yaxo ya fadi nasa ra'ayinne baiji namu ba, Inbanda baka da kunya har kaxo gabana kana fadawa 'yata haka , bakaji kunyar cewa ni na haifeta ba da kake ikirarin xaka aureta,Aiko baka mutun tani ta matar Dan uwan mahaifinkaba xaka mutun tani ta uwar wacce kake ikirarin xaka aura din , ....


Ta Kalli Ruky wacce taketa gurxa kuka ta kamota ta zaunar ta kusa da ita tace ki kwantar da hankalinki tunda har bakya so babu Wanda zai Miki dole,ta kalli lateef tace tunda har kaji abinda ta fada katashi ka fita kabamu wuri lateef ya mike cikin fushi da bacin Rai Irin na Yan Shaye shaye ,dama Kuma kusan abigen yake, yace wlh saina AURE ta ,Bata da miji sama Dani ,sannan ya nuna ruky da yatsa yace ki shirya cikin satinnan xa'a daura mana AURE saidai ki mutu,ya dubi mamah Wacce ke kallansa cikin mamaki yace wlh saina fadawa dady duk abinda kika fada,tunda dama kece kike z....


Bai karasa fada ba a ka wanke masa fuska da wani lapiyayyan Mari a fuska kafin ya dawo dai dai an Kara masa Wani, cikin axaba lateef ya dafe kuncinsa Yana kallan Wanda yay Marin,daga ruky har mamah kowa kallansa yake cikin mamakin yaushe ya dawo Basu saniba,....


ya nuna lateef da yatsa yace cikin huci da bacin Rai ,wato mahaifinka yaxo ya fadawa mamah maganganu san ransa shine kaima kaxo xaka Dora akan nasa kome,karka kuskura wannan kaxamin bakin naka marar tsarki yayi kuskuren fadawa mamah wadannan kaxaman kalaman naka, kai yanxu wuyanka har yayi Kaurin da xaka Tako mana kaxo har gidanmu kace xaka fadawa mamah irin wadannan kala mannaka, aure ne baxa a baka ba anhanaka, yau ko Auta tana sanka wlh baxamu taba aura maka itaba sbd kwata kwata baka da qualities din da zamu dauki ya abaka, inaso kaje kafadawa Baban naka cewa ni hanaf nace baxa'a taba b.....


Maganarsa ta katsene , sakamakon mamah data dakatar dashi ,ta mike tace hanaf kul karkayi ko bamu komai shidin Dan uwan mahaifinkune, Yaci wannan darajar sannan karka manta banasan ayiwa babba Rashin kunya ta nuna lateef dayake rike da kunci Yana xaxxare ido ,yana huci kamar xaki,tace katafi ga hanya nan lateef sai Yanxu ya dawo daga suman tsayen da yay sakamakon Marin da hanaf ya masa,yay kansa wai zai rama hanaf shima ya xaburo,yace kai har ka Isa nai maka Abu kace xaka rama ,Kuma ka gwada ka Gani wlh sainayi fata fata dakai a falon nan,mamah ce ta kamo hannunsa,....

Tana hanashi qarasa ga lateef Daya tsaya a tsaye svd yanayin hanaf yasan ko hauka yake Bai isa yace xai Rama ba,svd Hanaf yafishi komai da komai,Rashin mafitane yasashi nuna ruky da yatsa yace ke Kuma wlh Allah saikin Raini kanki ki jira nan da sati Daya wlh sai an daura AURAN nan saidai idan mutuwa ma zaki ki mutu daga haka yay hanyar fita daga falon Saida yaje bakin kofa sannan ya juyo ya Kallesu yace Kuma wlh saina fadawa dady duk abinda Kuka fada ,kujira xuwansa daga haka yasa kansa ya fice ,hanaf dama dayakejin haushinsa daga shi har ubannasa yay kansa ya juye haushin uban nasa Daya keji akansa ,mamah ce ta rikeshi ta hanashi xuwa,....


Bayan fitar lateef haka ruky ta qara sautin Kukan ta ,sbd kalaman sa na qarshe wai nan da sati Daya wlh tasan Babansa tsabar zai yadda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login