Showing 234001 words to 237000 words out of 278032 words

Chapter 79 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1098

Babu abinda ya faru,har dai suka gama wayar suka rabu suna Mai Jin kewar junansu.

A b'angaren Hajiya SA'A kuwa,komai ya k'are mata hatta zuwa gun lateef da Alhaji sunusi da take sonyi an Hanata ganinsu ,gidan da take ciki ma an fitar ta daga cikinsa saboda shima Yana hannun jami'an tsaro ne,kai ko Mai dai da Alhaji sunusi da babajo Ali da suka mallaka hukuma ta karb'e su har sai angama bincike tukunna,su kansu ma'aikatan gidan da masu aikin ansallamesu kowa ya kama gabansa.

Ata k'aicedai Hajiya SA'A yanzu haka tana gidansu na gado in kuka ganta saikuma tausaya mata, saboda yadda ta rame tayi duhu ta fita a hayyacinta, kullum cikin zubar da hawaye take,sai Babar tace da 'yan uwanta suke faman Bata Baki Amma Ina kwata kwata tariga da tayi nisa, kamar ba Hajiya SA'A 'yar Garu Mai sa gwala gwalai da juya naira yadda ranta yake so ba,ga Kuma wulak'anta mutane da Masu aiki ,to Allah dai yasa mudace dama ai ita duniyar nan juyi juyi ce.Allah dai yasa mufi k'arfin zuciyarmu>?2?.....





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*




*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 9?? 2??



____________?&


Tun daga wannan Rana Kuma sai soyayya Mai k'arfi ta da ratsa zta shiga zuciyar masoyan nan Babu kama hannun yaro babu abinda ya ragu saika k'aruwa da yay,wannan kenan.


ya Tahir shima dai yace bazai bari Auta ta rigashi aure ba ,Dan haka shima ya samu matar AURE a nan kano 'yar gidan Wani tsohon senator, ganin haka yasa Mamah tace shima ya hanaf ya fito da matar AURE duk tayi auransu ta huta, Amma shiyace baida matar AURE,Dan har yanzu Baiga Wacce tai masa ba.


Yau ya kasance asabar farkon hutun karshen mako , k'arfe 11 Saura na safe,Yanzu haka Suna tare a dining suna cin abinci gabakid'ayansu kamar yadda suka Saba,bayan sun gama ci ya hanaf ya mik'e zai bar dining d'in Mamah ta kira sunan sa .ya juya Yana kallan ta bayan ya ansa,tace


"Koma ka zauna magana zamuyi",ta fad'a in a serious talk,babu musu ya koma ya zauna Yana sunkuyar da kai k'asa,Dan yasan akan abinda zatai masa maganar.

Mamah ta kalleshi kafin kira sunan sa da .

"Hanaf! ayina muka tsaya kan batun samun matar auran naka?", ta fad'a tana kallan sa.

Ya hanaf ya shafa kansa kafin yace .

"Mamah har yanzu nifa bansamu ba ",

Mamah ta Jin jina kai zatai magana ruky ta rigata da cewa .

"Mamah idan yanaso zan zab'o masa matar auran",ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa,


Mamah ta Kalle shi taga yay shiru baiyi magana ba ,ya k'urawa waje D'aya ido, mamah ta Maida kallanta kan ruky kafin tace .

"indai da gaske kike Auta ki Nemo masa mana", ta fad'a tana kallan ya hanaf taga me zaice. tace,Dan ita har ga Allah a wasa ta d'auki maganar.

Ruky tace.

"wallahi mamah da gaske nake in dai Yana Sonta", ta fad'a tana kallan sa.

Mamah ta Kalli ya hanaf Ganin Bai d'ago da kansa ba har lokacin kuma baiyi magana ba tace.


"to ai dama na gaji da zamansu haka Babu aure kaga shi Tahir yayiwa kansa fad'a yace ya Samu matar AURE yanzu haka ma Nanda next week ZA'A je masa tambayar AUREN,Kuma Yama ce shi saiya riga Auta AURE" ,ta kalli ya hanaf ta ce .

"kai kuma fa? kana da wacce kake son ko asamo makan ? Ta fad'a tana kallan sa,.


Ya hanaf d'ago da kansa ya Kalli mamah yace.

"ba tace zata samo min ba",ya fad'a Yana kallan Ruky.

Mamah ta Sauke numfashi ta maida duban ta kan Ruky tace.

"Wace ce wacce zaki samo masan?",


Ruky tai murmushi tana kallan ya hanaf sai Kuma ta kalli mamah kafin tace.

"Zan fad'a miki bari Yabar gun", ta fad'a tana kallan sa.

"ya hanaf ya mik'e yana kallan Ruky yace .


"Ki fara sanar min ko wacecen kafin ki yanke hukuncin",ya fad'a Yana barin wajen.


Mamah ta girgiza kai tace.

"Wai da Gaske kake hanaf?",

Ya Jin Jina mata kai ,mama tai murmushi tace.


"Hanaf ba kunya",

Ya Shafa kansa Bai juyo ba yace.

"Mamah ai gara na fara sanin ko wacece kar naje a had'ani da wacce batamin ba,Dan nace asamomin ko wacece",

Mamah tai murmushi tana girgiza kai ta kalli ruky tace .

"Wacece wacce zaki had'a ta da Hanaf d'in?",ta fad'a tana kallan Ruky.


Ruky tai k'asa da murya tace.

"Hanan nake nufi", Mamah ta Jin jina kai kafin tace .

"Aiko kinyi tunani Mai kyau danni ma naso ace Wani a cikinsu ya auri Hanan,Dan yarinyar kirkice ga hankali da tarbiya,to Allah dai ya dai dai tasu",


Ruky tana murmushi har lokacin tace .

"Ameen".

Mamah tace.


"Kin fad'a matane da zaki yanke hukuncin da kanki haka",

Ruky tai murmushi tace .

" a'a ban fad'a mata ba mamah!,barema nasan bazata k'i yarda ba, anjima dai nake so naje gidansu na fad'a mata",

Mamah ta sauke numfashi kafin tace .


"To shikenan Allah yasa, Amma ki fara fad'awa hanaf d'in Muji Mai zaice duk da shi ya Baki wuk'a da nama",


Ruky ta gyad'a mata kai kafin tace.

"In Sha Allah"

Mamah ta mik'e ta shige D'aki,ruky Kuma ta fita zuwa part d'in su ya hanaf.


Tana shiga ta tarar da shi a falon d'akinsu Yana kallon Ball tai sallama ta k'arasa Shiga ciki.ya kalleta kafin ya ansa mata sallamarta.


Ruky ta kalleshi bayan ta zauna tace.

"Yaya! "Ta k'ira sunansa .

Ya hanaf ya juya Yana kallan ta,ta cigaba tana wasa da yatsun hannun tace .

"Nazo in fad'a Maka wacece? Dan anjima nake so naje har gida na fad'a mata",ta fad'a tana kallan sa.

Ya gyad'a mata kai Yana kallan ta .

Ruky tace .

"Amma Dan Allah Yaya idan na fad'a Maka ko wacece Dan Allah karka k'i amincewa",ta fad'a cikin shagwab'a.

Ya hanaf yace .

"A'a bakice dai idan ta min ba",ya fad'a Yana ya Mutsa fuska.

Ruky tai dariya tace .


"Ai nasan ma zatai Maka shiyasa na zab'a Maka saboda ta dace da kai",

Ya Jin Jina mata kai kafin yace.

"Ok, Ina jinki fad'amin Wacece?",

Ruky tai k'asa da murya tace .

"Hanan!",

Take k'irjinsa yay Wani Irin harbawa kafin ya lumshe ido ya Bud'esu lokaci D'aya Yana Hana yanayin Daya shiga bayyana a fuskarsa ya Dake ya yamutsa fuska yace .

"Wace Hanan?",

Ruky ta waro ido waje tace .

"Kai Yaya!, Yanzu Hanan d'ince zakace baka sani ba?, Hanan fa k'awata", ta fad'a tana kallan sa .

Ya Shafa kansa yace .

"I'm sorry, sai yanzu na Gane ta",

Ruky tace.

"To ita Yaya kana son ta Dan Allah,tayi Maka Aiko?, Dan Allah kace kana son ta", duk ta jero masa wannan tambayar ta fad'a tana kallan sa.

Hanaf ya kalleta Yana waro ido waje yace,

"ba ke kika zab'a min ba?,idan har ta Miki to Nima tamin", ya fad'a Yana murmushi


Ruky ta Bud'e ido cikin mamaki ta ce .

"Da Gaske kake Yaya kana sonta Dan Allah ,ka amince" ta fad'a cikin murna.

Ya hanaf Yana murmushi ya gyad'a mata kai, ai ruky saboda murna da farin ciki ta kamo hannunsa tana kallan sa da murmushi kafin tace .

"Nagode sosai Yaya da wannan karb'ar zab'in nawa da kai , nagode sosai, bari anjima tayi naje har gidansu na fad'a", mata ta fad'a tana sakina hannunsa ta mik'e.

Ya hanaf ya bita da kallo Yana Shafa kansa Yana murmushi,bayan fitar Ruky ya sauke ajiyar zuciya Yana Mai Jin Wani nauyi Daya tokare masa mak'oshi Yana narkewa kad'an kad'an da fatan Allah yasa Hanan ta yarda ta amince da soyayyar sa,Dan dama tun lokacin data dawo gidansu da zama a lokacin da aka sace ruky yaji tana burgeshi, lokaci D'aya kumu ya kamu da son Hanan,Yana so ya fad'a mata Amma Kuma ya kasa,Kuma har yau abin Yana ransa Allah NEMA yasa ruky zata rigashi fad'a Amma da acikin wannan kwanakin yakeso ya samu Hanan ya fad'a mata ,kawai miskilanci ne da zurfin ciki yasa ya kasa fad'a mata har yau .sai gashi Allah yaga zuciyar sa, kamar ruky ta San yana dakon soyayyar Hanan tai masa zab'i da ita...



___________?&


Hanan was speechless & shock da wannan batun da ruky tazo mata dashi,

Cikin sayin murya tace.

"No ruky, stop joking please,ko kad'an bazan tab'a yadda ba ,ni nasan ba Sona yake ba Kawai kece kika yanke hukuncin Hakan Dan bakyason kiyi AURE ki barni",ta fad'a tana girgiza kai.


Ruky itama girgiza kan tai ta kamo hannun Hanan kafin tace .

"Haba Hanan! yanzu kenan Baki yadda da duk magan ganun Dana fad'a miki ba",ta k'arasa fad'a cikin damuwa.


Hanan ta sauke numfashi kafin tace .

"Ni bawai yarda bane banyiba , Amma ruky Tayaya ya hanaf zai Aiko kizo ki fad'a min haka ,ni Gani nake ya hanaf ai yafi k'arfina.ta fad'a cikin damuwa

Ruky ta a gimtse dariyar tana kallan fuskar hanan yadda ta Sauya lokaci D'aya kafin ta harareta tace .

"A'a wallahi babu Wani fun k'arfinki da yay ,kawai kin Fad'i hakane dan bai zama dai dai da zab'in kiba shiyasa kika Fad'i haka",

Hanan ta girgiza kai kafin tace .

"Yanzu ruky ko nice naji Wani ya Fad'i haka bana masa kallan Wanda Bai San kyau da aji da komai da ya hanaf yake dashi ba,Wanda ko Wacce mace take fatan samun mijin AURE Irin Sa",

Ruky ta Sauke numfashi kafin tace .

"To indai hakane Dan Allah sis ki amshi soyayyar ya hanaf Wallahi Hanan Yana sonki tunda har kikaga ya ansa babu musu babu komai,kema kinsan halin ya hanaf idan Abu yayi masa ko a fuskarsa saika Gane haka ma idan Bai masa ba saika Gane bare Kuma yanzu da ake maganar matar AURE ,haba Hanan ai ko iya wannan ma Kya yarda da abinda na fad'a miki, bare ma kinsan ya hanaf mugun miskiline kema kinsani bayason magana ko kad'an shiyasa naga Kun dace ke surutu shi Kuma Miskili, Dan nasan tuni zaki chanza min Yaya ",ta k'arasa fad'a tana murmushi.


Hanan ta bugeta a cinyar tana hara rarta ,ruky ta kamo hannun ta tace .

"Please sisi Dan Allah Kice kin Amince, idan na koma na fad'a masa Dan wallahi Yanzu ma jiran amsarki kawai yake",ta fad'a cikin damuwa.


Hanan tace.

"ni wallahi ruky da kin bar maganar nan Kawai",

Ruky ta had'e Rai Kafin tace .


"Kawai fitowa zakiyi kice min ke bakyason Yaya na, sannan Kinga yadda mamah take murna da farin ciki kuwa",

Hanan ta zaro ido waje tace.

"Wai yanzu Mamah ma har ta sani?",

Ruky ta ce .

"Sosai ma, abunda a gaban ta ma akayi",

Hanan ta rufe Baki tana cewa ruky kin kashe ni innalillahi wainna ilaihi rajiun, yanzu tsakani da Allah haka zakimun", ta fad'a tana rufe fuskarta kamar mamah ce a gabanta.

Ruky tai murmushi, tace.

"Ni Dan Allah kiban ansa kin Amince ko yaya ?",ta fad'a tana kallan Hanan wacce taji gabad'aya ruky ta d'aureta da jijiyoyin jikinta.

Tai narai narai da fuska kafin ta gyad'a mata kai,ai da Wani Irin farin ciki takaiwa Hanan wata wawuyar runguma tana cewa .


"thank you k'awata nagode sosai Allah ubangiji ya nuna mana lokacin bikinku,amaryar ya hanaf" ta k'arasa fad'a da D'an k'arfi.


Hanan tai saurin rufe mata Baki tana nuna mata k'ofa akan tai shiru, ruky tace .

" Ke ba dole nai farin ciki ba",yanzu Kinga idan na koma gida zan koma da K'warin gwiwa ta",ta fad'a tana murmushi.

Hanan tace.


" Amma dai Kya bari na fad'awa ummah ko?,

Ruky tace .

"Nasan ma ummah bazata tab'a ki amincewa ba", Hanan ta rausayar da kai tana kallon ruky wacce bakin ta ya kasa rufuwa sai murna take .

Ruky ta kalli Hanan Ganin yadda Lokaci D'aya ta nutsu kamar ba Hanan ba wacce bakinta baya shiru indai tana waje, cikin tsokana tace .


"Yanaga kinyi Shiru Kuma",

Hanan tace.

"To mezance?",

Ruky tace .

"Dama Hanan akwai abinda zai saki nutsuwa lokaci D'aya haka?,

Hanan tace .

"Kamar ya?"

Ruky tace.


"Gani nai daga fad'a miki wannan maganar har kin Wani nutsu",


Hanan ta k'ara rau rau da fuska kafin tace .

" ba dole ba aure fa akace"

Ruky ta kwashe da dariya kafin tace .


" 'yar rainin hankali Ashe kema Dan Bai biyo ta kanki bane da har ranar kike min tsiyar wai nak'i sakin jikina lokacin da za'a kawo kud'in aurane , Amma ke gashi fad'a miki ma akai ba kawo kud'in ba Amma kika nutsu lokaci D'aya,to wannan Inaga ranar da za'a kawo kud'in Inaga jinya zakiyi harda gudawa", ta fad'a tana Dariya,Hanan ta D'aka mata duka acinyarta tana cewa "banaso ruky", ruky ta dafe wurin tana sakin ihu kad'an,haka dai ruky tasa Hanan agaba tai ta tsokanar Hanan a d'akin nan , da Hanan taga abin na ruky bana k'are bane tace ta fasa, ruky tace ai Bata isaba zancen farko shi ake Kamawa,haka ta cigaba da tsokanarta ,Hanan tai banza ta k'yaleta.....



Mamah ta Kalli ya hanaf Wanda ta k'ira shi zuwa d'akin ta tana kallan sa ,tace.

"To kaji yarinyar ta a mince Kuma munyi magana ma da mamanta d'azu, sukace duk sunyi farin ciki da haka Kuma sun amince,yanzu kashirya zuwa nan da kwana biyu akai kud'in AURE,sai a had'a Dana Tahir gabad'aya ayi tunda shiya ce kafin bikin Auta yake so ayi nasa", ta fad'a tana kallan ya hanaf.

Ya hanaf ya sauke numfashi kansa a K'asa yace.

"Mamah duk abinda kuka yanke yayi",

Mamah ta Jin jina kai kafin tace .


"Allah ya Maka albarka zaka iya tafiya", ya hanaf yay mata godiya ya Mik'e ya bar d'akin a hankali, mamah ta bishi da kallo tana Jin Wani farin ciki na ratsa ta ganin Amanar da aka Bata gabad'aya zata Aurar dasu nan Bada dad'ewa ba,ta d'aga hannu sama tana yiwa Allah godiya da Kuma ya nuna mata ranar.....




07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*




*____(MRS SARAKIES =؋?)____*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season one ep 9?? 3??




__________?&


*Bayan kwana biyu*


A yau dai za'a kai kud'in auran ya Tahir da ya hanaf zuwa gidajen 'yan matan da zasu aura,masu kaiwa kud'in auran biyu suka Rabu wasu suka tafi kai na ya Tahir zuwa kano wasu Kuma suka tafi gidansu Hanan,fuskar ruky ta kasa b'oye farin cikin da take ciki a wannan Rana, Ganin yau dai za'a kai kud'in auran ya hanaf gidansu Hanan, wuni tai cikin farin ciki,bata k'ara samun nutsuwa ba Saida taga antafi gidan ,take ta saki ajiyar zuciya tana maijin Wani Irin farin ciki na ratsa har cikin zuciyar ta Dan Allah ya Gani tanayiwa Hanan kwad'ayin samun mijin AURE Irin yayanta,bawai Dan ya kasance yayan taba, a'a saidan ya kasance Irin mijin da ko Wacce mace zatai patan samu ne a matsayin Mijin AURE.


Da daddare wajen k'arfe 8:30pm tana cikin d'akin kwance akan gado tai darling number Hanan,Saida tai mata miss call har biyu ana ukun ne tai picking cikin sanyin murya taiwa ruky sallama, ruky ta saki dariyar shak'iyanci kafin tace .

"Matar yayan! yanzu ke Kuma shikenan ko ki k'irani kice min ankai kud'in AURE da Kuma an Tsayar da Rana ko?".ta fad'a tana dariya.


Hanan ta Sauke numfashi ganin idan ta K'yale Ruky ta samu lagonta kenan taga alamar shirun da take matane yasa take mata duk abinda taga dama yanzu yasa tace cikin dauriya,

"ke! wai ke yanzu Baki San babu wasa a tsakanin muba ne, tunda zan zama yayarki soon" ta fad'a tana murmushi k'asa k'asa.


Ruky ta rik'e baki kafin tace cikin mamaki .


"eh lallai bakinki Bai mutu ba yarinyar nan,ke yanzu ko kunyar fad'ar wannan maganar ma bakiyi ba ,har Kin Isa kizama Yaya ta?,

Hanan tai murmushi tace .

"Ai wallahi kema kinsan har nafi haka",

Ruky tace .

"Wallahi Baki isa ba yarinya Kina nan a matsayin da kike awajena haryanzu",


Hanan tace .

"Kisa aranki kinsan Allah tunda har soon zan zama matar yayanki Kuma dole kimin biyay, sannan Kuma ki k'irani da anty", ta fad'a tana gimtse dariyar ta .

Ruky tace .


"Wallahi kema kinsan Baki isa ba",


Hanan tai murmushi tace.


"Oh haka kika ce?,to shikenan bari ki Gani a d'aura AURAN zakice na fad'a miki",.

Ruky ta rik'e baki cikin mamakin Hanan tace .


"Na shiga uku Hanan wallahi Allah kinfi k'arfina ke yanzu ko kunyata bakyaji kike fad'ar Irin wannan maganar a gabana",

Hanan tace .

"Yanzu ke har kina tunanin akwai ranar da zanji kunyarki ne right ruky!?,to wallahi garama ki cire wannan aranki",

Ruky tace .


"Ai ko Baki fad'a ba dole na cire",ta fad'a tana dariya.

Hanan tace.

"Ke na manta ban fad'a miki ba, Kuma Ina taso na fad'a miki, d'azu Ameer fa ya k'irani",ta fad'a tana sauraran taji me ruky zata ce.


Ruky taja tsaki kafin tace .

"Dan Allah kark'i Kayra kawomin maganar Wani Ameer",ta fad'a cikin Jin haushin maganar da Hanan tai mata.


Hanan tai murmushi tace .

"Ai Baki tsayama kinji Mai zan fad'a miki ba kike wannan kumfar bakin haka,batajira ruky tai magana ba ta cigaba tace.


"Cewa yayi Wai Dan Allah na tai Maka masa na shawo masa kanki ,Niko nace ai yanzu ruky ma ansaka mata ranar AURE, sai dai kayi hak'uri,cikin damuwa yace da Gaske kike Hanan?,nace masa eh da Gaske nake.ai wallahi Ruky tunda ya saki Wani salati bai K'ara magana awayar nan ba,da naji yay shiru yasa nai tai masa magana Amma Bai ansa ba kuma Bai kashe wayar ba sai ni na hak'ura na kashe wayata ,wallahi na Dad'e Ina sak'awa araina cewa Allah yasa ba Wani Abu ne ya sameshi ba, lallai ruky Ameer ba k'aramin so yake Miki ba , wallahi gabad'aya saiya ban tausayi",ta fad'a cikin damuwa itama.


Ruky ta sauke numfashi kafin tace .

"To naji,Allah ya bashi wacce tafini",ta fad'a cikin k'osawa da maganar.


Hanan tai murmushi tace .

"Ameen dai Nima haka nace ",

Ruky ta kawar da zancen wajen cewa .

"Sis ansaka Rana koh? Wallahi bakiji dad'in da naji ba",ta fad'a har a cikin zuciyarta.


Hanan tace .

"Uhmm"

Ruky tai murmushi tace

"Zakiga uhmm,Nanda wata D'aya da sati biyu ne ko?, batajira cewar Hanan ba tace.


"yanzu kuma sai mu fara shirye shiryen abubuwan da zamuyi koh fitar da ashobe da sauran abinda ya kamata", ta fad'a tsakanin ta Allah Dan ita yanzu Bata bikinta take ba ta bikin yayunta take da Kuma k'awarta.


Hanan tace .

"Tundaga yanzu uwar zumud'i ",


Ruky tai dayiya tace .

"Ke ba dole nai zumud'i ba ,bikin manyan yayuna sannan Kuma bikin k'awata ai ko me nai karma kiga laifina,me ma zamu jira da baza mu fara shirye shiryen mu yanzu ba?",

Hanan ta sauke numfashi tace.

"Uhmm", Amma batai magana ba.


Ruky tace.


"Wake sai kiyi ta cewa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login