Showing 240001 words to 243000 words out of 278032 words

Chapter 81 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1061

ido yanajin Wani Abu na fusgarsa aduniyar Santa ya Busa mata numfashin sa Asaman fuskarta yace cikin shak'akk'iyar murya.

" I love u fiancee!",ya fada idawansa na rikid'ewa daga farare zuwa jaaa,ruky ta gyad'a masa kai kafin tai saurin k'wace jikin tana matsawa baya tana kasa had'a ido dashi k'irjinta na bugawa da k'arfi...


Ganin yanayin Data shiga yasa ya sauke numfashi Yana dai dai ta kansa,they take time like five minutes haka Kuma duk cikinsu babu Wanda yace komai ,Saida ya bari Ruky ta D'an samu nutsuwa Yana kallan ta yace.


" let's go", ya fad'a yana yin Hanyar k'ofar fita,sai Alokacin ruky ta d'ago da kanta tabisa da kallo tana dafe k'irjita harya fita kafin tabi bayansa.


Yana zaune a driver seat Yana kallan ta da rinan nun idanuwan sa da basu dawo dai dai ba har lokacin yay k'asa da murya yace cikin shak'akk'iyar muryarsa.

"Thanks alot fiancee!, good night & sweet dreams",ya fad'a Yana kashe mata ido tare da murmushi,

Duk'ar da kanta tai k'asa tana Jin jina masa kai alamar ansawa kafin ya K'ara sauke numfashi Yana kallan ta yace

" I love u more princess!", ya fad'a cikin k'asa da murya,Yana Wani kashe mata ido kamar tana kallan sa , nan ma batai magana ba illa gyad'a masa kan datai ya fara k'ok'arin tada motar ganin tana k'ok'arin susu tashi,ta juya ta bar wajen ya bita da kallo kafin yaja motar yayi hanyar gate Dan fita daga gidan jiki ba k'wari .......






07966508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y







*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 9?? 5?? ??



___________?&


*Bayan sati D'aya*



Da yay dai dai da saura Kwana ki bakwai bikin su ya Tahir, gida ya fara haramar d'aukar Bak'i Dan har anty mufeeda tazo yau ita da iyalanta , ruky ta tafi gidan su Hanan tun bayan data dawo daga Aiki sakamakon K'iranta da tai akan abubuwan da basu k'arasa ba ,gashi za'a fara event nan da Kwana ki hud'u masu zuwa.tana zaune acikin d'akin Hanan akan gado Hanan Kuma tana Bakin gadon Tasha gyara Irin na Amare in Banda glowing babu abinda take Yi gabad'aya jikinta Wani sihirtaccen kamamshine kawai yake tashi acikin jikinta, ruky ta d'ago daga Kallan tsaddan rigar da yake hannun ta Wanda Hanan zata Saka a cocktail party da zasuyi da Kuma dinner tana kallanta with expression tace.


"Ke wallahi d'in kin nan yayi bala'in kyau harna hangoki a ciki yadda zaki baza capacity",ta fad'a tana murmushi.


Hanan itama murmushin tai Amma batace komai ba ,kafin ta kau da zancen da cewa "ai baza capacity sai ke amaryar Yaya Ahamad"ta fad'a tana dariya.


ruky ta harareta kafin tace .


"Hmmm ni wallahi har far gaba nake Hanan gabad'aya mutumin nan baida kunya idan muna tare sai kiga ya furgicemin lokaci D'aya", ta fad'a tana tura Baki gaba .


Hanan ta Bud'e ido cikin mamakin zancen Ruky tana murmushi kafin tace bangane bashida kunya Kuma Yana firgice miki ba?,bani labari", ta fad'a tana gyara zama.


Ruky Ta shagwab'e fuska kafin tace.


Kinga wasu abubuwa kuwa da nake hangowa a fuskarsa",ta fada kamar zatai kuka.

Hanan ta k'yalk'yale da Dariya kafin tace .


"Ke Dan Allah?,ai daga ganin yadda yake rawar k'afar nan akanki wallahi ni nasan bazai tab'a daga miki k'afa ba yarinya, inma zaki kwantar da hankalinki wallahi gara ki kwantar Dan wannan daga ganinsa bazai sassauciba taba"ta fad'a tana K'ara sakin wata dariyar ganin yadda Ruky ta zaro ido waje tana kallan Hanan atsorace .kafin Kuma ta tab'e Baki tace .


"Dan Allah a Bar zancen kawai",ta fad'a cikin Jin haushi.


Hanan ta D'aka mata duka a cinyar ta tace .


"Zakiga Abar zancen yarinya,indai yaya Ahmad ne wallahi Allah saikin Gane kuranki a hannunsa", ta fad'a tana K'ara sakin wata dariyar, ruky ta tsuke fuska kafin tace.


" banasan Irin wannan Hanan", ta fad'a tana harararta ,


Hanan ta Bud'e ido kafin tace.


"Au Ashe babu Dad'i ni Kuma kike min",ta fad'a tana hararar ruky.


Ruky tace .

"Amma aini ban tab'a miki Irin wannan wasan ba ai koh?",ta fad'a tana tsareta da ido.


Hanan tace.

"Ai idan kasan abinda zaka fad'a kaima bakasan me za'a Maida Maka ba",.

Ruky tai shiru bata k'ara magana ba ganin Hanan tana k'ok'arin tsorata ta ,daga k'arshe ma kwanciya tai akan gadon tana juyawa Hanan baya tana tunanin maganar ta,itako Hanan tab'e Baki tai ta mik'e ta bar mata d'akin sakamakon K'iranta da akai daga falo.



Yau laraba ya kasance za'a fara event .yau cocktail party za'a Yi gobe Kuma Al'hamis ya kama za'a Yi dinner Friday Kuma d'aurin AURE.


Can na hango ruky ta fito daga wata bak'ar mota k'irarr land Prosser,sanye take cikin Wani blue black d'in yadi Wanda in banda walwali da kawo wutar haske babu abinda dayake, da yake dare ne misalin karfe 8:30pm,bayan ta fito daga cikin motar ta tsaya tana kallan motocin da suke ta parking a gefen Wani tafkeken hole Wanda da dukan alamu awurin za'a Yi parting,naga ta kamo hannun aminiyar tata tana tai Maka mata Dan ganin ta fito daga cikin motar itama ,ya ilaihi na ambata araina wato duk inda amarya take tafita daban da sauran mata,dayake patyn iya na 'Yan matane suka had'a abinsu Banda Maza bare Kuma iyaye,dan daga su sai zugar k'awayensu 'Yan makarantar su da Kuma abokanan aikinsu,bayan Hanan ta fito Hannun ta rik'e dana ruky naga ta tsaya kusa da ita suna magana da ruky k'asa k'asa banji Mai suke fad'a ba kafin naga wasu k'awayensu sun k'araso wurinsu cikin shiga Iri D'aya ko Wacce Tasha d'inkin yadin da sukai ankonsa Mai kalar royal blue , cikin shiga ta Alfarma,suma inbanda walwali babu abinda suke da tashin k'amshi.


Dayake abakin hole d'in motar tai parking yasa k'awayen suka hau layi Wanda yasa suka Rabu biyu ya zamto amarya da aminiyarta wato Rukayya suke a tsakiyar su, cikin k'an k'anin lokaci suka shirya kansu kafin naga photographers sun fara d'aukar hotuna ta ko Ina ana Kuma video at the same time suka fara shiga cikin hole d'in a nutse,bayan sun shiga hole d'in ya ilahi nanma wato wata duniyar ce, Dan decorations akayi na balooms da flowers wuri dai yayi kyau iyasa hasashen Mai tunani, amarya ta zauna awurin da aka tana da domin zaman ta ruky kuma tana gefenta daga b'angaren dama ,Nan suka fara gabatar da patynsu cikin kwanciyar hankali dayake gabad'aya 'Yan mata ne babu Yara yasa sukai abinsu cikin nutsuwa Babu hayaniya bare Kuma tashin hankali,sai wajen k'arfe goma suka tashi ,Saida ruky ma suka fara Sauke Hanan agidan su sannan ita Kuma aka wuce da ita gida tare da wata cousin sister d'inta.


Washe gari ya kama alhamis za'ayi dinner kenan, a Wani k'aton hole Dake garin Kaduna ,Wanda anan ne za'a Yi dinner, gabad'aya 'yan uwa da abokan arzik'i sun cika hole d'in mak'il da mutane,wasu daga cikin 'yan uwan su mamah sun wuce can kano wurin na ya Tahir tunda shi amaryar tasa 'yar can ce,Kuma shima sai yau ya tafi.


Su ruky kuwa ai su 'yan Kaduna ne,tun K'arfe 9 na dare suka iso cikin wurin dayake yau abin na kowa da kowane dan har da angon kansa Wanda tare suka zo ma da amaryar tasa cikin mota d'aya,sai baza kamshi suke ta ko Ina ,dayake yau ba mota d'aya suka hau da ruky ba yasa Basu zauna waje D'aya ba, ita Ruky awata mota suka zo ita da anty mufeeda da 'ya'yan Hajiya Maryam wato maman Shareef kenan ,Kuma su duka yayun shareef ne,tana gaban motar ta fito daga motar bayan anyi parking,ta iso motar su Hanan Wanda take ciki,can na hango amaryar cikin Wani coffee d'in color d'in material Wanda ya Yayi mata bala'in kyau inbanda k'amshi babu abinda ke tashi ajikinta, tayi kyauta harta gaji,shima angon sanye yake cikin Wani yadi Mai taushi ta tsada Wanda sai d'aukar ido yake shima kalar coffe color ne Wanda yaji D'inkin zamani yazamto sunyi anko kenan shida amarya ruky ta kama handle d'in motar kenan zata Bud'e ya hanaf ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu,ta Tsaya saroro tana kallansa da mamaki.


Har Abokanan angon Suma suka k'araso wajen hakan yasa ya Bud'e murfin motar ya fita Yana zagayowa ta site d'in Hanan ya Bud'e mata Yana mata murmushinsa Mai tsada keda kin Gani kinsan Yana cikin farin ciki marar misaltuwa kuwa wannan angon,cikin Jin kunya Hanan ta kalleshi kafin ta Maida masa da Martanin murmushin sa tana K'ara duk'ar da kanta k'asa.ita dai ruky tana tsaye tana kallan wannan soyayya da ake a gaban ta ko kunyar ta ba sa ji ,da kansa ya kamo hannun ta ya tai Maka mata ta fito daga cikin motar cikin nutsuwa, Saida ta fito Sannan suka jire suka fara tafiya zuwa bakin hole d'in Wanda k'awayen amarya dana angon suna tsaye suna jiransu su karaso dan su shiga tare.


Bayan sun shiga cikin hole d'in mutane ne ta ko Ina mak'il awurin zamansu, photographers suka bisu suna d'aukar hotunansu da video ,har suka k'araso wurin zamansu hannunsu sark'e cikin na juna hotuna kawai ake tai musu ta ko ina.bayan ango da amarya sun zauna ,Suma abokan angon dana amarya duk suka koma wurin zamansu inda already aka tana da musu suka zauna,cikin k'an k'anin lokaci aka aka fara gudanar da dinner cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.


Kusan mintuna 40 da fara events d'in,wayar Ruky ta fara vibrate alamar k'ira,Koda ta duba ta ga Mai K'iran take murmushi ya bayyana a saman kyakkyawar fuskarta wacce tasha simple make up da ya K'ara fitowa da ainihin kyanta fuskarta, sai Kuma tai saurin tsuke fuska cikin shagwab'ar data zame mata jiki tai picking takai kunne,bayan wasu seconds ta sauke wayar ta mik'e ta silale ta fita daga cikin hole d'in gabad'aya.


Tana fita ta fara waige waigen inda zata hango motar tashi,ganin wata mota ta kawo haske daga can gefen hole d'in yasa ta sauke ajiyar zuciya ta fara takawa zuwa wajen motar cikin tafiya ta Jan hankali.


Shiko AA Arab tunda ta fito ya zuba mata ido Yana kallan ta daga sama har k'asa ,ba k'aramin kyau yaga yau ta k'ara masa ba na musamman ,duba da yanayin shigar da tai sanye take cikin Wani ash color d'in material,sai walwali yakeyi saboda Wani tartsatsin haske da yake kawowa ta ko Ina, D'inkin doguwar riga fitted gown,tasha d'auri Irin na zamani kamar itace amaryar,ga takalmin k'afar highheel ne sai Wani taku take na Jan hankali, Amma ita naturally haka take tafiyar ta.


Yana wannan tunanin baisan ma ta k'araso wurin ba sai ganin ta yayi ta duk'o da kanta saitin inda yake tana kallan sa a shagwab'e tace.


" shine baka zo tun dazu ba sai yanzu", ta fad'a tana tura Baki gaba.


Ya ilahi ya ambata a ransa kafin ya lumshe ido Yana bud'ewa lokaci D'aya ya zuba mata su Yana kallan ta,ruky ta matsa baya da sauri ganin Irin kallon da yake mata tana duk'ar da kanta k'asa kafin ya sauke numfashi Yana kallan ta da rinan nun idanuwan sa yay k'asa da murya yace .


"Come in side please, kin tsaya cikin wannan shigar kowa Yana kallan ki ya fad'a da alamar Jin haushi.


Ai Batasan lokacin da d'ago da kanta tana kallan sa b ,ganin Irin kallon da yake mata yasa tai murmushi ganin yadda yay da fuska ta zagaya D'aya site d'in bayan ya Bud'e mata ta shiga ta rufo kofar ta mak'ale karshen motar kamar Wanda zai kama ta tana kallan sa tace cikin k'asa da murya.


"Sannu da zuwa",ta fad'a tana kallan sa ganin yadda yay mata kyau shima,da akai Sa'a shima ash color d'in shadda ce ajikinsa yasa sukai anko sumar kansa Tasha gyara sai shek'i take.


Ya lumshe ido kafin ya ansa mata har lokacin idonsa Yana kanta,sai Kuma ya juyo gabad'ayansa Yana fuskantar ta kafin yay k'asa da murya yace.

"U look very beautiful & attractive fiancee!"ya fad'a da wata iriyar murya Yana Kuma Kallan ta.

Tana murmushi itama tace .

"U look very handsome Dee" ta fad'a tana rufe fuskarta da tafukan Hannunta.

Ya D'an Bud'e ido kafin yace .


"Bantab'a Jin kince nayi kyau ba sai yau , thanks alot fiancee & I love u so much"ya fad'a Yana murmushi.

Ruky ta Bud'e fuskarta tana kallan sa kafin tace .

"Ai ko ban fad'a ba ni nasan kai handsome ne acikin Maza wanda sai an Tona kafin asamu Irin ka",ta fad'a tana masa Wani kallo Mai ratsa zuciya.


AA Arab ya Wani zuba mata mayun idanuwan sa Yana kallan ta kafin ya matso kusa da ita Yana kallan ta ido cikin ido yace cikin kasa lalliyar murya.


"I thanks to almighty God Daya bani mace D'aya tamkar da dubu shiyasa a kullum Banda soyayyar ki Babu abinda yake k'aruwa acikin zuciyata,Ina sonki kuma Ina k'aunarki inaso ki zamto uwar 'ya'yana har a aljannah in Sha Allah", ya fada Yana Wani kashe mata ido D'aya.


Ruky tai murmushi tana sunkuyar da kanta k'asa , Amma batace komai ba tana murza Hannun ta Wanda yasha lalle jaaa da Bak'i ,sai d'aukar ido yake.


Ya k'urawa hannun nata Ido kafin ya kamo Yana kallan k'unshin itama kallon nasa tai atsorace ganin ya kamo hannun ta take ta fara tunowa da abinda ya faru ranar ta fara k'ok'arin kwace hannun nata,ya d'ago yana kallan ta da idanuwan sa Wanda suka kad'a lokaci D'aya cikin shak'akk'iyar muryarsa yace .


"Please fiancee! kar k'wace babu abinda zan miki Gani kawai Zanyi",ya fad'a Yana kallan ta ,take ta d'auke kanta k'irjinta na bugawa da k'arfi tana Jin kamar ta k'wace hannun nata Amma kuma gabad'aya sai taji ta kasa Hakan ,ya fara murza mata Yana kallan ta yace.

"yayi min kyau sosai I like your structure", ya fad'a Yana K'ara murza mata hannun tare da Yi mata Wani narkekken kallo ,ganin yana k'ok'arin wuce Gona da iri yasa tai k'asa da murya cikin nutsuwa tana kallan sa tace.


" please Dee ka bari"ta fad'a tana k'ok'arin k'wace Hannun na ta ,take ya saki hannun nata yana kallan ta ganin Yana k'ok'arin barin nutsuwar ya zuba mata ido Yana kallan ta yana kuma Sauke numfashi,ta sunkuyar da kanta k'asa ta matsa ta takure jikin murfin motar tana b'oye hannun nata kamar Wanda yace zai K'ara kamowa yay k'asa da murya yana kallan yace.


" I like this henna fiancee!",

ruky tai shiru batai magana ba,har lokacin gabanta Bai daina fad'uwa ba,yay shiru shima baiyi magana ba Yana kallan ta,motar tayi shiru for more than 1O minutes kowa da abinda yake sak'awa aransa kafin ya d'ago Yana kallan ta ya sauke numfashi ya katse shirun da cewa.


" Ya hidimar biki?", ya fad'a Yana kallan ta .

Bata d'ago da kanta ba Tace" Alhamdulillah",.

Yace. "muma nan da two weeks in Sha Allah iyanzu namu akeyi koh?".ya fad'a Yana kallan ta.


Ta k'ara sunkuyar da kanta k'asa nanma batai magana ba,

Yace. "Say something please, banason naga kina shiru idan muna magana",


Ta d'ago da Dara daran idanuwanta tana kallan sa a shagwab'e tai k'asa da murya tace .


"Me zance?",ta fad'a tana kallan sa.


Ya k'urawa Dan k'aramin bakinta ido dayay maganar yana Jin Wani Abu na fusgarsa zuwa gareta kawai sai yay saurin kawar da zancen ta hanyar cewa.


"ya kamata Nima dai yau na shiga ciki na gaisa da ango da amarya kafin na tafi koh?",ya fad'a Yana kallan ta.


Ta d'ago ta kalleshi ta gyad'a masa kai,

yace .

"Ok bari muje yanzu",

Tace."to", ya Bud'e motar ya sauko ya zagaya ya Bud'e mata Yana mata Wani kallo ta kauda kanta kafin ta fito tana cewa

"Thanks", Asaman lab'b'anta,Bai yi magana ba Suka jere suka shiga har cikin hole d'in keda kin gansu kinsan sun dace da juna.

Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y








*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 9?? 5??



____________?&


Washe gari Friday ya kama ranar d'aurin AURE,tunda garin Allah ya waye Jama'a na nesa Dana kusa suka fara zuwa garin Kaduna domin halartar d'aurin AUREN,dayake daurin AUREN K'arfe 11:30am ne na safe ,tuni tun wajen k'arfe goma da mintuna wadanda zasu tafi kano suka fara hanarmar tafiya,abokan aikin ya Tahir Wanda ba'a garin suke ba dama Wanda sukai school dasu tare duk sunzo dama kuma tacan zasu wuce baza su zo Kaduna ba ,sai idan zasu dawo su dawo da amarya tare , wad'anda Kuma na ya Hanaf zasuje da abokansa da komai duk suna nan garin Kaduna suna tare da ango a Wani extra gida Wanda Saboda su sake yasa suka zauna acikinsa ,dayake duk d'aurin auran lokaci D'aya ne Dana ya Tahir.



K'arfe 11:30am dai dai aka d'aura da
Duka AURAN, A b'angaren su ya hanaf daga wurin d'aurin a direct gidansu amarya suka wuce Dan zuwa gaida iyayen amarya.ya hanaf na hango cikin wata dakakkiyar shadda blue black wacce tai masa bala'in kyau ,aka Bud'e masa mota ya fito suka Shiga gidansu Hanan...


Gida ya cika mak'il da 'yan uwa da abokan arzik'i na kusa Dana nesa .ruky ma tana cikin gidan wajen aminiyarta tana tayata zama tunda itace babbar K'awa kuma k'anwar anago ,bayan angwaye Sunyi gaisuwar iyaye ,can na hango ruky ta fito daga Wani falor Hannun ta rik'e cikin na Hanan wacce take cikin Wani blue black d'in yadi D'inkin doguwar riga, fuskarta Tasha simple make,ba k'aramin kyau tai ba.


Ruky ta tsayar da ita kusa da ango Wanda inbanda annuri babu abinda yake fita a saman fuskarsa,akayi hotuna da videos kafin su tafi,idan Allah ya kaimu bayan magrib Kuma Azo d'aukar amarya...




A nan kano kuwa dai da yake da amarya zasu tafi da aka d'aura AURE basu zo gidan su amarya ba,hotel suka tafi inda can ne sukai lugging room's suka zauna Dan su huta kafin lokacin tafiya da amarya yayi su je su d'auko ta daga nan Kuma sai wuce Kaduna ,yan zunma wajen k'arfe uku na Rana ya Tahir na hango cikin wata dakakkiyar shadda fara k'al da ita sai tashin k'amshi yake acikinta ,ga abokanansa na wajen aiki da Wad'anda sukai school tare dasu duk sun masa Kara sunzo,suna tare a gidansu amarya bayan sunyi hotona suka fito k'ofar gidan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login