Showing 204001 words to 207000 words out of 278032 words

Chapter 69 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1067

iya sawa yay abun kunya ya ce cikin qaguwa "Ina ruwana " nidai kituramin yanxu idan ba hakaba wlh sai ranki ya B'aci"daga haka ya kashe wayar, Yana sauke numfashi kamar Wanda yay gudun tsere,ruky ta sauke wayar tabi ta da kallo tana hararar wayar ,Jin abinda ya fad'a mata...




Ruky ta tura Baki gaba ta mik'e Dak'yar ta d'auko laptop din ta Dake kan side drawer Dan tunda ta gama anan ta ajiyeta,ta Bud'e ta sannan ta shiga ta fara tura Mai tana gamawa ta rufe to koma ta kwanta .AA Arab ko yana nan xaune Yana tunanun abinda yaji da yaji muryar ruky gabad'aya yaji hankalinsa ya tashi,Yana nan xaune Yana jiran ta ta turo masa, ganin ta turo masa yasa ya Bud'e ya fara aikin Amma gabadaya abinda da yake ji ya fara fin karfinsa da k'yar ya qarasa, sannan ya rufe ya mike da ya shiga toilet yana fitowa ya kwanta akan gadon yay tufda ciki Yana Jin Wani iri,sai dai har yanxu muryar ta kasa barin k'wak'walwarsa take ya rintse ido ko zaiji ya daina ji , Amma sai ya ji kamar yanxu yake Jin muryar tata,Haka nan ya runtse ido yana mamakin meke shirin faruwa da shine wai shi Ahmad......



Niko nace Ahmad Aliyu Arab A.k.A(AA Arab)>?#?>?#?......


"Fan" mutumin fa ya fara shiga >???...nayi nan >?#?









07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*___JAMI'AR TSARO ___*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*('TAURARI WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM THE 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?wo ep 8?? 1??



____________?&


Baaba asabe da taga sun kusa xuwa gida,sbd bataso kowa ya fahimci halin da suke ciki ta goge hawayen Daya k'i tsaya mata a fuskarta,tana kallan malam Auwalu da shak'akk'iyar murya ta ce "Malam Dan Allah karka fad'awa kowa wannan abin da ya farun"ta fad'a kamar zatai kuka,malam Auwalu ya juyo Yana kallan ta ya ce "hmmm asabe kenen aishi abun duniya baya tab'a b'uya,kinsan kina Jin kunyar mutanen kika bar ' yarki ta lalace?nasan wa kike gudu karyaji abinda zaliha ta aikata,idan ma ban fad'awa kowa ba kinsan shi ciki D'an duma ne duk mun daran dad'ewa zai fito koh? sbd haka idan kika K'ara yimin magana wlh asabe zan ci miki mutunci"daga haka ya juya Yana rintse idonsa Wanda ya kad'a yay jajur sbd b'acin Rai, baba asabe ta juyar da kanta gefe tana Mai danne kukan Dake San kufce mata, lallai zaliha ta jawo mata abin kunya ita ko meta aikata haka da wannan k'addarorin ke xuwa mata D'aya bayan D'aya haka, Bata fita daga wannan ba wata ma ta qara shigowa.ita dai zaliha ta takure waje D'aya sai ajiyar xuciyar kuka take saukewa ta kasa yarda wai cikin haihuwa ne ajikin ta.har suka isa gida Babu Wanda ya qara magana acikin su, kowa da tunanin da yakeyi, bayan sun sauka malam Auwalu ya bawa Mai napep d'in kud'insa sannan ya shige cikin gidan jikinsa na rawa kamar me,Yabar Baba asabe Da zaliha,itama Baba asabe gaba tai ta kasa jurewa Dan haka batama jira zaliha ba tai gaba abinta tana Mai danne abinda takeji aranta,jiki ba k'wari itama zaliha ta biyo bayan baba asabe tana Jin kunyar duniya ta taru akanta ......



Malam Auwalu Yana shiga gidan direct d'akinsa ya shige ya rufo k'ofar ya kwanta kan katifar sa Yana sauke numfashi,kan kice me zazzab'i me zafi ya rufe shi,ya runtse idonsa yana anbaton sunan Allah,sai ga hawaye shar shar kamar Wani qaramin yaro sbd wlh Allah ya Gani bai tab'a tunanin akwai wannan k'addarar cikin rayuwarsa ba,Dan abin yazo masa abaxata , shikuma asabe itace kaddararsa,baisan Wani Irin hukunci ya kamata ya yanke mata ba,ga k'arin bak'in cikin ya'yan natama ansako su suka su biyun,iya bilkisu ce kawai take d'akin mijinta, Amma gabad'aya su biyun anasako su ,suna zaune Rid'a Rid'a dasu agida, Batasan wannan bak'in cikin ma Yana ransa ba,shina itama zaliha Tayo cikin shege,Kuma yasan duk baba asabe ita ta jawo komai ,tunda da Bata nunuwa zaliha hanyar San kud'i da Kula samari ba da batayo cikin nan ba,take ya dafe kansa ya na ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun kawai yake Mai Mai tawa, asabe ta cuce shi ta zalince shi ta wahalar dashi ,ko Kuma ma ya ce tana kan wahalar dashi d'in,shiko Mai zai mata ya huce wannan Bak'in cikin data cusa masa, gabad'aya ilahirin jikinsa kar karwa ya d'auka,ya Dad'e ahaka,baisan tsawan lokacin Daya d'auka ahaka ba,baisan ma bacci ya d'auke Shiba,Saida ya ji K'iran sallahn farko na ASuba sannan ya tashi Dak'yar Yana Jin kansa na masa ciwo kamar me,ga zazzab'in har yanxu baisa sakeshi ba da bin bango ya tashi ya fito tsakar gidan Dan xuwa bayi.....



A bangaren su baba asabe kuwa , tana shiga falon ta, direct d'akinta ta shige batama bi ta kan su lawisa ba Dake musu sannu da xuwa ba, ganin batai musu magana ba harta shige d'akin ta yasa suka gane lallai ba lafiya,suka bita da kallo,sai kuma suka Maida Kallan su kan zaliha wacce ta shigo yanzu kanta a k'asa ta zauna afalon ganin suna kallan ta yasa ta mik'e ta shige cikin d'akin jiki a Sanyaye, mardiya da bakin ta baya shiru ta ce "sannu zaliha Kun dawo? me akace Yana damun ki? Duk ta jera Mata wannan tambayar, zaliha itadai Bata kula taba har ta shige cikin d'akin,ta tarar baba asabe tana zaune bakin gado tana share hawayen dayak'i tsaya mata, zaliha ta Tsaya daga bakin k'ofar dak'in ta kasa shiga ciki sbd Irin kallon da taga Baba asabe tana yi mata, Baba asabe kallan ta kawai take tana Jin zuciyar ta na Neman Yin binduga sbd Abun ne yazo mata a yadda batai zatoba ,wai zaliha da ciki, cikin ma na shege ,yanzu 'yar data d'auki so da burin duniya ta d'orawa shine ta janyo mata wannan abun kunyar,take ta mik'e daga inda take zaune xuciya ta d'ebeta tayo kan zaliha batai wata wata ba ta shak'o ta juyowa ta xuwa cikin d'akin tana kallon zaliha ido war waje cikin wata iriyar murya wacce Zaliha Bata tab'a ganin baba asabe tayi taba ta ce "uban waye yay miki wannan shegen cikin zaliha?ta fad'a tana qara shake wuyan zaliha.....



Zaliha da taji shak'a wacce ta kusan tafiya da numfashinta tasa kuka Dak'yar sbd yadda numfashin ta ke barazanar barin jikinta ta ce "Babar mu, wlh Nima bansaniba" Baba asabe ta qara shakota ta na zaro ido waje ta ce"baxa ki fad'amin ba saina sumar Dake a d'akin nan? Ta fad'a tana qara dank'e wuyan zaliha, zaliha ta fara k'ak'ari tana girgixa kai,baba asabe ta ce "wlh Zaliha idan Baki fad'a min Wanda yay miki wannan shegen cikin ba ,wlh kashe ki Zanyi na bunne ki Babu Wanda ya sani"zaliha tana girgixa kai ta ce"da GSK nake Babar mu wlh bansan Wanda yamin ba"Baba asabe ta kwantar tar ta a k'asa,tana k'ok'arin hawa kan ruwan cikin zaliha,ganin haka yasa zaliha ta sa ihu, mardiya da lawisa suka shigo d'akin da gudu Jin hayaniya yasa suka shigo ganin abinda ke faruwa baba asabe tana k'ok'arin hawa ruwan cikin zaliha yasa suka rik'e ta suna cewa "lpy babarmu me ya faru? Baba asabe tana huci ta ce "ku k'yaleni yau dai na kashe yarinyar nan Ko na huta da wannan Bak'in cikin da nake ciki"ta fad'a tana k'ok'arin D'ora k'afar ta kan ruwan cikin zaliha, zaliha ta rik'e kafar tana sakin Wani Irin kuka,tana rok'ar baba asabe tayi hakuri zata fad'a mata, lawisa data kasa fahimtar meke furuwa ta ce "wai meya faru ne babarmu duk kunyi shiru? Ta fad'a tana jiran su Bata ansa,Baba asabe ta sa Kuka ta ce "wannan yarinyar da kike gani abin kunya ta jawomin ashe wannan jinyar da take ba komai bane Ashe ciki ne da ita"ta fadya tana K'ara sautin Kukan ta,.....



Mardiya tasa ihun salati tana sakin baba asabe jikinta na sanyi tana dafe k'irji ta ce "ciki Kuma babarmu? baba asabe ta ce tana kallan zaliha wacce ta takure waje D'aya "wlh baza ki tab'a jawomin zagi da cin mutuncin ci awurin mak'iyana ba, ko ki fad'amin Wanda yay mike wannan shegen cikin ko Kuma na kashe ki na huta"ta fad'a tana K'ara yowa kan zaliha, zaliha ta sa ihu tana matsawa baya ta ce "zan fad'a, zan fad'a babarmu Dan Allah karki kashe ni"baba asabe tana huci ta ce "to ki fad'a min Ina jinki" zaliha ta ce" Alhaji tanko ne"ta fad'a tana rushewa da Kuka,take lawisa tasa salati,ita ko baba asabe tama kasa tuno waye Alhaji tankon da zaliha ta fad'a bare har ta gano shi, sai da taji mardiya na cewa kardai wannan tsohon saurayin naki,da jiki duk jijiya? Zaliha ita dai tai shiru tana rere kuka, lawisa ta karb'e da cewa badai Wanda ke kawo mana tsire da daddare kullum ba? mardiya ta ce "yo idan ba Shiba waye?shidai" lawisa ta ce "innalillahi wainna ilaihi rajiun,ke yanxu zaliha me zaki samu jikin wannan tsohon da har kika bashi kanki, innalillahi wainna ilaihi rajiun,dama D'an iska ne tsohon banza Bamu saniba? madiya ta ce "Sosai ma, wlh ni nama rasa me zance sbd takai ci"sai alokacin baba asabe tai magana ta na kallan zaliha ta ce "yanxu wannan tsinan nan tsohon banzan zaliha kika bawa kanki wannan kazamin , innalillahi wainna ilaihi rajiun"ta sa Kuka ta ce "Allah ya isa tsakanin mun dashi In Sha Allahu sai anyi 'yarsa abinda yay mana ,kuma wlh sai anzubar da wannan tsinan cikin nan saidai malam yay abinda yaga dama" daga haka ta koma kan gadonta ta xube tana rusa kuka, mardiya tab'e Baki tai ta koma falon, lawisa ce ta Kalli zaliha ta ce "taso muje falor ki kwanta" sannan ta Kalli baba ta ce "gsky babarmu xubar da Cikin nan kan xa'ayi" baba asabe batai magana sbd takaici wlh ko sunan Cikin nan aka ambata Wani Irin Bak'in cikine ke taso mata, zaliha kasa tashi tai kuka Kawai take,da k'yar lawisa ta kamota suka fito daga d'akin xuwa falor......



A bangaren ummah kuwa,Batasan meke furuwa ba,Dan Batasan ma sun dawo gidan ba, Tunda tana d'aki lokacin da suka dawo ma Dan har sun fara bacci ma,Saida taji ihun zaliha da hayaniyar Dake fitowa daga dak'in baba asabe sannan ta mikie daga kwancen da take tana Jin gabanta na fad'uwa, da tunanin meke furuwa ,Ameenah Dake kwance kan katifar su itama taji ihun zaliha Hakan yasa ta tashi tana kallan ummah,dake salati ta ce "ummah lpy kuwa? bakiji ihun kuka a d'akin baba asabe ba "ta fada tana kallan ummah, ummah ta kalli Ameenah ta ce"naji Ameenah"ko lpy?Allah dai yasa lpy?kafin suyi Wani yunk'urin suka ji Baba asabe na cewa zata kashe zaliha idan Bata fad'a mata Wanda yay mata cikin ba,tunda dare ne Kuma da qarfi baba asabe tai maganar,yasa sukaji ,ummah na Jin haka ta dafe k'irjinta Daya buga mata lokaci D'aya ta ce "innalillahi wainna ilaihi rajiun,kai Jama'a yanxu dama abinda ya samu zaliha kenan,Karaf itama a kunnan Ameenah,take itama gaban ta ya fadi,ta ce "ummah kinji abinda naji kuwa? Ummah ta ce " kwanta Ameenah Saida safe, Ameenah batai musuba ta koma ta kwanta Amma gabanta Bai daina fad'uwa ba, Jin abinda kunnuwanta suka jiyo mata, ummah itama kwanciyar tai Amma dai bacci kasa xuwa mata yay awannan dare ,yanzu Saida asabe ta jawowa kanta abin kunya tasa 'yarta ta Bat'a tarbiyar ta a Banxa , innalillahi wainna ilaihi rajiun,take taji tausayin malam Auwalu ya kamata tasan yanxu shima yaji tunda dashi akaje asibitin,ko a wanne halin yake Yanxu?sbd tasan duk iyaye nagari duk Wanda yaji wannan Abu dole hankalinsa ya tashi, Dak'yar bacci b'arawa ya d'auketa sbd tunani.....



Malam Auwalu Yana kan sallaya Yana ta addu'a Dan sallar ma baisamu ya fita xuwa masallaci ba, sbd zazzabin Daya rufeshi,har wajen k'arfe takwas Bai iya tashi ba Yana kwance akan katifar sa ya rufe duka jikan sa da bargo har kansa, ummah ta shigo d'akin da sallama abakinta ta ajiye masa abin karyawar sa a tsakiyar d'akin, ta k'arasa gaban katifar sa tana kallansa ita tasan ba lpy ba, tunda har taga malam Auwalu kwance a wannan lokacin,ta ce "malam"malam Auwalu yanajin ta Dan ba bacci yake ba Amma Kuma ya kasa tashi, ta qara K'iran sunan sa, ya Bud'e kansa daga cikin bargon Yana kallanta da idanuwan sa Wanda suka sauya daga fari xuwa ja, jan ma Irin jajur d'in nan, ganin idansa Saida ummah ta tsorata sbd Bata tab'a ganin sa cikin wannan yanayin ba Amma ta daure ta ce "lpy malam? Na ganka a kwance? Ta fad'a da tausayawa,malam Auwalu da k'yar ya ce "maimuna Banda lpy ne" ummah ta ce cikin alhini "Allah ya baka lpy malam" malam Auwalu ya ce "Ameen " ummah ta ce "kasha magani kuwa"malam Auwalu ya girgixa mata kai alamar a'a, ummah ta ce "to kataso kaci abincin In yaso saina d'auko maka maganin kasha" malam Auwalu ya ce"baxan iyaba maimuna"ummah ta ce "daurewa zakai malam katashi ko iya Kunun ne saika kasha inyaso saika kasha magani"Dak'yar malam Auwalu ya iya tashi daga kwancen da yake ya karb'i Kunin da take Mik'a masa ya karb'a ya Sha kad'an ya ce "ya isheshi" ummah ta ce"kadaure ka K'ara malam" Yana girgixa mata kai ya ce "ya isa maimuna karnai amai"ummah ta karb'a ta ajiye agefe tai shiru tana kallan malam Auwalu ganin ya koma ya kwanta.....



Ta sauke numfashi ta ce "Allah ya sawake malam, sannan Ta mik'e zata fita daga d'akin malam Auwalu yay K'iran sunan ta , ummah ta juyo tana kallon sa da k'yar ya Bud'e Baki ya ce "maimuna Kinga Ashe zaliha ciki tai" ya fad'a Yana rintse ido, ummah ta ce "innalillahi wainna ilaihi rajiun, banji dad'in wannan Abu ba malam" malam Auwalu yay Wani murmushi ya ce "asabe ta cuce ni maimuna ta cuci 'ya'yana ta Bat'a musu tarbiyar su" ya fad'a Yana sakin Wani murmushi ,ummah ta ce cikin kwantar da murya "hakuri xakayi malam" malam Auwalu ya ce "hmmm maimuna kenan Bakisan me nake ji bane shiyasa " ummah ta ce "nasani malam Amma Dan Allah karka sawa kanka damuwa har Wani ciwon ya kama ka" ta fad'a kamar zatai kuka,malam Auwalu ya juyar dakai baice komai ba, ummah ta ce "kaji malam" malam Auwalu ya gyada mata kai kawai baice komai ba, ummah ta fice daga d'akin tana k'ok'arin danne kukan da take rikewa Dan kada ya kufce mata ,malam Auwalu ya k'urawa waje D'aya ido Yana Jin zuciyar sa kamar zata fashe sbd abinda yake ji......


___________?&


AA Arab haka ya kwana da tunanin ruky da Kuma Yanayin Daya shiga, Kusan kwana yay Yana juyi shiyasa Bai samu isashshen bacci jiya ba,Koda ya tashi da ASuba bayan yay sallan sai yaji wani irin bacci na fusgarsa Hakan yasa Yana dawowa daga masallaci ya shige d'akinsa ya rufo k'ofar, Bai tashi ba Sai da yaji ana masa knocking k'ofar tareda K'iran sunan sa,cikin bacci yaji knocking d'in Dan haka ya tashi da k'yar ya Bud'e k'ofar ya Kalli ummi Dake tsaye bakin k'ofar tana kallan sa kafin yay magana,yaji ta ce "Ahmad" lpy baka fito ba? Nasan Kuma zaka fita aiki, gashi yanxun 9 Saura fa"ta fad'a tana kallan sa,AA Arab ya zaro ido waje, Jin abinda ummi ta ce Dan wlh baisan lokacin ya tafi har haka ba,Yana kallan ummi ya ce "ummi bansan lokaci ya tafi haka ba , Amma yanxu zan fito" ummi ta sauke numfashi ta ce "shikenan tunda lafiyan ka lau saika fito" daga haka ta bar bakin k'ofar ta sauka qasa,AA Arab ya juya ya koma ciki ya fara rage kayan jikinsa sannan ya shiga toilet ya had'a ruwan wanka ......



Ruky tana office d'in tana zaune kan kujerar ta, tai mamaki da taga har yanxu AA Arab yau baishigo da wuri ba, bayan tasan yana rigata xuwa kullum,yanxu haka k'arfe goma Saura data Kalli agogon Dake tsintsiyar Hannunta, ta sauke numfashi batace komai ba,ta cigaba da aikin ta, Amma Kuma tana tunanin meya hanashi xuwa haka, bayan wasu mintuna taji alamar za'a Bud'e k'ofar falon da take ciki, take ta d'ago kai tana kallon bakin k'ofar har ya turo ya shigo ciki ya Maida k'ofar ya rufe, ruky dai kallansa kawai take haka kawai ta tsinci Kanta da kallonsa, shiko kallo D'aya yay mata ya d'auke kansa daga kallanta,ya fara takowa xuwa cikin falon , ganin zai shige office d'insa yasa ruky ta ce "good morning sir"batareda ya kalleta ba ya ansa mata, sbd gabad'aya sai yaji abinda yasamu ya ragu Amma ya fara dawo masa sabo,har ya shige office d'insa itadai ruky kallansa kawai take ,sbd taga yau gabad'aya ya sauya mata,saita d'auke kanta ta Maida kan laptop d'in gabanta....



Tunda AA Arab ya shige office d'insa aiki kawai yake Amma har lokacin Bai dawo dai dai ba,game da abinda ya sameshi,ya sauke numfashi ya dafe kansa ya ce "wai meke faruwa Dani ne? Ya kasa fahimtar meke shirin faruwa dashi haka,to wai meyasa ma ya k'ira ta awannan lokacin duk shine ya jawo masa wannan abun,haka ya fad'a azuciyarsa Yana Jan tsaki ,ya mik'e ganin lokacin sallahn Azhar ya gabato ya shiga toilet d'in office d'insa ya d'auro alwala, Ruky tana xaune itama ta mik'e ta shiga toilet d'in Dake falon Dan d'auro alwala,tana cikin yin alwalan ta Yi shafar kai kenan d'agowar da zatai zata Saka hular ta akanta, sukai ido hud'u da tsaka ,aibatasan lokacin data sa ihu ba ta fito da gudu cikin falon tana kuka kamar taga abinda tsoro ,AA Arab Daya Bud'e k'ofar office d'insa ya fito zai tafi masallaci ya ga ta fito da gudu afirgice take hankalinsa ya tashi ,Dan daukar sa Wani Abunne ya same ta,kafin kice me ta rugo cikin falon sukai karo da juna sai ihu take AA Arab ya rik'eta ganin yadda ta fita hayyacinta lokaci D'aya ya ce"lpy? meya faru? Ya fad'a cikin tsawa,itadai ruky ihu take tana kuka ya rasa ya zai Mata ga kanta ba bu D'an kwali


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login