Showing 45001 words to 48000 words out of 278032 words

Chapter 16 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1024

yace,a yaune safiyar laraba inda muke kawo muku maimaicin shirin ,jiya talata mun xiyarci wani qauye,Wanda Yan ta addar nan suka kai musu hari a daran jiya talata,Yan ta addar nan da suka addabi al'umma suka shiga Wani qauye Dake jihar Kaduna karamar hukumar ZARI'A,inda suke shiga suke musu dauki dai dai Amma yanxu gabadaya ma shiga suke mutanan kauyan suna kallan su haka xasu dauki duk Wanda sukai ido hudu dashi yanxu ta kai ta kawoma harma gidaje suke shiga,yanxu xakuji ta bakin wasu mutane Dake qauyen ZARI'A,Wanda muka dauki rahotansu, Inda yanxu abin ya kaima har qauyuka Yan ta addar nan suke shiga suke sace mutane,babu yara babu manya,babu maxa babu mata kowa suka Samu dauka kawai suke,Kuma a rasa inda suke kaisu gashi ba dawo dasu akeba,yanxu xakuji daga bakin wadanda abun ya shafa


Inda Aka hasko Wani tsoho sai kuka yake gabadaya jikinsa rawa yake Yama rasa ta Ina xai fara,sbd kukan da yaci karfinsa, ga Yara da manya anyi cirko cirko suna kallan Yan jarida,wasu Kuma suna koke koke kamar dai Wanda aka kwashewa Yara,can ya tsagaita yace Dan Allah gwamnati ki taimaka ku kawo mana dauki wlh muna cikin Wani Hali, gabadaya Yan ta addar nan sun addabemu,da dauka???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?r 'ya'yan mu,wlh ni 'ya'yana uku mata suka dauke mini Kuma gabadayansu ansa Musa ranar AURE, auran ma baifi sati biyu ba, Amma jiya tsakar dare haka suka shigo mana gidaje suka kwashe mana Yan mata da samarinmu na cikin wannan qauyen namu, wasu idan sukai gardama sai a harbesu,wasu Kuma suyi musu yankan rago yanxu dubi. Can gabadaya gawar wadanda aka kashe ne xa'a sallacesu yanxu ,ya fada Yana nuna mutanan Dake baje akasa jikinsu duk bullet ne ga jini wasu Kuma Anyankasu har lokacin Bai daina xuba daga jijinsuba,.....



Iyayan wasu suna rungeme da yayansu ajikinsu sai kuka sukeyi Mai cin Rai, gwanin ban tausayi,tsohon ya juyo ga kallansa kan camera yace dan Allah gaunan Kaduna da jami'an tsaro ku taimaka mana Dan Allah,muna rokonku da girman Allah ku kawo mana dauki a qauyenmu Dan Allah,ya qarasa fada da gunjin kuka,Mai daukar rahotan ya qara hasko qauyen bawani girmane dashi ba Amma Kuma akwai yawan mutane acikinsa ,Dan gabadaya a haka suke waje Daya,ya qara hasko wasu mutanan Wanda gabadaya kamar sun xauje suna kururuwar Neman dauki gashi sun zagaye ga wawwakin sun ma rasa ta Ina xasu fara,....


Mai daukar rahotan yace to Jama'a Kuna dai ganin wannan qauye a halin da suke ciki ,Wanda gabadaya Yan ta addar nan sun musu illa ba kadan ba, suna Kuma kawo kukansu xuwa ga gomnati data tai Maka musu a kawo musu tsaro ,akuma maido musu da yaransu, atai Maka a kawo musu qarshen wadannan Yan ta addar,Kuma Nima Ina mana addu'ar Allah ya kawo karshen wannan ta qaddamar ,sunana Junaid dalhat,nine na kawo muku wannan rahoto daga gidan TV na GADANGA & radio,adamadin wadanda suka taimaka shirin yazo gareku,dani Dana tattako na dauki rahotan tareda da abokan aikina Ina muka patan muwuni cikin amincin ubangiji, kukasance damu awani makon idan Allah ya kaimu, danji wasu labaran masu tava xuciya, Allah yasa mufi karfin xucikatanmu,bissalam,daga haka aka kawo qarshen shirin, adai dai lokacin Kuma motar jami'an tsaron ta shigo qauyen,....


Mamah da baba hasiya Dake falon gabadaya furkarsu ta jike da hawayen tausayin bayin Allah nan,itama ruky data fito cikin shirin fita ganin wannan abin al'ajabin,da Rashin imani da wadannan yan ta addar sukayi yasa ta kamewa a inda take tsaye tana kallan mutane akwance da sunan ga warwaki,me gomnati,takeyi tana Ina da ake wannan xalinci a qasa,Ina jami'an tsaron suke daga police har army's din,ace akwai jami'an tsaro a jihar Amma Yan ta addar nan suke a binda sukaga dama,....

Sai Kuma Wani tunani yaxo mata,Kodan ba laifin gomnati bane ko jami'an tsaro tunda Suma dai kusan kullum sai sunji ance ankashe jami'an tsaro kusan uku ko hudu,shin daga Ina matsalar takene,me yake kawo yawan wannan sace sacen ne, Bata da ansar tambayar ta yasa jiki mace ta qaraso kusa da mamah wacce ke goge fuskar ta da tissue,murya a shake tace mamah xan tafi, mamah ta kalleta tace auta wai Dan Allah meyake kawo wannan ,ta addancin,ruky tace wlh mamah bansani ba,mamah tace gashi har jami'an tsaronma Basu tsiraba , kashesu sukeyi sukuma dauke Maka mansu wannan Wani Irin xalincine,meye anfanin gomnati, Ruky tace wlh mamah gomnatinnan tana iya Bakin kokarin ta,Amma gabadaya Daya abin anrasa daga Ina matsalar take,ankasa gano bakin zaran ,baba hasiya tace kuyi Shuru ga gaunan Yana magana,....


Governor nan Kaduna na xaune a office dinsa, ga Yan jaridu nan da gidajen tv duk ansa masa mic a gabansa da lasifikoki ,Yana magana idansa ya kada yay jajur yace, assalamualaikum,kafin nace komai Ina Mai bawa mutane hkr wlh nidai a bangarena Ina iya bakin kokarina,haka Kuma jami'an tsaron mu ma suna nasu qoqarinsu, saidai Suma basu tsiraba kashesun kawai ake,Amma Dan Allah kuyi hkr da gazawarmu ,Dan nasan wasu zasuga gazawarmu ,Amma Allah shine shaidanmu muna iya bakin kokarinmu,in Sha Allah nan Bada dadewa ba xamu kawo muku dauki in Sha Allah kuyi hkr,yanxu haka jami'an tsaro sun isa kauyan ZA'A sallaci mutanan, Kuma in Sha Allah xa'a dawo muku da yaranku,ya hada hannayensa biyu alamun roko Sannan ya dauki hanky ya goge goshinsa Rashin abinda zaice yasa ya Mike svd gabadaya Gani yake kamar gazawarsace ta kawo wannan ta addancin yay hanyar barin wajen escort suka take masa baya,daga haka aka dauke wajen saikuma hayaniyar mutane,...

Mamah tace Allah sarkie bawan Allah nan wlh balaifinsa bane,wannan Wani Irin masifa ne,wai wayake tai Maka musu suke kashe al'umma ne basuji ba ,Basu Gani ba Dan Allah kiga fa wannan qauyan yadda akayiwa wasu yankan rago wasu Kuma aka harbesu da bullet ya Allah ya kawo mana dauki Alfarmar Annabi( s a w e&?)baba hasiya ta ansa da Ameen haka ma ruky wacce ta mike take sake yiwa mamah sallama,mamah ta kalleta tace auta ki kula kinji ni wlh dama aje aikinnan kikayi , Dan wlh hankalina ya fara tashi da lamarin nan,,baba hasiya da kamar tai Kuka tace, Hajiya Nima dai tsoro nakeji wlh ,ruky tai murmushin da Bata shiryaba tace mamah in Sha Allah babu abinda xai samemu kudai ku tayamu da addu'a, mamah tace in Sha Allah, Allah ya kareku aduk inda kuke ruky ta ansa da Ameen tai hanyar fita ,baba hasiya ma tana tai mata addu'ar dawowa lpy,haka ta ansa musu da Ameen tana qarasa ficewa daga falon, xuciya ta gabadaya babu dadi.....



_______?&


Alhaji sunusi ne xaune a katon falonsa Dake gidan hutswarsa shida babajo Ali sai babbaka dariya suke kamar wasu sabbin kamun hauka,gabansu Kuma kayan marmarine kala kala,ga kwalaben alcohol kala kala a agaban su,wasu ansha wasu Kuma ba'a Shaba, babajo Ali ya Dan tsagaita da dariyar da yake ya kalli Alhaji sunusi,yace lallai mutumina kaidin shaidannin mutum ne, Alhaji sunusi ya aje kwalbar Hannansa kan table din gabansu,yace ka dauka nidin na wasa ne, Amma babu babban shaidani Irin goga , lallai yarannan ya iya aiki ,duk abinda yasa agaba saiya cinmasa kaga dai yadda ya kwaso yaran kauyan nan gabadaya,shida yaransa kaga dai yadda suka musu kisan wulakanci,.....


Babajo Ali yace shiyasa fa yarannan banaso ya kufcemana domin Yana mana yadda Mukeso,inafa tuna nin ba lallai ma ya cika satinnan da muka dibar masa ba,zai maye mana gurbin wadancan yaran da muka rasa, Alhaji sunusi yace nima Ina tunanin haka,Jin governor Yana magana yasa babajo Ali cewa Kalli wannan Shashan ne yake magana, Alhaji sunusi ya kalli TV,bayan sun gama sauraran abinda governor ya fada, Alhaji sunusi yay tsaki yace bar Sha Sha, xai ta tufkane muna masa warwara indai mune,mu xuba dashi Dan halak ka
fasa,...


Babajo Ali yace Allah mutumina, Alhaji sunusi yace wlh honorable ai tunda mutumin yasa na Fadi takarata wacce saida
shugaban jam'iya yasa baki sannan aka bani tun daga nan nace wlh saina ga bayansa saina sashi ya xubar da hawaye ,gashi Kuma yanxunma idan ka kula saida ya xubar da hawayen sbd hanky din dayasa mutane sun dauka gumi yake sharewa to hawayene ya sharewa,...

Babajo Ali yace shege MaiTama dadina dakai baka yafiya, Alhaji sunusi yace wlh ko ciki Daya muke dakai indai kamun Badai daiba saina rama, Babajo Ali yace nidai tunda aikinmu yayi kyau shikenan ,yanxu kiramana goga Muji yaran Saura nawa a cika su,kafin suyi magana an daga labulan falon , gabadaya suka daga kai suna kallan Wanda ke tsaye bakin kofar falon, Alhaji sunusi ya Mike cikin farin cikin ganin goga yace barka da xuwa dan halak, goga dayake tsaye kafarsa daya ya dage Wandon Daya Kuma ya sauka har qasa ,yaqarasa shigowa cikin falon fuskarsa a murtuke kamar yadda take Koda yaushe,ya xauna cikin Daya daga cikin kujerun falon Yana karewa su Alhaji sunusi kallo Kuma har lokacin Bai magana ba,...

Alhaji sunusi ya koma ya xauna yana tsinewa goga axuciyarsa Jin wai har shine xai masa magana Amma yay Banxa ya kyaleshi,meyake takama dashine,babajo Ali shidai kallan goga kawai yake, ganin yadda ya hakimce kan kujera kamar yadda ya samesu da ace ba aiki yake musuba wannan Yaran ko kallo ai Bai ishesuba, tunaninsa ya katsene lokacin da goga yace cikin yanayin muryarsa ankammala aiki Yara duka sun cika harma da qari,....

Alhaji sunusi cikin farin cikin samun nasara yace ,goga shiyasa nake San aiki da kai , indai har kasa Abu agaba tofa saika cinmasa tukunna hankalinka zai kwanta ,Ina patan dai komai yayi yadda muka tsara ,ya fada Yana jiran abinda goga zai fada,goga ya Jin jina kai, Alhaji sunusi yace Ina kuma Sakona patan shima ya samu,goga yace Yan Shilan naka sun samu , Dan baxama su haura shekara goma Sha Daya VA ,xuwa shabiyu ,suna Daya part din sonake sai komai ya lafa tukunna xan kawo Maka su har nan gidan ko Kuma kaje can ka daukosu,Dan kulawannan naga sun fata patrol, yanxunma Dakyar nazo nan din Dan gabadaya sun tattare hanyoyi,....


Alhaji sunusi yace goga Ashe kanaso ai wannan tafiyar dakai, ALKawarin ka Yana nan da zarar ansamu kujerar senator nan,lallai tunda kasamo abinda aka umarceni danai anfani dasu lallai kamar bukata ta biya ne, saikuma Alhaji sunusi yay saurin rufe bakinsa Jin katobarar da xaiyi a gaban goga,shiko goga nunawa ma yay kamar bai jiba, goga ya mike cikin basarwa ya Mika hannu,Hakan Dayay Sunsan abinda yake nufi Dan haka babajo Ali ya dauko jakar kudi me nauyi ya dire gaban goga,goga ya dauka ya savata a ka fada Sannan ya nufi hanyar fita daga falon bataredaya Kara kallan suba, .....


Alhaji sunusi ya dubi babajo Ali Dake kallansa yace honorable,bukata ta biya, babajo Ali yace naji dadin wannan aiki yanxu abinda xa'ayi shine bari nakirasu nace ansa samu yadda ake so,svd Yanayin hanya zamu turo su nanda kwana biyu in Sha Allah, Alhaji sunusi yace kwarai kuwa,duk yadda xamuyi Dole sai ansamu hanyar fitar da yarannan,daga qasar nan dole,wlh mutanan nan danma sunga bama musu wasane shiyasa kawai sukai hkr Amma da ace muna musu wasa wlh da baxasu tava yadda damu ba,....


Babajo Ali yace sosai wlh Dan dai kawai ba yau muka fara wannan harkar dasu bane, Alhaji sunusi yay dariya yace asha giya,ya fada Yana daukar kwalbar gabansa,babajo Ali ya tuntsire da wata mahaukaciyar dariya yace harka tunomun da mawakinnan me cewa In xaka Sha giya kasha ta dubu , Alhaji sunusi yace Aiko inma ta dubunnaice mu sai munsha aidole yau ai shagali,babajo Ali yace shagali ma sai an kawo mana Yan shila,haka suka sa dariya tare, farin ciki fal ransu,....



________?&


Ni gsky baba wlh ni bana San Wani salisu bayan nace mike akwai Wani Alhaji atasha Dayace Yana Sona AURENAH xaiyi , naga shekaran jiya ma shine Yaxo,ya kawo mana lemon kwalbar nan ,Wanda kikace sai kace Zuma,baba asabe tai kasa da murya tace Dallacan Sha Sha,ana ga Gabas kina ga yamma ,me xaki da Wani tsohon Alhaji keda kike da quruciyarki da komai ,ga salisu Mai jini ajika,wai kodai Baki gane wani salisu nake magana ba,....


Zaliha data ci ado cikin wata yaluwar atamfa ta chava kwalliya, xata siyayyar abincin siyar warsu tace babarmu na ganeshi mana Ina Dan gidan Alhaji hamza Mai taki, asave ta washe bakinta Wanda yake jajir tace shifa Yo ahema kinganeshi kike min Wani iskanci, zaliha ta turo baki gava Wanda yasha jan janbaki tace naga babarmu ba kince Nana yaxo yace Akira masa ba,yace yanaso, baba asabe ta hade Rai tai kasa da murya tace ita uwarta tace bata isa fita xance yanxu ba, Saita gama bokon kafirci da baxata anfanesu da komai ba saima bakin talauci da suke fama dashi,....


Zaliha tace GSKy baba bansan Taya salisu zaice Yana sonaba,Kinga fa dan gayune fa Dan Boko Kuma gashi wlh kyakkyawane,baba asabe tace ai shi namiji bashida wahalar ka jawo hankalinsa, matukar kinbi abinda xan fada miki,kamar kinsamu salisu ne kingama , zaliha tace baba tayaya,....


Baba asabe ta qara qasa da murya tace kidinga wucewa kullum ta kofar gidansu,na tabbata iyanxu ya dawo daga aikinsa,Yana shagon kofar gidansu a xaune, kullum kidinga bi ta hanyar Kuma ko siyayya xakiyi kidinga xuwa shagonsu,idan kikaje kidinga kwarkwasa kina shagawaba kina karairaya agavansa,na tabbata wlh saikinga ya fada miki cewa Yana sanki,tuni xakiji ya cire wata Nana azuciyarsa Kuma Nima xan dage ta bangarena na karbi miki tsimako wajen Wani malamin,...

Zaliha tace baba Kuma idan ya dakenifa, baba asabe tace Kiji Sha Sha aisu maza abinda sukeso kenan, zaliha badan ta gamsu da maganar baba asabe ba tace to babarmu bani kudin yanxu dai bari na tafi siyayyar nan kar dare yayi baba asabe tace yauwa ko kefa yar Albarka ta miko mata kudin ,zaliha ta karba,tace ki tabbatar fa yanxu Kin bi ta kofar gidannasu danya ganki ,Kuma idan kindawo mafa ki tabbatar kinbiya ta shagon nasu, zaliha tace toh babarmu ta fada tana yin waje,baba asabe Kuma ta sauke ajiyar xuciya tana murmushin jindadin yadda zaliha xata amince da kudurinsu inbanda zaliha Bata ta da hankali wazaiki miji kamar salisu yaro Dan gayu ga kudi ,sai Kuma ta tuntsire da dariya tunowa datai babbar wawta da babbar asarar da ummah Tai akan salisu ita ai gashi ta tsinci Dami akala,....





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD



*____JAMI'AR TSARO____*


*____THE WOMEN POLICE____*



*NA*


*____NAJAATU UMAR FAROOQ ____*


*____(MRS SARAKIES)____*



*QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA)=?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season one ep 2?? 1??



________?&

Ameenah ce ke shara a tsakar gidan ta wajen karfe bakwai da Rabi na safe ,tayi nisa acikin tunanin data ke, bataji Kabiru ya shigoba gidan ba,domin batama kula dashiba saukar dundu data taji Abayanta,yasa ta dogo a raxane tana jefar da tsintsiyar hannunta tana kallan Kabiru da bakaken ledoji a hannunsa,ya wurga mata Wani kallo yace ke wacce Irin jakace ana Kiranki tundazu Baki ansa ba kika kyaleni sai kumfar Baki nake,ta kalleshi da fuskar ta wacce ta jike da hawaye Dan wlh taji xafin dundun ba kadan ba,tace wlh banjiba,yace dama Taya ZA'Ayi Kiji tunda kwa kwalwace Irin ta tsofi Dallacan ungo kwannan da indomin nan ki dafamin Yan xunnan ,ya fada Yana Mika mata ledojin ,cikin rawar jiki Ameenah ta karba tai hanyar murhu,yace kiyi sauri wlh kafinnan da mintuna Ashirin Dan sauri nakeyi akwai inda xani,ga Lipton harda sugar,ki sauri, Ameenah ta ansa masa tana daukar tukunya,....


Kabiru Kuma ya shige daki Dan oga goga ne ke kiransu Dan yauma akwai aiki,bayan shigar Kabiru daki ya tarar wayarsa na ringing Yana dubawa yaga oga goga ne ke kiransa cikin girmamawa ya daga daga Daya bangaren goga cikin muryar Shaye shaye yace kb ka kira zailani karya manta, domin na kira wayarsa bana samu ya fito da wuri karya haura lokacin da muke bukata,Kuma mu hadu a Inda muka Saba ku Kula da hanyar domin kulawannan suna nan sun kafa sun tsare nemanmu kawai suke,kb shima yace cikin yanayin muryarsa yace no yawa oga goga angama,yanxu kuwa daga haka Suka yanke wayar,ya kira zailani bugu kadan ya daga,daga Daya bangaren zailani yace oga kb antashi lpy,kb yace normal zali,yanxu oga goga ya kirani yace yay ta Kiran wayarka baya samu nai tunanin bashida wannan number naka,zailani yace gsky ne meya faru ,kb yace, yace karka manta ka fito da wuri kasan jiya a buge kake over ba lallai ma kaji abinda ya fada ba shiyasa yace na tuna Maka,zailani yace aijiyannan gabadaya rasa ma kaina nayi badan ka tallafamin na,kb yace aikaidinne inka samu kwaya baka mata ta dadi, zailani ya kece da dariya ,kb yace patan yanxu dai ta sakeka zailani yace normal nakejina yanxu oga,ai na fahimta oga kb yanxu kuwa xan shirya,....


Kb yace yauwa sai ka fito kafa kula Dan wlh kulawannan sun kafa sun tsare,nemanmu kawai suke, zailani ya kece da dariya yace xako susha wahala indai da mu xasu Kara,Dan wlh munfisu hatsabibanci,ga Kuma ubangida s MaiTama,kb yace ai shine ma babban shedani,dai dai nan Ameenah ta shigo cikin dakin da Kofi da kwanuka a hannun ta,kb Yace normal ne zali saimun Hadu daga haka suka yanke wayar ya Kalli Ameenah bayan ta gama dire kwanukan tana kallansa ya hade Rai yace meye kike kallonta ta kawar da kanta gefe tace dama na gama ne,yace to tunda kingama ba saikije ba Amma kinxo kinsani agaba Ina waya kawai Dan gulma saikinji me nake fada a wayar , Ameenah tace kayi hkr daga haka tai hanyar kofa ,...

Kabiru ya bita da harara sai Kuma ya bubbuda kwanukan yaga ko tamai jagwal gwalo yanxu nan ya tattakata sai Kuma yaga akasin haka yaga abincin sai kamshi yake ga shayin ma sai tiriri yake,tuni ya sauko kasa ya jawo indomin ya fara kaiwa bakinsa Yana kutsirar Kwan Yana kurbar shayin, ganin ya kusa cinyewa yasa ya kira Ameenah yasan hailinta kila ita Bata diva ba,Dan wlh shaf ya manta ma da ita, Ameenah ta shigo tace gani yace kin diva ta girgixa masa kai ,a fusace yace ba magana nake mikiba xaki Wani ansa min da ka koni kadangarene,da Baki xaki ansa min cikin rawar jiki tace a'a ya tura mata ta gaban ta yace ungo je kici , kafin Kiji dadin fadamin magana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login