Showing 114001 words to 117000 words out of 278032 words

Chapter 39 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1041

ya sani Amma Bai tanka mata ba,illah ido Daya kawo ya xuba mata,danshi yanxu lallabata xaiyi ya bita ahankali harta sauko daga fushin da takeyi dashi ,Dan wannan fushin da takeyi dashi ba qaramin axabtar dashi takeyi ba,daurewa kawai yakeyi harta sauko,Tunda ba ita xatajeba aida sauki, Amma Kuma kasan ransa Yana tunanin maganarta,ummah Babu abinda ta fasa na Daya daga cikin abinda take masa na kysauta tawa kamar yadda ta Saba kawai dai taga alamar saitayi masa Haka tukunna,saiya gane kuransa na daga abinda takesan fahimtar dashi tukunna,Nana da taje ta samu Ameenah ta Dan ciko tunda Babar saude babu laifi kullum saita aika mata da abinci sau biyu arana,duk da itama bawai karfi garesu ba,rufun asirine kawai,....


Kuma Kabiru ma yafi sati biyu baixo gidanba,bare ya gallaza mata kamar yadda ya Saba,shiyasa ma ta Dan samu relief ta wannan bangaren,harta Dan ware Amma kullum cikin Fargaba take na xuwansa Dan tasan xaixo din,Dan shi xuwansa bawai sani take ba saidai taga ya fado gidan,ummah ta bawa Nana wata yar qaramar waya ta Nokia data aika Nana ta Siyo mata second hands tace ta kai mata Dan sudinga waya Koda yaushe tana Jin halin da Ameenah ke ciki,ko hankalinta zai kwanta,ta Kuma gargadeta akan kome karta boye mata ko me Kabiru yake mata ta fada mata,idan ta boye mata wlh saita Saba mata, Ameenah ta ansa mata da to,Saida Nana ta wuni a kaduna harta leka gidan Babar saude ta kaimata sakon da ummah ta Bada ta kai mata, ta Kuma Yi mata godiya wannan sakon ummah ne,sannan ta dawo gida bayan ta kaiwa Ameenah kayan abinci,.....



Tsakanin ummah da baba asabe ido ne kawai,babu Mai shiga harkar kowa,ita ummah ta kudiri aniyar wlh duk randa baba asabe ta qara shiga sabgarta ta kai mata munafurci wajen malam Auwalu wlh saita sauya mata kamanni,tunda taga yadda ta kumbura mata wuyan baba asabe ya kumbura tasan ba karamin shaka tai mata ba,Kuma Hakan datai mata xaisa ta shiga hankalinta ,taga Kuma Hakan da tai mata shikadai xaisa ta daina yi Mata muna furci da katsalandan acikin ruyuwarta, data 'ya'yanta,tafiso kamar yadda Bata shiga tata rayuwar itama baba asabe ta daina shiga sabgarta,......



Abangaren baba asabe kuwa tafi sati Daya wuyan Bai daina mata ciwo ba,da kyar ta warke Dan Saida Tasha pain relief,Dan babu laifi Tasha wahala, abinda yasa ta daina shiga harkar maimuna yanxu abu Daya ne yasa ta Dan daga mata kafa ,kula bawai daina shiga sabgarta taiba Lambo tai mata,so take ta warke daga wannan ciwon da ummah taji mata ,Dan wlh shiga sabgarta tama yanxu ta fara,kuma wlh indai tana numfashi baxa ta tava bari ummah tai farin ciki ba arayuwarta , daga ita har 'ya'yanta, saita kuntata musu,Kuma ta qarqashin qasa xata bi mata tana kuntatawa xuciyarta,.....



Yanxu abinda ke gabanta burinta kawai salisu ya karbi soyayyar zaliha,idan Hakan ta tabbata saitafi kowa murna aduniyar nan, Kuma taga alamar salisu taurin Kaine dashi,ba irin kissa da kisisinar da Bata kowaya zaliha tai masa ba, Amma kamar Dutse,ko kallan ta bayayi,haka zaliha zata dawo ta fada mata,Amma baba asabe Bata fasa tura taba, rannan ta takurawa zaliha akan ta tareshi tace tana sanshi, ai dole kila ya saurareta,zaliha da kyar ta amince,bayan ta fada masa zaginta yay yace ko mata sun Kare aduniya baxai Aureta ba kaiko itace autar mata mai xaiyi da ita, idan ta qara xuwa Mai shago saiya sa anmata dukan tsiya, da zaliha ta dawo ta fada mata tana kuka tana Bata lvr , baba asabe tace ta kwantar da hankalinta, tasan ta Yaya zata bi dashi,salisu da kafarsa saiya xo yace Yana Santa,.....



Zaliha ta share hawayen ta tace tareda gyada mata kai, baba asabe tace karki damu ninasan mexanyi akai kinji dai koh ,zaliha ta turo Bakinta gaba,tana kallan baba asabe tace shikenan Babar mu,..da daddare wannan tsohon alhajin yaxo Wanda yake kawo musu tsire da lemo me gas, zaliha ta fita cikin sanda tana waige waige ta shige motarsa, tana shiga ya washe Baki Wanda yake jajir duk goro yacinye gaba Daya,ya jawota yace amaryata, zaliha ta kwace jikinta da sauri tana waigen window,kar malam Auwalu ya ganta, saikuma ta juyo ta Bata Rai tace Dan Allah ka bari tun ranar fa nace Maka banaso, Alhaji tanko ya Kara washe Baki yace to Dan Allah ki bari na rike ko hannun kine, ya fada Yana Kara kawo hannunsa jikin ta,zaliha tai baya ta qara Bata Rai tace nidai a'a, Alhaji tanko yay murmushi ya dauko ledar dayaxo da ita yace idan Baki bari na rike hannun kiba yau baxan bakiba, zaliha ta juyar da kanta gefe tana waigen kada malam Auwalu ya dawo ya sameta, haka dai ya dinga mata wayo, zaliha taita waigen window kada malam Auwalu ya ganta,ganin Bata ganshiba yasa ta Mikawa
Alhaji tanko hannunta,....



Alhaji tanko ya rike hannun ta ya fara murxa matashi, Yana kallonta,itadai xaliha daurewa kawai take,haka dai Suna xance Yana murxa hannunsa da nata, Yana murmushi,hardaga karshe suka gama hira,yadauko ledar ya Bata, ta koma gida Kuma cikin iKon Allah malam Auwalu baidawoba,baba asabe ta washe Baki ganin wannan uban kayan makulashe da , Alhaji tanko yake kawo musu,gefe Daya Kuma tana ganin cin kudinsa kawai xasuyi ta aurawa zaliha salisu yaro Dan gayu Mai kudi,me zaliha xatai da Wani tsoho Wanda ya kusan haifar ubanta,...washe gari da safe sukai abincin siyarwa,ta tafi dashi Tasha, bayan ta gama siyarwa,ta fara hado kudinta,sai Wani ne Wani rikekken Dan daba Irin  yan iskannan na Tasha Bai Bata kudinta taba,tai tabin kansa akan ya Bata Amma ya hanata saima Wani wasan Banxa dayake mata,,wai saita biyo shi dakinsu Dake Tasha ta karba itako taki,ganin fa da GSK ba Batan xaiyiba ita Kuma baxata iya bar mishi ba yasa ta rike masa riga shiko ya zille zaliha ta dinga binsa Yana guduwa daga haka harya jata inda yakeson suje din,yay bayan wani daki da ita ya shammaceta ,ya cafkota yamatseta ajikinsa , zaliha ta fara kokarin kwace kanta Amma ta kasa,Saida ya Dan samu relief sannan saketa ya wurga mata kudin yay gaba abinsa, zaliha ta karkade jikinta tai masa Allah ya isa shiko baima jitaba yay gaba abinsa,.....



Haka dai kullum idan Alhaji tanko yaxo xance wajen zaliha da kalar abinda xaice xai mata idan taki Kuma yace baxai Bata ledar abunda yaxo mata dashi ba, ita Kuma baxa taso ya hanata ba,tunda baba asabe tana so,Kuma cewa take karta sake ta Rabu da Alhaji tanko, akwai lokacin rabuwar tasu, Dan lokacin rabuwar su baiyi ba,daga taba hannu aka koma runguma ,idan taki yace ai duk acikin soyayya ce, zaliha haka take daurewa Alhaji tanko yake rungumarta da jikinsa duk jijiya ga Wani wari da yakeyi,Dan wlh wannan ya kusa haifar malam Auwalu,....


Kuma harga Allah ita zaliha Batasan abinda yake mata,idan suka gama hira ta koma gida haka xakiga tana dan mammatse jikinta,ko Kuma kiganta kamar atukure, Amma baba asabe Bata taba kula da wannan ba ita Damuwarta taci kayan Dadi, akawo mata Banxa ta kwasa,haka Kuma kullum idan taje Tasha Wani lokacin alhaji tanko yaxo yace ta kawo masa abinci ananma yace saiya rungumeta ba yadda ta iya take yarda Kuma ya Bata kudi Wanda yafi kudin abincin dayaci tunda aidama anan suka hadu, ummah duk abinda suke kallansu kawai take tana jiyewa baba asabe wlh watarana kartaxo tana cixan yasa,.....



Baba asabe ce xaune a gaban Wani malamin xaure,bayan ya gama sauraranta yace mudai kinsan ba asiri muke ba taimako muke sbd haka,baxan gaji da fada miki ba,baba asabe tace nasani malam, ya jinjina kai yace ungo wannan,baba asabe ta karba jiki na rawa,yace tai wanka dashi Sau uku arana, idan tai wanka tai sati tana wucewa ta gaban shagonsa da yardar Allah xakiga abin mamaki da kafarsa zaixo yace Yana San zaliha,baba asabe ta washe Baki tace na gode,malam sai Kuma inaso a Kara kauda hankalin malam daga kan yarsa Ameenah, banaso kwata kwata ya fahimci halin da take ciki,da Kuma shi yayan matar yadda shima tunaninsa baxai taba kawowa kan halin da yarinyar ke ciki ba,sai Kuma mijin Ameenah, shima inaso ya qara tsanarta Yana musguna mata, malamin xaure yace angama yay Yan sidda barinsa yace kuje har anyi miki aikinki baba asabe, ta qara washe bakinta ta ciro kudi ahabar xaninta ta dire gaban malam daga nan ta koma gida ranta fes tana jiran Saka mako,....



____________ ?&



*ASALIN labarin su malam Auwalu da matansa biyu Asabe da Kuma maimuna*



Malam Auwalu ya kasance almajiri ne,Kuma almajiri ma, na Baban matarsa ta farko wato Asabe, ankawo shi almajiranta tun Yana shekara goma Sha biyu,anan qauyan ZARI'A anan yake karatunsa ba Allo da ruwarsa saidai ya koma gida da sunan hutu,malam Auwalu mutum ne me hankali da nutsuwa dama tun Yana qaraminsa, shiyasa baban asabe ya yadda dashi,har ya aminta dashi,shine ma babban almajirinsa,akwana a tashi bayan 'Yan shekaru baban asabe wato malam mamman yace ya bawa Auwalu auran asabe,duk da malam Auwalu yasan asave Amma Bai taba Jin santaba axuciyarsa ba, baiyi musu ba ya karba danshi yaro ne Mai biyayya awannan lokacin,bare Kuma malamin sa ai Bai cancanci yay musu dashi ba,...



asabe da aka fada mata taji dadi Dan ita dama tana sanshi , kawai dai Bata taba nunawa bane ba,dukda har sukai kafin auren,Bai taba xuwa gunta zanceba, Bayan shekara biyu akai bikinsu,bayan anyaye malam Auwalu ya xama malami shima, Yana Dan sana'arsa ta kayan masa rufi,haka dai aka kai amarya asabe gidan mijinta,Dake cikin kauyan, tana nunawa malam Auwalu soyayya shima balaifi Yana kulawa da ita tunda Amana aka bashi ,Kuma ma ai matarsace xancen Wani, bayasan ta ai Bai taso ba, tunda harya karbi auranta Kuma koda wasa Bai taba nunawa asabe kiyayya ba ,duk ba itace xabin Saba,haka dai suke xamansu da asabe lpy lau, babu Wani tashin hankali, sai abinda ba'a rasaba, na tsakanin miji da mata,Ba'a cika shekara ba baba asabe ta haihu aka samu yarinya mace,aka sa mata suna lawisa,.....




Bayan shekara biyu Kuma ta qara haifar mace aka Saka mata,bilkisu,bilkisu tana da shekara Daya da Rabi malam Auwalu ya hadu da ummah acikin garin ZARI'A Dan anan yake kasuwancin sa, ummah ce kadai macen daya taba so arayuwarsa,haka dai yaje gidansu ummah tambayar ixni aka bashi,ya fara xuwa xance suka fara soyayya da ummah kamar Babu gove,Kuma har lokacin asabe Bata saniba,malam Auwalu ya tura iyayensa suka je tambayar masa auran ummah take awajen aka bashi ita akasa ranar AURE Nanda wata biyu,ya koma gida ,baban asabe ya fara samu ya fadawa wato malam mamman baiyi musu ba illah farin ciki da yay yasa masa albarka, sannan ya dawo gida ya fadawa baba asabe,.....



Baba asabenki tai tsalle ta dire tace wlh Babu Wanda ya isa yay mata kishiya ita kadai ce agidan mijinta, malam Auwalu Dan ita kadai aka yishi,malam Auwalu kuwa yace Bata isa ba Dan aure Babu fashi, baba asabe ita Kuma tace Bai isa yayi aure ba,Dan arayuwarta ta tsani kishiya, asabe Irin matan nanne masu bala'in kishi ,ataikaice dai ranar baba asabe Bata bar malam Auwalu ya rintsa ba,sbd masifar data kunna masa ranar Dan baba asabe babu laifi akwai masifa,Saida suka kusan sati suna Abu Daya baba asabe tana masa tijara kala kala,ganin bazai fasa ba yasata tattara kayanta da yaran ta ta tafi gida,bayan taje babanta ya tambayi babarta maiya kawo ta gida ta fada masa,Aiko yay kan baba asabe da fada yay mata kaca kaca yay mata tas yace Kuma ayau ba sai gobeba ta tattara kayanta da yaran ta ta koma gidan mijinta,baba asabe tasa kuka,haka dai ta tattaro kayanta suka koma gida,malam Auwalu baisan tayi yaji ba, daga ranar ta qara cin damarar kunnowa malam Auwalu wuta akan ya fasa auran, Amma ko kadan Bai fasa ba,haka dai kullum suna cikin tashin hankali,aka cigaba da gurgurawa har lokacin biki yay,.....



Aka kawo ummah gidan Malam Auwalu,aka Sakata a Daya dakin Dake cikin gidan,Dan dama dakuna,biyu ne ,washe gari malam Auwalu ya hadasu waje Daya yay musu nasiha sannan aka Raba kwana ko Wacce kwana biyu zaina mata idan ummah ta cika sati Daya,aida Asabe taga ummah kyakkyawar GSK da ita yasa ta qara cin damarar kunnowa malam Auwalu wuta agidan kullum cikin masifa take da ummah,ta dinga takalarta da fada ita dai ummah Bata kulata,Dan macece Mai hkr , Malam Auwalu yay mata fada Amma ta bayan kunnanta yake wucewa Dan kamar xugata yakeyi ,ganin abun na asabe gaba yake yasa ya yanke shawarar zai fadawa mahaifin ta,ko Allah zaisa shi taji maganarsa Dan wlh sbd mahaifin ta kawai yasa Bai saki asabe ba,yake daga mata kafa ,da mahaifin ta yaji wannan maganar ransa ya Baci Dan dama yasan Asabe masifaffiya ce batajin magana,malam mamman da kansa ya tako yaxo gidan yaywa asabe kaca kaca yace Kuma idan ta qara saiyasa yayan ta yaxo har gida ya mata dukan tsiya sannan yasa malam Auwalu ya saketa, a'a baba asabe duk cikin kashe din da babanta yay mata babu Wanda yafi daga mata hankali Irin wai malam Auwalu ya saketa Allah ya Gani tana mutuwar sanshi baxata taba bari ta rasa Shiba, wanna fadan da malam mamman yazo yaywa asabe yasa ta shiga hankalinta ta daina shiga harkar kowa agidan daga ita sai yayanta,haka dai suke xaman kurame agidan ,bayan an yaye bilkisu asabe ta qara samun Wani cikin ,bayan watanni uku haka itama ummah ta samu nata cikin,....



Aifa asabe ganin wannan ciki na ummah yasa ta tada Hankalinta, Amma Bata nunawa kowa ba, Bata bar kowa ya fahimta ba har asabe ta haihu, wannan Karan ma dai macece ,Dan Allah ya Gani ta Saka Rai da namiji xata haifa,aka sakawa yarinyar mardiya, ganin ummah ce xata haihu tunda ia ta haihu,nanfa hankaliinta ya qara tashi Dan farga barta Daya kada ummah ta rigata haihuwar da namiji agidan malam Auwalu, ataikaice dai hankalinta Bai kwanta Saida taga ummah ta haifi 'ya mace, sannan ta sassautawa ranta,Dan ita dama Dan kada ummah ta haifi d'a namiji ne shiyasa ta tada Hankalinta,ranar suna aka sakawa yarinya Ameenah,kunga kenan mardiya sa'ar Ameenah ce,haka suka cigaba da rainon 'ya'yansu, asabe da maimuna,ita asabe tana da uku ita Kuma maimuna tanada Daya,.....



Akwana atashi,babu wuya awurin Allah, hardai ,su Ameenah suna girma gefe Daya kuma su lawisa Suma sun fara tasawa, Ameenah tana girma tana qara kyaune domin gabadaya kamannin ummah ta dauko,wajen kyau ,fari,gashi,ido da sauransu,ga malam Auwalu shima yadda yake nunawa Ameenah so kamar me Dan baya iya boyewa Koda ko agaban asabe ne,ganin haka yasa ummah ce masa ya daina haka Dan babu dadi tunkafin asabe ta farga, ai duka suma sauran 'ya'yane, agabanta saiyace ya daina, Amma Kuma Bai fasa ba,tun baba asabe Bata Fargaba har dai ta farga nanfa,baba asabe ta dinga masa masifa tana,Yana nuna banbanci,sai Allah ya Saka mata,malam Auwalu baice komai ba, ganin haka yasa itama ummah ta qara Yi masa magana,ya nuna mata ya daina Amma fa baidaina dinba,Dan xamu iya cewa son da malam Auwalu yakeyiwa ummah shiya shafi yarta,.baba asabe tana hankalce dashi taga baidaina ba nanma ta dinga masifa tana tsinewa ummah akan ta shiga tsakanin ta da malam Auwalu wlh baxa ta kyaleta taba,to tundaga nan baba asabe ta daura damarar ganin maimuna bazata taba samun farin ciki ba arayuwarta daga ita har Ameenah,. anan ne xamu iya cewa tsanar da baba asabe takewa ummah ta samo ASALI....







07066508376_______
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t






*_____JAMI'AR TSARO _____*



*_____THE WOMEN POLICE _____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =?1?)____*







*Bismillahirrahmanirrahim*



_________sesson one ep 5?? 0??



____________?&



"Haka dai gidan Malam Auwalu suke cigaba da rayuwa yau Da di gobe a kasin haka.hardai Allah ya hore masa ya sayi fili a cikin garin ZARI'A .inda anan yake kasuwancin sa,Dan zirga zirga zirgar da yake daga qauyensu xuwa ZARI'A ai tayi yawa. Dan Haka ya yanke hukuncin ya sayi fili kawai yayi Gini. bayan ya sayi filin ya fara gi na wa anan garin ZARI'A unguwar tudun wada laying transformer.,Nan da nan Allah ya Buda masa ya fara Gina .bayan Yan watanni Allah ya bashi iKon kammala gininsa, ya tattara iyalansa suka koma ZARI'A ,.....



Haka suka cigaba da rayuwa.bayan anyaye su Ameenah da mardiya sai Allah ya kuma bawa baba asabe ciki.bayan wata uku, itama maimuna sai Allah ya qara Bata ciki.awannan Karan ma baba asabe tai ta sa Ran samun d'a namiji,sai dai Allah Mai Yi da ayi. 'ya macen dai ya qara Bata ranar suna yarinyar taci suna zaliha.akayi tsaron suna aka watse,.baba asabe sai hankalinta ya koma kan cikin maimuna ,kan me xata haifa.Dan ko kadan bataso ace maimuna ta haifi d'a namiji ita Kuma ace Bata haifa ba,haka dai kullum hankalinta atashe yake,na ganin me maimuna xata haifa.bayan watanni uku da haihuwar zaliha again itama, ummah ta haifi 'yarta mace. tofa sai alokacin baba asabe ta saki ajiyar xuciyar data ke ta dakon Riketa acan kasan xuciyar ta. ita ko ummah Babu abinda ya dameta ita har kar gaban ta kawai take,.duk Wanda Allah ya Bata tana San kayan ta....



Ranar suna yarinya taci zainab, su nan Babar malam Auwalu kenan ,wacce ta rasu tun tuni. nanfa bala'i ya qara tashi awajen baba asabe tace malam Auwalu Sam Bai kyau taba ,Dan Me ya sawa yar gidan maimuna sunan mahaifiyar sa,mugune shi azzalumi ne marar adalci,ita da ta fara haihuwa daya kamata yasa sunan mahaifiyar ta sa cikin 'ya'yanta shine baisa ba,Dan zalinci Saida ya jira ummah ta haihu sannan yasa,sbd sankai Irin nasa,da nuna banbanci.malam Auwalu Bai kula taba,Dan ya mata uxuri,kuma daga mata kafa kawai yake Yi sbd Wani dalili,haka ma ummah, haka baba asabe taita masifa kamar ta Ari Baki.masifar yau daban ta gobe daban .tofa tunda ga nan baba asabe ta Dorawa ummah da 'ya'yanta Karan tsana,ta Kuma kudiri aniyar saita dandanawa maimuna bakin cikin data Dora mata na shekaru, da Kuma San kan da malam Auwalu yake nunawa 'ya'yan ta,yake fifita yayan maimuna akan nata 'ya'yan......



Gashi Kuma bugu da qari yadda har yau malam Auwalu baya boye iya boye soyayyar da yake yiwa 'ya'yan maimuna, wannan bakin cikin da take shaqa shiyasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login