Showing 150001 words to 153000 words out of 278032 words

Chapter 51 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1097

AA Arab da rinan nun idanuwan sa.ya Sauke numfashi yace "Ahmad Aliyu Arab,ni ka kama ,Kuma yau ni kake tuhuma.....



AA Arab ya hade Rai yace"honorable sunusi MaiTama, ka san ni na sanka ba tun yau ba,ankama ka din ko ban isa bane na kama ka din ,to sai me Kuma kake San sani bayan wannan, tambayar da nai maka ita kawai nake San ka ansa min, Alhaji sunusi yay murmushi yace "baxa ka taba sani ba,sbd kai baka isa ka tilasta min fada Maka ba.AA Arab yay murmushi yace "oh really,wai kai baka saduda ba haryanxu ,wakake takama dashi ne a yanxu,? Alhaji sunusi yace kaima kasan Niko nake da Wanda nake takama dasu Kuma Nan da awa Ashirin da hudu zan fita daga cikin wurin nan kasa wannan aranka,idan ko na fita wlh saina wulakanta ka.AA ya gir girgixa kai yace "awannan Karan Kuma baka isa ba, Ayanxu zaka fadamin abinda nake tubumar ka dashi ko baza ka fada ba.Alhaji sunusi yace "Tayaya? kai ka Isa,AA Arab yace "idan baka fada cikin salama ba xaka fada ta qarfi,idan Kuma ahakan ma baka fada ba,shi abokin naka da kuke aikata barnar dashi zai fada mana,kafin Alhaji sunusi ya samu zarafin magana har an shigo da babajo Ali daga cikin dakin Dake falon,Wanda a kwana biyun nan harya fita daga hayyacinsa,.....



Baki Bude Alhaji sunusi ke kallan babajo Ali cikin mamakin shi kuma yaushe aka kama shi,har aka shigo dashi wurin nan.bayan an xaunar da babajo Ali kusa da Alhaji sunusi,AA Arab ya kalleshi yace inaso ka fadamin abun da kuke aikatawa da bakin ku,kafin ku fadamin ta qarfi . gabadaya shiru sukayi,shi Alhaji sunusi Wani Irin kallo yake yiwa AA Arab Mai wahalar fassaruwa, shi Kuma babajo Ali Yama kasa hada ido dashi, AA Arab ya dubi Wani police yace mikomin shocking din nan,cikin rawar jiki suka Mika masa ,ya karba ya jujjuya su aduka hannunsa biyu, sannan ya dubi wani cikin police din yace ku daura min su duka biyun kan kujera sannan ku dad daure su ,Babu musu sukayi yadda ya sakasu.Alhaji sunusi ya dinga tirjewa Amma Ina tuni AA Arab ya Basu umarnin su rirrikesu, da kyar suka daure su sannan AA Arab ya karbi shocking din yasa kujerar sa a gabansu ya zauna Yana kallansu ga shocking din a hannunsa fuskarsa daure yace "xaku fada min ko baxa ku fadamin ba,suka kalli juna suna mamakin AA Arab.Alhaji sunusi yay Masa Wani kallo yace"wlh baka isa ka Saka mu fada Maka abinda bamuyi Niya ba. AA Arab ya juya ya kalli Wani police yay Masa alama da ido, hakan yasa ya tafi jikin bangon falon ya yaye Wani farin Abu ,sai Wani police Dake kan Wani desk ga laptop gabansu suna latsa wa,take Wani babban screen ya bayyana,ajikin bangon . Wasu police ne suka shigo tareda Wani babban Dan jaridan gomnati da wasu camera's a hannayensu,bayan sun shigo take suka warware su ,suka sassaita camera's da wannan screen din na bangon falon suka hadu aka kunna labarai Amma live,ga Bluetooth a kunnan AA Arab suna communicating da governor jihar Kaduna,take fuskokinsu Alhaji sunusi ya bayyana akowani gidajen TV,sbd kowa ya riga da ya sani yau xa'a yiwa su Alhaji sunusi tambayoyi Kuma su ansa a idon duniya, kafin a shigar dasu kotu,kowa ya kunna TV Yana Gani, duk inda ka shiga a jihar Kaduna awannan lokacin to zaka tarar suna ganin wannan labaran sbd Abu ne da kowa kesan sani da Kuma Gani......



Masu Gani awaya ma duk sun kunna wayoyinsu, suna jiran afara .to kamar hakane suma su mamah Dake xaune a asibiti adakin da Rukayya take suma sun kunna TV Dan yau Suma sunji sanar war da akace xa'a Yi hira dasu Alhaji sunusi.shikansa governor Yana office dinsa Yana Gani shida sauran mutanan sa,AA Arab ya Kalli Alhaji sunusi ganin yadda suka fito tarwal a acikin screen din yace "honorable sunusi ta kanka zan fara duniya ce ke kallanku ,inaso kuyi introducing kanku kafin na fara jero muku da tamboyin da nake tafe dasu.kuma inason kowa ya ansamun tamboyin da xan muku cikin sauki karkusa na taba lpyrku , Alhaji sunusi Daya xubawa camera's da screen din ido Yana kallan kansu shida babajo Ali wai duniya tana kallansu ,wai yau sune aka kaskantar dasu aka wulakanta su,akan idan duniya , yau duniya su ke kallansu cikin qasaqanci,da cin zaraf, Kuma asunan masu laifi, ba 'yan siyasa ba , kamar yadda duniyar ta shaida.babajo Ali shi kansa tunanin da yake kenan xuciyarsa ta raunana,inbanda tafasa babu abinda takeyi sosai ganin Irin cin mutuncin da aka musu, Kuma wai wannan yaron Dan cikinsu shiyake tuhumaru. Alhaji sunusi zufa harta tsatstsafo masa, mutane koh sai kallan su suke ta screen din abun da suke kallo.....


AA Arab yace "honorable Kun shirya fada, Alhaji sunusi ya Kalli babajo Ali, shima babajo Ali ya kalleshi, sannan suka Kal camera's Dake daukarsu da screen din Dake jikin bangon.ganin suna batawa mutane lokaci yasa AA Arab daukar shocking din ya danna musu duka biyun kowa a hannunsa take suka fara rintse ido,suna goggocewa suna kokarin kwace jikinsu, Amma babu damar yin Hakan,Dan ba qaramin dauri aka musu ba,cikin qanqanun lokaci suka hada wata mahaukaciyar xufa, gabadaya jikinsu ya jike sharkaf da xufa tun suna daurewa har suka kasa take Babajo Ali yace cikin azabar data ratsashi "zamu fada, zamu fada yallabai"AA Arab Bai Kulashi ba,Dan so yake yaji Alhaji sunusi shima yay magana tukunna, Amma Alhaji sunusi shiru yayi,sai rintse ido kawai da yakeyi .shima AA Arab Bai fasa ba,kafin kice me babajo Ali ya fara ihu Yana sakin salati,ganin fa Alhaji sunusi bazai magana ba,Kuma yaga kamar AA Arab shi yakeso yay magana yasa ya fara jero masa Irin abubuwan da suka dinga aikatawa,ai kafin kice me mutane sun fara Salati suna tsine musu albarka,Kuma AA Arab Bai daina Abin da yake musu ba, Alhaji sunusi Saida yaga uwar bari sannan yace cikin azaba da xubar hawaye "zan fada Maka,zan fada Maka Dan Allah kayi hkr.AA Arab Bai Kulashi ba,Saida yaga suna Neman sumewa sannan ya tsaya,ya dubesu ganin yadda suke sauke numfashi ajajjere, gashi sunyi laushi, sannan ya ce"muna jinku......



Take Alhaji sunusi ya fara jero Irin abubuwan da sukeyi, idan Bai Fadi Wani abun ba, babajo Ali ya fada.abubuwa suka dinga fada naban al'ajabi,take mutanen gari Dake kallansu a live, suka girgixa da Jin wannan tashin hankalin,da Irin masifar da suka Dade suna aikatawa.bayan sun gama fadar abubuwan da suka aikata wanda mutane Basu taba tunanin xasu fada ba.AA Arab ya sauke numfashi ya?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
ce shima cikin mamaki "meyasa kuka xabi daku cutar da mutanan da basuji ba Basu Gani ba ta wannn hanyar?sukai shiru ,AA Arab ya dauko shocking din alamar zai qara musu idan Basu fada ba,take sukai saurin hada baki, wajen fadin muna da Dalilai,Shi Alhaji sunusi yace tun Yana , matashin sa yake aikatawa Dan shima koya yayi awurin su yallabai taju, anan suka hadu da babajo Ali,Dan su din yaran sune tun kafin su shiga siyasa,Alhaji sunusi ya cigaba da fadin Kuma ba iya a jihar Kaduna mujeyi ba tun ASALI a qasa Baki daya mukeyi,Dan sai hawan wannan governor na yanxu ma yasa muka fara farmakar kuduna ,muke sawa ake qauyukan jihar kuduna, sannan bari na fada Maka Wani Abu yallabai taju shiyasa aka fitarka daga kasar nan sbd kanason tona musu asiri"AA Arab yay murmushi yace ni nasan da wannan,bashi nake tambayar kaba, ka bani ansar abinda nake tambayar ku.Ina Jinka, Alhaji sunusi yace cikin azaba " bugu da qari Kuma abinda yasa na fara kawowa jihar Kaduna Hari , ko nace nake sawa ake shiga kauyukan Kaduna ake kai hari sbd governor, shine yasa na kusan faduwa takarata ,badan shugaban jam iya yay ruwa yay tsaki ba da baxan taba samun kujera taba ,to wannan abun daya mun shiyasa na kulla ceshi azaciya ta,tun daga wannan ranar nace wlh saina kunta ta masa saina sa mutanen gari sun tsaneshi yadda zai kasa sukuni ya kasa samun kwanciyar hankali a cikin mulkin nasa,ta yadda Zabe me xuwa Bai isa ya ciba.AA Arab ya xubawa Alhaji sunusi Ido Yana Jin wannan hassadar dayake yiwa Wani bawa ta kaishi ta baro shi,AA Arab ya ce "to idan kun dauki yaran Ina kuke kaisu? Alhaji sunusi ya sunkuyar da kansa qasa ya kasa magana.....



AA Arab yace cikin tsawa "ka fadamin" Alhaji sunusi yace kasar muke bari dasu",AA Arab yace "eh nasan kasar kuke bari dasu to wacce kasar kuke kaisu? Alhaji sunusi yace can kasar Paris muke kaisu suke siyansu ,mu kuma idan suka siya su bamu kudin.AA Arab yace "yanxu idan Kuka kaisu me suke musu? Alhaji sunusi yace "wannan ne Kuma ban saniba, AA Arab ya sauke numfashi yace " shima Kun sani xan dawo gareshi ne, Amma kafinnan ka fadamin yanxu akalla Yara nawa Kuka dauka, tun farkon farawarku xuwa yanxu iya na jihar kuduna, Alhaji sunusi yace sama da Yara miliyon Daya,iya na jihar Kaduna,AA Arab yace" cikin mamaki yanxu ku idan aka Raba ku da naku 'ya'yan xakuji Dadi?sukai shiru, AA Arab ya cigaba ya ce"a Faris din wadanne mutane kuke Saidawa na tabbata kunsan su, Kuma wlh sai Kun Nemo mana su, Alhaji sunusi yace mu bamu sansuba hadamu kawai akai dasu muke, communicating,AA Arab yace "wannan Kuma ku kuka sani Amma karyane ace wai bakusan suba,wlh sai kunne mona su,ko Kuma mu muje har,qasar taso anemo mana su....



,yace Abu na gaba Kuma meyasa ka sace 'yar Dan uwanka AIG umar MaiTama,wato Rukayya umar MaiTama?,Mai tai Maka ,?itada shahararran Dan jarida ibrahim Khalil, meyasa,? Alhaji sunusi yace ko kunya Baijiba "shiga gona ta tai ita da wannan Dan jaridan, Kuma dama na mata warning taki ji, shiyasa ita da shi Dan jaridan na daukesu,AA Arab ya ce Inaso kafada mana dalilin dayasa kai Hakan ,da Kuma inda ka kaisu tsawan kwana kinnan sannan Meka aikata musu,wlh idan ka boye Abu Daya saina sumar dakai, Nan alhaji sunusi ya fada musu komai,da Irin axabar Daya dinga gana musu. take mutanen gari Dake kallansu bayan sun gama Jin abinda ya fada wasu harda hawaye wasu Kuma xuciyoyinsu sun raunana,suna mamakin xuciya Irin ta Alhaji sunusi wacce babu digon imani acikin ta.aka dinga zaginsu shida lateef,AA Arab ya dubi Alhaji sunusi yace "Kuma duk wannan wahalar dakai ka_yi abanxa domin saimun biwa yarinyar kadinta SHikansa Dan naka, Wanda kake Yi Dan shi din mun kama shi , yanxu haka Yana tsare nan cikin heardquater.Abu na karshe da nakeso ka fada duniya ta sani shine kace Kaine ka kashe 'Dan uwanka AIG umar MaiTama,haka ka fadawa 'yarsa agabanta, da akuma gaban Ibrahim Khalil, sannan Nima da kunne na naji,ka Fadi yadda akai ka kashe shi,so inaso yanxu ka Mai maitawa duniya abinda ka fada ta sani .take Alhaji sunusi ya shiga shock Dan Bai taba tunanin xa'a masa wannan tonon silulin ba , wannan tambayar tayi tsauri ,yasan dama tunda Rukayya ta kubuta daga hannunsa dole saita fada , meyasa tun farko ma Bai kashe taba, Amma Bai dauka duniya xata sani ba,AA Arab yace "muna sauraronka, ka fada mana kowa yaji? Alhaji sunusi ganin AA Arab yau bazai kyaleshi ba yasa ya fara maimaita abinda ya fadawa Rukayya jiki na rawa.take mutane suka qara shiga tsantsar mamakin bakin hali da mugunta Irin na Alhaji sunusi,AA Arab yace "Wani Irin Abu yay maka da har ka zabi daka rabashi da duniyar?Alhaji sunusi yace "wannan Kuma bazan iya fada muku ba iya abinda xan iya fada muku kenan".....



AA Arab yace "baka isa ba, ka fada mana dalilinka na yin Hakan? Alhaji sunusi ya rasa ya xaiyi ganin AA Arab ba shirin qara Dora masa shocking yasa yace "sbd yace lallai sai doka tayi aiki akaina,ni Kuma naga baxan taba bari asirina ya tonu ba gara na rabashi da duniyar in yaso saina ga Wanda zai tonawa asirin.AA Arab idansa ya kada yay jajur haka ya juya ya kalli camera yace cikin dauriya"Assalamualaikum masu kallanmu na tabbata yanxu dai kunriga da kunji komai,ko nace kila kadan daga bakin Wanda ya kamata kuji,nasan Kuma kunsansu tunda su din shahararran Yan siyasa ne,Wanda suka Dade suna fafatawa tun a gomnatin baya,Kuma yanxu nasan kun fahimci sune masu ta-da mana da tashin hankali acikin jiharmu,Wanda suka Dade suna zalintar mutanan da basuji ba Basu Gani ba,mu daga nan kotu xamu turasu ayanke musu hukunci, sannan abiyawa kowa hakkinsa, Suma yaran nasu duk mun Samu nasarar kamosu suna nan cikin heardquater, dukkansu babu Wanda zai Sha in Sha Allah,kuma gabadaya xamu turasu kotu.sannan idan Allah ya kaimu da daddare governor zai fito yay magana ,so na barku lpy,daga haka AA Arab ya mike adai dai lokacin Kuma da aka tsaida camrori,Aka dauki su Alhaji sunusi aka maidasu inda suke,AA Arab ya fita daga wajen ma gabadaya.....


___________?&


Abangaren mutanan gari kuwa ,bayan sun gama Jin wannan tashin hankalin.tab hankulansu ya tashi ba kadan ba,Dan Basu taba gani ko Jin tashin hankali Wanda ya girgixa su Irin na wannan ranar ba, sunga mutane marasa imani,masu San xuciya,da San duniya kamar bazasu mutu ba,tuni aka hau Allah Wadai dasu Dan wasu marasa Jin magana ma har sun hada tawaga zasu nufi duk inda sukasan gidajen dasu Alhaji sunusi suke ginasa just for Kadara,da kamfanu nuwansu,da plazas dinsu,sun xari fetur dasu ashana sun tafi xasu Kona su.abangaren Hajiya SA'A ta shiga Tashin hankali ba kadan ba,Dan ta nemi number lateef sama ko kasa taki shiga,tayi Kiran abokansa sunce bayanan Basu San inda yake ba,ta shiga social media taga sai zancen ankama Alhaji sunusi ake da Kuma Irin mugun laifukan dasuka aikata shida babajo Ali, duk inda ta shiga hotonan su Alhaji sunusi ne kawai yake yawo amatsayin masu laifi,jiya dakyar tai bacci sbd Tashin hankali.bata taba shiga tashin hankali Irin wannan ba, tunda take....


yanxu ma haka tana xaune ne a main falorn gidan waya ce ahannu tunda ta tashi yanxu gashi karfe Sha Daya na safe Abu Daya take shine,Kiran wayar lateef hartayi ta gaji ta kasa jurewa harda hawayenta, hankalinta in yayi dubu to ya tashi,kasa jurewa tai Dan wlh har Bata_san ta kunna data ta hau media taga abinda ke faruwa ba , saidai tai ta jujjuya wayar ko Kuma tai trying number lateef,amma Abu Daya ake fada mata wayar akashe.kamar Kuma wacce aka tsikara kawai ta kunna data ta hau face book tana scrolling kawai cin karo take da hotunan Alhaji sunusi da babajo Ali,da Bata san Gani ,Wanda har Yanxu ta kasa yarda da abinda ake ta fada akansu,take ta tsaya cak ganin yin Arba da hotunnan lateef datai amatsayin shima ankama shi tun jiya sakamakon yaywa wata yarinya fyade,ada Kuma akamashi Amma ubansa ya banxatar da xancen ya karbo shi daga hannun hukuma ta karfi da yaji, yanxu haka shima Yana hannu ankama shi,Yana tsare a headquarter take Hajiya SA'A ta jefar da wayar Hannunta Dan batama tsaya qarasa Karan ta abinda aka rubuta ba,ta toshe bakinta sbd kukan Daya zo mata,ta mike tsaye ta hau fadin ta shiga uku ta lalace,yanxu shikenan Babu uban Babu 'Dan,d'anta shikadai take dashi aduniya gashi shima ankama shi ita yanxu ya zatayi tuni ta haura sama Dan dauko mayafinta ta tafi heardquater din......



Abangaren su mamah kuwa,ba karamin kaduwa sukai da abinda Alhaji sunusi ya fada sukai ba,bayama akan yadda ya kashe wa 'ya'yan ta mahaifin su,ita Kuma ya kashe mata miji,Wanda baijiba Bai ganiba,Ashe mijinta ba mutuwar Allah da Annabi yay ba,Ashe Kashe shi akayi,kisanma na wulakanci Kuma 'Dan uwansa uwa daya uba daya, shiya aikata masa wannan zalincin.innalillahi wainna ilaihi rajiun, wannan wanni Irin maciface,wlh baxata taba yafewa Alhaji sunusi ba, dole ma abi mata kadinta ita da 'ya'yanta, gabadayansu kuka suke har mazan Saida suka xubar da hawaye ganin Irin yadda Alhaji sunusi ya bayyana Irin mutuwar da mahaifin su yay, ruky tana rungume jikin mamah sai kuka take gwanin ban tausayi,babu abinda kake ji adakin nan sai sheshshekar kukansu_ su matan.take mamah ta tuno Irin rayuwar da sukayi itada 'ya'yan ta da Kuma mijinta uban 'ya'yan ta ,Wanda har yau ta kasa mantawa da mutuwar sa, indai zata tuno da mutuwar dawo mata take sabuwa,ji take kamar alokacin abin ya faru.......




*ASALIN labarin iyalan gidan AIG UMAR MAITAMA da iyalansa*






07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*_____NAJA'ATU UMAR FAROOQ _____*




*____(MRS SARAKIES)____=?1?*




*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season two ep 6?? 3??



____________?&


AIG umar MaiTama ASALIN su dama 'yan ASALIN jihar Kaduna, unguwar sabon gari, sunan mahaifin su Muhammad MaiTama, mahaifiyar su Kuma sunan ta Bilkisu.iyayensu su hudu kadai suka haifa aduniya,biyu Maza biyu mata,to matan tun suna Yara banyan an yaye su suke rasuwa,sai ya xamto su biyu Maza kawai Allah ya barwa iyayensu.umar da Kuma sunusi. Kuma tsakanin UMAR da sunusi akwai tazarar shekaru atsakanin su,Dan akwai mace a tsakaninsu tun tana qarama Kuma ta rasu UMAR ya baiwa sunusi tazarar shekaru akal ba'a kasaru ba shekaru bakwai, sannan aka haifi sunusi.shi dama umar tun Yana Dan saurayi baifi shekaru goma Sha biyar aduniya ba yake San aikin damara,bayan ya gama secondary school kuma saiya nemi aikin damarar,ya nemi shawarar iyayensa suka amince masa,ya samu duk ya cike Irin su police, army, custom, emigration da sauran su,to sai Allah yasa rabonsa a aikin police din yake , Allah cikin ikonsa Kuma sunansa ya fito,suka xana jarabawa.da sukai jarabawa results ya fito saiya samu suka tafi training....



Shi Kuma sunusi dama can Allah ya yishi baya ji,baya Jin magana ko kadan , bashida aiki sai biye biyen abokan Banxa,ga baya Neman na kansa,Dan makaranta ma da kyar yayi Junior,iyayensa Sunyi fadan sunyi nasihar Amma bayajiba ,har ya kai ya kawo sun kawo Ido sun xuba masa.sai Kuma Allah yasa masa San siyasa aransa,Kuma ita siyasa Saida ilimi nan nefa ya dage ya kammala secondary school.alokacin daya kammala alokacin shikuma umar ya dawo daga training aka turashi cos Adamawa,farkon albashinsa gabadaya iyayensa yay wa hidima dasu,Kuma sai wlh ya Dora masa San Dan uwansa sunusi aransa, Amma shi sunusi kwata kwata Bai damu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login