Showing 225001 words to 228000 words out of 278032 words

Chapter 76 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1084

kawunnansa sanzo da wuri ,yanzu haka ma suna falon Abba ne a zaune suna tattaunawa,...


A bangaren gidan su Ruky kuwa baba hasiya da "
'ya'yan Hajiya Maryam (maman Shareef)Wanda suke AURE anan garin kaduna sunzo Taya Baba hasiya girki suna a kitchen suna har had'a kayan da za'a tarb'i Bak'in dashi, abinci ne da kayan snacks Wanda za'a tarb'i Bak'in dashi, kawunnan ruky da baffan nin ta Wanda suke cousin da Baban ta, suma suna hanya zasuzo da ajima kasan ake Saka ran zuwansu,ruky tana gidan su Hanan Dan can ta tafi ,tace ita kunya take ji bazata ya iya zama agidan ba,....


Yanzu haka suna tare da Hanan a gidan su wajen k'arfe uku na Rana, suna Zaune a d'akin Hanan,ita ruky tana kwance a kan gadon Hanan tai lamo da ita kamar wata Mai bacci kuma ba baccin take ba haka kawai jinta take jikinta gabad'aya ya mutu muss kamar wacce akyiwa duka saboda Fargabar da takeji ga Wani irin zazzab'i dake nefan rufeta ta .


Hanan ce ta shigo d'akin hannun ta d'auke da plate na abinci ta ajiye plate d'in abincin nan tsakiyar d'akin ta k'arasa bakin gadon ta zauna tana kallan Ruky da mamakin yadda tai Wani laushi lokaci D'aya,ta tab'o tace .


"Ke taso muci abincin", ta fad'a tana kallan Ruky.


Ruky ta juyo da fuskar ta tana kallan hanan sannan ta girgiza mata kai , alamar ta k'oshi,

Hanan ta harareta kafin tace .


"Waike Dan Allah miye Hakan tunda kika zo gidan nan gabad'aya kin Wani takure waje D'aya sai kace wacce ake kyara,wai Dan Allah miye Hakan", ta fad'a cikin takai ci.


Ruky ta mik'e Zaune days kwancen da take da k'yar tana kallan Hanan kafin ta kamo hannun ta ta marai raice fuska tace .

"Wallahi Hanan gabad'aya sai naji dama kawai a fasa auran nan, Dan wallahi jinai gabad'aya kamar bazan iya auran nan ba", ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa.


Hanan ta harareta cikin takaice ,kafin tace.


"ke wallahi kinma Raina mini hankali ni banasan gulma da muna furci, naga ke da bakinki kika ce kin Amince to Kuma sai yanzu ne zaki Wani ce kin fasa saboda gulma Irin taki,da lokacin Kuka fara soyayyar na sani,ai Baki fad'a min ba, saboda soyayya tai Dad'i, shine kuma yanzu Dan gulma zaki cemin kin fasa", ta fad'a tana ture Hannun ruky daga nata.


Ruky ta fashe da kuke tace.

" Haba Hanan keda zaki fi kowa fahimta ta amma kece mai juya min baya shikenan nagode wallahi Dan ba ke bace a situation d'in da nake shiyasa zakice haka", ta fad'a tana k'ok'arin juyawa hanan baya, jikin Hanan yayi sanyi dan ita wallahi d'aukar ta ruky pretending ne kawai take Bata d'auka da gaske take ba,tana dariya tace.


" sorry Mrs Ahmad ni wallahi ban d'auka da Gaske kike ba",ta fad'a tana rik'o hannun ruky wacce ke k'ok'arin k'wace Hannun ta, kafin tace cikin kwantar da ruky hankali.

"Haba sis miye Kuma haka?, bangane ma wai kin fasa auran ba , haba ruky wannan wanni Irin magana ce kikeyi", ta fad'a tana kallan Ruky.


ruky ta d'ago da idon ta tana kallan Hanan kafin tace.

"Wallahi Hanan ji nake yanzu gabad'aya hankali na ya tashi Wani Irin fad'uwar gaba nakeji da bansan dalili ba,ga Kuma tsoro na shiga ta", ta fad'a tana goge hawayen daya gangaro mata saman fuskarta.


Hanan ta saki Baki tana kallan Ruky da mamaki azuciyarta tace eh lallai ruky Autanci har yanzu bai gama sakin taba, afili Kuma sai ta qara kwantar da murya kafin tace.


"Ruky Hakan normal ne ga ko wacce mace indai har akazo Neman AURAN ta kowa da kalar yanayin da yake ji , Amma Hakan ba komai bane kiyi hak'uri ina Mai tabbatar miki in Sha Allah zaki daina nan Bada dad'ewa ba,sai Kuma tai saurin cewa "ke nama Baki daga nan zuwa gobe zakiji komai ya dawo miki normal in Sha Allah",ta fad'a da sigar lallashi tana kuma murmushi .


Ruky ta sauke numfashi tace.

"Anya ko Hanan zan daina?wallahi Dan bakisan me nake ji bane shiyasa",Hanan tace.

" nasani Amma ruky daurewa zakiyi ,ko ya Ahmad d'in ne bakya so yanzu ta fad'a tana kallan ta.


Ruky ta harareta kafin ta juyar da kanta gefe, Hanan tai murmushi tace .


"muna fuka Ashe dai kina Son nashi shine kuma kike Wani ke kaza ke kaza,ai dama nasan duk na muna furci ne wayasanima ko acikin zuciyarki murna kike kamar me",ta fad'a tana hararar ruky.

Ruky ta d'auki filon kan gadon ta wullawa Hanan tana murmushi.hanan tai saurin yin baya tana dariya, ruky Bata samu Hanan ba ta goce shine ta samu bangon d'akin ,tana kallon Hanan tace .


"Wallahi zan kama kine Muna fuka",

Hanan dai dariya kawai take kafin ta koma k'asa kan carpet d'in d'akin inda ta ajiye musu abincin tana kallan Ruky tace.


"Lallai ma ni bance miki Muna fuka kaba har kece zaki cemin muna fuka ,Kuma Idan kin huce to Sakko muci abincin?",


Ruky tace."Anki din", ta fad'a tana hararar Hanan.

Hanan tace.

" dallacan ki sauko ko Kuma wallahi na fita na fad'a wa ummah ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa,ganin haka yasa ruky ta sauko suka zauna a k'asa suna cin abinci Hanan tana tsokanar ta,Saida suka gama ci sannan Hanan ta Mik'e ta fita Dan mayar da plate d'in kitchen, ruky ta mik'e ta koma saman gadon ganin wayar ta na kawo haske alamar k'ira, Koda ta duba taga AA Arab ne ke K'iran ta take gaban ta yay Wani rin fad'uwa ta ayyan aranta kardai ace har sunje masu Neman auran, ta fad'a tana dafe k'irji,wannan tunanin da tai ya K'ara tsurar da ita tana ganin wayar tana tana ta kawo haske Amma ta kasa picking,haka kawai yau dai ta tsinci Kanta da k'in picking call d'in nasa.,harta gama ringing batai picking ba,ya K'ara k'ira nan ma ta zubawa wayar ido tana Jin Fargabar yin picking call d'in.



___________?&


Wajen k'arfe uku da Rabi kawunnan su ruky sunzo har an sauke su a falon Bak'i ankai musu abinci da ruwan Sha da lemuka, bayan sun huta su mamah suka shigo suka gaisa sannan suka tafi,wajen k'arfe hud'u da Rabi bak'i suka iso,masu gadi suka wangale musu gate manya Mayan motocine guda uku suka shigo cikin compound d'in gidan, keda kin gansu kinsan lallai akwai dukiya atare dasu Babu k'arya,..

Sannu a hankali suka fara fitowa daga cikin motar bayan sunyi parking,manya manyan mutane ne cikin manyan kaya , mutane biyu cikin kawun nan su ruky suka fito Dan tarbar su,suna musu barka da zuwa suka ansawa cikin sakewa suma,suka musu jagora har zuwa cikin falon Bak'in Wanda ya ke gyare tsaf sai tashin kamshi yake Yi.


Bayan sun shiga Suka Zauna suka gaisa cikin girmamawa,Saida suka gama gaisawa sannan aka gabatar musu da abinci suka ce sun k'oshi, Basu ta kura musu ba ,zasu bari idan sun gama abinda ya kawo sun sa Rakasu dashi ko zuwa motane ...


Baffan nin AA Arab Suka gabatar musu da kansu a matsayin masu ne mawa Ahmad AURE, su kuma suka amince sannan suka fito da kud'i naira million D'aya amatsayin kud'in AURE sai dubi Dari biyar kud'in tambaya sannan ma aikatan gidan suka
Shigo da katan kayan katan d'in ruwa da lemuka da kwalayen biscuits Dana chocolate,Wanda daga gidan su AA Arab ska zo dashi haka suka zube musu kaya kamar Wanda za'a Bud'e D'an k'aramin shop, sannan suka neme a tsaida ranar AURE, kawunnan ruky sukace su zab'i duk lokacin Daya musu ,suma sukace a'a su su fara yankewa,sukace a'a ganin dai ambasu Basu wuka da nama Kuma dama sun gama yankewa tun agida yasa sukace to sun yanke nan da sati twakas wato wata biyu , Babu musu sukace to sun amince , kawunnan AA Arab sunji Dad'i da suka ce su yanke ranar AURAN Dan dama Abba wata biyu yace musu,sai gashi Kuma fad'uwa tazo dai dai da zama .


Bayan sun kammala
suka musu godiya sosai sannan sukai shirin tafiya suka Rakasu har gaban motar su ,sukai sallama cikin aminci bayan ankawo musu kayan da aka musu parkeging Wanda zasu tafi dashi Suma haka dai suka Rabi cikin girmamawa...


A b'angaren ruky kuwa tun da AA Arab ya k'ira ta batai picking ba,har yanzu,sama da awa biyu ,sai yanzu Daya K'ara k'ira yanzu ma Dan Hanan ce ta lura da haka Dan haka tana kallon ruky tace .


"Ruky ba K'iran ki akeba ki d'auka mana", ta fad'a tana lek'a wayar, ganin AA Arab ne yasa Hanan tace "ke shine fa miye Hakan Dan Allah ki d'auka,ta fad'a tana mik'a mata wayar,ruky ta girgiza kai Hanan tai picking tasa handsfree tana Jin yadda AA Arab ya sauke ajiyar zuciya kafin taji yace .


"Fiancee why didn't picking my call",ya fad'a cikin damuwa.


Hanan na Jin haka ta zaro ido waje ta ajiye mata wayar kan cinyar ta_ ta matsa baya tana Jin yadda yake yiwa Ruky magiya , Amma ruky tai shiru tak'i magana, Hanan ta harari ruky da rok'on ta da ido akan Dan Allah tayi magana ,ruky ta d'auke kanta daga kallan Hanan, Hanan dai ta cika tai fam ganin Ruky tak'i magana tai mata tai shiru sai Kuma daga baya taji tace .


"Uhmm"

AA Arab yace "say something please",


Ruky tace "babu komai fa".

AA Arab ya sauke numfashi kafin yace .

"Gabad'aya fiancee Kinsa na shiga Damuwa ma d'auka laifi nai miki da kika k'i picking call d'ina ,Kinsan d'azu Kiran me nake miki kuwa?" Ya fad'a Yana jiran ansar ta

Ruky ta girgiza masa kai kamar Yana gabanta, Amma Batai magana ba ,shima ganin yau mulki take ji dashi yasa Bai takura Mata ba,ya cigaba Yace .


"Dama zan fad'a miki ne CEWA antafi nemar min AURANKI,shine kuma baki picking can d'in ba ,gashi yanzu har sun dawo,nan ma ruky tai shiru tana sauraran sa.


AA Arab ya cigaba yace .

"Albishirin ki",ya fad'a Yana murmushi ,


Ruky tace ."goro cikin k'asa da murya.


AA Arab yace.


" kinsan an bani AURANKI",ya fad'a yana jin Wani shauki da annashuwa aransa,..


Ruky ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta,tana Jin Wani Abu ya doko zuciyar ta Mai nauyi .

Jin yayi shiru yasa AA Arab yace cikin damuwa.


" Fiancee please kiyi magana mana ko bakiji Dad'i bane",ya fad'a cikin damuwa,

ruky tai dauriyar fad'in a'a a k'asan mak'oshi.


AA Arab yace .


"Why can't ' not talk",.

ruky tai shiru nan ma ,yace "ko kunyar ce haryanzu?", ta gyad'a masa kai sannan tai k'asa da murya ta ce

"Uhmm", a k'asan mak'oshi,

AA Arab yay murmushi kafin yace .


"Zakiga kunya yarinya",ya fad'a Yana Wani cije leb'ensa",


ruky ta tura Baki gaba cikin shagwab'a tace.

" nidai ka daina",


AA Arab Yay murmushi kafin ya kauda maganar wurin cewa .


"har yanzu kina gidansu Hanan d'in ne?",


Ruky ta gyad'a masa kai kafin tace.


"Eh".


AA Arab yace .


"Ok Yaushe zaki koma gida?",

Ruky tace "anjima in Sha Allah".


ya ce .


"Ok ki bari zanzo na d'auke keki ",

Ruky tai shiru kafin tace.


"Da ka barshi zanma iya komawa",ta fad'a cikin fad'uwar gaba Dan Allah ya Gani kunyar sa take ji ga Kuma tsoronsa da take ji.

AA Arab yace .


"Nidai zanzo ",.

Ruky ta sauke numfashi tace.


" shikenan".


AA Arab yay k'asa da da yace.

"Thank u ,fiancee,Kuma amarya ta" ya k'arasa fad'a yana murmushi,

Ruky ta rufe fuskarta tana Murmushi itama,da haka dai ya dinga janta da hira sosai har dai ta saki jikinta dashi sosai tun suna hira tana nok'ewa har dai ta ware ganin ana K'iran sallahn magrib yasa ya ce bari yaje yay sallah,ruky tace.

" to" yace kuma bayan sallan isha'i zai zo ya d'auke ta da haka suka rabu.....



Tana Sauke wayar ta sauke wata wawuyar ajiyar zuciya,adai lokacin da Hanan ta shigo d'akin,tana kallon ruky ta harareta tana cewa.


"Wallahi abinda kike kiwa yayana sai Allah ya Saka Masa ,ya za'a Yi Dan wulak'anci kiyi ta Raina masa hankali da ja masa ra'ayi haka ,bayan kina sanshi kina kuma kaiwa kasuwa ,kuma Dan sabon wulakanci ga shi Yay ta k'iranki Amma kik'i d'aga wayar sa ,saboda samun waje koh?, Allah ubangiji ya D'ora miki sanshi kamar yadda yake Miki Kiji idan da Dad'i abinda kike masa,ta k'arasa fad'a tana k'ok'arin shiga toilet Dan yin alwala,


Ruky tai murmushi kafin tace.

" To Masu Yaya ,anyi d'in ko zaki hanane Kuma kisa aranki yanzu na fara ma da wayace yace Yana son nawa", ta fad'a tana hararar Hanan sai Kuma tace "kai Inama ban Amince ba naga yadda zakiyi kuma dole Amin biyayya,ta fad'a tana hararar Hanan.

Hanan ta juyo tace ..

"Wannan Kuma ke kika sani naga yanzu Ina bakin k'ofa kafin na shigo naji kin saukar da kai kina soyayya 'yar rainin hankali sai anyi magana kice Wani nan ke kin fasa auran,aini yanzu na daina yadda Dake tunda ke tattabara ce ba'a Gane inda kika dosa", ta fad'a tana k'ok'arin shiga toilet d'in, ruky tai dariya tace .


"Wallahi Hanan ke muna fuka ce Ashe lab'e kikemin ,hanan tana toilet tana jinta tana dariya k'asa k'asa,harta fito ruky tana mita kafin ta mik'e itama ta shiga San d'auro alwalan....





Ruky suna tsaye a falon gidan su Hanan tanayiwa maman Hanan sallama,suka fito har k'ofar gidansu Hanan inda suka tadda AA Arab Yana cikin motar sa Yana jiran ta, Hanan ta zagaya inda yake ta risina tana kallansa tace .

"Good evening sir"ta fad'a tana murmushi.


AA Arab ya ansa mata yana murmushi Shima,yana tambayar Hanan gida da mutanan gida,ta ansa masa cikin girmamawa, kafin tace.

" congratulations sir" ta fad'a tana murmushi,AA Arab ya shafa kansa yace .

"Thank u Hanan".

Basu Dad'e ba Sukai sallama da Hanan, hanan tana d'aga musu hannu sannan ta koma gida....





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 8?? 9??



___________ ?&


Suna hawa kan titi ya juya Yana kallan Ruky data sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da zoben hannun ta,Dan gabad'aya jinta take a takure ,Yana kallan ta dakyau yay k'asa da murya yace.


"Fiancee!",


Ruky ta d'aga kanta ta dubeshi Amma Batai magana ba.


Yace .


"Meya faru ne?",Ya fad'a Yana kallan ta ,

ruky tace cikin sanyin murya.


"Babu komai",.


Yace "no ban yardaba ,why are you so silent ", ya fad'a Yana tsareta da mayun idanuwan sa.


Ruky tai murmushi tace .


"Nothing ",

Yace ."ok tunda babu komai bani labari ",ya fad'a yana kallan gabansa.

Ruky tace .

"Wani irin labari?".


Yace. "Koma wani irine abani Inaso", ya fad'a Yana k'ok'arin Shan wata kwana.


Ruky ta rausayar da kai tace.


"Ni bani da Wani labari ",

Yad'an Bud'e ido kafin yace "really ",

???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?
Ta gyad'a masa kai,ya jinjina kai yace "to ni bari na baki",


Tai shiru tana kallan sa idansa akan titi yace.

"kinsan yaushe aka tsaida ranar Auren",

Ruky ta kalleshi ta ce .


"Wai kana nufin kace har an tsaida ranar Auren", ta fad'a tana kallan sa


AA Arab yay murmushi yace "wannan tsoron fa Daya fito a fuskar ki haka",ruky ta juyar da kanta tace .

"Wani Irin tsoro kuma?",


Yace "gashi ya bayyana har Asaman fuskarkarki ",ya fad'a Yana murmushi,


Ruky ta kalleshi tace."ni babu Wani tsoro Daya bayyana a saman fuskata ",ta fad'a tana tura Baki gaba.


AA Arab ya ce "alright I understand,to wata biyu akasa bikin ya fad'a Yana murmushi,


Ruky ta kalleshi da mamaki kafin tace .


"Ai yayi kusa".


AA Arab ya zaro ido waje yace "oh damma ba'a sa wata D'aya ba aini San samuna wata D'aya za'a Saka bikin Dan wata biyu ni yamin nisa ",ya fad'a Yana tsuke fuska Irin shi ba haka yaso d'in nan ba kafin Kuma ya kashe mata ido D'aya.


Ruky ta harareshi kafin tace "ai ko da saidai kanemi wata matar Amma baniba, Wani Irin wata D'aya sai kace ana gaggawa",ta fad'a tana Wani tura Baki gaba.


AA Arab yay k'asa da murya yace "eh mana Baki sani ba aini gaggawa nake,ko Baki Gani a yanayi naba",ya fad'a Yana Wani narke mata.


ruky ta harareshi batai magana ba,Dan wannan abun dai yafi k'arfin ta,


Ya cigaba yace "uhmmn Mai yasa bazaki tausayawa min bane ,nifa bari Kiji na fad'a miki gaskiya a matse nake , wallahi so nake kawai na ganki a gidana wai Baki ga yadda na rame bane Kwana biyun nan",ya fad'a cikin Wani yanayi.


Ruky ta juyar da kai gefe tace "Allah nidai ka daina banaso kai Mai yasa bakajin kunyar fad'ar ko Wacce Irin magana ne",ta fad'a cikin shagwab'a,AA Arab da har ya fara Neman barin nutsuwar yace cikin wata iriyar murya wacce ruky Batasan shi da itaba.

"please fiancee nace ki daina min wannan shagwab'ar wai bakisan me nake ji bane shiyasa", ya fad'a Yana damk'e stiarin motar.


Ruky tai shiru tana Jin gabanta na fad'uwa ita Batasan ma Wani tsautsayin ne yasa ma ta yarda yazo d'aukar taba.haka kowa yay shiru a motar kowa da abinda yake sak'awa a ransa har suka isa unguwar su Ruky malali.


Yana yin parking a k'ofar gidan ruky,ruky tasa hannun zata Bud'e motar kamar ya sani yasa lock,ya tsaya yana kallanta.ruky ta Murd'a taji a kulle ,ta juyo Batare da ta kalleshi tace.


"Please ka Bud'e min na fita nagode",ta fad'a tana Wani tura Baki gaba,

AA Arab ya k'urawa D'an k'aramin bakinta ido Yana kallan bakinta da Yay maganar Allah ya Gani Yana D'aya daga cikin abinda yake K'ara zautar dashi a duniyar soyayyar ruky.ganin yak'i magana yasa ruky ta d'ago tana kallan sa taga kallan ta yake ,idon da suka had'a da abinda ta hango acikinsu ne ganin yadda suka sauya launi lokaci D'aya Hakan yasa ta tsorata.

Jitai yayi magana da shak'akk'iyar murya yace.


"Fiancee!".

Ruky tai sunkuyar da kanta k'asa tace .


"Uhmm",


Yace "d'ago ki Kalleni "ya fad'a Yana tsareta da idonsa Wanda ya sauya launi daga fari zuwa jaa.


Ruky ta girgiza masa kai alamar bazata iya ba.

Ya juyo Yana fuskantar ta yay k'asa da murya yace .


"Meyasa?".


Tace "bazan iyaba ",


AA Arab yace .

"Zaki iya,please ki d'ago ki kalleni ko zaki iya ganin abinda nake ji game Dake ",


Ruky ta girgiza masa kai tace "bazan iya ba ",

Ya kamo hannun ta Yana kallan ta ,Hakan yasa ruky ta kalleshi a firgice kafin tai Wani yunk'urin ya kai hannun nata bakinsa yay kissing,ai take ruky ta rikice tace .

"Please sir ka bari miye haka Babu kyau fa",ta fad'a arazane tana k'ok'arin k'wace Hannun ta , Amma Ina rik'on da AA Arab yay wa hannun ta yafi k'arfin ta k'wace,yace cikin wata iriyar murya da Batasan shi dashi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login