Showing 90001 words to 93000 words out of 278032 words

Chapter 31 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1049

zaliha ta mike taje ta Dora ruwan zafi,saida ta jira ya tafasa sannan ta juyoshi adan plastic sannan ta dawo dakin , alokacin ne Kuma taga fitowar ummah daga dakinta cikin shirin fita,zaliha ta bita da kallo sannan ta shige dakinsu,ta samu baba asabe tana rike da wuya har lokacin,ta qarasa ta aje ruwan gaban baba asabe, tace gashi Babar mu,baba asabe tace dauko wancen Dan kwalin nawa kixo ki dunduma min,babu musu zaliha ta dauko,baba asabe ta sauke hannunta daga wuyanta,hakan bama zaliha damar ganin inda baba asabe ke rikewa ya Dan kumbura kadan,cikin xaro ido waje zaliha tace wayay miki wannan abun haka babar mu,....



Baba asabe dakyar tace idan baxaki Yi abinda nace kiminba kibarmin kayana ,banasan wannan tambayar zaliha ,sai Kuma tace bigewa nai jiya dazan shigo daki, zaliha tace shikenan bari nai miki ta tsoma Dankwalin cikin ruwan zafin, ta fara dundumawa baba asabe Wacce Dan azaba ,sai cike lebe take Amma Kuma Batasan tai ihu Wani yajita, Amma wlh zafi takeji,anya ko maimuna ba maiya bace,yo inba maiya bace, ai baxatace xata kashetaba,sbd ta kashe tanfa tai mata wannan shakar,Amma Kuma wlh saita rama,dan ita xuciyarta xatai ta Kona mata,bayan angama ta Dan shafa wajen jin yadan rage kumburin, Kuma yadan rage xugin,yasata cewa zaliha ta bari haka, zaliha ta mike takai plastic din waje sannan ta Shanya Dan kwalin shima sannan ta dawo dakin tai qasa da murya tace babarmu Kinga can ummah maimuna tayi shiga cikin shiri Kuma Inaga fita xatayi ...



Baba asabe tai murmushi tace da GSK, zaliha tace wlh babarmu mu,dazu na ganta yanxu Kuma kin ganta can abakin kofar gidan a tsaye Inaga gidan arufe yake,baba asabe tai murmushi tace, hmmm Inaga malam ne ya rufe ta waje,kafin zaliha tayi magana sukaji anbude kofar gidan Kuma anshigo da sallamar mutane guda biyu,ko ba'a fada ba Baba asabe tasan Yaya sabi'u ne, take ta qara sakin Wani murmushin, azuciyarta tace maimuna kenan ai Baki isa kin taba raba aurannan ba,...


Jin muryar ummah da malam Auwalu yasata mikewa cikin sauri tai jikin window ta tsaya ta fara lekensu,ilai kuwa Yaya sabi'u ne ,tsaye yake akan ummah wacce ke gabansa ya fara yiwa ummah fada ganin tana shirin fita daga gidan ko kallan su ma batai ba, malam Auwalu Kuma ya shiga dakinsa ya dauko katuwar tavarma ya shimfida dai dai kofar dakinsa Yana Yaya bismillah ga wuri ka xauna,Yaya sabi'u ya kalli ummah wacce ta sunkuyar da kanta kasa yace wuce muje ki xauna,....



Ummah ta dago tace wato xuwa yay ya kafada Maka kenan,danka hanani xuwa koh, tafada hawaye na xubowa daga idanta,tace nifa yaya wlh banason ya dinga xuwa Yana hadoni da kai,ko Dan yaga idan ka hanani Abu Ina hanuwa,Yaya sabi'u yace naji muje ki xauna sai muyi magana, ummah tace Amma Yaya,Yaya sabi'u daga mata hannu yace wuce muje nace maimuna saiki fadi abinda ke ranki,babu yadda ummah ta iya haka ta wuce gaba Yaya sabi'u Kuma ya biyo bayanta, ummah Kuma ta dauko kujerar zama ta zauna nesa dasu kadan ,ta hade Rai waje Daya,....


Yaya sabi'u yay gyaran murya yace meyasa maimuna bakyajin magana ne,naga kwanaki naxo akan Irin wannan maganar Amma shine Baki jiba kika qara dawowa da ita, ummah tace Amma Yaya ai ka tambayeni meyasa na dawo da ita kaji dalilina,yaya sabi'u yace naji komai mijinki ya fadamin komai,Ashe xuwa akai aka xuga ki, aka kawo Miki gulmar qarya da gsky ke Kuma ba bincike ba Komai kika hau kai kika xauna, ummah ta dago da kanta idan ta ya kada yay jajur sbd bacin Rai, tace yaya wlh bakarya bane wlh Yaya gsky ne,wato malam xuwa yay ya fada Maka yadda ransa yakeso shine Kuma kai Yaya baxaka tsaya kaji ta bakina ba wato abinda ya fada shine dai dai ne kenan baxa'a tsaya a saurareniba, meyasa mu mata ake tauye mana hakkine,ta fada hawaye na xubowa daga idanuwanta,...



Yaya sabi'u yace ba haka nake nufi ba maimuna,ke dadina Dake bakya tunani kafin ki yanke hukuncin abinda zakiyi,yau ko GSK ne abinda akaxo aka fada mikin aikin hkr, tunda mijinki bayaso ya hanaki xuwa sai kiyi hkr,ki xauna Amma shine Bai isa ya hana kiba, kawai gulma ce Irin ta mata,Amma babu Wani Abu da akeyiwa Ameenah, idan ma ana matan baxai wuce ko Irin sabani da ake samu tsakanin mata da miji ba, Wanda kowa yasan da wannan kema Yana faruwa Dake, Kuma Nima yana faruwa Dani ,nasan Kuma kinsan da haka , tunda Dama shi AURE ibadane,ibada Kuma dole sai an hada da hkr, Amma bawai ke kice sai kinje kin shiga tsakanin mata da miji ba kila ma suna can suna zamansu lpy, kawai so ake a rabasu,kawai kece kika kasa fahimta,kika dage akan ke lallai tafiya xakiyi koya yarda ko karya yarda kije ki dauko Ameenah sbd bakida hankali,to ni nace Babu inda xaki idan Kuma ban isaba to saina Gani, ummah cikin kuka tace haba yaya wlh nidai baxan xuba ido akashe Ameenah ba wai meyasa vabu Mai fahimta tane,Bafa Irin sabanin daka lissafofa sukeyi bafa,Horan yunwa fa da duka yake mata fa, nidai gsky Yaya kabari ni naje naga Ameenah,karya kashe min ita,Yaya sabi'u yace waya fada miki xa'a kashe Ameenah, ummah tace wlh Yaya Nana ma ta gano halin da take ciki,kwanaki,idan Kuma qarya ne kaima kaje mana ka Gani,idan ni Kun hanani xuwa,Yaya sabi'u ya mike yace maimuna kisawa xuciyarki ruwan sanyi akan wannan San 'ya'yan da kika dorawa kanki nidai nace kibi umarnin mijinki Kuma wlh karna qara Jin ya kawamin qararki akan ya hanaki Abu kinki hamnuwa,wlh idan ya qara kawomin qarar ki sai ranki yayi mummunan Baci,tunda ke har yanxu baxa kiyi hankali ba,halin qananan Yara gareki,yanxu ko Nanace xatai wannan Shirman aike ya kamata ki hanata, Amma wai da girman ki kike haka,daga haka yaya sabi'u yay wa malam Auwalu sallama Wanda ya mike Dan xuwa ya rakashi jiki na rawa, ummah Kuma ta mike ta shige daki tana Mai rushewa da Kukan bakin ciki wlh saitayi maganin malam Auwalu agidannan,....



Baba asabe kuwa tana Jin kome ke faruwa Dan yaudai bazatai magana,baza ta shiga sabgar maimuna ba ,harsai ta gama warkewa daga wannan ciwon data ji mata,ai koyanxu bukatarta ta biya tunda anhanata xuwa duba Ameenah,dama xuwan ne Bata sanyi,Dan haka ko yanxu anbiya ta,daga haka tabar bakin window ta koma kan gadon ta ranta fes,......




___________?&



A bangaren su ruky kuwa tunda ta xauna a seat dinta Bata daga kanta ba, kawai tana sauraran jawabin da AA Arab keyine cikin kwarewa,da muryarsa Mai ratsa jiki,da Kuma nutsuwa,gefe gud Kuma tana Dan latsa wayarta jefi jefi, itadai Hanan gabadaya ido ta xubawa AA Arab tana kallan haiba da Kuma kyau awurin wannan bawan Allah,gashi komai nasa abin burgewa ne, a haka dai ana meetings ana Kuma rubuta attendance,har akaxo kansu ruky itama ta rubuta bayan Hanan ta rubuta ta miko mata,...



AA Arab kuwa kansa tsaye yake jawabinsa,bayan ya gama ya umarci shima CP ya fadi abinda yake San fada,bayan CP yayi sai DCP Shima DCP yadan takaita , kafin daga bisani AA Arab yace ZA'Ayi posting,na nashiga cikin dajin nan da Yan ta addar nan suke,da Kuma shiga lungu da Sako na inda suke boyewa,Amma Banda mata,Kuma duk fita Yana daya daga cikin wadanda zasu jagoranci tafiyar, Yana fada Yana Dan lumshe idansa,Wanda yin Hakan ba karamin Kara masa masa kyau yake ba,Dan daga Maza har mata wlh ba karamin goge musu hadda yake ba,wasu matan ko Dake xaune har wasu sun kamu da soyayyarsa,bayan ya gama ya nemi a rufe taro da addu'a,....




Bayan anyi addu'a shine ya fara mikewa, alokacin Kuma Wani police Dake bayansa tsaye yay Maza yaja masa kujerar baya, Hakan ya bashi damar fita daga desk din gabansa,ya fito cikin nutsuwa ya fara takawa yay hanyar kofar fita daga hole din,su CP da DCP sukai saurin bin bayansa cikin girmamawa,Hanan da take ganin komai ta mike ta kalli ruky wacce itama ta mike ,tace ke kiga ruwar jiki a wajen su CP ,dama akwai Wanda CP xaiyi rawar jiki akansa ,ganin mu yadda yake mana Wani cin magani shi adole shugaba, ruky ta tabe Baki ta fita daga seat dinta tai hanyar kofar fita tace hmm aini mamaki CP ya bani,bayan sun fita Hanan ta hango su can harabar wurin su CP manne da AA Arab sai xance yake masa shikuma AA Arab jinsa kawai yake,....


Hanan tace ke kiga shishshigi awurin CP ruky ta Kallesu ta tabe. Baki sai Kuma sukaga wasu police mata da Maza suna xuwa gaidashi, Yana ansa musu cikin kamewa,can saiga wata feenah ta taho cikin kwarkwasa ta nufi AA Arab,Wanda yadan juya baya CP suna nuna masa abu,Hanan tace Kalli wannan feenah Niko bari naga Ina xata uwar San Maza kenan, itama ruky saita xubawa feenah ido tana Kallanta, bayan feenah taje dab da AA Arab tai masa Wani kallo tace sir barka da xuwa,AA Arab baiji tava hankalinsa yay gava wurin da CP ke nuna masa abu, saima Dan qara yin gava dayay Yana tunkarar inda CP ke nuna masa, DCP ne ya kula da feenah yace lpy lau safeenah ,daga haka shima yabi bayansu,tab feenah ba haka taso ba taso ace AA Arab ne ya ansa , Amma hakanma babu komai ta masa uxuri tunda hankalinsa ba'a gunta yake ba,...


Hanan da take kallan komai tasa shewa yadda feenah xatajita tace Amma anji kunya anan dinma sai annuna Hali ,ta fada tana hararar feenah ruky takama hannun Hanan tace mutafi Dan Allah,karki ja mana idan mutane kanmu,feenah Kuma ta makawa Hanan Harara tabar wajen jiki a Sanyaye,....








07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD






*____JAMI'AR TSARO____*




*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*




*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*




*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA) =?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*




______season one ep 3?? 9??



__________?&


Ayau ma da Daren ranar dasu AA Arab sukai meeting heardquater ,Saida aka kai hari Wani qauye Dake nan jihar Kaduna,wajen karfe dayan dare,andauke Yara da mata da Maza kanana harma da manya,Saida sukai wa qauyan nan tas Yan tsuraru kawai aka bari da tsofaffi,amma duk 'Yan mata yawanci su akafi dauka Dan wasu ma da ranar AURENSU akansu,haka Yan ta'addar nan suka kwashe musu 'Ya'ya sunaji suna Gani babu yadda suka iya, Kuma idan kai magana aka she ka ko Kuma aji Maka rauni,acikin wadanda suka dauka ma idan yaro ko yarinya tai gaddama yankan rago kawai xasu musu,su tsallake su,sbd Rashin imani Irin nasu,...



anjiwa mutane da dama rauni ,abindai abin ban tausayi,adaran ranar da aka kira jami'an tsaro aka fada musu adaren su AA Arab sukaje qauyan babu Wani Bata lokaci , Amma kwata kwata kafin suje har mutanan nan sun gudu iya mutanan garin kawai suka tadda cikin mawuya cin Hali,AA Arab yasa wasu jami'an subi bayansu , shikuma ya tsaya a qauyan da wasu police Wanda ke tare dashi,Amma kamar masu layar Bata tuni annemusu an rasa,haka suka Karachi binciken su da dube dubensu Amma Basu Samu mutanan nan ba,haka suka dawo suka tadda AA Arab a qauyan Wanda alokacin har ambulance taxo antafi da wadanda suka ji rauni , general hospital mafi kusa,Dan Basu taimakon gaggawa, wadanda Kuma suka mutu take awajen aka tattarasu waje daya , Wanda idan Allah ya kaimu gobe xa'ayi Jana isarsu,....



Washe gari, tuni gari ya dauka cewar ankai hari Wani qauye Yan jaridu iyayen gulma tuni sun isa wurin wajen karfe takwas aka gama sallatarsu,Kuma AA Arab ne ke jagorantar komai,Dan xamu iya cewa awannan cikin tashin hakalin gari ya waye masa,Wanda tun kan akai su Yan jarida suke San suyiwa AA Arab tambaya Dan suji ta bakinsa Amma Bai Basu damar Hakan ba,bayan anmikasu gidansu na gsky,AA Arab yasa antallafawa mutanan garin da abin ya shafa, da abunda xasu rage radadin abinda aka musu,Kuma AA Arab yace in Sha Allah xasuyi bincika Dan ganin andawo musu da 'ya'yansu cikin koshin lpy,haka mutanen nan suka dinga sakawa AA Arab albarka duk da suna cikin radidin abinda ya faru dasu, Amma Kuma AA Arab yayi musu abinda babu Wanda ya taba musu,domin yayi namijin kokari, tunda duk wannan ta'addancin da ake babu jami'in tsaron Daya Taba barin baccin da yazo ya kawo musu dauki alokacin sai xuwan AA Arab,suko ai babu abinda xasuce masa sai godiya domin yadda ya nuna damuwa akansu,sai kace Wani danginsa ne abin ya faru dasu,Dan wlh yayi matukar kokari,,...



Anan ne Kuma Yan jarida suka samu damar Taresa lokacin da zai Shiga mota Dan tun karfe biyun dare yake kauyan gashi har wayewar garin yau,Wani Dan jaridane ya tareshi me bala'in naci , Wanda tun daxu shine San magana dashi,AA Arab badan yaso ba ya tsaya Dan baiyi niyyar cewa komai ba, Amma Kuma akwai sakon dayake san isarwa Kuma Yana patan sakon yaje inda yake San xuwa, tambayar da Dan jaridar nan ya jefo masa ne yasa shi juyowa gareshi,Dan jaridan yace yallabai ,me xakace game da abinda ya faru a qauyan nan Daren jiya dukda mu bamu samu damar xuwa ba a lokacin, sai safiyar yau, Kuma muma muntadda abinda ya bamu mamaki kwarai da GSK,....



Na xuwan da kai wannan qauran adaran ranar da abin ya faru ,Dan abune Wanda xan iya cewa tunda na fara aikinnan ban taba ganin Wani babban jami'i yaxo ba ,sai dawowarka jiharka, lallai kayi namijin kokarin da bakowane zai yiba ,musamman ma a wannan lokacin da kowa kansa ya sani,idan kaga mutum ya damu da damurwani to kila akan nasa ya faru,ka Hana idanka bacci ka bar duk abinda kake ka taho wannan qauyen nan acikin sulusainin dare bakai tunanin abinda xai iya faruwa da kaiba,sbd hatsabibancin Yan ta'addar nan, Amma haka ka kutso hanya ka shigo, lallai kayi abinda xa'a Jin jina Maka,nikaina Ban taba ganin jajirtaccen jami'i irin kaba, lallai dole a Jin jina Maka,dole mutanen jihar Kaduna suso dawowarka mahaifarka,Dan bazasu so suyi asarar jajirtaccen jami'i irin kaba,.....



Shin yallabai zaka iya bayyana mana ya abin yake, lokacin da aka bi 'Yan ta'addar shin ansamu nasarar kamasu, ko Kuma shin ka Gano wadanda suke aikata wannan ta'addancin, Dan jaridan ya ya dakata da maganar sa , Yana jiran me AA Arab xaice,AA Arab ya sauke numfashi tareda gyara tsayuwarsa ya xubawa Dan jaridannan ido cikin cool voice dinsa,yace da baxance komai ba, Amma maganar da kai na cewa wai ba'a taba samun babban jami'in Dayazo kawo dauki ranar da Yan ta'adda suke kaiwa mutane hariba, shine,yadan ganta da yanayin da suka dauki aikinsu ne,so ni bamu ruwana da wannan,ni duk abinda kaga inayi inayi ne bisa ga hakkin dayake rataya awuya na ,na ALKawarin Dana dauka cewa zanyi aikina bisa gsky da Amana,sbd nayi ALKawarin cewa zan kare kasata,Zanyi aiki tukuru,Kuma Alhamdulillah nayi iya bakin kokarina na xuwa Daren jiyan da Abu ya faru,.....



Saidai abinda muka tadda bayin Allah nan aciki abin yayi Muni dayawa, so saidai akwai sakon Danake San fada, Ina Kuma fatan yaje inda nake bukatar yaje din,Abu Daya xan fada xuwa biyu,na farko shine, wadannan Yan ta'addar da suka, takurawa al'umma suka hanasu sakat suke xuwa suke daukar 'ya'yansu babu laifin da suka musu,inaso ku sani cewa, idanma saka ku akeyi to kufadawa wadannan suke sakakun cewa sunyi na farko sunyi na qarshe,idan har suka bari na gano su billah saina qaskantar dasu,idan Kuma su suke sa kansu suka sake suka shigo hannuna wlh sai sunyi danasanin xuwansu duniya,daga haka ya bar wajen ya shiga mota akaja suka tafi,.....




__________?&


Abangaren su Alhaji sunusi kuwa dariya sukasa da ganin wannan abin Daya faru,Dan wannan labaran da suke Gani tamkar komai a gabansu akayi,Dan su sukasa ai wannan aikin ba kowaba, yanxuma suna gidan hutswarsa Dake can bayan gari shida babajo Ali inda suka Saba haduwa idan Irin Hakan ta faru, musamman Alhaji sunusi Dan Gani yake yanxu bashi da damuwar komai Dan yanxu ya cire Damuwar kotun da Rukayya takai lateef qara, Dan yasan wannan matsalar batakai ta kawo ba,da har zai sata aransa ba,Dan yasan barrister Salman baxai tava bari yaje qasa,ya tabbatar a xaman da xa'ayi jibi,yasan anan Shari'ar xataxo karshe, Kuma yasan suke da nasara Dan barrister Salman ya tabbatar masa da haka,to shiyasa ya watsar da zancen ya Maida hankali kan yadda Kuma xasu kuntatawa AA Arab suga karshensa,suga me yake takama dashine,....



Agabansu akai komai domin Sunsan Yan jarida zasuje wajen shiyasa ma tun karfe shida na safe yake gidannasa dashi da babajo Ali, yanxuma TV ce agabansu suna kallan komai,har maganar da AA Arab yayi babu wacce Basu jiba,Saida sukaga ya gama maganar ya shiga mota sannan suka kece da dariya,harda kyalkyale da dariya, babajo Ali ya tsagaita dariyar dayake yace kaga ko yadda idansa yay ja kuwa,wlh Saura kiris yayi kuka,....


Alhaji sunusi Yana murmushi bayan ya aje kwalbar Hannansa yace hmm babajo kenan iyama idansa ne yay ja,ai baiga komai ba, Ina fada Maka,nan gaba kadan wlh kuka xaisa ,Kuma ya aje aikin yace shi wlh baxai iyaba , babajo Ali ya qara tuntsire wa da dariya yace Allah MaiTama, Alhaji sunusi yace babajo kana wasa Dani,sai kace baka saniba,kasanni indai NASA abu agaba ,to saina cinmasa sannan hankali na ke kwanciya,wlh kadan ya Gani indai damu zaija,wlh yanxu ya fara shiga Tashin hankali,Dan bananxa na rayu a qarqashin yallabai taju ba,Dan na dauki course awurin su yallabai taju,....



Babajo Ali ya gyara xamansa yace,wato MaiTama duniya sabuwa zamu Bude yanxu kenan ,kajifa harda Wani wai idanma sasu ake kasan damu yake ,wai idan ya kamamu saiya qaskantar damu, wai wannan yaran ne yake fada mana haka,aikafin ya qaskantar dasu mu zamu fara qaskantar dashi,wlh dolema mu quntata masa, Alhaji sunusi yay tsaki yace kasan Wani Abu wlh yanxu nake qara Jin kekashewar xuciyata, harda mu xai ja,wlh wannan yaron sai munga bayansa,ka kyaleshi,da sannu xamu dinga Kona masa xuciya muna Bata masa aikinsa,da haka har mutanan gari su tsane shi, governor ma ya tsaneshi,kaga idan mukai masa haka wlh mungama dashi, babajo Ali ya jinjina kai yace wannan yayi,yanxu Kuma next target din da xamuyi cikin Kaduna zamu fara hara mu kaiwa hari, Alhaji sunusi yace Inaga bayanxu ba,sai mun karasa daga inda muka faro tukunna, babajo Ali yace shikenan,daga haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login