Showing 21001 words to 24000 words out of 278032 words

Chapter 8 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1081

yunwa ga jinya wlh ko tantama babu yunwa ce ta kawo mata wannan ciwon,saude ta fara duba dakin ta hango Ameenah akan gadon ta qaraso da sauri cikin tausayawa ganin Ameenah a kwance tana numfar fashi ta kama hannunta tace Anty Ameenah bakida lpy Ameenah ta gyada mata kai,tace tashi ki xauna anty Ameenah,Dakyar Ameenah tace baxan iyaba saude , cikin tausayawa saude tace bari na kira miki babarmu,daga haka saude ta fita da gudu tai gidansu,...

Tana xuwa ta Tarar da babarta tana bawa qaninta kunu, ganin saude ta shigo gidan da gudu tana haki tace ke lpynki Ina kitsan da kika tafi, saude cikin rudewa na yarinta tace babarmu naje anty Ameenah nagani a kwance ko tashi Bata iyayi Bata da lpy,cikin Mamaki babar saude tace ita Ameenahr, saude ta gyada mata kai,tace bari naje ta goya dannata sannan tasa hijab dinta,tace da saude suje ,haka suka fita bayan taja kofar gidan,...

Suna xuwa taga Ameenah a wannan halin tai kanta da sauri,tace uwar kitso, taga Ameenah kamar ranta xai fita tama kasa magana sauwani numfashi take,bavar saude tai sauri ta daga ta tace Ameenah,ganin bata da nauyi xata iya daukar ta yasa tai sauri ta kwanto Dan ta Mikawa saude tace goyashi bari na kaita shagon shafi'u Mai chemist,haka ta dauki ameenah Dama ba jiki gareta ba,suka fita da sauri inda ta kaita chemist din shafi'u, shafi'u ya dubata yace gsky yunwa ce saikuma maleria,inda abinci kamar shayi ko Kunu a fara Bata,bavar saude tace akwai kunu bari na kawo mata,haka ta fita ba'a dau lokaci ba ta dawo da kunu a katon Kofi, shafi'u yace tunda ta Dan farfado Bata yanxu,haka bavar saude ta bawa Ameenah kunun nan Ameenah tasha,sosai bayan kamar minti biyar sai amai ta Dunga amai ,babar saude tace ko cikine da ita , shafi'u yace nayi gwanin tun farko bashi bane,kila ta Dade vataci abinciba, shiyasa take aman Amma bari nai mata allurar aman,haka shafi'u yayi mata,....


Bayan da kamar minti goma yace a Bata kunun Tasha danshi zaufi warware mata ciki,Dan haka bavar saude tai sauri ta Bata kunun,Ameenah da jikinta ya gama yin laushi ta karfi kunun Tasha bayan ta koshi,bayan kamar minutina gomatace bacci take ji,haka babar saude ta kwatar da ita ,wajen karfe hudu da Rabi aka sallami Ameenah haka babar saude ta biya kudin komai ,ta kamo hannun Ameenah wacce yanxu tana jinkarfin jikinta sosai ,haka babar saude ta kaita gida bayan ta zaunar ta bakin Gado itama ta xauna,ta dubi Ameenah on a serious face tace Ameenah ki fadamin meke damunki,, Ameenah tace babar saude nagode sosai Allah ya Saka da Alkhairi wlh badan keba da tuni na mutu,domin na fadawa Kabiru cewa bani da lpy kafin ya fita ya kaini chemist ko ya siyo min magani Amma yace wai bashi da kudi nayi addu'a,ta qarasa fada tana Mai rushewa da gunjin kuka,.....

Bavar saude ta dafa kafadar ta tace ,kina nufin Kabirun yasan bakida lpy Amma yasa kafarsa ya fita ya barki cikin wannan halin, Ameenah ta gyada mata kai, tana xubar da hawaye,bavar saude tace ko Baki fito kin fadamin ba,nasan ba jindadin xama da Kabiru kike ba, shafi'u yace bakyacin abinci meyasa, Ameenah tace baya bani abinci, na manta yaushe rabon daya kawomin kayan abinci gidannan,tace Wanda ummah ta ma ta Aiko min dashi ya dauke ya Saida,nai magana ya rufe ni da duka, bavar saude was speechless ta tsaya tana kallan Ameenah tausayin ta na qara kamata, wannan yarinyar karama haka, Amma a dinga axaftar da ita da yunwa,ita wlh Allah ne ya Dora mata kaunar Ameenah,tarasa ma me zatace,ta gyara xama tace ki tafi gida ji fadawa iyayenki abinda kawai yake Miki wannan ai Rashin imani ne ya xa'ayi abawa mutum marar hankali AURANKI,marar imani, karkiji haushina akan abinda nake fadawa mijinki Amma wlh wannan abun babbane dole saikin fada agida a dauki mataki,...

Cikin Kuka Ameenah tace idan na fada agida ba yadda baba zaiyi ba,sbd Kabiru Yana xuwa Yana tsara musu gsky da karya, Kuma baba baya bincike baya komai xaice na koma dakin mijinah, babar saude tace innalillahi wainna ilaihi rajiun, gsky wannan ba rayuwa baceva,Rashin abinci ai babbar illah ce, Amma Kabiru Bai kyautava,inane garinku Ameenah tace ZARI'A,babar saude tace, shikenan ki kwantar da hankalinki in Sha Allah sai Allah ya kawo Miki sauki idan nai girki in Sha Allah xandinga kawo Miki abinci Koda yaushe, Ameenah ta share hawayen idanta tace nagode sosai babar saude Allah ya Saka da Alkhairi babar saude tana mikewa tace Ameen,bari naje gida saude xata tayaki xama har magrib xanje na daura girki daga haka ta fita daga dakin tai gidan ta, tana tunin magan ganun Ameenah,....


*Headquarter*

Haka Ruky ta qaraso wajen da CP ke xaune Yana jawavi,bayan ta qarasa ta tsaya nesa dashi kanta a kasa ,yace from where are u tana wasa da pingers dinta tace, from hospital da mamaki yace hospital to due what,tace I'm not feeling fine, yace are come to report,tace no yace why,tai shiru yace what are feeling now,ta kalleshi tace northing yece ok
Go and seat down, wishing u quick recovery, cikin sauke numfashi ta Jin Dadi tace thank u sir, yace no thank u for ur self,yace next time don't miss this meeting tace in Sha Allah,daga haka ta samu wani seat Dake bakin kofa ta xauna,tana mamakin kanta ita kanta Batasan ya akai wannan dabarar taxo mata ba, haka aka cigaba da meeting din nan har aka tashi ganin time din sallah yayi,maxa suka nufi masallaci, ruky ta wuce office dinta danyi acan,....

Shareef ne ya shigo yace Keko ruky Ina kika tsaya da kwanan bakya xuwa office da wuri ,ta harareshi tace uban Yan sa ido, bansaniba,yace seriously Ruky wlh da bakya kaiwa wannan time din Baki shigo office ba,dubufa har Daya Saura Baki shigo ba,ga kinsan akwai general meeting, nai ta Kiran wayarki bakya picking, har mamah na kira, Amma tana ringing Bata daga ba,nace kila ko Bata kusa, ruky ta xaro ido Jin yace wai har mamah ya kira , saitaje Sanyi Jin yace batai picking ba,ta yamutsa fuska tace na taho naji gabadaya banajin dadin jikina tun jiya shiyasa na wuce asibiti , Kuma da naje doctor din da nake Gani baixo ba shiyasa kaga nakai wannan time din Kuma wayar na barshi a mota ne yana silent,..

Shareef dai kallanta yake Amma Bai gansu da itaba,Dan haka yace wlh Allah ne ya taimakeki yau a hannun CP Dan wlh yau ransa a bace ya shigo, bakiga mutanan Daya wulakanta ba yau Ruky ta tabe Baki tace Dan Allah kyaleni haka Shareef bani Aran laptop dinka xan duba Abu,duk Dan ta kauda xancen yasa ta fadi haka,...

Da daddare ruky suna falor da mamah suna kallan labarai a gidan TV na GADANGA TV & RADIO,inda ake fadan yadda akai garkuwa da Yara Yan makaranta ,Wanda har yau kwana biyu ba'a San inda suke ba,mamah tace wannan kasar tamu Allah ya kawo mana sauki ruky tace Ameen, mamah tace Kuma hukuma baxata shigo ciki ba aje a bincika ruky tace hmmm ni ban ma jiba Saiyanxu idanma sukaji aidole sai gomnati tasa Baki tukunna mamah tace Allah dai ya tona musu asiri ruky tace Ameen,tace mamah bari naje na kwanta,mamah tace Saida safe ,kiyi addu'a sosai ruky tai murmushi tace in Sha Allah,daga haka ta haye sama,...


Ruky tana xaune a dakin ta tana chatting da Hanan akan labaran dasuka ga daxu Dan itama Hanan ta gani,inda suke tattaunawa akan AL'amarin,Miss call din lateef ya shigo wayarta,inda taki picking, yasake kira nanma takiyi, ganin batai picking ba yasashi Yi mata text message akan ,idan batai picking ba wlh Allah yanxu zaixo gidan Jin haka tasan Kuma zai iya yasata dauka, yasake Kiranta cikin sauri ta daga ,tai sallama, lateef yace wato da baxakiyi picking call dinba koh ,da ban fada miki haka ba koh,tai shiru, yace wlh na gaji da abinda kikemin dinnan , daddy xan samu kawai ai maganar aurannan a daura ma kowannan week dinne dama ai lallabaki nake Amma tunda har bakya Gani,wlh Allah ya kaimu gobe kinsan Allah saina fadawa daddy yaxo ya samu mamah a tsaida magana ,aSaka ranar aurannan ko Kuma ma adaura kawai,in yaso saikiyi duk abinda kikaga dama idanma fashewa xakiyi ki fashe , Ruky cikin faduwar gaba da rawar murya tace Dan Allah ya lateef kayi h???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kr nace ka bani lokaci,yayi murmushin mugunta yace wanni lokacin kike so bayan Wanda aka Baki kinmanta tun kafin tafiyata america kikace ce na Baki lokacin na Baki,naita kiran wayarki bakya picking, na dawo ma again ,ko daga call Dina bakyayi,look Ruky wlh nagaji AURE nakeso, na dawo wannan shine dawowana ta karshe Dan ke nake yawan barin qasar nan sbd kince Ina takura miki,na barki ki huta ,Amma bakya Gani,Tom tunda ke bakisan Kara ba,wlh baxan tava janyewa ba yanxu,koki shirya ko karki shirya wlh AURE babu fashi,daga haka yay rejecting call Din,..

Ruky da tun time din Da lateef fara magana ta fara kuka ,tai shiru tana jinsa,Mai lateef yake nufi da itane,wato adaura AURANSU wlh Allah baxata tava auran lateef ba saidai komai xai faru ya faru, gabadaya jitai komai ya tsaya mata ta kashe wayar ma gabadaya kamar ta taje ta fadawa mamah yadda sukai da lateef saikuma kawai ta hkr xata jira taga goven Baban nasa xaixo din,haka ta dinga juye juye akan gadon nan da kyar bacci ya dauketa, washe gari haka ruky ta tashi jiki a Sanya ye,ta fito bayan tayi shirin fita aiki,ta gaida mamah mamah ansa Mata ganinta kamar Bata cikin walwala kamar, Wacce akwai abinda ke damunta mamah tace auta lpyanki kuwa, ruky ta yamutsa fuska tace lpy lau mamah kawai kaina ne ke ciyo, Amma idan Nasha magani in Sha Allah xaidaina , Mamah tace oya Maza kici bari na kawo Miki maganin saiki Sha,daga haka ta bar wajen , ruky ta fara cin abincin , ba'a dau lokaci ba mamah ta kawo mata maganin bayan ruky ta gama cin abincin takarva mamah ta tsiya ya mata ruwan a glass cup,haka ruky ta karba Tasha bayan Dan lokaci tace mamah bari na wuce mamah tace kodai ki fasa xuwa office dinnan ki kira Shareef a waya ki fada Masa bakida lpy yayi reporting,ruky ta girgixa mata kai tace mamah aiba Wani ciwo bane,xai daina in Sha Allah,mamah dai ba haka taso ba haka ta Barta ta tafi ,ruky ta wuce wajen aiki,Dan yau aiki xata fara xuwa tukunna ta wuce asibitin daga can tunda yau zasuga gynie Dr din....


Bayan tafiyar Ruky, mamah ta aika ,baba hasiya kasuwa ta Siyo mata agusi Dan nasu ya qare Kuma so take ayi anfani dashi yau,driver ne yakai ta,wajen karbe shadaya Alhaji sunusi MaiTama ya shigo gidan da Yan sandansa abayansa ,haka suka bude masa Mota ya fito Yana karewa gidan IG umar MaiTama Kallo,Yana tuno da wasu abubuwan da suka shude shekarun vaya ,haka Alhaji sunusi,ya taka har kofar falon Shiga gidan police dinnan suna take masa baya suka tsaya ganin zaishiga falon suka tsaya suna gadin bakin kofar kamar Wanda zasu hana a dauki rayuwar sa,sannan ya shiga dakin babu kowa a falon Dan haka ya samu waje ya xauna a Daya daga cikin kujerun falon sannan ya dauki wayarsa yayi dealing number mamah, ba'a dau lokaci ba tai picking, yace hajiya Halima gani a falon gidanki, cikin dan mamaki tace a'a Alhaji sunusi yau Kaine agidannamu bari naxo,haka mamah ta Sako hijab dinta ta fito Aiko shine Yana xaune tana mamakin meya kawoshi gidannan,...


Ta boye mamakinta ta nemi wuri ta xauna kan Daya daga cikin kujerun falon,suka gaisa ,ya numfasa yace Hajiya halima xuwa nai akan maganar auran lateef da Rukayya na Baku lokaci Amma har yau Baku bamu ansa Mai kyauba, Hajiya Halima inada iKo akan Rukayya domin yar Dan uwanace ,Kuma ni nake da iKon xaba mata mijin AURE tunda babu mahaifin a duniya sbd haka ,ni nan na yanke hukuncin nan one month xa'a daurewa Rukayya aure ita da lateef,mamah tace cikin dauriya Alhaji sunusi tabbas kana da iKon akan Rukayya Amma,ai sai aji ta bakinta tukunna,bawai kawai kaxo da maganar nan da Wata Daya xa'a daura mata AURE ba,yace Hajiya Halima ,duk lokacin dana baku Bai ishekuba bakugama yanke hukunci ba, kema na fuskanci bakyasan ki aurawa lateef yarki,to wlh koshi yayan da Yana nan wlh da sai anyi aurannan ,sai munjira me zatace ,sai minjira ta bamu umarni Kome to bari Kiji,tunda har bawai sanshine Bata yiba dole saita aureshi ke koma Bata sanshi wlh saita auri lateef idan Kinga ba'ai ba aurannan ba to wlh saidai Daya ne ya mutu acikinsu, daga haka ya mike yay ficewarsa,mamah ta kasa tashi hawaye ya fara xuba idan ta tasan Alhaji sunusi bashida mutunci xaiyi abinda yafi hakama ita tasan Auta basan lateef take ba, mahaifin ta har nasiha ya bar mata akan taiwa ruky duk abinda takeso matukar Vai sabawa shariah ba,Kuma idan Allah yaso ya yarda xata cika masa burinsa,ita Damuwarta Batasan ya ruky xata karbi xancenba Wani Hali xata shigava,haka ta dinga xubar da hawaye tunawa datai da mijinta abun kaunar ta Wanda mutuwa me yankewa taxo ta yanke zamansu,Wanda Alhaji sunusi ya dasa mata Wani ciwo axuciyarta Wanda Baxata tava mantawa dashi ba,Wanda take ganin shi dashi Wanda shi Bai saniba, Amma lokaci Yana nan shi xai warware komai,....




07066508376_______
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*____JAMI'AR TSARO____*


*____THE WOMEN POLICE____*



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*NA*


*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*


*____(MRS SARAKIES)____*


*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA)* =?1?


*Bismillahirrahmanirrahim*


____season one ep 1?? 2??

_______
'?
'?

Ruky saida ta fara xuwa wajen aiki harma suka fita xuwa,wata unguwa inda nan ma dai sata akai aka kawo report shine suka shigo unguwar Dan yin bincike,bayan sundawo Kuma yau Hanan ta biyo office dinsu tace suntashi yau da wuri,hanan tace yaudai direct gidansu Ruky xata biya Dan sai dare xata tafi gidansu,ruky ba haka tasoba,svd xata biya wajensu su baba lami,gashi Khalil ya kirata shima wajen uku da Rabi Yana asibitin sbd yau shafa xataga doctor din,ruky ta rasa wacce dabara xata yiwa Hanan hardai karfe hudu Saura yayi lokacin tafiyar ta asibitin yayi ,haka ta tattara ta kardun gabanta ta ajiye,ta dauki handbag dinta tace da Hanan ta fito su tafi, Hanan tace yau Kuma da wuri xaki tafi,tace xan biya wani wurinne,,ba yadda xatai da Hanan dole saidai sutafi tare,Hanan tace ok muje,daga haka suka tafi , ruky ta shiga motarta Hanan Kuma tana gefenta,tana mata hira itadai ruky jinta kawai take....

Bawai bataso Hanan ta sani bane a'a tasan halin Hanan ne ba lallai ta yadda da abinda take shiryawa bane, barinma idan taga gidan da a kaiwa shafa wannan xaluncin itama,kanta Rukyn tasan cewa wlh duk Wanda yay wa shafa wannan xaluncin jikinta Yana Bata Dan masu kudi ne sbd Yana yin gidan da yadda shafa ta tabbatar mata da gidan mutumin ne,Kuma tace mata matashin saurayine , haka ta cigaba da driving har suka karaso asibitin, ganin inda suka qaraso yasa Hanan ce mata a'a Ruky nan fa asibiti ne waxaki duba, ruky ta kalleta tace zakiga ko wama naxo dubawa,adai lokacin da take kokarin fita daga motar Hanan ta kamo hannun ta tace dan Allah ki fadamin, Ruky tace Dan Allah Hanan ki kyaleni xakiga ni ai idan muka shiga ciki daga haka ruky ta fita daga motar,Hanan ma ta fito , ta bita ganin inda suka dosa....

Haka Hanan ta kyaleta ta xuba mata ido har suka qarasa dakin da aka kwantar da shafa, ibrahim Khalil ya nufota yace ranki dade sannu da xuwa,tai murmushi tace yauwa malam Khalil sannu ,ya gaida Hanan Ganin ta cikin shiga irinta ruky ,alamu ya nuna cewa itama police ce, itama Hanan ta ansa masa tana mamakin meya kawo ruky nan meye Hadinta da mutanen nan Dan ita tanama Khalil kallan sani Amma Batasan babar shafa ba,babar shafa tace jami'a sannu da xuwa ruky tace yauwa baba ya Mai Jiki baba lami tace Jiki da sauki ya aiki, ruky tace Alhamdulillah, ta gaida hanan ma, Hanan ta ansa har sannan mamaki ne shimfide a fuskarta, ruky tace yauwa baba kin shiryata ko, Yanxu doctor din taxo ki kamota sai muje abi layi ,baba lami tace toh,ta kamo shafa wacce Dama already ta gama shiryata Dan tunda Ibrahim Khalil ya shigo dama ya fada mata,haka suka tafi ganin likita, inda masu ganin nata Basu da yawa sosai ,bavar shafa ta xauna ta rike shafa a jikinta,sai ibrahim Khalil yana gefe atsaye sai Hanan tana tsaye wacce mamaki ya kasheta sbd abinda take gani, kusa da ruky wacce ke latsa wayar ta ,tama ki Bata damar tambayar komai,...

Haka aka dinga Kiran mutane suna shiga office din, hardai Suma aka kirasu suka shiga,inda bavar shafa da Ruky ne suka shiga,bayan ta bawa hanan hand bag dinta, Hanan ta koma motar ta xauna Dan baxata iya xama a wurinba sun Sami doc Fatima xaune akan kujerar ta ,keda Kinganta Kinga yar gayu Kuma ba wata babba bace ba Dan gsky baxata wuce Irin shekara 33 dinnan ba,Amma sai ilimi,xaune take da farin glass sai lapcoat Dake saman kayan nata,bavar shafa ta xaunar da shafa sannan itama ta xauna ruky Kuma tana tsaye,matar ta dauko file din shafa ta duba,ta cire glass dinta a daidai lokacin da ta kalli ruky xatai magana sai Kuma ta ganta da kaki, saitai shiru tace shafa'atu haladu,babar shafa tace gata, doc Fatima tace ta taso ta hau kan bed din da ake duba Marasa lpy Wanda ke office din doctor,haka babar shafa ta dorata,doc Fatima ta kalleta tace xaki iya fita ta kalli ruky tace ASP Naga case din naku babbane Kuma ke kike tsaye kan case din sbd haka ke xaki tsaya,baba ki fita ki jiramu,babar shafa tace toh likita,haka ta fita,....


Doctor Fatima ta qarasa gavan gadon inda ta ke kwance,ta duba shafa ciki da Bai wacce ta tsorata da lamarin haka dai tai rubece rubuce ta cikin file din shafa sannan ta rufe ,tace da shafa ta sauko ,ta kira babar shafa tace ta kamata sujirasu awaje magana Zasuyi,haka ta kama hannun shafa suka fita waje,inda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login