Showing 213001 words to 216000 words out of 278032 words

Chapter 72 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1100

ita Gani take ba komai bane tunda tambayar ta yayi.


AA Arab ya gimtse dariyar sa kafin ya ce.

"Wani Irin kallo kuma nake miki?, bayan kinsan ni haka nake".


Ruky ta ce A shagwab'e "wallahi sir a'a yanxu ne ka koyi haka".


AA Arab ya ce Yana gimtse dariya "ok da Wani Irin kallo nake miki?.

Ruky ta ce "normal kallo kake min".


AA Arab ya ce" to yanxu Kuma fa?


Ruky tai shiru tak'i yin magana.


AA Arab ya ce "Ina jinki ki bani ansa".


Ruky ta ce "kaima ai ka sani"yay wata dariya wacce ruky taji ta burgeta sannan ta ce azuciyarta dama Yana dariya haka muryar sa ce ta sa ta dawo daga tunanin da take taji ya ce.

" Ina jinki".

Ta ce "sir Abar maganar kawai" AA Arab ya ce "Baki isa ba ai sai an K'arasa tunda ke kika d'auko ta, ya cigaba ya ce "I'm All ears ".


Ruky ta ce "wallahi sir banzan iya ba ".

Ya ce " ok to bari ni na lissaafo Wani Irin kallo nake miki ke Kuma sai ki Fad'i wanne ne daga ciki ".

Ciki Rashin damuwa ruky ta ce "ok Ina Jinka".


AA Arab ya ce"kallo normal nake miki ko Kuma na soyayya? Ya fad'a Yana gimtse dariyar sa.


Ruky tajj tambayar ta girmeta saikuma ta basar ta ce.

" nidai ba kallan normal kakemin ba".

AA Arab ya ce ok Wani kallon ne nake miki?ko kallan soyayya ne?,


Ruky tai shiru Bata ce komai ba Amma Kuma tana tunanin maganar sa.


Ya ce "ki fad'a mana acikin biyun saiki zab'i d'aya"

Ruky ta rufe Idon ta kafin ta ce "kallan soyayyar kake min,Kuma ai kasan babu kyau" ta fad'a tana rarumar bargon gefenta ta rufe fuskarta dashi....



AA Arab ya saki Wani Miskilin murmushi sannan ya ce "ok to tunda har kin Gane kallon meye nake miki to shi d'in nake miki ".


Ruky ta rik'e baki kamar zata kashe wayar,ai AA Arab kamar yasani ya ce.

" karki kashe min waya".

sai Kuma ya ce.

"Rukayya! ni Ahmad Aliyu Arab Ina sonki,Ina Kuma son Rukayya ,Ina Kuma k'aunar ki Ina Kuma fatan kema zaki Soni kamar yadda na ke sonki "

Ruky tai shiru ta kasa magana, saboda gabad'aya AA Arab ya gama da ita,dama haka yake bashida kunya yanxu yau ita yake cewa yana so kai Ina..

ganin tak'i magana ya sa AA Arab ya ce "please say something mana ".


Ruky tai shiru jiki a Sanyaye ta ce "sir kayi hakuri bansan me zan ce Maka ba" ta fad'a kamar zatai kuka ...


AA Arab Yana murmushi ya ce "kawai kema ki ce kina Sona kina so na,kina son Ahmad kamar yadda na fad'a miki ".


Ruky ta girgiza kai kafin ta ce cikin sanyin murya"bazan iya ba sir,kayi hakuri".


AA Arab ya ce "xaki iya".

Ruky ta ce "to Amma ba yanxu ba".ta fad'a kawai Dan ya k'yaleta.


Ya ce "sai yaushe?.

Ta ce "sai na Yi tunani"


AA Arab ya ce "ni bana son Wani tunani please ki fad'a min yanxu ko samu nayi bacci Mai Dad'i Wanda da bana samun nayi shi".


Ruky ta ce "to gobe zan fad'a Maka" Dan wallahi ita kawai so take ya k'yaleta..


Ya ce "kin tabbata".

ta ce "eh ".


AA Arab ya ce "ok Good night sweet dreams".

ai ruky Bata jira ya k'arasa ba ta kashe wayar tana dafe k'irji tana Jin kamar a mafarki,Bata tab'a tunanin jin irin wannan kalmar daga bakin AA Arab ba,kasa bacci tai awannan lokacin ,ta dinga juyi tana tunanin itako ya zatai da AA Arab bata ji bata sanshi ba sannan bataji tana Son Shiba kawai Irin feeling d'in nan takeji akansa na Daban,haka ta kwanta tana juyi da k'yar bacci ya d'auke ta..


A bangaren AA Arab kuwa shima kasa baccin Yayi Amma Kuma sai yaji Dad'i Daya sauke wannan nauyin Dake kansa , addu'ar D'aya ita ce Allah yasa ruky ta amince da soyayyar sa ,a wannan ranar dai bacci Yayi cikin nutsuwa Mai d'auke da mafar kin ruky.....




07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*___THE WOMEN POLICE ___*



*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*




*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*




*('TAURARI WRITER'S ASSOCIATION ('*




*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*




*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 8?? 4??



____________?&


Da safe ruky data tashi da Wani Irin sanyin jiki ta tashi da tuna nin yadda xataje office ta Had'u da AA Arab har su zauna the same roof tare kawai take.Koda tashi wanka ta fara Yi bayan ta shirya cikin uniform d'inta bayan ta kammala ta fito daga d'akin ta ta sauko k'asa ta Tarar da Mamah tana kallan labaran safe kamar yadda ta Saba, baba hasiya Bata nan taje ganin gida ammo gobe zata dawo,Dan haka sai iya Mamah ita kad'ai ce a gidan,ta k'araso kusa da mamah har lokacin jikinta a Sanyaye yake ta zauna kusa da ita tana kallan mamah ta gaida ta, mamah ta ansa tana kallan Ruky kafin tace.


"Auta! Anfito"ta fad'a tana kallan Ruky,

Ruky tai murmushi ta ce.

"Eh Mamah".


Mamah ta ce .

"To tashi kije kiyi breakfast Maza karki makara".


Ruky ta jinjina kai sannan ta mik'e tai hanyar dining,bayan ta zauna ta fara cin abincin,iya abinda tasan zata iya ci shita tsakura taci shima ba Sosai taci ba ,bayan Wani lokaci ta gama ta tashi ta qaraso har falon tana kallan mamah tace .


"Mama! zan tafi " ta fad'a tana kallan mamah.


Mamah ta d'ago tana kallan Ruky ta ce .


"Allah ya kiyaye Auta! ki gaida Ahmad".


Ruky ta ansa mata a Sanyaye sannan ta juya ta fita daga falon ma gabad'aya.


Tana fita compound d'in gidan nasu ta shiga motar ta wacce already anfito mata da ita ,bayan anbud'e mata gate d'in direct asibitin da su shafa suke ta nufa Dan shekaran jiya taje doc Fatima ta ce jibi ma za'a sallame su tunda jikin shafa yanxu ta Sami lpy saidai Rashin karfin jiki shima da kad'an kad'an In Sha Allah zata daina ji ta warke gabad'aya...


Tana shiga d'akin da aka kwantar da shafa tai sallama ta k'arasa shigowa cikin d'akin, baba lami ta taso fuskarta d'auke da murmushi ta na lalle lale sannu zuwa jami'a ta fad'a tana k'ok'arin aje mata kujera gaban ta, ruky tai murmushi tace.

"Sannu Baba !Amma basai kin kawo kujera ba zan ma zauna bakin gadon" ta fad'a tana K'arasawa har bakin gadon ta da shafa take kai ta zauna tana kallan shafa wacce itama kallan ta take tana murmushi..

Shafa ta mik'e Zaune daga kwancen da take tana yiwa Ruky murmushi ta ce.

" Anty! sannu da zuwa,Ina kwana"duk ta fad'a lokaci D'aya.

Ruky tana kallan Shafa ta ce.

"Yauwa shafa sannu, lpy lau Alhamdulillah,ya jiki kuma?".


Shafa ta ce .

"Da sauki anty! ".


Ruky ta jinjina kai kafin ta ce .


"Yanzu bakya jin ko Wani ciwo, Ko kuma fitar ruwan"ta fad'a tana kallan shafa".


Shafa ta Jin jina kai kafin tace.


"Bana Jin komai Anty!Kuma bana ganin shima ruwan Yana fita yanzu , Babu abinda nakeji Yanzu anty!" .


Ruky ta sauke numfashi tare da cewa "Alhamdulillah Allah mungode Maka ".


Baba lami ta na murmushi ta ce .

"Wlh jami'a ! Kinga dai Yanxu shafa tace babu abinda take ji yanzu,mudai Babu abinda xamu ce Dake da Kuma sauran wad'anda kuka taka rawa mana wajen ganin Kunga shafa ta samu lafiya , Allah ne kad'ai zai biya ku, Allah ya biya muku buk'atunku na alkhairi yasa kufi haka ,bakiga yadda 'yallabaima Wanda yace min sunan sa Ahmad, bakiga yadda yake mana k'ok'ari ba shima ,kusan kullum idan ya tashi daga aiki sai ya zo ya duba mu Kuma bazai zo haka ba ,saiya kawo mana kayay yaki ,Dan Allah ki Tayamu Yi masa godiya mungode mungode" ta k'arasa fad'a tana matse k'walla.


Itadai ruky murmushi kawai take,kafin ta Kalli Baba lami ta ce.


"Dan Allah Baba kidaina kukan nan haka ,duk Wanda ya taimaki Wani shima Allah zai taimake shi ,mu Dan Allah mukayi kar Kiji komai"ruky ta fad'a tana murmushi har lokacin,


Baba lami ta share hawayen ta sannan ta ce.


"shikenan jami'a mungode sosai".

ruky tana mik'ewa ta ce.


" Allah ya K'ara lafiya baba,bari na tafi idan Allah ya kaimu jibin zan dawo in Sha Allah ".


Baba lami tace .

"To shikenan jami'a mungode sosai Allah ya kaimu".

Ruky tace "Ameen Baba " ta fad'a tana nufar k'ofar fita daga dakin.


Shafa ta ce ,"Allah ya kiyaye anty",

Ruky ta ansa mata , Baba lami Kuma ta rakota har bakin k'ofar dak'in ruky ta juya tana kallon ta tace.


"Basai kin rakani ba kitsaya ma daga nan Nagode sai anjima".


Baba lami ta ce.

" shikenan Allah ya kiyaye jami'a".

Ruky ta ansa da Ameen sannan ta nufi inda tai parking motar ta,tana duba time taga lokaci har ya jaa Dan ta makara sosai take ta zaro ido waje ganin yadda Lokaci yaja ta saki ajiyar zuciya sannan ta fara k'ok'arin tada motar .bayan ta fita daga asibitin a hanya ta dinga Jin wayar ta na ringing Koda ta duba sai taga AA Arab ne ,tsintar kanta tai da kasa picking call d'in har dai ta Isa office....


A b'angaren AA Arab kuwa yau da zumud'insa ya shigo office saboda zaiga ruky, Amma Kuma bazaka tab'a ganewa ko a fuskarsa ba , bare Kuma Yanayin sa ,saboda yadda fuskarsa take a kame,da wuri ma yau ya shigo office d'in, saboda kawai yana so ya ganta.sai dai ruky Bata zoba har lokacin , gashi lokacin ma da take zuwa d'in har ya wuce batazo ba , Hakan yasa yay deciding Daya k'irata ,Dan ya tabbata kad'an daga cikin aikinta tak'i zuwa office d'in ma gabad'aya.Hakan yasa ya k'irata saidai har ta gama ringing batai picking ba,Saida yay mata miss call biyu duk Bata picking take ya fara tunanin k'ila fa baza ta zo d'in ba,ya sauke ajiyar ya fara safa da marwa acikin office d'in nasa ,Daya gaji Kuma ya zauna kan kujerar Dake gaban table d'in sa ya dafe kansa Yana Jin Wani iri ajikinsa....


Yana wannan tunanin yaji kamar k'arar Bud'e k'ofar falon,ya tsaya ya kashe kunne yaji ko Wani ne zai shigo office d'insa, sai dai Jin ba'a shigo na sannan ba Kuma ba'a fita ba,take ya gane cewa ruky tazo kenen.sai yaji abinda ya to Kare masa k'irji Yana narkewa ahankali,ya sauke ajiyar zuciyar salama tare da lumshe idonsa ya Bud'e su lokaci D'aya, kafin ya Bud'e laptop dinshi ya fara aiki....


Ruky kuwa gabad'aya jiki asanyaye ta shigo cikin office d'in, kai tun da ta shigo ma cikin headquater ta fara Jin fad'uwar gaban nata na qara tsanan ta ,Saida ta Had'u da DCP ma kafin ta k'araso cikin office d'in,ya Dinga Kiran sunan ta ita dai tai banza ta k'yaleshi,har ya biyo bayan ta,Ganin inada ta shiga yasa ya juya ya Rabu da ita...


Ta zauna kan kujerar ta tana ajiye handbag d'inta gefe, sannan ta zauna ta jawo wasu File data ajiye su tun jiya batai aikin su ba ta Bud'e laptop d'inta ta fara aikin,gefe D'aya kuma tana Fargabar ya zasu kwashe da AA Arab yau a office d'in nan gefe D'aya Kuma tana ganin Bata Kyau taba da bataje ta gaida Shiba Sai dai Allah ya Gani baza ta iya ba...


Haka sukai wannan zaman har lokacin sallah yayi Babu Wanda yazo wajen wani, Ruky ta jawo wayar ta ganin lokacin sallahn Azhar yayi yasa ta matsar da laptop d'in gabanta gefe sannan ta sauke numfashi tai baya ta jinginar da Kanta jikin kujerar,tana zaune taji ya Bud'e k'ofar office d'in nasa take ruky taji wani mugun fad'uwar gaba ,ta juyar da fuskar ta gefe tana rufe idanuwan ta...


Bayan AA Arab ya fito ya tsaya yana kallan ta mamaki ganin yadda ta juya masa k'eya, kawai sai ya tsinci kansa da K'arasawa kusa da ita, sannu a hankali taji kamshin turaransa na Kara kusan toto take ta qara runtse idanu wanta tak'i Bud'e wa harya tsaya akanta,Yana kallan ta ya zubawa zara zaran eye lashes d'in ta Ido Yana kallo baya ko kiftawa,Yana Jin Yana K'ara macewa a duniyar sonta, itadai ruky taji bud'e ido domin tasan shine a kanta...

Kawai Sai Jin muryar sa tai a tsakiyar kanta Yana ce wa cikin deep voice d'insa.


"Yau Kuma me nayi Kuma da ba'a zo an gaishe Niba"ya karasa fad'a kamar Mai rad'a.

Ya Allah haka ruky ta Ambata aranta ,tana qara juyar da fuskarta ta gefe tare da rufewa da tafukan Hannunta.


AA Arab ya saki wani miskilin murmushin kafin yace cikin deep voice d'insa.


" Say something my fiancee".

Ruky ta Bud'e idonta kad'an tana kallan sa ta tsaka nin yatsunta ya Wani kashe mata ido D'aya Yana murmushi.

Ruky ta ce cikin shagwab'a.


"Sir Dan Allah ka bari" ta fad'a tana tura Baki gaba.

AA Arab ya duk'o da kansa k'asa k'asa ya ce .

"Ki shirya bani ansa ta da kika ce yau zaki bani " ya fad'awa Yana K'ara narke mata .


Ruky ta zaro ido waje kafin ta marai raice ta ce.

" nifa da wasa nake maka fa ".


AA Arab shima zaro Idon yayi sai Kuma ya K'ara d'uko da kansa dai dai fuskarta wacce take arufe s tafukan Hannunta, ganin abinda yay yasa ruky tai saurin juyar da kanta gefe..

AA Arab yace .

"Amma kinsan kema bazan iya hakura ba koh? Dole saikin bani ansa ta".


Ruky ta ce "sir Dan Allah ka tafi, Kuma lokacin sallah dai na wucewa "ta fad'a har lokacin Kanta yana gefe .

AA Arab ya ce "bazani ko Ina ba har sai kince zaki fad'a min".

Ruky ta juyo ta kalleshi ta ce ".

"Sir Dan Allah kayi hak'uri".

AA Arab ya k'ura mata ido da lumsassun idanuwan sa Yana kallanta ta,Kafin ya ce.


"Rukayya! meyasa bazaki tausaya min bane wai bakiga halin da nake cika ba" ya k'arasa fad'a da wata Irin murya wacce ta kusan zautar da Ruky jin yadda yay maganar,ga sunan ta ma daya k'ira full sai taji Kamar yafi kowa iya k'ira .


ta ce cikin shagwab'a r da Batasan ta yiba.


" to shikenan kaje dai masallacin ka dawo".

AA Arab Yana kallan har lokacin ya ce "kin tabbatar zaki fad'a,karfa na dawo kice ba haka ba".


Rukya ta ce cikin kosawa.

"Naji Zanyi ".

AA Arab ya sauke numfashi sannan ya ce.

" ok to kalleni",ya fad'a da wata Irin murya Yana Kuma narke mata tare da tsura mata ido.

Ruky tai saurin yin k'asa da kanta,tana girgiza masa kai alamar baza ta iya ba.

AA Arab ya ce "please my fiancee".

Ruky kasa d'ago ta kanta tai tana girgiza masa kai ,kafin tace .

"Ni kunya nake ji sir"



AA Arab yay murmushi Yana Wani cije leb'ensa kafin ya ce .


"ok zan tafi masallaci saina dawo ya fad'a Yana kashe mata ido D'aya,daga haka ya juya ya fita ..


ruky ta kifar da kanta kan table d'in gabanta tana jin Wani iri a duk kanin jikinta,ta Dad'e tana zaune kafin ta iya mik'ewa ta shiga toilet d'in first falor ta d'auro alwala,bayan ta fito ta shimfid'a darduma sannan ta tayar da sallah...



Bayan ta idar da sallah ta Dad'e kan sallaya tana addu'oi sannan ta mik'e ta koma wurin zamanta ta cigaba da aikinta,hade D'aya Kuma tana tunanin yadda d'azu suka kasance da AA Arab tana dad'a mamakin Dama haka yake tana ganin sa da kamar bazai yiba.har k'arfe uku na Rana AA Arab Bai Dawo office d'in ba,ta basar dai ta cigaba da aikin ta ,sai Kuma tai tunanin k'ila idan akai la'asar ya dawo ,saidai har Akai sallan la'asar nan Bai dawo ba,kai atak'ai ce dai har akai sallar baidawoba kai har lokacin tashin ruky yay Bata ga AA Arab ya dawo office d'in ba,sai kuma taji ta D'an damu da Rashin ganin nasa,kota ta fito daga office d'in ma zuwa parking lot bataga motarsa a wurin ba ,take ta fara tunanin to Ina yaje Bai fad'a mata ba,sai Kuma tace to ni a suwa da dazai fad'a min,duk inda zashi,haka dai ta kawar da tunanin ta gefe har ta shiga mota jiki a gsky ta qarasa gida......



___________?&


Da daddare Ruky tana kwance a d'akinta ita kad'ai sai juyi take a kan gado tama kasa bacci ko kad'an ,Koda ta d'aga idonta ta Kalli gogon bangon Dake d'akin k'arfe 10 Saura na dare kawai sai taji ta damu ganin AA Arab Bai K'irata ba,sai Kuma tace a fili to wai Mai zaisa ma na Damu kawai Dan yace Yana Sona ,tai tsaki sai Kuma taji ta fara Jin haushin kanta ita da batace tana sanshi ba shine Kuma ta fara damuwa dashi har haka to me Hakan yake nufi.take rufe Bakinta da duka hannayenta biyu Jin abinda zuciyar ta ta Bata ansa dashi,tana wannan tunanin taji wayar ta na ringing ai da sauri ta duba d'aukar AA Arab ne ganin Ameer ne yasa taja tsaki tare rejecting call d'in,sau Kusan Ashirin yau Yana K'iranta kenan idan har ba mantawa tai ba Kuma duk ciki Babu Wanda tai picking,ita damuwar ta yanzu Rashin Jin AA Arab da batai ba ko kad'an, Gashi Kuma ko kad'an ta kasa cire tuninsa aranta tana wanna tunanin wayar ta ta sake ringing ta d'auka ta duba ganin AA Arab ne yasa ta sauke Wani numfashi tare da sakin murmushin da Batasan ko na mene ne ba ,Saida ta seta kanta sannan tai picking call d'in tare da sallama sai Kuma tai shiru...

Daga D'aya bangaren AA Arab ya ansa mata sallamarta sannan yace coin k'asa da murya.

"Shine wato Ko ki K'irani Kiji lafiya ta ko? Ai kinsan yau dai tunda na fita bandawo ba" ya fad'a da wata murya.


Ruky ta tura Baki gaba kawai ta tsinci Kanta da cewa .

"Nima ai baka ce min zaka tafi Wani wurin ba bare Kuma ka K'irani kace ka zakaje Wani wurin " ta fad'a a shagwab'e.


AA Arab yay murmushi jik anfara kishin sa ya ce .

"Ok I'm sorry my fiancee bazan sake ba".

Ruky ta langwabar da kai kafin ta ce .

"To ina kaje?".

AA Arab ya ce"to ai bakicemin Kin hak'ura ba?"ya fada Yana kwai kwayon muryarta.


Ruky ta sauke numfashi ta ce "

"Na hakura ".


AA Arab yay murmushi ya ce "thanks u my fiance"....

kafin ya cigaba ya ce.


" K'auyen ZARI'A muka shiga wai wasu 'yan fashine suka shigo garin da Rana shine fa na samu K'iran gaggawa muka tafi, bamu muka dawo ba sai wajen k'arfe 9".

Ruky zaro ido waje kafin tace .

"Ayya sorry Sir


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login