Showing 3001 words to 6000 words out of 278032 words

Chapter 2 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1773

fara ganin sauyin Wani Abu a tattare da itaba Saida naga ta rage walwala,idan na tambayeta,saitacemin babu komai ni ban kawo komai ba,Saida naga ta fara tafiya ba dai daiba, ,daga karshema kasa tafiya take idan xatai fitsari Saida kuka,idan xata xauna saida kuka,abin ya isheni na turketa adaki na dauko wuka nace saita fadamin meyasa Bata tafiya dai dai meya sameta,...

Cikin tsoro da Fargaba nake mata wannan tambayar,inda tasamin kuka tana wlh inna babu komai,nace karya kike akwai abinda kike boyemin,wlh ko ki fadamin ko Kuma na kasheki da wukar nan na binneki adakinnan babu Wanda ya sani,cikin Kuka tace inna xan fada miki Amma Dan Allah karki fadawa kowa,yace indai na fada saiya kasheki ,danima, nace mata to kirjina na dukan uku uku ...

Haka na sauka daga kanta inda na xauna Dan tana kwance ko xama Bata iyayi sbd ciwo,tace inna wanine tun ranar Daya ganni ina talla a mota yake ,yace min nazo ,naje, daukata awarar xai siya yace na biyoshi,nace masa a'a inda yace min aiki ake masa agidansa xai siyawa masu aikin abincine shine ya ganni da awara,zai siya musu ,..

Ya budemin motar yace na shiga nace masa ni baxan shiga ba sbd Kin hanani Amma yace wai babu abinda zaimin siya kawai xaiyi haka ya dage saina shiga inda dakyar nashiga muka fara tafiya ganin munfara barin cikin mutane Hakan yasa na fara tsorata,nace Ina xamu yace min ai gidan babu nisa karna tsorata,.


Haka ya kaini cikin Wani kango Amma arufe yake da gate inda yace mushiga,nabishi a tsorace,muna shiga ya rufe gate din ,nidai nasan babu kowa agidan tunda Banga masu aiki ba,Hakan yasa ni tsorata inda nace ni nafasa tafiya xanyi inda ya hade Rai yace Babu inda xani sai mun shiga ciki,...

Haka na dage akan babu inda xani,Hakan yasashi daukata da hannu daya yayi ciki Dani na fara ihu Ina kururuwa ya toshe min Baki ya shiga Dani,inda yayi abinda yaga dama Dani,..

Saida na dawo hayyacina yamin kashedi akan karna kuskura na fadawa Wani indai na fada saiya kashemin iyayena Kuma ya kasheni nimaHakan yasa ni ansa masa inda yace kullum idan na fito xaidinga xuwa Yana daukata,idan nafada ko Wani ya Gane wlh saiya aikata abinda yafi haka,na ansa masa da toh,...

Haka ya daukoni ya saukeni inda ya bani kudi Mai yawa,Wanda Saida na kirgi iya na yadda kika fadi kudin awarar na Baki ,sauran Kuma na ajiyesu,Dan yamin kashedi shiyasa naki fada miki inna Amma Nima abin Yana damuna,...

Kullum haka xaixo ya daukeni, hardai taki ta kawo yanxu inna ko xama bana iyaYi,ta qarasa fada tana xubar da hawaye tareda da Kuka Mai cin Rai,Nima tunda ta fara bani lvrn nai mutuwar xaune Ina Jin duniyar ta isheni,Inajin kaina Yana juyamin,haka nai kuka na tsinewa wannan mutumin ,nace ta fada min ayina yake tace min wai Batasan ayina yake xauneba kawai itadai tana ganinsa a unguwar,

Banzauna ba haka na shirya ta da niyar mutafi asibiti,Ina fita na Nemo abin hawa haka na kinkimeta muka tafi asibiti suka ce baxa su karbe muba Saida yan sanda ,haka na tafi Wani division inda aka hadana da Dan sanda Daya,sai alokacin aka karbeta....

Haka aka likitocin suka kirani nida Dan dansannan suka ce nai musu bayanin komai haka nai musu ,inda suka jajanta lamarin sannan ,suka barni da dansandan a fadarsu case din Yana Hannun hukuma ne,haka wannan dansandan yace muje division ayi reporting komai,bayan anyi suka ce naje in Sha Allah zasuyi bincike akai,haka na tafi Ina Dan Jin sanyi araina,na ganin xa'a kwatarwa yarinya ta hakkin ta, ..

Nikuma na koma asibiti Dan
Kula da yarinya ta,wlh malam Ibrahim abin yayi Muni domin yadda nake xato Ashe abin yafi haka Dan yariga daya gama Bata mata rayuwa wacce ba lallai ta moruba,ta karasa fada tana share hawayen dayaki tsaya mata har lokacin,

Haka na zauna kusan sati uku banji daga
Dansandan nanba Dan har lokacin tunda yaxo asibitin nan sau daya Bai qara xuwa ba ni Kuma jinyar yata ya daukemin hankali,ta samun lpyar ta kawai nake....




07066508376________
'?
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*___JAMI'AR TSARO___*


*___THE WOMEN POLICE*___


______THIS STORY IS TOUCHING HEART, I WAS SPEECHLESS TO EXPLAIN IT, BUT WE SHOULD SEE, ON WHAT HAPPENED TO OUR LIFE KNOW, SO, BE WITH ME,&U LOVE IT MORE THAN U EXPECTED_______
'?

*__NA*

*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ*___

*_____(MRS SARAKIES*)____


*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION*(QUWA)=?1?


*Bismillahirrahmanirrahim*


_________season one , episode 3??



_________
'?
'?

Likitocin suna iya bakin kokarinsu,sbd wannan kudin datake boyewa shina dauko na dinga siyan duk abinda xa'a bukata na neman mata lpy, saida naga abin ya Dan fara sauki sannan na koma division din,inda nace wacce ta kawo qarar anketawa yata haddi Kuma akace xa'ayi bincike akai,..

Inda Wannan Dan sandan ya tabbatar min da suna iya bakin kokarinsu Amma sunkasa Gano ko wanene Amma sun min ALKawarin xasu cigaba da bincike,inda na qara hadasu da Allah akan su taimakamin sukace in Sha Allah zasuyi haka na koma asibitin,...

Har aka sallamemu inda yanxu dai da sauki tana zama Kuma bata kuka idan xatai fitsari,Amma fa abin babu kyau Dan cuta anriga da an cuci yarinyar nan,haka muka koma gida inda na cigaba daga inda likitocin suka tsaya wajen kula da ita, Amma har lokacin babu abinda jami'an tsaron nan sukayi, kullum idan naje da kalar uxurin da xasu bani hardai naga ba binciken xasuyi ba kawai na hakura na fauwalawa Allah komai domin shi maijine kuma Mai ganine Mai sakawa Wanda aka zalunta domin shi baya xalinci Kuma baya goyan bayan xalinci,...

Ibrahim Khalil yace, ban katsekiba,Amma Bai war Allah Kuma bayan kinkai wannan division din kina nufin babu Wanda ya qara wai wayarki ,akan batun yarinyar,Sannan, Baki kai Wani wurin qaraba ,duba da yadda su wadannan ja'amin tsaron Basu bada Wani goyan bayan bincukar lamarin ba,sannan babu Wani lvr game dashi Wanda ya aikata ta'asar,,...

tai murmushin takaici tace babu Wanda ya qara waiwayarmu,sannan ni bankai Wani wurin qara ba tunda babu inda na sani a Kuduna sosai,iya dai wannan division na yankinmu ita nakai, Ibrahim Khalil yace , Allah yasa mudace muna sauraranki,....

Ta cigaba da fadin,haka muke zaune ni da ita abindai kamar da tawarke, Dan munkai kusan wata 4 ko 5,Amma sai me daga baya ta dinga fitar da Wani Irin ruwa ta kasanta Wanda babu kyan Gani,ga bani da kudin da xan kaita asibiti, nafara kokarin yadda Zanyi na samu kudi danna maidata asibiti sbd banida kudi,haka na fara kame kamen sana'a,nice wanki,nice surfe nice aikatau babu kalar sana'ar,da banyiba , haka na Dan kukuta na samu kudin na kaita asibiti,...

Inda da mukaje,akace ai aiki xa'a mata Wanda xaici makudan kudi Dan aikinma ance ba'a duka asibitin State din qasar nan akeyinsa ba,ko scanning ma sukace wlh shima kudi ne sosai bana wasa ba,malam Ibrahim ni bashine dani ba ,ga mahaifinta,baya raye nice dai ,dolen ta , ba Yan uwa garemu ba masu karfi kowa ma ta kansa yakeyi,sukace saidai Sudan bata wasu magun gunan abin ya lafa Amma bawai ya tafi kenan ba,saidai indinga karba mata magani duk karshen wata,Wanda ko kudin hannuna Basu kai kudin maganinba ,haka na karva muka dawo gida nake Bata maganin,...

Ina vata maganin babu laifi Ina ganin Dan sauki Amma fa da zarar maganin ya qare abin xai dawo savo,ahaka nake jajir cewa wurin Sana'a ta,nake siya mata maganin,malam Ibrahim yauda gove ta Kori komai,ahaka har ta kai Nima na kwanta jinya sbd wahala wuni nake Ina aiki babu dare babu Rana,ahaka na kamu da hawanjini,...

Ita tana kwance Nima haka babu Wanda xai iya taimakawa Wani,naje gidan radio Neman taimako Amma abin ya gagara,yanxu xancen Danake Maka tana can kwance ,Rai ahannun Allah,Sbd na barota a mawuyacin Hali,sbd kullum,ciwon qara qaruwa yakeyi,wannan shine iya abinda xan iya fada maka malam Ibrahim,ta qarasa fada tana Mai rushewa da Kuka Mai cin Rai,...

Yace to yanxu Wani bukatar temako kikeso ko gwamnati ko wasu masu ji a fada a kasar nan kike bukata, tace Ina bukatar gomnati data tai makamin ta duba halin da muke ciki,a biwa yata hakkinta,sannan atai Maka mana wajen samun lpyar ta,wlh ita kadai ce ta ragemin Dan Allah Dan Annabi ataimaka mana,...

Ibrahim Khalil yace masu kallanmu Kuna daijin wannan xalinci da akayiwa wannan baiwar Allah,dama halin da yarinyar takeci,da yadda aka wofantar da qarar data kai xuwa ga hukuma,sbd haka Dan Allah gomnati ta tai Maka,dama wasu masu ji a fada akasar nan anemawa yarinyar nan lpy,sannan atsananta bincike akan wanwan aika Aikan da akayima yarinyar nan,sannan anemo me lefi a gurfanar dashi ay masa hukunci dai dai da yadda Shari'a ta tana dar,yadda duk Wanda yake Irin aikata barnar dayake xaiji tsoron yi idan yaga anhukanta masu aukatawa irinsu,Hakan zaisa rage duk wata barna raguwa a qasa,sannan,daga qarshe muna Mai rokan ubangiji ya tona asirin Wanda yayi ma yarinyar nan wannan zalincin ,

Har Yanxu dai muna kan shirinnan na mu Mai suna mukula da iyali, sai muyiDuba da Yanayin sunan shirin Nanu,mu kula da iyalinmu a kowani Hali muke,sannan yanxu kiwon mutum ake bana Dabba ba,Duba da Yanayin lokacin ,anan muka kawo karshen shirin namu ni ibrahim Khalil,nace kukasance damu awani makon idan Allah ya kaimu,bissalam

Mamah ta sauke numfashi tareda goge hawayen datake tayi tun lokacin da matar nan ta fara Bada labarin yarta,wacce ta tausayawa halin da yar take ciki harma da uwar ,yanxu Ashe abunnan kullum qara gaba yake wannan wanne Irin wulakanta rayuwar yarinyar nan akayi,....

Wanne axxaluminne marar imani ya aikata mata wannan xaluncin haka,Amma Kuma takai qara hukuma Amma ba'a Maida hankali an tsanan ta bincike wajen gano Mai laifinba sai kawai su banxatar da magana Dan dai kawai suna talakawa marasa qarfi da galihu,Yo ba'a dauki mataki akaiva adole aci gaba da samun rape cases a qasar nan,tunda ba'a dauki matsalar talaka a bakin komai ba,...

Tunanin ta ya katsene lokacin da ruky ta tava kafadarta tareda rungumeta, ta fashe da Kuka itama mamah sai nata kukan ya tsananta ganin Autar ta jaruma ruky tana kuka Mai tava xuciya,aidole tayi kuka domin duk Wani Mai imani indai yaji wannan labarin bayin Allah wlh dole sai ya xubar da hawaye, ruky tace mama Kiji wannan Rashin tsoron Allah,Kiji wannan xalinci da akayiwa yarinyar nan, sannan takai qasa hukuma Amma su banxatar da maganar,mama ba dole a dinga aikata duk wata barna a qasar nan ba ace talaka ba'a dauke shi abakin komai ba,sannan daga qarshe Kiji Irin jinyar da aka barta da ita wacce mamah kinsan wuyar magani gareta,mamah kinsan kukane ya sarketa,yasa ta yin shiru, mamah tace naji komai Auta, su barwa Allah komai in Sha Allah duk Wanda yayi ma wannan yarinyar zalincin nan baxai taba ganin dai dai ba arayuwarsa,....

Ruky ta dago Jin furucin mamah Amma tai shiru sbd indai tafadawa mamah cewa xata shiga case din baxa ta tava barin tava gara ta xabi tai shiru in yaso daga baya maman ta sani , ita dai baxata tava barin case dinnan ba in Sha sai inda karfinta ya qare xataje tai bincike ta gano inda matar nan take da zama,domin dole sai ankwatawa yarinyar ta hakkinta,ta share hawayen ta tace mamah bari na tafi wajen aiki karnai let ,mamah tace shikenan auta saikin dawo Amma ki share hawayen ki tukunna bana so a Raina min auta,ta qarasa fada tana murmushi Dan Bata so ko kadan taga abinda xai batawa autar tata Rai, ruky cikin dauriya ta qaqaro murmushi tace,saina dawo mamah haka taima mamah sallama sannan ta fita xuwa compound har parking lot inda ta tarar da har driver su ya gama mata warming din motar bayan Mai wankewa ya gama gogeta,haka ta shiga cikin motar tareda ansa gaisuwar da ma aikatan gidan ke mata haka tai reverse bayan me gadi ya gama wangale mata gate tasa kan motarta ta wuce wajen aiki , tunani fal ranta,...


______ZARI'A______

Sabon gari ,11:25am, Ameenah Ina kika je kifadamin wlh ko Kuma na miki dukan mutuwa,nan mijinki yaxo yace ya nemeki ya rasa ,kinfita gida tsakar dare ya nemiki ya rasa Kuma yace ke kika masa laifi danya miki fada shine kika sa qafa kika bar gidan mijin ki,ya dauka ma gida kika taho Ashe yawanki kika tafi,nace ki fadamin Ina kikaje tsawan wata daya bakixomin nan ba sannan Baki koma gidan mijinki ba,baba ya fada Yana iyowa kaina kamar xai dakeni haka nai baya amugun tsorace naje na makale a bayan ummah,...

Ina kuka Bakina Yana karkarwa nace baba wlh abinda na fada Maka gsky ne wlh baba saceni akayi Wanda da kyar na kubuto,ga nana itama sheda tace ita da ummah a gaban su wadanda suka tsinceni suka dawo dani gida Dan dai kawai ranar baka nan ne daka gansu,Kuma wlh baba Kabiru shiya koroni tsakar dare yace saina bar masa gidansa na rokeshi ya barni ma da safe na taho yace ba gidan ubana bane na bar masa gidansa,haka ya koroni waje,....

Yanxu kina nufin kicemin daga kaduna hayin rigasa xuwa ZARI'A kicemin ansaceki , yaushe mutum ya xama kamar ledar pure water da har xa'a saceki,wlh karya kike Kabiru baxai taba korarki ba ,ke kikasan inda kika tafi, asabe Dake bakin kofar ta tana hada kayan Miya ta tabe Baki tace Yo dama malam Allah na tuba yarinyar data Dade tana yawan ta xubar dinta na miye zaka tsaya kana Bata lokacnka da Ina ta tafi aikasan Ina xata , yarinyar da tun tana kankanuwar ta take biye biye ai baxa kai mamakiba Dan yanxu ta tafi biye biyen nata na tsawan wata daya ba,Banda Kabirun ya rufa musu asiri ya aureta wa kake Gani xai kwashe ta,Taya Kabiru ma xai koreta yaro me hankali da nutsuwa,ka duba kaga yadda yaxo gidannan a hargitse Yana Neman ta ai daukar sa tana nan gidan , Ashe lokacin ma sati Daya da barinta gidan nasa aidama ba Kaunarsa takeba shiyasa kullum saita masa laifi Kuma tace saita taho gida, kodan ai balaifinta bane inma da laifinata to xugata ake kartai xaman AURE ta samu lada,..

Sbd haka ita tasan inda ta tafi tunda dama can ta Saba y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????awan ta xubar dinta ta qarasa fada tana Mai watsawa ummah Wani kallo ita da Ameenah, ummah da tunlokacin da malam Auwalu Baban su Ameenah ya fara fada da cewa baiyarda da tsintar Ameenah akai aka kawota ba , ita tasan inda ta tafi take xubar da hawaye,yanxu Ace Ameenah kullum kalaman mahaifinta bazai bar kanta ba , harshima yanxu ya fara daukar maganar asabe na cewa Ameenah tana biye biye to me suke nufi kenan, tunanin tane ya katse lokacin da malam yake cewa ai itace take daurewa Ameenah kugu take duk abinda taga dama ,ai charaf sai asabe tace,yo gashi kuwa Tana boyeta a bayanta Dan karka hukuntata,malam Auwalu yace ai yanxu na kira Kabirun nace yaxo wlh saita koma gidansa Dan baxata kawomin abunkunya ba,inda Ameenah ta xube awurin tana rokarsa da Dan Allah karya ce ta koma gidan kabiru wlh Allah da gsk take ba yawo ta tafi ba ya yadda da ita inda malam Auwalu yayi tsaki ya bargidan ,inda akabar Ameenah ta rungume.ummah tana kuka itama ummah kukan take Nana na ta tayasu,Taya ZA'Ayi ace mahaifinsu baxai bincike akan magana ba Saidai kawai ya hau kai ya xauna Kuma tasan ba kowa ne yake xuga shiba sai wannan muna fukar matar da Bata kaunarsu da cigabansu ko kadan inda suka shige daki,ita Kuma baba asabe,ta cigaba da aikinta tana dariya ,da farinciki fal ranta ganin makiyanta a cikin damuwa,tana wake wakenta na habaici....



07066508376_______
'?

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD

*___JAMI'AR TSARO*___


*___THE WOMEN POLICE*___


_____THIS STORY IS TOUCHING HEART, I WAS SPEECHLESS TO EXPLAIN IT, BUT WE SHOULD SEE ON WHAT HAPPENED TO OUR LIFE KNOW, SO, BE WITH ME U LOVE IT MORE THAN U EXPECTED _______
'?


*NA*

*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ*___

*____(MRS SARAKIES)___*


*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION =?1?(QOWA)*


*Bismillahirrahmanirrahim*

_________season one episode 4??



_________
'?
'?

Ruky tana isa wajen aiki tai parking motarta a inda aka tanada domin yi, ta fito daga motar ta a Headquarter take aiki,Dan ita a bangaren binciki take Dan haka kai tsaye tai department dinsu,cikin tafiyar ta ta nutsuwa da Jan hankali,take takunta inda tana ratsa yaransu suna faman saluting dinta, kamar su cofur da Kuma sajens , da dai Wanda tafi rank ,Dan ita ASP ce haka dai take ansa musu ba yadda ta Sababa sbd kallo daya xakai mata kasan akwai abinda ke damunta, ...


Hardai ta qarasa office dinsu ,inda tana shiga bakinta dauke da sallama , tai saluting Wanda suka fita a rank Itama wadanda tafi sukai saluting nata, tareda da ansa sallamarta, kai tsaye ta nufi office dinsu Wanda suke su uku ne aciki,seat dinta ta nufa ta zauna,Bata ko kalli inda Shareef yake mata maganaba,Shareef yace a'a kaga ASP Auta yau kuma ko magana babu Ina magana ma ankyaleni kodai yau mulkinne ya tashi,...

Ta kalli Shareef da dara daran idanuwanta , masu Kyau da daukar hankali,Wanda Suke daukar hankalin duk Wanda ta xubawa su,ta Maka masa hararar wasa,ya ce to ya naga idan ki kamar wacce tai Kuka kodai,yauma mutumin yasamana ke Kuka ne,muje da rundunar yan sanda mu kamo shi musashi a cell,Dan baxamu yarda adinga samana JAMI'AR TSARANMU kuka BA,tai murmushi sbd shidai Shareef baxai taba ganin ta cikin damuwa ba yayi shiru ,Koda ko Batasan yin magana dole Shareef saiya sata tayi,sai Kuma ta ya Mutsa fuska tace please stop this thing waya fada Maka kuka nai,kawai Abu ne ya fadamin a ido ,mamah ta ciremin shiyasa kaga yayi haka,be side waya isa ma ya sani kuka kaima ka sani,wlh never, Shareef da dama so yake ya kunna ta ,ta cire Damuwar data ke ciki yace ai shikenan, police officer jajirtacciya kenan tai fari da ido tace fadi ka qara yayi dariya,yace to ya mamah, patan tana lpy ....

Tace lpyanta lau wlh,kaidama ka Dade bakajeba kullum Saita tambayeni kai, Shareef ya shafa kansa yace wlh kinsan kema ba xama mukeba,ke dama duk kece kika kwace Wani Jin Dadinmu,Muda kullum acikin aiki muke Amma ke gashi ana daga miki kafa Sosai,tace dama ku maxa baxa ku hada


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login