Showing 177001 words to 180000 words out of 278032 words

Chapter 60 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1099

kicibis da barrister's din su Alhaji sunusi Suma su biyu suka gaisawa cikin girmamawa kafin suka rabu, su_ su AA Arab cikin kotun suka shiga direct su Kuma naga sun Dan fita harabar kotun sun tsaya daga gefe suna magana, alokacin da su AA Arab suka shiga cikin kotun adai dai da motar Hanan ta shigo cikin kotun wacce suke tare ita da ruky,ya hanaf shima tare suka shigo Dan shiya kawo anty mufeeda wacce taxo tun jiya,Dan dama tace zatazo ,bayan sunyi parking duk suka fito suka tsaya ajikin motocin su, naga su Ruky sun k'araso kusa da anty mufeeda Dake jikin motar ya hanaf, hannu wanta harde a kirjinta tana kallan harabar kotun.Hanan ita uniform ne ajikinta sai after dress data Dora akai kamar dai kullum, ita ko Ruky mofty ne ajikinta ,sanye take cikin Wata maroon din Abaya wacce ta fito da ainihin kyanta da hasken ta Wanda ya fara Dawowa kwana goman nan datai agida yasa kalar fatar ta da hasken ta suka fara dawowa Dan ko wannan ramar datai ta ciko ba kad'an ba.....


Bayan sun qaraso suka tsaya abakin motar suna ta hirar su sama sama,ya hanaf dai yaja gefe suna waya Da ya Tahir Wanda ke tambayar sa sunxo kotun ne? shi Kuma ya hanaf ya bashi ansa da yanzu hakama suna cikin kotun, doc Fatima ce ta hango su Ruky yasa ta_ ta qaraso wurin su tana musu murmushi kafin ta ce "Assalamualaikum ASP sannun ku" duk suka daga kai suka kalleta kafin Hanan tai mata murmushi tana "doc kece? Kun iso kenan ? Ta fada tana murmushi ,doc Fatima tace " wlh Babu dadewa muka iso" sai Kuma ta kalli ruky wacce ke mata murmushi ta ce "ASP sannu koh? ruky ta ce
"Yauwa doc patan Kina lpy" doc Fatima tana murmushi tace "lpy lau ASP ya kuma abinda ya faru? Allah ya kiyaye gava" ruky ta ansa da Ameen, sannan ta ce "su baba sunxo ne ?tare kuke dasu? ta fada tana kallan doc Fatima, Doc Fatima ta juya tana kallon motar dasu baba lami suke ciki sai Kuma ta juyo tana kallon ruky ta ce " eh tare muke dasu suna ciki " ko zakije ki gansu ne? Ruky ta Bude ido kan ta ce "why not doc Muje ta Kalli anty mufeeda ta ce bari Muje wajensu anty ? Anty mufeeda ta gyada mata kai,daga haka suka qarasa har wurin motar dasu baba lami suke ciki,Hanan ce ta budewa baba lami motar ta fito ,ganin Ruky yasa ta Bude Baki alamar mamaki sai Kuma ta fashe da Kuka ta ce "sannu jami'a sannu, sannu kinji Allah ya Kiyaye gaba,itadai ruky murmushi kawai take mata tana kallan ta,can sai ta rike hannun baba lami ganin yadda ta rikice lokaci D'aya ta ce "Ameen thumma Ameen nagode sosai baaba , kidaina kuka yaudai gashi mun hadu Kuma cikin koshin lpy kin ganni" baba lami tana gyada kai ta ce " dole nai kuka jami'a Dan Allah ki yafe mun nasan duk nina jefa ku cikin wannan masifar da Kuka fada ta fada tana matse kwalla, Ruky ta girgixa mata kai ta ce "ba ku bane baba dama can haka Allah ya kaddara kuma Babu Wanda ya isa ya canza kaddararsa,sbd haka kiyi shiru" baba lami ta ce sosai kan wannan haka yake wlh naji Dadi jami'a Allah ya kiyaye gaba"ruky ta ansa da Ameen" kafin ta ce " Ina shafa" baba lami ta matsa daga jikin motar Hakan ya bawa Ruky damar ganin shafa Dake xaune a bayan motar, Ruky ta kalli shafa da murmushi a fuskarta ,kafin tai magana shafa ta gaida Ruky, ruky ta ansa tana tambayar ta jikinta shafa ta ce " da sauki Anty"ruky ta jinjina kai tace Allah ya sawake duk suka ansa da Ameen baba lami ta gaida Hanan, Hanan ta ansa mata, sannan shafa ma ta gaidata ta ansa mata da kulawa da tambayar jikinta....



suna nan tsaye suka hango AA Arab ya fito daga cikin kotun su sajen jabir suna biye dashi ya tunkaro motocin dasu Alhaji sunusi suke ciki,Hanan data hango shi ta Kalli Ruky ta ce " kai Kinga sir Ashe yazo tun dazu, Inaga ma tun dazu Yana cikin kotun kenan" gabasaya sai suka juya suna kallansa, sanye yake cikin ainihin uniform dinsu na police Wanda yay Masa bala'in kyau ga idanuwan sa rufe suke cikin bakin glass Wanda ake cewa tinted glass Wanda ya fito da ainihin kyansa ya ilaihi xo kuga kallo awurin doc Fatima suna tare da su ruky Amma hankalinta Yana kansa tunda Hanan ta ce "ga AA Arab ya fito" Idon ta daya sauka akansa taji nutsuwarta gabadaya ta bar jikinta,Yana Isowa wajen motocin ya Bada umarnin afito dasu, suka ansa masa cikin girmamawa,suna nan tsaye aka fara fito da yaran Alhaji sunusi aka jera su alayi daya , police din suka fara shigar dasu ajere xuwa cikin kotun.....



Bayan angama shigar dasu sai aka shigar da lateef Shima Wanda hannunsa suke sanye da handcuff yayi duhu yayi Baki yayi laushi abun dai abun tausayi ,Saida suka tabbatar da anshigar da kowa sannan sai su Alhaji sunusi su biyu shida babajo Ali sune na qarshe sanye suke da handcuff a hannunsu idan ka Kallesu sai ka tausaya musu Sbd yadda suka koma kamar ba manya manyan 'yan siyasar nan na jihar Kaduna ba Wanda ake ji dasu,haka Suma aka shigar dasu ,ya hanaf Daya Kalli Alhaji sunusi ji yake kamar yaje ya shake shi har sai ya daina numfashi tunda shima shiya kashe musu mahaifi,ai yaso ace mamah ta bari Suma ankwato masu hakkinsu da wlh sai yayi shari'a da Alhaji sunusi har sai yaga andaure shi,Ammasa daurin Rai da Rai sannan hankalinsa xai kwanta,Suma Kuma iya lansu duk sunxo kotun sbd sun San yau xa'a fara Shari'ar,su Hajiya SA'A sunzo ita da Samira in kika ganta ta zama abar tausayi duk ta zare sbd damuwa.....



Bayan anshigar dasu Alhaji sunusi cikin kotun,AA Arab ya qaraso kusa da motar su shafa,su DCP suna tareda shi, CP Bai baixoba shi Yana headquarter Yana kula da ita Amma zai xo anjima da zarar anfara zaman kotun,bayan sun iso Hanan ta washe Baki tana gaidasu duk suka ansa suna tambayar ta aiki ta ansa da Alhamdulillah, sauran duk suka gaidasu,sannan Hanan ta juya ta kalli AA Arab shima ta gaidashi ya ansa mata da kulawa,doc Fatima ta gaida AA Arab cikin Wani Irin salon da yaja hankalin Hanan Dan ita Allah ya Bata baiwar Gane Irin masu wannan halin,Amma batace komai ba tai shiru tana kallan Ruky wacce suke gaisawa da DCP asake, Amma baza tace komai ba har sai qara kama ta da maka mancin wannan, Bayan ruky sun gama gaisawa da abokanan aikinta da su sai alokacin suke mata jajen abunda ya faru sai ta Dan kalli AA Arab Wanda ke magana da Shareef, ganin ya juyo yasa ta gaidashi ya ansa mata Yana kallan hanan ya ce "hanan ku fito dasu ana gama wannan shari'ar Suma ZA'A Yi tasu in Sha Allah" babu musu hanan ta ansa masa cikin girmamawa sannan Yabar wajen yay gaba su DCP suka mara masa baya,bayan su baba lami sun fito Hanan da ruky da doc Fatima suka nufi cikin kotun suma wasu police suna biye dasu abaya.....



___________?&


A wannan lokacin da su ruky suke shiga kotu akuma lokacin da su ummah suke bakin gate din headquater an hanasu shiga,Dan karfe bakwai na safe ma agarin Kaduna tai musu,a Kuma gabansu, gabadaya motocin da aka fitar dasu Alhaji sunusi da motar dasu Ameenah suke ciki suka fito daga cikin headquarter Amma abunka da Wanda Basu sani ba,sai Basu d'auka su bane ba,yanxu k'arbe goma Saura na safe , ummah da idonta ya kumbura sbd kukan da taci jiya ga Kuma Rashin baccin da batai ba Daren jiyan ga sunzo anki barinsu su shiga ta Kalli malam Auwalu Wanda shima dauriya kawai yake Amma har ga Allah ya gaji ta ce " malam kaga sunki sauraran mu koh? malam Auwalu ya ce " to Kinga sunki sauraran mu ma yau kenen,yanxu da ace jiyan da daddaren mukaxo aida ba wannan zancen ake ba" ummah ta sauke kanta qasa tai shiru batai magana ba,suna nan xaune motar CP taxo xata fita daga cikin headquarter, driver ya tsaya ganin sunje bakin gate din,police din wurin suka mike suka hau saluting dinsa tareda gaida shi cikin girmamawa, CP ya Kallesu ya ce "me mutanan can sukeyi anan tun safe Dana shigo d'azu ma nagan su gashi har yanxu suna nan basu tafi ba?ya fada Yana nuna musu su ummah da malam Auwalu Dake xaune acan gefen gate din....



Daya daga cikin police din ne ya ce " sir wai 'yarsu ne da aka dauko jiya wai ahayin rigasa,take CP ya Gane inda suka dosa Dan haka ya daga musu hannu ya cewa driver su tafi , driver yaja motar Saida suka zo dai dai inda su ummah suke sannan yasa driver ya tsaya da motar,ya Kallesu ya ce "malam lpy? Me kuke yi anan?malam Auwalu ya taso cikin rawar jiki da girmamawa ya gaida CP, CP ansa Mai da kulawa,ya ce "me kuke yi anan tun safe ,me kuke so ne ?ya fada Yana kallan su,cikin damuwa Malam Auwalu ya fadawa CP komai, CP ya jinjina kai kafin ya ce "GSKy Anyi haka, Amma yanxu 'yar taku Bata cikin headquarter,tana can kotu, tare ummah da malam Auwalu suka hada baki wurin fadin kotu Kuma yallabai?CP yay murmushi ya ce"karku damu ba ita kad'ai bace akwai wasu ba Kuma Wani abun bane duk suna kotun can aka tafi dasu ,yanxu abinda xa'ayi ku shigo motar Nima kotun zanje in yaso Acan zaku ganta Amma ku kwantar da hankalinku babu Wani abun ana gama Shari'ar ne za'a sallamesu in Sha Allah".....



Malam Auwalu ya Sauke numfashi kafin ya ce "mun gode yallabai"Sai Kuma ya Kalli ummah da itama ta sauke ajiyar xuciya ya ce "shiga muje" ummah ta ansa masa sannan ta hau Yiwa CP godiya, CP ya ce "Babu komai"ummah ta shiga gaban motar shi kuma malam Auwalu ya shigo baya Aiko haka akayi bayan sun shiga driver yaja suka tafi kotu.....




Suna shiga kotun, Babu Bata lokaci suka shige cikin kotun adai lokacin da kowanni barrister ya gama gabatarwa da kotu kansa amatsayin lauyan wanda yake karewa, ummah tsoro ya kamata ganin irin girman kotun da mutanan dake cikin ta kamar me,Bata iya hango Ameenah ba sbd wurin zamansu daban yake ,su su ummah sun xauna ne awajen zaman masu xuwa kallan qara daga can baya, lauyan gomnati ya tashi ya gabatarwa da kotu hujjojinsu ,Suma Kuma barrister Wanda suke karewar ya tashi ya Bada hujjojisa ,andade ana fafatawa kafin daga karshe, lauyan gomnati yay nasara ,anyankewa yaran su Alhaji sunusi hukuncin xaman gidan yari na dun dun ,har qarshen rayuwar su, ummah bawani sanin Kabiru tai ba Amma Kuma idan ta ganshi zata iya Gane shi shiko malam Auwalu azau nan da yake ya hango Kabiru sbd gabadaya a tsaye suke agaban kotun an anjeresu......



Su Kuma su Alhaji sunusi matansu sunce Basu yadda ba zasu dauka kaka qara Dan Hajiya SA'A ita Kanta taxo,yanzu and'age Shari'ar su Alhaji sunusi sai nan da mako biyu, Kuma acikin kotun za'a Yi Shari'ar.Ameenah daga zaunan da take_ take kuka ita Kanta batason kukan me take ba, tabbas taga shigowar su ummahn ta Amma babu damar tashi daga inda take sbd Suma a hannun hukuma suke,ta Kuma ji Dadi da akai komai agabansu ummah da malam Auwalu sbd sai sunfi yarda wai Gani ya Kori ji.sai shari'ar shafa da lateef Suma sai andawo Wani xaman sai nan da mako daya.anfara fitowa daga kotun Saida aka shigar da su Kabiru motocin da aka shigo Dasu aciki sai kuka suke kamar me Jin hukuncin da aka yanke musu xa'a kaisu prison, matansu sai kuka suke da dukan alamu kila ko sun hada xuri'a dasu ne.sai Alhaji sunusi suma ance prison za'a Mika sun bar hannun jami'an tsaro sun koma hannun kotu tunda yanxu suna qarqashin kotu ne. AA Arab ya fito daga cikin kotun suna tsaye shida barrister dinsu,su ruky sun fito sai ya Mutsa fuska take alamar ta gaji anty mufeeda sun shiga motar ya hanaf har sun tafi gida , Ruky taje sukai sallama da baba lami da tambayar ta ya jikin shafan Suna ganin canji kuwa? Baaba lami ta ce " babu laifi suna ganin canji tai musu patan samun lpy sannan suka nufi motar Hanan, Hanan ta dubi ruky ta ce "nifa ban ganewa wannan doc Fatima ba? Ruky ta kalleta ta ce "kamarya?Hanan ta ce "Kalli can" ruky ta kalli inda hanan ke nuna mata ta hango doc Fatima tsaye ita da AA Arab suna magana sai Wani karai raya take masa, ruky ta d'auke kai ta dubi Hanan ta ce "na gani, Amma ke miye naki aciki? Hanan ta ce "ke Babu komai nawa aciki Amma ke bakiga yadda doc Fatima ke shishshigema ya Ahmad ba" ruky ta tabe Baki ta ce "to ke Kuma Ina ruwanki naga kema haka kike shish shige masa ko haushi kikaji Dan itama tana shishshige masan" ta qarasa fada tana Dariya, Hanan tai tsaki ta ce "sai dai abinda yafi Nima haka nake masa kin taba ganin Ina masa wannan karai rayar ? Ke Dan bakiga abinda na gani bane shiyasa"ruky ta Bud'e ido ta ce "fadamin Dan Allah me kika gani? Hanan ta harareta ta ce "bazan fada ba"ruky ta kamo hannun Hanan tasa dariya ta ce "kiyi hkr sis ki fadamin Dan Allah sis" ta fada tana marai raice wa, Hanan ta ce "wlh bazan fada ba" ke ba kin Raina min hankali ba"ruky ta turata tace"kada Allah yasa ki fada din daga haka tana kokarin shiga cikin motar Hanan, Hanan tai murmushi tana kallan ta ta ce "xanyi maganin kine" tana kokarin shiga motar taga Khalil ya qaraso wajen su da murmushi a fuskarsa, ruky ta fasa shiga motar ta tsaya har Khalil ya qaraso suna yiwa juna murmushi,bayan ya iso suka gaisa harda Hanan , kafin Hanan ta ce "kaga Dan jarida har an dawo bakin aiki kenan" ta fada da sigar tsokana , Khalil yay murmushi ya ce "ai da k'yar su baba suka barni na dawo bakin aikina,Kuma da biyu na dawo Dan honorable sunusi ya ganni yasa nace ni xan dauki labaran yau, gabadaya Dariya suka Saka ruky ta ce"yo Nima bansan ya zan kwashe da mamah ba dan naji tana cewa ajiye aikin nan xanyi"Khalil ya kalleta ya ce "ai iyayan namu sun tsorata ne,Nima fa Dak'yar suka barni Saida MD dinmu yasa Baki" Hanan ta kalli ruky ta ce"muma idan mamah ta Hana da boss dinmu zamu had'ata ya Bata hkr" ta fada tana kallan Ruky,Khalil ya ce "shikenan koh "dama Yana da kirki" Hanan ta ce "sosai ma a idan kace kirki kad'an ka fada kadinga sa domma taini, Khalil yay dariya ita dai ruky sai hararar Hanan take,sun Dade suna tattaunawa kafin daga bisani suyi sallama Khalil ya tafi , bayan tafiyar Khalil ruky ta shige motar ,Hanan itama harta shiga Kuma sai Kiran AA Arab ya shigo wayarta ta Kalli Ruky wacce ke kallan ta ta ce "ya Ahmad na kirana bari naje"ruky ta gyada mata kai daga haka hanan ta Bude motar ta fita ruky Kuma ta dauko wayarta ta hau whatsapp ta fara viewing status ta dinga cin karo da labaran wanna xaman kotun da akayi,gefe Daya Kuma tana Jiran Hanan ta gama su tafi ......



Ameenah sun fito daga cikin kotun suka rungume juna da ummah bayan sun fito sun Hadu sai kuka kamar me malam Auwalu dai Yana gefe Yana kallansu da tausayi a fuskarsa Dan Bai taba Jin tausayin Ameenah Irin na wannan lokacin ba ,ga wata iriyar kunyar ta da yake ji ,Dan kafin su fito daga kotun ya sanar da ummah abinda Kabiru suka aikata har aka kawo su kotu ,ummah ta ce cikin kuka "ki yafe mana Ameenah kiyi hkr munyi kuskure "sai ta qara rungume ta,tana sakin kuka Mai tab'a xuciya, itama kanta Ameenah kukan take tana cewa "ummah Babu komai, ni bakiyimin laifin komai ba"police dinne yay musu magana yasa da kyar da kyar suka saki juna suna kuka suna komai suka rabu Dan sai sunje headquarter sannan za'a sallamesu, Ameenah tana tafiya kawai suka ci karo da mutum agabanta kawai d'agowar da zatayi Idansu ya sarke cikin na juna,kowa kallan kowa yake basa kiftawa, barrister shamsu ne ya fara cewa cikin mamakin ganin ta "Ameenah" Yana kallan ta da mamaki qarara a fuskarsa,itama Ameenah kallan sa take duk da shekaru sunja amma baxa ta taba mantawa da wannan fuskar ba, fuskar data sota tsakani da Allah acan shekarun baya kallanshi take cikin shiga ta lauyoyi kafin Police din ya qara Yi mata magana Hakan yasa ta bishi , shidai barrister shamsu ya bita da kallo kasa motsawa yay Dan har lokacin mamaki yake meya kawo Ameenah nan kawai saiya bi bayan ta.......





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ___*



*____THE WOMEN POLICE____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 7?? 3??


____________?&


*ZARI'A*


A lokacin da su ummah suke cikin garin Kaduna, a ZARI'A kuma lokacin da Rana wajen karfe D'aya baba asabe tana bakin murhu ta gama abincin siyarwa da suke Koda yaushe,tana xubawa acikin kuloli kawai taga lawisa kamar daga sama ta shigo cikin gidan da bakkon ta ta kaya a saman kanta ga 'ya'yanta data shigo Dasu suna binta abaya ragaje_ragaje dasu kusan su biyar, gasu Babu wata suturar kirki ajikinsu daga ita har yaran yadda kuka San 'yan gudun hijira da kaya duk ayay yage sun kod'e har sun shiga uku.baba asabe ta d'ago da kanta gaban ta na fad'uwa Tama kasa furta Komai kawai kallan lawisa take kamar Idon ta zai zazzago qasa sbd


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login