Showing 162001 words to 165000 words out of 278032 words

Chapter 55 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1107

Alhaji sunusi da yallabai taju da babajo Ali da sauran 'yan kungiyarsu suka,sako AA Arab agaba, yadda zasuyi shima su kawar dashi kawai suke so.ayauma suna wannan xaman kowa ya Bada tasa shawarar akazo kan Alhaji sunusi, ya Alhaji sunusi ya Bada shawarar shima a kashe shi kamar yadda ya kashe Dan uwansa, yallabai taju yay shiru yana tunanin maganar Alhaji sunusi,sai Kuma ya numfasa yace "ba haka xamuyi ba,idan mukace shima kashe shin xamuyi to ida nun mutane zai iya dawowa kanmu,ko Kuma asirinmu ya tonu,ni nasan yadda xa'ayi masa",sukace "me xa'a Yi masa yallabai? yallabai taju yay murmushi yace kasar zamusa a fitar dashi gabadaya.sukace "kamar Ya ya yallabai? yallabai taju yace "ana daukar wasu police akaisu wata qasar aiki,suyi shekaru acan ,to shima haka xamuyi masa kawai ya bar qasar gabadaya yadda babu Wanda zai qara Jin labarinsa, bare ya bawa wasu logic na dabarun aiyukansa ,Dan wannan yaran hatsa bibi ne,idan Yabar qasar anan ne xamuyi aikinmu yadda ranmu yakeso babu Mai sa mana ido,Suma sauran da suka rage duk zamu Ji dasu,tunda akwai kudi ai anwuce wajen tuni zamu siyesu .da wannan shawarar da yallabai taju ya kawo sukai na'am da ita suka tsaida matsayar shi yallabai taju zai kira president ya fada masa....



Washe gari ko haka akayi yallabai taju ya kira president sukai magana babu yadda president ya iya ya ansa umarnin uban gidan nasa, bayan sati Daya AA Arab Yana office sai ganin Kira yay daga federal government akan anmai transfe??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r anfitarshi daga kasar gabadaya xuwa qasar labanin daga nan xuwa Wani satin zai tafi .take AA Arab ya Gano suwaye sukai masa wannan aikin,haka ya tafi gida bayan ya tashi daga aiki, ya samu Abba da ummi ya fada musu yadda aka kira daga federal government aka bashi umarnin barin kasar.shi babbar damuwarsa da akace Koda wasa karya kuskura ya dawo kasarsa har sai anbashi umarnin yin haka,take ummi ta shiga Damuwa bayan AA Arab ya sanar musu yadda sukai dasu yallabai taju,yace"Yana Kuma tunanin su sukai masa haka.bayan sungama sauraran sa suma sunyi tunanin tabbas zai iya yiwuwa su yallabai taju ne suka sa aka masa wannan Rashin adalci sbd ai Babu Wanda Bai San shidin uban gidan president bane, Kuma shine god father's dinsu. ummi tace "ita zatabi danta" Abba yace "tayi hkr xasu dinga xuwa ganinsa akai akai".AA Arab yace "shi aikinma zai ajiye gabadaya Abba yace kar yay haka,ya bari kila wata gomnatin idan ta hau zata iya dawo dashi,da kyar dai ummi ta hkr sannan suka hadu suka lallashi AA Arab harya amince ya yadda zai tafi din....



kafin ranar baisan ya akayi mutanan gari suka san da maganar barin kasar da zaiyi ba,haka mutanan garin Kaduna, suka damu ganin sun samu saukin matsalar tsaron nan Amma shine Kuma xa'a fitar da AA Arab daga kasar.take matasa sukai dandazo suka shiga gidan radio suna ta fadar maganganu Dan ransu da xage xage da iFace iFace su Basu yarda ba abar musu AA Arab,adali ne me GSKY kaza kaza suka dinga fadar magana a social media suna baxa hotunan AA Arab suna justice for AA Arab,take gari ya dauka da k'asa Baki daya.yallai taju Yana xaune a falonsa Alhaji sunusi ya nuna masa abinda ke faruwa a social media,take ran yallabai taju ya Baci ya kira governor yace lallai lallai a tsawa tarwa yarannan, Aiko governor ya ansa masa Babu Bata lokaci yasa asanar da cewa duk Wanda aka kama Koda wasa yay xancen AA Arab ,sai ankama shi, Kuma idan aka kama mutum gidan yari xa'a Kaisa, idan ma aikacine kai a cire ka daga aikin sannan akai ka gidan yari, xa'a sa matakan tsaro na farin kaya zasu dinga bi majalisa majisa, suna xama ,da sun kama mutum Yana xancen AA Arab take xa'a kama shi,to wannan abin shiyasa mutanan gari suka nutsu suka daina xancen AA Arab,sati na cika AA Arab ya bar qasar bisa ga rakiyar sister's dinsa, sunyi kukan rabuwa dashi ba kadan ba harda ummi, sun masa addu'o'i sosai, wannan kenan.....


Anty mufeeda saida tai sati uku sannan ta koma dakin mijinta, lokacin mamah harta Dan gana mikawa Allah lamuransu,ta rike 'ya'yan ta hannu bibbiyu,gefe Daya tana kula da amanar da Allah ya Bata ta tarbiyar tar da 'ya'yanta.har kuma lokacin Alhaji sunusi Bai dawo gidanba,abin saiya bawa mamah mamaki ganin Irin yadda ya damu lokacin da Dan uwansa ya rasu.Amma Batai magana ba,har ranar sadakar arba'in taxo akayi su anty mufeeda Da ya Tahir sunxo, Sai da anty mufeeda tai sati Daya sannan ta koma ya Tahir Kuma kwana uku yay ya koma.akuma lokacin aka bawa hanaf Aiki,Yana aiki a CBN na garin Kaduna.haka dai su mamah suke cikin kulawar ubangiji,har ruky sukai jamb ta samu 220 dama tunda Abba ya rasu tace da Mamah ita xata gaji Abba,mamah batai mata musu ba ta amince mata da mata faran alkhairi, first choice dinta ta cike police academy wudil.sai Kuma suka fara shirye shiryen xana SSCE,babu dadewa suka duka xana har suka kammala bayan watanni results ya fito Rukayya ta samu 9 credit ,Dan haka suka xana jarabawa taci,bayan sati biyu xasu tafi makarantar, alokacin Kuma anti mufeeda ta haihu aka samu 'ya mace suka tafi suna yarinya taci sunan mamah ,wato Halima ake ce mata mimie,bayan Rukayya ta dawo da sati Daya suka tafi makaranta to anan ne suka hadu da Hanan shima shareef dama can ya cike sai suka hadu su uku kenan.gefe Daya Kuma lateef Yana damun Rukayya da kira awaya Yana ce mata yanasonta har lokacin ita Kuma Ruky tana cewa masa ita amatsayin Dan uwa ta daukeshi ,Dan Bata taba cewa tana Sansa ba Koda wasa .idan ya samu mamah ya fadawa sai tace ya jira mana ai haryanxu Rukayya batason menene soyayya.to idan mamah ta fadawa lateef haka baya tunin maganar ta sai ya dauka cewa Rukayya zata so shi.bayan shekara biyu da rasuwar AIG umar MaiTama shima yallabai taju ya rasu bayan doguwar jinya dayasha,Dan Saida ya koma kamar Wani karamin yaro sbd yadda ya rame ya kwanjame,aiko da yake wasu sun San tsiyar Daya aikata aqasa suka dinga Allah Wadai suna Allah ya qara,wasu Kuma suna cewa alhakin mutanen daya xalinta ne yake bibiyar sa. magan ganu dai ba'a cewa komai,wannan kenan.haka har su Rukayya suka gama karatunsu suka fito amatsayin ASP duka su ukun,Kuma akai posting dinsu headquarter anan aka aka rabasu da Hanan ita aka kaita government house, Shareef da Rukayya Kuma a barsu a headquarter wannan kenan.....



*Cigaban labari*





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y




*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)____=?1?*




*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season two ep 6?? 7??



____________?&

AA Arab Yana fita direct office dinsa ya shige Yana shiga ya Ra rufo kofar , ya jinginar da kansa ajikin kofar Yana Mai dafe kansa Dake barazanar rabe masa gida biyu ,da Jan kafa ya qarasa kan kujerar office din sa ya zauna yana sauke numfashi,har lokacin hannunsa na dafe da kansa,Dan da gsk yake Jin ciwon kan,ya jinginar da kansa jikin kujerar ya lumshe idonsa ,Yana nan xaune wayarsa tai vibrate alamar kira,kamar baxai picking ba saikuma ya jawota Yana ganin sunan Dake yawo kan screen din wayar,ganin me kiran yasa saida ta kusan tsinkewa yay picking ya kai kunne.shiru yay yana sauraran abinda ake fada masa,bayan ya gama sauraran abinda Wanda ya kirashin ya fada masa ya sauke wayar Yana furxar da iska Mai xafi daga bakinsa,sai Kuma ya mike ya shige toilet din cikin office din nasa .karfe biyar Saura na Ranar AA Arab ne tsaye shida DCP ya fito daga Wani building Dake cikin heardquater gefensa DCP ne,daga Gani magana suke Mai muhimmanci Ganin yadda AA Arab ya Bada All ears dinsa Yana sauraran DCP....


Bayan ya gama sauraran DCP Ya sauke numfashi yace "muktar kabar wannan zancen sai na dawo may be ma kila sai dai xuwa gobe sbd after isha'i prayer xance government house governor Yana nemana"DCP yace cikin girmamawa "okay sir"Allah ya kiyaye"AA Arab ya ansa masa da kai ,daga suka rabu DCP ya koma ciki AA Arab Kuma ya shiga mota da driver ke jiransa tun dazu,Dan xuwa asibiti,Dan dazu babu dadewa Hanan ta kirashi tace likita yace yanxu xasu sallami Rukayya....


Cikin mintuna da Basu Gaza 20 ya kawosu asibitin ,ya fito daga motar bayan anbude masa,ya fara zuro da kafafuwansa Wanda suke sanye cikin bakin cover shoe me bala'in tsada da yarari,babu Bata lokaci Cikin nutsuwa ya fara tafiya xuwa dakin da aka kwantar da rukayya.saida yay knocking aka bashi ixnin Shiga, Sannan ya tura kofar ya shiga kansa a qasa bakinsa dauke da sallama.suka ansa masa da kulawa suna Bashi wurin xama Saida ya shiga ciki sannan ya dago da kansa ya Kallesu ya taddasu idanuwasu duk sun kumbura sbd kukan da sukai dazu.ya risina ya gaida mamah.mamah ta sakar masa murmushi ta ansa da lpy lau Ahmad ya aiki ya kokari,kansa a Kasa Yake ansa mata,ya gaida baba hasiya da anty mufeeda duk suka ansa masa asake.ya juya su ya Tahir suka Mika masa hannu yay Musa baha dasu duk fuskar su a sake.Hanan tace sir good evening,yace evening Hanan, Rukayya Dake zaune jikin anty mufeeda ta gaidashi batareda ta kalleshi ba murya can qasa,kallo Daya yay mata ya dauke kansa yana ansa mata kamar yadda ta gaidashi.har lokacin Kuma TV dakin tanayi Amma wannan Karan Wani shirin suke ba labarai ba.nan ya Gane kila sun Kalli labaran dazu...


Xuwansa babu dadewa doc Hadi ya shigo bakinsa dauke da sallama fuskarsa dauke da murmushi bayan sa wata nurse ce ke biye dashi.bayan ya shigo dakin ya gaida mamah ta ansa Sannan ya juya suka gaisa da mutanan cikin dakin .ya Kalli Ruky wacce tai lakwas jikin anty mufeeda kamar wata qaramar yarinya tana tura Baki gaba ,da murmushi a fuskarsa ya ce " ASP ya jiki ?ruky ta ansa masa Batare da ta kalleshi ba,ya ce "babu inda ke miki ciwa yanxu ? Rukayya ta gyada masa kai tareda dacewa "eh"cikin sanyin murya,sai Kuma ta ya Mutsa fuska tace"kawai iya kaina ne ke ciwo"ta qarasa fada kamar xata saki kuka.doc Hadi yay murmushi yace "wannan ba matsala bane ASP zai daina Indai kika cigaba da Shan maganin da muka rubuta miki in Sha Allah zai daina, ya kalli nurse din da suka shigo tare yace"gwada mata BP" Babu musu ta matsa gaban gadon da Rukayya take xaune,ganin haka yasa anty mufeeda mikewa xata matsa nurse din tai aikinta Rukayya ta riketa ta shagwabe fuska tana Kallanta tace "antyyy"taja tyyy din da Wani salon shagwaba,ba anty mufeeda ba kowa a dakin Saida ya Kalleta wannan sabon bacin na Rukayya, harshi kansa AA Arab baisan lokacin Daya kalleta ba,common BP ZA'A gwada mata Amma take kokarin yin kuka.anty mufeeda tace"ya akai ki tsaya BP kawai ZA'A gwada miki fa ba Wani Abun ba Auta . Rukayya ta qara turo Baki gaba ta mika hannun,AA Arab ya kauda kansa Yana mamakin ta .haka nurse din nan tai mata, data gama ta kalli doc Hadi Wanda ke sauraran yaji me zatace results din ya Bada tace" sir normal ne" doc Hadi yace "to Alhamdulillah,in Sha Allah Yanzu xamu sallameku,ya Mika musu takardar sallama ya tahir ya karba yace"mungode sosai doc.doc Hadi yay murmushi yace"Allah ya sawake daga haka ya mikawa AA Arab hannu sukai musabaha ya nufi kofa,AA Arab yabi doc Hadi waje Dan akwai maganar da xasuyi itace ma ta kawoshi....



Mamah ce ta fara mikewa ta qarasa gaban gadon da Rukayya take xaune tana kokarin kama Rukayya. Hanan ta hanata tace"ki bari mamah meye anfanina bari na riketa,mamah Bata hanata ba,Hanan ta kalli ruky ta mika mata hannu tana mata , itama ruky murmushin tai mata ta rike hannun Hanan data mika mata ta mike Dakyar, Hanan ta rungumota ta side Daya,anty mufeeda Kuma ta hado musu kayansu ya hanaf shiya riko hannun mimie ya Tahir Kuma ya riko hannun moha suka fito daga dakin gabadaya.sun tadda AA Arab tsaye Yana ansa waya ganinsu yasa ya katse ya karaso ya Kalli mamah yace"Allah ya sawake mamah, Allah ya kiyaye gaba in Sha Allah xanxo har gida sbd bamu gama wasu abubuwan ba, Amma idan mun gama xanxo in Sha Allah, mamah tace "shikenan Ahmad mungode sosai, Allah ya kareku aduk inda kake,yay murmushi baice komai ba.ya Tahir ya ce "officer mungode sosai Allah ya Saka da Alkhairi ya sa albarka acikin ayyukan ku ya kareku a duk inda kuke.AA Arab ya ansa da Ameen,ya Kalli moha Dake kallansa ya shafa kansa Yana masa murmushi,abin mamaki moha uban kiyiwa , Amma sai gashi yay Ma AA Arab murmushi,ya Tahir ya Kalli moha yace "uncle ne shima, oya great him moha,moha ya mikawa AA Arab hannunsa yace cikin gwarancin muryasa good evening uncle"AA Arab ya Mika masa nasa hannun yace"how are moha, moha yace " fine uncle"AA Arab yace"that's good,ya Tahir Yana murmushi har sannan yace "bari muje officer ,AA Arab ya ce"ok "moha ya dagawa AA Arab hannu ya ce"bye bye uncle "AA Arab yay murmushi yace "bye bye my friend,ya Tahir yay murmushi suka qara sallama sannan kowa ya nufi motarsa.....


Su mamah da anty mufeeda da baba hasiya da mimie har sun shiga motar da sukazo acikin ta ,Hanan Kuma da Rukayya da moha sun shiga Ta ya Tahir da yaje gida daxu ya dauko motar,Hanan da Rukayya abayan motar sai moha Dake gaban motar shida ya Tahir,motar ya hanaf ce ta fara yin gaba saita ya Tahir sannan saita AA Arab,ajere suke tafiya Saida sukaxo junction ne suka rabu su_ su Rukayya xasuyi malali shi Kuma AA zaiyi heardquater,ganin motar AA Arab tai gaba yasa ya tahir yay musu horn moha ya juya ya kalli gefen motar saiya hango gefen fuskar AA Arab ta cikin glass din window motar Da yake zaune a Baya Kuma ya Dan dage glass din window kadan,ya daga murya da iya karfin sa yace "uncle " AA Arab ya juyo yay Masa murmushi tareda daga masa hannu, Rukayya ta juya taga waye uncle din da moha yake kira,kafin ta juya har motar tai gaba Suma adai dai lokacin da suka hau kan titin da zai sadasu da malali , Amma Kuma ta hango motar tabbas motar AA Arab ce domin taga lokacin Daya shiga ciki dazu kafin su fito daga asibitin.ta tabe Baki ta jinginar da kanta bayan kujerar motar tana lumshe ido....



Suna isa gida bayan anbude musu gate Hanan ce ta fara fitowa daga cikin motar sai ta taimakawa ruky itama ta fito da kyar tana ya Mutsa fuska alamar akwai gjy tattare da ita.su mamah tuni sun fito daga cikin motar da suke ciki har anty mufeeda da baba hasiya suna shigar da kayan da sukazo dasu cikin falon, masu aikin gidan tuni sun qaraso suna musu sannu da xuwa,da Taya mamah murna na dawo war da Rukayya tai,suna yiwa Rukayya sannu, mamah ta answer musu da kulawa, sannan tai gaba ganin har su Rukayya sun shige falon.tana shiga ta tarar har Ruky ta zauna kan Daya daga cikin kujerun falon mamah ta kalle ta tace sannu Auta me zakice yanxu hasiya ta shiga kitchen ta girka miki.ruky ta kalli mamah sai Kuma ta girgixa kai tace "babu komai"mamah tace"a'a baxaiyu ki xauna haka ba tashi muje dakina kiyi wanka ko zakiji dadin jikinki kafinnan in Sha Allah angama dafa Miki ko pride rice ne,ko Kuma Abu medan sauki.baba hasiya ta ce "uwata daure WA zakiyi bari ko kunu ne saina dama miki kisamu kisa acikin ki kafin ayi girkin,ai bazaiyu ki xauna haka ba"ruky tai.mata murmushi ta gyada mata kai.mamah ta ce "ko kefa muje. babu musu ta mike Dan dama wlh ta matsu taji ta xuba ruwa ajikinta.gabadayasu Daki suka shige Dan watsa ruwa Dan rabonsu da wanka tun jiya .mazan ma part dinsu suka shige kafin anjima su fito....



Bayan magrib gabadayansu suna falor a zaz zaune har maman Shareef wacce taxo
tun dazu,dama ta je lokacin suna asibitin itada maman Hanan da Bata Dade da xuwa ba.yanxu haka mamah suna xaune itada maman Shareef da maman Hanan suna Maida yadda akai kan labarin da Rukayya ta Basu Wanda Alhaji sunusi ya dinga gana musu azaba kala kala, da Kuma hirar da sukaga dazu AA Arab yayi dasu Alhaji sunusi da tambayoyi da Irin ansar da yake bayarwa,itadai ruky suna gefe itada anty mufeeda da Hanan sai mimie Dake kan cinyar ta axaune tana shafa kanta, tunani fal ranta ,maman Shareef tace "wlh Halima karki yafewa wannan azzalumin mutumin Aiko bakiyi qararsa kan kashe miki miji da yay ba, zaki qararsa Dan sace miki 'yarki da yay, Kuma yake kokarin kasheta .mamah ta sauke numfashi tace"hmm"Amma batace komai ba.maman Shareef ta ce"bawai hmm zakice ba magana xakiyi Koba haka ba hasiya,ta fada tana kallan baba hasiya
.baba hasiya tai murmushi Amma batace komai ba.mamah tace"adda idan Kinga yadda zuciya ta take tafasa sai kin tausayamin,babban abinda na qara Jin dole ma sai anbiwa Rukayya hakkinta shine,wai mutumin Dan bashida imani kusan kullum sai yazo gidan nan Yana Wani bani bakin nai hkr ,ashe Raina mana hankali yay tayi Ashe shii yasan inda 'yata take, Ashe shiya dauke ta,Kuma Bai tsaya nan ba ya dinga gana musu azaba wacce ko kisan kai sukai baza'a musu Irin taba, bare suda suke kan gskyr su ,kai wlh na Dade Banga marar imani Irin sunusi ba",maman Shareef tai kwafa tace "wlh Halima alokacin da kike fadamin bakiji yadda gabana ya fadi ba, nifa dama na Dade da sanin wannan sunusi furkar kafiraice dashi,wlh dolema yagamu da masifa aduniyar nan kafin ma yaje lahira,ke kiga irin abubuwan da suka aikata,wlh shima Irin mutuwar da uban gidan nasu yay shima Irin ta zaiyi koma tafi tasa.suka ce sosai, sudai su Rukayya suna gefe suna jinsu nan dai sukai ta Maida yadda akayi da yadda Alhaji sunusi ya dinga xuwa Yana Raina musu hankali......



___________?&



Hajiya SA'A lokacin da taxo heardquater hanata shiga sukai tai tai su bari ta shiga sukaki ta Dunga musu hauka tana zaginsu Amma suka hanata,daga qarshe


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login