Showing 72001 words to 75000 words out of 278032 words

Chapter 25 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1025

gama wannan azababban Auran,malam Auwalu yace ni Kuma wlh Babu dalili babu yadda xa'ayi ki kashewa yarinyar nan auranta, tana xaman xamanta lpy adakin mijinta,ummah tace ni Kuma wlh saidai bani na haifi Ameenah ba, Amma wlh saiya sakarmin 'yata,tunda bashi ya haifarmin itaba da xai maidata baiwarsa daga haka ummah ta mike,....


Malam Auwalu shima mikewa yay yace maimuna harni kike fadawa haka,kinaso ki nunamin cewa ni Banda iko akan 'yata kenan,ban isa da 'yata ba kenan,to shikenan muxuba nidake mugani Amma wlh indai ni na haifi AMEENAH Baki isa ki kashe mata AURE ba,kodan banyi mamaki ba tunda xuwa akai har gida aka fada miki,tunda kinki ki fadamin, atunaninki bansan xuwa akai hargida aka fada miki karya da gsky ba,to shikenan xanyiwa tufkar hanci,...


Ummah ta juyo ko kadan batai Mamaki ba Dan malam yace yasan xuwa akai hargida aka fada mata ba,svd tariga da tasan baba asabe ce ta fada masa komai,ba kowa ba, ummah tace ainasan ka sani din shiyasa ma ban fada Makanba,tunda nasan babu Mai fada Maka sai wannan munafukar matar taka wacce Batasan cigaba na Dani da 'ya'yana, tafiso ta jimu kullum cikin tashin hankali, baba asabe Dake labe ta kasa jurewa ta shigo dakin ta rike qugu ,ta watsawa ummah Wani kallo tace fadi ki qara ni na fadawa malam , sbd kawai bakyasan zaman yartaki agidan mijinta,zaki dauki maganar wannan maqarya ciyar, matar muna fuka ,ko ke kadai ce me 'Ya'ya ni ba inada suva Amma kintavaji nazo muna dayan biyu nida malam akansu da rayuwar auransu Ina ruwana da rayuwar auransu tsakanin sune da mazajensu wannan, Amma ke sbd kulafucin 'Ya'ya Irin Baki kawai kidinga daukar duk abinda xa'a fada miki akan yarannan Kabiru,Ina mardiya ce sa'ar Ameenah Amma ko ita kin taba Jin nazo Ina dayan biyun nida malam
akanta.ko wacce mace ai tanada nata matsalan gidan mijin Amma kowa hkr yake....



Bakyason afada miki gsky kodan aidama baxaki wahalar daukar xuga ba indai akan auran Ameenah da Kabiru ne,sbd kedama ba San auran kike ba tunfarko ,bakuma qaunar Kabirun kikeba, aidole kice a Rava AURE,idan ke kina ganin ba komai bane aishi malam da yasan me yake da haka kawai sama ta ka BA Kabirun bane yaxo yace araba auran ba,ba Kuma Ameenah bace ba ,ba kowa ba,kawai yarinyar tana xamanta agidan mijinta lpy Amma kice wai araba auran,.....



Ummah rasa abin fada tai svd bakin cikin Irin yadda baba asabe take Shiga mata sabgar ta, ta tsakanin ta da mijinta da Kuma 'ya'yanta,gashi Saitayi yadda tai ta xuga malam,akan duk yadda xatai Dan ta shawo kan malam Dan yasan Irin wahalar da gana axabar da Kabiru yake yiwa Ameenah, Amma baba asabe saita ruguxa mata plan dinta, ummah batai wata wataba ta shako baba asabe Dake mata wannan murmushin da ita kadai tasan MA'Anarsa,ta shake mata wuya ta kaita bango ,ta shake mata wuya yadda ta tabbatar da numfashi ma saiya gagareta , baba asabe ta xaro ido waje ,gashi tai tai ta kwace wuyanta a hannun ummah kasawa tai, numfashi Dakyar take ja,kukanma kasawa tai haka ta xaro ido waje,kamar xasu zazzago qasa,malam Auwalu tuni yay kansu yace maimuna meye Hakan ki saketa ya fada Yana kokarin cire hannun ummah daga wuyan Baba asabe,abinka da Wanda aka gama kureshi ko gixau ummah bataiba,Dan tafi baba asabe Jiki da tsayi ita Baba asabe Irin mutanan nan ne tsantsamai,marasa jiki,sai xare ido take tana numfashi Dakyar, tana yiwa malam Auwalu inkiya da hannu akan ya ceceta..



Malam Auwalu yay yay ya kwaci baba asabe daga shakar da ummah ta mata kasawa yay,Dan ummah ba karamin fushi tai ba,yay kasa da murya cikin lallashi yace maimuna Dan Allah ki saketa karki kisan kai ki jawa kanki ,Kingafa da kyar take numfashi ummah cikin huci tace,ka barni na kashetan kota daina shiga sabgata agidannan idan Ina magana da kai ta daina xuwa ta xigaka akan rayuwar auran Ameenah,kabarni na kashe munafukar matar nan annamimiya, koxan huce daga abinda takemin,malam Auwalu yace saketa ta daina , ki saketa sai muyi magana, ummah tace saika mata worning anan tukunna xan saketa saita yadda zata daina Shiga sabgata agidannan,baba asabe da kamar ta mutu Dan azava Dan bakaramin shaka ummah tai mata ba,wlh ko numfashi Mai kyau ta kasa yi Batasan haka maimuna take da qarfi ba da baxata tava barin ta risketa haka ba,tai saurin gyada ma ummah kai,malam Auwalu yace asave ki daina shiga harkar maimuna a gidannan ,baba asabe tai saurin gyada kai hawaye na sauka a fuskarta ,Dan wlh ba karamin azava takeji ba,malam Auwalu yace kinji ai kingama tace ta daina,..



Ummah ta watsa mata Wani kallo sannan ta wancakalar da baba asabe Wacce tai saurin xuvewa aqasa tana sakin numfarfashi,ga hannuta rike da wuyanta, aituni ta fice daga dakin da Jan uwawu,=??,(hmm baba asabe kenan to idan halinkine gobema xaki qara idan Kuma ba halinki bane xaki daina,aidama shi Mai hkr Bai iya fushi ba),malam Auwalu dashima ya tsorata da lamarin ummah Dan Bai tava Ganin bacin rantaba Irin hakaba,ta kalleshi tace inajinka,yace maimuna banji dadin abinda kukayiba, ummah tace sbd na taba matar sova,sbd bakasan laifinta kana fa ganin yadda take xuwa take hadamin munfurci agunka fa karka dauka bansani ba nasan komai wlh tar nake kallanta daga kai har ita, malam Auwalu yace ko kadan ba haka bane maimuna,kinsan halin asave saiki ci maganin xama da ita ummah,tace wlh Bata isa ba ,idan tsoranta kakeji ni bana tsoranta,sbd haka ni abinda nakeso shine gobe idan Allah ya kaimu xanje na dauko Ameenah Dan wlh aurannan angamashi kenan,malam Auwalu yace Dan Allah maimuna karki raba AURE,kinsan ko ubangiji bayasan saki , ni Abinda nake so Dake shine ki bari goben sai muje mu gano Ameenah mu tabbatar da abinda aka fada din,ummah tace oh bakama yadda ba kenan,...



Malam Auwalu yace bawai yaddace banyi ba, Amma so nake Muji ta bakin ita Ameenah, ummah tace nidai gove xuwan da xanyi tahowa da 'yata xanyi,malam Auwalu yace haba maimuna yanxu baxan fada miki magana kijiba, ummah tace nidai ga Abinda nace dan wlh na gaji daga haka tabar dakin ,malam Auwalu ya dafe kansa ya rasa ya xanyi ya shawo kan maimuna ta fahimci abinda takesan aikatawa ba dai dai bane ba,.....




___________?&



Washe gari da safe wajen karfe ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????9:30am,ruky ce xaune a office kan kujerar ta tana latsa computer tana Wani aiki,ga takardu agefenta tana shigar da Wani report ne,Kiran DCP ne ya shigo wayarta, Saida ta kusan tsinkewa sannan ta dauka,tai sallama cikin daddadar muryarta wacce ke kashe DCP,aduk lokacin dayajita,daga Daya bangaren DCP ya lumshe idansa,duk da acikin damuwa yake Amma Jin muryarta, ta Dan kauda damuwar kadan,yace patan muntashi lpy, ruky tace lpy lau sir,yace ya aikin tace Alhamdulillah sir,yace inva damuwa kixo office Dina akwai maganar danakeso keso muyi babu Bata lokaci,ruky tace ok sir, daga haka ta kashe wayar,ta rufe laptop dinta, ta tattare takardun gefe,sannan ta mike ta fita daga office din,bayan ta shiga office din DCP da sallama abakinta,ya ansa mata Yana nuna mata wurin xama,bayan ta xauna ruky ta kalleshi, taga Yanayinsa kamar Yana cikin damuwa, karo na farko tace sir Allah yasa lpy,....



DCP Ya sauke numfashi ya gyara xamansa yace Rukayya,ta dago ta kalleshi da dararan idanuwanta jin ya ambaci full Name dinta Dan da wuya ya kirata da full name dinta saidai yace my,Hakan da yay tasan lallai akwai abinda yakeso ya fada mata, Mai muhimmanci, DCP yace jiya Alhaji sunusi yaxo nan bayan kintashi daga office, nan dai ya kwashe duk yadda sukai ya fada mata,ruky tai murmushi tace nasan dama xa'ayi haka,Dan daka taba lateef gara ka xagi uncle sunusi Dan shi xai iya daga ma kafa akandai ka taba lateef,tace sir karkaji komai ka barni dasu duk na isheshu,Kuma belin baxa'a badashiba,,.....



DCP yace ba wannan ne matsalan ba, matsalan shine CP ya Kirani yau da ASuba yace lallai anjima Alhaji sunusi xaixo Kuma dole asaki lateef,nayi nayi nai Masa bayani yaki saurarata,yace lallai bayan an sakeshin sai mun bashi hkrn wai ai sharri aka masa,can u imagine ace CP shine ke fadar wannan maganar,bayan mu mun tavvatar da lateef ne yay wannan aikin ,naso na fahimtar dashi Amma kwata kwata yaki saurarata, yace idanba so nake na rasa aikina ba,na Kuma sa rayuwata a garari to na bar case din,yace kema lallai lallai dole saikin aje wannan case din,....


Ruky da mamaki ya kasheta tace wai yanxu sir CP da kansa yake fadar wannan maganar na dauka idan yaji xancennan xaifi kowa dagewa akan case din Amma shine me fadar haka,ta girgixa kai tace sir wlh baxan taba barin wannan case dinba saidai idan ni xan rasa aikinnawa ,wlh saidai na rasa Amma tunda har ankama Mai laifi dumu dumu dole saiya karbi hukuncinnsa Koda ko Bai ansa dinba,CP yace Rukayya karkice haka,tace kayi hkr sir kaidai karka damu ka cire hannunka daga case din ko CP yaxo Dan Allah kace kaika hkr da case din,ni xan fada masa cewa baxan iya barin case dinba, nagode da dawainiya da kai min akan case din nan, Allah ya Saka da Alkhairi,bansan haka kasarnan ta sake lalacewaba sai Yanxu,dan Mai kudi yay laifi Amma a qaryata,aki Bada hadin kai a hukuntashi yadda akewa kowa ba,dole sai anyi xalinci, dole sai annuna cewa shi Dan masu kudu ne, DCP yace sorry ASP tace sir bani files din Dana kawo Maka, DCP yace why ,tace sir kabani Inaso ne ya dawo hannuna,babu musu DCP ya jawo drawer Dake kusa dashi ya dauki file din da ta kawo masa ranan Dan yasan ranta ya gama baci,....


Haka ya ajiye agabansa,babu musu ta karba,tace sir bari naje idan sunxo na tavvatar xasu kirani,sir Dan Allah ka kyaleni nai aikina ,yanxu case ya dawo hannuna,idan sunxo kace musu case din na karbi kayana kai ka cire hannunka aciki,ni xanji dasu ,tace banaso kasa kanka amatsala,daga haka ta mike , shima DCP mikewa yay yace please Rukayya kema dan Allah karki sa kanki a matsala,tai murmushi tace me kakeso nayi so kake na ajiye aikin, bayan na musu ALKawarin cewa in Sha Allah tunda har aka kama Wanda yay wannan zalincin in Sha Allah dole sai an hukuntashi kamar yadda dokar kasa ta tanadar, DCP yace, Rukayya Dan Allah ki bari Abu komai asannu, ruky tace karka damu na gode sir daga haka ta fice daga office din, tana share hawayen takaici, wai Dan abin kunya CP shine da wannan Rashin adalci,DCP ya kai xaune kan kujerarsa ya dafe kansa,yaji gabadaya tausayin Rukayya yakeji, bayajin xai bari ta shiga matsala Dan a yadda ya lura indai Alhaji sunusi ne,zai iya batar da kowa akan Dansa,Koda ko ita Rukayya ce datake matsayin 'ya awajensa Dan yadda yaga yake Nanata siyasar sa,yasan cewa baxai taba bari sunansa ya Baci ba,....



Yana wannan tunanin CP ya kirashi akan yaxo su Alhaji sunusi sunxo Kuma ya kira Rukayya,babu yadda DCP ya iya dole haka ya kira Rukayya, babu dadewa suka nufi office din CP,suka sameshi shida su Alhaji sunusi, Alhaji sunusi farko Bai Gane Rukayya ba ,Saida ya kura mata ido sosai bayan sun qaraso cikin office din,har sannan, kallanta yake da mamakin ita Kuma maiya kawota nan, ruky ta gaida CP sannan ta dago ta gaida su Alhaji sunusi batareda ta nuna akwai wata sanayya ko alaqa a tsakaninsuba, Alhaji sunusi ya kasa jurewa ya kalli CP yace wannan Kuma fa meya kawota nan ,DCP yace itace wacce case din ke hannuta,...


Alhaji sunusi cikin mamaki yace Rukayya,bangane itace wacce case din ke hannuta ba,CP yace kwarai kuwa yallabai itace, Alhaji sunusi yace ke Rukayya lateef mijin naki keke kokarin lakawa sharri,waishin ma ko kinsan shine kuwa ko yaya, Rukayya ta dago da kai tace uncle, lateef shine Wanda ya aikata laifin nan ,ba Wani ba,ba Kuma sharri nake masa ba,Kuma dole akamashi ayimasa hukunci daidai da abinda ya aikata, Alhaji sunusi yace wai kinmanta cewa auranku nan da kwana uku ne, Amma kike kokarin Yi masa sharrin da xaisa akaishi prison, Rukayya tace Nifa lateef ba mijinah bane, tunda ba'a daura AURAN ba,wlh uncle ko mijin nawane wlh tunda harshi ya aikata wlh dole ya fuskanci hukunci,..



Alhaji sunusi cikin mamaki yace ke Rukayya yanxu har idanki yakai kidinga fadamin magana haka kanki tsaye,ko baki daukeni matsayin kanin mahaifin kiba aikya daukeni matsayin uban mijin da zaki aura koh,kodan baxan Yi mamaki ba,kinyi hakane kawai Dan ki gujewa auran lateef da akesan yi miki ,bisaga Rashin yardarki dama ai basanshi kike ba, shine kawai ya dage,daga ke har uwarki har Yan uwanki basan auran kukeba, shiyasa kukaje Kuka lalumo 'yar da Wani can Banxa ya gama lalatawa,xakuyiwa lateef sharri da ita,Dan kawai ki gujewa auransa,to bari Kiji basai ankai ga nisa ba, yanxu yanxu xan fadawa lateef abinda kikeso ku sharran ta masa akan AURANKI daya dage akan saiyayi,gara yaji koya hkr,ya kalli CP yace aje a taho da lateef,....



Cp cikin rawar jiki yace da DCP yasa a taho da lateef, Ruky itadai ta xubawa CP ido kawai Wanda ya Bata mamaki matuka,yanxu shine xai rufe ido asaki lateef,bayan ya aikata laifi ,kamar bashine mutumin nan Mai xafi ba,Wanda baya wasa da aikinsa ba,Amma shine yau a gava gaba wajen ganin ansaki Mai laifi,kuru kuru, tana cikin wannan tunanin babu dadewa akaxo da lateef Wanda yay wujiga wujiga,sai xare ido yake,ganin Alhaji sunusi,ya Dan fada kadan bawai Rashin abinci ko Wani abun ba, a'a kawai Rashin sabone yasa shi fadawa, Yana xuwa,yay kan Alhaji sunusi Wanda ya rungume shi,yace Dady kana ganin yadda aka wulakanta tani,aka min sharri,wlh Dady duk saika dauresu duk sai kasa ankoresu daga aiki, Alhaji sunusi da kamar shima yay Kuka svd ganin yadda lateef ya fada,ya dago shi yace kwantar da hankalinka,ayau xandauki mataki , lateef ya dago Yana Hararra su DCP ,sai idansa ya sauka akan Ruky wacce ke tsaye kanta a qasa Amma Kuma duk da haka Saida ya ganeta,ya nunata da yatsa cikin makamin ganin ta ,duk da yasan a heardquater take aiki ,Amma Bai taba tunanin yasan xata San Yana nan ba,atunaninsa, itace ta fadawa dadynsa cewa yana nan,yace Rukayya kece ,sai Kuma ya Kalli Alhaji sunusi yace Dady ko ita ta fada Maka cewa ankawo ni nan,...



Alhaji sunusi cikin bacin Rai ya nunawa Lateef Ruky yace ta fadamin ko Kuma itace wacce tasa akama ka , sannan hakan Bai ishetaba Saida ta hada da yi Maka sharri, lateef yace haba Dady Rukayya cefa ,itace fa wacce xan aura ,Nanda kwana uku fa, Taya ZA'Ayi tamin sharri,Alhaji sunusi yay tsaki yace bari na fada Maka yadda akayi Dan nasan ba yadda xakayi ba,idan kaji me tai Maka aidole ka yarda,Nanda Alhaji sunusi fadawa lateef komai,ya qasara fada da cewa Dan haka ayau saika sake tabbatar da bata sanka,Bata qaunar ka,Kuma baxata tava,san kaba sbd haka daga yau saika rabu da ita kasamu yar mutunci ka aura,....




Lateef cikin kasa yarda da abinda Alhaji sunusi ya fada masa ya Tako yaxo gaban ruky , kamar xai kuka yace Rukayya da GSK ne abinda Dady ya fada , Rukayya ta dago ta Wani hade Rai tace Wani haka yake wani Kuma ba haka bane,tace lateef Kaine kaiwa yarinyar nan fyade,ka ansa laifin ka kawai domin kasan kaika aikata kawai so kake ka kubutar da kanka, lateef ya Kalli Ruky da mamaki yace ashedai abinda Dady ya fada gsky ne,tunda har kika fadi haka da bakinki,ruky harni xakiywa sharri,harni zaki sa akama a kulleni ,sbd kawai San xuciyarki ,wlh saina Baki mamaki, ruky tai murmushin takaici tace lateef atunaninka ni xan ni zan Maka sharri,abinda muka tabbatar da kai ka aikatashi ,Kuma kaima kasan ka aikata, sannan tace hmm lateef kaji tsoran Allah,idan mu bama kallan ka lokacin dakake aikatawa ubangiji shi Yana kallanka,Kuma xaka taddashi a inda yake jiranmu, lateef ya daka mata tsawa yace enough,ya dawo gabanta ya nuna ta da yatsansa yace wlh karki sa na sharara miki mari,Kuma kijira aurenah nida ke nan da 3 days wlh saikin Gane kuranki,zakisan ni kika sa aka kama aka kawoni wannan kaxamin wajen ,har nai tsawan wannan kwanakin, ya kalli Dady yace Dady mu tafi , Alhaji sunusi yay tsaki yace CP na tafi ka rabuta belin din,CP yace shikenan ranka ya Dade a sauka lpy, Rukayya tai tsaki tace abanxa ,Kuma xanjira kan xanga iKon naka ta takamar da kake idan har ya kai ,daga haka ta kalli CP da idanta Wanda suka fara kwalla tace sir me laifine fa taya xa'a sakeshi ,CP yace Kinga wannan abunda ya faru ya riga Daya wuce, Rukayya ta xubo da kwallar da ta sauka a kan kyakkyawar fuskarta , ta kalli Alhaji sunusi da lateef da suke kokarin barin office din tace wlh case dinnan bai wuce ba,yanxuma aka fara,sai Kuma tace hmm yanxu dai kunsha Amma kai lateef kajira wlh sai an kamaka Kuma saika ansa laifin da kake ikirarin baka aikata VA,alhalin kasan kaika aikata,daga haka tai ficewarta daga office din tana share hawayen da yaki tsaya mata,CP ya kira sunan ta Amma kota kalleshi, Alhaji sunusi yay murmushi yace CP kyaleta ai wannan abun na gidane tunda har yanxu Bata hanani tafiya da lateef ba,ka gako ai xancen Banxa take,daga haka suka fice daga office din shima DCP ya fita akabar CP da daurewar kai,......





*Masu San a tallata musu hajarsu xasu iya Yin magana ta wannan number Dake qasa*







07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*




*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA)=?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season one ep 3?? 2??



____________?&


Mamah ce xaune a falor akan kujera sai ruky Dake kwance akan kujerar da Mamah take xaune,kanta akan cinyar mamah tana chatting, Amma Kuma har lokacin akwai damuwar abinda Alhaji sunusi yay mata daxu a office tana daurewa ne kawai Dan kada mamah ta fahimci tana cikin damuwa, Amma Alhaji sunusi yayi matukar Bata mamaki,da abinda ya aikata dazu,Bata taba tunanin haka yake da San xuciyarsaba sai alokacin,uwa uba Kuma CP,wlh CP yayi matukar Bata kunya da Bata mamaki ,Bata tava dauka haka yake ba, chatting dinma kawai yi take,so take ta fadawa Hanan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login