Showing 243001 words to 246000 words out of 278032 words

Chapter 82 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1058

suka shiga motocinsu suna jiran afito da amarya su tafi da ita.



Wajen mintuna 20 aka fito da amarya da Wad'anda zasu mata rakiya suka fito da ita cikin lullub'i aka Bud'e motar da za'a Sakata ,bayan anshigar da ita sauran wad'anda zasu mata rakiya suma suka shiga motocin ,daga nan Kuma kowa ya shiga mota suka tafi anayimusu fatan Sauka lafiya....


A Kaduna kuwa a wannan lokacin gidan mamah cike yake da Bak'i na nesa Dana kusa 'yan uwa da abokan arzik'i,sai hada hada ake ana shiga ana fita,anty mufeeda na hango cikin shiga ta Alfarma bakinta ya kasa rufuwa saboda farin ciki,haka zalika Mamah itama tayi shiga cikin ta'addan less sai Walwali take kamar wata tauraruwa,gefe guda Kuma ana ta shirye shiryen isowar amarya da tawagarta....


Wajen k'arfe biyar ko dai dai amarya suka iso gidan aka wangale musu gate suka k'arasa shigowa,bayan sun shigo drivers d'in sukai parking a inda aka tanada dominyi ,manyan matane na hango suka fara fitowa cikin shiga ta Alfarma kafin naga an fito da amarya cikin lullub'i ,sai da kowa ya gama fitowa sannan suka shiga da amarya cikin falon gidan fuskarta har lokacin a rufe take wajen surikarta aka nufa da ita Dan zuwa gaida ta kafin a wuce da ita gidanta.


Gabad'aya duk suna falon aka k'arasa da ita har gaban mamah wacce take zaune kan D'aya daga cikin kujerun falon fuskarta da Murmushi tanayi musu sannu da zuwa,ana Basu wurin zama,suka zaz zauna kafin su gaggaisa suka Bada Amanar amarya , mamah ta karb'a hannu bibbiyu sunji Dad'in tarb'ar da aka musu,anty mufeeda tai musu jagora zuwa Wani b'angare na musamman inda anan ne aka aje musu abincin da aka tanadar musu Dan su huta kafin sukai amarya gidan mijinta tunda bakwana zasuyi ba duk a yau zasu tafi..


Bayan magrib aka fito da amarya za'a tafi kaita gidan mijinta Wanda ya Gina anan garin Kaduna kafin su wuce Lagos inda yake aiki nan da two weeks.aka fito da amarya bayan an K'ara kaita wurin mamah ta k'ara sa musu albarka a cikin auransu suka shiga motocin da already suka iso Dan d'aukar amarya, bayan sun shiga aka tafi kai amarya......



A b'angaren Hanan kuwa alokacin da za'a tafi kai amaryar ya Tahir, alokacin ita Kuma ake fito da ita daga gidansu za'a kawota gidan Mamah Dan ta gaidata ,sai kuka take gwanin ban tausayi.ruky tana gida tunda ta dawo gida K'ara yin wanka bayan angwaye sun baro gidansu hanan to Bata koma ba ta kwanta Tasha baccin ta sai gab da la'asar ta tashi,to shine Kuma bata koma ba tace idan Ankowo Hanan gidan nasu ta bita tai mata rakiya har zuwa gidan mijin nata ....


Bayan sun shigo gidan aka fita da amarya daga cikin motar da take ciki akai cikin gidan da ita ,suna shiga falon gidan mata suka d'au guda take falon ya Kaure da hayaniya ana tai musu sannu da zuwa,
Suna ansawa cikin mutunci,suka zaunar da Hanan gaban mamah,kafin suma suka zauna ana gaisawa,fuskar mamah ta kasa b'oye farin cikin ta ,ta sawa Hanan albarka acikin auransu kafin tai musu addu'ar zaman lafiya na har abada ,bayan ta gama suka mik'ar da ita aka fito da ita Dan tafiya da ita gidan mijinta ,sai alokacin ruky ta sauko downstairs daga d'akin ta cikin shiga ta Alfarma itama tabi bayansu ta shiga gaban motar da amarya take ciki aka ja suka tafi ....


Gida ne Wanda ya ansa sunansa gida Dan upstairs ne ,komai na gidan yayi dai da tsarin gidan amarya ,aka shigar da amarya ciki har zuwa bedroom d'inta aka zaunar da ita a Bakinta gadon kafin su K'ara Yi mata nasiha bayan sun mata sallama suka fito Dan tafiya ,Bai war Allah Hanan sai kuka take kamar ranta zai fita , Amma babu yadda ta iya haka suka tafi suka barta daga ita sai sauran k'awayen ta.ruky ce ta zauna a kusa da ita tana Bata Baki tare da sauran k'awayen,Babu Dede'wa ango ya shigo shida zugar abokansa, suka sayi Baki kafin k'awayen ma su fara haramar tafiya ,nan fa Hanan tace ai Batasan zancen ba Babu inda ruky zata ,suna cikin wannan drama AA Arab ya k'ira wayar ruky akan ta fito Yana waje Yana jiranta,ruky ta kalli Hanan wacce ta k'an k'ameta tak'i sakinta kamar wacce zata b'allata tai k'asa da murya tace,.


"Sis!, kiyi hak'uri Kinga fa ga ya hanaf d'in fa yazo,kuma zan dawo gobe kinji?",ta fada cikin rawar murya da sigar lallashi Dan wallahi itama daurewa kawai take Dan ji take kamar ta saki Kukan itama.


Cikin Kuka Hanan tace .


"Dan Allah sis karki tafi ki barni wallahi tsoro nakeji",ta fad'a tana sheshshek'ar kuka.


Ruky ta rasa ya zatai mata Kawai sai itama ta fashe da kukan, haka suka rungumi juna suna kuka kusan mintuna 10 Babu Mai rarrashin Wani acikin su,dama k'awayen da sukaga haka tuni suka fito suka tafi,daga falon ya hanaf ya juyo kukan nasu ,yasa ya shigo d'akin ya gansu rungume da juna suna kuka kamar wasu k'ana nun yara,shi dariya ma abin ya shi kawai ya tsaya yana kallan su kafin ya k'arasa wurinsu yana kallan su yace.


"Kukan me kuke haka ne?", ya fad'a da yanayin muryarsa.basu kula shiba sannan Basu daina kukan ba bare Kuma su saki juna Hakan yasa _yasa hannunsa ya b'anb'aro Hanan Daga jikin ruky wacce fuskarta tai jagab da hawaye sai kuka take haka ma ruky kafin ya Kalli Ruky murya ba wasa yace.


"Wuce ki tafi", ya fad'a Yana kallan ta .


Batai musu ba ta Mik'e Kuma har lokacin Bata daina kukan ba,tai hanyar k'ofar fita daga d'akin,Hanan ta yunk'ura zata kamota ya hanaf ya rik'eta Yana jawota jikinsa tare da lallashin ta Daga nan sukai kan gado yana cigaba da rarrashinta tana kuka har lokacin....


Tunda ta fito idansa yake kanta Yana zaune acikin motar yana kallan ta harta k'araso ya Bud'e mata ta shiga kafin ta rufo k'ofar tana rufe fuskarta da tafukan Hannunta tana kuka marar sauti har lokacin ,ko ba'a fad'a ba Yasan kuka tai koma yace take Yi ,tana sheshshek'ar kuka a hankali ya kalleta yay k'asa da murya yace.


"Fiancee!", tai Shuru batai magana ba.saima sautin Kukan ta data K'ara dama Neman Wanda zatayiwa takeyi.


Ya K'ara K'iran sunan ta ,nan ma dai no respond, ganin tak'i yin magana yasa kawai ya ta-da motar suka fara tafiya a hankali sai da sukai nisa sannan ya gangara gefen titi ganin yadda take ta rusa kuka kamar wacce akyiwa mutuwa ,Batasan wannan kukan da take masaba ba k'aramin rud'ar dashi takeyi ba,ya juya Yana kallan ta da kyau wacce har lokacin kuka take Yace cikin k'asa da murya.


"Why are crying uhmm?",ya fad'a cikin damuwa.


"Cikin Kuka tace.

" Hanan..."


Ya Sauke numfashi kafin yace.

"Meya sameta?",

Cikin Kuka Tace.

"kuka fa take na taho na barta ita kad'ai",ta fad'a tsakaninta da Allah tana Kuma K'ara sautin Kukan nata.


AA Arab Ya saki Baki Yana kallanta da mamakin abinda ta fad'a wai ita kad'ai to mijin Hanan d'in data Bari agidan fa ko shi ba mutum bane , kawai saiya Sauke numfashi Yana kallan ta dakyau yace cikin nutsuwa.


"Shi Kuma mijinta ta kika baro agidan fa ko shi ba mutum bane?",ya fad'a Yana kallan ta, sai kuma ya cigaba Yace ."To idan Baki taho ba me zaki mata? itafa yanzu tana gidan Mijinta ne Kinga ko ai Bata da wada matsala yanzu,kuma Sannan kukan da take bawai na wani abun bane kawai normal kukane Wanda duk wacce aka kaita gidan mijin takeyinsa,kuma kema Zakiyi shi Nanda two weeks",ya fad'a Yana Wani kallan ta.


Tai shiru batai magana ba Jin abinda ya fad'a kafin ta d'ago tana kallan sa tace cikin sanyin murya.


"Amma Dee dan baka ga kukan da take bane shiyasa,ni wallahi tausayi ta bani", ta fad'a cikin damuwa.


Yay murmushi ya k'ara kasa da murya tare da matsowa kusa da ita kad'an Yana kallan ta da kyau yace.


"Oh" tausayi ma ta Baki koh?,hmm zakiga tausayi yarinya ",ya fad'a Yana Wani taune lips d'insa ,.

Ruky tai shiru tana sauraransa ganin yadda yake Wani lumshe mata ido ta kau kanta gefe kafin tace tana turo Baki gaba.

"nidai ka daina min wannan kallan banaso",ta fad'a a shagwab'e.


Ya K'ara matsowa kusa da ita kafin yasa hannu ya juyo da fuskar ta suna fuskarta juna yay k'asa da murya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? yace.


"Why?,bakyason Ina kallan my halal ne",ya fad'a Yana rarraba ido akanta ,itama k'ura masa idon tai tana kallan sa kafin ta lumshe idanta Dan baza ta iya jurar ganin k'wayar idonsa ba saboda abubuwan da take hangowa acikin su tace a shagwab'e.


"Kawai ni kunya nake ji",ta fad'a tana tura masa Baki gaba,ya k'urawa Dan k'aramin bakin nata Ido dayay maganar Kuma har lokacin idonta Yana lumshe ya kai bakinsa dai dai nata kamar zai sumbata take tai saurin Bud'e ido jin saukar numfashinsa a saman fuskarta tana kallan sa cikin fad'uwar gaba ta k'wace fuskarta daga hannunsa tana sunkuyar da kanta k'asa.


Ya k'ura mata ido a kasalance kafin yace cikin shak'akk'iyar muryarsa.


"Yarinya kema ki shirya nan da two weeks iyanzu kina nan ke kad'ai agidana dagani sai ke" ya fad'a Yana Kallan ta, Bata yarda ta kalleshi ba tace.


"Please mu tafi Dan Allah banaso ",ta fad'a kamar zatai Kuka Dan wallahi da Gaske Batasan Irin wannan maganganun da yake mata gabad'aya tsorata ta yake taji bama ta San AURAN,yay murmushi ya ta-da motar suka tafi ya dinga janta da hira lta dai tai shiru tana sauraran sa ......






07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y






*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*




*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*




*____(MRS SARAKIES =؋?)____=?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 9?? 6??



___________?&


Washe gari bayan Azhar Ruky ta koma gidan Hanan sakamakon K'iran data dinga doka mata akan tazo ta wai ai tace zata zo meyasa Bata zoba waye waye haka nan dai babu yadda ruky ta iya ta shirya ta tafi ,nan ta wunar mata har kusan magrib suna tare dawowar ya hanaf ne yasa ta fara shirin tafiya,Nan fa Hanan tai wuri wuri da ido kamar zatai kuka bataso ruky ta tafi,ita ko ruky ta Dunga mata dariya ganin yadda Hanan take da fuska kamar wata yarinya k'arama.babu Yadda ta iya dai tabarta ta tafi suna kewar juna....




*Bayan hud'u*



Daya kasance saura kwanaki goma bikin ruky,aKuma yau ya kasance za'a kawo lefan ruky daga gidansu AA Arab,dayake bayan da akai bikinsu ya Tahir anty mufeeda ta koma can Abuja saboda yanayin aikinta, to sai jiya tazo Dan karb'ar lefan da Kuma kayan gyaran ruky da tazo mata dashi ,Dan ma wadda zatai mata gyaran na kwana Tara ne zata zo gobe a fara Dan takanas daga kano ma aka d'auko Mai gyaran mai suna antyn Sudan Dan indai gyarane kikeso na kece raini sa Mai gida sun Batu to ki nemi antyn Sudan shiyasa tazo da wuri Dan ai komai agabanta Dan tafiso a gyara k'anwar tata Yadda ya kamata daga nan Kuma zata zauna har sai bayan anyi biki sannan zata koma, shirye shiryen abinda zasu tarb'i Bak'in kawai suke,anyi snacks da abinci kala kala anyi raping d'insu cikin poel paper komai sunyi shi a tsare yadda ya kamata,..


Wajen k'arfe uku da Rabi Bak'in suka iso,bayan anbud'e musu gate drivers d'in sukai parking a compound d'in gidan, kafin naga wasu hamshak'an mata sun fara fitowa daga cikin motocin da suka zo acikin su, drivers d'in sukaiwa ma'aikatan gidan magana akan su tayasu su fito da akwatunan daga cikin motar, basuyi musu ba suka k'araso har bakin motar suka fara tayasu fitowa da boxers d'in Daga cikin motar Wanda suka Sha decorations na flowers suna shiga dasu cikin k'aton falon gidan nasu ,Saida suka gama shigarwa tas kafin naga matan sunyi gaba sun shiga falon bakunansu d'auke da sallama.....


Masu tarb'ar tasu Suka ansa musu suna musu sannu da zuwa tare da Basu wurin zama,Hajiya maryam ce a folon sai wasu daga cikin K'awayen mamah Wanda suka zo karb'ar kayan da wasu daga cikin 'yan uwansu sai su anty mufeeda da Baba hasiya,duk suka ansa musu tare da Yi musu barka da zuwa,suka ansa da fara'arsu suna samun waje suka zauna...


Kafin a shiga kawo musu ruwa da lemuka ana ajiye musu a gabansu suna godiya, Baba hasiya dai ta rik'e baki tana kallan wannan tsadaddun akwatunan set ukune Dan haka ya kama 32 pecies kenan kuma ko Wani set different color ne masu bala'in kyau da tsada ,su kansu k'awayen mamah abinda suke tunani da mamaki kenan aransu ganin wannan ubansun kayan da aka kawowa ruky wasu kuma suna tunanin ai idan aka kawo yafi hakama baza suyi mamaki ba saboda ruky takai akawo mata fin hakama adai yadda take da kyan nan ga sura sai dai muce Masha Allah.....



Aka fara bubbud'e akwatunan ana kallan kayan ana Gud'a ana Kuma addu'a kafin a rufe,anata Yaba kayan bayan sun bada kudi dubu D'ari b'iyar kud'in d'inkin Basu Dad'e ba Sukai haramar tafiya,aka Rakasu da kayan da akai musu parkeging d'insu aka Rakasu dashi har Bakin motarsu kafin suyi godiya sosai suka shiga motocin suka bar gidan suna Yaba karamcin da aka musu.....



Bayan tafiyarsu Baba hasiya data kasa hakuri tana kallan anty mufeeda k'asa k'asa ta rik'e baki kafin tace.


"Mufeeda kiga wannan uban kayan da aka kawowa uwata? lallai wannan yaro ba k'aramin k'ok'ari yayi ba",ta fad'a cikin mamaki.


Anty mufeeda tai murmushi tana kallan ta kafin tace.


"Gaskiya kan baba babu laifi sunyi k'ok'ari sosai,baba hasiya dai ta kasa b'oye mamakinta ganin wannan uban dukiyar da aka kashe wajen siyan wannan kaya, suna wannan zancen Mamah tai K'iran anty mufeeda ,ta ansa tana K'arasawa wajenta....


Ana wannan shagalin a gidansu ruky, itako tana can gidan Hanan Suna ta hira,Dan k'in zama tai agidan nasu .Hanan ta kalleta bayan sun gama cin wainar fulawar da suka soya tana kallan ta da tsokana tace .


"Amaryar sir",ta fad'a tana dariya.


Ruky ta Wani harareta kafin tace .


"Ke wallahi har yanzu yarinya ce,kin girma Amma bakisan kin girma ba ",ta fad'a tana hararar ta.


Hanan ta zaro ido waje kafin tace .

"Lallai yarinyar nan har yanzu Baki da kunya,karki manta fa nifa yanzu yayarkice ba abokiyar wasan kiba",ta fad'a tana Wani hura hanci.


Ruky tai murmushi kafin tace .


"Wallahi idan kikai wannan maganar dariya kike bani Hanan,ke yanzu ko kunyar fad'ar wannan maganar ma bakyayi ba",ta fad'a tana hararar ta.


Hanan ta zuba mata ido cikin mamaki ta girgiza kai kafin tace .

"ba laifinki bane laifi nane da har na tsaya Ina wasa da ke",ta fad'a tana tsuke fuska ita Irin ga matar yayan nan...


Ruky ta rik'e baki tace.

"Dan Allah daga yau karki K'ara wasan Dani uwar 'yan San girma",

Hanan tai dariya tace.

"Ya bazan so girma ba kuwa tunda ubangiji ya bani",ta fad'a tana Wani Bud'e ido.

Ruky tai shiru batace komai ba,dan ganin Hanan baza ta tab'a sauyawa ba.


Sai taga kuma ta koma serious taji tana cewa.


"Ke ya batun kaiwa d'inkin nan kuwa?".ta fad'a tana kallan Ruky .


Ruky ta rausayar da kai tana kallon ta kafin tace .


"Kayan ma suna ajiye a gida ban kaiba",ta fad'a tana ya Mutsa fuska.


Hanan ta Bud'e ido cikin mamaki kafin tace.


"Meyasa Baki kaiba?",ta fad'a tana kallan Ruky.

Ruky tace.

"Yace ko ankawo ma Basu zan Saba akwai kayan da Yay mana order ina tunanin ma a week d'in nan za'a kawo su",ta fad'a cikin sanyin murya.


Hanan ta rik'e baki da mamaki kafin ta sauke numfashi tace.


"Gaskiya ne amaryar sir, wallahi kina hutawarki ,kayan ma order za'a muku saboda karki wahala da yawan dinki", ta fad'a tana murmushi.


Ruky ta harareta kafin tace.


"Uhmmm"Amma Batai magana ba.


Hanan tace kefa matar nan Kina zuba capaciya a k'asar nan, lallai sir ba k'aramin ji dake yakeba.ta fad'a tana murmushi


Ruky ta mik'e ta d'auki plate d'in wainar da suka ci tai hanyar kitchen tana cewa "koba capacity ba,ai capacity saiku keda yayana ina jinki fa d'azu yadda kike tai masa Wani shagwab'a shikuma sai biye miki yake ko kunyata bakwaji ",ta fad'a tana k'ok'arin shiga kitchen d'in.


Hanan ta d'aga murya tace.

"To karnayi shagwab'a saina zauna wata tazo ta k'wace min shi na shiga uku",ta fad'a tana d'aga murya,ita dai ruky murmushin kawai take tana yiwa Allah godiya Daya had'a wannan soyayyar tsakanin yayan ta da Kuma aminiyarta Dan wallahi abinda ta gani d'azu kafin ya hanaf ya fita yayi matuk'ar B'ata mamaki da kuma burgeta....



__________?&

*ZARI'A*


Ameenah dai jiya ta gama takabarta.yau da yamma suna zaune a tsakar gidan su wajen k'arfe biyar da Rabi na yamma tana kallan yadda 'ya'yan su lawisa suke ta fad'a akan wata guntuwar shinkafa da k'aramar yarinyar mardiya taci rage Saboda ta k'oshi to shine fa suke fad'a akai wannan Yana cewa shi ta bawa wannan ma haka ,baba asabe tana tai musu magana Amma sunk'i ji sai Yi suke saboda yaran sun Raina ta Kamar yadda iyayen Suma suka Raina ta,Dan Yanzu hakama a kwance take akan barandar k'ofar falonta Bata da lafiya d'azu ma suka dawo daga asibiti jinin tane ya sake hawa,Kuma ba komai ne yasa yake yawan hawan ba illah wannan hayaniyar yarance da Kuma Damuwa data sa a ranta yasa jinin nata yake yawan hawa ga talauci Daya Sako ta agaba Dan ko sisi yanzu Bata maganin ta ga malam Auwalu dama ba kud'i yake Basu ba kowa NEMA yake da kansa shiyasa gabad'aya damuwar tai mata yawa Dan bata Saba zama Babu kud'i ba ,yaro ne yayi sallama a tsakar gidan kafin yace .


"wai ana sallama da Mai gidan",ya fad'a Yana jiran ansarsu ,gabadaya suka juya suna kallan sa jin abinda ya fad'a.


malam Auwalu da tun d'azu ya shigo gidan bai fita ba ya lek'o daga cikin d'akinsa Jin ana sallama dashi ya cewa yaron yaje yace Yana zuwa, yaron ya juya yaje ya fad'a,babu dad'ewa malam Auwalu ya fito ya nufi hanyar fita daga gidan Dan zuwa ganin Mai sallamar gabad'aya suka bishi da kallo...


Wajen mintuna 20 sai gashi ya dawo gidan fuskarsa a Washe ga Yara biye dashi sai shigo da kayan abinci suke ana jibgewa a k'ofar d'akin ummah, gabad'aya sai kallo ya koma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login