Showing 171001 words to 174000 words out of 278032 words

Chapter 58 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1043

AA Arab da takeyi kamar ta Dade da saninsa, sai Kuma itama ta kalli AA Arab ta ce "thank you sir" asaman labbanta AA Arab Bai ansa mata ba illah mikewa tsaye da yay ya Kalli Hanan ya ce "kicewa mamah na tafi Hanan ta Mike ta shiga dakin mamah Dake qasa ta sanar da ita ,mamah ta fito ita da anty mufeeda.bayan ta qaraso falon mamah ta ce "har zaka tafi Ahmad? AA Arab ya ce"eh mamah"mamah ta ce"to mungode sosai ka kaida mamanka mungode sosai "Yana shafa kansa ya ce "in Sha Allah"moha ya shigo falon da gudu Dan daga dakin su ya hanaf yake Yana xuwa ya fada kan AA Arab ya rungume shi Yana murmushi,Yana cewa "uncle " AA Arab ya rike shi Yana murmushi ya ce "my friend" Hanan tai masa Allah ya kiyaye,ya ansa mata ,itadai ruky tsayawa tai tana kallan iKon Allah awurin nan ,AA Arab da moha kamar dama sun San juna, mimie itama xuwa tai kusa dashi tana masa murmushi ya shafa kanta, ganin mamah na kallanta yasa ta kalli AA Arab ta ce "mungode" ya ansa mata Yana fita daga falon da moha Wanda ya rike hannun sa ga mimie agefensa ,a compound ya tarar dasu ya Tahir suka Rakashi har gaban motar sa ya dauko wa su moha da mimie ledar chocolate ya Basu moha ya karba Yana tsalle Yana cewa "thank u uncle "sannan ya daga masa hannu alamar bye bye ,ya Tahir yace harda wahala haka officer? AA Arab yay murmushi ya ce "babu wata wahala"ya shafa kan moha ya ce"bye bye moha"moha shima ya daga masa hannu ya ce "bye bye uncle" sudai su ya Tahir da ya hanaf murmushi kawai suke suka daga masa hannu alamar Allah ya kiyaye daga haka driver yaje suka bar kofar gidan......





07066608376_______
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*



*___(MRS SARAKIES =؋?)=?1?___*



*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 7?? 0??



___________?&


Washe gari da safe su AA Arab gabadaya sunje gidajen su Alhaji sunusi da babajo Ali ciki kuwa harda gidan hutawarsa Dake can bayan gari inda suke shake ayarsu da batan Banxa da Kuma yaran da ake kawo musu wato 'yan shilar da ake kawo musu suyi amfani dasu.A gidan Alhaji sunusi abinda suka Gani Saida ya girgixa su sbd abun Babu kyan Gani yayi Muni da yawa sun shiga har Inda yake jefa yaran idan ya gama amfani dasu,ya jefa gawar cikin Rami,sun ga haka ne ta dalilin binciken da suka yi.abun babu kyan Gani ko kad'an, gawar wakin yaran duk sunyi tsutsa ,wasu Kuma sun bushe sbd akwai abinda suke Saka musu Dan kada suyi wari wato chemical,ga abubuwan tsafi agidan kala_kala.haka ma a gidan babajo Ali the same thing abinda suka tarar agidan Alhaji sunusi shima haka suka tarar agidan nasa,sun dauki report din komai da suke bukata sunyi dauke dauken hotonan Abu buwan da duk suka Gani.sunje duk Wani gida da yake malkakin nasu Alhaji sunusi sun duba ko Ina wasu gidajan nasu Wanda basa amfani dasu mutanan gari sun samu nasarar kona wasu daga ciki kafin xuwan jami'an tsaron, aranar ma Da kyar jami'an tsaron Suka hanasu sbd yadda suke kokawar sai sun K'ona .....



Bayan sun gama da gida Jan, a kowanni gida sun Saka jami'an tsaron just for security,daga nan Kuma suka nufi gidajen da suke xaune aciki da matan su,sun shiga sun sa su tattaro musu duk wata Kadara da suka tanada,motocinsu sun tattara su agidan sun rufe, iya gidan da suke ciki ne ya rage shima Yana karkashin kulawar jami'an tsaron sai anyi xaman kotu idan aka yanke hukuncin za'a San yadda xa'ayi.sannan sukace su kasance cikin shiri ZA'A iya nemansa a Koda yaushe.a lokacin da sukaje gidan Alhaji sunusi, Hajiya SA'A tamkar xatayi hauka haka tai , shikenan nanfa ta faru ta qare wai anyiwa Mai Dami Daya sata,ta tabbata kenan zancen duniya ya tabbata ankama Alhaji sunusi sannan ga lateef Shima Wanda zata kalla taji dadi shima Babu shi yanxu sai ita kadai,haka ta dinga kuka kamar ranta zai fita, danma Allah ya taimaketa yayar ta Samira tana nan tare da ita,ita take tausar ta take Bata Baki da d'ebe mata kewa dama baxa wara ce mijinta ya rasu.yanzunma bayan tafiyar su AA Arab Samira ta dubi hajiya SA'A ganin yadda take ta kuka tayi lallashin harta kyaleta,hajiya SA'A ta ce "Samira bakisan me nake ji bane kina ganin Basu barmin komai ba duk sun kwace komai gashi Babu Alhaji Babu lateef ya baxan Damu ba " sai ta fashe da Kuka samira ta ce " nasan xaki damu Amma Dan Allah SA'A kiyi hkr kisa Allah a ranki in Sha Allah Alhaji sunusi zai fito shida lateef" Hajiya SA'A ta girgixa kai tana kuka ta ce"anty Samira na shiga uku , shikenan bani da kowa" Samira ta rufe mata Baki tana girgixa kai kafin ta ce " kidaina fadin haka SA'A" Hajiya SA'A ta rufe fuskarta da tafukan Hannun ta tadinga rusa kuka kamar ranta xai fita......



Su AA Arab sun tattaro duk wata Kadara dasu Alhaji sunusi suka Tara kama daga kan gidajensu ,kamfa nunukan da suke dasu da Kuma plazas dinsu Dan yin bincike akai.sbd bincike suka dauka bana wasa ba,in kuka ga yadda Alhaji sunusi da babajo Ali Suka koma saiku tausaya musu sbd yadda suka fita hayyacinsu a iya wannan kwanakin da sukayi Babu wannan takamar da nuna isa da sukeyiwa al'umma uwa uba babu shi kansa mulkin da suke taqama dashi suke amfani da power dinsu suke zalintar al'umma dashi, lateef Shima kansa ya rame yayi duhu babu wannan kwalisar da fafar da yakeyi da Jiji da kai duk babu, Dan baisan ma ankama Alhaji sunusi ba ko kad'an har yau,tun Yana Saka ran Alhaji sunusi xai xo yay belin dinsa harya yau gashi babu wata hanya dazai samu Akira masa Alhaji sunusi, ballan tana yasaka ran xai fita, yayi hakurin yayi hakurin harya gaji tun Yana daurewa hardai ya gaji ya fara kuka wujiga wujiga abinda Bai Saba ba,gashi har Wata 'yar rama da jinya da yay sbd sauran da yake cizansa awurin Dan wannan d'akin da aka kawo shi yasha ban ban da Wanda aka kawo shi wancan lokacin......



Kamar yadda Ruky ta fada tun a jiya kafin Hanan ta tafi "sunk'ira barrister shamsu Wanda bama ya garin Yana patacort yaje wani aiki.bayan picking call din suka gaisa da Hanan ta sanar masa sakon da ruky ta Bada na suna San report din dake wajensa sannan AA Arab yana San ganinsa baiyi musu ba ya ce "dama Yana hanya idan anjima zai shigo garin idan ya dawo kuma in Sha Allah zai kirasu sai su karba ko Kuma ya kawo musu" sukace ba damuwa ya hadu da AA Arab din kawai.ya ansa musu da in Sha Allah,san nan ya
Ce Hanan ta bawa ruky wayar yay mata jajan abinda ya sameta ,bayan sun gaisa yayi mata Jaje ruky tai masa godiya daga nan sukai sallama. akuma lokacin Hanan ta kira AA Arab ta fada masa yadda sukai da barrister shamsu,AA Arab ya ce "Babu damuwa sai ya kirashin" daga nan sukai sallama.....



Washe gari Kuma da daddare bayan AA Arab ya tashi daga aiki sun Hadu da barrister shamsu agidan Wani cin abinci ,bayan waitress din sun kawo musu drinks da ruwa,AA Arab ya karbi takardun Yana dubawa, bayan Wani lokaci ya dago ya dubi barrister shamsu ya ce "naga komai barrister Kuma Kuma in Sha Allah zamu Dora shari'a ne daga inda kuka tsaya Kaima zaka kasance D'aya daga cikin barrister's dinmu" barrister shamsu yay murmushi ya ce "nagode sosai yallabai" AA Arab ya jinjina masa kai ya ce "mune da godiya barrister" barrister shamsu ya ce "yallabai sai dai akwai Wani record da sauran report din dake wayar ASP Rukayya da bansamu na tura awayata ba Wanda zamu nunawa kotu aranar da xa'ayi xaman qarshe to Kuma sai wannan abun ya sameta,AA Arab ya jinjina kai kafin ya ce "wannan ba matsala bane barrister wayarta tana guna za'a San yadda xa'ayi" barrister shamsu ya ce " to shikenan Babu damuwa" sun Dade suna tattaunawa kafin daga bisani suyi sallama kowa ya shiga motarsa ya tafi inda zashi...


____________?&


Gabadaya ruky ta sakaran AA Arab zai kawo mata wayarta,Dan tunda taji Hanan ta ce "wayarta tana wajen AA Arab,tayi tunanin zai kawo mata a jiyan dayaxo Amma shine shiru har lokacin Bai kawo mata ba ,ta tura Baki gaba axuciyarta ta ce "ko me zaimin da waya da zai rike har yanxu Bai kawo min ba oho .yau Kuma ya Tahir ya koma wajen aikinsa ,anty mufeeda Kuma sai gobe zata tafi idan anfara xaman kotu xata dawo.the same day da yamma wajen karfe 4:30 ruky tana xaune afalo da Al'qur'ani a hannun ta tana karantawa tunda tai sallah take xaune awajen tajiyo ihun moha a compound din gidan yana Kiran uncle da gwarancin muryarsa,tai shiru a inda take xaune Bata motsa ba sbd tasan da ya hanaf yake tunda tun dazu Yana can a part dinsu ,Saida taga ya hanaf ya shigo falon ta d'ago kai ta kalleshi taga kallan ta yake zatai magana taji ya ce "Ahmad ne yaxo Yana San ganinki zai iya shigowa? ya fada Yana kallan ta ,ruky tai tsai alamar tunani waye Kuma Ahmad Dan ita harga Allah Batasan Wani Ahmad ba,ta ce"ya hanaf waye Ahmad? Ya hanaf ya Harareta ya ce "bansani ba , idan yaxo Kya ganshi" daga haka ya fita daga falon, babu dadewa ta fara maraba da dadda d'an turaransa Wanda ya fara mata iso tun kafin Mai shigowar ya shigo Hakan yasa ta xubawa kofar falon ido tana kallan waye Mai shigowar, idon da suka hada dashi ne yasa ta tai saurin janyewa nata tana mai ansa sallamar da yay mata,shima idan nasa ya janye daga kallan ta ya qarasa shigowa falon tareda da moha ya zauna kan Daya daga cikin kujerun falon, hannun sa sarke Dana moha sai gwarancin sa yake masa,cikin sanyin murya ta ce "good evening sir" batareda ta kalleshi ba,AA Arab ya ansa mata shima batareda da ya kalleta ba,ta mike ta shiga kitchen ta dawo da tray ahannun ta wanda ta Dora ruwa da lemo akai ta kawo har gaban sa ta duka ta ajiye masa, sannan ta koma kan kujerar da take xaune ta sunkuyar da kai tana wasa da gefen hijab dinta, tana Jin yadda suke magana da moha kamar Wani babba yana tambayar sa anty mufeeda da mamah,moha Yana bashi ansa da muryarsa,AA Arab ya zaro chocolate a aljihun sa ya bawa moha, ai sai moha ya hau tsallen murna Yana cewa da gwarancin sa "thank u uncle" shidai AA Arab murmushi kawai yake masa Yana kallan sa, moha ya fita daga falon da gudu xuwa part din su ya hanaf, itadai ruky mamakin wannan Abu take tsakanin moha da AA Arab Dan sai kallansu take Bata ko kiftawa,Bayan fitar moha wurin ya DAU shiru na Wani lokaci Babu me magana awurin shi AA Arab Yana latsa wayarsa ne Yana tura Wani Sak'o ita Kuma Ruky tana sauraran sa taji me zai ce, can sai ga baba hasiya ta fito daga dakinta ganin AA Arab yasa tai saurin qarasowa falon tana murmushi ta ce "A'a Babana Kaine kazo? sannu da xuwa" ta fada tana Dan rusinawa shima AA Arab murmushi yay ya gaida baba hasiya ta ansa tana tambayar sa mutanan gida,ya ce "lpy lau suke" baba hasiya ta ce "to agaida su" yace in Sha Allah zasuji " sai ta kalli ruky ta ce "uwata Hajiya koh tasan yaxo? Ruky ta girgixa mata kai alamar a'a, baba hasiya ta ce " meyasa Baki fad'a mata ba uwata? Ruky ta ce "xan fada matan Kuma sai kika fito " AA Arab ya Dan kalleta Jin abinda ta fada sai kuma ya dauke kansa, baba hasiya tace "bari naje na fada mata daga haka ta haura sama xuwa dakin mamah,bayan tai knocking kofar mamah tana ciki ta Bata ixnin Shiga,bayan ta shiga ta sanar da ita AA Arab ya xo, mamah ta ce" to yaushe yaxo hasiya? bari naxo daga haka ta mike baba hasiya Kuma ta fito daga dakin ta sauko qasa ta shige kitchen dama can xata.....


Bayan mamah ta sauko qasa da sallama a Bakinta suka ansa mata tace " Ahmad yaushe kaxo? bansani ba" ta fada tana xama kan kujera ,AA Arab ya zamo daga kan kujerar cikin girmamawa ya gaida mamah, mamah ta ansa da murmushi afuskata ta tambayeshi mutanan gida da kuma aiki , ya ansa mata da lpy lau suke , mamah ta ce " to Masha Allah,ya ce "dama nazo wajen Rukayya ne xan tambayeta Abu game da case din yarinyar nan ne" mamah tai murmushi ta ce "Babu komai ai Ahmad , Allah ya taimaka ,AA Arab ya ansa da Ameen,mamah ta ce "ka gaida gida Ahmad " AA Arab ya ce "in Sha Allah" daga haka mamah ta mike Dan Basu waje ta haura sama.bayan tafiyar mamah shiru ne ya sake biyo WA baya kafin AA Arab ya kalii watch din hannunsa ganin lokaci na tafiya yasa ya xaro wayar Ruky daga aljihun suits dinsa ya Mika mata batareda da yayi magana ba,hakan da yay yasa ruky dake kallansa taga ya Mika mata waya yasata yin jimm tana kallansa, ganin taki karb'a yasa AA Arab ajiye mata kan center table din Dake gaban sa, ganin haka yasa ta Mikewa daga inda take zaune ta dauki wayar bayan ta zauna ta ce "thanks very hugely sir" maimakon ya ansa sai ya ce cikin cool voice dinsa "ki Bude wayar ki turamin da record din tareda report din da barrister shamsu ya ce suna gunki "ya qarasa fada yana kallan ta, ruky ta Wani kallesa sai Kuma ta kau dakai ta ce " ta Ina to zan tura Maka?" ya ce "duk ta inda kika ga dama" daga haka ya mike tsaye , ruky itama mikewa tai ta tura Baki gaba ta ce "Allah da GSK nake maka bansan ta ina zan tura maka ba" ta fada tana karya wuya ya dauke kansa daga kallanta , kamar Bazai magana ba sai Kuma ya ce " ta sama xaki tura"ruky ganin da GSK yake yasa ta ce " to aini Banda contact din ka bare na tura Maka, ya ce "ki karba a wajen Hanan Kuma ayau nakeso ki tura min daga haka yay waje abinsa, ruky ta bishi da kallo,sai Kuma ta tabe Baki ta ce " lallai ma mutumin nan ahaka Hanan take cewa wai yana da kirki tab ,ina Wani kirki anan ta tabe Baki ta koma ta zauna tana murnar ganin wayar ta _ta dawo gareta harga Allah taji dadi ba kadan ba,sai Kuma taji haushin Daya Bata ta daina ji ganin ya kawo mata wayar ta gashi harda charging aciki full ma kuwa.....





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*___THE WOMEN POLICE ___*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*___(MRS SARAKIES =؋?)=?1?*



*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 7?? 1??



___________?&


Sai da daddare lokacin ruky zata kwanta ta kira Hanan awaya tanayin picking bayan sun gaisa Ruky ta rasa me zatacewa Hanan sbd ita kanta Batasan me xata ce mata ba,da kyar ta samu gathering courage ta ce "am Dan Allah Hanan number yayanki xaki tura min" Hanan tai tsam alamar tunani,can sai Kuma ta ce "Wani yayan nawa"? ruky ta harari wayar kamar Hanan dince agaban ta tace "bansani ba" Hanan tai dariya sai Kuma tace "wlh bangane wannan yayan nawa kike fada ba?wai ya Habib? Ruky tace "oho" Hanan tace "sai dai ya Habib tunda kinsan shi kad'ai ne Yaya na" ruky ta ce"bashi ba" Hanan tace "to Wani yayan nawa" ruky ta rintse ido ta ce "yayan ki na kalan dangi mana" hanan tai dariya tace " wlh bangane ba? Ruky tai tsaki ta ce AA Arab " Hanan da Daka tsalle daga kwancen da take tace "to yau din Kuma? Kuma shine baza ki fito kan ki tsaye ki fadamin ba saikin min kwana kwana? Ruky ta ce "Dan Allah idan zaki tura min ki turamin idan Kuma baxa ki turamin ba ki fada min" hanan tace "a'a ki bini a hankali inba haka ba wlh baxan tura ba"


Ruky tai tsaki ta ce "ke Karkiyi tunanin haka kawai yasa nace ki turamin number zan kirashi bare ki Raina min hankali,xuwa yay har gida ya ce na tura masa record din nan na wayata Amma badan haka ba me Zanyi da number sa" Hanan sai dariyar isakanci takeyiwa ruky,ita ko ruky haushi kamar ya kashe ta ,afusace tace "tunda baxa ki turamin ba bari na kashe waya ta daga haka ta kashe wayar tana sakin tsaki ,dama tasan wlh sai Hanan ta fassara ta,tai tsaki da dangwa rar da wayar kan gadon.ita ko Hanan Sai da tai dariyar ta me isarta sannan ta turawa ruky number AA Arab tana kudurta aranta in suka hadu Saita mata tatas.....


*Bayan kwana hudu*


Bayan kwana hudu ya kasance yau Laraba , gobe Kuma ya kasance Ranar alhamis,ranar da xa'a Yi xaman kuto kenan idan Allah ya kaimu, kamar yadda his Excellency governor ya fada,a Kuma kwana biyun da suka wuce anyiwa shafa aiki Saidai har lokacin ana jiran aga aikin yayi ko Bai yu bane Dan dole sai a hankali bawai take xa'a Gane aikin yayi ko baiyi ba ,Amma akwai kwana kin da suka Bada suke sakaran idan aiki yayi kyau da xarar kwana kin sun cika koma Basu cika ba xa'a ga canji na samun saukin kenan .suna nan dai suna addu'ar Allah yasa anyi aikin cikin nasara, Allah yasa adace . AA Arab ya aika police gidan 'yan ta'addar nan masu mata da suka Bada address din gidan da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login