Showing 237001 words to 240000 words out of 278032 words

Chapter 80 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1096

uhmm kamar wata Mai ciwon Baki ",.


Hana tace .

"To Me zance?",

Ruky tace .

"Bansani ba", sai Kuma ta cigaba tace

"yanzu Yaushe ya kamata mu fara preparing d'in?",

Hanan ta sauke numfashi kafin tace.

"Duk lokacin da kikaga ya dace, sannan kuma kema da naki zamu had'a ",ta fad'a In a serious talk.

Ruky tai murmushi tace .

"Ai sai anfara naku sannan za'ayi ,Kinga ko ai naki zamu fara ",ta fad'a tana murmushi

Hanan tace.

" Wallahi baki isa ba ,tun yaushe nake bin kanki muje mu fitar da ashoben bikinki kika k'i, shine yanzu Dan Kinga nawa yazo zakice muje mu fitar to wallahi indai kina so afara preparing d'in to sai in kin yarda kema da naki zamu had'a,idanko Baki yarda mu had'a ba to saidai a barshi", ta fad'a cikin Jin haushi.


Ruky tai murmushi ta ce.

"To shikenan Maida wak'ar amaryar yayan"

Daga haka suka cigaba da hira.



Kamar yadda AA Arab ya fad'a da shafa tai sati biyu da sallamarta da akai daga asibiti ya koma gidan da suke ciki Dan duba jikinta ,kuma Alhamdulillah da sauk'i, Hakan yasa aka kaita tsadaddiyar makaranta tundaga matakin primary zata fara,yay mata registration da komai dai da ake idan za'a Saka new student a school duk shiya biya kud'in komai a aljihunsa, sannan ya Basu kud'in su Wanda akaci tarar lateef na cin zarafi da keta haddin shafa dayay, Baba lami tace ya ajiye musu a wurin sa ita Batasan ya zatai dasu ba idan ya bata ,yace baza'a Yi haka ba banki zasuje a Bud'e mata account asa mata kud'in aciki,baba lami ta amince suka je banki aka Bude mata account yasa musu duka kud'insu aciki da Shaidu da komai, sannan suka dawo,dayake gidan Daya siya musu babu abinda babu aciki yasa babu abinda zasu buk'ata nan kusa dai, bayan nan ma governor ma ya Basu gida sannan ya bawa baba lami jari na mak'udun kud'i masu yawa dan taja jari ,tai ta godiya kamar zata Ari Baki Dan harda kukunta,.



A b'angaren Khalil shima ya samu K'arin matsayi awajen aikinsu,sannan Kuma gomnati ta k'irashi ta masa shatara na arziki sannan tace idan Yana buk'atar K'aro kararu ma ashirye take data d'auki nauyin sa da zai tafi karatu zuwa k'asa shen k'etare ya Kuma zab'i duk k'asar da yake so , Khalil yayi godiya harda kukunsa iyayensa ma haka sukai ta godiya sannan Kuma yace ya amince zai tafi k'arin karatun,Dan haka take aka rubuta nan da watinni biyu masu zuwa komai zai kammala na tafiyar tasa wannan kenan.


Shikuma AA Arab, governor yace president ya Bada Sak'o a fad'a masa idan ya dawo daga ganin likita yanason ganinsa a Abuja, sannan shima kuma kansa governor akwai abin alkhairin Daya tanadar wa AA Arab jira kawai yake lokaci yayi ya gabatar masa da abinda yay niyyar yi masa. wannan kenan....



_________?&


A b'angaren su Alhaji sunusi kuwa , wannan mutumin da suka zalinta kuma suka had'u dashi a prison shekarun da suka wace,to dai babu abinda ya sauya na D'aya daga cikin azabar da yake gana musu, atak'aice dai ya Sako su a gaba dan azaba yake gana musu iri daban daban,ga sasu partic da yake Yi kala kala,kai hatta kayansu na prisoners da sai sati sati suke wankewa ,Amma yanzu Ganin su Alhaji sunusi kusan kullum sai yasa yaran sa sun had'o WA su Alhaji wankinsu yace su wanke musu shi tas,babu kuma damar musu dole suyi Hakan, inba haka ba suci duka agunsa, tun su Alhaji sunusi Basu Saba ba har dai suka Saba ta k'arfi da yaji,ga duka dayake musu ko kunyar girmansa da sukayi baiyi ba haka yake rufe ido yake gana musu azaba kamar me ,ko k'iransu Yayi jiki na rawa suke zuwa su zube a gabansa har k'asa suce gasu,kai azaba dai babu kalar wacce Basu Gani ba ko nace suke kan Gani,idan ku ka ga su Alhaji sunusi sai Kun tausaya musu saboda yadda suka fita hayyacinsu lokaci D'aya ,Kuma kaf cikin ma'aikatan Babu Wanda ya tab'a magana kan abinda ake musu tunda suma yafi k'arfinsa,..


Ga lateef Shima duk da a prison D'aya suke amma Kuma ba wajensu D'aya ba, b'angaren su da lateef daban.in kuka ga yadda lateef ya koma saiku tausaya masa Dan lateef yanzu ya koma abin tausayi gabad'aya yayi nadamar abinda ya aikata ,ya Gane kuskuransa ,yanzu babu laifin Wanda yake Gani Irin na Alhaji sunusi , tunda duk shiya D'ora shi a turbar tsiya gashi yanzu Yana girban in ya shuka,har gara ma Hajiya SA'A ita tana Hanashi Wani abun idan yanayi ko idan zaiyi , Amma shi Alhaji sunusi sai dai yace ta barshi yayi abinda ya ga dama yau ga Abinda yake yi d'in ya kawoshi kan gab'ar Dana sani,idan ya tuno da wannan abun sai yaji gabad'aya ya tsani kansa,sannan kuma Babu tsanar Wanda yake ji Irin Alhaji tsanar Alhaji sunusi,Dan ji yake yanzu ya tsani Alhaji sunusi kamar mutuwarsa, tsanako mafi Muni Wanda ko had'uwa dashi sukai awajen aiki baya tab'a bari su had'u ko da ko sun Had'un ,to baya tab'a masa magana, Alhaji sunusi yay ta kuka Yana cewa ya kula shi ko zaiji Dad'i aransa,sannan yace ya yafe masa abinda yay Masa Amma lateef kwata kwata baya Sauransa ,idan yaga hakama tashi yake yake bashi waje shima Yana kukan tausayin kansa,Yana Kuma Daya sanin abinda ya aikata, lateef da ada D'an Gayu D'an k'walisa Amma gabadaya yanzu duk babu wannan ya koma sak kalar 'Yan prisoners d'in, yanzu sallah Bata wuceshi kullum Yana cikin addu'a da Neman gafarar Allah akan duk abubuwan Daya aikata,Dan Yanzu ya Gane gaskiya .


Zaliha kuwa laulayin ciki take Sosai ga Abu ya fara fitowa fili kowa Yana Gani, Baba asabe tayi tayi taga Cikin nan ya zube Amma kuma Abu ya gagara Dan ciki dai gashi harya fara fitowa Dan zaiyi kimanin sati 8 ajikinta,baba asabe ta rame ta tsigi, kud'in tallar da take tak'ama dashi ma to duk sun k'are wajen Neman maganin zubar da ciki na gargajiya Dana asibiti ,yanzu Bata da komai ko naira biyar Bata maganinsa ,jiya fad'uwa ma tai tana tsaye ranga ranga aka kaita asibiti ,Koda aka dubata lokita cewa yayi ai jinin tane yahau sosai Allah ne ma ya taimaka Bai sa ta kamu da paralyzed ba, Amma yanzu sun d'orata akan magani sunce kuma ta cire Damuwa aranta,ta samu waje ta huta ta daina yawan tunani da hayaniya, Amma Ina baba asabe bazata tab'a iya cire Damuwar Dake damunta taba, Ameenah dai anyi wata biyu da fara iddar ta yanzu haka baifi wata D'aya da kwanaki ba ta gama,itama Nana tana can a makaranta tana ta karatu abinta sai dai patan Allah yasa a gama lafiya .....

Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y







*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)____*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 9?? 4?? ??




____________?&


Kwance tashi babu wuya awurin Allah, satuka suna ta shud'ewa,Kwanaki suna tafiya har yau ya kasance baifi Saura sati biyu bikin su ya Tahir ba,ankai kayan lefe kwana biyu da suka wuce akwatuna ne set bibbiyu sukayi wa matan da zasu Aura, ya kama guda goma Sha biyu Kenan,Kuma ko Wacce haka aka kai mata nata gidansu.


bikin ruky Kuma Saura one Month kacal ya rage kenan,shirye shirye kawai ake ta ko wanni b'angare.


Yau Gabad'aya ruky a gajiye ta dawo gida saboda yanzu ma haka daga wurin tailer suke ,Dan tun bayan la'asar suka tafi Amma Basu dawo gida ba ita da Hanan sai yanzu da ake K'iran sallahn magrib, shiyasa ta gaji tib'us ga sunyi da AA Arab yau zaizo, after isha'i prayer.


Tana shigowa d'akin ta tai cilli da handbag d'inta saman gadon ta tana sauke numfashin gajiya ,ta fara rage kayan jikinta Dan Allah ya Gani Wani Irin zafi take ji kamar me, duk da garin bawai lokacin zafi bane zamu iya cewa ma sanyi ya D'an fara shigowa kad'an kad'an Amma Kuma bawai ya shigo gabadaya bane ba,ta d'aura towel sannan Tai hanyar toilet danyin wanka ko zataji dad'in jikinta,tayi kusan 20 minutes acikin toilet d'in Kafin ta fito tana d'igar ruwa.


hannun ta rik'e da karamin towel tana tsane ruwan daki D'iga ajikinta ,ta samu samun stool d'in dake gaban mirror ta zauna ,bayan ta aje towel d'in a gefe ta fara Shafa lotion d'in ta masu dad'in kamshi da tsada bayan ta gama ta k'arasa gaban wardrobe d'inta ta Bud'e ta d'auki wata dogowar riga marar nauyi ta Shan iska ta Saka Sannan ta d'auki cap da Saka akanta kafin ta fito cikin sauri Dan sauka k'asa Dan wallahi wata Irin Yunwa takeji kamar me,dan d'azu da zasu fita bataci Abincin rana ba,bayan ta sauka downstairs Bata tarar da kowa a falon ba,ta k'arasa dining d'in tana bubbud'e warmers d'in tana ganin abinda aka dafa Wanda zata iya ci ,ta D'an tsakuri Wanda zata iya ci dai dai cikin ta sannan ta rufe warmer d'in,ta jawo plate d'in gabanta ta fara cin abincin cikin nutsuwa, bayan ta gama ta goge bakinta da tissue kafin tasha ruwa ta mik'e tana ambatan Alhamdulillah a saman lab'b'anta,tai hanyar d'akin mamah Dake k'asa ganin batanan yasa bar bakin k'ofar tai hanyar stairs Dan haurawa sama zuwa d'akin mamah Dake saman k'ila tana can.


Bayan ta isa Tai knocking kafin ta tura k'ofar ta shiga bakinta d'auke da sallama,ta Tarar da Mamah tana kan sallaya tana addu'oi,ta samu waje ta zauna har mamah ta idar da addu'ar ta kafin ta juya tana kallon ruky wacce ke kallan ta, ruky tai murmushi tace .


"Sannu da gida Mamah",ta fad'a tana murmushi.

Mamah ta kalleta kafin tace .

"yaushe kuka dawo?",

Ruky tana kallan ta tace.


"d'azu ana K'iran sallahn magrib,Dana shigo Banga kowa a falon ba,ga nadowa Ina Jin zafi shiyasa kawai na wuce d'aki nai wanka ",ta fad'a tana kallan mamah.


Mamah ta Jin jina kai kafin tace .

"Kinci abincin kuwa?",

Ruky ta gyad'a mata kai kafin tace ."eh naci".

Mamah ta k'ara Jin jina kai kafin ta mik'e daga zaunan da take tana linke sallayan hannunta ,ta ajiye saman site drower Dake d'akin tana kallon ruky tace.

"Ahmad d'in baizo ba Kenan?naji kince zaizo anjima",.

Ruky ta sunkuyar da kanta k'asa cikin Jin kunya tace.

"Eh, Amma nasan yanzu haka Yana hanya ", ta fad'a tana wasa da zoben hannun ta.

Mamah ta Jin jina kai kafin tace .


"Shikenan",


Ruky ta mik'e???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? tace .


"Mamah bari naje D'aki nabar wayata acan ",

Mamah tace shikenan sai kindawo", daga haka ruky ta mik'e ta bar d'akin, mamah ta bita da kallo kafin ta d'auke kanta tana Sauke numfashi,ta fara kar Kad'e saman gadon nata .


Ruky ta sauko downstairs tai hanyar fita daga falon bayan AA Arab ya K'irata cewar ya iso, dayake yanzu ya zama D'an gida su kansu ma'aikatan gidan sun motocin da yake zuwa dasu gidan,suna ganin ya iso sun San shine zasu Bud'e masa gate ya shigo yay parking sannan ya shige falon Bak'i kansa tsaye inda anan yake sauka already Dama ya sani.


To yanzunma hakance ta kasance Yana zaune a cikin falon akan kujera hannunsa rik'e da wayarsa Yana opporatig d'inta, dag'owar da zaiyi da kansa yaga ruky ta shigo falon bakinta d'auke da sallama kanta a k'asa,ya ansa mata har lokacin idonsa na kanta ,ya rasa Mai yasa har yau ruky Bata daina Jin kunyar Saba, Kuma Shima Hakan na burgeshi Dan yana son mace Mai kunya arayuwarsa, shiyasa har yau San ruky kullum K'ara ruruwa yake acikin zuciyarsa Baya ganin ko Wacce mace sai Ruky ita yake yiwa kallan mace Amma duk matan da yake Gani a mata Maza yake kallansu ,Bai saniba ko dan akanta yasan so ne, sannan kuma ya fara so oho.tunaninsa ya katsene lokacin data K'ara masa magana a karo na biyu tace cikin zazzak'ar muryarta wacce take K'ara tsunduma shi da susu tashi a duk lokacin da zatai masa magana tace .


"Deee! sunan data ke k'iransa dashi yanzu kenan,tai masa fari da ido tana murmushi kafin tace .


"wannan kallon fa",ta fad'a tana zama kan D'aya daga cikin kujerun falon wacce ke pessing d'in tasa.


Ya lumshe ido Yana bud'ewa lokaci D'aya kafin ya Shafa kansa Yana D'an murmushi yay k'asa da murya yana kallan shigar jikinta cikin abaya take coffe color wacce ta fito da ainihin haskenta da Kuma kyanta,kafin yace.

"wow! fiancee u look very very beautiful",ya fad'a Yana kallan ta tare da kashe mata ido D'aya Yana murmushi,


Ruky ta sunkuyar da kanta k'asa tana murmushi kafin ta d'ago ta kalleshi ganin har lokacin idonsa Yana kanta yasa ta tura Baki gaba ta kauda kanta gefe kafin ta ce .

"Shiyasa kakemin wannan kallon kenan", ta fad'a tana gyara zaman mayafin abayar.

Ya dan Bud'e ido Yana kallanta ,kafin yace cikin deep voice d'insa.


"Idan na Kalli halal D'ina nayi laifine ?"ya fad'a Yana zuba mata lumsassun idanuwan sa.

Ruky ta k'ara kau da kanta daga kallansa Ganin Yadda idonsa ya sauya lokaci D'aya tana D'an murmushi cikin kauda zancen tace .

"Bari ka fara Shan ruwa kafin kaci gaba da maganar",ta fad'a tana mik'ewa.


Ya zuba mata ido kawai Yana ganin movement d'inta ganin yadda komai nata yake Masha Allah, kafin Yay saurin kauda tunanin sa har ta tsiyaya masa ruwa ta kawo masa har gaban sa ,yay murmushi ya furta thanks a saman lab'b'ansa, kafin ya sa hannu ya karb'i ruwan hannunsu ya had'u Dana juna,gabad'ayansu Saida sukaji Wani yarrr lokaci D'aya aduka sassan jinkinsu bayama Ruky kafin tai saurin janye hannun ta tana Jin gabanta na fad'uwa ta koma gaban table d'in Dake shak'e da kayan abinci da aka kawo masa ta zabo masa pepper chicken d'in datai masa da Kanta d'azu ta ajiye masa kan Wani table d'in Dake gaban sa har lokacin Bata k'ara yarda sun had'a ido ba,shiko AA Arab idansa k'yar akanta ,Yana Jin Wani yanayi na fusgarsa,saida ta koma ta zauna kafin ya lumshe idonsa bayan ya sauke glass cup d'in Dake hannunsa kan table d'in gabansa ya D'an yamutsa fuska tare da shafa cikinsa yace.


"I'm full fiancee! bazan iya cin wannan abinda kika kawomin ba", ya fad'a Yana narke mata.


Sai alokacin ruky ta d'ago tana kallan sa da kyau blue black d'in Wani tsadaddan yadi ne ajikin sa Wanda in Banda shining Babu abinda yake Yi ke da Kin ganshi kinsan me tsada ne ,batasan me yasa manyan kaya suna bala'in yi masa kyau ba ,kodan kullum cikin uniform take ganin sa oho,tai saurin kauda tunanin ta kafin ta tura Baki gaba tana kallan sa tace cikin shagwab'ar da take Saka AA Arab shiga Wani yanayi aduk lokacin da tai masa ,Amma ita awajen Ruky ba komai bane saboda ta Saba tace.


"Nidai saika ci,wai meyasa bakasan kaci duk abinda na kawo makane?",ta fad'a tana K'ara tura Baki gaba.


AA Arab ya sauke numfashi kafin ya k'ira sunanta da .

"Fiancee! Ya cigaba Yace ."Kawai na k'oshi Amma kema kinsan da zanci ai",ya fad'a Yana tsareta da mayun idanuwan sa.


Ruky ta kauda kai tana tura Baki gaba kafin ta kalleshi ido cikin ido tace .

"Nidai idan ba so kake nai fushi yau ba to kaci",

Ya Sauke numfashi yana kallan pepper chicken d'in Dake gabansa Wanda Babu abinda yake tashi acikinsa sai Wani daddad'an k'amshi Dan daga Gani zaiyi Dad'i. Ya sauke numfashi yace .

"ok I'm sorry zanci Dan bazan so zuciyar Ahmad tai fushi ba",ya fad'a Yana murmushi.

Ruky ta juyo tana kallon sa itama murmushin ne a fuskarta,har ya sa fork ya fara d'aukar naman Yana kaiwa bakinsa ,ya d'anci da d'an yawa kafin ya goge bakinsa da tissue Yana cewa Alhamdulillah a saman lab'b'ansa .

Yana kallan Ruky yace .

"Gashi naci Aiko? Sai Kuma yace ."thank you fiancee!, gashi kuma yayi Dadi sosai" ya fada Yana Wani shafa cikinsa .

Ruky tai murmushi tace .

"Never mind Deee",

Ya gyara zamansa Yana kallan ta cikin nutsuwa kafin yace.

"Kuna ta shirin bikin Hanan, but ni Banga Kuna shirin naki bikin ba ke? ",ya fad'a Yana kallan ta.


Ruky ta Dan Bude ido tana kallanshi sai Kuma tace .

"Tare mukeyi mana harda nawa ai",ta fad'a tana kallan sa.

Ya lumshe ido yana bud'ewa akanta lokaci D'aya yace .

"Amma shine Baki fad'a min ba bayan nace duk abinda zakiyi ki fad'a mun" ya fad'a in a serious talk.

Ta sunkuyar da kanta k'asa kafin tace cikin K'asa da murya,

"ai ba Wani babban Abu muka fara ba kawai ashobe ne muka fitar ,sai wasu d'inkuna da mukayi Wanda duk ma na shirin bikin su Hanan ne",ta fad'a cikin marai raicewa.


Ya Sauke numfashi kafin yace .

"Ok,but kema ya kamata ace kin fara naki shirye shiryen koh?",ya fad'a Yana kallan ta .

Ta Jin Jin masa kai, Amma batace komai ba.

Yace."zan tura miki kud'i ki fara duk abinda kike so ", ya fad'a Yana kallan ta.

Ta sunkuyar da kanta k'asa kafin tace "ok, thanks",

Yace ."no thanks in between us, ok.ya fad'a Yana kallan ta.



Ruky ta kalleshi kafin ta Jin jina masa kai,

Yay k'asa da murya Yana kallan ta yace.

"I love u fiancee!",

Ruky ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta tana Murmushi,shima murmushi yay Yana jin Wani feeling akanta Wanda ya kasa Gane wani iri ne,nan dai suka Dan tab'a hira kafin ya Mik'e yana kallan tsadaddun watch d'in hannunsa Yana kallan ta yace .


"It's too late bari na tafi Kinga dare yayi koh?mayi waya ",


Ruky ta jin jina masa kai kafin itama ta mik'e ya Tako har gaban ta ya duk'a Yana lek'en fuskar Yana murmushi yace cikin k'asa da murya.

"A dago a kalleni Mana?", ya fad'a cikin wata iriyar murya Yana Kuma murmushi.

Gabad'aya Ruky dubur burcewa tai ganin sa dab da ita har suna iya Jin numfashin juna zata Matsa baya da sauri Kenan ta hard'e da rigar jikinta ta kusan fad'uwa k'asa take yayi azamar rik'ota zuwa jikinsa da sauri yana kallan ta ido cikin ido kafin yace cikin damuwa Amma Kuma a nutse Yay managar.

"Are okay, ya fad'a Yana binta da Wani Mayan Kallo.

Ai ruky hatta saddak'ar tama Fad'i Amma taji ta jikin mutum ta ,ta gyad'a masa kai itama tana kallon sa,ya Sauke numfashi ya K'ara duk'o da kansa dai dai fuskarta Yana kallan ta ido cikin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login