Showing 9001 words to 12000 words out of 278032 words

Chapter 4 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1079

daga office din DCP nake shima yace yayi ta kiranki bakiyi picking ba,...

Ta xuba masa mayun idanuwanta,ganin yadda ya dage Yana xuba, yace Ruky ,ta ya Mutsa fuska tace meyasa ake ta nemaba me nayi Kuma,yace wlh bansaniba Amma kije ,tunda DCP ne kadama ki tsorata,ni nasan may be baxai wuce xancen Kuba,ya fada da sigar tsokana,ta harareshi tace saidai sirrin mu ba xancen muba,ya hade hannayensa yace sorry karki fusata,Amma Dan Allah kijr xatai magana Kiran DCP ya ratso wayar ta inda ta dafe kai tareda karamin tsaki, tace bari naje, Shareef yace saikin dawo, ta fita shikuma Shareef ya xauna a gaban computer yana duba Abu,...



Ruky tana xuwa office din DCP,tai nocking aka Bata ixnin shiga,ta tsaya a falon DCP Dake falon da waya a hannu ya kalleta,yayi murmushi yayi kasa da murya,saikuma yadan tsuke fuska alamun damuwa yace tawan Ina kika shiga,ta dago ta kalleshi da idanta Wanda yake mugun sakashi a yanayi indai ta kalleshi dasu kuma take kashesa a Santa,maimakon ta bashi ansa sai cewa tai sir good morning, yadanyi murmushi yace morning tawan ,cikin damuwa yace Ina kika shigane,tai qasa da kanta tana Dan hade Rai tace sir I'm sorry Wani abune ya tsaida ni,yace wayarki fa da nai ta kira ,tace shikuma yana silent ne banganiba,yayi shiru Yana kallan dan bakinta Wanda shine yake kashesa a duniyar Santa,ta dago Jin yayi shiru ,taga ya kura mata ido kawai saita qara hade Rai,yay murmushi yace mu xauna mana,batai musu ba suka zauna akujerrun falon,yace kinsan meyasa na kiraki,ta girgixa kanta,yace akwai Wani case da nakeso kuyi handling dinsa keda Shareef shi na masa bayani kece dai kawai kika rage,akwai kowani information da zakubi nabawa Shareef, please tawan na sanki da kokari , so wannan dinma ayi kokarin sosai, please,tace in Sha Allah sir yace , shikenan, please xankiraki da daddare Dan Allah kiyi picking tai qasa da murya tace ok,taji yayi shiru for a minutes Dan haka ta mike tace thank u,bari naje ya daga mata kai har sannan Yana murmushi,ya bita da kallo ganin ya fita ,

Tana xuwa office tai kan Shareef tana masa masifar Ashe yasan Kiran da DCP yake mata shine Bai fada mata ba, Shareef ya Bude Baki yana jinta Saida ta gama tai tsaki ta xauna a seat dinta Shareef ya juya gareta yace a'a ni haka yace min , karna fada miki komai ,kawai na kiraki,tai Banxa ta kyaleshi yayi murmushi yace koba komai ai nasan ,Bai qarasa ba ta dago tace kasan me ,yay murmushi yace sorry tace ka karasa mana,yay shiru yana murmushi, ita Kuma tai kwafa ta cigaba da aikinta,Daya san yadda ta tsani mutumin nan da baxai dinga mata zancesaba harma Yana hadata dashi...

Duk da DCP a shekaru xaiyi Irin 40 dinnan Kuma ba tsufa yayi ba ita kawai Bai mata bane ,be side ita bama tasan ta AURI mijin wata tafiso ta AURI nata ita kadai


Da daddare ruky suna xaune a falor suna kallo ita da mamah, tana xaune ne kawai Amma hankalin ta Yana kan wayarta so take ta Kira Ibrahim Khalil awaya Dan so take cikin satinnan suje gidan matar nan sbd abun Yana ranta badanma aikin da DCP ya Basu ba da gobe takeso suje,Amma in Sha Allah suna gamawa xataje, ta miki a shagwabe tai mika,dama ajikin mamah take a kwance,tace mamah gud night xanje na kwanta bacci nakeji mamah tace shikenan auta Allah ya tashe mu lpy Nima yanxu xan tafi ,haka ta haura sama, bayan Sunyi waya da DCP,inda tashiga toilet tai wanka ta fito ta shirya, tana kokarin kashe wayar ta kira ya shigo ganin Mai Kiran yasata jan tsaki ta kashe wayar ma gabadaya sbd karma ya cigaba da kira Dan ba gajiya zaiyi ba,


_______ZAR'IA________


Ummah tana bakin kofar ta ,tana har hada Dan kayan abincin da zata aika Nana ta kaiwa Ameenah tunda taji tace Kabiru baya Bata abinci, gabadaya ta damu gasu ba wayace da Ameenah ba bare suyi, Baba asabe Kuma tana wanke wanke ,tana Dan wake wakenta ganin malam Auwalu, jiya ,yadda yayi wa ummah ta tas bayan tafiyan Ameenah,Nana Kuma taje islamiya itadai ummah Bata kulataba,Malam ya fito daga dakinsa cikin shirin fita,baba asabe cikin kissa akace malam fita xakayi Yana gyra hular kansa yace eh ,tace Allah ya kare malam yace Ameen Yana Mai qarasawa kusa da ummah wacce kallo Daya tai musu ta dauke kanta,malam ya qarasa wajen ummah yace maimuna ta dago ta kalleshi,yace xan fita Batare data kalleshi ba tace adawo lpy,yace ko har yanxu fushi kike ,tai Banxa ta kyaleshi Jin tambayar dayake mata,baba asabe ta cika ganin yadda malam yake yiwa maimuna magana tana ba Banxa ajiyar sa Amma ita tana masa magana yana kyaleta,ita da take masa magana ai duk Dan kada ya kula maimuna ne, Amma Saida ya kula ta,yajuya ga baba asabe yace asabe ki kira zaliha ta dawo
Gobe ai ko yanxu ta huta, asabe da haushi ya isheta ,tace ai gidanmu taje ba yawan ta xubar ba, malam yace ni dai na fada miki, saina dawo,daga haka yasa kansa ya fice daga gidan,inda ta bishi da harara Dan wlh da so tai ta kunnashi ta tsokalo aibun maimuna sannan ta fada masa cewa xata aika Nana ta kaimata kayan abinci In yaso ya hana Amma shine baima tsaya ba bare ya saurareta,haka tai fuuu ta qarasa wanke wankenta ta shige daki xuciyarta kamar ta Kone, meyasa malam wai yake qaunar maimuna ne duk abinda xata hada Koda yay tasiri to in Sha Allah aranar ko Washe gari dole saiya kula maimuna,tayi tayi ta rabasu Amma abin yaki,

Ummah kan ai jiya batai baccin kirkiba da tunanin Ameenah ta kwana,ko awani Hali take oho,ya xa'ayi ace yarinyar ga Abinda ta fada Amma me makon malam ya duba yaji ta bakin kowa Amma shine kwata kwata baxai wannan ba sbd matarsa duk abinda ta fada masa shikenan, yarinya karama Irin Ameenah wlh indai komai Bai sauyava wlh ta daura damarar kwatowa Ameenah yancinta saidai idan
sakinta ma xaiyi yayi,...




07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*_____JAMI'AR TSARO_____*


*_____THE WOMEN POLICE_____*


_____THIS STORY IS TOUCHING HEART, I WAS SPEECHLESS TO EXPLAIN IT, BUT WE SHOULD SEE ON WHAT HAPPENED TO OUR LIFE KNOW, SO, BE WITH ME U LOVE IT MORE THAN U EXPECTED ________
'?



*NA*


*_______NAJA'ATU UMAR FAROOQ_______*


*_____(MRS SARAKIES)_____*


*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION*(QUWA) =?1?


*Bismillahirrahmanirrahim*


______season one ep 6??


_________
'?
'?

KADUNA STATE

AREA:MALALI

yau weekend ,11:30am, Ruky tana shiryawa domin yau zasuje unguwar hayin rigasa,gidan matar nan inda sunyi waya da Ibrahim Khalil tace xata fito ne ta daukeshi a unguwar su Dake tudun wada,inda gefe Daya Kuma tana tunanin qaryar da zatayi mamah, domin ko hauka take baxata tava bari mamah tasan abinda take shiryawa ba,haka ta Sako blue black din hijab dinta har qasa ,bayan tasa riga da sket daga ciki,saitasa face mask,ta dauki designer hand bag dinta,da Kuma plat shoe, Wanda yake set din jakar ne,haka ta sauko kasa tana addu'ar Allah yasa karta hadu da mamah,Amma saidai me , addu'arta bata karbuba,mamah tana falor hasiya na gefenta, Jin taku alamun saukowa yasa su wai wayawa,mamah tace a'a yau Auta kece da fitowa da wuri,....

Hasiya Ta washe tace a'a uwata kece ,yanxu hajiya takecewa naje na tasheki sai Kuma gashi kinma sauko,Ta qarasa saukowa, da murmushi a futkarta tace wlh koh baba hasiya yaudai Kinganni na tashi da wuri ta fada tana xama a gefen mamah,tace mamah gud morning,mamah ta ansa mata tana kallanta ganin shirin da tai na Mai fita unguwa, tajuya tace baba hasiya Ina kwana,baba hasiya ta ansa mata kulawa,...

Tasa kanta kan kafadar mamah, tace mamah , mama tace na'am Auta wannan shirin fa da kikai haka Ina xaki tace mamah xanje gidansu Hanan ne ,Bata Dan jin Dadi ne shine xan je na dubata, cikin damuwa mamah tace Ayya Allah ya sawake gsky ya kamata kan kije Dan inda itace inta dinga sintirin xuwa duBaki harsai taga kin warke, Yi Maza kiyi break fast saiki tafi,yau kan Babu musu ruky ta mike ta Isa dining,ta fara Yin break fast din, tana farin ciki yadda xata fita,....

Bayan ta kammala taiwa mamah sallama da hasiya ta tafi mamah tana qara maimaita mata tai addu'ar fita daga gida Kuma taima Hanan ya jiki,ta ansa mata da toh,....

Tana fita Dama already motarta angama warming din ta,shiga tai reverse kawai ,inda aka wangale mata gate ta fita,tai hanyar unguwar tudun wada,tana xuwa ta kira Ibrahim Khalil, bayan ya daga yace gani nan na ganki cikin motarki ranki dade, haka ya karaso inda tai masa nuni Daya shiga front seat gefanta kenan ,haka ya shigo bakinsa dauke da sallama,yace ranki dade barka da safiya,ta ansa masa tana mai kokarin gyara zamanta,inda ta tada motar, suka dau hangar hayin rigasa, ibrahim Khalil ya dinga satar kallonta ta gefan ido yadda yaga ta Maida hankalinta kan tukinta,ga Kuma abin birgewa yadda take tukinnata cikin nutsuwa da kwarewa,haka suka karaso unguwar,sai anan ta juyo ta kalleshi ya Mika mata wayarsa Dan yariga dayayi settling komai na address din awayar , haka ta karba ta dinga bi hardai suka xo layin,tai parking, inda suka fito ,suka fara takowa cikin lungun gidan,Dan mota Bata shigo wurin,....

Suna isa kofar gidan Ibrahim Khalil yayi sallama,ita Kuma Ruky tana gefansa tana qarewa gidan kallo, Wanda ke kina ganinsa kinga gidan talakawa tubus,dan katangar gidanma ta xanace,zanan ba duka aka zagaye ba,haka
Matar ta fito,ta ansa musu Jin sallama,tana qare musu kallo, Ibrahim Khalil yayi murmushi yace Baki Gane niba koh,

Tai murmushi tace ya xa'ayi baxan Gane kaba malam Ibrahim Khalil,kushigo ta fada tana Mai Basu hanya da su shigo,ya qara Wani murmushi ya Kalli Ruky wacce ta tsaya tana kallan matar yace mushiga ranki dade,haka ta bishi xuwa tsakar gidan,inda matar nan ta shimfida musu wata tsohuwar ta barmar kaba,tana musu lale ,ta dauko Wani tsohon kofin silver ta xubo musu ruwa aciki,tace gashi kusha ruwa,...

Ruky tai murmushi tace mungode,sai Kuma ta shiga gaidata,inda matar ta ansa da fara'arta, shima Ibrahim Khalil ya gaida ta,yayi gyaran murya yace am abune Mai mahimmanci ya kawo mu nan akan maganar da kikaje can gidan TV na GADANGA kika kai kokenki, wanna itace ASP Rukayya umar MaiTama, JAMI'AR TSARO CE,taji kokenki shiyasa taxo ta sameni har gidan TV mu ,tana so ta shiga maganar ne, shiyasa mukaxo nan domin ku gana,...

Matar nan ta saki Baki tana Jin Ibrahim Khalil,tana Kuma kallan ruky at the same time,wacce wai akace JAMI'AR TSARO CE xata Shiga case din su, abinda ta Dade da fidda Rai Dan ta barwa Allah kawai domin shi xai saka musu, tunanin ta ne ya tsaya lokacin da ruky ta kalleta da murmushi ,tace Baba karkiji komai,nidai abinda nakeso Dake shine ki yarda Dani, domin naji abinda kika fada a gidan TV na GADANGA,saidai ko akwai abinda kikesan qara fadamin, Amma yanxu kafin komai inaso naga marar lpyr,


Haka tai musu jagora xuwa dakin da wannan yarinyar take,inda suka tadda ta akwance kamar wata Mai cutar HIV, yadda ta rame tai Wani iri kamar wata yarinya yar shekara 8 bakyace takai shekara goma Sha uku ba,badan da face mask,a furkar ruky ba ,da Babu abinda zaisa tai amai sbd yadda dakin yake Wani Irin wari,shima ibrahim Khalil daurewa kawai yake domin yanxu ba ta warin suke ba,inda suka zauna a gefan ta, ruky ta xuba mata ido ganin yadda yarinyar ta xuba musu,maman yarinyar tace yauwa kin ganta, jami'a, Ruky ta kalli yarinyar tace sannu , yarinyar ta kasa ansa mata kawai kallan ta take har Sannan,...


Ruky tace da matar ,baba ya sunanki ne da ita, Tace sunana lami ita Kuma shafa'atu , Ruky ta jinjina kai tace ita kadai ce yarki,lami ta girgixa kai tace itace dai kawai Allah ya barmin, 'Ya'ya na g???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?oma a kasa itace Kuma ta karshe wacce Allah ya barmin,domin duk haihuwa nake basa kwana arba'in suke mutuwa, cikin damuwa ruky ta jinjina kai,domin duk wannan abin da take daukar Statement take haka ma Khalil,tace baba haryanxu tana xubar da ruwan daga kasan nata,baba lami da hawaye ya xubo mata ta dubi shafa sannan ta dubi ruky tace, saima abinda ya qaru domin kullum ciwannan kamar qara mata shi akeyi,Yanxu takai ta kawoma ko magana da kyar takeyi, ruky tace Kuma har yanxu kina karba mata maganin,ta share hawayen tace nakai kusan wata uku bansiya mata ba sbd babu yadda xanyi na samu kudin na siya mata domin Yana da tsada, Ruky ta jinjina kai ta kalli Ibrahim Khalil shima dai duk tausayinsu yake ji ,wlh duk Mai imani ya Kalli halin da suke ciki saiya xubar da hawaye bayama shafa wacce itace ma ciwon ke jikinta, ruky tace shikenan yanxu abinda xa'ayi kafin komai inaso mu kaita asibiti tukunna inyaso koma miye saiya biyo baya,sbd sai anfara samun lpyar ta at first, Khalil ya Jin jina kai,baba lami ta rikice tace ai bani da kudin kaita, ibrahim Khalil yace ,baba itace xata dauko nauyin komai , karkiji komai baba,...


Lami ta rasa Ina xata sa kanta yau itace akaxo xa'a taimakawa akai shafa asibiti,ta Bude Baki kawai tana kallansa kamar Bata Gane abinda ya fada ba, saikuma hawaye da Kuka , Ruky Ma,ta share hawayen ta a kai kaice,sbd itama akwai ta da tausayi, shima ibrahim Khalil gabadaya jikinsa yayi sanyi ganin halin daya Tarar da shafa aciki,...

Ruky ta kalli Ibrahim Khalil tace,idan badamuwa mu kaita yanxu, Ibrahim Khalil cikin girmamawa yace duk yadda kikai dai daine ranki dade ,ta tubi baba lami tace, yanxu baba xamu dauke kune mu kaita asibiti, baba lami tafara yiwa Ruky godiya ,kira take Allah ya miki albarka yar nan,ya kareki a duk Inda kike, Allah ya albarkaci binda kika Saka agaba,yayiwa iyayenki albarka yasa ki rabu dasu lpy,tayiwa Ibrahim Khalil ma,ruky da ibrahim Khalil suna ansawa da Ameen, cikin rawar jiki ta mike ta shirya shafa wacce Bata da Wani qarfi,itama tasa hijab dinta ta , ruky koh sun fito kofar dakin,inda ta goyo shafa bayan ta mata napkin,taja kofar dakin wadda take ta katako,ganin haka yasa su ruky fita kofar gidan suka wuce inda tai parking, inda ruky ta Bude mata seat din bayan motar ta shiga, sai itama ta shiga bayan Khalil ya shiga haka suka bar unguwar Wanda direct daga nan Wani best private hospital suka wuce Dake nan Kaduna,...

GIDAN AMEENAH

Kabiru yaza ayi baka kawomin kayan abinci ba, Kuma iyayena sun kawo min kace xaka dauka kasiyar idan ka siyar nikuma Mai xanci tunda ba sanin ci da Shana kayiba, na fada ina kokarin kwace buhun daga hannunsa,Dan ya rikene Nima na rike,inda Kabiru ya juyo da jajayen idanuwansa ,Yana ke ni Sa'an kine har in rike Abu kema ki rike, Ina fada kina fada, ki sakemin kafin nai miki duka wlh, danma kinyi SA'A tsohon ki Ya rokeni akan ki dawo,wlh ko kisake ko Kuma na kira tsohon naki na fada masa cewa kince na sakeki,kinsan halinsa ai, tunda ke naga agidan nakuma Neman kai suke Dake sbd haka wlh karkisa yanxu nan na fasa miki jiki,...

Inda naki sakin buhun hawaye na xubomin tunda na Dawo gidan kabiru Bai bani abinciba,har Saida ummah ta Aiko min dashi,a fadarsa tunda iyayena sun gaji Dani suka lika masa ni shi bazai iya ciyar Dani ba,danshima ta kansa yake,saidai idan nayi kitso idan anban ladanyi nasai abinci dashi,tunda tun Ina gida na iya kitso dama, baxato ba tsammani naji Kabiru ya kawomin duka,inda na saki buhun babu shiri, haka ya iyo kaina Yana ta dukana kamar jaka,tun Ina ihu hardai na daina,sbd Irin dukan Daya min,haka ya tsallake ni ya dauki buhunyatafi, ya barni cikina duk jini ,Dan ya fasamin Baki da goshi, haka na tashi da dafa bango na hau gado na kwanta Dan ko hauka nake baxan koma gidanmu yanxuba,indai na koma wlh kila sai baba yamin Baki, haka na Kwanta Dan wlh Kaina kamar xai fashe haka nakeji sbd ciwo bansan lokacin da bacci ya dauke niba....



07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*_____JAMI'AR TSARO_____*


*_____THE WOMEN POLICE_____*


_____THIS STORY IS TOUCHING HEART, I WAS SPEECHLESS TO EXPLAIN IT,BUT WE SHOULD SEE ON WHAT HAPPENED TO OUR LIFE KNOW, SO, BE WITH ME U LOVE IT MORE THAN U EXPECTED ________
'?



*NA*


*______NAJA'ATU UMAR FAROOQ______*


*____(MRS SARAKIES)____*


*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA)* =?1?


*Bismillahirrahmanirrahim*


_____season one ep 7??


________
'?
'?

*Hospital*

Ruky suna xuwa asibitin dayake weekend ne Basu Samu Dr ba sai nurses kawai ,sbd basa shigowa da weekend, sai Kuma Wani Dr christian ne,Amma shi sai Sunday yake shigowa sbd Yana ganin masu manya manyan cuta,haka aka dauki shafa aka shiga da ita emergency Wanda sai anfara treating dinta,sbd gabadaya cuta ta gama cinye ta,inda ana shiga da ita wajen 30 minutes sai wata nurse ta fito inda tace daki ZA'A Basu before gobe Dr yaxo ,Yanxu dai sun mata wasu allurorin Kuma sunqara mata ruwa sbd ceto rayuwar ta Dan Babu ma ruwa ajikinta,....

Haka ruky tai mata godiya Saida suka qara kusan 30 minutes sannan aka fito da shafa aka kaita Wani daki ,inda ruky tace da baba lami ta jirasu suna xuwa,haka suka tafi itada Khalil taje can inda ake biyan bill,ta biya komai, shidai Khalil kallanta kawai yake yana mamakinta yadda yaga tana kashe wannan uban kudin ,kamar Batasan zafinne mansuba,Dan iya bill dinma data biya kudine wanda ya girgixa shi sbd yawan su,gashi Bata da hadi dasu Amma take San taimaka musu, gsky ruky tayi arayuwa,yanxu da ace haka mutane irinsu masu kaki suke aida baxa a taba koke a qasa ba, tunanin sane ya tsaya lokacin dayaji tace suje su wuce su siyo musu abinci,haka suka biya suka siya musu abincin da Kuma wasu abubuwan,bayan sundawo wajen baba lami,tace baba ga abinci nan , sannan in Sha Allah zandawo goben saimu gana da Dr,gaKhalil xai dinga waiwayonku in Sha Allah kafin goben duk abinda kuke bukata kuyiwa Khalil magana in Sha Allah,ZA'Ayi komai,ta kalli wayar ta da tundazu ake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login