Showing 93001 words to 96000 words out of 278032 words

Chapter 32 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1106

kowa ya dauki kwalbar alcohol aka fara kaiwa Baki,....




___________?&


Abangaren ruky kuwa Batasan meke furuwa ba,Dan jiya baccin ta tasha sosai,sai Yanxu ma ta sauko kasa cikin shirin fita aiki,Dan karfe Tara da mintuna yanxu,tana sakkowa nema ta tadda Mamah tana kallan labaran data Saba kalla duk wayewar garin duniya, bayan ta gama saukowa ne take ganin qarshen labaran,ananne ma tasan meke furuwa, Kuma mama haryau Batasan su Hajiya SA'A sun kawo lefe ba Dan ita jiran xuwan Alhaji sunusi take dayake cewa zai Aurawa lateef ruky,jiran xuwan ranar take Amma shiru haryanxu, Kuma shima hanaf bai fada mata ba,tun Yana jiran yaga ta masa maganar hardai yaji shiru,....



Xaman da Ruky tai kusa da ita tana gaidata Hadi da murmushi yasa mama juyowa ta xuba mata ido tana ansa mata,akuma lokacin aka gama labaran, mamah tace lpy lau anfito kenan Ruky tace eh,mamah tace kinci abinci, ruky ta girgixa mata kai,sai Kuma tace yanxu xanci,ta mike tai hanyar dining din, Bayan ruky ta xauna, mamah dubeta tace,Ashe wannan yaran Ahmad ya fara xuwa aikin kenan, yanxu naga an nuno shi awannan qauyan da aka kaiwa hari jiya,Kuma naga Shareef ma atare dashi....


Ruky tace waye Kuma haka mamah,mamah ta harari Ruky tace bansaniba, Ahmad mana oganku,gashi ankai hari Wani qauye jiya,haryaje take alokacin da abin ya faru batajira cewar ruky ba ta cigaba da fadin lallai wannan yaron,ba karamin jajirtaccen jami'i bane,nidai wlh rabona danaga ankai hari,anje alokacin daya dace ,Kuma Wani babban jami'i yaje aranar ko Kuma ya aika wlh harna manta tun lokacin da aka dauke shi Ahmad din aka fitar dashi daga qasar sa, ta qarfi da yaji sbd kawai Yana Irin wannan jajircewar akan aikinsa,sai dawowar nan tasa,a gsky irinsu ake so, sai gashi Kuma Allah ya Saka Masa yadawo kasarsa alokacin da ake bukatar sa, lallai Allah Mai ikone,Allah ubangiji ya dafa masa,su Kuma masu wannan aikin ta'addancin Allah ya tona musu asiri...


Ruky itakan batama San sunanshi haka ba,Dan ita da AA Arab ta sanshi, shima Kuma abakin Hanan takeji wacce take yawan Bata labarin sa,ganin mamah na kallanta taji me xata fada tace da Mamah uhnmn,kawai Dan ita Batasan Kuma me zatace ba,nan dai ta gama cin abincin ta ,taiwa mamah sallama ta fita,Dan har lokacin mamah fadar kirkin AA Arab kawai take,.....







07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD





*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA)=?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season one ep 4?? 0??



___________?&


*Bayan kwana biyu*


Ayau ne ya kama xa'ayi xaman kotu,inda kotun ta cika makil da mutane,bayan ansaurari qara da dama tasu ruky itace ta qarshe,Dan su ruky tun tuni suna kotun Wanda yanxu dai jiran su lateef kawai ake su kadaine Basu xoba,babu dadewa Kuma saiga su sun iso harda Alhaji sunusi, Wanda fuskarsa take sake, domin Gani yake ayau komai zaixo qarshe Dan ruky saitasan cewa yafi qarfinta,bayan sun xauna a mazauninsu Babu dadewa aka fara karanto qara kafin daga bisani a bukaci ganin shafa da lateef agaban kotu,....



Lauyan shafa ya mike tareda gabatar da kansa amatsayin sa na lauyan Wanda ke qara,ya nemi ixnin yiwa lateef tambayoyi,babu musu alkali ya bashi dama,ya sunkuyar da kai alamar godiya ya qarasa gaban lateef Wanda ke tsaye Yana Wani ciccin magani, barrister shamsu ya dubi lateef yace malam lateef ka dubi shafa'atu dakyau ya fada yana nuna shafa, yarinya ce qarama, marainiya Batada uba gashi basuda qarfi wacce batakai munxalin da xa'a mata wannan danyan aikin ba, Amma lateef baka duba wadannan abubuwan ba,ka katashi ka wulakanta rayuwar ta, ka keta mata haddi ta qarfi ta tsiya,Kuma sbd Rashin imani Irin naka kace wai ba kai bane,Kuma duk Irin hanyoyi da mukabi na bincike ya nuna mana dai kaidin nedai ba waniba,lateef ya dinga masa Wani kallo, barrister Salman ya mike cikin fushi yace objection my lot, barrister shamsu Yana wuce iyaka Yana kokarin lakawa lateef sharrin da bashi shi ya aikata ba,bashi da masaniya akai,kawai kokarin Dora masa laifi yake,sbd haka Ina Neman Alfarmar wannan kotu Mai adalci data hana barrister shamsu wuce iyaka, alkali ya kalli barrister shamsu yace akiyaye, barrister shamsu yay murmushi yace nagode ya Mai girma Mai Shari'a,....



Barrister shamsu ya dubi lateef har lokacin da murmushi a fuskarsa yace malam lateef inaso ka sani cewa munsan komai gara ka ansa laifin ka cikin ruwan sanyi,ya dubi alkali yace ya Mai girma Mai Shari'a inason wannan kotu Mai adalci data dubi Irin hujjojin da muka gabatar a gaban kotu tundaga kan recording da Kuma vedios din da baba lami wato mahaifiyar shafa xataje gidan radio ta shigar na GADANGA TV & RADIO, Wanda malam ibrahim Khalil shine Wanda ya saurari hira da ita a wannan lokacin data je shigar da kokenta na ataimaka abiwa shafa'atu kadinta, sbd haka inaso wannan kotu Mai adalci data bani dama na gabatar da hujjata ta farko Danjaridan wato malam ibrahim Khalil,babu musu alkali ya Bada goyon, baya,....



Khalil ya fito kotun,kallo saiya koma kansa yuuu, Alhaji sunusi gabadaya saiya rikice Jin wannan AL'amarin kamar a film yaushe Hakan ta faru,jikinsa saiyay sanyi,Jin wannan hujjoji da aka gabatar,ya dubi ibrahim Khalil Wanda ko a'a jikinsa ya juya ya kalli ruky wacce ta sakar masa murmushi,take ya cije lebensa,saiya juya Jin Khalil ya fara Bada labarin yadda Babar shafa taxo gidan radion su da Kuma ta bayyana komai ,har xuwa lokacin da ruky ta shiga Shari'ar,bayan ya gama akace yaje ya zauna ,sai Kuma aka bukaci ganin Ruky,.....



Itama ruky ta fito ta fara Bada labarin yadda suka Sha gwagwar maya, kafin su San lateef ne ya aikata wannan laifin har xuwa lokacin da aka kamashi aka kaishi heardquater da yadda Alhaji sunusi yaje yay belinsa, Kuma aka bashi Batare da anyi bincike ba,haba sai kotu ta dauki hayaniya da surutu kowa na fadar albarkacin bakinsa,wasu suce Allah Wadai wasu Kuma suce Allah ya kyauta da kyar aka samu sukayi shiru, ruky ta kalli lateef Wanda ya xuba mata ido kamar xasu zazzago tace lateef Kaine kai wannan aikin ba waniba,Kuma kaima kasan ka aikata din,sbd haka karka bawa kotu wahala gara kawai ka Fadi GSKY, lateef ya Kalli Ruky cikin rawar murya wacce kamar xaiyi kuka yace, Rukayya yanxu kece kike kokarin ganin bayanan, yanxu kema sharrin da zaki kullamin kenan kinmanta AURENAH Dake Nanda jibi ne,ruky ta Maka masa harara ta koma wurin xamanta da aka umarce ta data koma,



Alhaji sunusi ya dafe kansa,sai Kuma ya cire hular kansa Yana shafa sankonsa, Wanda ya fito tarwal,Yana tunanin kamar fa ba lallai suyi nasara ba ga shima kansa barrister Salman yayi shiru Yana sauraran komai, ganin ba'a bashi damar magana har barrister shamsu ya gama fito da shaidunsa, Amma fa duk da haka bazai sare ba ,zai jira yaji wake da nasara,ya tabbatar bazasu taba faduwa qasa ba, tunda barrister Salman ya fada masa Kuma Shima barrister Salman ya Karanto nasa hujjojin masu qarfi,Kuma yasan Bai gama ba har lokacin, barrister shamsu ya dubi alkali yace ya Mai girma Mai Shari'a inaso wannan kotu Mai adalci data dubi Irin hujjojin da muka bayar,ko iya wannan yaci ace an yadda cewa lateef shiya aikata wannan laifin da ake tuhumarsa dashi,.....



Inaso wannan kotu Mai adalci data dubi Irin xalincin da akayiwa shafa'atu Wanda yanxu haka tana kwance agadon asibiti,na private qarqashin kulawar likitoci, Wanda har yau ankasa gano Wani Irin cuta take fama da ita,Kuma sai anmata aiki tukunna, aikinma daxa'a mata kila wa qalane, ma'ana ba'a tabbatar da xa'ayi narasa ne ko baza ayiba,sbd haka Ina rokon wannan kotu Mai adalci data duba wadannan hujjojin da muka gabatar agabanta data biwa shafa hakkinta akan xalincin da aka mata nagode ya Mai girma Mai Shari'a,daga haka ya koma mazauninsa ya zauna,.....



Alkali ya dubi barrister Salman yace ko lauyan Wanda ake qara Yana da abin cewa, barrister Salman ya mike cikin girmamawa Yana gyara xaman rigar jikinsa,yace eh inada shi ya Mai girma Mai Shari'a, saikuma ya fito ya qaraso wajen ,shafa, wacce ta sunkuyar da kai hawaye nata xuba daga idanuwanta,yace shafa'atu sidi, inaso kiyi tunini da Kyau na wannan sharrin da kika kullawa lateef,ta yiyu Wani me kama dashi ne,yayi miki, Amma bashi ba, Tayaya lateef Wanda ubansa babban Dan siyasa ne a qasa bama jihar Kaduna ba,ace duk cikakkun matan da suke cikin garin Kaduna ya rasa da wa zaiyi mu'amala saidake wacce ke can wajen garin Kaduna,na tabbatar da cewa da auran qauye aka masa da zai iya haifar yake,, yarinya Dake qarama, Amma har ki iya yiwa babban saurayi Irin lateef wannan sharrin,idanma biyanki akai danki Bata Mai suna,ai ba haka ya kamata kiyiba, barrister shamsu ya mike yace objection my lot ya kamata barrister Salman ya kiyaye Irin tambayoyin da xaiyiwa shafa'atu Wanda sun Saba Shari'ar aiki, alkali yace akiyaye barrister Salman, barrister Salman, ya sunkuyar da kai yace nagode ya Mai girma Mai Shari'a,....



sai Kuma ya cigaba da cewa,shin kinada shaidar Gani da ido ma'ana alokacin da kikace yana xuwa har unguwar da kike yake daukarki xuwa gidansa,shin akwai Wanda ya taba ganinki tareda dashi,alokacin dayake daukarki amotar,ko kuma akwai Wanda kika tava fadawa haka, shafa ta girgixa kai hawaye na xubowa idan ta, cikin muryar kuka tace banida shaida sai Allah, barrister Salman yay murmushi yace oh Ashe Kinsan da Allah Amma kike yiwa lateef sharri, Shima Allah shine shaidansa,sai Kuma yace to Kinagani,tunda bakida shaidar Gani da ido,ai kinsan cewa bakida kwakkwaran da Lili,ya dubi alkali yace ya Mai girma Mai Shari'a, inaso wannan kotu Mai adalci data dubi qagen da sharrin da akayiwa lateef, tunda ba'a samu shaidar Gani da ido ba,da ayi watsi da wannan qarar Kuma abiwa lateef hakkinsa na sharrin da akayi masa,Ina Kuma rokon wannan kotu Mai adalci data duba da Irin hujjojin da muka kawo da duba,ayi nazari akai a biwa Lateef kadin sharrin da aka masa nagode ya Mai girma Mai Shari'a,daga haka ya koma ya zauna,haba sai alokacin Alhaji sunusi yaji sanyi aransa Jin cewa xasu Yi nasara,Saida alkali yayi shiru na tsawan second talatin sannan ya dago yace xa'a yanke hukuncin nan mako me xuwa,daga haka ya mike, kowa ya mike, shafa tana kokarin fitowa daga wurin baba lami ta kamota, suka fito, lateef Shima ya fita yay wurin Alhaji sunusi suka fito daga kotun ....



Bayan su ruky sun Fita direct mota suka nufa fuskokinsu dauke da farin ciki duk da Basu tabbatar dasu ne masu gsky ko akasin haka ba, Amma suna saran in Sha Allah sune suke da nasara, bisa ga hujjojin da suka gabatar agaban kotu, Basu bi takan Yan jaridun Dake San tattaunawa dasu ba,bayan sun shiga motocinsu haka suka fita daga cikin kotun gaba Daya, Alhaji sunusi kuwa shi baxai ce ,ga Abinda yake jiba , Dadi ko akasin haka, Amma yanaji aransa kamar baxa suyi nasara ba,Dan haka akwai matakin da xai dauka kafin Adawo Wani satin,Dan wlh Yana ji aransa cewa ba lallai suyi nasara ba, Amma ya riga Daya kudurta hukuncin da xai aiwatar kafinnan kafin Wani satin, haka barrister Salman yaxo ya kwantar musu da hankalin cewa in Sha Allah suke da nasara,Dan Alhaji sunusi ba karamin kudi ya kashe ba,akan Shari'ar nan,Dan baya so ace basuyi nasara ba,Dan wlh Siyasarsa kawai yake dubawa ba Wani abun ba,haka sukayi sallama da barrister Salman ya tafi shi Kuma suka shiga mota shida lateef Wanda gabadaya hankalinsa ya tashi Dan Bai yarda da maganar da barrister Salman yayi musu ba,Dan wlh Gani yake kamar baxa suyi nasara ba,haka driver yaja suka tafi, shikuma Alhaji sunusi Yana kissima Irin hukuncin daya yanke xai aiwatar kawai, Kuma Yana mamakin dama lateef Yana da gida ahayin rigasa Amma shine Bai saniba,,.....



__________?&


Washe gari da safe haka ruky tai shirin fita aiki kamar kullum, Kuma har lokacin mamah Batasan me ruky take aikatawa ba,bayan taiwa su mamah sallama da baba hasiya,ta fita daga falon,ta nufi parking lot ta dauki motar ta, ahanya ruky tana tuki gefe Daya Kuma suna waya da Khalil,Kuma duk hirar kan zaman kotun da akai jiyane,da yadda suke tunanin wake da nasara atsakanin su da Alhaji sunusi, kawai Khalil ya jefowa ruky wannan tambayar,Dan tun jiya ta dameshi yanaso yaji gskyr maganar,nan dai yay karfin halin cewa, dama ranki dade lateef dama shi xaki Aura,ruky tai murmushi har Khalil Yana Jin sautinsa tace Meka Gani yace naji yayi Wani furuci jiya a kotu wai shine wanda zaki aura, ruky tai murmushi tana kokarin Shan kwana tace ni bansan xancen ba, kawai fada yay,badan Khalil ya yadda ba yace shikenan, ranki dade,yanxu dai ki kwantar da hankalinki in Sha Allah Muke da nasara daga yadda naga Shari'ar nan jiya ta dau zafi ,ga mutane suna ta xagin lateef da Kuma yadda alkali ya nuna reaction dinsa kan hujjojin da muke ta badawa nasan cewa in Sha Allah mu xamu zamuyi nasara,.....



Ruky ta sauke numfashi tace Allah yasa Khalil,wlh burinah kawai shine abiwa shafa'atu kadinta,idan aka hukunta laleef tofa anan ne,?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? kowa zai shiga hankalinsa musamman masu aikata barna irin tasa, Khalil yace wannan haka yake ranki dade, ruky tace to kaga Allah dai yasa mudace, Khalil yace Ameen daga haka sukai sallama,bayan ruky ta Isa wajen aiki, yanxu haka tana gaban system dinta, tana aiki saiga Hanan ta shigo , da sallama abakinta,kamar wacce aka jefo,ruky ta ansa mata tareda dagowa ta dubeta,Hanan tai murmushi tace kinganni koh,wlh xuwa nai takas naxo Dan na gaida AA ARAB,so nake muje ki rakani,....


Ruky tai mata Wani kallo tace Amma wlh Hanan bakida hankali , yanxu government house din kika baro,Kuma kika bar aikinki kika taho nan Dan kawai xuwa kigaida Wani AA Arab,Hanan tana kokarin xama tace ke nagama aikina malama yau babu inda xamuje ,na tashi ganinai Dana tafi gida Kuma alhalin babu abinda xanyi yasa nace bari naxo yau dai ki rakani na gaidashi har office dinsa ta qarasa fada tana murmushi,....



Ruky tai tsaki tace wlh Babu inda xani,Hanan ta Bata rai tace Dan Allah ruky, ruky tace kedai da Kika ga xaki iya sai kije Amma nikan baxani ya wulakanta tani ba,Dan ban shirya wannan wulakancin ba,Hanan tace wlh kema Kinsan baiyi kala da Wanda xai wulakanta mutum ba, ruky tace to ai agoshi ake Gani koh,Hanan ta kamo hannunta ,ruky ta hade Rai tace wlh kinji na rantse baxa niba,kedai Kije, Hanan ta mike tace danma kinsamu Ina lallabaki da rokonki , karkije din ai inada qafa ba gurguwa bace, ruky tai murmushi tace kinsan da Hakan shine kika debo kafa waina rakaki, Hanan tai Banxa ta kyaleta ta nufi kofar fita,ta fita daga office din Ruky , ruky ta bita da kallon mamaki,.....



Bayan Hanan ta bar office din Ruky,haka ta Dake tai hanyar office din AA Arab dukda gabanta na faduwa Dan Batasan Kuma me zatace masa ba,haka ta isa office din nasa Wanda yake gari guda acikin heardquater Dan yafi ko Ina girma da haduwa danshi office din ma kansa falor biyune,ga police ta ko Ina,dayake itama police ce Kuma sun Santa yasa babu Wanda ya hanata xuwa office din nasa,bayan ta tambayi inane da ta Kuma tambayar yananan, sukace mata eh Yana ciki, bayan tai knocking sau biyu AA Arab Dake zaune bisa kujerar sa me juyawa, idansa kan screen din laptop dinshi Yana latsawa,tashiga da sallama abakinta,Jin muryar mace yasashi dan dagowa daga abinda yake ya Kalleta, tareda ansa mata....


Ganinta da yay da uniform, ya Gane cewa itama police ce,Hakan yasa ya maida kansa ga screen din laptop dinshi Yana jiran Jin me taxoyi,kodai matan da suka Saba xuwa masane any how,ya cigava da aikinsa,Hanan Dake tsaye daga bakin kofar ita Bata shigo ba ita Bata koma ba tana nan dai tsaye ga gabanta sai faduwa yakeyi,tai kundun bala cewa sir good afternoon,ya Dan dago yace afternoon, saikuma tai shiru,ganin tai shiru Kuma taki shigowa yace and then what,ta Dan dubur burce tace dama sir xuwa nai na gaida kai,ya kalleta da mamaki sai Kuma yace thanks, Hanan ta juya zata fita yace Hy please,tadan juyo,ta kalleshi yace kece wacce ranar muna meeting kuka shigo alet koh,Hanan tai murmushi tace yes sir but we are sorry, yace no zancen sorry aiya wuce,cikin Jin dadin maganar da AA Arab ya mata tace sir dama xuwa nai kawai na gaisheka,AA Arab ya qara xuva mata ido da mamakin maganarta,sai Kuma yace thanks for visit me,Hanan tace Nike da godiya sir bari na tafi gida,ya Kalli agogon hannunsa yace antashi ne, tace sir ai a government house ni nake aiki , kawai naxo ne danna gaidaka,nace da qawata wacce tareda da ita mukayi lattin ranar Dake aiki ananta rakani na gaidaka shine tace min aiki take naje kawai,AA Arab yace ok kin kyauta, Amma meye sunan ki,cikin Jin dadi Hanan, tace sunana Hanan yace nagode Hanan,daga haka ta Fita daga office din direct office din ruky tai danta Bata labarin yadda sukai da AA Arab, tana mamakin Ashe haka yake da saukin kai da Kuma kirki,shiko AA Arab mamakinta kawai yay, wai taxo gaidashi, dan dai kawai shi wulakanci baya cikin tsarinsane, shiyasa ya karbeta hannu biyu,Kuma ba yau ya saba da Irin haka ba.....









07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=r_c





*_____JAMI'AR TSARO _____*


*____THE WOMEN POLICE ____*




*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*




*____( MRS SARAKIES)____*



*=?1? QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA) =?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season One ep 4?? 1??




___________?&



Ruky ce kwance akan gadonta wajen karfe 9 na dare, bayan ta gama chatting da Hanan wacce tunda daxu a office dinta Data dawo daga office din AA Arab,ta dameta da xancensa,wai dama haka yake da kirki,ai Bata ga Irin tarbar Daya mata ba, meye meye ,itadai ruky jinta kawai take, batace komai ba,kuma shine yanxu ma ganinta a online shine ta biyota nan dinma tana mata xancensa, tsaki tai ta kashe data ta sauka daga online dinma gabadaya, har xata ajiye wayar saikuma ta fasa tashiga call history,tai darling number Khalil, Amma bata tafiya,Dan dazu da sukai waya yake ce mata akwai maganar da xasuyi xai kirata da daddare,ganin Bai kirata ba yasata deciding kiransa, Saidai, Kuma gashi Bata tafiya,....


Saikuma ta kunna data tahau online da nufin anjima koxata sameshi, saidai tana hawa online din,Kiran lateef ya shigo wayarta, ta xubawa screen


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login