Showing 249001 words to 252000 words out of 278032 words

Chapter 84 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1055

kafin tace.


"Anty! Kinga yadda kikai kyau kuwa? wallahi kinyi kyau sosai wazai ganki yace kin haifi Yara har biyu".ta fad'a tana murmushi.


Anty mufeeda ta Bud'e ido ta saki murmushi kafin tace.


"A'a bansan tsokana fa Hanan".ta fad'a tanayin fari da ido.


Hanan ta Bud'e ido kafin tace. "Wallahi anty Babu ba tun tsokana da Gaske nake bakiga yadda kikai kyau ba ko sis saudat?", ta fad'a tana kallan saudat.


Saudat ta saki murmushi kafin tace.


Ai Saida na fad'a mata tun sanda na gama kwalliyar, d'aukarta wasa nake mata wallahi mom mimie kinyi kyau sosai Kuma kowa ya ganki saiya yaba sai dai mak'iyi",ta fad'a tana kallan ta .


Anty mufeeda tai murmushi tace .


"To godiya nike Hajiyan kwalliya tare da matar k'anin"ta fad'a tana kallan Hanan, hanan tai murmushi tana rufe fuskarta da tafukan Hannunta alamun kunya,anty mufeeda ta kalleta kafin tace.


" Yauwa Hanan auta ta fito daga wankan kuwa?".ta fad'a tana kallan Hanan.


Hanan ta Bud'e fuskarta tana Jin jina mata kai kafin tace.


"Eh ta fito shiyasa nazo ma ayimin kwalliyata kafin sis saudat taje tai mata nata ",anty mufeeda ta Jin jina kai kafin tace .


"Shikenan ki zauna ai miki bari naje na sameta", Hanan tace ."shikenan anty",daga haka anty mufeeda tabar d'akin.Hanan ta zauna kan kujerar dake gaban saudat Wacce already Dama ita take jira nan da nan suka fara....


Saudat ta sakawa ruky wata tsadaddiyar sark'a silver color bayan ta gama mata make up d'in,Hanan tasa mata takalminta Wanda ya kasance highheel kalar silver color shima da Kuma Pos d'in ta itama kalar silver,Hanan ta d'ago kai tana kallan Ruky yadda tai more than kyau,tana Yaba baiwa Irin ta ubangiji da wannan halittar da Yay tana kuma kallan shigar ta at the same time,sanye take cikin Wani farin rantsatstsan yadi white color, gabad'aya jikinsa stones ne silver color D'inkin doguwar riga wacce ta kasance fitted gown Amma ta baje daga k'asa tana Jan k'asa,ya subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangijin halittu,Mai kowa Mai komai,Wanda bashi da abokin tarayya haka kawai take ambata acikin ranta. gabad'aya wanda suka shigo d'akin nan kowa kallan ruky kawai yake Yana Jin jina Irin kyan da tai da Kuma tsaddan sitirar jikinta, saudat ta shiga Yi mata pictures da videos acikin wayarta tanayi k'awayensu ma sunayi dama wasu daga cikin 'yan uwansu wanda sukazo bikin suna tai mata pictures da Kuma videos,bakinsu sai ambatan Masha Allah kawai yakeyi suna yi suka shiga d'orawa ashafukansu na sada zumunta,anty mufeeda ce tashigo tana kallan su tace.

" ya isa haka lokaci fa na tafiya ga motocin har sun zo saboda haka kowa ya fito duk Wanda zashi yaje ya Shiga mota suna can suna jiranku",ta fad'a tana kallan su ,babu musu suka fara fita D'aya bayan D'aya sai ya rage daga anty mufeeda sai Hanan wacce tace mata ta tsaya su fito da ruky.



Saida aka gama kwashe duk Wanda zasuje sannan aka fito da amaryar an rufe mata fuska ta Wani farin net Wanda yasha stone shima sai Wani hasken tartsatsine kawai yake fita daga jikinsa, Hanan ta Bud'e wata rantsatstsiyar Mota bak'a inbanda k'yalli Babu abinda take keda ganin motar Kinsan sabouwa ce fill malam,Dan zai iya yiwuwa ma ayau aka tab'a fito da ita ko Kuma an tab'a hawanta Amma bazaifi sau biyu ba,saboda yadda take Wani k'yalli kamar me ,hanan ta kama hannun ta ta tai Maka mata ta shiga ciki Saida taga ta zauna kafin ta juya itama ta nufi motar mijinta Dan tare zasu tafi .


K'amshin turaransa ta faraji kafin ta farga da cewar Ashe yana cikin motar ,Bata yarda ta Kalli direction d'in da yake ba saboda yadda takejin Wani Irin tsoro da fargaba na shigarta,ta takure jikinta a jikin motar,shidai AA Arab tunda ta shigo idonsa yake kanta, Yana gannin yadda tai masa bala'in kyau,Yana kuma Jin yadda jikinta yake tashin k'amshi, ya sauke numfashi ganin tak'i juyowa ta kalleshi yasa hannunsa ya rik'o hannunta Yana kallan lallen hannunta Wanda yay mata bala'in kyau,kafin ya d'ago yana Kallan afuskarta ,Bata juyo ba iyaka kawai da jikinta ya d'auki rawa ,yay k'asa da murya yace .


"Look at me fiancee!", ya fad'a Yana lek'en fuskar ta ,ta runtse idonta da kyau har lokacin Bata yarda ta juyo ba,ya K'ara k'asa da murya yace.

"Please"yaja please d'in da Wani Irin salo,da k'yar ta iya daurewa ta Dan juyo kad'an tana kallan shi,sanye yake shima cikin wasu fararen suites rigar sa fara k'al sai Wanda jikinsa Daya kasance Bak'i kansa Yasha gyara sai Wani shek'i yakeyi duk acikin seconds tai masa wanna kallon kafin ta sauke kanta k'asa ganin yadda ya k'ura mata ido Yana mata wani Irin kallo Mai kashe jiki, yay k'asa da murya wacce iya ita kad'ai ce Dake kusa dashi zataji yace.


"U look more beautiful"ya fad'a Yana murza Hannun ta dake cikin nashi , Ruky ta runtse idonta Amma Batai magana ba ,yace cikin deep voice d'insa" please look at me fiancee!",ta d'ago ta kalleshi.ganin tak'i magana yasa yace.


"Please say something mana fiancee!", ya fad'a da wata iriyar murya.ta juyo tana kallon sa ganin ya sakar mata murmushi yasa itama ta Maida masa da Martanin murmushin da yay mata ya ilaihi haka ya ambata acikin ransa ganin yadda tsantsar kyawunta ya fito,ganin tana kallan ta yasa tace .


"Thank you ",ya Bud'e idonsa still Yana kallan ta yace.

"Do you know you are very beautiful",tai murmushi Amma batace komai ba,ya cigaba da murza Hannun tai yunk'urin k'wacewa tareda da cewa.

"Stop it please ",

"Ya Bud'e ido yace why?",

Ta tura baki gaba tace.

"I don't want it",

Yay Wani killer smile kafin yace .

"Even me I wanted",ta Bat'a Rai tace .

"Akwai driver fa",

???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Ya tab'e Baki kafin yace.


"So"tai shiru ta juyar da kanta gefe tana ta mutsu mutsu da hannun tana San k'wacewa Amma kuma ya hana Hakan, motar tai shiru har suka isa wurin ,driver yay parking motar a k'ofar Wani babban hole inda anan ne za'ayi dinner, motocine Dan K'ara Dan K'ara suketa parking awajen mutane sai kaiwa da komowa sukeyi kamar ba dare ba .


Ana noticing motar Amarya da ango ta iso take MC ya fara sanarwa acikin hole d'in cewar ango da amarya sun iso ,nan aka fara gyara zama ana jiran shigowar ango da Amarya ,dama already k'awayen amarya da abokan angon suna nan tsaitsaye bakin home d'in suna jiran amarya da angon su k'araso Dan su zasu shiga dasu cikin hole d'in,Hanan ta k'arasa har gaban motar ita da some k'awayen su Wanda zasu shigo da amarya cikin ankonsa material ne kalar Bak'i sai wasu friends d'in AA Arab Wanda sukai school dasu tare da Kuma abokanan aikinsa Wanda sukai aiki dasu da tun tuni kuma suna mutunci dasu sosai saboda zasuyi sword crossing shiyasa ma harda yaran aikinsa acikinsu duk sukazo.


Suka k'arasa,kafin su Isa har AA Arab ya Bud'e motar ya fito da amaryarsa,suna tsaye jikin motar,bayan sun k'araso sukai two line maza a D'aya side d'in Matanma haka ya zamo ango da amarya suna tsakiyar su ,haka suka jera suka shiga cikin hole d'in Hanan amarya na sark'e cikin na ango ,suna fara shiga DJ ya saki wata sassanyar wak'a ,wacce take ratsa zuciyar masoya,ga wasu Barbies girls su uku a gabansu mimie da yaran cousins d'insu ruky hannuwansu rik'e da Wani box sai watsa flowers suke abun abun burgewa ahaka aka Rakasu har wurin zamansu,Kafin abokan ango su koma wurin zamansu, k'awayen amarya ma haka suka koma mazaunin su. mazaunin kowa daban na Maza daban na mata ma daban ,na iyaye daban na 'Yan mata ma daban na yayu ma daban ,Aciki kuwa harda dangin ango,ummi ma tazo da wasu daga cikin goggonin AA Arab da yayunsa ,Irin su ukty Aysha da ukty hameeda da su ameeera da zuhra ,ke kaf dai 'Yan uwansa sunzo wurin nan suma sai farin ciki suke tare da Yaba kyan da amarya tai,ko Ina ansanya lemuka da ruwa da abince akan table d'in dake gabansu ,can na hango Wani table na musamman Wanda yasha decorations.Wa zan Gani 'yan JAMI'AR TSARO fans na hango irinsu ,bint isah da mommy's girl tare da ummulkhair da fabdulkadir Baki yak'i rufuwa,sai kwasar shinkafar da aka kawo musu suke ko Irin Jan ajin nan Babu=??bare su jira a fara dinner da sword crossing d'in.


Sai table d'in Dake gefensu na hango ikleema Adam,da Nana Asama'u da Zainab kabeer da saudat Abba sani harma da Asama'u kabeer sukan Basu tab'a abinda aka ajiye musu ba kallan AA Arab kawai Suke da ruky yadda AA Arab yake Wani bin ruky da Wani kallon soyayya itako sai sunkuyar da kanta take k'asa tak'i kallansa, Nana Asama'u ta jinjina kai kafin tace afili "lallai wannan alamari ya girmi kaina, saudat sani umar tace uhmmm,Dan tama kasa furta Komai saboda mamaki,dama sauran da ban Fad'i Sunan suba Sukuma sai kokowa suke da lemon jarka Baki yak'i rufuwa =??ana ta k'ok'arin cusawa acikin Jaka.Anty Rabi'a dai tana zaune tai shiru tana kallan iKon Allah =??.


Nikan Ina gefe rik'e da Alk'alamina Ina d'aukar rahoto saiga bint isah ta taso daga inda ta kasa zama tazo ta sameni tai k'asa da murya tace .


"wai anty naja! Gaskiya na amince zan Basu mubeena ta tai musu zaman d'aki Irin haka wannan liyafa da muke kwasa", Niko nai murmushi nace" ai suncema sun hak'uri zasuyi zamansu haka",nanfa hankalin bint isah ya tashi tace a gaskiya na taimaka na tambayar mata su nace sai dai taje da kanta shine fa ta tafi fuu da zumar idan antashi zataje ta samesu Dan bazata bari kanta yay murfi ba=??.


Haka aka fara shagalin biki kafin asa amarya da ango su fito za'ayi sword crossing,suka fito tsakiyar hole d'in, abokan aikinsa saukai two line cikin shigar uniform su duka sunyi bala'in kyau, mutane biyune suka fito suka k'arasa har gabansu suka sarawa AA Arab da ruky sannan suka Mik'a masa hannu sukai musabaha tare da gaisuwa,sannan suka Mik'a musu wasu flowers da wasu boxes Wanda akai raping d'insu,Kafin naga sun koma Sun k'ame a inda suke tsaye , ahaka kowa Saida ya fito yay gaisuwa kafin agama suka koma mazaunin su abin dai abin ban sha'awa,mc ya K'ara K'iran amarya da ango akan Yana San ganinsu a takaiyar fili Babu musu suka fito ruky duk ta gaji sai Wani tura Baki take gaba .


Bayan sun fito MC ya k'ira 'yan uwan amarya akan su fito su nuna farin cikin su, suka fito aka Saka musu Wak'a Nan fa suka fara Yi musu Karin kud'i kamar ruwa anty mufeeda ta fito tai musu Karin dollars,ya hanaf ma ya fito shida Hanan sai ya Tahir da amaryarsa Mai suna Khadija, sukai musu Karin 'yan dubu dubu,ahaka dangin amarya da k'awayen ta suka fito suna tai musu Kari,sai da 'yan uwan amarya suka gama tas kafin mc ya k'ira Dangin ango suma gabad'aya suka fito suka fara musu Karin kud'i ukty Aisha itama dollars ta Kara musu ,sai ummi da itama ta Kara musu 'yan dubu dubu ahaka suma Dangin ango suka fara fitowa suka dinga Kara musu kud'i kafin Kuma su koma su zauna aka umarci amarya da ango akan suma su koma su zauna ,haka aka cigaba da gudanar da shagali cikin kwanciyar hankali da nutsuwa har aka gama basu suka tashi ba sai after 11 aka tashi.....


Haka mutane suka fara fita Daga hole d'in dama already motacin suna nan ,nan kowa ya shishshiga mota Aka fara Maida kowa gidanjesu wanda kuma za'a kaisu gidannsu amarya suma aka tafi dasu,idan Allah ya kaimu gobe Friday Kuma za'ayi mother's events Wanda ya kasance na mamah .





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*___THE WOMEN POLICE ___*



*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*



*____(MRS SARAKIES =؋?)____*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 9?? 9??



___________?&


Ranar Friday da yamma misalin k'arfe biyar da Rabi na Ranar ,manya manyan matane masu ji da kansu na hango su zaz zaune kan kujeru gaban wasu tables da aka jajjera a harabar gidan AIG umar MaiTama,kowacce cikin shiga ta Alfarma take,sunsha sutura bana k'ana nan kud'ad'e ba,daga gefe kuma sauran 'yan bikine suma kan kujerun gaban table d'in,akan tables d'in ko wanne an D'ora musu lemuka da ruwa da abinci akan ko Wani table Dake gaban matan,wajen k'awayen mamah daban hakama wajen 'yan uwa daban an tsara Abin dai very attractive, Anty mufeeda na hango ita da Hanan cikin tsadaddun sutura sai kaiwa da komowa suke suna ta k'ok'arin ganin kowa ya zama compotable awajen ,Saida suka tabbatar da kowa anbashi wurin zama da Kuma ruwa da abinci kafin naga sun bi ta wata k'ofa sun shiga falon gidan...


Yayar mamah Hajiya Maryam na hango ta rik'o hannun amarya ta D'aya site d'in itada wata cousin sister d'in su mamah suka fito da amarya cikin lullub'i Tasha Wani blue black d'in less Mai adon stones da ratsin maroon,kanta yasa lullub'i da Wani ubansun mayafi Mai shegen tsada hannayenta kowanne sunsha awarwaren gold da zobunan gold duka hannu biyun,suna rik'e da duka hannayenta kowa ya kamo hannunta D'aya suka k'araso da ita har zuwa wurin zamanta da aka tanada domin ita,bayan sun zaunarta suka koma wurin zamansu Suma suka zauna...


Wannan mother's events d'in ya ban banta da Wanda akeyi na wannan zamanin, mai makon a d'auko Mai DJ ayi rawa a'a ,ita mamah wata malama ta d'auko wacce zataiwa amarya wa'azi dama wad'anda suka zo su amfana,bayan anzaunar da Amarya malama ta mik'e ta fito tsakiyar filin ta tsaya ta fara gabatar da kanta kafin ta fara yin nasihohi Masu ratsa zuciya ta fara Karanto hakk'ok'in mace akan mijinta da Kuma hakk'ok'in miji akan matar sa wurin nan ya d'auki shiru idan kacire gwarancin Yara da sukeyi, su anty mufeeda da Hanan dama kowa da kowa sun nutsu sai Jin wannan wa'azi sukeyi suna K'ara yiwa Allah kirari a zuciyar su ,itadai ruky tunda ta sunkuyar da kanta Bata yarda ta d'ago ba kuka kawai take tana daga cikin mayafinta ,kowa agunnan Saida zuciyar sa ta raunana saboda wa'azin da akayi,Dan wa'azi ne Mai Ratsa zuciyar duk wani Mai hankali,bayan Malama ta tsagaita da wa'azin ta umarci mamah da itama taiwa amarya tata na nasihar dama sauran yaran Dake wajen suma su amfana.


Babu musu mama ta fito tai sallama tare da yiwa autarta nasiha wacce ko Wacce uwa ya kamata taiwa 'ya'yanta, bayan ta gama tai mata fatan alkhairi kafin ta k'arasa gunta ta Bud'e mayafinta taga kuka kawai ruky takeyi harda Jan zuciya hakan yasa zuciyar mamah itama ta Karaya ta kamo hannun ruky ta mik'ar da ita tsaye kafin tai Wani Abu ruky ta fad'a jikinta ta saki Wani marayan kuka Mai ratsa zuciya,take Mamah ta rungumeta tana shafa bayan ta alamar rarrashi tana k'ok'arin ganin itama ta Hana hawayen Ida nuwanta saukowa Amma Kuma Ina Hakan ya gagara,babu Wanda baiji wani rauni azuciyar saba ,sun D'an Dad'e ahaka kafin mamah tai k'arfin halin b'an b'are ruky daga jikinta tana zaunar da ita a wurin zamanta itadai ruky kuka kawai take Dan Bata fasa ba, Mamah ta koma wurin zamanta ta zauna tana murmushin k'arfin hali Dan Allah ya Gani ba k'aramin tausayi da matuk'ar son autar tata takeyi ba.haka malama ta cigaba da gudanar da wa'azin ta har sai daf da magrib sannan aka tashi,kafin atashi Wani zazzafan zazzab'in ya rufe ruky Dan Saida Hanan da Anty mufeeda suka taimaka mata ta koma dak'i suka Bata magani bayan tayi sallahn magrib ta kwanta tuni Wani bacci Mai nauyi ya d'auketa....



*Washe gari*


Daya kasance asabar Ranar kuma d'aurin AURE, dayake d'aurin AUREN na Rana ne bayan ansakko daga sallahn Azhar za'ayi anan babban masallacin dake unguwar su Ruky Dan wannan d'aurin AURAN manya manyan mutane ne zasu halarta...


K'arfe biyu dot aka d'aura AURAN, can na hango AA Arab cikin Wani rantsatstsan farin yadi wanda akecewa mainless,suna gaisawa da governorn kaduna Wanda ya halarci d'aurin AUREN dama wasu daga cikin manya manyan jihar harma da wakilin president Wanda shi Bai samu halartar zuwa ba Amma kuma ya Aiko da wakilinsa,fuskar AA sai Wani fitar da annuri take na farin ciki.yana gaisawa da manya manyan mutane sai Allah ya Sanya alkhairi suke masa Cikin k'ank'anin lokaci wannan d'aurin auren ya karad'e ko Ina na shafukan SADA zumunta Akan AA Arab yayi AURE abunka da nasanne tuni har duniya ta sani,Dan hotunan da aka d'auka awurin d'aurin AUREN Babu inda basu karad'e ba a fad'in jihar nan musamman ma Wanda sukai da governor da Kuma wakilin president dama Wand'ansu manya manyan da sukai hoto dasu,Kuma dukkansu babu Wanda Basu masa alkhairi sama da million d'ai d'ai ba, Banda sak'on president Dana governor.haka aka gama d'aurin AUREN bayan ya sallami bak'insa Wad'an zasu tafi , shikuma da sauran friends d'in sa da suka zo suka taho gidannsu Amarya Dan gaida iyaye....



Acikin gida kuwa Dak'yar ruky ta yarda tai wanka harta shirya Dan ta jangwabe tace ita Bata da lafiya Saida anty mufeeda tai mata Jan ido sannan tai wanka harta shirya saudat tai mata make up,tana zaune gefen gado Hanan tana kusa da ita sai aikin kwantar mata da hankali takeyi domin tasan duk rigimar me takeyi k'awayensu duk suna zazzaune acikin d'akin,sanye take cikin wani farin material mai ratsin pitch color sai shek'i yake saboda tsadarsa d'inkin doguwar riga fitted gown sai Wani annurin hasken amarci take fitarwa an yane mata duka kanta mayafin jikinta iya fuskar ta ce kawai da aka bari a Bud'e,sai dai fuskartata Babu yabo babu fallasa,har angwaye suka iso gidan.


Bayan sun gaisa da iyaye anty mufeeda ta shigo d'akin tana kallan Hanan tace.


"Kamo ta ku fito sun iso ku suke jira",babu musu Hanan tai Abinda anty mufeeda ta fad'a ganin anty mufeeda tana mata wani kallo yasa ruky ta turo Baki gaba Tare da mik'ewa tsaye Hanan tai mata rad'a a kunne ruky ta tureta tana hararar ta Hanan ta saki murmushi kafin tai mata magiya da ido , ruky Bata kula taba har suka fito Hanan rik'e da hannun ta dama tuni k'awayen har sun fita Daga cikin dakin,ta bayan d'akuna gidan Hanan ta fita da ita sukai can


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login