Showing 210001 words to 213000 words out of 278032 words

Chapter 71 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1078

ruky ta zaro ido waje Jin abinda ya fad'a sai Kuma ta ce "akwai Wani Abu ne sir?AA Arab ya qara gyara kwanciyar sa Yana Jin kamar ya jawo ruky kusa dashi ya rungume sbd Irin abunda yake feeling akan ta,ya ce cikin muryarsa wacce ta fara sauyawa "just wanted to talk to u"me meya faru a office yau da bana nan,Baki bani labari ba?ya fad'a Yana rungume filon dake kan gadon nasa ,ruky ta saki murmushi ta ce "Babu abinda ya faru sir"ya ce are sure,Babu abinda ya faru? Ruky ta gyad'a masa kai kamar Yana ganin ta sannan ta ce "yeah" AA Arab ya ce "ok Ina tsakar ranan da kika gani a toilet Kuma ?Ruky Batasan lokacin da tai murmushi ba,sai Kuma ta ce "kai ko" ai tunda ka sa aka fitar da ita banqara shiga toilet d'in ba"AA Arab ya zaro ido waje ya ce "ok, to Wani toilet kike shiga kuma ? Ruky ta ce "naka mana"ta fad'a tana danne dariyarta Dan harga Allah saita tsinci Kanta kamar dasu ya hanaf take magana"AA Arab ya ce "wato nawa kike shiga koh? ruky Ta shagwab'e Baki ta ce " toba Kaine kace ranar na shiga ba, shiyasa ni Kuma yanxu nake shiga "AA Arab ya ce "kuma ai i??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ya ranar ne kawai bance kullum ba"...



Ruky ta ce "to idan banshiga naka ba Ina kake so na dinga shiga"AA Arab ya ce "I don't know"ruky ta ce"to idan har bakaso na qara shiga naka, to ka maidani office d'in mu"AA Arab ya ce "aikin riga da kin dawo kenan"ruky ta ce "cikin shagwab'a tareda sa kukan k'arya Allah nidai sir na gaji da zaman offiice d'in nan naka,wlh kwana biyun nan Daba ka sani aiki ba gashi harna Yi kiba" ta fad'a tana dariya,AA Arab ya zaro ido ya ce "me kike nufi kina so dai kice Ina takura miki koh? ruky ta ce "ni bance haka ba" AA Arab ya ce " to me kika ce?ruky tai saurin,sai Kuma ya ce"ba kiyi missing D'ina ba Kenan" ruky tai saurin cewa a'a ni bance ba,sai Kuma ta tsinci Kanta da cewa nayi missing D'inka mana Sosai ma,sai kuma tai saurin rik'e baki Jin abinda ta fad'a,AA Arab ya ce "kinyi Missing D'ina kenan koh? ruky tana dariya tareda jin kunyar abinda ta fad'a tai saurin kashe wayar,AA Arab yay murmushi Jin ta kashe wayar ya qara darling number nata Amma harta gama ringing Batai picking ba ,kawai sai yay murmushi Shima Yana Jin duk Wani ciwon da yake ya sakeshi take ya lumshe idonsa ya D'ora wayar kan kirjin sa yanajin Wani Irin yanayi na shigarsa.....


Ruky kuwa,ihu ne kawai Bata Saba sbd kunya ita Mai yasa ma ta fad'i haka,tana kallan k'iransa Amma Batai picking ba ta kifar da wayar akan gadon,sai Kuma ta fara mamakin Dama haka yake da xance da Kuma saukin kai hama,take ta saki murmushi sannan ta gyara kwanciyar ta tana Jin Wani Irin Abu na tasiri acikin zuciyarta da Batasan ko mene ne ba.......





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____ JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*('TAURARI WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 8?? 3??


___________?&



Washe gari da safe AA Arab fresh ya Tashi da shi,dan ji Yayi kamar babu wata jinya da ya tab'a Yi , saboda gabad'aya sai yaji babu inda yake masa wani ciwo. ita Kanta ummi tai mamakin yadda ya samu sauk'i cikin k'an k'a nin lokaci haka, abinda Kuma ya K'ara Bata mamaki ma shine Daya tashi da ASuba Saida yaje har d'akin ta ya gaida ta ,Dan da ita harta na shirin xuwa ta duba jikin nasa idan tai sallahn ASuba, sai gashi kuma Ya ma zo da kansa,tayi farin ciki sosai Ganin yadda ya samu sauk'i lokaci D'aya,har zata tambayeshi meye damuwar da doc yace tana damunsa sai kuma kawai ta k'yaleshi, har ya bar d'akin ta bishi da kallo kawai .wajen k'arfe Tara na safe AA Arab ne tsaye ahabar gidan su waye ce kare a kunnan sa daga gefe Kuma drivern sa ne ya fito da mota zasu fita,sanye yake cikin bak'ak'en suits Wanda suka amshi farar fatar sa, kansa babu hula,Hakan ya bani damar ganin gashin kansa Wanda ya kasance Irin na larabawa kwance zagaye da kansa,yayi matuk'ar kyau sosai kamar me Dan duk Wanda ya Gani dole ya Yaba ko da ko mak'iyin sane,Saida ya gama wayar Sannan ya k'arasa inda driver ke jiransa ya shiga back seat d'in motar bayan an Bud'e masa sannan driver yaja suka tafi.tafiya 10 minutes ce ta kawo su headquarters,bayan ya shiga second falor na office d'insa Saida ya tsaya yana kallan table d'in da ruky ke zama,ganin Bata zoba yasa ya saki numfashi Ya k'arasa Shiga har cikin office d'in nasa.zuwan sa babu dad'ewa ruky itama ta qaraso cikin office d'in wajen karfe Tara da Rabi na safe,bayan ta ajiye handbag d'inta ta tsaya tana kallan k'ofar office d'in nasa tasan yaxo tunda taga motar sa a parking lot kafin ta shigo,sai Kuma ta tsaya tana tunanin ta shiga ta gaida shi ne ko kar ta shiga Dan Allah ya Gani kunyar sa take ji,tun abinda ya faru Daren jiya,har ta zauna Kuma sai taga bazata iya ba kawai saita mik'e ta qasara bakin koyfar ta tsaya ta kasa shiga ciki,tafi mintuna biyu ahaka sannan tai k'undun balan kama handle d'in k'ofar ,nan ma Saida ta shefe seconni sai kamu ta Murd'a sannan ta shiga da sallama abakinta .....


AA Arab Dake zaune kan kujerarsa ga laptop d'in shi a gaban sa Yana aiki ya d'ago Yana kallan Wanda ya shigo office d'in,ganin ta kawai da Yayi sai da yaji zuciyar sa ta harba,take ya zuba mata ido Yana kallan ta Wanda Baima San yayi Hakan ba....


Ruky dake tsaye ta sauke idan ta k'asa ganin Yana mata Wani Irin kallo me kashe sassan jiki,kafin ta motsa lips d'inta kad'an ta ce.

"Good morning sir"


AA Arab Daya shagala a kallan ta ganin yadda tai kyau Kamar me, ya k'urawa D'an karamin bakin ta datai maganar dashi ido Yana kallo ,Allah ya Gani kawai ganin yau yayi ruky tayi masa Wani mugun kyau Wanda Bai tab'a ganin ta dashi ba duk kuwa da zaman da suke waje D'aya.


Ruky ta ta k'ara d'ago da kanta ta kalleshi ganin ta gaida shi Bai ansa ba,ga Kuma yadda ya k'ure ta da ido hakan yasa ta D'an tsorata kad'an tana tunanin ko Wani abun ta k'ara yi masa Kuma, tunin nan da tai yasa ta juya zata bar office d'in.


Take AA Arab ya lumshe idonsa sannan ya ce cikin wata iriyar murya.

"Ina zaki Kuma ?"


Ruky ta runtse idon ta Bata juyo ba ,sbd yadda ya tsorata ta,Saida ya k'ara Mai Mai ta mata san nan ta juyo da k'yar Amma Bata yadda ta k'ara kallan shi ba, ta dai sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da yatsun hannun ta.AA Arab ya k'ure ta da ido kafin ya ce.


"Ina Kuma zaki bayan bamu gaisa ba?"Ya k'arasa fada yana Wani lumshe ido tare da narke mata murya .


Ruky ta D'an dubur burce ta ce.

"Sir xance nai aikine dama nazo na gaisheka ne" ta fad'a har lokacin Bata k'ara d'ogo da kanta ba.


AA Arab ya K'ara lumshe ido sa sai kuma ya Bud'e at the same Yana kallan ta,kafin ya D'an furzar da huci me zafi ya ce.


"Ki d'ago ki kalleni"ya fad'a Yana wani tsareta da idonsa.


Kasa d'ago da kanta tai ta girgixa masa kai kafin ta motsa lips d'inta kad'an ta ce.


"Baxan iya ba sir".


AA Arab ya sauke numfashi kafin ya ce.


" Aiko baza ki fita ba indai Baki kalleni ba".


Ruky ta rasa ya xatayi Dan Allah ya gani baza ta iya jure kallan Sa ba saboda Irin abinda ta karan to daga cikin k'wayar idanuwan nasa,Ga ta matsu kawai ta koma wurin zamanta ta zauna,to wai ma Wani tsautsayin ne ma ya kawo ta office d'in sa,kawai sai tai k'undun balan d'agowa Dak'yar tana kallan sa ,abinda ta gani Saida tai Dana sanin kallan na sa saboda yadda taga Idanuwan sa sun sauya lokaci D'aya take ta juya har tana Neman fad'uwa ta bar office d'in, ta koma wurin xamanta tana sauke numfashi a jajjere tare da jin gabadaya jikinta ya mutu Batasan tsawan lokacin data d'auka ahaka ba,Dan gabad'aya kasa aikin ma tai .


AA Arab ko gabad'aya ji yay ya kasa jurewa ne da da abinda yake ji akan ta, Shiyasa kawai ya zab'i ya fara nuna mata abinda yakeji acikin zuciyar sa game da ita ko ta Gane ,kai idan ma Bata Gane ba yayi ALK'awarin ayau basai gobe ba zai fito ya fad'a mata sirrin Dake zuciyar sa akanta, ya gaji da wannan dakon wahalar da yakeyi akan soyayyar ta.da k'yar Dak'yar ya samu ya Maida hankalinsa kan aikin gabansa harya samu yayi,gefe D'aya Kuma Yana tunanin Irin abinda ya Gani akan idon ruky Wanda ya nuna tsoro k'arara acikin su , take ya saki murmushi shikad'ai Yana cije leb'ensa barin ma idan ya tuno da wannan moment d'in nasu ....


Da lokacin sallahn Azhar yayi ya d'auro alwala ya fito zai tafi masallaci,ai ruky tana Jin k'arar Bud'e k'ofar office d'in nasa tai saurin juyar ta kanta gefe daban ,AA Arab ya kalleta ganin yadda ta juyar da kai tana Wani sunne kai da bubur burcewa kawai ya girgiza kai yay hanyar k'ofar fita daga office d'in ma gabad'aya ya nuna Kamar Wanda shi baisan komai ba...


Ruky ta juya Jin ya fita ta sauke numfashi tana dafe k'irji wlh yanxu AA Arab tsoro yake Bata ,da wannan sabon salon dayazo mata dashi ita Gsky gara a yadda suke da dadai ya dinga mata wannan salon Yana mata wani kallo data kasa Gane ma'anar sa, ga sai ya dinga narke mata murya bayan da ba haka yake mata ba...


Tana nan zaune ganin lokacin sallah Yana Neman wuce ta yasa ta tashi ta shige toilet d'in cikin office d'in sa,kafin ya dawo ya tarar ta, ta dauro alwala sannan ta fito cikin sauri ta shimfid'a darduma anan falon ta tayar da sallah...


Da AA Arab ya dawo daga masallaci Bai mata magana ba,sbd indai ya ce zai mata magana ZA'A iYi samun matsala, saboda ko iya Muryarta yaji bak'aramin hargitse masa Lissa fi take ba da shiga Wani Irin yanayi yake shiga ba, bare Kuma harta kalleshi da idanuwanta Wanda suke k'ara narkar dashi a duniyar soyayyar ta ...


Haka sukai wannan zaman kuramen daga ita harshi Babu Wanda ya zo wurin D'an uwansa bare Yay masa magana,Dan ko aikin Daya Saba Bata ma a wannan ranar Bai bata ba...


Da yamman wajen k'arfe biyar saiga Hanan ta shigo office d'in falon farko ta tarar da ruky tana tsaye tana mata murmushi, ruky kawai ganin ta tai a kanta Kamar wacce aka hankad'o Hanan tai sallama ta k'araso har cikin office d'in ta zauna kan kujera tana kallan Ruky wacce itama ita take kallo..


Hanan sauke ajiyar zuciya tana kallan Ruky ta ce.


"Ke ya naga kina min Wani kallo ne haka lpy?"

Hanan ta fad'a tana tsare ruky da ido.


Ruk ta sauke numfashi ta ce "Babu komai kawai gani nai yau ko sanar Dani zakizo bakiyi ba" ta fad'a tana kallan hanan.


Hanan ta harare
ta ce .

"Aiba wajenki naxo ba",


Ruky tai murmushi ta ce.

"To wajen wa kika zo?",

Hanan ta ce " wajen Yaya na mana".


Ruky ta Bud'e Baki alamar mamaki tare da dariya sai Kuma ta D'an ya mutsa fuska kafin ta ce.


"To tashi ki ban waje sai kije kisa meshi yana ciki ai".

ta fad'a tana ture Hannun Hanan Dake kan table d'in gabanta.


Hanan tai murmushi ta ce "wannan kishin fa?,Kawai Dan na ce ba gunki na zo ba shine zaki Koreni".


Ruky ta ce "eh an korekin".

Hanan ta Mik'e ta ce.

"shikenan bari naje ".

Daga haka ta Mik'e ta qarasa gaban k'ofar office d'in AA Arab ta fara knocking.ita dai Ruky ta bita da kallo tana mamakin k'arfin hali da shishshigi Irin na Hanan kafin ta d'auke kanta ta cigaba da aikin Dake gaban ta....


AA Arab Dake ciki Yana kwancen kan sofan office d'in,Dan wani Irin feeling yake ji kamar me, daukar sa ma ruky ce Dan haka ya tashi daga kwancen da yake ya na gyara zaman sa a kan sofan ya ce

"Coming ",


Hanan ta Murd'a k'ofar ta shiga bakin ta d'auke da sallama tana murmushi ganin AA Arab.


AA Arab ya ansa mata sallamarta Yana Maida mata da Martanin
murmushin da tai masa.


Hanan ta tsaya atsakiyar office d'in tana kallan AA Arab ta risina ta ce.

" good evening sir".

AA Arab ya ce "evening Hanan"Patan kina lpy?.


Hanan ta ce " lpy lau Alhamdulillah sir ".

AA Arab ya jinjina kai kafin ya ce "ya aikin ?.

Hanan tana murna ta ce .

"Lpy lau Alhamdulillah sir".


AA Arab ya ce "Masha Allah ".


Hanan ta ce "dama na Tashi da wuri ne daga office shiyasa nace Bari nazo na gaida ka "ta fad'a tana murmushi..


AA Arab ya ce " Aiko Nagode sosai Hanan sannu da k'ok'ari",ya fad'a Yana mik'ewa Dan zawa ya kawo mata lemo da ruwa cikin fridge d'in offer d'in sa , ganin abinda zai yi yasa Hanan tai saurin ce wa "noo sir ba saika kawo Komai ba Alhamdulillah, zan ma tafi ne yanzu"ta fad'a tana juyawa zata nufi k'ofar.


AA yace "baza kisha ko ruwa bane".


Hanan juyo ta ce "thank u sir".


AA Arab ya ce "alright thank u very hugely Hanan Allah ya Saka da Alkhairi".


Hanan tana murmushi ta ansa da Ameen sannan ta fita daga office d'in. Ya koma ya zauna yana k'iyasta inama yadda suke da sakewa tsakanin sa da Hanan haka suke da ruky ,sai Kuma a zuciyar sa ya ce "In Sha Allah a yau zan kawo k'arshen komai.....


Hanan tana fita ta samu Ruky Zaune tana aikin ta a laptop d'inta tana Jin fitowar Hanan Amma ta nuna kamar Bata jiba,har hanan ta k'araso gaban Ruky tana kallan Ruky ta ce .


"ke na fito tafiya Zanyi, da xan jiraki ne ki sauke ni a gida yau ban fito da mota ta ba, tana wurin gyara shine nakeso da ki saukeni a gida Amma naga sai Wani had'e mun Rai kike" ,ta fada tana hararar ruky.


Ruky da kamar bazata ta d'ago ba sai Kuma kawai ta fasa ta d'ago tana kallan Hanan ta ce "naga ai ba guna kika xoba Ball an tana kice na miki Rashin mutunci koh?,sai ki koma gun Wanda kikazo idan ya tashi tafiya gida saiya tafi Dake"ta fad'a tana d'auke kallan ta daga kan Hanan.


Hanan mamaki ne ya kamata Tama kasa cewa komai sai Kuma ta mik'e ta ce.

"Nagode da Wulakanta ni da kikai sai anjima".


Ta fad'a tana mikewa, ruky ta riko Hannunta tana murmushi ta ce "dawasa nake miki bari na had'a kayana mu tafi", daga haka ta fara had'a kayanta,Saida da gama tas sannan ta kalli Hanan ta ce.

" mu ta fi".

Hanan tana kallan ta da mamaki ta ce "Yanaga zaki tafi bakije kin masa sallama ba"ta fad'a tana kallan Ruky.


Ruky ta Wani yamutsa fuska ta ce " wazan yiwa sallamar " ta fad'a tana hararar Hanan.


Hanan ta ce da mamaki "wai dama haka kike fitowa bakya yimai sallama ruky,lallai Baki kyau taba,wannan ba irin hali nane Dake ba,sai Kuma ta ce Aiko saina fad'a wa mamah duk abinda kike masa".


Ruky tac "eh karki fasa fad'a matan ,ko anfad'a miki dole saina masa sallamar ne".


Hanan ta D'an kwantar da murya Dan kada AA Arab ya juyo su ta ce.


"Dan Allah ruky kije kimai sallama mana wlh Hakan Allah badai dai bane".

ruky ta ce "aini bansan dai dai ba sai ke Hanan".


Hanan ta ce cikin rarrashi "a'a bance haka ba Yi hakuri kije Dan Allah badan niba kimai sallamar".da k'yar da k'yar Ruky ta yadda ta je taiwa AA Arab sallama, saidai tana shiga ma da ta ganshi kwance kan sofan ta tsaya daga bakin kofar ta ce

"Sir na tafi " tana fad'ar haka ta fito daga office d'in .


Shidai AA Arab da kallo ya bita tare da mamakinta ganin Irin sallamar da tai masa kamar Wanda zai kamata ko Kuma Wani tineger,da ai ba haka ta saba masa sallamar ba,kawai ya sauke numfashi ya ce s fili "lallai akwai akai agabana ba kad'an ba".saiya koma ya kwanta Yana tunani.


Ruky tana fita ta Samu Hanan Dake jiranta ta ce.

" muje" ta fad'a tana yin gaba,hanan ta ce.

"yanzun ke har kika Mai sallama".


ruky ta juyo ta ce "idan baza ki fito ba kiyi ta zama uwar San gwanin ta". ta na fadar haka ta juya.


Hanan ta tab'e Baki sannan tabi bayan ruky suka tafi.



___________?&


Da daddare wajen k'arfe 9 na dare ruky tana chatting taga K'iran AA Arab ya shigo wayar ta kamar baza tai picking ba sai Kuma kawai ta tsinci Kanta da San tai picking call d'in ko Dan taji muryar sa ma ai tayi, bayan tai picking call d'in tai sallama Had'i da gaidashi lokaci D'aya, daga nan tai shiru....


AA Arab Dake cikin d'akinsa a kwance kan gado,Jin muryar ta yasa yadian gyara kwanciyar sa Yana ansa mata gaisuwar da take masa,sai Kuma yaji tayi shiru,yasa ya ce.

" meyasa yau kika baro office Batare da kin jira kinji me zance ba?


Ruky tai shiru tana sauraran sa,ya ce .

"Ki bani ansa"

Ruky ta ce "Babu komai".

AA Arab ya ce ban yadda ba ".

Ruky ta ce "da Gaske sir".

AA ya ya lumshe ido Yana sauraran daddad'ar muryar ta sannan ya ce cikin k'asa da murya .

"Meyasa bakya iya kallo na yanxu?,ya fad'a da Wani Irin yanayi.

Ruky taji tambayar ta girmeta ta ce.

"Nothing"

AA Arab ya ce "akwai,
Ki fad'a min kawai".


Ruky ta ce cikin shagwab'a"to ba Kaine ba"sai Kuma tai shiru.

AA Arab ya gyara kwanciyar Jin anxo inda yake son Azo d'in ya ce.

"nine me?.

Ruky ta ce "saika dinga min Wani kallo Wanda da bakamin" ,ta fad'a tsakanin ta da Allah,Dan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login