Showing 120001 words to 123000 words out of 278032 words

Chapter 41 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1028

baba asabe ta tsuke fuska tace "Babar mu Dan Allah ki barni naje kingafa shikadai ne yake xuwa guna, baba asabe ta buga mata tsawar da Saida Mardiya ta tsorata tace "baxa kiba matsiyaci dashi kullum idan yaxo babu abinda yake kawo Miki Amma sai iya dauko kafa yaxo, to Babu inda xaki, haka mardiya tai ta kuka, Washe gari haka baba asabe taita xaman jiran xuwan Kabiru tun safe Amma har kusan magrib bai xoba,da harta cira Rai da xuwansa Kuma can saiga shi an Aiko Wani yaro yay Kiran Ameenah, ummah tace "waye?. yaron yace"wai sunan sa Kabiru. ummah tace "kaje kace yayi hkr anmata miji,yaro ya jura zai koma baba asabe ta faki idan ummah ta yafi to yaron xuwa wajen,tai qasa da murya tace "kaje kace tana xuwa,...




Bayan fitar yaron baba asabe ta shirya ta fita ta samu Kabiru tsaye daga gefen gidansu ta washe Baki ta hau gaidashi tace "wlh kaxo Bata da lpy,da Kyar take iya tashi, Amma Dan Allah kabari xuwa jibi saika dawo, Kabiru ya Wani kalli baba asabe sai Kuma yace "gsky xanyi wata tafiyar ne Kuma bana tunanin xan dawo kwana kusa, Baba asabe tace" yaushe xaka dawo?, Kabiru yace "nan da sati biyu."baba tace babu komai nidai indai xaka dawo din, ai Babu matsala,tana nan tana jiranka, Kabiru yay jimm sai Kuma yace "shikenan Babu komai,baba asabe ta hau Yi masa godiya,daga haka suka rabu,...

____________?&


*Bayan sati biyu*



Bayan sati biyu lokacin har aikin Malamin xaure ya fara ci,Dan dama yace "nan da sati biyu,gashi har kwana biyu ya karu,Dan har baba asabe ta fara ganin canji awajen malam Auwalu yanxu in ta fada masa abu jiki na rawa yake Yi, Kuma baya musu Koda ko abun ba haka bane,akuma yau sukai da Kabiru zai xo,bayan magrib ko saiga shi, yana sallama ummah har tace "Ameenah baza ta fita, Amma baba asabe ta bankado musu labule tace" Ameenah ta fita, ummah zata Bude Baki tayi magana Amma ta kasa kwata kwata ,taji kamar an datse mata harshan ta,Kuma sai taji baxa ta iya musu da baba asabe ba,taji bata San batawa baba asabe Rai,babu yadda ta iya Ameenah ta fita waje cikin mamakin ummah batace komai ba,bayan tasan shamsu zata aura, Kuma ita take hanata fita duk Wanda yaxo sbd anruga da anbawa shamsu auranta,wacce tai ta mamakin ummah da Bata hanata fita ba,yanxu ummah ta yarda taje gunsa,ganin Kabiru Saida gaban Ameenah ya fadi, ganin shi kamar mahaukaci,Haka ta daure ta ce Gani ,ta fada tana hade ranta, Dan itama ba haka taso ba,tunda ta fara San shamsu,ganin farko da Kabiru yayi wa Ameenah yaji aransa itace wacce ya kamata ya zafa amatsayin wacce xata xauna agidansa amatsayin matar gida sbd abinda yakeso ya cinma,yay aikinsa cikin nutsuwa, Amma bawai yana Santa so na mata da miji ba, a'a kowa xaiyi rayuwar sa sane,yace "ni suna na Kabiru Kuma AURANKI nakeso nayi Babar kice ta bani ke,nidai kinmun, bansaniba ko nima na miki ,ya fada Yana kallan Ameenah wacce fuskarta ke daure har lokacin.Ameenah ta dubeshi sama da qasa tace" kayi hkr Ina da mijin AURE daga haka ta koma gida,...



Kabiru ya bita da kallo,baba asabe ganin Ameenah ta dawo da wuri yasa ta fito waje da sauri ta dubi Kabiru Wanda ke tsaye har lokacin Bai tafi ba, tace "ya kukai da ita, Kabiru ya fada mata.duk yadda sukai da Ameenah,baba asabe tace "karka damu indai ta Maka shikenan, Kabiru yace" tayi, baba asabe tace shikenan,sai dai yar mijinah nace duk abinda zaka fuskanta kayi hkr, Kabiru yace "yar mijinki Kuma?,baba asabe tace eh Amma kamar 'yata take bubu ruwan uwarta, Kabiru yay jimm ,kamar zai magana Kuma ya fasa yace "shikenan,"baba ta washe Baki tace "Wani satin kawai ka turo manyanka a tsaida maganar AURE . Kabiru yace "shikenan nagode baba,"baba asabe tace karka damu daga haka Kabiru yay mata sallama ya tafi,baba asabe Kuma koma gida,ranta fes .,to tun daga wannan Rana Kabiru kullum sai yaxo babu fashi,babu yadda Ameenah ta iya ,dole ta Fita, domin daga malam Auwalu har ummah basa iya hanata,idan baba asabe tace ta fitan.da shamsu yaxo kuwa baba asabe da kanta ta fita gunsa tace " karya qara xuwa",dayaki ji tasa Malam Auwalu ya fada masa ,ya Kuma Maida masa da kudin auransa, shi kansa shamsu yay mamaki, Ameenah ta fita aboye ta fada masa komai shamsu yay Kuka yace ta dage da addu'a, wannan itace rabuwar Ameenah da shamsu,da sati ya cika Kabiru ya Aiko da iyayen bogi da sadaki da kudin AURE, itama mardiya saurayinta ayuba , Wanda baba asabe ta tsaneshi sbd bashi dashi dole sai shi din tunda bata da me xuwa gunta, haka aka tsaida auransu wata daya Dan baba asabe so take kawai ta cika burinta, akan maimuna da 'yar ta shiyasa Bata Wani damu ba da mardiya zata auri ayuba, Kuma bs haka taso ba,Dan dai kawai mardiya ta dage ita ayuba take so.,akwana a tashi har ranar biki taxo ummah tana ji tana Gani aka aurawa Kabiru Ameenah,aka kaita gidan ta Dake Kaduna hayin rigasa, ummah kuka malam Auwalu kuka,babu yadda suka iya aka kai Ameenah, itama mardiya aka kaita Wani qauye Dake cikin ZARI'A,sai abayan da akai bikin aikin da aka musu ya war ware,ummah tai tai ta Raba auran Kabiru da Ameenah Amma abun yaci tura dan baba asabe ta qara xuwa an rufe kawar da hankalin malam Auwalu Dan kada ya fahimci halin da Ameenah take ciki, shine Kuma har yau ya kasa fahimta,....




*Jan hankali*

_A nan _malam Auwalu kwata kwata Bai kyau taba,duk abinda baba asabe ta zama , Yana da laifi .zamu iya cewa shine Sila,dalili kuwa shine ,sankan daya fito fili qarara ya nuna na yafison maimuna da 'ya'yanta,Akan baba asabe ,Bai kyau taba,Bai kamata ace Yana nuna Fifi ko akan matansa ba. duk da dole ana samun Irin haka,kaji kafison wance akan wance .yes, ko matanka hudu, dole sai kaji akwai wacce kafiso, Kuma tafi shiga xuciyar ka,Amma ba'a nunawa kiriri saika bash shi axuciyarka.ko acikin 'ya'yan Kane dole sai kaji wanda kafiso.to wannan shine kuskuren sa,duk abinda baba asabe ta janyo wa kanta,ko na xunubi kona Lada ne, dole zamu iya cewa malam Auwalu Yana da nasa kamason aciki ,. bawai nace baba asabe Bata da laifi ba, a'a itama tana da laifi,laifinta kuwa shine _na kin daukar kukan ta kaiwa Allah, saita Saba, ta tafi wajen Wani mushu riki,Mai sabawa Allah, Wanda baxai taba magan ce mata matsalar taba,da ace ta Mikawa Allah lamarin ta da tuni ta samu warakar abin da take NEMA din, domin Allah Mai jine Kuma Mai ganine, shiya ce ku rokeni xan ansa muku, Amma Batai haka gashi ta kauce hanya,Allah ya kiyaye mana imanin mu>?2?.so ,sbd haka Dan Allah mudaina nuna banbancin mu afili nawai kafi son wance akan wance,ko Kuma kafison 'ya'yan wance akan na wance,duk mu hada mu rungume su, domin bakasan Wanda xaka mora ba, da d'a da dukiya ba'a musu mugunta,ta iya yiwa shi Wanda kake so din baxai taba jikan kaba, Amma shi Wanda baka so din shine wata Rana zai jikinka, Allah yasa mu gyara, Allah kiyaye mana imanin mu,Allah yasa mudace >?2?.



*Dawowa daga labari*




07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t





*_____JAMI'AR TSARO _____*




*____THE WOMEN POLICE ____*




*NA*




*_____NAJA'ATU UMAR FAROOQ _____*



*____(MRS SARAKIES)____*





*Bismillahirrahmanirrahim*




_______season two ep 5?? 2??



_____________?&



*Cigaban labari*



Baba asabe ta koma gida tana Mai farin cikin zaliha zata auri salisu...washe gari baba asabe ta_ tisa zaliha acikin uwar dakinta, ta bawa zaliha wannan maganin data karbo wajen malamin xaure.sannan ta kwatanta ta mata yadda xatai anfani dashi, kamar yadda malamin xaure ya fada, babu musu zaliha ta karba ta fara anfani dashi awannan lokacin...da Rana wajen karfe dayan Rana zaliha ce tsaye gaban madubi tana Saka Janbaki a labbanta .ta shirya tsaf ta fito waje ta tarar da komai ya kammala.tasa Mai napep ya shigo ya dauki kulolin abincin yakaisu cikin napep din. sannan zaliha ta fito ta shiga _ suka nufi Tasha, ..tana Isa ta tadda customers dinta , suna jiranta .bayan ta shirya komai a inda take xama ., costumers din suka fara xuwa dansu sayi abincin .wasu su Bata kudin kafin suci abincin wasu Kuma sai sun ci, suke biya.ta fara xuxxuba musu, Saida ta gama bawa duk Wanda suka ce ta xuba musu sannan ta zauna, zaman ta keda wuya saiga wannan Dan smoking din na Ranar Wanda ya ShaSh shafe ta,ya qara xuwa yauma,ya samu benci kusa da zaliha ya xauna ya kalli zaliha wacce ta hade Rai yay murmushi yace ,cikin yanayin maganar sa "xuba min Nima idan afa", zaliha ta kalleshi sai Kuma ta kau dakai ,tai kamar Bata ji me yace ba ..ganin taki Kulashi yasa ya tashi daga xaunan da yake ya matso kusa da ita ya kai hannu habarta, zai taba ta,zaliha tai baya da sauri ta hade Rai tace "bana son Irin wannan,"shaho ya qara sakin murmushi yace " to idan bakya so kixuba min abincin," zaliha ta mika masa hannu tace "bani kudin tukunna.", shaho yay dariya yace "oh yau Kuma haka zaki mun kamar Wanda zan gudu ,sai kace bana Baki kudin ". zaliha tace "nidai saika bani tukunna". Shaho ya xura hannunsa a aljihun Wandansa ya zaro kudi ya mikawa zaliha . zaliha ta xuba masa abincin ta bashi,ya karbi plate din abincin ya shimma ceta ya tabo kirjinta . zaliha tai baya da sauri tana hade Rai ta nuna shaho da yatsa tace "wlh idan ka Kara tabani wlh saina wanka Maka tafi, shaho ya zaro ido waje Irin yay mamakin nan, Dan abuge yake, Yana layi Yana lumshe ido hadi da budewa yace"ke 'ke kin Isa ki mareni ,wl _wlh da saina kwantar Dake a gunnan,. sai Kuma ya qara matsowa tareda kawo hannu kirjinta ,yace "bari ma kiga na qara na gani xaki iya Marin nawa", zaliha ta qara yin baya da sauri.shaho ya kece da wata dariya harda kyakyatawa yace"ashema ke karamar kwaruwa ce,"daga haka yay gaba da plate din abincin a hannunsa,Wanda yake tan gadi kiris ya rage ya kife abincin sbd yadda yake tangadi..zaliha batai magana ba illah Hararar shaho Kawai da takeyi,ta bishi da kallo harya shige dakinsu Dake Tasha,tana tsine masa axuciyarta.Dan shaho Irin rikakkun Yan iskan nan ne na cikin Tasha, gashi bashi da mutunci,Dan har 'yan uwansa Maza ma tsoron sa suke ji,....



Wajen karfe shida zaliha ta fara hado kudinta. Dan ta gama Saida abincin gida zata tafi ,ta gama tattara kudinta tsaf , me napep din ta yaxo ya dauke ta ya mayar da ita gida . kafin magrib ta iso gida....wajen karfe takwas da Rabi zaliha tana xaune a kofar dakinsu tana cin abinci.,taji keypad dinta Dake kan cinyar ta na vibration ta duba taga me kiran ,Alhaji tanko ne,ke kira, ta tsuke fuska Hadi da tsaki qasa qasa Dan wlh Allah Yana Gani ta tsani wannan mutumin Dan dai kawai baba asabe ta_,ta kura mata ne akan tana fita. Amma wlh Allah Yana Gani ya isheta kullum idan yaxo da sabon abinda xaici tayi masa ko Kuma shi yay mata.tana wannan tunanin har wayar ta katse Bata saniba Saida ya qara Kiran har ta kusa tsinkewa sannan tai picking takai kunne,tai shiru tana sauraran sa, Saida ta gama sauraran sannan tace "gata nan xuwa",......



Ta mike ta wanko hannunta,ta dauki mayafinta ta kalli baba asabe tace "baba bari naje yaxo ".baba asabe ta washe Baki tai qasa da murya tace "shikenan maxa jeki Mai kashin arxiki sai kin dawo," zaliha Bata ansa ba.ta nufi kofar fita daga gidan . ummah ta bita da kallo tana musu addu'ar shiriya azuciyarta.zaliha tana fita,ta tarar da Alhaji tanko acikin tsohuwar motarsa Yana xaune ga uban tunbi agabansa kamar kwarya,ya Kalli zaliha Data coge taki shiga motar yace "shigo mana baby," zaliha ta kasa yin magana sbd takaici,kamar baxa ta shiga ba, axuciyarta tai dariya tace "wai baby ,? wlh abun dariya ya Bata,"sai Kuma kawai ta Bude motar ta Shiga, ta juyar da kanta gefen window.Alhaji tanko ya juyo da murmushi yace yau meya samu amarya ta,? Ya fada Yana kokarin juyo da fuskar ta,zaliha ta qaqalo murmushi sai asannan ta kalleshi tace "babu komai kawai dai kaina ke ciwo , Alhaji tanko ya qara matsowa ya taba goshinta cikin damuwa yace"ko Muje na siya miki maganine amarya ta?.zaliha ta girgixa kai, Alhaji tanko ya rike hannun ta gam yace"sannu "zaliha ta daga masa kai kawai Dan wlh wannan maganar ma dayake Yi wlh daurewa kawai take Amma gabadaya tsami taji yanayi. ,tana wannan tunanin,ya kawo bakinsa yay mata kiss zaliha xatai baya ya hanata ya Kara Yi mata Wani wawan runguma, zaliha tai _tai ta kwace kasawa tai Saida ya gama ShaSh shafe ta sannan ya kyaleta, zaliha ta fara kokarin bude motar ta fita Amma ta kasa, Alhaji tanko yay kasa da murya yace "haba baby? bafa Wani abun nai Miki ba, Dan kawai na rungumeki ",idan ban rungume kiba waxan yiwa, zaliha ta juyo afusace tace "nidai banaso "Alhaji tanko yace "to naji Amma Dan Allah ki bari na qara ko saudaya ne in yaso saina Baki kayan danaxo miki dashi ki tafi ,daga wannan shikenan Bai jira cewar zaliha VA ya qara kawo mata runguma Hadi da shafa kirjinta, zaliha tai lakwas tana amsar sakon,sai Kuma tai saurin janye jikinta,ya saketa ya Mika mata ledojin yace "gashi nagode sosai Kinga ko yanxu ai kin faran tamin," zaliha Bata bashi ansa ba ta Bude motar ta fita,.. Alhaji tanko ya bita da kallo harta shige gida, sai Kuma ya sauke ajiyar xuciya Yana Mai ayyana abubuwa aransa,.....



Bayan shigar zaliha gida ta tarar da Nana akan barandar falonsu tana karatu Dan jam xata zana,ranar Monday ,xata shiga jami'a ko Kuma ta cike form ta shiga school of nursing. cikin biyu xatai Daya .dan ummah ta dage cewa in Sha Allah sai Nana tayi karatu me xurfi, itama Kuma Nana tana so shiyasa ta Maida hankali kan karatun ta.,tunda anyiwa Ameenah mugunta.,Nana ta bita da kallo sai Kuma ta tabe Baki ,ta cigaba da karatun ta ganin yadda zaliha ta wuce a firgice kamar hankalinta baya jikinta.., umma data fito daga dakinta yanxu tabi zaliha da kallo Dan itama taga yanayin na_ta,ta girgixa kai kawai ta samu waje ta zauna ta kunna radio Yana sauraran labaran da suke.....


Malam Auwalu ne ya shigo gidan ransa a bala'in bace,Ya shiga kwalawa zaliha kira. baba asabe ta fito agadarance tace "lpy malam kakeyiwa zaliha wannan Kiran ?".malam Auwalu Bai kula taba ya cigaba da Kiran zaliha, zaliha ta fito da sauri kamar xatai tun tube tana gyara Dan kwalin kanta tace" baba Gani "malam Auwalu yace "waya sauke ki a mota yanxu? , atare baba asabe da zaliha suka zaro ido waje , har suna hada baki wurin cewa mota Kuma?, malam Auwalu ya harari baba asabe yace "kwarai kuwa",yanxun nan na dawo aka tareni ake fada min anga zaliha ta fito daga motar wani.zaliha tace" wlh baba sharri aka min bani bace,ta fada tana Mai rushewa da Kukan qarya,"malam Auwalu ya daka mata tsawa yace "zaliha nawa ce a unguwar nan da zakice bake bace? Bai jira cewar taba yace" karya kikeyi ai wadanda suka fadamin baxa sumin qarya ba, yanxu ke nawa kike da har kika San ki hau motar saurayi....



Baba asabe tace " cikin bacin Rai wai malam meye kake cewa haka ne,ya xa'ayi Kawai yarinyar Bata San bawa ba, batasan sauka ba kawai aje afada Maka qarya da gsky wai an ganta amotar Wani wanne munufukinne,ya fada Maka haka.? babu bincike babu komai kai kuma kawai ka hau kai ka xauna ,kaxo ka kama yarinya da fada kamar xaka daketa.malam Auwalu yay mata Wani kallo yay kan zaliha yace "ki fadamin Ina kikaje da daddaran nan ?,waye Kuma ya sauki amotar da aka ganki?, zaliha tai baya ta kasa magana ta qara sautin Kukan ta,malam Auwalu yay wajen inda suke aje iccensu na girki ya zaro Daya ya iyo kan zaliha dashi, Yana "gara naji miki rauni Dani ki kawomin abin kunya." Bazaki xubar min da mutunci ba,..ganin haka yasa zaliha ta ruga aguje tai daki ta sakota .malam Auwalu yace "kota Bude kofar ko Kuma ya balla ta ," baba asabe ta tare kofar tace "wlh baxa ka Dake taba, agama xuga ka baxa kai bincike ba, Kawai kaxo xaka daki yarinya. Kuma da kake cewa baxa ta ja maka abin kunya ba,ni 'ya'yana in Allah ya yarda baxasu taba jami'an abin kunya ba,sai dai fatan da kake musu ya koma kan 'ya'yan matar so,(wato ummah) ".malam Auwalu yace cikin bacin Rai "matsa asabe". ,baba asabe ta qara tare kofar tace "wlh baxan matsaba ."malam Auwalu ya aje icen hannunsa ya nuna baba asabe da yatsansa yace "naga alamar ke kike daurewa zaliha kugu agidan nan take duk abinda taga dama,"naga alamar Baki damu da halin da xata shiga ba koh?, .yace "to wlh asabe idan kika sake na fita harkarki keda 'yar ki agidan nan wlh kome tayi babu ruwana, Kuma ko me ZA'Ayi wlh banga Wanda ya isa ya canxa min ra'ayi ba "..baba asabe ta kalleshi shekeke tace " in Sha Allah babu abinda xai samu 'yata saidai wasu,"malam Auwalu yace "haka kika ce "?baba asabe tace "kwarai kuwa,"malam Auwalu ya girgixa kai yace" yanxu wannan abun kin taba ganin Nana tanayi,? baba asabe tai murmushin takaici tace "aidama nasan haka xakace wato 'ya'yan maimuna????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? Basa ba dai_dai ba sai nawa 'ya'yan koh, ?,malam Auwalu yace" asabe wlh kibi duniya ahankali, Kuma"daga yau baxan qara Sa miki baki wurin tarbiyar zaliha ba tunda har kina kareta.,Babar ki da ita baba asabe tace" da yafi dai", naji ,Kuma na yarda,.malam Auwalu ya girgixa kai sannan ya wuce dakinsa Yana Mai Jin nauyi akirjinsa.duk wannan abun da ake ummah tana jinsu,tai Allah ya kyauta kawai acikin ranta,tana Mai tausaya wa baba asabe Wacce bataji Bata Gani.....



_____________?&



Tun ranar da AA Arab ya Bada umarnin a dinga bibiyar Alhaji sunusi. tofa aranar suka fara bibiyar sa, aranar Alhaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login