Showing 219001 words to 222000 words out of 278032 words

Chapter 74 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1057

cikakkiyar 'yar makaranta....





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y







____*JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*




*('TAURARI WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 8?? 6??



____________?&


Yau dai da wuri ruky ta shiryawa zata fita wajen aiki saboda ayau za'a sallami shafa daga asibitin,yanzu haka ta fito daga gida tana cikin motar ta tana k'ok'arin tadawa taga K'iran AA Arab ya shigo wayarta take ta saki murmushi bayan taga me K'iran, cikin daddad'ar muryar tai picking call d'in Sannan takai kunne tare da sallama sai Kuma tai shiru tana sauraran sa, daga D'aya bangaren AA dayake Cikin office tun tuni yana jiran ta yace cikin cool voice d'insa.


"Fiancee kin fito ne?" Ya fad'a Yana sauraran ta.


Ruky tai murmushi kafin ta ce.

" I'm on my way"

Ya lumshe ido kafin yace .


"Ki biyo ta office idan yaso sai mu wuce asibitin tanan tare ".


Ruky tai shiru kamar bazatai magana ba sai Kuma ta ce.


"Alright saina zo "..

AA Arab yace .

"Thank you,sai Kun k'araso ". daga sukai sallama, ruky tai murmushi bayan ta sauke wayar kafin ta ta-da motar me gadi ya Bud'e mata get ta fita daga gidan gabad'aya....


Bayan ta shiga office d'in tana K'arasawa bakin table d'in ta AA Arab ya Bud'e k'ofar office d'in sa ya fito ya tsaya Yana kallan ta kafin ya langwab'ar da kai Yana D'an had'erai yace.


" meyasa da kika shigo Baki zo kin cemin kin zoba?".ya fad'a Yana narke mata.


Ruky ta kalleshi kafin tai murmushi ta ce.


"Yanzu na shigo fa, Kuma kaima nasan jin shigowar danai ne yasa ka fito".ta fad'a tana murmushi ...


AA Arab ya lumshe ido ya sauke akan Dyan k'aramin bakinta da yay maganar kafin yay saurin d'aukewa saboda yadda jikinsa ya k'ok'arin mutuwa lokaci D'aya,Yana kallan ta ya k'araso har gabanta ya tsaya ya zuba duka hannayensa biyu acikin aljihun suits d'insa Yana kallan ta, ruky ta sunkuyar da kanta k'asa tana Jin baza ta iya jure kallansa ba, AA Arab yay k'asa da murya yace.



" u know what fiancee?".


Ruky ta girgiza kanta har sannan kanta Yana k'asa. Ya Kara yin k'asa da murya yace.


"I miss you".


Ruky ta k'ara sunkuyar da kanta k'asa tana Jin Wani Irin mugun sonsa na fusgarta...

ganin kunyarsa take ji Yasa ya bar zancen kafin ya Kalli watch d'in hannunsa ganin lokaci na tafiya yasa yace.


"Let's go" ya fad'a Yana yin gaba.

Ruky ta d'auki handbag d'inta kafin ta bishi Yana gaba tana binsa Abaya,har suka isa parking lot d'in inda yake parking motar sa,gabadaya ma'aikatan suna nan kowa Yana bakin aikinsa wasu har sun fara zargin wani Abu a tsakaninsu su ganin yadda Ruky da AA Arab suke fita tare, Amma babu damar magana Haka nan suka bisu ta kallo ciki kuwa harda DCP Daya shigo cikin headquarter yanzu,ya bisu da kallo kafin ya K'arasa bakin office d'insa Yana kallansu gaban sa Yana fad'uwa Yana tananin shima Wani Abu daban.


AA ARAB da Kansa zaiyi driving d'in saboda Yana San ruky ta K'ara sakewa Dashi,ya shiga mazaunin driver Ruky Kuma ta shige gefensa, wato kujera Mai zaman banza...


Ya ta-da motar suka fita daga cikin headquater bayan an Bud'e musu get d'in...

A hanya Babu Wanda Yay magana acikin su, ganin shirun yayi yawa yasa AA Arab Yana kallan Ruky Yay k'asa da murya ya ce .


"Fiancee" ya fad'a Yana D'an kallanta kafin ya Kalli hanya.


Ruky ta juya tana kallon sa da dara daran idanuwanta, Amma Batai magana.


AA Arab yay murmushi yace .

"Meyasa har yanzu kike Jin kunya tane ?".ya fada Yana kashe mata ido D'aya.


Ruky tai murmushi sannan ta Maida Kallan ta kan titi tace cikin sanyin murya.


"Me ka Gani?".

AA Arab Yana murmushi har sannan ya ce .

"Gashi tunda muka shigo motar nan bakiyi magana ba "?.ya fad'a Yana kallanta.


Ruky tai murmushin da Bata shiryaba kafin ta kalleshi ta ce


"To me zance?"..


AA Arab Yana kallan titin gabansa yace.


"Bani labarin soyayya ta, shin tana k'aruwa a zuciyar ki ne ko kuwa", ya fad'a Yana tsaida idansa akanta"...

Ruky ta rufe fuskarta da tafukan Hannunta tana murmushi ta ce .


"Sir wannan tambayar tamin girma da yawa".


AA yay Wani Miskilin murmushi kafin yace.


"Shikenan tunda baza ki fad'a min ba,ni Kuma bari na fad'a miki tunda ke kink'i fad'a min.yana kallan titi yace..


"Fiancee! a kullum soyayyar ki K'ara ruruwa take acikin zuciyata ,har mamakin kaina nake yadda babu Wani seconds ko minutes da zai wuce Batare da nayi tunanin ki ba,ko Kuma tunaninki Bai fad'o min arai ba,ni kaina bansan iya adadin k'aunar da nake miki ba,ya juya Yana kallan ta kafin ya cigaba yay K'asa da murya yace.


" fiancee! I love you more than what you expected,Ina sonki Ina kuma K'aunar ki , wacce bansan ta Yaya zan fara bayanin taba kawai ni dai abinda na sani Kuma nake fara shine Bai wuci Allah ya nuna min ranar da zan mallakeki a matsayin mata ta ba,ya k'arasa fad'a Yana zubawa ruky lumsassun idanuwan sa Wanda ko Bai fito ya fad'a mata ba ,ruky taga tsan tsar soyayyar ta a fuskar AA Arab dama zuciyar sa , take ruky ta rufe fuskarta tana Jin tamkar Ita kad'ai tai Sa'ar samun saurayi Irin AA Arab a rayuwa tana Jin Wani Irin soyayyarsa na k'aruwa a Zuciyar ta da duka sassan jikinta gabad'aya,AA Arab ko ya Maida kallansa kan titi ganin Yana Neman barin nutsuwar sa,haka motar nan tai shiru har suka isa asibitin...



Gabad'aya suna tsaye a bakin motar AA Arab har da baba lami da shafa,bayan doc ya sallamesu ,ruky tana tsaye kusa da shafa da baba lami, AA Arab Kuma Yana tare da doc Bala da Kuma doc Fatima da sukayo musu rakiya zuwa Bakin motar su, doc Bala ya mikawa AA Arab hannu sukai musabaha kafin ya ce .


"Ranka ya Dad'e Allah ya kiyaye thank you very much".ya fad'a Yana murmushi.


AA Arab ya Maida masa da Martanin murmushin sa kafin ya ce .

"Muke da godoya doc Allah ya Saka da Alkhairi".


Doc Bala ya ce .


"Allah ya kiyaye Allah ya K'ara lafiya".ya fad'a Yana kallan baba lami.


Baba asabe ta Ansa da Ameen tana masa godiya,daga haka ya juya ya koma cikin asibitin,.ita koh doc Fatima ta tsare AA Arab da ido tana masa Wani kallo kamar ta had'iye shi,Karaf akan idon ruky tana kallan ta tana kuma tunoda magan ganun Hanan da take mata ranar,take taji Wani Abu Mai kama da kishi koma tace kishin ne ya tsaya mata a wuya Batasan lokacin da ta dinga Hararar doc Fatima ba ...

Ganin AA Arab na shirin juyawa yasa doc Fatima ta ce cikin in Ina .


"am yallab'ai Ina son magana da kai".ta fad'a da wata Irin murya wacce tasa Ruky taji tamkar mashi ta soka mata,..


take ruky taji Wani Abu Mai d'aci ya tokare mata wuya,ta Kalli AA Arab taga zai je ko Kuma bazai jeba,sai me kawai taga ya juya Yana kallan doc Fatima kafin yace .

"Ok Ina jinki?" Ya fad'a Yana kallan ta .


Doc Fatima ta marai raice kafin ta ce.

" idan badamuwa inaso mud'an ja gefe tukunna ta fad'a tana kallan sa.


AA Arab yay jmm kamar Bazai jeba sai Kuma ya ce .

"Alright ba damuwa".

Daga haka ya bita suka D'an tsaya nesa dasu..


ruky ta cika tai fam tana kallan AA Arab ko zai kalleta Amma taga ko ya juya bare ya kalleta Hakan yasa ta kalli baba lami bayan ta Bud'e musu back seat tana seta yanayin ta tace.

"Baba ku Shiga"ta fad'a tana k'ok'arin boye abinda yake San bayyana a saman fuskarta wato b'acin Rai, Babu musu baba lami ta shiga ita da shafa tana cewa "to jami'a".


itama Ruky ta matsa bayan ta rufe musu motar ta shiga front seat tana Jin zuciyar ta na Neman tar watsewa ganin AA Arab Bai dawoba,kasa juya wa ma tai bare ta Kallesu tunda ba nisa sukai dasu ba,Saida suka kusan mintuna biyar sannan AA Arab ya dawo ya shiga motar Yana kallan Ruky wacce tak'i juyowa nare ta kalli inda yake , Hakan yasa ya D'an juya Yana kallan baba lami ya ce .


"bari Muji baba , Amma ba gidan da kuke ada zamu je ba, Wani ne daban inda yanzu zaku cigaba da rayuwa acikin sa in Sha Allah",ya fad'a Yana k'ok'arin tada motar ,baba lami ta ce.


mungode sosai yallab'ai Allah ya Saka da Alkhairi,ta fad'a kamar zata Ari Baki saboda godiya AA Arab yay murmushi kawai Amma baice komai ba ,har suka bar asibitin baiga ruky ta kalleshi ba,shima yay shiru baiyi magana ba Amma Yana tunanin meya sauya Yana yinta lokaci D'aya haka kamar zai magana Amma yay shiru ganin su baba lami a motar ,sunyi tafiya Mai D'an nisa kafin suka isa wata unguwa Mai manyan gidaje,kafin su tsaya a Wani k'aton gida Masha Allah,ita dai baba lami sai baza ido kawai take a wannan k'aton gidan ,bayan yayi parking AA Arab ya juya Yana kallan baba lami ya ce,


"Ga gidan nan baba munzo",ya fad'a Yana satar kallan Ruky ganin yadda tai kicin kicin da fuska...


Ita dai baba lami kallan wannan tangameman gidan kawai take ,kafin tace .


"to ranka ya Dad'e cikin rawar Baki da Kuma mugun shock data shiga lokaci D'aya ta fito daga cikin motar shafa ma ta fito suka tsaya suna k'arewa gidan Kallo,kafin ruky itama ta fito AA Arab yay murmushi Yana binta da Kallo kafin shima ya fito,duk suka tsaya ya k'arasa har bakin Bud'e get d'in gidan ya a'a key ya Bud:e ya juya Yana kallan su baba lami ya ce.


" bismillahirrah ku shigo", ya fad'a Yana Basu hanya,..


Ita dai baba lami batasan me yasa ba ta kasa furta Komai, kawai ko me ya fad'a da to take binsa,Dan jitai kamar an kulle mata Baki da sarqa haka taji,kafin suka shiga cikin gidan gabad'ayansu ...


Bayan sun shiga gidan AA Arab ya tsaya a tsakiyar gidan kafin ya ce.


" baba nan ne gidan da zaku cigaba da rayuwa aciki Ina fatan yayi muku? ".ya fad'a Yana kallan baba lami.


Baba lami kasa magana tai saboda mamaki sai kawai ta fashe da Wani gunjin kuka ganin Irin girman gidan tana kallan AA Arab tace cikin mamakin Daya kasa boyuwa a fuskarta.

" yanzu wannan k'aton gidan ne namu?" Ta fad'a tana kallan AA Arab , shidai Yana murmushi ya ce .

"Eh baba Amma Dan Allah kidai na kukan nan haka".

Baba lami ta ce." Dole ne nai kuka kun min abinda da wuya wasu su yimin a wannan zamanin ,Kunyi iya bakin k'ok'arinku wajen ganin 'yata ta Samu lafiya, sannan kun k'wato mata hak'k'inta gashi yanzu ka bamu gida ni yanzu bansan da Wani Irin Baki zan gode Maka ba " ta K'arasa fad'a tana Mai rushewa da gunjin kuka...

AA Arab ya ce "ki bar kukun Nan haka baba , Allah zaki godewa bamu ba",


itama ruky sai alokacin tai magana ta ce .

"Baba ki daina wannan kukan ki godewa Allah kawai, domin shiya tsara komai Amma mune Sila , kiyi hakuri ki bar ku kan nan muje kiga cikin gidan,ta fad'a tana rik'e hannun baba lami,baba lami ta bita a Baya har cikin karon falon gidan Wanda ya gaji da kayan more rayuwa AA Arab ya gama bubbud'e musu ko Ina na cikin gidan komai yayi sosai ga k'aton falon guda biyu ga d'akuna manya guda hudu ga dining kai Babu abinda babu agidan Nan Dan itama kanta ruky ta Yaba ta Kuma jin jinawa k'ok'arin AA Arab,Saida suka gama Zageye ko Ina na gidan sannan suka yiwa baba lami sallama suka fito zasu tafi su baba lami suka rakosu har gaban motar da suka zo da ita , sannan ruky tana kallon Baba lami da murmushi a fuskarta tace .


"In Sha Allah baba zan dinga zuwa ina duba ku, lokaci bayan lokaci",ta fada tana murmushi.


Baba lami tace.


"Shikenan jami'a! Allah yasa,mungode sosai Dan Allah ki K'ara yiwa yallab'ai godiya ".


Ruky ta ya Jin Jina mata kai kafin tace .


"In Sha Allah baba".

AA Arab yace "zamu dawo in Sha Allah baba idan an kwana biyu zan dawo domin za'a Saka shafa'atu a makaranta idan har ta K'ara samun karfin jikinta ".


Baba lami tace .

" To! Harda wannan wahalar kuma? Kafin ta cigaba ta ce "Shikenan yallab'ai mungode, mungode sosai Allah ya Saka da Alkhairi " ta fad'a tana matse k'walla.


Suka ansa da Ameen Sannan suka shiga mota ,saidai baba lami ta daina Ganin motarsu sannan ta shige cikin gidan tana Mai Jin Wani Irin farin ciki na mamaye mata duka Zuciyar ta Wanda ta Dad'e rabon ta dashi....


A ahanya babu Wanda yayiwa Wani magana acikin su, shidai AA Arab daurewa kawai yake Amma Kuma take ya gane fushin Mai ruky takeyi Dan haka yay shiru yafison idan suka isa office sayi magana...



Suna isa cikin heardquater ruky tai saurin fita daga motar ta bar AA Arab da binta da Kallo Yana mamakin wannan kishin sa da akeyi haka, azuciyarsa kuma yace Ashe ana sona shine ba'a nuna min kafin Yay murmushi ya fita daga motar...


Ruky ta zauna kan kujerar ta,har AA Arab ya shigo tana ganinsa ta juyar da kanta gefe,ya k'araso har gabanta Yana kallan ta kafin yay k'asa da murya yace.


"Fiancee Fushin me kike Dani haka?". Ya fad'a Yana kallan ta ...

Ruky tai banza ta k'yaleshi saima tura Baki da tai gaba.

Yayi murmushi Yace "ok na Gane wallahi ba bunda kike tunani bane ,magana tamin akan magun gunan shafa sannan ta nemi na bata contact d'ina ni Kuma nace mata tayi hakuri ina da matar da zan aura saboda na Gane me take nufi", ya fad'a kamar zai Yi kuka Dan wallahi bayason ya samu matsala da ruky,ko Kuma tai fushi dashi dan bazai iya d'auka ba...

Ruky ta juya tana kallon sa kafin tace cikin b'acin Rai .


"shine taja ka gefe ko? Idan maganar magani zatai Maka Mai zaisa taja ka gefe tace zatai magana da kai aida agabanmu zatai Maka magana, na miye saita jaka gefe kuyi magana",ta fad'a tana tsare shi da idanuwanta..


AA ya rasa ya zaiyi kafin yace cikin k'asa da murya.


"Look Rukayya billah abinda na fad'a miki shine gaskiyar magana, Amma kema kinsan bazan tab'a Yi miki k'arya ba",ya fad'a cikin damuwa..

Ruky ta ce .

"Hmmm idan iya wannan maganar kukai me zaisa kuje ku Dad'e Kuna magana".ta fad'a tana tsaida idanta a kansa ..


AA Arab ya dafe kansa kafin yace

"Idan har kin yarda Dani billah iya gaskiya na fad'a miki,ni Ahmad bani da wata mace idan ba Rukayya ba,Babu wata mace da zata samu wuri azuciya ta har naji Ina son ta idan ba keba, Rukayya! a akanki na faro so akuma kanki zan k'are ". Ya fad'a Yana k'ok'arin ganin ta yarda dashi..

Ruky tai shiru tana sauraran sa kafin ta sauke numfashi tace.


"Shikenan I understand u"


"AA Arab yace .


" To yanzu Kin yadda"?.


Ruky tace "eh saboda na yarda da kai nasan Kuma baza kamin k'arya ba shiyasa , Amma Dan Allah karka K'ara wallahi bazan iya d'auka ba" ta fad'a da wata murya wacce takusan zautar da AA Arab.take Yay murmushi Yana kashe mata ido D'aya kafin yace .


"Dama Haka ake kishina ,Ashe dai ana sona lallai ni nayi Sa'a "ya fad'a Yana wani sunkuyo wa da fuskar sa dai dai fuskar ruky.,

Ruky tai murmushi ta rufe fuskarta ta tafukan Hannunta tana Murmushi.


AA Arab yay k'asa da murya Yana shakar kamshi jikinta Yana lumshe ido kafin yace " thank you very much fiancee,i love you more princess" sai Kuma yace "ni Ahmad na Rukayya ne ita kad'ai in Sha Allah"kafin ya d'ago Yana kallan agogon hannunsa ya ce",bari nayi alwala na tafi masallaci lokacin sallah yayi", ya fad'a Yana k'ok'arin barin wajen ruky ta Bud'e fuskarta tana kallan sa tana Jin Wani Sansa na K'ara ruruwa azuciyarsa..




daga haka ya Bud'e office dinsa ya shiga ,ganin ya tafi yasa ruky ta sauke wata ajiyar zuciyar salama tana dafe k'irji Had'i da murmushi lokaci D'aya...



__________?&





*Bayan Kwana biyu*


Ata k'aice dai soyayya mar k'arfi ce ta k'ullu tsakanin masoyan nan guda biyu,wato AA Arab da ruky San Junan su suke kamar me Batare da Wani shamaki ba,yau ya kasance weekend ranar Daya kasance Ranar da AA Arab zai fara zuwa hira wajen ruky,tana d'akin ta ta rasa ya zatai ta sanar wa da mama8 zuwan sa ,kawai sai Wani tunani ya fad'o mata ta sauko k'asa tai d'akin baba hasiya Dan ita kad'ai ce zata iya Samu ta fad'a mata ita Kuma ta fad'awa Mamah, wannan tunanin da tai yasa ta Murd'a k'ofar dak'in baba hasiya ta Shiga ciki....


Baba hasiya tana zaune a bakin gadonta taga ruky ta shigo d'akin da sallama a Bakinta,ta mik'e tana cewa


"A'a uwata kece da kanki"ta fad'a tana murmushi.

Ruky ta zauna kan kujerar d'akin tana kallon baba hasiya tace .

" Nice Baba ,Dan Allah zuwa nai kimin Wani taimako,ta fad'a cikin fad'uwar gaba..


Baba hasiya ta ce .


"To! ni Kuma Kuma uwata? Wani irin tai makone zan miki haka",ta fad'a tana kallan Ruky.

Ruky ta sauke numfashi kafin tace .


"Ya Ahmad ne zai zo to shine nake so ki fad'awa mamah Kuma kar t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aga yazo ban fad'a mata ba ni Kuma kunya nake ji" ,ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa...

Take baba hasiya ta Gane wa take nufi ,da Kuma kunyar me take ji,da dukan alamu ta Gano Wani Abun,Dan haka ta ce .


"Shikenan uwata indai wannan ne babu matsala Karkiji komai,ai ko ke ce kika fad'awa Hajiya haka ai kinsan baza ta k'iba" ta fad'a tana murmushi,kafin tace shikenan bari naje na sameta yaushe zaizo?,ta fad'a tana kallan Ruky..


Ruky tai murmushi tace.

" da yamma",


Baba hasiya tace .

"Shikenan babu damuwa jeki abunki bari naje na sameta",


Ruky tai mata godiya sannan ta tashi ta bar d'akin tana Jin Salama aranta,ba hasiya ta bita da kallo tana addu'ar Allah yasa hasa shen da take ya zama gaskiya,kafin tai murmushi ta mik'e Dan zuwa d'akin mamah ta sanar mata.....



BAYAN Mamah ta gama sauraran Baba hasiya tace .


"To Dan Ahmad d'in zaizo shine sai an fad'a min", ta fad'a tana kallan baba hasiya,


Baba hasiya tai murmushi kafin ta ce .


" To Hajiya ai wannan zuwan da zaiyi na musamman ne",ta fad'a tana murmushi...


"Mamah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login