Showing 198001 words to 201000 words out of 278032 words

Chapter 67 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1059

kadai a hannunta , bayan ta fito ta jingina jikin motar tana qarewa harabar kotun kallo, Wanda mutane sai shigowa suke Babu k'akk'autawa ,AA Arab barin wurin yay waya kare a kunnansa Babu jimawa wasu Barrister's suka fito daga cikin kotun suka nufo AA Arab sannan suka had'e D'an nesa da inda sukai parking motarsu suka tsaya suna magana,ita dai ruky kallan Hajiya SA'A kawai take , wacce ta kasa xama waje D'aya,wlh ji take kamar tai mata kuka sbd yadda ta rame ta Wani susu ce Babu wannan kwalliyar dasaka gwala gwalan nan,sai wani Hange Hange take ,ta rasa me take NEMA,.....



Ruky tana nan tsaye babu dad'ewa motar gidan prison ta danno kai cikin kotun, gabanta da bayan motar gandurobas ce da Motar police guda d'aya,ai Hajiya SA'A Wani Irin xabura tai , Samira da cousin sister dinta suka rirrik'eta,motocin suna yin parking gabad'aya police d'in nan da gandurobas suka dir diro daga motocin su sukai kan wacce su Alhaji sunusi suke ciki gabad'aya suka zagaye ta,aka Bud'e bayan motar take aka fito dasu Alhaji sunusi wanda hannunsu ke sanye da handcuff ga kayan prisoners nan ajikinsu blue sunyi Wani Irin Bak'i da ramewa kamar me,Hajiya SA'A Dake kallon motar tun lokacin da suka shigo har sukai parking idonta na kan motar,hawaye sai ambaliya yake a saman fuskarta,ganin amfito da Alhaji sunusi Wanda shine farko sai babajo Ali dake bayansa,ta Kalli Samira ta ce "ku sakeni naje na ganshi"Samira ta girgixa kai ta ce "a'a SA'A kiyi hak'uri baza su tab'a bari kije kusa dashi ba, ki kalleshi kawai daga nan, Hajiya SA'A ta girgixa kai ta ce "nan yamin nesa da yawa Dan Allah ku kyaleni bazan Yi komai ba kawai ganinsa Zanyi da kyau na dawo,cousin sister dinta ta kalli Samira ta ce "mu k'yaleta Samira tunda har ta ce bazatai komai ba kawai kallans??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a zatai shikenan,Samira ta ce "Anya ko bahijja a barta?kinsan SA'A da raunan niyyar xuciya ba lallai ta iya jurewa ba"bahijja ta ce "mu k'yaleta kawai ta samu nutsuwar zuciya" badan Samira taso ba ta cika Hajiya SA'A.....



Hajiya SA'A ta fara takawa a hankali idan ta akan Alhaji sunusi Wanda ya sunkuyar da kansa k'asa Yana Jin kunyar duniya ta gama lulluab'eshi , Hajiya SA'A kallanshi kawai take tun daga sama har qasa ganin kafafuwansa ko ta kalmi Babu, police d'in Suna gabansu Alhaji sunusi su Kuma ya xamto suna tsakiyar su Dan akwai wasu gandurobas bayansu,tana k'ok'arin tun kararsu suka Daka mata tsawa suka ce karta sake ta k'araso wurin ,hajiya SA'A tasa kuka ta ce "Dan Allah kubarni na ganshi" suka ce "idan kika qaraso wurin nan sai mun fasa miki kai da bindigar nan" Alhaji sunusi duk wannan abin da suke Alhaji sunusi yana jinsu ya sunkuyar da kansa qasa sai alokacin ya d'ago da kansa ya Kalli Hajiya SA'A ganin yadda itama ta fita a hayyacinta sbd damuwa da Rashin kwanciya hankali, Hajiya SA'A ta xube qasa ta fashe da Kuka Mai tsuma zuciya , tana K'iran sunan Alhaji sunusi,su samira sukai saurin qarasowa gareta suka d'ago ta suna Bata Baki , Hajiya SA'A ta rungume Samira ta dinga rusa kuka kamar ranta zai fita,sudai rarrashinta kawai suke ganin lokaci na tafiya yasa suka kama hannun Hajiya SA'A suka shiga cikin kotun da ita....



duk wannan abun daya faru akan idon ruky Komai ya faru saida ta xubar da hawaye bakuma komai ne yasa tai hawayen ba sai Dan tunowa da tai da Abbansu , lallai baiyi sa'ar D'an uwa ba, Allah dai yay Masa Rahma ta share hawayen fuskarta,tana wannan tunanin AA Arab ya dawo wurin ya sameta ,kallo D'aya yay mata ya d'auke idonsa a kanta ya Bud'e bayan motar inda ya zauna ya dauk'o Wani envelope sannan ya rufe Yana kallan Ruky dake tsaye har lokacin ya ce cikin cool voice dinsa "ko anan zakiyi ta tsayuwa? Ruky ta kalleshi sai Kuma ta kau da kai, sannan tabi bayansa gain har yayi gaba.. acikin kotun kuwa ,idan kuka ga yadda mutane suka cika wannan kotun sai kunyi mamaki harda Irin 'yan iskan garin wanda suka K'ona gidajensu su Alhaji sunusi,Dan ayau ma sun k'udiri aniyar indai ba'a yanke musu hukunci ba to su xasu d'auki mataki da kansu, Dan harda makamansu suke tafe babu Wanda ya sani Dan duk sun boye su.bayan an karan to qara agaban kotu, barrister gomnati Wanda suke da qara ya tashi ya gabatarwa da kotu kansa a matsayin barrister Wanda ke qara wato gomnati ,sannan sai barrister su Alhaji sunusi shima ya tashi ya gabatarwa da kotu kansa amatsayin lauyan wanda yake karewa,daga Nan ya koma ya zauna ....



Barrister gomnati ya Tashi ya k'ira su Alhaji sunusi shida babajo Ali gaban kotun,inda ya hau musu tambayoyi,wasu su ansa wasu Kuma suyi shiru,daga nan ya fara gabatarwa da kotu hujjojinsu,shima barrister su Alhaji sunusi ya tashi ya gabatarwa da kotu nasa hojjojin.haka sukai tayi daga wannan ya tashi ya Yi, sai wannan ma ya tashi yayi ,anjima ana fafatawa Dan sun d'auki some hours sunayi ,kafin daga bisani kotu ta tabbatar da cewa su Alhaji sunusi sune Masu laifi ,tunda ra'ayul ainu aka kama su,Kuma sun Fad'i Abubuwan duk da suka aikata ma da bakinsu,sbd haka kotu ta yankewa su Alhaji sunusi hukuncin kisa ta hanyar rataya sannan xasu Bada tarar kud'i na kimanin naira million 200 ko wanne, Dan abawa iyayen yaran da suke satowa su rage zafi , sannan alk'ali ya qara da cewa ba yanxu xa'a rataye su ba,sai nan da watanni biyar masu xuwa sbd har yanxu ba'a gama bincike ba, sannan za'a ware dukiyar su , za'a aware ta Haram data halas daga haka alk'ali ya buga guduwamarsa alamar kowa zai iya tashi,....



Ai Hajiya SA'A ihu tasa daga inda take zaune, ta taso da gudu Tayo gaban kotun xatai wajen Alhaji sunusi, gandurobas d'in nan suka tareta take ta xube ak'asa sumammiya, su Samira sukai saurin tareta,shi kansa Alhaji sunusi runtse ida nuwansa Yaya sbd hukuncin yayi masa tsauri da yawa, ko kallon Hajiya SA'A bai iya ba,sbd haka kawai sai yau Yana Jin kunyar ta bazai iya had'a ido da ita ba,ga babban Damuwarsa shine an yankewa lateef Shima xaman gidan yarin, wannan Abu yayi matukar girgixa shi,Bai tab'a Jin kunyar abinda ya aikata ba sai yau,ji yake tamkar ya nutse haka yaji Dan kunya, yana jin yadda mutane suke zaginsu da aibatasu, Amma babu yadda suka iya.iyalan Babajo Ali Suma ihun kuka suka Saka, shima dai babajo Ali harda hawayensa .take kotun nan ta kaure da koke koke, mutanen gari ko da Wanda su Alhaji sunusi suka zalinta da Wanda dama suke Jin haushin su , sai murna suke suna yuwa alk'alin nan addu'a, shiko barrister su Alhaji sunusi yasha zagi da ihu, suka dinga cewa yaji kunya ,shiko bai kula suba sbd yasan yanayin aikin na sune haka,awannan halin aka fitar dasu Alhaji sunusi daga cikin kotun, kafin kice me 'yan iskan garin nan suka fara jifan su Alhaji sunusi,sai da police d'in suka d'auko bindi gunsa xasuyi harbi sannan suka gudu,da k'yar mutane suka bari aka shigar dasu Alhaji sunusi cikin motar da aka kawo su ,sbd yadda 'yan jaridu kesan wai adole sai sunyi musu tambayoyi aiko ba'a bari ba , Suna shigar dasu suka rufe motar take aka fitarsu daga cikin kotun ma gabad'aya. Hajiya SA'A dai tunda ta Suma Bata farfad'o ba ,su Samira suka d'auke ta suka fitar da ita daga cikin kotun suka shigarta motar Samira wacce suka zo da ita,Dan gabad'aya an k'wace motocin gidan Alhaji sunusi babu wacce aka bar musu......



Ruky jiki a Sanyaye ta fito daga cikin Kotun direct motar AA Arab da sukazo da ita ta nufa ta Bud'e zata shiga saiga Khalil nan ya taho daga bayan ta yana K'iran sunan ta, ruky ta juya Jin ana K'iran ta,ganin Khalil ne yasa ta tsaya tana kallansa harya k'araso inda take tsaye,ya k'araso fuskar sa dauke da murmushi Yana kallan ta ya ce "ranki ya Dad'e kinshigo Ashe,ina tai miki magana tunda kika fito Baki jiba" ruky tai murmushi tana kallan Khalil ta ce "wlh Khalil na shigo ya gida yasu mama"Khalil yay murmushi ya ce "lafiyansu lau "ruky ta ce"Masha Allah" Kahlil ya ce "nasan ranki Dadad'e duk da D'an uwan mahaifin kine zakiji babu Dad'i da wannan hukuncin da ake yanke masa duk da abinda ya aikata muku? Amma Ranki Dad'e Dan Allah inaso kar kisa abunnan aranki kiyi hkr"ruky tai murmushi ta ce"Kahlil"ko kad'an banji haushin wannan hukuncin da kotu ta yankewa uncle ba, hasalima Gani nai wannan hukuncin data yanke musu shine dai dai dasu,karka manta fa mahaifina ya kashe min, sannan Nima ya sace ni akan gsky ta ,bai tsaya iya nan ba ya dinga axabtar Dani,ya kuma yi ik'irarin saiya kashe ni,uwa uba ya kusan b'atamin rayuwa ta ,to Kuma Wani haushi zanji bayan shima an masa hukunci ne dai dai da abinda ya aikata, kawai haushina D'aya ne,Daya kasan ce shid'in D'an uwan mahaifina ne ko yaya nasan idan aka tashi kwatance za'a Dan gan tashi da mahaifina to wannan shine damuwa ta Amma bawai hukuncin da aka yanke masa ba"Khalil ya sauke numfashi ya ce "gsky ne duk abinda kika fad'a ranki ya Dad'e Allah yasa mufe karfin xuciyar mu" ruky ta ansa da Ameen,sun Dan Dad'e suna hira kafin Khalil yay mata sallama ya tafi .....



Ruky tana nan tsaye DCP ya hango ta, Aiko ya taho gunta,ita ko ruky ta had'e Rai tana latsa wayarta ya qaraso da murmushi a fuskarsa yay qasa da murya ya ce "my" meyasa kika k'arya ALKawarin da kika min? ruky ta d'ago ta kalleshi zatai magana ta hango AA Arab Yana tahowa ai tuni ta bar wajen ta Bud'e motar back seat ta shiga ,shidai DCP mamaki ta bashi,to meyasa tai masa haka,ya bita da kallo kawai , sai ya juya yaga wata Gani har tai saurin shiga mota haka,kawai juya war da zaiyi suka had'a ido da shi,take kunya ta kama shi ya sunkuyar da kai qasa,AA Arab ya qaraso wurin Bai ko Kalli DCP ba Yana k'ok'arin Shiga Motar DCP ya ce cikin basarwa"sir congratulations"AA Arab ya kalleshi Babu yabo babu fallasa ya ce "thank you" daga haka ya shige bayan motar driver ya ta-da motar Dan barin wurin,sai a sannan DCP yay baya da sauri yana mamakin wannan Abu tsakanin ruky da AA Arab Kuma.....



Acikin motar kuwa,tunda ruky taga AA Arab ya shigo motar Bata yarda sun had'a ido dashi ba ,tama juyar da kanta gefen window tai,ga wayar ta sai ringing take Amma tak'i tai picking sbd tasan halinsa , Kuma ba kowa bane ke kira illah Hanan,dan yau ma dai Bata samu xuwa kotun ba bama sa garin ita da first lady sunje Abuja,shima AA Arab baiyi Mata magana ba haka motar tai shiru har suka je headquarter.....



___________?&


Da yamma wajen k'arfe biyar da Rabi lokacin tashin ruky yayi AA Arab Kuma ya samu Wani emergency call a time d'in ,ruky ta fito daga headquarter ashe DCP ya biyo bayan ta Bata sani ba,tana nan tsaye bakin titi tana jiran napep saiga DCP ya fito daga headquarter ya k'araso har Inda take tsaye yay mata sallama, ruky ta juya kawai sai ganin mutum tai agefenta, ta D'an matsa baya kad'an tana had'e Rai ta ce "sir Dan Allah ka k'yaleni,na ce kayi hakuri inada Wanda zan aura"DCP ya ce cikin damuwa"my" Dan meyasa kike ta wahalar Dani haka ne? ya fad'a kamar xaiyi kuka,ruky qara tsuke fuska ta ce "niba wahalar Dakai nake ba hasalima ni so nake karna wahalar dakai kayi hakuri kawai"DCP ya ce"Amma meyasa"ruky ta ce"sbd agida an hanani kula kowa Kuma ansa adinga kula Dani Dan Allah karka sa ma Wanda aka sa d'in yaxo ya samemu nida kai ya fad'a agida,kaga ranar ma Saida aka kusa a fad'awa mamah ,DCP ya ce cikin damuwa"Dan Allah ki bani dama Rukayya na gabatar da kaina agidan ku,idan har kika bani dama ni Kuma in Sha Allah bazan qara takura miki ba" ruky ta rasa ya zatai dashi ya kasa fahimtar ta har yanxu kawai ta juyar da kanta gefe aiko saiga motar AA Arab nan ta fito daga cikin headquarter d'in, Tayo bakin titin,take ruky ta rikice shikenan kuma ai yau Kuma Batasan me zai ce mata ba, DCP Daya juya shima yaga me take kallo take ya ji kunya ta kama shi , ya juya sum sum Yabar wajen tun kafin ma AA Arab ya Kara so ya tadda shi....



Ruky ta sunkuyar da kanta qasa gabanta Yana fad'uwa,har motar ta fara tunkaro inda take tsaye ,Dan shi kad'ai ne acikin motar shike driving din ma sbd ba nisa xaiyi ba shiyasa ya karb'i key d'in wurin driver ya ce da kansa zaiyi driving,Bayan yazo sai tin inda ruky take tsaye kamar baxai tsaya ba sai Kuma ya tsaya yana Mata Wani mummunan kallo ita dai ruky Bata d'ago ba,sai Jin muryar sa tai a tsakiyar kanta,bawai da k'arfi yay maganar ba,Amma a kausashe yayi ta Kuma cikin nutsuwa ya ce "wato Baki daina Abinda kike ba koh? shine sbd kin Raina ni,sbd ban isa da keba kina so ki nunamin cewa "to tunda na hanaki aciki bari ki fito waje ku hadu dashi koh? ruky ta d'ago da mugun mamakin zancensa ta kalleshi a Sanyaye ta ce "shine fa ya biyo ni Ina nan tsaye Ina Jiran napep" AA Arab ya ce "shut up"wato ke ko kunyar k'arya ma bakya ji koh? Ruky ta ce "wlh da GSK nake" AA Arab ya kauda kansa gefe ya ce shigo kafin na fito na same ki awurin nan, ruky ta tura Baki gaba ta qasara warin motar zata Bud'e back seat ta shiga yay mata Wani kallo kafin ya ce " driver ki ne ni? Ruky ta matsa xuwa front seat ta shiga,tana tura Baki gaba,yay kwafa ya ta-da motar suka tafi sun fara tafiya batareda ya kalleta ba Yana kallan hanya ya ce "Kuma ayau duk abinda kike aikatawa sai na fad'awa mamah,Dan baza kisa abani amanar kulawa Dake ba sannan Ina kallo kina abinda kika ga dama Kuma na xuba miki ido Ina kallon kiba, sannan kisa Allah ya kamami abanxa ba"ruky ta marai raice ta ce "Dan Allah sir kayi hakuri wlh shiya zo ya sameni har Inda nake tsaye"ta fad'a kamar zatai kuka,AA Arab ya ce "ai dazu ma muna kotu Ina kallo Kuna tare ko kin d'auka banganku bane ? Kawai k'yale ki nai ,sbd Kinga banyi magana ba shiyasa yanxu ma kika qara Mai Mai tawa koh? Ruky ta ce "wlh alokacin ma shine yaxo ya sameni "AA Arab ya ce "ni ban hanaki soyayya dashi ba Amma ki bari idan kin koma gida saiya zo idan Kwana zakuyi kuna tare wannan nasan kin fita daga hannuna" ruky ta Maka masa harara Amma Bata bari ya Gani ba sbd gabansa kawai yake kallo ,kafin ta ce " ni ba saurayina bane"AA Arab ya ce "whatever ma I don't care"sannan yay shiru baice komai ba, ruky ta ce "wlh ni dai ba saurayina bane"shidai AA Arab baice komai ba har suka isa unguwar su Ruky,bayan yay parking a kofar gidan ya kalleta,ganin tak'i fita ya ce "what" Ruky ta marai raice ta ce "dan Allah sir karka fad'awa Mamah"ta fad'a kamar zatai kuka "AA Arab ji yay kamar Yay dariya sbd shi har ya manta ma da yace zai fad'awa mamah, Amma saiya tsuke fuska ya ce "kina b'atamin lokaci malama ki fita"ruky ta ce"Dan Allah sir"AA Arab ya ce "idan Baki fita ba zakisa na fad'a matan ma "Jin haka yasa ruky ta fita,bayan ta sauka tana kallan sa ta ce "thank u sir "shidai AA Arab Bai ce mata komai ba ya juya yay rivers sannan ya bar wajen,ruky ta bishi da kallo sannan ta juya ta shiga gida tana sauke ajiyar Xuciya......







07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y






*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*(' TAURARI WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM THE 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 8?? 0??


___________?&


*ZARI'A*


"Zaliha! Zaliha!! Zaliha!!!"baba asabe tai ta K'iran sunan zaliha Jin tak'i fitowa daga dak'in,Wanda tun d'azu take ta K'iran ta akan ta fito ta tafi Tasha,bayan ta gama abincin tun d'axu.zaliha ta fito daga cikin d'akin baba asabe da gudu ta xube a tsakar gidan tana kwarara amai , baba asabe ta saki Baki da hanci tana kallan zaliha Data xube a tsakar gidan tana kwarara amai ,da mugun mamakin meya samu zaliha haka,sai Wani k'ak'ari take kamar zata amaryar da hanjin cikinta, bayan ta gama ta dinga sauke numfashi a wahalce,baba asabe ta taso daga bakin murhun da take xaune ta tsaya akanta tana kallan yadda zaliha ta galabaita sbd aman da tai, ga sai Wani numfarfashi take saki,da k'yar ta iya Bud'e Baki tana kallan zaliha ta ce "zaliha meya sameki haka? kardai kice min tun xazzabin ta kikace kike kinayi Tun shekaran jiya shine Bai sake ki ba? zaliha ta d'ago da kanta da k'yar tana kallan baba asabe ta gyada mata kai cikin azabar da take ji.Baba asabe ta ce"Ina kin ce min kin sha magani?zaliha ta mik'e Dak'yar tana Jin yadda jire ke neman kada ta k'asa tana ya Mutsa fuska da k'yar ta ce "eh Babar mu Nasha"baba hasiya tai saurin rik'eta ganin yadda take layi tana Neman fad'uwa ta ce "bari to ajima asiyo miki maganin zazzabi ko Kuma na maleria nasan bazai wuce maleria ba"ta fad'a tana kallan zaliha,zaliha ta gyada mata kai kawai Amma batace komai ba Dan sai wani Jin tashin zuciya take ,baba asabe ta rik'e ta da kyau ganin tana k'ok'arin fad'uwa ta kaita har d'aki,tasa ta ta kwanta,bayan zaliha ta kwanta baba asabe ta dubeta da damuwa a fuskarta ta ce "ga nayi abinci zaliha yanxu ya zamuyi dashi?mardiya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login