Showing 174001 words to 177000 words out of 278032 words

Chapter 59 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1056

suke tare da matansu, xa'a je kowa ataho da matarsa sauran biyun a kauyan Kaduna suke sai shi d'ayan Daya rage a hayin rigasa gidansa yake wato Kabiru, ASP Anas da sajen jabir gidan Kabiru aka tura su wato gidan Ameenah.wajen karfe 4:30 na yamman Ranar, Ameenah tana zaune atsak'ar gidan ta tana yiwa maman saude kitso sai hira suke daga xaunan da suke,sau??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????de Kuma suna waje suna wasa da yaran unguwar ,can suka ga saude ta shigo gidan da gudu tana haki tana kallan Bakin kofar gidan kamar wacce tai gudun tsere, gabadaya suka tsaya suna kallan da mamakin meya sata gudu haka , babar saude tai tsaki ta kuda kai sai Kuma ta kalleta ta ce "meye kika shigo da gudu kina haki kamar wacce aka Koro" ta fada tana Dan hararar ta, still saude tana haki tana nuna kofar gidan ta ce "umma 'yan sanda nagani anan kofar gidan,ta fada tana
Nuna kofar,gabadaya sai suka kalli juna sannan suka kalli kofar,kafin maman saude ta ce "cikin mamaki 'yan sanda Kuma saude? Saude ta gyada mata kai kafin ta ce "wlh ummah sune suna nan k'ofar gidan" kafin maman saude ta samu zarafin magana sukajiyo ana sallama ak'ofar gidan, tareda bugu,cikin rawar jiki maman saude ta lullube kanta da hijab dinta,ta kalli Ameenah wacce take zazzare ido tana mamakin meye kawo 'yan sanda kuma kofar gidan, adai dai lokacin da aka qara buga kofar gidan maman saude ta ce cikin rawar Baki "Ameenah tashi kije ki gano suwaye?....



Ameenah ta mike cikin mutuwar jiki ta shiga dakinta ta dauko hijab dinta sannan ta fita kofar gidan adai dai lokacin da aka qara buga gidan gabanta na faduwa,ta qarasa ta Bude ,ai sai wani sabon tsoro ya kama ta ganin fa da GSK ne 'yan sandan ne sukazo,da k'yar tai musu sallama suka ansa mata da kulawa, ASP Anas Yana kallan ta da kyau ya ce " nan ne gidan Kabiru? Jiki asan yaye Ameenah ta gyada masa kai,ASP Anas ya jinjina kai sannan ya ce "Kece matar sa? Ya fad'a Yana k'arewa Ameenah kallo, nan ma Ameenah gyada masa kai tai har lokacin a tsorace take , ASP Anas ya gyara tsayuwarsa kafin ya ce "meye sunan ki? Ameenah ta ce "suna na Ameenah "ASP Anas ya jinjina kai ya ce " Ameenah muna inaso ki bani Aran hankalinki nan sannan ki kwantar da hankalinki da abinda zamu fada miki, mu jami'an tsaro ne , bawai masu cutarwa ba,an kama mijin ki Kabiru da aikata babban laifi ,yanzu haka Yana tsare ne, anan heardquater tamu Dake cikin garin Kaduna" Ameenah gabanta ya yanke ya fadi ras ta ce cikin firgici "meya Aikata yallab'ai? ASP Anas ya ce " babu bukatar kisan meya aikata har harsai kinje can , yanxu abinda xa'ayi muna so ne ki rufo gidan ki Dake xamu TAFI " ya fada Yana kallan Ameenah.....



Ameenah ta dafe kirji ta ce cikin tashin hankali" na shiga uku yallabai ni kuma mena aikata? Ta fada tana zare ido, ASP Anas yay murmushi ya ce " ki kwantar da hankalinki kanwata babu abinda kika aikata kawai dai ana bukatar kije d'inne" karki damu kinji, babu komai yanxu ki shiga ki rufo gidan mu tafi , jiki asan yaye Ameenah ta gyada masa kai,kafin ta koma cikin gidan ,ta tarar da maman saude ta xuba uban ta gumi a inda take xaune tana tunani, Ganin shigowar Ameenah yasata mikewa tsaye da sauri ta tareta tana tambayar ta da GSK 'yan sandan ne meya kawo su wa suka NEMA? Duk ta jerowa Ameenah wannan tambayoyin, Ameenah ta kalli maman saude ta ce "wai Kabiru aka kama Yana can headquarter ta Kaduna shine suka ce zasu tafi Dani" maman saude ta k'walalo ido waje ta ce "headquarter kuma Ameenah ta gyada mata kai wasu zafafan hawaye suna gangaro mata saman fuskarta.....



Maman saude tafe hannu ta ce " mumshiga uku Ameenah meya aikata haka? Ameenah ta girgixa kai ta ce "cikin kukan Daya taho mata "Nima bansaniba" maman saude ta ce "Amma ke Kuma me kikayi da ZA'A tafi Dake? Ameenah ta ce "sunce dole saina bisu" maman saude ta riketa tace"innalillahi wainna ilaihi rajiun,wlh nama rasa me zance " Kuma ke saiki bisu Dan bakida hankali Ameenah"ta fada tana kallan ta,Ameenah ta ce" to ya xanyi Kinga sunce dole sai naje" maman saude ta xauna dab'as a qasa ta ce innalillahi wainna ilaihi rajiun,tarasa Wani Irin tunani ma zatayi , Ameenah ta dubeta cikin mutuwar jiki tace "bari na kira ummah na fada mata" maman saude ta ce ,bani wayar taki ki bari xan kirata anjima saina fada mata, tunda ai kince headquarter ne koh? Ameenah ta gyada mata kai,maman saude ta ce xan kirata na fada mata Dan gara tasan halin da kike ciki"sai Kuma ta saki salati tana sallallami ta ce "kai Allah ne kad'ai yasan me Kabiru ya aikata da har aka kaishi heardquater Kuma axo ace sai antafi dake , Ameenah ta mika mata wayar maman saude ta ce " bari na rurrufo Miki ko Ina , daga haka Ameenah ta shiga d'aki ta daukon wani key din kofar gidan sannan ta jawo kofar dak'in sannan ta Mikawa maman saude key din tana kuka tana komai suka fito kofar gidan itama kanta maman saude kukan take ga Yara sun cika kofar gidan sai kallansu ake harma da manyan kamar Wanda Ameenah ta aikata Wani babban laifin , haka maman tana ji tana gani aka shigar da Ameenah cikin motar 'yan sandan nan aka tafi da ita,maman saude ta bisu da kallo tana addu'ar Allah yasa kar ayiwa Ameenah Wani Abun kafin ta wuce gidan ta tana hawaye ko kula masu tambayar ta me Ameenah tai aka tafi da ita batayi ba,ta shige gidan ta ta rufo kofar Dan Kiran ummahn Ameenah ta fada mata.......



___________?&


A ZARI'A kuwa yau kwa nan mardiya 6 da Zuwa har Kuma lokacin, ummah Batasan meya faru ba Amma ita ta tabbata ba lpy ba,ba kuma Dad'i ne ya dawo da mardiya gida ba duba da yadda ta fita hayyacinta kamar wata mahaukaciya, ba'a fad'a mata ba itama Kuma Bata tambaya ba Dan ma halinta bane shiga abinda babu ruwanta ,Amma tasan ai duk mun daran dad'ewa zata ji,tana xaune a falorn ta wajen karfe karfe shida Saura,taga Nana ta shigo falon bakinta dauke da sallama , ummah ta daga kai ta kalleta ta ansa mata Dan dawowar ta daga islamiya Kenan,ta wuce hanyar bedroom dinsu tashi ga daki tana cire dogon hijab din jikinta taji wayar ummah tana ringing a saman mirror dakin ta qarasa ta dauka taga me kiran Hakan yasa ta fito daga dakin ta fito falor ta mikawa ummah wayar tana cewa "Yaya Ameenah ce" ummah ta karbi wayarta tai picking ta kai kunne Hadi da sallama tana cewa "Ameenah" Mai makon sai taji muryar wata take gaban ta ya yanke ya fadi,daga Daya bangaren maman saude ta gaida ummah, ummah ta ansa cikin karfin hali,sannan ta ce "ummah ba Ameenah bace nice maman saude"....



Ummah ta gyara xama cikin fad'uwar gabar Daya shige ta lokaci Daya ta ce " to Ina jinki" sannan suka gaisa, ummah ta ce "lpy Ina Ameenahr,?


Maman saude ta fada mata komai cikin tashin hankali, ummah Batasan lokacin data tashi tsaye daga xaunan da take ba tana salati tana sallallami ,ta ce "metai ni maimuna? Maman saude ta ce "wlh bansaniba dama na kira ne Dan ku sani" ummah ta ce "nagode sosai,bari yanxu xan kira mahaifin ta in Sha Allah Yanzu xamu tafi daga haka ummah ta kashe wayar,sai ta kai zauna jagab tana maimaita innalillahi wainna ilaihi rajiun Nana da duk ta rude ta qagu taji me ya samu yaya Ameenah,ta matso kusa da ummah ta ce " ummah meya samu yaya Ameenahr? ummah da tuni hawaye ya gangaro mata daga saman fuskar ta ta fadawa Nana abinda ya faru, itama kanta Nana ta firgita ba kad'an, ummah ta ce "ungo wayar nan kira min malam" haka Nana ta karbi wayar jiki na rawa tai darling number malam Auwalu sannan ta Mikawa ummah,ummah ta karba ta mike tsaye ta fara zagaye falon Jin wayar ta shiga ,Saida ta kusan tsinkewa sannan akai picking, ummah ta sakarwa malam Auwalu kuka, malam Auwalu Dake cikin kasuwa ya rud'e yace "maimuna lpy? meya faru? kike wannan kukan ummah dai Kuka kawai take, malam Auwalu ya qara rudewa yace "mutuwa akayi?Dan Allah ki fadamin" Dak'yar Dak'yar cikin Kuka ummah ta fada masa Abinda ya faru Malam Auwalu shima kansa hankalinsa ya tashi ba kad'an ba,sai Kuma ya nutsu ya rarrashi ummah ya ce "maimuna kiyi hkr gani nan xuwa "daga ya kashe wayar , ummah ta dinga kuka qasa qasa tana addu'ar Allah yasa ba Wani abun Kabiru ya aikata ba har ya jawo wa 'yarta xuwa station,tana addu'ar Allah yasa abinda Kabiru ya aikata karya shafi Ameenah, aranta kuma ta kuduri aniyar wannan Karan Ameenah ta gama auran Kabiru, wlh Kuma kome zai faru baza ta tab'a bari Ameenah ta koma gidan Kabiru ba,sai dai duk abinda zai faru ya faru,itama kanta Nana kuka take,tana tausayin yayar tata.....



Malam Auwalu shima kansa a wannan Karan abinda ya faru da Ameenah ya sosa masa ransa ba kad'an ba,ganin lokacin magrib ya gabato yasa Saida yay sallahn magrib sannan ya taho gida, alokacin ko ummah ta masa miss call yafi akirga ,Dan gabadaya Gani take wannan Karan ba malam Auwalu ma ba lallai ya goya mata baya ba akan Ameenah kamar yadda ya saba,malam Auwalu Yana shigowa gidan direct dakin ummah ya nufo ya shigo bakinsa dauke da sallama.ummah ta mike kamar jira take dama da k'yar ta samu tai sallahn magrib sbd yadda hankalinta yake atashe,ta matso ta ce "malam mu tafi " malam Auwalu ya kalleta cikin nutsuwa ya ce "zauna maimuna" ummah ta kalleshi ta ce "bangane na zauna ba malam wai bakaji me na fad'a Maka bane? ta fada tana kallan sa, malam Auwalu ya kwantar da murya yace "naji abinda kika fada maimuna Amma yanxu maimuna bakiga Dare yayi ba, ki bari mana idan Allah ya kaimu gobe sai mu tafi " ummah ta girgixa kai ta ce "malam wlh wannan Karan baxan tab'a yadda da abinda kuke mun ba kana fa ganin headquarter fa akace ankai Ameenah fa,bama division ba,Amma xakace na kwantar da hankalina bansan halin da 'yata take ciki ba,taya xan kwantar da hankalina ,wlh ko kai baxa kaba ni xani, Kuma wlh daga wannan Karan auran Ameenah da wannan yaron marar ASALI ya k'are" ummah ta fada tana huci ga hawaye sai xuba yake.....



Malam Auwalu ya sauke numfashi yace cikin lallashi "duk naji maimuna Kuma na goyi bayanki Amma Dan Allah kiyi hkr maimuna mu barwa goben ,Kuma a wannan Karan dinma Nima baxan hanakiba Amma Dan Allah kiyi hkr ki kwantar da hankalinki kibari idan Allah ya kaimu gobe da safe sai mu tafi Amma yanzu kan ai dare yayi Kaduna fa akace miki, Yanxu tsakanin Kaduna da ZARI'A ai da nisa,Dan Allah kiyi hkr mu barwa gobe "ummah ta dafe kanta Wanda yake barazanar rabe mata biyu haka takeji ta ce "malam hankali na bazai tab'a kwanciya ba, ace Ameenah tana can headquarter Kaduna ni Kuma Ina gida malam Kuma kake tunanin hankali na zai kwanta? Auwalu ya ce "kiyi hkr daurewa zakiyi"ummah ta koma ta zauna jagwab tana kuka malam Auwalu shima zaman yay Yana Bata Baki , Nana tana gefe itama ta hada kai da gwiwa tana nata kukan......



Baaba asabe tunda mardiya ta dawo gida itama take cikin tashin hankali Allah ya Gani daurewa kawai take Yi, ga 'ya'yan ta da bala'in ci kamar me itama kanta mardiya cin ne da ita Dan idan ta xubo mata abinci sai dai taga kwanan, Kuma a hakan ma Neman qari take, gefe Daya Kuma baba asabe tana ta xuba idon taga jamilu yaxo bikon mardiya Amma shiru kakeji gashi har ta kusan sati agida,Dan bataso ko kad'an ummah tasan ansaki mardiya,dan Kada tai musu dariya.ga Kwana biyun nan sai tai ta Jin faduwar gaba ta rasa na mene ne Dan har Wata 'yar rama tai ,sbd Damuwa....


Yanxu ma haka suna zaune da daddaren nan Dan Batasan halin da ummah take ciki ba,sbd itama yanxu ta kanta take Bata damuwar Wani ba,bayan zaliha ta dawo daga wajen Alhaji tanko sunci kaji sunyi bake bake , Baba asabe ta gama k'udurta aranta Dan yau zata kira jamilu ta Bashi hkr mardiya ta koma dakin ta,Dan tun da safe tasa zaliha ta kwafo mara number jamilu a wayar malam Auwalu,ta kalli zaliha Dake ta nuk'u nuk'u da Abu ajikinta ta ce "zaliha bani Aran wayarki a kira jamilu na bashi hkr mardiya ta koma dakin ta" mardiya ta Wani Kalli Baba asabe tace "Ni babar mu wlh Allah bazan koma gidan jamilu ba wai sai kace ban fad'a miki abubuwan Daya dinga munba" baba asabe ta harareta tace "to idan Baki koma ba me zakiyi uban me zakiyi agidan wlh komawa zakiyi" Mardiya ta mike tace wlh Allah nidai baxan koma ba" ta fad'a tana harar baba asabe.baba asabe ta Daka mata tsawa ta ce " ni xaki tonawa asiri mardiya wlh saikin Koma ta dauko takar data sa zaliha ta kwafo mata number awayar malam Auwalu tace "ungo zaliha kiramin shi , zaliha ta karbi takardar ta tasaka number acikin wayarta, Baba asabe tace "kirashi" Babu musu zaliha tayi darling number Kabiru , Saida tai masa Miss call biyu sannan ya daga cikin muryar maye , ita f
dai mardiya tana gefe tana hara rar baba asabe,tana Kuma rantsuwar babu inda zata , baba tace bayan yay picking din "jamilu ne? ta fada da fara'a, daga Daya bangaren jamilu cikin yanayin muryarsa wacce smoking ya gama Huda ta ya ce "eh shine ya akayi? baba asabe ta gyara tsayuwarta tana washe Baki tace "Babar matar kace Mardiya" jamilu yace "ya akayi tsohuwa? baba asabe ta gwalo ido waje cikin fad'uwar gabar yadda jamilu yake mata magana, kamar ba shine da lokacin Yana xuwa gun mardiya xance yake mata biyay ya ba, Amma Daya ke ita take NEMA sai Bata damu ba tace "Dan Allah dama hkr nakira ka na baka kome mardiya tai Maka Dan Allah kayi hkr ka Maida mardiya dakin ta".....


Jalmilu ya kece da wata mahaukaciyar dariya ,sai Kuma ya tsagaita yace "koba hkr ba? kai Amma kin Raina min hankali tsohuwa ,to bari Kiji dama sakin D'aya ne ya rage koh? To na qarashe dayanma na saketa Kinga saki uku kenan? babu kome kenan tsakanin mu koh? daga haka ya kashe wayar sa,ai baba asabe sandarewa tai a inda take tsaye,Batasan lokacin da wayar ta fadi daga hannun taba ta Dora hannu aka tana na shiga uku na lalace ni Asabe.....





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*___JAMI'AR TSARO ___*



*___THE WOMEN POLICE ___*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?____*



*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 7?? 2??



____________?&


Yau ya kasance Ranar alhamis D'aya ga watan aprilu shekara ta Dubu biyu da Ashirin da biyar (2025) Ranar da tai dai dai da Ranar Al'hamis, a kuma Ranar ZA'A fara xaman kotu kamar yadda yaxo a rubuce,a nan shari'a court Dake cikin garin Kaduna, za'a Yi Shari'ar .A cikin harabar kotun na hango mutane sai shiga da fice suke acikin kotun da dukkan alamu dai akwai wasu qarar rakin da za'a Saurara bayan ta gomnati wato Shari'ar su Alhaji sunusi da gomnati ta shigar , ga 'yan jaridu iyayen gul>?-?>?#? afwan,sun iso Suma Dan daukar rahoto.wasu manya manyan motoci ne na hango suka danno kai cikin kotun ajere suke tafiya su_su hudu reras Irin manya manyan motocin nan ne Irin na prison,motar police itace a gaba sai sauran motocin a bayansu, saikuma daga karshe tasu AA Arab da Kuma DCP.bayan sunyi parking duk police din suka diddiro daga motacin su suka karasa gun wad'an nan manyan motocin guda hudu,Wanda su Alhaji sunusi ke ciki da yaran su , police din suka zagaye motocin da bindigusu a hannu fuskarsu babu alamun Rahma atattare su......


Adai dai lokacin da motar asibiti ta shigo cikin kotun wacce su baba lami ne ke cikin ta ita da shafa,sai doc Fatima,Suma sunyi parking a inda aka umar cesu da suyi , Amma Basu fito ba doc Fatima dai ta fito daga cikin motar ta tsaya daga jikin motar itama cikin shigar lokitoci,tana qarewa harabar kotun kallo.....



Sai d'aya motar wacce ta kasance ta su Ameenah suma suna cikin ta ,basu fito ba. A hankali AA Arab ya juya bayan anbude masa motar sa ya fito yana qarewa motocin kallo ganin komai ya kammala yasa ya kalli watch din hannunsa yaga da sauran lokaci , kafin ya furzar da huci me xafi daga bakinsa Yana kallan harabar kotun ganin barrister's din Basu xoba har lokacin,har ya fara takawa xuwa kofar kotun, sai Kuma ya tsaya sakamakon wayarsa datai vibrate ya duba ganin sak'on Daya shigo waryar tasa yasa ya dawo baya kadan ya tsaya ,kamar ance ya juya bakin gate din kotun ya hango motocin suna shigowa,Hakan yasa ya tsaya Yana kallan motocin da ke shigowa cikin kotun, Daya bayan Daya bayan sunyi parking kamar abun had'in Baki adai lokacin da wasu barrister's suke fitowa cikin wasu manyan motoci masu aji Wanda kudi sukai kuka wurin siyansu,cikin shiga Irin ta lauyoyi masu aji , su su uku ne ,ko wanne Kuma motar Dayake cikin ta shi kad'ai ne sannu ahankali suka fara tafiya har suka hadu waje Daya kowa da murmushi afuskarsa sukai musabaha, sannan suka qaraso har Inda AA Arab ke tsaye,suka mika masa hannu daya bayan daya suna gaisawa kamar sun San juna ,kafin naga sunja gefe sun tsaya fuskarsu da murmushi,magana suke sosai,Dan sun d'au lokaci suna magana kafin naga sun tunkari cikin kotun suna tafiya ajere cikin nutsuwa......



Suna isa bakin kofar kotun sukai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login