Showing 96001 words to 99000 words out of 278032 words

Chapter 33 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1036

din wayar ido tana kallan number nasa Bata ko kiftawa, kamar baxatai picking ba saikuma ta fasa, Saida ta kusan tsinkewa sannan tai picking ta kai kunne,Tai shiru,tana sauraran sa, daga Daya bangaren lateef yace cikin kakkausar murya, wato Rukayya ni xakiyi qara koh, Dani da Dady,baijira cewartaba yacigaba da padin, yanxu ke dan Allah Bakiji kunya ba, Baki duba alakar Dake tsakaninmu ba,abarma xancen Alaka, yanxu Ina matsayin mijin da zaki aura ruky kikai karata,kuka hada baki keda wadannan Yan kauyen,sbd anbiyaku kudi koh danku batawa Dady suna Dani kaina,....


To bari Kiji ni lateef nafi karfinki Kuma kema kinsani, tunda har na fito daga headquarter to kotu ma kinsan bazatamin wahala , akashe qarar ba,kum kisa aranki ni xanyi nasara,sbd haka tunwuri Ina mai Baki shawara gara ki janye qarar nan kafin kiga abinda xai biyo baya ,ya ta-da miki da hankali,ya gurbata miki rayuwa , ruky da tunda ya fara magana tai shiru tana sauraran sa, tareda lumshe ido,Jin abinda yake fada yasa tai murmushi, Wanda lateef yajishi har cikin ransa,tace ya lateef kenan kaiyanxu da kake tunanin anbani kudi to wazai bani kudin,kasan ni babu Wanda ya isa ya siyeni da kudi kaima ka sani , domin ni aikina bisa gsky da Amana nake yinsa,Kuma da kake cewa yar kauye ai ahaka ka bita ka keta mata haddi ka wulakanta rayuwar ta,bakaji kyan kyaminta ba,baka duba kauyan cin nata ba,Kuma sannan kasan Wani Abu wlh ya lateef babu abinda Kuka isa kumin ,sai abinda Allah ya rubuta akaina sai faru Dani,ni da Allah na dogara,Kuma alakar da kake fada ni bansan taba indai akan aikinane, xancen nasara kuwa Ina tunanin kamanta Irin hujjojin da muka gabatar agaban kotu koh, reaction din mutanan kotun da na alkali kadai yaci ace kasan inda muka muka dosa,sbd haka Ina mai baka shawara tun tuni gara ka Mika kanka kafin hukunci ya hau kanka...


Lateef yay murmushi me ciwo yace oh really, lallai Rukayya na jinjina kwazanki amaryata,to Rukayya idan nace miki Nina aikata din me xaki iya,me kika isa kiyi akai, bari na tuna miki Wani Abu da kike mantawa dashi,wai kinmanta AURENAH Dake ne,Ina nufin kinmanta da cewa nan da jibi ZA'A daura mana AURE,to idan kikai ruwa kikai tsaki aka kai angonnaki gidan yari,dawa xakiyi angwancin ko jirana xakiyi da AURENAH akanki har nayi shekarun da xa'a yankemin din har na dawo na sameki xaki jirani,ya qarasa fada da ixgilanci,.....



Ruky tai murmushi Wanda ke Kona ran lateef,tace wai ya lateef Ina tunanin ai munwuce wannan maganar tuntuni, nafada Maka cewa ni bantaba cewa insanka da AUREBA, ni amatsayin Dan uwa na daukeka,sbd haka karka qara fadar wannan maganar,karma ka sake batawa kanka lokaci a karo na biyu ,lateef yace wlh Rukayya baki isaba bakida miji sama Dani kema kinsani, tunda har Kikasa nai xaman jiranki na shekara da shekaru, wlh kinsan aure ba fashi,ruky ta qara sakin Wani murmushin tace ni bantaba cewa ka jirani ba, Kaine dai ka daukawa kanka wannan, lateef yace cikin kakkausar murya wlh Rukayya kisa aranki AURE dai babu fashi kijira daga nan xuwa jibi, Ruky tai tsaki tace kaga sai anjima daga haka ta kashe wayar ta,ta jefarta saman gadon, saikuma ta sauka daga kan gadon ta shiga toilet,...


Ba'a dau lokaci ba ta fito daga toilet din tana goge hannunta da towel, sannan ta hawo saman gadon ta kwanta rigin gine ta kurawa pop din dakin ido tana tunani,takai kusan 10 minutes ahaka, saitai saurin kauda tunanin ganin Yana neman yi Mata tasiri azuciyarta,sannan ta Mike xaune ta fara karanto addu'ar bacci, bayan ta gama ta shafe duka jikinta, sannan ta
Koma ta kwanta taja duvet ta lullube duka jikinta, sannan ta gyara kwanciyar ta ta lumshe idanta Babu dadewa bacci ya dauketa,....



Washe gari Ruky ta sauko daga sama xuwa downstairs,cikin shirin fita aiki, rike take da wayarta tana darling number Khalil,da har lokacin Bata shiga, bayan ta gama saukowa ta tarar da mamah tana kallon labarai na safe kamar ko yaushe,a gidan TV na GADANGA,ta qaraso har kujerar da take xaune ta xauna kusa da ita tareda Dora kanta bisa kafadar Mamah tana good morning,ta fada da murmushi a fuskarta...


Mamah ta juyo tareda shafa kanta tace patan Auta ta tashi lpy, ruky tana murmushi har sannan ta ansa da lpy, mamah tace Masha Allah aje ayi breakfast, ruky ta mike ta wuce dining,tana tambayar maman Ina ya hanaf Mamah tace ya fita aiki daxu ,tayi nisa da cin abincin da take ciki,taji anfara sanarwa da cewa an sace ma'aikacin gidan TV na GADANGA TV & RADIO, tareda da nuno hoton sa,da Kuma sunansa akasan hoton, ruky Batasan lokacin data saki spoon din hannunta tava, tareda mikewa tsaye idanuwanta awar waje, jikinta ya dauki rawa bakinta na rawa,ta tunana TV da hannun ta, Amma ta kasa furta Komai, mamah Dake xaune kan kujerarta tace innalillahi wainna ilaihi rajiun, yanxu Kuma tanan suka bullo, wannan wace iriyar rayuwa muke ciki, kullum abubuwan qara tabar barewa sukeyi, Allah ya kawo mana dauki, shikuma ubangiji Allah ya bayyana shi,....


Ruky ta baro dining din ta nufi kofar fita daga falon, hankalinta a mugun tashe,Kuma still tana darling number Khalil,Gani take kamar xata sameshi, kamar Bada GSK bane cewa ansa ce shi,Amma still dai har lokacin Kiran baya tafiya , gani take kamar a mafarki,ta fita daga falon gabadaya, mamah dataga ayanayin data fita,Kuma ko sallamar data Saba mata yau Bata mata ba, yasata mikewa tsaye tana Kiran sunan ruky, Amma harta fita Bata ansa ba, mamah ta rasa meyasa mu ruky da xata fita cikin wannan Yanayin, lokaci Daya,kawai saita bi bayan ta,....


Ruky Batamaji Kiran da mamah take mataba Dan gabadaya Hankalinta baya jikinta,haka ta fita cikin tashin hankali ta Shiga mota megadi ya wangale mata gate taja motar da mugun speed, adai lokacin mamah ta fito daga falon, tabi motar da kallo ganin yadda Ruky taja motar da mugun speed, mamah ta koma ciki hankalinta bai kwanta ba, tarasa ya xatai wa zata kira,kawai saitai deciding data kira Ruky hopping ace tai picking, Aiko cikin iKon Allah tai picking call din batajira cewar Mamah ba,tace mamah don't bother ur self I'm okay, daga haka ta kashe wayar, tana cigaba da driving.idanta akan titi,hankalinta idan yay dubu ya tashe...



Direct gidan TV na GADANGA TV RADIO ta nufa,Dan tabbatar da abinda aka fada, Aiko tana xuwa direct department din su Khalil din ta nufa,Bata ko kallan gabanta,tana xuwa dayake sun Santa sun San yadda suke da Khalil dan wasu daukar ma ko Yan uwane, suka tabbbar mata da cewa tunjiya wajen karfe uku na yamma, Daya bar Yabar office, suke tunanin abin ya faru,su Basu saniba Saida mahaifinsa yaxo wajen karfe 9 na dare,yaxo nemansa, ganin Bai koma gida ba, Kuma ba haka ya Saba musu ba,duk inda xashi saiya fada musu, Kuma Neman duniya ammasa Amma ba'a sameshiba har yau, Jin wannan Batu yasa hankalinta qara tashi ruky tai godiya ta baro gidan TV,....


Ta Shiga motarta direct headquarter ta nufa,sai alokacin hawaye masu bala'in zafi suka fara ambaliya akan fuskarta ta, tana tunanin waye xai sace Khalil,ta fara rera kuka ahankali, tana tausayin Khalil ko Wani Hali yake oho, tana driving Amma kwata kwata hankalinta baya jikinta,sai motocinne kawai suke kauce mata...




__________?&


iKon Allah ne kawai ya kai Ruky headquarter Dan gabadaya Hankalinta baya jikinta,bayan ta fito daga motarta hannunta rike da handbag dinta, fuskarta sai xubar da hawaye take har lokacin, ko lucking motar batai ba,bamata kallon gabanta burinta kawai ta isa office dinta,ta kira Hanan,Karan datai da Abu agabanta yasa ta yin baya da sauri,ta xubawa Wanda taci karon dashi ido tana kallansa Bata ko kiftawa, kamar yadda shima kallan nata yake, ganin Wanda taci karon dashi yasa ta sauke idanta kasa Asaman labbanta tace I'm sorry Sir, daga haka tai gaba abinta, ...



AA Arab ya bita da kallo Yana tunanin itako me take kallo da har ta bigeshi, ganin yanayin Daya ganta aciki ga hawaye jaga jaga a fuskarta yasa ya Gane tana cikin damuwa ne, kawai saiya bar wajen yay hanyar office dinsa,....


Ruky kuwa bayan ta isa office dinta,ta ciro wayar ta daga handbag dinta tai darling number Hanan,babu dadewa tai picking har xatai magana Kuma tai shiru Jin yadda Ruky ta rushe mata da Kuka,cikin tashin hankali hanan ta mike daga xaunan da take ta fara tambayar ruky da lpy meya sameta, Ruky ta qara sautin Kukan ta, cikin damuwa Hanan tace please sis meke furuwa,kiyi nutsu kiyi min bayani mutuwa akayi, cikin Kuka ruky tace Khalil,....


Hanan tace meyasa mu Khalil din, ruky Bata kulataba tacigaba da kukanta ganin taki kulata yasa Hanan ce mata tana Ina, cikin Kuka ruky tace tana office,Hanan tace mata gatanan xuwa ta katse Kiran ganin Hanan ta katse Kiran,wayar Hannunta ta silale qasa,ita Kuma ta Dora kanta kan table din gabanta tana rera kuka,...


Wajen 30 minutes Hanan ta shigo office din Ruky cikin tashin hankali, tana xuwa ruky ta fada jikinta, Hanan ta rungume ruky, tana lallashin ta, saida ta tsagaita da kukunta Sannan Hanan ta xaunar da ita itama ta xauna,ta fara tambayarta meyake faruwa,cikin xubar da hawaye ruky ta bawa Hanan lvr Komai na sace Khalil da akayi,Hanan was speechless &compuse,Tama kasa magana, kawai tai jimm na Wani lokaci sannan ta nisa tace sis su waye suka sace Khalil, ruky tace ni akwai Wanda nake tunani , Hanan tace wa kike tunanin xai iya sace Khalil, ruky tace uncle sunusi nake tunani, Hanan tace meyasa kikace haka, ruky tace sbd Gani yake ba lallai Lateef yayi nasara akan case din ba,wai ranar bakiga Irin kallon dayake jifanmu dashi bane,Hanan tai jimm saikuma tace na gani Amma Kuma bana tunanin uncle sunusi zai iya sace Khalil, Amma baka shaidar mutum,....


Hanan tace bari dai daga nan xuwa yamma saimu bincika Muji,ruky ta jinjina kai,wayar Hanan ce tai ringing,ta duba taga Mai Kiran saitai picking, bayan ta gama saurara tace ok sannan ta kashe wayar, ta dubi Ruky wacce ke kallan Wani wurin daban, tace daga government house ne ake kirana,na samu emergency call, ta dafa kafadar ruky tace sis ki kwantar da hankalinki in Sha Allah xa'a samu Khalil,ruky ta fashewa Hanan da Kuka tace Hanan Khalil bansan aWani Hali yake cikiba, bansaniba ko akan wannan case din aka sace shi, sis idan Wani Abu ya samu Khalil sanadiyyar wannan case din baxan yafewa kaina ba,ta qarasa fada da gunjin kuka,Hanan da itama hawayen harya ciko a idanta ta toshe mata Baki,tana girgixa mata kai,tace kidaina fadin haka sis in Sha Allah bama akan haka bane,sai Kuma ta rungumeta tana patting bayanta tareda lalashinta tace in Sha Allah Khalil he is safe, please sis don't bother ur self with damuwa, addu'a kawai xamuyi in Sha Allah Khalil yana lpy,....



Ta share kwallan Daya samu damar xubo mata a fuskarta tace Ki bari Da yamma idan muka tashi daga aiki,sai naxo muje har gidansu Khalil din Muji meke furuwa, ruky ta gyada mata kai kawai,Hanan ta saketa tace bari naje sis Dan Allah kiyi shiru,ruky tana goge hawayen idanta tace in Sha Allah,Hanan ta mike tace bari naje, ruky itama ta mike Dan ta mata rakiya Hanan ta dakatar ita tace ki xauna basaikinje ba bakiga yanayin da kike ciki ba,sai naxo daga haka ta nufi kofar fita,bayan Hanan ta fita Ruky ta kai xaune jagwab kan kujerar da take xaune saikuma ta Dora kanta visa table din gabanta tana sauke numfashi,...



Bayan fitar Hanan harta nufi gate kamar ance ta daga kanta tajuya ta hango AA Arab tsaye agaban office dinsa Yana latsa wayarsa Hannunsa Daya a aljihun suits dinsa,,har xata wuce saikuma ta fasa ta karasa wajensa, tana murmushi tai sallama, AA Arab ya dago da kansa daga latsa wayar da yake ya ansa mata sallamarta, tai saluting nasa,sai Kuma ta ta sunkuyar da kai ta gaidashi AA Arab ya ansa mata da kulawa,yace Hanan right,cikin Jin dadin sunan ta da AA Arab Bai mantaba ya Ambata tace yes sir, yace ko yauma kin kawo mana xiyara ne,Hanan tai murmushi tace naxo duba sister nane,AA Arab ya jinjina kai yace Masha Allah,Hanan tace sir thank u bari naje yace ok,safe trive, Hanan tace thank u sir,daga haka suka rabu,AA Arab ya shiga office dinsa ita Kuma Hanan ta nufi gate Dan yau bataxo da motarta ba,....




Da yamma wajen karfe biyar da Rabi, lokacin da Ruky ta tashi daga aiki,ta nufi parking lot sanye take da bakin glass Wanda yay mata masifar Kyau,sbd yadda idanta yadan kumbura yasa ta sanyawa Bataso a fuskanci halin da take ciki, danma Allah ya taimaketa su shareef basa nan anyi posting dinsu out side,da ta shiga uku da tambaya awajen Shareef,tsaye yake a bakin office dinsa wayace kare akunnansa kamar ance ya juya ya hangota tana kokarin shiga motarta bayan ta isa parking lot din, Dai dai inda tai parking motarta shima Kuma tasa awurin take,ya xuba mata ido Yana kallan ta,tabbas itace sbd awurin da sukai parking anan itama tai ya ganeta, waya take da Hanan wacce kece mata ta bari taxo ta dauketa tunda ga halin da take ciki, kartai tuki ayanayin data ke ciki,....



Ita Kuma Ruky ta dage xata iya ta bar gatanan xuwa,badan Hanan taso ba, tace to shikenan saitaxo,Yana tsaye Yana kallan ta harta shiga motar tai reverse ta nufi gate aka Bude mata ta wuce,ya sauke numfashi ya koma ciki dama ya gama wayar da yake,....



Bayan fitar ta daga heardquater direct government house ta nufa, Amma ta wata hanya da ba'a wucewa sosai tabi sbd hanyar tafi sauri,Dan ta Isa da wuri, shiyasa itama tabi hanyar,tayi nisa da tafiyar,ta mirror take hango motar da take binta tunda ta baro heardquater ta lura suna biye da ita, Amma bata kawo komai aranta va,Dan daukar ta suma hanya ce ta biyo dasu,...


Ganin Kuma motaci na wucewa jefi jefi yasata kauda tunanin da take,ta cigaba da tukinta,babu zato babu tsammani kawai taga motar Tasha gabanta,sun nufo motarta,cikin tashin hankali ta taka burki tana addu'a tana waige waige, ganin Babu mota Kodaya yasa hankalinta qara tashi,kafin ta farga har sun qaraso inda motarta take, suka Bude inda take suka fito da ita,tana tambayar su metai musu, Amma Basu kulataba xatayi ihu suka toshe mata Baki, suka jata har gaban motar su tana tirjewa tana tambayar su metai musu,Basu kulataba haka suka jefata bayan motarsu tareda shaka mata Wani Abu, take ta silale awurin,tun tana gane halin da take ciki hardai hankalinta ya gushe gabadaya, bayan sun shiga suka ta-da motar su,suka bi wata hanya, daban.....






07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t






*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA)=?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season one ep 4?? 2??




___________?&



Alhaji sunusi tunda abunnan ya faru ko nace tunda aka fara xaman kotunnan gabadaya yake atsorace,Bai tava tunanin Rukayya zatai musu hakaba,yasan barrister Salman, jajirtaccen mutum ne akan aikinsa,indai yasa Shari'a agaba tofa saiya samun biyan bukatar sa sannan hankalinsa yake kwanciya,da wuya kiga ankadashi a shari'a,saidai idan shine yaso,Kuma batun yau, yakeyiwa Alhaji sunusi aikiba,Dan shine ma barrister sa idan Irin wannan ta taso, babban Damuwarsa Ayanxu Dayace yadda Rukayya ta rufe idonta wai tai qarar lateef, amatsayinsa na Dan uwanta, abunnan ya Dade Yana bashi mamaki, Bai taba tunanin Rashin kunyar Rukayya yakai har hakaba daukar sa abin nata iya aheardquater ne Ashe abun nata yafi haka,.....



Kodan Yana matsayin kanin mahaifin ta aita raga masa taji kunyar wannan dangan takar,Dake tsakaninsu, Amma kokadan bata duba wannan ba,tunda yaga anfara zaman kuto ganin Irin hujjojin da barrister shamsu dasu Rukayya suke badawa wlh ya dauka wasa ne, lateef Bai aikataba Kuma har yanxu Bai yadda lateef xai iya hada jiki da wannan yar mitsitsiyar yarinyar ba,yar talakawa qaxama Irin taba,Kuma abinda ya qara bashi mamaki Bai wuci wai gidan da akace na lateef bane Dake can hayin rigasa, yaushe lateef har yay Gini haryay gida a hayin rigasa Amma ace wai Bai saniba,....


Bayan sun dawo gida ya tambayi lateef, lateef ya tabbatar masa da cewa shi qarya ake masa,shi baisan xancen ba , Aiko wannan dagiya da lateef yay na cewa Bai aikataba yasa Alhaji sunusi yadda dashi, Dan SHikan ya yadda da dansa,yasan baxai aikata dinba kamar yadda ya fada masa, Hajiya SA'A itakan ta dasuka labarta Mata ta Wani gun ta yarda ta Wani gun kuma Bata yarda ba, saidai badama tai magana yanxu sai Alhaji sunusi ya hayayyako mata, ita dai ta dage cewar lateef baxai auri Rukayya ba, Tunda ita ba yar arxiki bace,SHikan Alhaji sunusi kitstsima Irin hukuncin da xai dauka akan Rukayya kawai yake,bayan dogon nazarin da yay yasa ya yanke hukuncin abinda xaiyi kafin nan kafin xaman yanke hukunci,Dan yariga daya san cewar ba lallai Lateef yay nasara ba, shiyasa ya zabi ya kau dasu kafinnan kafin ranar, Dan Vai shirya rasa lateef akusa dashiba, bayaso yayiwa alkali tayin cin hanci ya xata cewar dama basuda gsky ba,.....


Kuma karyaje yaki karba ayanke hukuncin cewar lateef shine me laifi Kuma muddun akai haka,Koda ya aiwatar da shirin sa akan su to tabbas xa'ayi saurin ganowar koshi yasa asace su ko Kuma Yana da hannu Asace sun da akayi, shiyasa ya biyo musu ta qarqashin qasa,Dan tabbas da Rukayya ta tona masa asiri, gara ya kau da ita kawai,Dan kwata kwata bayasan abinda zai tava masa siyasar sa,da Kuma mutuncin sa, dazuma agidan TV yaga sanarwar da akai na cewar ansace Dan jarida Mai suna ibrahim Khalil,Yana Gani saidai ya saki murmushin da Bai shirya ba dan tabbas shine,ya furta azuciyarsa cewar anjima Kuma sai ita babar wato sai Rukayya kafin wayewar garin itama a fara cigiyar tata,...


Dama Rukayya da Khalil sune matsalarsa Dan wadannan Yan kauyen bazasu Zame masa barazana ba, yanxu haka Yana xaune agida falonsa Dake sama wajen karfe shida wayarsa ta hau ringing,Yana dubawa yaga masu Kiran take murmushi ya bayyana Asaman fuskarsa Yana shafa gemunsa Wanda ba gashi ajiki,sbd yasan lvr Mai Dadi xa'a sanar masa,bayan yay picking,daga Daya bangaren goga yace cikin yanayin muryarsa yallabai komai ya kammala, itama mundauko ta, Alhaji sunusi yay dariya yace aikinka kullum qara kyau yake goga,abinda xa'ayi kuyi mata Irin yadda kukaiwa, wanna yaron na jiya goga yace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login