Showing 129001 words to 132000 words out of 278032 words

Chapter 44 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1047

Amma har yau ta kasa samun nutsuwa, tunaninta Rukayya ko awani Hali take oho ,Hanan ma tana xuwa akai akai Dan ganin Yaya suke ko xasu bukaci Wani abun,tunda kudi AA Arab ya turawa Hanan ta account din ta Wanda ZA'A cigaba da kulawa dasu,.....



Baba lami kullum saita tashi sallar tsakar dare tana rokon Allah ya kubutar da Rukayya, kullum wannan itace addu'ar ta, Allah karya Basu iKon cutar da Rukayya, shafa itama dai gatanan yau lpy gobe babu.gashi ankusa Yi mata aiki,ga damuwa itama da take ciki na Batan Rukayya da tai kullum itama cikin addu'a take akan Allah ya bayyana Rukayya...



___________?&


*Bayan sati Daya*


A sati Dayan nan babu kalar azabar da Rukayya batasha ba ita da Khalil ahanun yaran Alhaji sunusi,a Kuma yaune take cika sati biyu da sacetan da akayi.ta kode ta rame tayi Baki kamar ba Rukayya ba, kullum tunanin ta mamah da 'yan uwanta dakuma wadanda suka damu da halin da take ciki, aciki kuwa harda Hanan itama tana ranta,adduar ta kullum Allah ya bawa mamah Dan gana , gashi Wani lokacin saitayi mafarkin mamah bata da lpy .tana cikin kewar ta ,idan ta tuno da wannan shike karyar mata zuciya,taji ta damu, tanaso ta koma ga mamah ko da ko na wuni daya ne sai dai babu damar Hakan,ta fawwalawa Allah komai, Allah shine gatanta shi maijine Kuma Mai Gani, Mai sakawa Wanda aka xalinta....AA Arab har yau suna nan suna bin diddigin Alhaji sunusi Amma saidai har yanxu sun gagara samun wani evidence akan sace Rukayya da suke zarginsa dashi , sai dai jiya wadanda ya saka bibiyar Alhaji sunusi sun tabbatar masa da cewa sunga Alhaji sunusi Yana yawan xuwa Wani gida Wanda yake mazaunin kamar gidan hutawarsa Dake can bayan gari, AA Arab take yace "subishi yau suga meyake Yi agidan."babu musu suka ansa masa.da toh .....


A yau Kuma AA Arab yay shiri na musamman Dan xuwa wannan dajin Neman goga,tunda_ tun ranar da suka kai musu hari sau biyu kawai yaje sbd Yana nan Yana shiri na musamman Dan kama goga Dan ba qaramin hatsa bibi bane.,ya aika police dasu xagaye dajin wasu Kuma su shiga ciki su bincika lungu da Sako Dan police aka tura dajinnan sunfi su hamsin. suka Kuma yi abinda yace din,wasu Kuma sun baxu suna Neman goga Amma har lokacin Basu sameshi ba.. wajen karfe hudu da Rabi na yamma AA Arab ya fito daga office dinsa Dan Kiran gaggawa ya samu akan cewa ana tunanin goga Yana cikin Wani kogon dutsi Dake cikin dajin, shiyasa yanxu ya fito da kansa Dan xuwa suyi bincike,take ya Basu umarnin wasu su zagaye kogon.Dan kwana biyun nan a office yake kusan kwana tun ummi na mita harta hkr ta kyaleshi.....



Sun isa dajin a wannan lokacin, akuma lokacin da masu bibiyar Alhaji sunusi Suma suka mara masa baya gab da magrib ganin motar Alhaji sunusi tayi inda suka Saba ganinsa Yana yawan xuwa wurin.batareda Alhaji sunusi ya sani ba Dan ayau yakeso ya kawo karshen komai,a Kuma yau yakeso ya kashe Khalil da Rukayya.tunda xabensu yau saura kwana biyar....AA Arab tunda sukaje wajen karfe biyar da Rabi,dayaje Bai xauna ba Saida ya shiga ayarin Wanda suke binciken cikin kogon Dan Neman goga,tun wajen karfe shida Saura suke Abu Daya har wajen karfe 8 na dare Basu Samu goga ba,AA Arab haryace su hkr kawai yaji ihun mutum cikin kogon Dutse nan ,kafin kace me tuni sun afka ciki , suna kokarin hana AA Arab Amma Ina baiji suba tuni ya shige wajen suma suka mara masa baya suna xuwa suka tadda Daya daga cikin yaron goga ya fadi Yana rike da kafarsa Yana ihun kunama ta harbeshi, Ashe bashi kadai bane aciki harda yaransa kusan su biyar suka buya .AA Arab ya Danko wuyan goga Suma sauran police din suka cakumo sauran suka fito dasu AA Arab ya jawo shi ya fito dashi daga cikin kogon Dutsen ,Dan ya Gane fuskarsa,bayan ya fito ya dauki waya yay kira yace "kowa ya fito daga inda yake ansamu goga.iya wadanda suke suke zagaye dajin aka bari sbd AA Arab yaja tunanin Basu kadai bane ya fiso a duba dajin tsaf.bayan yasa wasu police din su dauko makaman su goga dasuka boye cikin wannan kogon ,atabbatar babu Wani Dan ta'adda aciki . Amma yanxu tunda sun kama goga ai sunyi me wuyar Suma sauran baxasu ga garaba in Sha Allah.....



?& Abangaren Alhaji sunusi kuwa dama indai xaixo wajen su Rukayya sai gab da magrib ko Kuma bayan magrib immediately yake xuwa.kuma duk dare indai zaixo wajen su ruky shikadai yake tahowa,baya tahowa da masu tsarar sa.. Saida ya fara xuwa wajen Khalil ya Bada umarnin a rufe masa fuska kafin yaje wajen Rukayya itama a dauko ta arufe mata fuskarta Dan a waje Daya yake son kashe su..Yana fadar haka ya fice daga wurin direct inda aka kai Rukayya ya nufa.yana isa bakin kofar dakin aka Bude masa ya shiga, sukuma suka koma baya , Alhaji sunusi ya shiga dakin ya rufe kofar bayan ya shiga.Rukayya tana kwance kan tiles .ba bacci take ba kawai dai ta kwanta ne.tayi nisa cikin tunanin da take kawai saijin saukar maganar sa tai cikin kunnanta,ta mike arazane,tana takure jikinta waje Daya....



Alhaji sunusi yace cikin hade Rai "Rukayya xaki fada ko baxa ki fada ba ,wlh daga yanxu shine worning din da zan miki na qarshe daga shi sai kisa , Rukayya ta kura masa ido haryagama maganar sa,kamar bazatai magana ba,sai Kuma ta numfasa cikin muryar ta da Bata fita sosai sbd azaba tace"wlh uncle saidai ka kashenin, Amma wlh bazan taba bin San xuciyar kaba ".Alhaji sunusi yay murmushin dabai shirya ba yace"shikenan Amma kafin na kashekin saina wulakanta rayuwar ki ta hanyar Yi miki fyade, Rukayya ta zaro ido waje cikin tashin hankali ta fara motsa lips dinta jikinta na rawa hawaye na kwaran yowa daga fuskarta ta hade hannayenta waje Daya alamar roko muryar ta na rawa tace "Dan Allah uncle karka min haka gara ka kashe nin kawai, Alhaji sunusi yay murmushi yace"ai wannan ba komai bane,bari na fada miki Abu na qarshe Wanda Babu Wani Mahaluki Daya taba sani daga ni sai shi Wanda na aikawa sai Kuma Allah ....



Rukayya ta kura masa ido dukkan ilahirin jikinta na rawa, tana jiran taji me zaice .Alhaji sunusi ya fara struggling a dakin hannayensa goye a bayansa yace nine nan na kashe mahaifinku wato Dan uwana UMAR MAITAMA, a bala'in arazane Rukayya ta dago tana kallan Alhaji sunusi ta fara nuna shi da yatsa Amma Kuma ta kasa furta Komai, Alhaji sunusi ya cigaba da fadin,ba accident yay ba kamar yadda kuka sani ,sai Kuma ya dakata daga struggling din da yake ya juyo ya Kalli Ruky yace "Saida na kasheshi da hannu na sannan nasa mota nabi ta kansa , atake awurin ya mutu ko shurawa baiyiba,to wannan abin da aka Gani shine kowa ya dauka accident yay, to nine nan na kashe shi da hannu na,bawai accident yay ba ,ba kuma sbd komai nai Hakan ba, saidan sbd Yana kokarin tonamin asiri akan aikin da nake aikata wa,tundaga lokacin da na Gane ya gano Irin Sana'ar da nake ,ya Gano sirrina wanda na shafe shekaru Ina boyewa to tundaga nan na dinga kokarin tayaya xan ga bayansa, nashiga damuwa alokacin daya gano sirrinah ,gashi Kuma jami'in tsaro,Kuma jami'in tsaron ma babba daga IG sai shi a kasar nan,gashi da GSKY da Amana kamar yadda kike dinnan .to wannan abin Daya min shiyasa na kashe shi domin bazai batamin go be naba ,sbd haka kema ayau xaki bishi, tunda naga wannan taurin kannaki gadon shi kikayi ,wannan abun Dana fada miki na fada miki ne sbd ki tafi dashi lahira,kidinga tunawa,nasan daga ke babu Wanda zai qara Jin wannan rufeffen sirrin nawa Dana Dade Ina adanashi ,ya qarasa fada cikin nishadi yana kallan Rukayya.rukayya da tun lokacin Daya fara maganar cewar shiya kashe abban ta tai suman wucin gadi na seconni ,ta nuna Alhaji sunusi da yatsa da muryarta a rarrabe tace ".......






07066508376_______
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t




*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*




*____(MRS SARAKIES)____=?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season two ep 5?? 5??



___________?&



Ankawo su goga headwater wajen karfe 9 na dare , direct ana kawo su bangaren bincike suma akayi dasu .goga daki daban aka ware masa, sbd shine shugabansu .sauran ne aka hadasu waje Daya ko wanne da handcuff a hannunsa da Kuma kafa funsu,da CP da DCP, da AA Arab ne tsaye a haraban headquarter suna magana .bayan AA Arab ya tabbatar komai yayi yadda yakeso AA .Arab ya dubi DCP yace "muktar yanxu abinda xa'ayi shine kuje gida ku huta Tunda yanxu nasan kun kwaso gajiya . DCP yace "sir kai Kuma fa? "AA Arab yay murmushi yace "ni karka damu akwai aikin da Zanyi a office , shiyasa so karkaji komai,CP yace " a office dinka kenan? . AA Arab yace "in Sha Allah" . CP ya jinjina kai yace Nima akwai Wani aikin da zan qarasa a office dina "AA Arab ya daga kafada yace"shikenan kowa yaje babu damuwa,"daga haka kowa ya nufi office,sai dai Banda DCP wanda shi babu abinda zaiyi a office daga nan parking lot ma ya nufa Dan tafiya gida,AA Arab Yana shiga office ya yaji wayarsa Dake aljihun Wandansa Yana vibrate, yasa hannu a aljihun ya zaro ta ganin me kiran yasa yay picking ya kai kunne, daga Daya bangaren akace "ranka ya Dade munsamu gano gidan daya shiga saidai bamu kai ga shiga gidanba ,umarnin ka kawai muje jira ",AA Arab yasa hannu ya shafo goshinsa tareda sauke ajiyar xuciya yace "jabir inaso kuyi kokari wajen shiga inda ya Shigan ko ta cikin dabara ne , nafiso mu samu hujja me karfi tukunna ,so inaso ko kai kadai ne kayi kokarin sanin me yake agidan idan yaje ,me Kuma yake kaishi gidan ,tunda kunce kusan sau biyu Kuna ganinsa Yana xuwa gidan .Kuma sai a Irin wannan lokacin yake xuwa,kaga we need to know what his did at that place.so abinda xa'a Yi daga nan xuwa 1 hour inaso nasan meyake Yi awannan gidan "sajen jabir yace"in Sha Allah sir "AA Arab yace "idan kun gano Wani Abu Wanda yay dai dai da abinda muke xargi inaso karkuyi Wani Yin Kuri,let me know,kawai direct ku Kirani,& be careful"sajen jabir yace "yes sir daga haka sukai sallama.....



AA Arab ya kai zaune kan kujerarsa ya dafe kansa, Wanda ya fara masa ciwo Dan har Wani haxo hazo yake Gani sbd stress da struggling din da yake yawan Yi a sati biyun nan ko kadan baya zama,bare Kuma yay baccin kirki.ya jawo laptop dinma da niyyar yayi Wani aikin, Amma kwata kwata yaji bazai iya aikin ba . kawai saiya ya mike ya koma kan sofa Dake office din nasa ya kwanta, Yana so yadan samu refreshment Kona 15 minutes ne yasan zai iya samun relief,in yaso idan ya tashi sai yayi abinda zaiyi din.....



Mamah haka kawai yau tun safe take Jin jikinta babu Dadi, takejin gabadaya duniyar tayi mata zafi ga Wani faduwar gaba da take taji,Dan xata iya cewa tun bayan da taji wannan labaran dazu da safe taji jikinta gabadaya asanyaye.gashi yanxu har karfe 9 na dare abin Bai sauya Mata ba,sai Wani qaruwa da taji faduwar gaban nata yanayi , Haka nan dai ta daure Dan bataso ta nuna damuwa anty mufeeda ta damu Dan ko kadan Batasan abinda xai ta-da musu da hankali Suma ko kadan.Dan ita Kanta tasan wannan damuwar da take ciki, ba lallai ta fita lokaci Daya ba, dole sai dai da kadan kadan .gara ta dinga daurewa a gabansu ko yaya ne ,in ba haka ba Suma tana qara musu damuwar ne, gara ta Dunga daurewa ko Suma sa Dan saki jikinsu , duk da tasan baxata taba iya danne abinda take jiba Amma zatai kokari taga ta Dan rinka daurewa,tana nuna musu cewa kamar ta dangana.danma kullum sai ta tashi sallar dare daga karfe shabiyu suke farawa har karfe hudu na asubahi suna kan darduma suna salloli tareda addu'o'i da Kuma Mikawa Allah lamuransu, gabadayansu,har Hanan da take gidan Ayanxu, Dan har yau Bata koma gidansu ba,da Kuma baba hasiya itama ba'a barta abaya ba ....yanxu haka abinci ne agabanta take wannan tunanin.bayan ta danci abincin da anty mufeeda ta takura Mata akan taci,ta kalli agogon bangon Dake falon nasu,taga karfe takwas da Rabi na dare,tunda har sunyi sallahn isha'i babu dadewa.tai musu sallama ta shige daki tunda zasu tashi sallan dare gara ta kwanta da wuri ta huta,idan ba kwantawa tai ba ,xata iya fallasa abinda ke cikin ranta na halin da take ciki,Bata dauka xatai bacci ba, duba da yanayin da take ciki, Amma bayan kamar kusan mintuna 20 da kwanciyar ta kan gado bacci Mai nauyi ya dauketa Wanda rabon da tayi shi tun kafin Rukayya ta Bata,acan falon kuwa baba hasiya da Hanan da anty mufeeda sai ya hanaf Daya shigo suke dan taba hira sama sama Wanda yawanci hirar ruky kawai suke da nuna alhini har lokacin ,da Kuma mamakin har yau ba'a San inda take ba.Hanan dai tana dan share hawayen ta akai kaice.basu jima ba suka shige daki Dan xuwa anjima zasu tashi sallah ,idan ko suka tashi har sai sunyi sallahn ASuba suke barin kan sallayan sbd yadda suke kusan kwana suna addu'ar akan Allah ya bayyana musu Rukayya cikin gaggawa.....


___________?&


Ruky tace" uncle kace Kaine ka kashe abban mu, sai Kuma ta fara girgixa kai tana a'a uncle,bakai ne ka kashe Abba ba,kace wasa kake min Bada GSK bane,Dan Allah uncle kace ba haka bane,ka manta Abba accident yay ko_ka manta ne, ko dai kanaso ka fadamin hakane Dan kawai kanasan ka kashe ni da bakin ciki," ta qarasa fada tana toshe kunnuwanta tareda rushewa da gunjin kuka..Alhaji sunusi yace "Rukayya Kinga wasa a xancena ,to duk abinda kika ga na fada miki wannan shine gskyr maganar,kema kinsan Baki isa nai miki qarya ba ko Kuma wasa.Amma tunda kina kokonto idan na aikata Hakan ga wancan Dan jaridan na fara kasheshi agaban ki ,kafin kema nazo kanki kila zaki yarda....


Rukayya ta dafe kanta Tareda xaro ido waje cikin mugun mamakin Rashin imani Irin na Alhaji sunusi tace "uncle Yanxu kanaso kacemin Kaine ka kashe Abba,. Yana Dan uwanka uwa daya uba daya,Wanda iyayenku suka dai suka bari aduniya rayayyu daga kai saishi Amma yau Kaine kake cewa Kaine ka kashe shi.duk wannan maganar da Rukayya take hannunta na dafe da kirjinta, numfashinta nayin sama sama tsabar shock din da tashiga.Alhaji sunusi yace"hmm yarinya kenan ai har yanxu bakisan wanene niba shiyasa. Zahiri na kika sani bakisan ciki Nava,ni nan da kike ganina ,na kashe mutum ba komai bane ba,kisa baya yimin wahala, Rukayya ta girgixa kai tace "yanxu uncle ka manta lokacin da kaxo gidanmu ranar da aka kawo Abba daga hanyar Abuja akace accident yay ,Kuma akace take awajen ya rasu sannan kaxo gidannan kaita kuka,aka dawo ma sai hkr ake baka ganin yadda ka damu,ka kamanta yadda kafi kowa damuwa Ashe Kaine ka kashe Abba, kaina ka masa mummunan kisa meyayi Maka, nace me yay maka,ta qasara fada tana Mai rushewa da gunjin kuka ta buga Kanta jikin bango dakin da take ciki.tana girgixa kai....



Alhaji sunusi yay murmushi, yace "ai wannan kadan daga cikin iya acting Dina ne, Kinga wannan abun da kika fada to de same thing akan yadda nai acting dana naje gidanku na nuna alhini na akan batan da kikayi ,haka na ari fuskar damuwa nasa afuskata, .Rukayya ta dago da fuskar ta wacce tai ja sbd kukan da taci,ta xubawa Alhaji idanuwanta,sai Kuma tace "uncle Anya ko kai musulmi ne,Anya ko baka fita daga cikin musulunci ba, meya ribarka da kake aikata wannan ta'addancin a qasa,sbd duniya,sbd duniya duk kake aikata wannan xalincin,in Sha Allah kai dai kana qarqashin wutar ja hannama,kana can kasanta,wlh Allah baxan taba yafewa Maka ba, kashe Abba ma da kai wlh baxaka taba samun nutsuwa ba in Sha Allah. Kaida samun farin ciki da kwanciyar hankali kuwa har abada,mugu ,azzalumi, kafiri jahili.,tas tas kake ji a fuskar Rukayya da Alhaji ya wanketa da Mari wacce saida taga taurari, sannan ya hanka data baya ,kanta ya bugu da bangon dakin .take tasa ihun da Saida gidan nan ya ansa gabadaya....



Sajen jabir tuni yayi yanda AA Arab ya fada masa.ta baya suka zagaya bayan sunyi parking motarsu daga can cikin wasu duhun bishiyoyi.wasu police din Dake tare dasu suka lafe ta gefen gaban katangar wasu Kuma suka Yi bayan katangar aciki kuwa harda sajen jabir,anan sajen jabir ya samu ya haye katangar bayan sunyi disconnecting wayoyin wutar Dake jikin katangar,ya Dira ta ciki, Wani police ma ya biyo shi, yakasance su biyu kenan .suka fara bin jikin katangar cikin sanda da iya taku, suna bi ta cikin flowers din Dake gidan,tunda dare ne , apartment ne guda biyu acikin building din,Daya akwai wutar nefa Daya haske gabadaya apartment din,Daya Kuma Babu ,take suka nufi Wanda suka hango da wutar nefar,.....



. suna bi cikin sanda suna bi har suka isa Wannan apartment din saidai shiru babu motsin kowa ,suka tsaya daidai Wani window Wanda suke Jin magana kamar sama sama haka cikin fada fada,da murya mace da murya namiji , Amma Basu fahimci komai ba Saida sajen jabir suka tsaya suka kashe kunne na wajen 20 minutes sannan sukaji Wannan ihun na Rukayya Wanda Saida gidan ya ansa take sajen jabir ya leka ta window glass din ya hango Alhaji sunusi yayi kan Rukayya ya taka ta,Bai Gane ko wacece ba, Amma ya Gane Alhaji sunusi take yayi baya daya police din shima ya buya, Jin kamar wani ya hango su, sajen jabir ya boye bayan wasu flowers,ilai ko Daya daga cikin yaran alhaji sunusi ne,Wanda ke gadin harabar gidan yaji kamar motsi shine fa ya zagayo Dan ganin menene,Saida ya gama zagaye xagayensa da dube dubensa , ganin baiga kowa ba sannan ya koma .....



Wani Irin ajiyar xuciya sajen jabir ya sauke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login