Showing 54001 words to 57000 words out of 278032 words

Chapter 19 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1094

sai Wanda takeso tukunna , ita maimuna datace yarta baxatai zanceba,ai baka takura musu ba saini ,katangarka Mai dadin tsallaka wacce ka Raina koh,to wlh babu Wanda ya isa,malam Auwalu ya shige dakinsa yace shikenan muxuba nida ke, mugani agidan, Baba asabe ta kama fada tana wlh babu wanda ya isa yaywa zaliha AURE tunda itama yar gidan maimuna ba takura Mata akai ba Dan haka itama wlh baxa'a takuwa rayuwar yarta ba,daga haka ta shige dakinta, bayan tayi bugu zaliha ta Bude....


Baba asabe tace ke zaliha zonan , zaliha ta karaso wurinta, Baba asabe tace mesaya kika shiga wannan tsohon, zaliha ta fara wasa da yatsun hannun ta,baba asabe tace Kanna qara ganinki kinshiga motar wannan tsohon zaliha tace to babarmu, baba asabe tace yanxu Banda Allah yasa nai borin kunya nace ba haka ba aida tuni ,kinsa naji kunya gaban makiyanmu suji dadin mana dariya , zaliha tace babarmu baxan sake ba, Baba asabe tace yauwa me kashin arxiki,Ina Kuma ledar danaga kin shigo da ita,...


Zaliha tace tana kan barandar nan wlh babane ya firgitani,bari na dauko daga haka ta fita ta dauki ledojin ta dire gaban baba asabe, Wacce ta washe Baki tana kallan ledar,bayan zaliha ta Bude , baba asabe tai ido hudu da kaza ga Kuma youghurt L&Z,ga Tsire da gurasa,ka lemo kwalbar da takeso da dai sauransu,aituni suka manta da wata damuwar Malam Auwalu suka fara kaiwa bakinsu,....


A bangaren ummah kuwa,ko uffan batace ba, saima Allah ya shirya datai axuciyarta,wai yarinya karama Irin zaliha ce take shiga motar saurayi lallai abin na baba asabe babba ne,aitasan malam baxai qarya ba,akan taiwa zaliha fada shine take Wani kareta,hmm asabe kenan haryanxu batasan yadda duniya ke ciki bane,ita yanxu baxatai tunanin wannan siyayyar da akeyiwa zaliha watarana ZA'A iya fanshewa bawai fata take musuba, Tunda wasu samarin yanxu bani gishiri inbaka manda suke , Allah dai ya kyauta kawai ,ita abinda baxata koya danta ba kenan karbar kayan saurayi bare kuma shiga motarsa,daga haka ta shige warta daki dama tun tuni Nana tana ciki,.....



*Zaku iya jina kwana biyu shiru sbd Wani dalilin Mai mahimmanci,so ba lallai kullum xandinga posting ba,idan ansamu akaranta idan Kuma ba'a samuba ayi hkr harsaina samu lokaci komai ya dai dai ta*



*Wanda sukeso a tallata musu hajarsu xasu iya Yin magana ta wannan number Dake qasa*





07066508376_______
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*_____JAMI'AR TSARO_____*



*____THE WOMEN POLICE____*


*NA*



*_____NAJA'ATU UMAR FAROOQ _____*



*____(MRS SARAKIES)____*



*QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA) =?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*


______season one ep 2?? 4??


__________?&

Washe gari da yamma wajen karfe uku da Rabi na yamma, mamah na zaune a daya daga cikin kujerun kantameman falonsu ga azkar a hannunta tana karantawa, baba hasiya kuma tana kitchen,taji Karan Buda gate Bata kawo kowa a rantaba sai ma hanaf data kawo,Dan ta dauka shine ya dawo daga wajen aiki,Dan ruky kan tasan sai 5:30pm to 6 ma take dawo gidan ,jim kadan kawai taji sallama ta juya ta ansa ma me sallamar, ganinsa da akwati ,harya qaraso ya ajiye a tsakiyar falon ,sai ga wani ma ya shigo data hannunsa ,ta tsaya tana kallon yadda aketa shigo da akwatuna,kawai ta tsaya tana kallan iKon Allah,eh iKon Allah mana, tana tunanin wadannan akwatunanfa daga Ina haka itadai tasan batai da kowaba da xa'a kawo mata akwati ,haka dai ta tsaya taji Kuma waye zai shigo,kafin ta karasa tunaninta wasu hamshakan mata sun shigo cikin katon falon nata,su hudu, gabadaya jikinsu walwali kawai yake da sarkokin gwala_gwalai,....


Suka qaraso bakinsu dauke da sallama ko Wacce saiji da kanta kawai take,Amma ganin Irin yadda falon ya qawatu da tsadaddun, kayan ado yasa su sauke jiji da kan da suka xo dashi,mamah wacce mamaki ya kasheta ta ansa musu tareda nuna musu wurin xama,babu Bata lokaci suka zauna ,baba hasiya tana kitchen Jin yar hayaniya yasata Dan lekowa taga suwaye,ganin Baki ne yasata komawa kitchen din ta shiga kawo musu ruwa da lemuka ,da snacks tana direwa agabansu bayan ta gaidasu haka suka ansa babu yabo babu fallasa,suka kalli mamah suka fara gaisawa mamah ta ansa musu wacce har lokacin Bata gama dawowa daga mamakin da take ba,....


Hajiya mansura ce tai murmushi tace Hajiya kinganmu baxata koh,mamah tace eh ,ainayi mamaki sosai, Hajiya mansura wacce har lokacin murmushi ne a fuskarta tace yauwa daga gidan honorable sunusi ne ,anwakiltamu ne da mukawo kayan tambayar lateef,ta fada tana nuna akwatunan , mamah cikin mamaki tace to auran lateef Kuma da wa,ko kawowa akai mugani Kune xaku kai, Hajiya mansura tace a'a Hajiya kodai Baki fahimci me nake nufi bane,ai haka akace mukawo nan gidan na Rukayya ne mana,ba ita lateef din xai Aura ba,ai ita yake neman AURENTA mana, Mamah ranta yay bala'in Baci Jin Rashin mutunci Irin na Alhaji sunusi,Amma gudun kartasa aga akwai Wani Abu a qasa yasa ta Dan sassauta fuskarta tace,ok Allah sarkie na sha'afane Ashe yau suka ce xa'a kawo ,....


Hajiya mansura ta qara sakin murmushi tace wlh hajiya,ai wannan Hadi yayi, tuwona maina ,Kinga xumunci xai qara qarfi, Allah dai ya jikan gwarzan Maza ,Kuma dp IG na qasa,wato ALHAJI UMAR MAITAMA, mamah cikin dauriya,Dan karta fallasa yanayin da take ciki ta Dan sassauta fuskarta tace Ameen, Hajiya mansura ta Bude jakar ta ta ciro #million Daya cash ta ajiye kan Daya daga cikin akwatun tace wannan kudin gaisuwa ne,....


Mamah dai kallanta kawai take, Hajiya mansura akace Ina diyar tamu mamah tace tana wajen aiki Bata dawoba, Hajiya mansura akace Masha Allah,Allah dai ya kaimu lokacin,mamah day Bata ansa ba saima ce musu datai kusha ruwa mana Hajiya, Hajiya mansura ta kalli wadanda sukaxo, wadanda tuni suka kama kansu ganin cikin falon ma dai annarkar da dukiya,tuni suka Raina kansu Dan tun daga haraban gidan sun San an narkar da dukiya wurin Gina gidan,ya qawatu ,domin gidannansu ruky ya hadu iya haduwa, Sannan uwa uba yadda mamah tai musu kwarjini, tuni sun saki Baki suna kallan kyau iya kyau awurin mamah, danma yanxu anmanyanta,Hajiya mansura ta qara musu tayi tace bismillahirrah ku Hajiya,kusha ruwa, suka ansa mata da toh,....



Haka suka dan Sha ruwa kafin daga bisani su mike suce zasu tafi , haka mamah ta mike cikin dauriya tai musu rakiya xuwa kofar falon gidan sannan ta dawo ,ko kallan akwatunan batai ba ta xauna kan kujera ta dafe kanta, dayake Neman Sara mata, lallai Alhaji sunusi bashida mutunci,daga shi har matarsa wato nuna musu isar dayake ikirarin zaiyi shine yanxu kenan ta fara Gani,tunda gashi sun Yo gaban kansu sun Aiko da akwatunan sa Rana, batareda da Jin ta bakinsu ba,bare Kuma a kirata afada mata cewa xa'a kawo kaya,wato ita Bata da mutuncin ma da zasu fada mata,,to shikenan su xuba su Gani Dan halak ka fasa,saita nunawa Alhaji sunusi true color dinta,itako baxata kirashi ba,zata xuba masa ido ne taga iya gudun ruwansa da ikon dayake ikirarin zai nuna musu akan yarta,ko ruky baxata bari taji taga kayan ba,bare Kuma su hanaf ,kartaje ta shiga damuwa ta dauka ZA'A mata kar fa karfa ne ta AURI lateef,tana lura da ita har yau ta kasa sakin jikinta kamar da ,tun lokacin da Alhaji sunusi yaxo ,ya fada musu AURAN ta da lateef babu fashi yasata take cikin damuwa,....



Haka Mamah ta kira baba hasiya, baba hasiya ta wanke hannunta ta fito daga kitchen din,ta qaraso falon tace Hajiya Gani,mamah ta kalleta da yanayin fuskarta da har lokacin Bata dawo dai dai ba ranta ya gama baci tace Hasiya kiramin me gadi da me gyaran flowers din nan su shigar min da akwatunan nan dakin Dake cikin store dinnan,haka baba hasiya ta ansa wa mamah da toh ta fita,babu dadewa ta dawo da mutanen guda biyu ,tace Hajiya gasu ,suka gaida mamah wacce ta ansa musu ,cikin yanayin da take ciki tace ku kwashe akwatunan nan kukai dakin Dake cikin store dinnan haka suka ansa mata suka fara kinkimar boxes din , suna kaiwa harsaida suka gama kwashewa Sannan mamah ta haura sama, baba Hasiya bita da kallo ,ta jinjina kai tana mamakin karfin halin Alhaji sunusi,.....



__________?&

Ruky ce xaune a office dinta ita kadai suna video call da Hanan,wacce tunda suka fara wayar take ce mata wai AA Arab zaidawo Nigeria, Ruky tai tsaki tace Dan Allah Hanan kidaina kawomin maganar wannan mutumin,nida bansanshiba bansan ma ya yake ba,meye hadinki dashine da kika damu dashi haka, Hanan tace ke wlh baxa ki Geneva banida Hadi dashi hasalima ko labarinsa ban saniba sai shekaran jiya da yaya Nura yake ta fada agudanmu, harsaida ummin mu tace yay mana shiru ya daina maganar sa sannan yay shiru, Amma Inkika yadda yake yawan xancen sa a gidanmu kamar karatu.....


Niko da gulma na bishi har part dinsu nace ya van labarinsa waye shi,wannan AA, Arab din,shine yace min wai,Wani jami'in tsaro ne, abin mamakin ma da alfari matashin saurayine Wanda ya shigo aikinsa Yana da kana nan shekaru,kamar mudai,da muka shiga aiki da qananun shekaru, shekara kusan 6 tun waccan gwamnatin da yay tashe ya rugur guza yan ta addar qasar nan,har masu goya musu baya duk ya sani yana kokarin tona musu asiri shine fa aka fitar dashi daga qasar babu Wanda yasan wacce qasa aka kaishi,Kuma har Rana Mai kama ta yau tunda ya bar kasar Bai qara xuwan tava,shine fa yanxu da wannan gomnatin taga Yan ta addar nan suna Neman gagarar hukuma, Ganin Kuma suna da jajirtaccen jami'i shine tace xata dawo dashi qasarsa ya cigaba da aiki,Kuma ance nanda few weeks xai dawo qasar sa.....


Ruky ta tabe Baki tace an so what ,Kuma ke meye naki aciki, Hanan tace wlh baxa ki Geneva ruky ni kwazan mutumin kawai yasa naji ya shiga Raina tunma kafinma na ganshi, ruky tai murmushi tace yar wahala aisaiki ta dakon jiran dawowar tasa,kila baza ki ganshi yadda kike tunani ba, Hanan tace hmm ruky kenan kedai Baki da gwani,nidai wlh murna nake ya dawo ko ya Yi maganin wa'yan nan Yan iskan yan ta addar nan da suka addabemu,da jami'an mu,ko a Bude mana hanya muyi ziyara,Dan wlh inasan tafiya ziyara na bar garinnan Amma mutanan nan sun hanani, .....


Ruky tace lallai kan ,iska na wahalar dame kayan Kara, Hanan tace nidai wlh am with him100%, ruky tace Dan Allah ya Isa na gaji da Jin hirar wannan mutumin da baisan ma da zaman kiba, baima San kina ta Wani kumfar Baki akansaba please enough, Hanan tai dariya tace muna nan Dake wlh saiya San da zamana Kuma wlh indai yasan da zama na ki shirya saina fada masa duk yadda kike nuna masa kiyayya, ruky tai dariya tace ki bari idan ya dawo kije har Inda yake ki fada Masa,tunma kafin yasan da xaman naki, Hanan tace haka kika ce, ruky tai fari da ido tace eh haka na fada,Hanan ta ciji yatsa tace Aiko wlh ki shirya daukar duk Wani hukuncin da xai dauka akanki, ruky tace Kinga naga alamar kinfara fita daga hankalinki kan Wanda baima San kinayi ba idan kin dawo hankalinki mayi maganar ,daga haka ta kashe wayar tata , tana sakin tsaki, Hanan tai murmushi ta girgixa kai tana mamakin ruky,.......



__________?&


Wani matashin saurayine, Wanda hutu da jindadi yake a bayyane ajikinsa,Yana sanye da wata light blue din tshirts,da farin Wando 3quater ,kansa Wanda gashi Irin na larabawa Ya kwanta akansa yay luf ,ga gargasa ajikinsa, tsaye yake abakin ruwa wanda yake kalar white &blue dinnan, ruwan sai wasa yake , ya tashi sama ya hautsina,yaxo baki ya koma cikin abin sha'awa,Wani balara bene ya janyo masa water mashin din Dake bakin ruwan , Wanda ke tsayen ya karba ganin Yana miko masa,.....


Yay Masa murmushi cikin harshen larabci ,yace shukran , balaraban,ya ansa masa shima da laba'asa,haka ya karva ya hau kan machine din,inda ya jashi xuwa cikin ruwan da mugun speed,Wanda ruwan sai da ya tarwatsewa ,haka yake ratsa ruwan nan Yana gudu acikinsa, keda Gani kinsan kwararrene kan iya hawan water machine dinnan,Saida ya kusan awa Daya da Rabi yanayi sannan ya dawo bakin ruwan ya aje machine din, Yana furxar da iska a bakinsa,Bayan ya sauko ya fara takowa cikin nutsuwa,harya fito daga ruwan gabadaya, ya dan jike da ruwan Amma ba sosai ba,.....


Haka yay musabaha da balarabannan ,ya wuce motarsa, iskar nan saikada rigarsa take,ga gashin kansa sai tashi yake , kyakkyawa ne ,idan nace kyakkyawa Ina nufin kyakkyawan GSK,Dan yayi kala sak da larabawan qasar , kodan dama shima ya hada jini da sune,gashi dogo dashi, fatarsa sai daukar ido take, ya lumshe ido ya Bude lokaci Daya Yana shafa sumar kansa,Yana kallan Irin yanayin garin Da dayake yamma yayi,sai yaji weather ya masa Dadi,yay unlocking motar ya shiga ya wuce gida, Yana Jin jikinsa yadda ya Dan ware ,....




__________?&


Ameenah ce xaune a tsakar gidan tana yiwa saude kitso , babar saude ta shigo da sallama ta qaraso wurinsu tace a'a Ameenah wai har yanxu kitson ake Baku gama ba,ta kalli kan saude Wanda Ameenah ke yarfa mata kana nun kitso,maman saude ta aje kwanan abincin ta-da kawowa Ameenah tace Kinga yaudai munyi ranar girki, Ameenah tai murmushi tace nagode maman saude,maman saude tai murmushi tace ,nasan saude ce ta saki wannan wahalar ko,....


Ameenah tai murmushi tace a'a, kawai ni nake mata,maman saude tace aini banasan saude ta dinga sakaki Irin wannan wahala,yanxu dai ki saki kitson nan kici abincin nan, Ameenah tace inna dan Allah ki bari na qarasa maman saude tace a'a saifa kunci abincinnan sannan xaku cigaba da kitson ,Babu yadda Ameenah ta iya haka ta saki kan saude ta Bude kwanan abincin ta faraci Dan wlh dama yunwa takeji,babar saude ta dinga kalleta a kaikaice ganin yadda take lauma, gabadaya tausayin Ameenah takeji, yarinyar ta rame ta bushe duk tayi baki,ta Kuma qudiri aniyar in Sha Allah saita tambayi Ameenah garinsu da unguwar da take ko da dabara ne ,saita taimaka mata ta fitarta daga wannan xalincin na Kabiru,.....

Anya koh iyayenta Sunsan koh tana cikin wannan halin,Amma Kuma duk iyayanda suka San me suke baxasu tabs bawa Kabiru auran Ameenah, sbd gabadaya Daya Bai cancantaba, yarinyar gata tubar kalla Masha Allah, Amma ta qare a auran Kabiru,duk da ba sanin Kabirun taiba sosai Dan Bata taba xuwa gidan ta tadda Shiba,???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tana tuna nin makoh Anya Yana kwana agidan, GSKy ba lallai ba, dole gsky tasan yadda zatai ta nemi gidansu Ameenah,.....




07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*_____JAMI'AR TSARO _____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*_____NAJA'ATU UMAR FAROOQ_____*



*____(MRS SARAKIES)____*




*QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA)*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_____Season one ep 2?? 5??


___________?&


Bayan DCP ya Gama sauraran sajen jabir ,tuni ya aje waya,ya dauki key din motarsa,ya fito ya kira ASP Anas yace su wuce hayin rigasa,bayan ya mika masa key din ,ASP anas ya karba cikin girmamawa suka wuce parking lot ya dauki motar ya fito ya budewa DCP ,DCP ya shiga ,shima ASP anas yay sauri ya shiga driver seat yaywa motar key,Sanna suka wuce hayin rigasa,da mungun speed,babu dadewa suka isa,suna xuwa suka tadda sajen jabir da cofur Audu a bakin gate din gidan , DCP Bai tsaya jiran ASP anas ya Bude masa ba ya fita daga motar cikin sauri,suna ganinsu sukai saluting DCP , suka gaida ASP anas cikin girmamawa ,DCP ya
daga musu hannu ya tsaya daga gefe , shida ASP anas, cofur Audu ya fara konkosa gidan ,sajen jabir Kuma fara zagaye wurin....



Alokacin da su DCP suke tsaye awurin cofur Audu Kuma yake Kwan kwasa gidan ,alokacin shi kuma Wanda ke cikin gidan sunyi nisa cikin alfashar da suke aikatawa,ganin ana Buga get babu kakkautawa tun Basu jiba har suka fara ji,cikin Dan mamaki ya tashi daga kan hany Dake kwance rashe rashe,yay tsaki haka kawai an tsaida shi Yana tsaka da jindadinsa,ya miki ya shiga toilet ya fara tsarkake jikinsa ,bayan ya fito, yay gaban wardrobe ya sauya kaya har lokacin ba'a fasa buga gidanba,...


Ya qara sakin tsaki har lokacin akaro na babu adadi,Yana mamakin waye yake nocking gate haka kodai haydar ne ko saleem,sukuma idan sune xasu kirashi Kuma ai suna da key din gidan ,ya cika da mamaki sosai bayan ya shirya ya nufi gaban mirror ya dauki key din gate din yay hanyar fita Dan ganin Wanna jakin ne ke buga masa get haka ,kamar xai balla, hany ta mike ta nufi hanyar toilet tana cewa beb waye ke knocking haka kamar xai balla gate din,yay Banxa ya kyaleta ya fita daga dakin,Dan xuwa yaga waye ke knocking din,ganin Bai kulataba yasa ta tai shigewar fa toilet Dan watsa ruwa itama,....



yana fita compound kamar karawa gidan bugu suke cikin hasala bayan ya qarasa yace please who is knocking like stupidly,akai shiru yay tsaki cikin hasala yasake cewa are dept,if u are not talking I will not opening,cikin bacin ran Rashin da'a irin na mutumin , DCP yace bakine, yace who are the visitors, Jabir yace idan ka Bude xaka gani ai,yay tsaki harya juya zai koma sbd ganin babu amfanin budewar tunda shi baiyi da Wani xaixo ba yasa ya juya din,saidai Kuma Mai ya tuno ,yasa ya dawo ya qasara bakin gate din yasa key ya Bude , ido hudu sukai da DCP Wanda ke kallansa daga sama har qasa,shima kallansu yake with confusion ganin jami'an tsaro a kofar gidansa ,saikuma ya basar ya fara kalle kalle Irin yaga suwaye visitors din,yace where are the visitors din, DCP yace our,....


Ya gyara tsayuwarsa Yace ok then what are u coming to,DCP yace just wants to talked to u,yadan tabe Baki yace ok am all ears,DCP yace maganar Bata nan bace,yace so ta inace , DCP ya Danyi murmushin gefen Baki ganin yadda ya Wani tsuke fuska kamar ba'a gaban Jama'an tsaro yake ba,sai Kuma ya dawo serious yace a office dinmu,muke San mu tattauna, mutumin yay tsaki yace u are not ready to talk to me, idan har sainaje office dinkune sai kace Wani criminal,so if u are ready to talk to me,then u should get back to me ,daga haka ya fara kokarin banging kofar,sajen jabir ya Wani rike kofar cikin bacin Rai yace,harmu zaka na Wani yiwa shouting, mutumin ya Wani qara tsuke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login