Showing 195001 words to 198000 words out of 278032 words

Chapter 66 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1042

kamar Allah ne ya Aiko su, babu Wanda ya kawo Mai d'auki cikin ma aikatan bare ma yaran, Dan duk yaran sarkin gida ne Dan su agunsu daka tab'a sarkin gida gara ka tab'a su ,Saida suka kusan sumar dashi Sannan sarkin gida ya ce su Rabu dashi,ya Kalli Alhaji sunusi Dake sauke numfashin wahala Yana hawaye kamar me , sarkin gida ya ce "wannan kad'an ka Gani ai ni agidan nan ba 'a taba Sab'a min umarni na idan ko kayi Yanzu zaka ji duka ,ya ce "ka tashi kamin tausa tun kafin su qara nad'a maka Wani dukun, Alhaji sunusi yay shiru yak'i tashi Yana kallan sarkin gida gani yake ai Kamar yafi karfin yin haka ,.....



Sarkin gida ya daka Masa tsawa ya ce " zaka tashi ko sai na taso da kaina na sumar da kai" cikin yaran sarkin gida Wani ya taso yay kan Alhaji sunusi gadan gadan zai dakeshi ya ce cikin yanayin maganar "kai har ka isa sarki ya saka ka Abu kak'iyi" ya Kalli sarkin gida ya ce"bar mana shi sarki yanzu mu sauya masa kaman ninsa"ya fad'a Yana wani goggoce Baki,sarkin gida ya wani kalleshi ya ce "rabu dashi babban saurayi idan ya'ki tasowa ka afka masa kawai" Alhaji sunusi ganin fa da GSK suke ga ko yanzu ma ai yaji jiki yasa ya tashi cikin rawar jiki ya fara yima sarkin gida tausa ,abunka da Wanda Bai Saba ba tuni yaji har ya fara gjy ,tun Yana daurewa har ya kasa yi sarkin gida ya wulla masa wata harara ai jiki na rawa ya cigaba da Yi ,ya Kalli babajo Ali ya ce "kai Kuma sai nayi bacci xaka min Fifi ta har gari ya waye kaji ko baka jiba" Babajo Ali cikin tsoro da rawar ciki ya ce"naji" sarkin gida yay wata mahaukaciyar dariya ya ce "hmmm Allah nagode Maka daka nuna min wannan ranar, wai yau nine nake mulkar su sunusi shida wannan babajo,da sai dai su mulkemu sannan su wulakanta mu,kai Allah na gode Maka,ya kalle su ya ce "wlh azaba ma yanzu kuka fara Gani Dan Yanzu Baku ga komai ba,duk abinda kukamin wlh da sannu xan rama sannan na D'ora muku nawa akai , Alhaji sunusi ya ce cikin rawar murya"Dan Allah sarki kayi hakuri? Sarkin gida ya D'aka masa duka akafad'arsa ya ce "hakuri kai kasan kalmar hakuri ne sunusi? Lokacin da kadinga samu kisan kai idan mukai kuskare kadinga zaginmu kana ci mana mutunci shine yanxu xakace nai hakuri kai ka da muke baka hakurin alokacin kasan shine?ya fad'a cikin tsawa, Alhaji sunusi ya sunkuyar da kansa qasa ,sarkin gida ya ce a fusace "ka cigaba kafin nasa ai Maka dukan mutuwa, ai jiki na rawa Alhaji sunusi ya cigaba dayi ,Yana Yi Yana hawayen tausayin kansa da yadda rayuwa tayi dasu ,shiko sarkin gida ya kishingide sai Wani lumshe ido yake Yana Jin Dad'in yadda yau yake gara su Alhaji sunusi San ransa.....



Haka Alhaji sunusi suke Shan wahala awurin sarkin gida ya takura musu kwata baya tab'a bari su huta daga ya ce suyi masa wannan saidai yace suyi masa wannan,har fada jansu da suke kwana akai sarkin gida ya k'wace ya ce Basu isa Yana kwana a kan gado Suma suna kai ba,ya ce "daga yau Kun dawo kwanciya a qasa babu yadda suka iya aqasa suke kwana cikin wannan uban sanyin tiles d'in,sunyi wata muguwar rama kamar me,gashi kaf Cikin 'yan prison din babu Wanda yake kulasu bare ya tausaya musu Dan duk yaran sarkin gida ne,kai sarkn gida idan yaga dama ma sai Ya ce su Alhaji sunusi su zasuyi aikin da aka Basu na ranar gabad'aya kuma dole suyi idan ma baiyiba wlh sarkin gida da yaransa sun Yi ta dukansu kenan da Basu fatik kala kala...




A b'angaren barrister shamsu kuwa tun ranar da malam Auwalu ya sanar masa da abinda ya faru da Ameenah yaji mugun taimusayin ta ya kama shi aduk wannan shekarun da take dashi,Gani yake wannan Abu yayi mata nauyin da zata iya d'auka akanta , duk da dai a shekara baxata wuce 20 xuwa Ashirin da Daya ba ,tun ranar da suka rabu da Ameenah tausayin ta ya makale masa a xuciyarsa ko Wani motsi yay sai ya hango yadda yaga ta rame tai Baki da dukan alamu Kuma ba dad'in auran takeji ba,duk da ance mijin nata D'an kidnapping ne,haka dai ya ke daurewa yake cire tunanin aransa , Amma ya k'udiri aniyar in Sha Allah idan ankwana biyu zai tai Maka mata ita da iyayen ta......




A bangaren Ruky kuwa da Ameer ,ya takura Mata da k'ira Babu dare babu Rana kullum acikin K'iranta yake gashi Bata picking call din nasa Amma baya hak'ura, idan tayi blocking d'insa sai dai taga take ya qara K'iranta da wata number,Dan sunyi haka dashi yafi a k'irga har mamaki take da yadda yake sa sim card kala kala, gashi ko a office ne ya dinga K'iran ta kenan kamar hauka, Rashin mutunci babu Wanda bata masa Amma Dan Rashin xuciya Iran tasa Hakan baisa ya hakura ba,Dan wata k'aunar ta Allah ya D'ora masa kamar me, Dan shi duk wannan abun da take masa Hakan baisa d'igon Santa ya ragu ko D'aya daga cikin Wanda yake mata ba,ga AA Arab shima yayi mugun takura Mata da sa ido ,ga aikin da yake sa ta kamar hauka ,ta rasa ya zatai dashi,har mamah ta samu ta fad'a mata cewa ya Maida ta office dinsa tasa Baki ta ce ya maida ta office din su , Amma mamah ta ce ai ita Hakan da yay mata yayi mata dai dai..yauma dai kamar kullum tana zaune a office d'in wajen karfe hud'u da Rabi na yamma harma sun kusa tashi daga office d'in tana aiki a laptop Wanda AA Arab ne d'azu ya kawo mata Dan gabad'aya rantama a b'ace yake taji anyi knocking kofar office d'in,ta d'aga kai tana kallan kofar,ganin an K'ara knocking d'in yasa ta ce"yes coming"....



Turo k'ofar akayi aka shigo ta d'aga kai tana kallon waye ,taga feenah ce tai mamakin meya kawo ta headquarter Kuma bayan tasan ba'a nan take aikiba sai dai idan za'a Yi general meeting ko Kuma lecture ne take xuwa Amma yau da yamma Kuma tazo,to kodai wani Abu ne Wanda ya shafi aiki ya kawo ta ,saita kau da tunanin har feenah ta shigo tana Wani cin cingom ,ruky ta d'auke kanta ta Maida kan laptop din gabanta,Dan feenah 'yar rainin hankali ce ta bugawa ajarida shiyasa basayi da Hanan Dan Hanan Batasan raini, ita Kuma feenah idan ta samu gu akwai ta da raina mutane,feenah ta qaraso kusa da ita ta ce "Ruky ya na ganki anan? Ina office d'in naku yake kika zo nan? sai a sannan ruky ta d'ago ta kalleta kamar baza tai magana ba Jin Wani tambayar rainin hankali da feenah tai mata sai Kuma ta ce "nan aka dawo Dani"ta fad'a tana kallan feenah Dan ta tabbatar da abinda hanan ta fad'a mata akan feenah ranar,aiko hasa shenta ya zama gsky Dan take fuskar feenah ta nuna kishi sai Kuma tai saurin gyara yanayinta ta ce "aishikenan" am boss ko Yana nan ? Ruky ta kalli kofar ta ce "eh" cikin halin ko in kula, feenah ta matsa ta ce "ok thanks bari na shiga" daga ta matsa kusa da kofar ta fara knocking, saida tai kusan sau uku sannan AA Arab ya bata ixnin Shiga, feenah tai Wani murmushi sannan ta shiga harda rufo k'ofar, ruky ta bita da kallo tana mamakin meya kawo feenah office din AA Arab Kuma Shima harda Bata ixnin Shiga Kodan k'ila Dama yasan da xuwan ta,wata zuciyar ta ce "ke Kuma Ina ruwanki da zaki damu,kika sani ko akan aiki ne tazo,k'ila yasan da xuwan ta shiyasa har ya Bata ixnin Shiga,take ta tab'e Baki ta cigaba da aikin ta.....


AA Arab kuwa Yana ciki ya gama aikin da yake Yana kwance kan sofan Dake cikin office din ya rufe idanuwan sa Amma ba bacci yake ba kawai dai D'an hutawa yake, wannan knocking din ma da akayi duk d'aukar sa ruky ce ta kawo masa aikin Daya Bata shiyasa har ya Bata iznin shiga. shigowar da feenah tai da ganin ta da Yay Yasa yay saurin tashi zaune daga kwancen da yake Yana ansa gaisuwar ta idansa akanta Yana mamakin meya kawo ta office d'insa, feenah ta sunkuyar da kanta qasa ta risina ta ce "sir good evening"AA Arab ya kauda kansa daga kallanta ya ansa mata gaisuwar data masa ataikaice Yana jiran yaji meya kawo ta har office dinsa,feenah ta Wani d'ago ta kalleshi ta ce "sir Kwana biyu? shiyasa nace bari naxo na gaida kai "AA Arab ya ce "ok thanks" feenah ta rasa me kuma zatace Dan Allah ya gani wlh mugun San AA Arab take kamar hauka dan ko bacci bata iya Yi,tun ranar data fara ganin shi taji nutsuwarta gabadaya ta kau,shiko AA Arab har lokacin direction daban yake kallo ganin tak'i yin magana sai kame kame da take ,kuma da dukan alamu ba Wani abun ne Wanda ya Dan ganci aiki ne ya kawo taba yasa ya hade Rai ya ce "akwai Wani Abu ne?feenah tai murmushin yak'e ta ce "babu komai sir"AA Arab Ya ce "ok thanks for caring zaki iya tafiya"feenah tai murmushi ta ce "thank u sir"daga haka ta fita daga office d'in tana Mai Jin sanyi aranta Jin AA Arab ya saurareta.....



Ruky ta d'aga kai ta kalleta Jin ta Bud'e k'ofar office d'in, feenah Bata kula ruky ba har ta fice ma gabadaya daga office din,Dan sai taji wannan xaman da ruky tai a office din AA Arab Bai mata ba,Dan gani take yadda Ruky take da wannan kyau haka kila AA Arab ya ce Yana sonta.bayan fitar feenah daga office d'in ruky ta jinjina kai azuciyarta ta ce "wato mutumin nan Niya rainawa hankali kenan, ga feenah nan ta shiga har office din sa,kuma na tabbatar ba har kar aiki ce ta kaitaba Sbd babu Wanda baisan feenah da San Maza ba ,Amma ita ko K'iran ta akai awaya idan yaji yadinga cewa tana waya da samari,tai k'wafa ta ce "wlh Nima saina fad'a masa magana idan har ya qara cewa Ina waya da samari, wajen k'arfe biyar da 20 ruky harta fara har had'a kayanta ganin lokacin tashi yayi ,AA Arab ne ya fito daga office d'in,Yana kallanta fuska d'aure ya ce "wayace ki bar wannan yarinyar ta shigo min office?ruky ta kalleshi da mamaki ta ce " iKon Allah,bangane meyasa na bari ta shigo ba,Dan ta shigo saina nace karta shiga ,nasani ko Kaine kace tazo d'in, kaga malam ni ban tambayeka ba kamar yadda kake tambaya ta ba,nasani ko budurwar kace kawai so kake karna xargi komai ,ai ba laifi bane Dan budurwar ka tazo takanas Dan xuwa gun kaba"ta fad'a tana kauda kai Dan wlh ba karamin dauriya tai ba wannan maganar data fad'a masa ba.AA Arab ya zaro ido waje cikin mamakin ta ya ce "ke" ni kike fad'awa wannan maganar?ruky ta harareshi ta ce "aiba k'arya naiba Koba budurwar taka bace,Baga shi ta shiga har cikin office d'in ka Ina nan xaune ka Bata ixnin Shiga ba" naga kunfi mintuna goma aciki Ina nan Ina zaune,me kukeyi to idan ba hira ba,ko Wani abun ta kawo Maka Wanda ya Dan ganci aiki "AA Arab yay yo kanta a fusace ya ce "ni kike fad'awa haka?i my ur Mate"ruky tai saurin matsawa baya tareda sa ihuu kad'an Dan wlh ta d'auka dukan ta zaiyi ,duk da haka batai shiru ba ta ce "Ashe ba Dad'i ni ranar kace min wai nida DCP mun shiga ciki muna abunda muka ga dama" AA Arab ya daka mata tsawa ya ce "would u shut up, Baki da kunya koh?ruky ta juyar da kai gefe yay k'wafa ya ce "Kuma Babu inda xaki sai karfe shida na fad'a miki"ruky ta ce"wlh baxan xauna ba"AA Arab ya ce "to shikenan ki fita ga hanya nan mugani, idan ma kin tafi ai xaki dawo gobe Koh?ruky ta fara kukan k'arya yay tsaki ya koma cikin office d'in Yana Jin xantukan ruky data fad'a masa kamar alokacin take qara Mai Mai ta masa, itako Ruky ganin ya Banko k'ofar da k'arfi alamun yaji haushin abinda ta fad'a masa yasa tai wata dariya harta tana rike ciki ta ce ai ko yanxu ta rama itama .....



___________?&



Da daddare ruky tana kan kujera a falor tana chatting, mamah tana d'aki baba hasiya ma haka ,sai ita kad'ai message din Hanan ne ya shigo wayarta,tak'i dubawa sau hud'u kenan tana mata magana Amma babu Wanda tai respond akai Dan tun ranar da Hanan ta bawa Ameer number ta take Jin haushin ta,Dan yayi mugun takura mata, kiran Hanan ne ya shigo wayarta tak'i tai picking sai da tai mata 2 miss call ana ukun ne tai picking,tai shiru
,Hanan ta ce cikin damuwa "haba ruky Dan Allah wai baxa ki fahim ce niba? Na fad'a miki wlh Allah takuramin yay shiyasa na bashi" ruky tai tsaki ta ce "Daya takuramikin baxa kiyi blocking dinsa ba" Hanan ta ce "wlh kwata kwata ban kawo Hakan araina ba, Dan Allah kiyi hkr"ruky ta ce "ni babban takai cina yaddace ya takuramin da k'ira Babu dare babu Rana"Hanan ta ce "to kiyi blocking number dinsa mana"ruky ta ce "sau nawa Ina blocking dinsa,wlh ko sau goma Zanyi blocking dinsa wlh saiya sa wata number ya k'irani,idan nai blocking dinsa yanzu to kafin ajima xakiga ya k'irani da wata number,....


Hanan ta ce "kai amma da naci yake ,to Amma ga shawara"ruky ta ce "wacce Irin shawara? Hanan ta gyara xaman ta kamar tana gaban Ruky ta ce"wai Dan Allah meyasa bakyasan Ameer ne?wlh nidai banga laifinsa ba ,yaro D'an gata D'an gayu D'an masu kud'i, Wanda hutu da Jin dad'i suka zauna ajikinsa,Haba sis ya kamata ace munyi aure yanxu, ke tunda kinsamu ba sai afara nakiba kafin Nima Allah ya kawomin nawa na garin"ruky ta ce "wannan itace shawarar taki ? Hanan ta ce cikin zumud'i "eh " ruky ta ce "to ki rik'e kayarki banaso , aure Kuma lokacine Amma ni wannan yaron Bai min dai dai da zab'ina ba,idan Kuma ke ya Miki to xakiyi k'iransa ku dai dai ta "Hanan ta ce "kai ruky me Kuma ya kawo wannan maganar?Amma wlh kiyi tunani,Kuma wlh kinsan dai ba yaro bane Dan wlh zaiyi 30 years koma fiye da haka" ruky ta ce "to nidai bai min ba Kuma baxai tab'a yimin ba"Hanan ta ce"Dan Allah kiyi tunani wlh tausayin Ameer nake Dan wlh ya kamu da sanki ba kad'an ba,ai ka auri Wanda yafi ka sanka shine zaka samu jin dad'in da kake so a gidan AURE,ruky taja tsaki ta ce "ai ba'a dole a soyayya koh? Nace ke kije mana ku dai dai ta ,shine zan San kina tausayin nasa "Hanan ta ce "please ruky kibar wannan maganar just leave the joke are side,wlh kinsan Ameer dai ya can can ta ya xamto mijin AURE koh? Sai Kuma tai wata dariya ta ce"wlh kuma Kun dace kema kinsani" ruky ta rasa abin fad'a saboda takai ci kawai tai tsaki ta kashe wayar ta tana Jin xuciyarta na tafar fasa, lallai wlh Hanan tayi mugun Raina mata hankali Amma zatai maganin ta kwa nan nan.....





07066508376_______
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)____*



*(' TAURARI WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM THE 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 7?? 9??



____________?&


Yau ya kasance 24 ga watan aprilu shekara ta 2025,Wanda yay dai dai da Ranar alhamis,a kuma yau za'a koma zaman kotun kamar yadda aka sa lokaci.kotun cike take da Dan dazon al'umma Wanda suka zo daga wurare da Dama, ciki Kuwa harda mutanen garin Kaduna harma da qauyunkanta Dan xuwa kallo da Saura rar wannan shari'ar,a harabar kotun mutane sai kai da kawo wa suke ,kamar me.daga bakin kotun wasu barristers na hango su hud'u suna magana wacce da da dukan alamu magana suke Mai matuk'ar muhimmanci, iyalan su Alhaji da babajo Ali duk sunxo suma suna tsaitsaye a harabar kotun,can na hango Hajiya SA'A,itada Samira da wannan cousin sister tasu Mai suna bahijja da wasu mata su biyu Wanda bansan suwaye ba Amma na Gane d'ayar itace k'awar Hajiya SA'A wato mansura,duk idan ka Kalli fuskokinsu damuwa ce qarara a cikin ta, Hajiya SA'A gabad'aya ta gama susucewa Dan Gani take tun da suka d'auka ka qarar nan ,Gani take Alhaji sunusi bazaiyi xaman gidan yariba,akuma tagging dinta Yana fitowa zai sa a fito da lateef,Dan ba qaramin kud'i suka had'awa barrister da duka d'auko ba Wanda xai kare su Alhaji sunusi,Dan babu laifi sun kashe mak'udun kud'ad'e wajen samo Wannan babban barrister Wanda da wuya kikaga an kada shi a Shari'a, tundaga Lagos sukai hayar sa har Kaduna......



Jira kawai take taga shigowar motar da za'a shigo Dasu Alhaji sunusi.suna wannan xaman motar ya hanaf ta shigo cikin kotun ,shi kad'ai Dan wannan Karan anty mufeeda batazo kaduna ba,ya Tahir shima dai Bai zoba d:in ba Yana can wajen aikinsu ,ya hanaf ya fito yay cikin kotun yana kallan su Hajiya SA'A Dake ta Hange Hange tama kasa xama waje D'aya ,Kallo D'aya yay mata ya d'auke kansa yay shigewar sa cikin kotun, Dan itama ba qaramin haushin ta yake jiba.shigar sa babu dad'ewa motar AA Arab ta shigo cikin kotun, sai motar police Dake bayansu, driver yay parking motar ,wani cikin police d'in ya diro da sauri yaxo ya bud'ewa AA Arab motar , ya fito cikin shigar sa ta uniform as usual sai Wani bakin glass Daya Saka a idonsa Wanda Yay bala'in yi masa kyau, ruky Dake d'aya site d'in itama fitowar tai,sanye take itama cikin uniform Amma tasa wata blue black d'in Abaya,handa bag d'in tace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login