Showing 159001 words to 162000 words out of 278032 words

Chapter 54 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1083

saiga IG ya taho da kansa bayan an Bude masa motar sa ya fito ya nufo inda suke cikin tashin hankalin abinda ya semesu follow by minister,take police din suka nufi wajen su suna Sara musu cikin girmamawa,suna fada musu yadda abun yake,da yadda suka ga komai ,take IG da minster suka nufi wajen motar da akace AIG acikin ta ,take Saida xuciyar su tai tsalle ta buga da qarfi ganin wannan abin al'ajabin dayafi karfin ganin su take suka rintse Ida nuwansa, sbd abin yayi Muni da yawa . take suka sa aka kira asibiti . babu Bata lokaci wajen mintuna 20 saiga shi sun karaso,da motar ambulance dinsu ,su sukai aikin fito da gawar AIG cikin motar da kyar sbd yadda motar tai raga_raga, gabadaya Saida suka kau da kansa daga kallansa sbd gabadaya tundaga cinyar sa xuwa kafa fuwansa sun dagar gaje babu kyan Gani.kansa ne kawai Bai dagar gaje ba Amma ya fashe . Amma gabadaya jikinsa ya tashi daga aiki,take aka shigar shi ambulance jini sai xuba yake kamar Wanda tun kudo shi. an samu nasarar samun wayarsa aka bawa IG ya karva,idan sun samu lokaci su bincika Dan ganin waye last call din sa kamar yadda police din sa suka ce,take IG da minster suka bi bayan ambulance din,xuwa asibitin .aka bar wasu police din dasu tsaya awajen suda masu patrol din,sai yaran AIG da akace sukai kansa babbar heardquater Dake Abuja kafin bincike ya biyo ta kansu....



____________?&


Mamah tun daran jiya taita xuba idan ganin Kiran mijin nata Dan tasan xai kirata , tunda ta Saba duk daran duniya kafin su kwanta bacci xai kirata suyi waya yaji lpyarta data yaransa sannan daga karshe yace abawa Rukayya wayar idan batai bacci ba,sai dai shiru Hakan yasa mamah Tai deciding data kirashi.tai masa miss call kusan biyar baiyi picking ba,Kuma wayar tana ta ringing Amma Bai Yi picking ba, tai tunanin xuwa anjima Idan ya Gani ya kirata,sai dai har sama da awaya Daya Bai biyo bayan Kiran nata ba,Hakan yasa ta qara kiransa hoping yay picking call din,sai dai wannan Karan wayar akashe,take gaban mamah ya fadi ,Dan dama tun safe take Jin jikinta sanyi kalau babu dadi.gashi babu Wanda xata kira taji ko suna tare ,Hakan yasa ta cikin damuwa ta fito falor ta tar Rukayya da hanaf suna Kallo a falon sai hasiya me aikin ta .baba hasiya tai mata sannu da fitowa mamah ta ansa mata da kulawa .jiki asan yaye ta qarasa shigowa falon ta zauna kan Daya daga cikin kujerun falon, ganin yanayin ta yasa duka yaran suka hau tambayar ta da lpy ganin ba yadda suka Saba Ganin ba. Mamah tai murmushin karfin hali tace "lpy lau" Rukayya dawo kusa da ita ta xauna ta ce "mamah Abba nasan ya kira shine yau Baki bani wayar mungaisa ba koh?"ta fada tana kokarin karbar wayar Hannun mamah. ....



Mamah ta shafa kanta tace "Bai kiraba yau, Inaga Yana Wani abun ne Amma idan ya kira, zan kawo Miki ko kinyi bacci xan tashe ki kinji?" Rukayya ta gyada mata kai.ta kalli hanaf Wanda ke kallan ta tace"Maza hanaf tashi kuje ku kwanta dare yayi babu musu suka kashe kallan da sukeyi kowa ya shige dakinsa Dan kwanciyar bacci.bayan mamah ta shige dakinta haka kawai taji jikinta yayi sanyi kalau gabadaya ta dinga Jin faduwar gaba,take ta hau ambaton sunan Allah tana Kiran innalillahi wainna ilaihi rajiun,ta dauro alwala ta fara gabatar da sallah Saida tai kusan awa biyu tana kan sallaya sannan ta mike ta linke sallayan ta hau saman gadon ta ta kwanta tana fatan bacci ya dauketa,ta Dade kafin bacci barawo ya sacetan.....



Washe gari da safe wajen karfe tara da Rabi na safe ,mamah tana kitchen tana musu break fast Dan su Rukayya Basu tashi ba sai Mai aikinta hasiya wacce aka kawo ta daga kauye Dan taya mamah wasu abubuwan duk da bawai tana Shan wahalar aikin bane sai dai shi Abba da kansa yaga ya dace ta samu Mai tayata aikin tun bayan data farka daga bacci ta jawo wayar ta _ta qara darling number Abba, Amma har lokacin wayar akashe take, take Kuma ta fara Jin tsoro aranta Fargabar ta karu, Amma ta kawar da tunanin ta suka cigaba da aikin su jikinta har lokacin a mace yake .suna cikin yin aikin acikin kitchen ita da hasiya karar jiniyar motar police da suka ji daga waje yasa gabanta qara yankewa ya fadi , Amma Kuma batace komai ba, tunda Abba idan xai dawo da jiniya yake dawowa Amma Kuma da sassafe yau , Allah yasa lpy .saidai taji wannan jiniyar kamar tafi karfin ace iya Abba ne,Dan haka tai shiru tana sake sake aranta har baba hasiya na cewa yau yallabai ya dawo da wuri Hajiya.Amma mamah Bata ji taba,sbd tayi nisa cikin tunanin da take yi...



Kafin ta farga saijin qarar Bude gate tai ana kokarin budewa,su Rukayya da ya hanaf suka fito falor Jin qarar jiniya Dan sun tabbata Abba sune ya dawo haka suka fito cikin Doki da murna.mamah ta fito daga kitchen tana leko compound ta window falor,sai dai gabanta ya qara faduwa ne Saka makon ganin motar Dake bayan wata bakar mota Irin wacce mijinta ke xuwa acikin ta idan zaidawo ta shigo gidan,ta qara murxa idonta dai dakyau Dan tabbatar da abinda take Gani,ilai ko motar ce, motar asibiti, ambulance waye aciki? wa aka kawo ?Babu Mai Bata wannan ansar,Hakan yasa ta cigaba da kallon motocin Dake donnowa kai cikin gidan.iya motoci hudu ne kawai suka shigo gidan sauran motocin kusan shida suna waje Basu Samu damar shigowa ba,tuni ya hanaf ya fita compound Dan xuwa yaga abban sa ya tar beshi kamar yadda suka saba idan ya dawo . Rukayya Bata bishi ba ta koma kusa da mamah ta tsaya wacce ta kurawa motar da ta fara shigowa gidan ido taga ta Ina mijin nata zai fito , Amma har aka gama Bude musu motar mutanan ciki suka fito Bata ga mijin ta ya fito ba ,ta Maida dubanta kan ambulance din kirjinta na bugawa,baba hasiya itama fitowa tai daga kitchen din,Jin har lokacin jiniyar tanayi,har Wani police din Dake tsaron gidan nasu ya tsaya daga kofar falon bakinsa dauke da sallama tareda Neman ixnin shigowa,aka bashi damar shigowa,bayan shigo ya gaida mamah ,Bata ansa ba illa kallan ambulance din nan kawai take,ganin Bata ansa ba yasa yace"Hajiya ance ana Neman ixnin shigowa falon nan wurin ki, mamah gabanta ya qara yayenkewa ras ya fadi,ya cigaba Yace"IG ne da minister da sauran manyan mutane,mamah dai batace komai ba, Rukayya tace"su shigo cikin sanyin jikin Daya shigeta lokaci Daya,ya Fita daga falon domin xuwa ya Tarar dasu,tai Maza ta kawowa mamah hijab, mamah Bata karba ba Dan kamar suman wucin gadi ma tai Ba ta san abinda take tunani axuciyarta ya zama gsky, gabadayansu acikin rudani suke,ta juya ta cigaba da kallan ambulance din,gabanta na faduwa , ganin mutanan xasu shigo yasa Rukayya ta Saka mata hijab din ajikinta........






07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?*



*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*




*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*




*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 6?? 6??



___________?&

IG da minster tsaro suka shigo falon Baku nan su dauke sallama.har lokacin Kuma mamah tana tsaye tana kallan window Bata zauna ba . suka nemi waje suka xauna,sai alokacin mamah ta juyo xuwa garesu ta daga kafarta Dakyar ta dawo cikin falon ta zauna kan kujera, Rukayya ta gaidasu suka ansa mata da kulawa.babu Bata lokaci IG ya fara jawabin abinda ya kawo su da Kuma abinda ya faru. tunda IG ya fara magana mamah take kallansa Tama kasa fahimtar me yake fada kukan da Hanaf da Rukayya suka fashe dashi shiya dawo da mamah hayyacinta, Amma Batai magana ba,kukan ma Bai xo mata ba, sbd yadda abun ya shigeta da yawa .baba hasiya cikin Kuka da kyar tace Allahu Akbar, Allah Mai girma, Allah sarkie yallabai,wayyo Allah na ,wayyo Allah.sudai su IG hkr kawai suke Basu suna xaune har akace su taso ankai gawar part din Abba .....



Da kyar suka samu mamah ta tashi da tai makon baba hasiya har Kuma lokacin mamah ko digon hawaye Bai xubo mata ba,Dan kamar ma suman xaune tai ,da kyar mamah ta qarasa cikin falon ,suna shiga IG ya Bude musu iya Wani sashi na fuskarsa Dan su ganshi,Dan baza su iya ganinsa gabadaya ba, Dan indai suka ganshi wlh zasu iya Suma sbd munin abun .suna yin Arba da furkarsa da sunan matacce, Rukayya ta yanke jiki awurin ta fadi,hanaf durqushewa yay awajen ya rungumo abban nasu Yana cewa Dan Allah Abba katashi innalillahi wainna ilaihi rajiun.da kyar aka janyeshi sbd yadda ya dakumu gawar gashi jini sai xuba yake kamar me,Dan ahakan ma baku ga Irin likkafanin da aka linka masa ba,sbd jinin yaki tsayawa,mamah k'ura masa ido kawai tai ,Dan har lokacin Gani take kamar a mafarki kamar ba GSK ba .ganin wannan jinin da tai Yana xuba daga jikin mijinta sai alokacin mamah fasa Wani Gigi taccen kuka ta fadi awajen sumammiya baba hasiya tai kanta tana kuka tana ambatar sunanta tana jijjiga ta......



Kafin kice me rasuwarsa AIG umar MaiTama ta karade duka Nigeria bama iya Kaduna ba, awannan lokacin Alhaji sunusi ya shigo gidan wujiga wujiga dashi Yana surutai da sunbatun karya .dayaga gawar shine harda faduwa sai kace GSK, harda kukansa wujiga wujiga, maman Shareef ma taji lvr ta taho gidan 'yar uwarta a gigice sbd abunne ya bugesu .mutuwa lokaci Daya Babu wata jinya ba komai.Hajiya SA'A ma taxo ta,da mijinta ya fada mata.aka dauki su mamah aka shigar su part din su,aka kira doc tuni suka dukufa akansu Dan Basu taimakon gaggawa,maman Shareef sai Kuka take kamar ranta zai fita.karfe biyun ba Ranar juma'a akasa xa'ayi jana'izar Marigayi AIG umar MaiTama,sbd shugaban kasa zaixo da manya manyan mutane,da Kuma sarakuna.gomnan kaduna shine Mai tarbar Baki,kafin karfe 11na safe gidan AIG umar MaiTama ya cika da dun bin al'ummar musulmai Dan halartar samun jana'izar. Yaya Tahir ya taho daga garin Lagos a hargitse.anty mufeeda ma ta xo ita da mijinta, cikin tashin hankali,in kuka ga yadda ta susu ce saiku rausaya mata, lokacin Bata haihu ba Amma da karamin ciki dai ajikinta.....



Lokacin da Mamah ta farka data tuno da tashin hankalin Daya samesu take ta fashe da Kuka, gabadaya 'ya'yan ta suna zagaye da ita.suna kuka suna rokonta itama ta tashi karsu rasata.bayan ta farka ta mike xaune da kyar daga kwancen da take, tana kokarin sauka daga saman gadon,maman Shareef ta riketa,cikin tausayawa da lallashi tace "Ina xaki Halima?mamah tace cikin Kuka "adda zance naga abban mufeeda,bangan Shiba inaso naje muyi ban Kwana kuma na nemi yafiyarsa " ta karasa fada tana Mai rushewa da gunjin kuka.maman Shareef ta girgixa mata kai tace cikin kwantar da murya da lallashi " ai kinganshi dazu Halima banaso ki Kara xuwa ki Suma kamar yadda kikai dazu"mamah ta fashe da Kuka tace "adda yanxu shikenan na rabu da mijinah uban 'ya'yana," yanxu yarana sun zama marayu?waye ya kashe min miji ,me yay musu? Meya tare musu?innalillahi wainna ilaihi rajiun, Allah na tuba Allah ka yafe min,ya Allah kajikan Abba ,kai masa Rahma kasa ya huta,duk suka ansa da Ameen....


Gabadaya ta rungumo yaranta ta fashe da Kuka kamar yadda Suma suka fashe da Kuka,maman Shareef Bata hanasu ba, ta xuba musu ido tana kallansu da tausayawa tabbas dole suyi kuka, dole Irin wannan mutuwar bazatan tafi kowacce mutuwa ciwo, ba'a tayar ba ba'a kwantar ba kawai sai gawar mutum aka kawo Maka da sunan ya mutu.innalillahi wainna ilaihi rajiun,itama sai hawaye shar shar haka suka Hadu suna ta kuka babu me bawa Wani Baki acikin su .wajen karfe biyu na Ranar aka da lokaci xa'a ayi masa sallah daga can a mikashi gidansa na gsky.aka kira su mamah da yaransa dasu fito suyi masa addu'o'i,maman Shareef ce ta rike Mamah wacce da kyar take tafiya sbd jire Dake Neman kada ta,ta zaunar ta gaban gawar akace basai an Bude Shiba suyi masa addu'ar ahaka, Alhaji sunusi shine ma gaba ga wajen kamo gawar su kawota ciki.anan ma Saida mamah ta kusan Suma sbd yadda ta qara sakin Wani sabon kukan da kyar ta tsagaita da kukun itada yaran suka fara jero masa addu'o'in dacewa a lahira,da Kuma rokar Allah ya yafe masa xunubansa,inka ga wannan ahalin dole saika tausaya musu sbd tausayi.....



Karfe biyun Rana akayi yiwa AIG umar MaiTama sallah a babban masallacin unguwar su Dake malali,bayan andawo daga Kaishi Alhaji sunusi sheki karbar gaisuwa,shida Yaya Tahir sai ya hanaf .shugaban kasa ya shiga cikin gidan Dan yiwa su mamah ta'aziya,Dan Yana so su koma da wuri.da zai fito yasa aka tura musu kudi Naira miliyon 50, IG da minster ma da wasu manya manyan kasar da suka halarci wannan jana'izar Marigayi AIG umar MaiTama sun shiga sunyiwa iyalansa gaisuwa tareda Basu makudan kudade,haka suka fito suka tafi,akabar iya wasu yan garin da Kuma 'yan uwa da abokan arxiki, commissioner 'yan sanda ma yaxo har dasu AA Arab Amma shi awaje suka tsaya,basu shiga gidan ba, governor kaduna shima ya zauna dashi ake karbar gaisuwa,har lokacin mamah Bata dawo hayyacin ta ba, tunda aka tafi kai Abba gidansa na gsky take ta surutai da Kuka kamar ranta zai fita.dakyar maman Shareef take rarrashinta da nasiha da ban Baki.shima Alhaji sunusi ya shigo gidan ya dinga kuka yana bawa su mamah hkr da cewa ai wannan mutuwar su aka yiwa Allah ya Saka musu ko suwaye suka kashe Dan uwansa baxai taba yafewa ba.....



To haka dai wannan ahalin suka Wuni suka kwana basu rintsa ba.washe gari ma anyi ta karbar gaisuwa da kyar mamah ta dan nutsu sbd karatun Qur'anin data dinga Yi anan ne ta 'Dan samu nutsuwa,sai dai kukan ne dai Bai tsaya ba har lokacin.dan tanayi lokaci xuwa lokaci,har akai kwana uku da rasuwar ,akai sadakar uku, Alhaji sunusi kullum Yana wurin xaman makoki Yana karbar gaisuwa.su IG sun koma anyi bincike an Gano cewa da Dan uwansa sukai waya,wato Alhaji sunusi Dan shine last call din sa.take akace adauko Alhaji sunusi,duk inda yake anemo shi .a ranar kwana na hudu da rasuwa , Alhaji sunusi Yana gidan yallabai taju,suna kulla kullarsu kamar yadda suka Saba.motar jami'an tsaro ta Dira a kofar gidan yallabai taju bisaga tracking dinsa da sukayi anan suka gano Yana gidan . Alhaji sunusi suna tareda yallabai taju da sauran mutanan su,akashigo har falon da suke xaune akace ana Neman Alhaji sunusi, akace suwaye police din suka ce wasu jami'ai ne, yallabai taju yasa a shigo Dasu,bayan sun shigo suka gaisa , sannan suka fadi abinda ke tafe dasu.Alhaji sunusi na Jin haka ya mike jikinsa na rawa ya ce"shi me yayi nan dai ya tubure yace"shi me yayi baxa Shiba" sukace idan yaje can office Abuja ZA'A Sanar dashi abinda ya aikata, ya kalli yallabai taju a firgice yaji me zaice,sai ji yay yallabai taju yace "kaje sunusi "ya dubi jami'an yace ,"kuje waje zai biyo ku yanxu,bayan sun fita , Alhaji sunusi yace cikin tashin hankali"yallabai na bisu Kuma? yallabai taju ya gyada kai yace"kaje sunusi babu komai ni nayi maka alqawari kome ka aikata daga yau xuwa gobe xa'a kashe case din, babu yadda Alhaji sunusi ya ya iya ya fita compound din gidan haka suka tusa keyarsa suka tafi dashi Abuja kamar yadda aka umarceshi su.kafin su sauka har yallabai taju ya kira IG ya tambayeshi me Alhaji sunusi yay da za'axo har gida atafi dashi.nan IG ya sanarwa da yallabai taju komai game da zargin da suke yiwa Alhaji sunusi.bayan ya gama magana.yallabai taju yace "To Kuma yanxu IG Taya ya kake ganin xai iya kashe Dan uwansa guda daya Daya rage masa aduniya, kuyi tunani da kyau,kawai Dan sunyi waya dashi shikenan saiya zamanto cewa shiya aikata haka , shiya kashe shi?.....




IG yace"y'allabai kaima kasan koba shi bane dole hakace xata kasance tunda shine last call din sa, yallabai taju yace "naji Amma IG inaso kamin wata Alfarma kai kasan cewa kai nawane,Dan Allah arufe wannan case din, banaso kowa yaji ciki kuwa harda iyalan AIG, IG yace"yallabai kasan ba iya ni kadai bane kan case din harda president ga amininsa minister tsaro"yallabai taju yace"indai wannan ne babu matsala president ai nawane, IG yace shikenan yallabai,ni dai yanxu duk abinda president yace"ai Banda ta cewa akai"yallabai taju yace"xanyi magana da president din yanxu" daga haka sukai sallama...



Bayan president ya gama sauraran yallabai taju ya numfasa yace "Amma yallabai kasan wannan maganar ba lallai ta kasu cikin ruwan sanyi ba koh?,kasan minister yaji,kila Kuma ba iya mu kadai maganar xata tsaya ba"yallabai taju yace"sai dai idan baxakamun abinda na umar ce kaba president Amma waye minister,kasan minister xabin Kane duk yadda kace masa dole yabi ka,ai tunda babu Wanda ya sani daga ku _ku uku aishikenan.sbd haka ni dai ga Abinda nace Ina jiran naga sunusi ya dawo gida daga nan xuwa gobe da safe,daga haka ya kashe wayar.shiru minster yay bayan ya gama sauraran president meyasa president zaice su bar case din bayan kowa ya Gani cewa Dan uwansa shine Wanda sukai waya dashi na qarshe,Kuma suna tunanin gunsa ya tafi,maganar da president yay ita ta dawo dashi daga tunanin daya tafi,yace "shikenan sir, Amma su iyalansa fa da muka fada musu cewa xamuyi bincike" president yace "wannan karka damu ni nasan me zan fada musu, babu yadda minister ya iya ya sauke numfashi yace "shikenan sir"daga haka sukai sallama, minister ya Dade baiji bakin ciki da haushi Irin na wannan lokacin ba,ace wannan kasar kullum bamu da aiki sai cin zalin na qasa damu,sai corruption Allah dai ya sawake.....


_____________?&


Washe gari da safe kamar yadda yallabai taju ya bawa president umarni sakin Alhaji sunusi hakance ta faru,sai gashi da safe an sake shi,ya dawo gida.bayan anyi bakwai din AIG UMAR MAITAMA ya Tahir ya koma wajen aiki,ita Anty mufeeda ba yanxu ba saitayi sati biyu Dan xama a kusa da mamah tana kwantar mata da hankali.tunda akai bakwai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login