Showing 153001 words to 156000 words out of 278032 words

Chapter 52 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1092

da Dan uwansa ba kamar yadda shi ya damu dashi, kawai shi duk abinda yasa agaba to shi yakeso,Kuma saiya cinmasa .ahaka dai sunusi yake bin'yan siyasa gari gari suna musu bauta,ko Kuma su dinga samo musu 'yan mata suna aikata alfasha dasu , batareda iyayensa sun saniba bayan ya samu ya gama secondary school,su iyayensa basason ya dinga bin 'yan siyasa, sun fiso ya neme aiki Irin yadda Dan uwansa yay, ko Kuma ya nemi wata Sana'ar,acewarsu siyasa ba Abar arziki bace,shikuma sunusi ya nuna musu yafison siyasa,ganin yaki Jin maganarsu ,yasa suka samu umar suka tun tube beshi da maganar akan yaywa Dan uwansa fada ya Kuma bashi shawarar ya bar bin 'yan siyasa,ya nemi Sana'a yafi masa.umar ya ansa musu da in Sha Allah zai masa magana, baiyi kasa agwiwa ba ya samu sunusi yay Masa fada ya Kuma bashi shawara....



Sai dai shi sunusi Bai dauka ba, dan abinda ya fadawa iyayensa shiya fadawa umar,umar yay yay da sunusi ya fahimci abinda yake San Ankarar dashi Amma sunusi yace shi ga Abinda yake so ,Kuma shi zaiyi,ganin yaki saurararsa yasa ya fadawa iyayensa yadda sukai da sunusi, basuji Dadi ba, Dan dama sunfi Jin dadin zama da umar akan sunusi, umar ya ce"su kyaleshi kawai su bishi da addu'a tunda haka ya xaba kila hanyar cin abincinsa da Kuma alkhairinsa Yana ga siyasar ne,babu yadda suka iya suka kyale sunusi yake bin 'yan siyasa.haka suka cigaba da gurgurawa, har Allah yasa shekara suka Dan karu alokacin Kuma umar ya hadu da Halima yaxo Wani Dan huta Daya samu Kaduna,ita Kuma taxo xiyara wajen yayarta maman Shareef,wato Hajiya Maryam......



Alokacin suka hadu,da umar da Kuma Halima Asalinasu 'yan jihar Adamawa ne,to saitaxo Kaduna xiyara daga bayama saita dawo kaduna da zama gabadaya.to awannan lokacin Kuma suka kulla soyayya tsakanin UMAR da Halima hardai ta kullu harta kaisu ga zancen aure suka amince wa junansu xasuyi aure karkashin inuwa Daya, ganin sun dai dai ta yasa umar alokacin ya samu iyayensa yace AURE zaiyi, babu musu iyayensa suka yarje masa .Kuma iyayensa sunyi murna sosai da haka, akayi bincike aka gano yarinya ta kirkice, shima Kuma anyi bincike akansa,har ta kai ga ansaka ranar AURE, Babu dadewa Kuma ranar biki taxo akayi biki.bayan anyi biki amarya ta tare anan cikin Kaduna , gefe Daya shikuma umar yana cigaba da aiki a Adamawa.saida ya danyi kwanakin amarcinsa sannan yay sallama da iyayensa da matarsa ya koma wurin aiki.Bayan bikinsu da sati uku mahaifinsu Muhammad MaiTama Allah yay Masa rasuwa,sunji mutuwar nan sosai UMAR ya dawo gida.bayan anyi sadakar bakwai umar ya koma wajen aiki, bayan anyi arba'in ma yaxo, akuma lokacin ya tafi qara karatu,bayan wata goma Allah ya sauki Halima lpy ta haifi danta namiji,yaci suna Tahir,.....



Tahir Yana shekara Daya Allah yaywa babarsu rasuwa,itama mutuwar nan ta jijjigasu sosai,ya xamto yanxu Basu da kowa sai Allah,Hakan yasa umar bayaso Yabar Dan uwansa shi kadai agidan bazaiji Dadi ba,hakan zaisa ya dinga tunawa da mahaifansu ,Dan haka yasa ya ce"ya dawo gidansa da zama babu musu sunusi ya dawo gidan da zama, Babu abinda umar baya yiwa sunusi a arayuwa komai shi yake masa,kamar lokacin da iyayensu na yare,babu abinda ya rageshi dashi, duk Dan bayasan ganinsa a damuwa,bugu da qari ma atunaninsa ko Hakan xaisa sunusi ya daina siyasar da yake ya dawo ya cigaba da karatu,sai dai shi sunusi babu hakan a lissafin sa, yayi masa nasihar yayi masa fadan Amma sunusi yaki ji ganin yayi nisa bayajin kira yasa umar kyaleshi ya cigaba da siyasar sa,sai dai abinda umar Bai saniba shi sunusi bashida da kunya ga San rayuwar qarya acikinsa,to ahaka dai Halima take hakurin zama dashi Kuma ko kadan bata taba tunanin fadawa Dan uwansa ba.kwance tashi babu wuya awurin Allah haka suke gurgura rayuwa har shekara uku suka wuce suna rayuwar su cikin kwanciyar hankali da soyayyar Mai tsafta suke ginawa suna son junansu kamar me, tsaka Fatima da mijinta babu wata matsala saima soyayya da shakuwa Dake qara shiga suka xuciyoyinsu.haka dai Halima ta qara haihuwa wannan Karan Kuma mace ta haifa,taci sunan mahaifiyar su umar wato bilkisu ake ce mata mufeeda....



Akuma lokacin umar bayan mufeeda tai shekaru biyu ya gama karatun Daya tafi Yi,ya qara samun qarin girma awurin aiki , star (' biyu, sunyi farin ciki sosai,akuma lokacin shima sunusi yaxo da maganar ya samu matar AURE,babu musu umar ya amince masa Dan babu laifi shima Yana Dan samun kudi sosai Kuma Shima umar yana Bashi.Dan har mamaki umar yake ganin yadda sunusi yake facaka da kudi,kamar Wani Mai Sana'ar kirki.saidai baya taba taimaka musu, Su_ma Kuma Basu taba rokarsa ba,abinda ya qara basu mamaki Bai wuce kyautar gidan sunusi yazo yace anbashi ba,sunyi matukar mamaki,wai har gida Wani Dan siyasa ya bashi,UMAR Baiyi magana ba, Amma ya tambayi sunusi yadda akai shi Wanda ya bashi gidan ya bashi, sunusi ya fada masa cewa kawai kyautar yay musu su_su biyu shida Wani abokinsa, sakamakon aikin da suke musu ,Bai gamsu ba Amma dai yasa masa albarka,sai dai abinda umar Bai saniba shine, sunusi Yana Neman mata,Dan kamar bunsuru haka yake idan yaga mace,Dan dalilin lalacewarsa ma wannan matan da suke kawalcinsu, suke kawowa su yallabai taju,to anan Suma suka lalace,idan suka gama dasu Suma saisu Basu Wani Abun suyi amfani dasu wannan kenan.akai komai na qa idar aure kamar yadda addini ya gindaya mana, amarya SA'ADATU , wacce ake ce mata SA'A, suka tare awannan gidan,akuma lokacin babu abinda Halima (mamah)Bata saniba na halin sunusi sbd ta zauna dashi ta karanci komai na halayyar sa, akuma lokacin tasan yana da San kansa,da Kuma San xuciya.bayan watanni da auran Mamah ta qara samun Wani cikin,babu dadewa Kuma itama matar sunusi ta samu ciki, tsakanin su da Halima wata hudu ne,Saida mamah ta fara haihuwa sannan itama SA'A ta haihu.mamah ta samu Da namiji Wanda yaci sunan babansu umar Muhammad Amma ana ce masa hanaf,shi Kuma Dan gidan SA'A yaci sunan uban gidan sunusi Abdul_lateef,suke ce masa lateef,to anan dai zamu iya cewa tare mamah da SA'A sukai goyon hanaf da lateef , suna Kuma xiyartar juna lokaci xuwa lokaci.....



Akuma lokacin ma Alhaji sunusi ya samu wuri cikin 'Yan siyasa Dan ya zama babba,shida babajo Ali Dan anan suka hadu.bayan shekaru biyar mamah ta qara samun Wani cikin ita kuma Hajiya SA'A shiru Bata samu ba, lokacin haihuwa yayi mamah ta haifi 'ya mace taci suna Rukayya ,daga nan haihuwa ta tsayawa mamah, akuma lokacin umar Wanda 'ya'yan sa suke ce masa ( Abba)ya qara tafiya qaro karatu masters kenan,shima Alhaji sunusi ya Dan samu yayi diploma sbd uban gidansa yace yayi Dan xasu iya xama Wani Abu Suma nan gaba.Yaransu duk sun fara wayo Dan babu Wanda ba'a Sa amakaranta ba,iya Rukayya ce kawai ba'a Sa taba,ga Hajiya SA'A ta damu ta haihu saidai Bata samu ba, lateef Kuma kullum Yana gidansu hanaf wajen Rukayya Dan Allah ya Dora masa kaunar ta axuciyarsa wannan kenan.....


___________?&


*Bayan shekaru goma Sha biyar*



Awannan shekarun abubuwa xun ja kuma sun sauya,aciki kuwa harda qarin matsayin da umar MaiTama ya samu na matsayin AIG na qasa wato matai makin IG na qasa,da Kuma girman yaran da Kuma shekarun su,Dan ya Tahir kan yanxu akalla zaiyi shekaru 28,anty mufeeda 25,ya hanaf 22 shida lateef,ita Kuma Rukayya 16 ,akuma lokacin tana ss3, sune bana zasuyi candy ,anty mufeeda tayi degree dinta,ta gama akuma lokacin ta samu mijin AURE,aka Saka ranar AURE shekara Daya, lokaci babu wuya awurin Allah ahaka itama akai auran anty mufeeda inda aka kai ta Abuja,ya Tahir Kuma ya samu aiki a kamfanin oil &gas Dake jihar Lagos,saiya hanaf Wanda shi Bai gama hada degree dinsa ba sai nan da next year Dan a Oxford university yake ,sai Kuma lateef Shima ba'a kasar yake karatunsa ba, Yana can intanbul anan yake karatunsa ta qasar turkey.sai shi Kuma Alhaji sunusi Wanda ya xama Daya daga cikin manya manyan cikin 'Yan siyasa ajihar Kaduna,burinsa daya Dade Yana dakon jiran sa ya cika,gasu Kuma yaran su yallabai taju, Wanda su yanxu sun xama god father's acikin siyasa,suke sawa Kuma suke hanawa,ko president na wannan lokacin Dan jam iyayarsu ne Kuma a qarqashin su yake Kuma dole duk abinda sukace shi xa'a Yi,kai xamu iya cewa shi president shi yake da mulkin Amma Kuma su_su suke aiwatar da abinda xa'ayi akan mulkin.....



Akuma lokacin Alhaji sunusi ya xama dan Majalisar Tayayya,Mai wailtar Kaduna da ZARI'A,bisa ga taimakon su yallabai taju.bayan shekara Daya da fara mulkinsu matsalar tsaro ta qara dawowa sabuwa,aqasa Baki daya da abin yayi sauki Amma yanxu abun yayi yawa, alokacin dasu yallabai taju sukai nasu mulkin shima ansha wahalar Rashin tsaro da Kuma satar 'ya'yan mutane ana safarar su ana fitarsu daga kasar, Kuma anrasa ta Ina matsalar take,akuma lokacin su_ su AIG umar MaiTama da minister tsaro da duk masu ruwa da tsaki akan harkar tsaro sukai meeting akan xa'a dakile wannan matsalar,sai dai abinda Basu sani ba,shi IG na wannan lokacin bakinsu Daya dasu yallabai taju,Dan da saninsa su yallabai taju suke sawa ake wannan ta'addancin,shikuma AIG umar MaiTama da minister na wannan lokacin Basu saniba, marasa gskyr cikin su sunfi masu gskyr cikin su yawa,to akuma lokacin akasamu Wani jajir taccen ASP Wanda baifi shekaru biyu da gama karatunsa ba,ya fito a rank din ASP,Mai suna Ahmad Aliyu Arab, Wanda abokanan sa ke kiransa da AA Arab,Wanda alokacin Kaduna akafi takura da katsina da Kuma zamfara,sai akasa ko Wani commisner na jiha ya zabu jajur tattun 'yan sanda ayi training dinsu sannan a kaisu inda ake yawan kaiwa harin to anan ne sunan AA Arab ya fado akuma lokacin yasan su waye yallabai taju, awannan lokacin Kuma AIG umar MaiTama shima ya tsaurara bincike sosai lungu da Sako, akuma wannan lokacin shi hanaf ya dawo gida bayan ya gama karatun sa,shi lateef bama Yasan Karatun shiyasa har lokacin Bai gama ba sai bin abokanan Banxa da bin matan Banxa,akuma lokacin ita Rukayya take shirye shiryen gama secondary school.akuma lokacin yaji ya kamu da son Rukayya so na aure, bawai na 'yan uwan taka ba kamar yadda yake mata ada .akwai lokacin da lateef yaxo hutu yaxo gidan yaga yadda Rukayya ta qara girma ta Kuma qara kyau, to tun daga nan ya qara sawa aransa Rukayya tasace Dan dama can Yana San Rukayya,gashi iyayensa sun Dora masa Sorayayyar duniyar nan akansa kamar me,ko kadan basa san laifinsa......






07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y

____JAMI'AR TSARO ____

____THE WOMEN POLICE ____

NA

____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____

_(MRS SARAKIES)

TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('

TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S

Bismillahirrahmanirrahim

_______season two ep 6?? 4??

___________?&

Awannan tsaron da aka Saka yasa su yallabai taju shiga Wani yanayi Dan basa San ko kadan asirinsu ya tonu asan Irin Sana'ar da sukeyi,gashi shima kansa Alhaji sunusi idan akace xa'a tsaurara tsaro tofa bashi da wata hanyar samun kudi Kuma dama siyasar ce sai wannan harkar dasu yallabai taju suka jefasu acikin ta,idan aka rabashi da ita ai asirinsa ya tonu.commissioners sunyi abinda aka umarcesu dasuyi, ajihar Kaduna su AA Arab sun fara aiki yadda ya kamata sai Kuma abubuwan suka fara sauki, gashi da GSKY da Amana,da hajircewa kan aikinsa.su yallabai taju Suka rasa ya zasuyi,kawai Alhaji sunusi ya Bada shawarar me xai hana a kira AA Arab tunda shine shugaban committee suyi masa tayin makudan kudaden da sai gigi tashi, gabadaya sai sukai na'am da shawarar Alhaji sunusi . babu Bata lokaci Suka kira AA Arab xuwa gidan hutawarsu.ganinsa kamar yaro ne suke ganin ai baxasuyi wahalar shawo kansa ba, Kuma baxai wahalar siyewa da kudi ba .yasa suka sa Alhaji sunusi da babajo Ali su kira AA Arab Dan alokacin shine shugaban committee da aka Saka na jihar Kaduna,AA Arab yayi mamakin Kiran dasu yallabai taju sukai masa, Amma baiyi magana ba,Saida yaxo Suka gaisa cikin mutunci sannan suka bude masa cikinsu gabadaya da Kuma abinda sukeso yay musu tareda tayin makudan kudaden da zai ishe shi rayuwa har karshen rayuwar sa bazai talauci ba.....

AA Arab baiyi magana ba, illa xuba musu ido kawai da yay Yana sauraran su,har suka kai karshe, suna jiran suji me zaice,AA Arab Saida ya maula dan kansa sannan ya numfasa calmly yace "gsky y'allabai Kun bani mamaki,ban taba tunanin haka kuke ba ko kadan Ashe dama fuska biyu gareku ,azahiri ku nunawa al'umma ku mutanan arxiki be,abadini Kuma Ashe kune Masu sawa ake aikata duk wannan ta'addancin da akeyi a qasa,? Alhaji sunusi ya daka masa tsawa yace" kai ka iya bakinka ka san agaban WA kake kuwa" ya fada kamar xai kaiwa AA Arab duka. Yace "yallabai ne fa.AA Arab yay wa Alhaji sunusi Wani kallo, ganin haka yasa yallabai taju yay murmushinsu na manya, sannan ya dubi AA yace"Dan samari kenan,to idan bamuyi haka ba, Tayaya Kake tunanin xamu samu abinda mukesu,mutara dukiya yadda ranmu yakeso.kai ma ka amince ka samu kudin da zaka Gina rayuwar ka data iyalanka,kai harma da iyayan ka,Dan na tabbata indai ka amince da sharadin mu, sannan muka baka makudan kudin nan dakaji mun am Bata to Ina Mai tabbatar Maka kaida talauci kunyi hannun riga har abada, kar da zuri'ar Kuma baxa suyi talauci ba,ya karasa fada yana murmushi tareda kure AA Arab da ido.AA ya girgixa kai ya mike yace "bazan iya ba,kurike kudin ku, Allah ya tsare ni da Gina jikina da haram,ku da Kukaga zaku iya kuje kuyi tayi, sannan Abu na qarshe da zan fada muku shine kuji tsaron Allah, ku tuba ixuwa gareshi karku sake ku mutu Kuna aikata wannan xalincin, sannan idan Baku daina ba wlh ni da kaina xan tona muku asiri kowa ya sani.....

Alhaji sunusi ya qara xaburowa zai qara magana, yallabai taju ya qara dakatar dashi,saiya koma ya na huci kamar Wanda akayiwa ubansa Rashin kunya.yallabai taju ya Kalli AA Arab yay murmushi yace "cool down abokina koma ka zauna" ya kalli babajo Ali yace "mikomin jakar kudin nan naga alamar Dan baiga kudin bane shiyasa yace baxai yiba, Babajo Ali ya kawo jakar kudin ya dire gaban yallabai taju, yallabai taju yace "kai masa gabansa ya Buda ya Gani",babu musu ya dire gaban AA Arab, yallabai taju yace "gashi ka Buda ka Gani kasan cewa Bada wasa muke ba,ashirye muke,"AA Arab yay Wani Dan iskan murmushi yace "kai atunaninka Ahmad Aliyu Arab zai siyu da kudi ne,to Kun makaro domin ni ba haka nake ba,ko kundau ka nima Irin gurba tattun jami'an tsaron nan ne,da xuciyar su ta mutu toni ba haka nake ba,ya ture kudin xuwa gaban yallabai taju yace "Kuma sai duniya tasan da abinda kuke aikatawa kunji na fada muku".yallabai taju shima ransa ya Baci da taurin kai Irin na AA Arab yace"to waxa ka fadawa,?nace waxaka fadawa ?ya cigaba Yace"to idan baka sani ba bari na fada Maka da babban Baki. ita Kanta kasar nan da kake ganin ta, to atafin hannun mu take,da masu mulkarta da al'ummar cikin ta duka a tafin a hannun mu suke ,sbd haka kaje duk inda zakaje ka fada, Kuma wlh saina dauki mummunan mataki akanka, kaskantaccen jami'i kawai daga haka yallabai taju ya tashi daga kan kujerar da yake xaune ya ya shiga ciki fuuuu kamar xai tashi sama.AA Arab ya bisa da Wani kallo sannan ya nufi kofar fita, Yana Jin su Alhaji sunusi suna ta xaginsa Amma Bai kula suba.....

To tun daga nan su yallabai taju suke kokarin suga ko_su kawar da AA Arab ko Kuma su dauki mummunan mataki akansa, yadda babu yadda xaiyi ya fadawa Wani abinda suka tattauna dashi.shikuma Alhaji sunusi shima Yana ta iya bakin kokarinsa wajen ganin kar wata baraka ta shigo cikin harqallarsu.gefe guda Kuma yallabai taju Yana masa hannunka Mai sanda akan wai AIG Dan uwansa ne, Kuma shine jagoran wannan committee da aka Saka sbd haka me xai hana yay convincing dinsa ya cire hannunsa aciki, shidai Alhaji sunusi Yana cikin tsaka Mai wuya tunda Dan uwansa ne AIG uwa daya uba daya,haka dai yallabai taju ke cewa zaiyi maganin su _su duka,ganin Irin takurawar da yallabai taju ke masa akan yaje ya jama dan uwansa kunne yasa ya yanke shawarar xuwa har gida idan AIG umar MaiTama yaxo weekend ya same shi.kawai rana kwatsam Alhaji sunusi ya tafi gidan AIG umar MaiTama, dama weekend ne dan ya tabbatar yanxu ya xo weekend.....

Ranar wata asabar ya shirya Dan xuwa ya sameshi yay Masa magana a siya sance, batareda ya gano me yake nufi ba .dan ya cire hannunsa cikin wannan tsaurara tsaron Dayasa akeyi ko yace sukeyi gabadaya.bayan ya isa gidan anyiwa Alhaji sunusi iso cikin falon gidan. Amma yace wajen Dan uwansa yaxo,babu musu akace ya shiga part din Abba, Alhaji sunusi ya nufi part din Dan uwansa,ya zauna a falor,shi Kuma Abba Yana ciki Yana kokarin fitowa warin Dan uwan nasa,bayan kamar mintuna 4 da zaman Alhaji sunusi a falon yayan nasa, wayarsa ta fara ringing ya dauko ya duba Mai Kiran sai yaga y'allabai taju ne ke kiransa ,Dan haka yay picking cikin rawar jiki, tareda gaisheshi kamar duka masa .daga Daya bangaren yallabai taju yace cikin takama da Isa "sunusi MaiTama kaje gunnasan , Alhaji sunusi ya ansa cikin girmamawa,eh yallabai yanxu haka ma Ina falonsa, Amma Bai qaraso ba,Ina xaman jiran fitowarsa.daga Daya bangaren yallabai taju ya jinjina kai kamar Alhaji sunusi Yana gabansa yace "ya Maka kyau sai kayi abinda nace" Alhaji sunusi yace cikin girmamawa "eh yallabai in Sha Allah zanyi yadda ka ce ,daga nan yallabai taju ya dinga fada masa Irin abubuwan da zai fada danya shawo kan AIG umar MaiTama,daga nanfa suka saki layi, suka dinga zantuttu kan Irin abubuwan da suke aikatawa da Kuma illar abinda zaj jawo muddin akace xa'a cigaba da tsaurara tsaron nan, daga Alhaji sunusi har yallabai taju mantawa sukai a inda Alhaji sunusi yake,har AIG ya nufo falon nasa bakinsa dauke da sallama xuciyar sa Daya .Alhaji sunusi Bai jiba,ganin ba'a ansa ba yasa qara Mai Mai tawa nan ma shiru magan ganun da yaji Alhaji sunusi yanayi sama sama da Irin zantuttu kan dayaji Dan uwannasa nayi ta waya da Wanda baisan wanene ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login