Showing 147001 words to 150000 words out of 278032 words

Chapter 50 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1060

kamshi yake,ta dube shi aSanyaye tace "lateef dadyn kafa har yanxu shiru Ina ya tafi.lateef ya tsaya yana kallanta sai Kuma ya Dan yamutsa fuska yace "mom ki kwantar da hankalinki Dady fa yana nan kila ko yayi tafiyane, Hajiya SA'A tace A Sanyaye "Wani Irin tafiya lateef duk Inda Alhaji xashi ai Yana fadamin.....



Lateef Yana gyara xaman glass din fuskar ya ce " kika sani ko yanxu ya sauya bayan so ki sani , Hajiya SA'A ta Bude Baki tana kallan lateef da mamaki ganin shi baima damuba .sai Kuma ya ce"ki bari xuwa anjima Idan Bai dawo ba ki sake gwada Kiran nasa Kiji , Hajiya SA'A ta gyada kai tace "shikenan,yanzu Ina xaka" lateef yace "xan Dan fita ne, Hajiya SA'A tace " shikenan saika dawo,daga haka lateef ya bar falon tabishi da kallo tana tunanin mafita.bayan fitar lateef Saida yay nisa da gida,ya kure volume din wakar da yake ji , kawai take motar police Tasha gabansa, take yay saurin taka burki ,ya juya ransa nace Yana kallan suwaye sukai masa wannan haukan,idansa ya sauka kan jami'an tsaro suna nufowa xuwa motarsa ,sukai saurin fitowa daga tasu motar suka nufi ta lateef Wanda ke musu kallan sun ma Raina masa hankali shine xasu wane tare masa mota meyay musu.suna xuwa basuyi wata wataba suka Bude site din da lateef yake suka Danko shi suka fito dashi daga motar, lateef ya coge yaki tafiya ya fara tambayarsu meyay musu,take daya daga cikin police din ya kwarfeshi ya kusan kaiwa qasa Wani ya dago shi suka tuso keyarsa suka kaishi cikin tasu motar ko takan tambayar da yake musu na Mai yay musu basubi ba sukaiwa motarsu key direct sai heardquater aka bar mutum biyu xasu taho da motar tasa,..



Abangaren Hajiya SA'A kuwa,bayan fitar lateef TV ta kunna kawai saita kamo labarai adai dai lokacin da ake sanarwa da cewa ankama Yan ta'adda,bayan nan Kuma saiga hoton Alhaji sunusi da babajo Ali,Yana yawo kan screen din TV,akan wai su suke sawa ake wannan ta'addancin, sannan Kuma shi Alhaji sunusi shiya sace 'yar Dan uwansa ASP Rukayya da Khalil, yanxu haka Yana heardquater atsare tun Daren jiya,ga hoton AA Arab agefe amatsayin jami'in wanda yay nasarar kama su,take Hajiya SA'A ta mike tsaye daga xaunan da take,jikinta y dauki rawa, take kanta ya fara juyawa,Hajiya SA'A ta rude,ta rasa Yama xatai , kawai ta fara girgixa kanta,tana surutai da qarfe,Hakan yasa Daya Daga cikin 'yan aikin ta fitowa dama a kitchen take tana yin abincin da Hajiya SA'A tasa ta tayiwa Alhaji sunusi .yar aikinta ta fito xata tambayeta Abu itama idanta ya sauka kan abinda ake fada a TV,take ta bar gun ganin Hajiya SA'A kamar xata zare..in ta sake ta ganta tasan saita karya ta....



Adai dai lokacin da Kuma ma'aikatan gidan suka afko dakin aguje,babu ixni Babu komai.Hajiya SA'A tai kansu cikin masifa tace "meya zaku shigo mun falor a haukace bakuda hankali ne, dayan ne yana haki yace "Hajiya, Hajiya," Hajiya SA'A ta qara qunduma musu zagi tace "meye Hakan,baxaku fadamin ba". suna haki suka ce wai ana jifan su ne daga waje suna bakin gate ga mutane sai muga gate din suke suna ihun wai saisun kona gidan,take Hajiya SA'A ta tari ido waje tareda dafe kirji tace suwaye,sai ta fita daga falon xuwa compound ai kafin ta qarasa compound ai saijin Dutse tai agoshin ta,take ta afko falon a mugun guje dafe da goshinta tana ihun atai Maka mata .adai dai lokacin da jiniyar 'yan jami'an tsaron ta karade unguwar......





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y



*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE____*



*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*



*____(Mrs sarakies)____=?1?*




*('TAURARI WRITES ASSOCIATION ('*



*Team for star (' writers*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season one ep 6?? 1??



___________?&



AA Arab Yana xuwa dakin da akai admitting Khalil,ya tarar da maman Khalil xaune bakin gadon da khalil ke kwance,babansa Kuma Yana kan kujera a xaune,ya shigo bakinsa dauke da sallama.suka ansa masa da kulawa.adai dai lokacin da Doc ma ya shigo ya da nufin sallamar Khalil ,babansa Yana tare dashi gefe Daya Kuma mahaifiyar sace, gabadaya sun cika da farincikin ganin Khalil ya ware kamar Wanda Bai taba ciwo ba sai dai rama kawai data bayyana,doc ya karaso kusa da Khalil,ya dudduba Khalil ganin Babu wata matsala yasa ya dubi Khalil da kyau yace "babu wata matsala ko?Ina nufin bakajin komai naciwo yanxu koh ?Khalil yay murmushi ya Kalli doc ya ce "babu Wani ciwo doc " .AA Arab shidai Yana gefe tsaye Yana kallan su, hannayensa harde a kirjinsa ,Baban Khalil ya dubi maman Khalil yace ladidi wanna fa shine Wanda na fada miki ya Samo Khalil, jami'in tsaro ne Ahmad, ai wlh sai daxu Khalil ke ban labarinsa ,Kuma bangane shi ba alokacin.dan lokacin Daya bar qasar nan be kai haka ba, Allah kenan dama haka abin yake komai yay farko xaiyi karshe sannu Ahmad kaji.wacce aka kira da ladidi ta ce Allah sarkie bawan Allah mungode fa , mungode sosai Allah ya Saka Maka da mafificin alkhairi ya kare ka aduk inda kake,yanda kasamu farinki, Allah kaima ya dauwamar da Kai cikin farin ciki,ya kare gabanka da bayanka, Allah ya Dora ka akan makiyanka,ko yanxu ai sunji kunya tunda gashi ka dawo kasar ka,sannu kaji sannu Allah ubangiji ya Kara baka hkr.shidai AA Arab ansa mata yake cikin girmamawa,Saida tai ta jero masa addu'o'i kamar me,sbd farin ciki sannan tau shiru, ganin doc na magana .AA Arab ya dubi Khalil yace " ya jikin? bakajin komai ?, Khalil Yana murmushi yace "banajin Komai yallabai, Babu abinda xamu ce da kai Saidai muce Allah ya Saka Maka da mafificin alkhairi ya kareka aduk inda kake,AA Arab ya jinjina masa kai "......



Khalil yace"yallabai Ina ASP Rukayya patan tana lpy itama ,AA Arab yace " lpy lau itama ta farka babu wata matsala,?Baban Khalil ya kasa hkr yace"ko itama tare aka kama Kun , Khalil ya jinjina masa kai Amma baice komai ba, Baban Khalil yace "Allah sarkie lallai ba qaramin jihadi kaiba yallabai Allah ya Saka Maka da Alkhairi, samun irinku arayuwa ba karamar nasara bace.AA Arab yace"em Babu komai baba ,ai aikin mune wannan Babu Wani damuwa nagode sosai da addu'a "ya kalli doc yace shikenan koh,?doc yace " eh yallabai shikenan,ya dubi Khalil yace Allah ya sawake sannan ya mika musu takardar sallama, shima Suka hau jero masa addu'o'i ya ansa musu sannan ya fita waje, A'A Arab yabi bayansa.Baban Khalil ya kalli Khalil ,xai taimaka masa ya sauka,ganin Yana kokarin saukowa, Khalil yay murmushi yace"baba ka bari naji sauki,maman Khalil tana kwashe kwanukan abincin da taxo musu dashi daxu tace malam ka rabu dashi ai mu Alhamdulillah tunda Allah ya bashi lpy xai iya tashi.baban Khalil yace "Allah kan shine abin godiya,ka sauko ahankali .Khalil ya sauko daga saman gadon ,maman Khalil tai gaba bayan ta kwashe komai da taxo dashi.Khalil da babansa suka bi bayanta.bayan sun fita suka samu AA Arab ya na tsaya bakin kofar dakin,suna magana da doc har lokacin.Yana ganinsu ya qarasa garesu sukai musabaha , sukai masa patan sauka lpy ya ansa musu ,sannan ya wuce inda driver yay parking ya shiga mota .direct office suka nufa tunda sunyi magana da Doc yace ita Rukayyan sai gobe da safe xa'a sallame ta...
Sun isa office ana kiraye Kirayen sallahn magrib,Dan haka Yana sauka direct masallacin Dake cikin heardquater suka nufa shida driver sa.......



__________?&



*Hayin rigasa*



Ameenah Zata iya cewa ta kusan wata daya bata Saka Kabiru a idonta taba,gashi abun Yana damunta, bawai damuwa na ta damu dashi ba. a'a kawai abinda ke damunta Ina Kabiru yake xuwa,ita dai tasan ba Neman kudi yake tafiya ba , bare tace Neman kudi ya tafi ,ba Dabba ya ajiye ba dazai tafiyar sa ya barta babu ci Babu Sha, bare Kuma yasan halin da take ciki,wato idan mutuwa xatai ta mutu shi baida asara.kai ko Dabba ya ajiye agidan aiya kamata ya dawo ya tadda halin da take ciki,gashi ita basanin Yana Sana'a tai ba ko yaya, ko Dan uwansa Bata taba gani ba,ballan tana iyayensa, Kabiru kawai ta sani.Allah ya Gani ta gaji da wannan xaman kuncin da take agidan Kabiru.wanda da wannan AURAN gara babu, sai tari saita xauna itakadai tayi ta tuna nin shin ko abban ta baya Santa ne yasa ya aura mata miji marar ASALI Wanda su kansu Basu San wanene Shiba, ga yay ta mata abinda yaga dama Amma babu Wanda zai goyi bayanta.wlh na gaji da wannan AURAN,dan wannan ba aure bane ba,Dan da wlh gara wanda bashi da auran,Dan wlh Bata da banbanci da Wanda baida AURE.....



Yanxu haka tana xaune a tsakar gidan ta wajen karfe biyar da mintuna na yamma,tayi nisa cikin tunanin da take,taji an dafa kafadar ta,ta juya a firgice tana kallan ta.maman saude ce,ta sauke ajiyar xuciya ganin itace,Sai Kuma ta hau gaidata ,maman saude ta ansa da lpy tana xama a gefen Ameenah,ta ce ", ke ko Ameenah lpy ki ke wannan uban ta gumi haka,?kamar Wanda aka miki mutuwa.Ameenah tai murmushi tana gyara xaman ta ,ta ce "lpy lau maman saude"maman saude ta dafo kafadar Ameenah ta kura mata ido cikin damuwa ta ce "Ameenah ko xaki boyewa Wani damuwar ki ,ni Bai kamata ki boye min ba,bansan me yasa kike da xurfin ciki haka ba Ameenah.yanxu a nan garin idan Baki fadamin damuwar kiba waxa ki fadawa,nifa Ameenah amatsayin kanwa ta na dauke ki, kanwar ma wacce muka fito ciki Daya,uwa daya uba daya,haba Ameenah meyasa kike so ki dinga barin damuwa tana Neman Yi miki illah kina qanqanu warki dake.ki fadamin damuwar ki ,idan na shawara ne saina Baki Amma bawai kullum kidinga sa kanki adamuwa ba, gashi yanxu kina qanqamuwarki Dake kin rame kin fita hayyacinki,haba Ameenah so kike ki kamu da Wani ciwon, kisaka ummanki awani Halin?"ta fada tana tsurawa Ameenah ido ganin yadda jikinta yay sanyi .....



Ameenah tai shiru Tana sauraran Babar saude, hawaye ya gama wanke mata fuskarta,ta sauke numfashi tana kallan maman saude ido cikin ido ta ce"maman saude Ina tunanin rayuwa ta ne? kuncin rayuwar da nake ciki yaushe xanji Dadi ne,? yaushe zan bar wannan qaddarar ran gidan nan,maman saude mahaifina ya kasa fahimtar halin da nake ciki haryanxu.kina dai kallo , Irin axabar da Kabiru yake min agidan nan ya tafi ya barni babu abinci yanxu badan keba ya xanyi ni ba waya ba bare na kira ummah nace ta aikomin da abinci, inbanda kwanan nan da ummah ta Aiko min da waya ,kema kinsani wlh da bansan Wani Hali xanshiga ba,maman saude saike wacce kike bani abinci safa Rana dare babu abinda xance Dake sai dai nace Allah ya Saka miki da Alkhairi.kina ganin Kabiru yasa kafarsa ya bar gidan nan sama da wata Daya Bai dawo ba, ko ban fada miki ba nasan kin Dade da lura da hakan.gashi ni bansan Neman kudi take tafiya yiba ko Kuma Sana'a yake koba Sana'a yake ba,bansani ba. gashi baba yaki barin na koma gida,wlh maman saude xuciya ta xafi takemin ji nake kamar xan mutu".ta karasa fada tana Mai rushewa da gunjin kuka, maman saude ta Dora kanta kan kafadarta ,tana rarrashinta tace " ya isa haka Ameenah kiyi hkr,ki kwantar da hankalinki in Sha Allah komai ya kusan xuwa qarshe.tabbas dole ki damu. Bama iya niba ko mu 'Yan unguwar nan bama ce ga Sana'ar da Kabiru yake ba, tabbas ko yanxu kinyi kokari, Ameenah shawarar da xan Baki shine ki dage da addu'a in Sha Allah komai zaixo miki da sauki,in Allahu da yarda Allah zai ansa miki addu'ar ki, babanki xai fahimci ceki, Ameenah Kuma suna sanki kowa da qaddarar arayuwa ke kila wannan ce taki,kiyi addu'a Allah ya Baki iKon cinyeta....



Ameenah tana sheshshekar kuka ta ce "wlh maman saude ai ko yanxu nayi hkr,Wani Irin hkr ne banyi ba.wlh guduwa xanyi nabar gidan nan,maman saude ,ta dago ta,ta dubeta tace, Ameenah yanxu idan kika gudu Ina xaki ? Ameenah tana goge hawayen fuskarta tace wlh gara na shiga duniya da dai na xauna bakin ciki ya kasheni ,ko Kuma na kamu da Wani ciwon tun Ina 'yar kan kanuwa ta .maman saude ta toshe mata Bakinta,tana girgixa mata kai tace " karkiyi haka Ameenah,kiyi hkr, Ameenah ta ce cikin Kuka,"Wani Irin hkr ne banyi ba".maman saude tace "ki qara akan na da," Ameenah ta girgixa kai,maman saude ta dinga rarrashinta tareda fada mata illolin da Hakan xai haifar, Dakyar Ameenah ta fahimceta,haka maman saude ta xauna da ita ta dinga Bata Baki, Saida ta tabbatar da ta fahimce ta sannan ta tafi gidan ta , tana Mai tausayin Ameenah.....



___________?&



Hajiya SA'A ,ihu kawai take tana leka windows din falon nasu ganin yadda ake ta jefo duwatsu har compound, kamar Wanda suka aikata Wani mugun Abu.duk sun far fasa glasses din motocin gidan,ga glasses din windows dinma sun fara fasasu da duwatsu,cikin kan kanin lokaci sukai daga Rava da glasses din cikin gidan,adai dai lokacin da police suka samu nasarar xuwa suka tadda su suna ta fafatawa da police din gidan Alhaji sunusi da Kuma security,Dan kowani Dan takara ana bashi polices , ko bama haka ba dama can gidan Alhaji sunusi akwai police da Kuma security.ganin suna kokarin fin karfin police din da security Dake gidan yasa suka fara korarsu, Amma matasan nan Kiran suke sai sun Kona gidan Alhaji sunusi,haka suka dinga kokawa da samarinnan Amma sunki tafiya.....



ganin sunki tafiya yasa suka fara harbe harbe, suna Harbin iska ,ganin haka yasa suka fara guduwa, saida police din nan suka tabbatar da sun korasu gabadaya sannan suka bar gun. suka bar police din gidan Alhaji sunusi da security da sauke numfashi, sunce musu Kuma idan suka qara dawowa suyi gaggauwar sanar dasu kamar yadda suka sanar dasu dazu.saida police din nan suka qaraso har cikin falon Hajiya SA'A sukace masu aikin gidan su fito sun tafi, Hajiya SA'A ta nufosu da kumburar goshi, tana haki tace "suwaye suka xo mana gida suke Neman kashe mu, police din ya fada mata duk yadda mutanan suka fada, Hajiya SA'A ta dafe kirji tace "innalillahi wainna ilaihi rajiun, Allah ya tsine musu albarka wlh sai Sunsan mu sukayiwa haka,bari Alhaji ya dawo.police din yace kiyi hkr Hajiya.hajiya SA'A Bata Kulashi ba ta dauki wayarta Dake kan center table din falon ta haura sama tana kokarin darling number lateef,Dan ta sanar masa halin da ake ciki Dan ta tabbatar ba lallai yaji ba .tana dafe da koshin ta Wanda ya kumbura yay suntum.....


__________?&



*____ZARI'A____*



Nana ta samu nasarar zana jarabawar jamb din ta.Kuma Alhamdulillah gashi harya fito ta samu points 250 dama Abu ZARI'A ta cike, Kuma bangaren medicine,yanxu Kuma sai xana WAEC da neko,xo kiga murna agunta itama ummah tayi farin ciki sosai,baba asabe da taji suna xancen a tsakar gidan tabe Baki tai tayi,tana habaice habaice,ita dai ummah Bata kula taba Dan yanxu ta mata uxuri ,Bata kula ta.....


Baba asabe liyafa taci gaba Dan ta dage Sana'a take sosai kullum idan xaliha ta fita saidai ta dawo mata da tulin kudi,Bata bincike Bata komai ita kawai Burinta akawo mata kudi.ga malam Auwalu ya kawo Ido ya xuba mata daga ita har zaliha,Dan dama yace ya daina fada mata gsky, duniya ma zata fada musu.bangaren zaliha da Alhaji tanko
Kuwa sai dai muce abubuwan yin gaba kawai suke itada Alhaji tanko Dan tun Bata san abinda yake mata hardai ta dawo tana amsar sakon,sai su kai Wani lokacin suna hira awaje a cikin motarsa da daddare idan yaxo. Amma baba asabe baxata taba tambayar ta Dan me take yin dare awaje ba ita kawai burinta, akawo mata tsire da lemo me gas ta kora da sauran kayan makulashe,bare Kuma idan ta tafi talla saiya bita Tasha yayi mata juyan abincin yace kowa ya karbi yadda ransa yakeso,idan ya kare tas ta fada masa ko na nawane ya kirge kudin ta ya Bata Wani lokacin ma har ya haura adadin kudin, itako zaliha Dadi takeji kamar me, Kuma idan ya kawo mata bukata ta yarda.......



Kamar ko yaushe yauma yaxo,gidan da daddare zaliha ta fito cikin Irin kwalliyar data Saba cabawa, tana xuwa ta shige cikin tsohuwar motarsa,Yana xaune ya saka uban ciki agaba kamar kwarya sai faman washe Baki yake,ya dubi zaliha yace"baby wlh kullum qara kyau kike miye sirrin ne?,ya fada Yana washe mata Baki, jajur dashi, zaliha tai fari da ido tace"Allah Alhaji nah."Alhaji tanko yace "sosai ma."ai idan na aureki na more sosai, zaliha ta qara fari da ido tace "na gode,"yay qasa da murya yace" yau me xan samu ne,? zaliha ta Bude ido tace " babu komai, Alhaji tanko ya qara matsowa yace, aikema kinsan bazan iya xuwa na koma ba'a barni nayi abinda ke samun nutsuwa ba, zaliha ta ce"yau dai saikai hkr baza ka samu ba, Alhaji tanko yay murmushi ya kamo hannun ta,ya fara shafawa,Irin dai yadda yasan akwana kinnan Yana riki tata,Aiko zaliha Bata kwace hannunta ba,da Abu yay Abu ganin ta fara karbar sakon,ya fara lalubeta, zaliha ta fara Jin Dadi tai lakwas can taji ya nufi Wani gun daban take ta dawo hayyacin ta, ta fara kokarin kwace jikinta.Amma Alhaji tanko ya dinga lallabata Yana mata ALKawarir rika har dai ta yadda yay abinda yake da ita .bayan ya ya Samu abinda yakeso.ya dauko kudi me yawa ya bata.....






07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y







*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)____=?1?*




*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season two ep 6?? 2??



__________?&



Washe gari da safe wajen karfe 9 na safe AA Arab ne tsaye a cikin Wani babban falor,sai ga wasu police biyu sun fito da Alhaji sunusi,acikin Wani Dan daki wanda hannayensa ke sanye cikin handcuff.suka sashi ya xauna a qasa,kan tiles din dakin, shidai AA Arab kallansa kawai yake,bayan Wani lokaci ya samu waje ya xauna kan wata kujera da aka ajiye masa.AA Arab ya sauke numfashi Yana kallan Alhaji sunusi yace " ba Wani Abu ne ya kawoni gunka ba ,illah na tambayeka Ina ku ke kai yaran mutane idan kun daukesu? Ya fada Yana kallan Alhaji sunusi Wanda ke kallan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login