Showing 267001 words to 270000 words out of 278032 words

Chapter 90 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1021

juya ta kalleshi ya k'araso cikin d'akin har gaban mirror inda ya tsaya daga bayanta yana kallan ta ya zuro da hannunsa ta k'ugunta ya zagayo dashi ta cikin, sannan ya D'ora kansa a kan shoulder d'in??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ta ya sauke numfashi yana busa mata a wuyanta yay k'asa da murya yace.


" wifey".


Ruky tai murmushi tana kallonsa ta cikin mirror itama Jin abinda yake mata acikinta kafin ta kai hannunta ta rik'e nasa tana cewa.

"Stop it Dee!muje na gama". ta fad'a tana k'ok'arin cire Hannun ta daga cikinta.


Ya hura mata iskar bakinsa a kunnenta kafin yace cikin Wani irin yanayi.


"Nooo!! Let me kiss u first before we leave".ya fad'a Yana juyo da ita facing d'insa,tai saurin kawar da kanta gefe tana tureshi da iya k'arfinta kafin tana B'ata Rai tai k'asa da murya tace .

"So kake kawai ka b'atamin kwalliya kamar yadda kake min Koda yaushe ba".ta fad'a tana tura masa bakinta gaba .

Ya K'ara matsowa kusa da ita Yana kallanta Yace cikin husky voice d'insa.

"Wait!Kinga lip gloss d'in da kika Saka yayi Miki yawa bari na rage miki". bai jira cewar taba ya had'e bakinsa da nata waje D'aya ya dinga kissing deeply,Nan fa itama ruky ta karb'e ta dinga maida masa da Martani Saida tafiya tai tafiyar ganin Yana k'ok'arin kaita kan gado ta dawo hankalinta ta k'wace bakinta daga nasa tana cewa.

"Stop it Dee! Unguwa fa zamu".ta fad'a tana kallan sa itama da idanuwan Wanda suka fara sauyawa saboda yanayin Data shiga,ya dafe kansa Yana mata Wani Irin kallo da lumsassun idanuwan sa Wanda suka fara sauya launi lokaci D'aya kafin ya juya ya shige toilet d'in d'akin ya sakar wa kansa ruwa bayan ya nutsu ya fito Yana goge kansa da towel kafin ya canza wasu kayan ita dai ruky kallansa kawai take bayan ya gama ya Tako har gaban ta ya Busa mata isakar bakinsa Ganin yadda take kallansa Bata ko kiftawa,Yay k'asa da murya yace .

"Wannan kallan fa? kodai kina sone a fasa tafiyar kawai mu koma kan gadon mucigaba". ya fad'a Yana k'ok'arin juwota jikinsa.ai Jin haka yasa ruky tai saurin mik'ewa tana Matsawa daga gefen sa da sauri tana cewa.

"Mu tafi Dan Allah ".

Yay murmushi yabi bayanta Ganin hatta nufi kofar fita,ya danna Wani D'an Abu take k'ofar ta rufe ruf kafin su sauka downstairs nanfa sun kakkashe kayan wutar gidan gabanta kafin su fito daga falon gabad'aya.yana rik'e da Hannunta suka k'arasa har bakin motar ya Bud'e mata front seat ta shiga kafin shima ya zaga driver seat ya Bud'e ya shiga yay motar Key suka fita daga gidan gabad'aya...


Suna zuwa gidansu baba lami nanma AA Arab Bai shiga ba yace da ruky ta shiga ta fara Yi masa iso tukunna .Babu musu ruky ta shiga cikin gidan har zuwa falon gidan.babu kowa a falon tai sallama shafa ce ta fito daga kitchen tana ansa mata sallamar ta ta ganin Ruky ce yasa ta taho da sauri zuwa cikin falon tana murmushi tace.

"Anty! Sannunku da zuwa Ina wuni".ta fad'a tana Mai farin cikin ganin Ruky.

Itama ruky murmushin tai mata kafin tace .

Lafiya lau shafa ya school".


shafa tace.

" lafiya lau Anty".

Ruky Tai murmushin tace "Allah ya taimaka"

Shafa tace.

"Ameen bari na kira baban tana d'aki daga haka ta wuce d'akin Dake nan gefen kitchen d'in.babu dad'ewa baba lami ta fito da fara'a tana cewa sannun ku da zuwa jami'a sannu sannu ki zauna mana ta fad'a tana K'arasawa cikin falon.ruky tai murmushi tace.


"Tare muke dashi bari Nai Masa magana ya shigo"baba lami tace.

"Ah!! to shikenan kishigo dashi mana" , ruky ta juya ta fita babu dad'ewa suka shiga da AA Arab tare da sallama.baba lami ta ansa tana murmushi har lokacin tana cewa sannu da zuwa yallab'ai sannu ku ta fad'a tana kasa b'oye farin cikita .AA Arab yay murmushi Yana zama kan kujerar Dake falon ya gaida Baba lami,itama baba lami ta hau gaishe shi lokaci D'aya shima Yana ansawa sannan ta gaida Ruky itama ta ansa tana murmushi da tambayarta gida da lafiyar Shafa baba lami tace.

"Ai yanzu kan komai yayi dai dai Alhamdulillah".ta fad'a tana murmushi.nan shafa ta shiga kawo musu ruwa da lemo ta ajiye a gabansu.sannan ta tsugunna har k'asa ta gaida AA Arab ya ansa Yana tambayar ta school tace.

" Alhamdulillah".

Suka D'an tab'a hira kusan mintuna 30 sukai agidan kafin su tafi ,baba lami ta rasa Mai zata bawa ruky kawai ta d'auko mata kayan miya irinsu kalwa da Kuka da bushashshiyar kub'ewa,da k'yar Ruky ta karb'a tai godiya baba lami tana cewa babu yawa haka Dai har sukakoma gida.



*ZARI'A*

Kwanan baba Asabe bakwai a asibiti kafin nan aka sallamota ,kuma wannan kwanakin da tai duk ummah ce ta zauna take kwana a gunta take Bata duk wata kulawa da take buk'ata ,kamar wanka,wankin kayanta idan ta b'ata,Bata abinci da sauran su, kai Babu abinda ummah Bata mata ba awannan kwanakin baba asabe tayi nadamar duk abubuwan Data aikatawa ummah harma da malam Auwalu,Dan har kunyar had'a Ido take da ummah saboda abubuwan Data aikata mata,ita ko ummah duk ta fahimce ta Amma ita Bata Nuna mata ba domin Dan Allah take komai bawai Dan halin baba asabe ban tana dai yiwa Baba asabe fatan shiriya , Allah yasa wannan abun Daya sameta ya zame mata izna.baba asabe dai tasa aranta zata neme yafiyar ummah harda malam Auwalu shima, tai ta kuka Dan babu abinda take iya yiwa kanta idan kukaga yadda baba asabe ta koma sai Kun tausaya mata.babu laifi shima malam Auwalu ya sauko daga fushin da yake da baba asabe ganin Irin halin da take ciki Dan abun tausayi ce agurin duk Wani Mai imani Dan abin a tausaya mata ne.Amma ba duka ya sauko ba shima dan dai ummah tayi ta rok'ar sane shiyasa ya sauko d'in,shi yake biyan Komai idan aka buk'ata na kud'i Wanda ake kashewa a asibitin,har aka sallame ta ganin jikin da D'an sauk'i babu laifi ,


Bayan sun koma ummah ta Tara su lawisa tai musu fad'a akan su daina hayaniya sannan su Hana 'ya'yan Suma hayaniya tunda dai sunga babarsu babu lafiya sannan likitoci ma sunce adai na Yin abinda zai ta-da mata da hankali har jininta ya K'ara hawa, sannan duk Wani aiki da sukasan na gidane na b'angaren su su dingayi basai sun jira baba asabe tai musu magana ba,abin Mamaki duk suka amince babu musu babu komai sukaiwa ummah godiya , ummah ta tafi b'angaren,babu laifi Kuma ummah taga sauyi bayan kwana biyu.


Ahaka har bikin Ameenah ya rage Saura sati D'aya aka kawo lefe daga Kaduna Dan iyayen barrister shamsu duk sun koma Kaduna da zama,ankawo lefe kamar lefen budurwa akwatuna shabiyu haka aka kawo da zasu tafi suma su ummah sukai musu abun arziki.har ranar biki tazo iya walima kawai akai washe gari akai d'aurin AURE aka kai Ameenah cikin garin Kaduna anan aka mata jeran kayanta ,gidan kowa da ban ita da kishiyarta Maryam wacce babu ruwanta Dan ta karb'e su hannu bibbiyu aka wuce da Ameenah gidan ta ,wai aljannar duniya inji Mardiya da lawisa Dan dasu aka zo gabad'aya Dan sunce baza a barsu a Baya ba sai sunga k'wak'waf ,aiko sunga k'wak'waf d'in Dan gidan Ameenah gilasaine ko Ina a gidan ,gida dai ya Had'u iya had'uwa Dan upstairs ne kamar yadda gidan kishiyarta yake maman saude tazo bikin da ita aka kawo Ameenah Dan zumunci suke da ummah sosai.,


Haka suka watse suka bar Ameenah ita kad'ai a gidan mijinta,su mardiya da bilkisu itama tazo bikin da Kuma suna baba asabe suka koma gida sukai ta yaba gidan Ameenah baba asabe Babu damar magana sai dai ido haka tai ta kuka tana nadamar duk abinda ta aikatawa ummah da 'ya'yanta, da bata aikata abinda ta aikata ba da tuni itama yanzu tana Cikin k'oshin lafiya 'yayanta ma suna gidajen Maza jensu ba'a Sako su ba Dan Yanzu ta tabbatar da cewa duk abinda ta aikata ne yake dawowa kanta da 'ya'yanta D'aya bayan D'aya ita gashi yadda k'arshen yazo mata babu kyau kaiconta haka ta dinga fad'aa kanta tana ta nadama da Kuka kamar ranta zai fita.haka suka kwana suna Yaba gidan Ameenah da cewa Ina ma sune ita, baba asabe Babu damar magana sai kuka,cikin dare Nak'uda ta tasowa zaliha ummah ce ita da lawisa suka kai ta asibiti, wajen ASuba ta haifi 'yarta mace ,da safe aka sallamesu ,suka koma gida da aka Mik'awa baba asabe 'yar kasa karb'a tai haka ta fashe da Kuka ,ummah tai ta Bata hak'uri , sannan tsu shiru Amma fa kwata kwata hankaiinta ya tashi sosai, ummah ce tai ta kula da zaliha,da sati ya zagayo ranar suna aka sawa 'ya suna suwaiba.



Malam Auwalu yakai k'arar Alhaji tanko kotu akan cewa shiyay wa 'yarsa ciki Dan dama jira yake Zaliha ta haihu ya d'auki mata ki akan abinda Alhaji tanko ya aikata mata Dan so yake baba asabe ta girbi abinda ta shuka shiyasa ya bari har zaliha ta haihu Kuma gashi ta haihun baba asabe taga abinda ta shuka d'in gashi kuma ta girba,aka kaiwa Alhaji tanko sammaci yazo kotu kuwa aka karanta masa abinda ya aikata yace ai bashi bane alk'ali yace aje ayi DNA test akaje akayi aka kawo Saka mako ya nuna positive cewar 'yarinya dai 'yar Alhaji tanko ce, alkyali ya yanke hukuncin zai dinga biyan kud'in shayarwa har zuwa sanda yarinya zata koma gunsa , Malam Auwalu yace idan aka yayeta ma za'a kawo masa 'yarsa , alkaline yace .

"To Alhaji tanko ai kaji?".Babu yadda ya iya Alhaji tanko ya karb'i 'yarsa ya Kuma amince da duk Wani sharad'i da aka ginda ya masa.haka aka gama zaman kotu aka watse.....

*Gidan Ameenah*


Bayan sunci abinci akaje kwanciya bacci barrister shamsu dai Bai d'agawa Ameenah kafa ba ,haka Nan dai akafara Abu Ameenah sai kuka da kakkarwa barrister shamsu Bai tab'a tunanin abinda yaji akan Ameenah ba, Dan da ahankali yajewa Ameenah d'aukar Ameenah tasan namiji Amma sai yaji sab'anin haka Dan shi ya fara sanin Ameenah dai, Jama'a Ameenah dai budurwa ce Dan zaman da sukai da Kabiru ko kad'an Bai tab'a yin kokarin kusan tar taba shi dama amatsayin kariya ya aureta bawai Dan Yana son Wani abu atare da ita ba.wanna shine albishir d'in da zan muku JAMI'AR TSARO fans Ina fatan ya faran ta muku Rai =??lol.haka nan ya k'ank'ame Ameenah ajikinsa bayan ya gama samun nutsuwa yadinga sa mata albarka kamar ya ari Baki itadai Ameenah sai kuka take tanajin Wani Irin zafi da Bata tab'a Jin irin Saba arayuwar ta.haka nan dai take daurewa saida sukai kwana hud'u kafin Ameenah ta daina jin zafin sosai haka suke soyayya kamar Babu gobe.



Bayan kwana biyu governor ya k'ira AA Arab har office d'insa ya bashi muk'amin Mai bawa governor shawara ta hanyar TSARO , agaban manya manyan gomnati masu muk'ami akai wannan taro aka k'addarar dashi,Dan Bai tab'a tunanin haka ba governor ya shammace shi a gaskiya baiyi niyyar karb'ar wannan muk'amin ba Dan ko kad'an bayaso aikinsa ya had'asa da siyasa,har aka gama Taron Nan baiga hankalinsa ya kwanta da wannan muk'amin da aka bashi ba Bai watsawa governor k'asa a ido ba yay Masa godiya sosai, governor yace Babu komai ai ya can can tane har dai suka rabu lafiya.daya dawo gida Saida ya bari da daddare lokacin kwanciyar su yayi ruky tana kwance a jikinsa shi kuma Yana wasa da gashin kanta ya fad'a ya fad'a mata K'iran da governor yay Masa .ruky tayi farin ciki sosai da hakan ya sauke numfashi yace .

"But fiancee! ni wallahi banason wannan muk'amin da governor ya bani Kinga fa kamar ya had'a da siyasa".

Ruky ta shiru kafin tace cikin nutsuwa.


"to kai me kake so ayi?".

Ya sauke numfashi Yana kallan ta kafin yace.

"Bazan iya cewa his Excellency bazan kar karb'a ba Amma dai zan Samu Abba na fad'a masa naji Mai zaice sannan saiya bani shawara koh?".ya fad'a Yana kallan ruky,ruky ta sauke numfashi kafin tace .

"Idan kai Hakan ma yayi, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi". Yace .
Ameen thumma Ameen fiancee!ruky tai murmushin ta Sara masa.


Ya K'ara jawota jikinsa yace .

"Ke ko",ta tura masa bakinta gaba ya had'e bakinsu wuri D'aya ya fara aika mata da hot kises tana Maida masa da Martani daga haka suka fad'a duniyar ma'aurata.


Gabad'aya ruky a 'yan Kwana kin nan Bata jin dad'in jikinta Dan jinya take atafe atafe Bata tab'a bari AA Arab ya sani ba bare har ya kura Amma Kuma Wani lokacin Yana lura idan ya tambayeta sai tace lafiyar ta lau.yau dai gabad'aya Abun yafi k'arfinta ta kasa jurewa. tana kwance har AA Arab ya gama shiri yana kallan ta yace .

"Fiance!". Tai shiru Bata ansa ba .
Ya Tako har gaban gadon kafin ya hawo kai ya kai hannunsa Yana Bud'e bargon data lullub'e harkanta dashi yana kallan yadda ta had'a uban zuba ga jikinta yadda zafi ya buso masa har fuskarsa Cikin tashin hankali ya shiga K'iran sunan ta ,ta Bud'e idonta tana kallan sa Wanda suka sauya launi.yay k'asa da murya cikin Kulawa yace .

"Fiancee! bakida lafiya ne?".ya fad'a Yana tab'a goshinta,
Ta gyad'a masa kai cikin damuwa yace .

"Amma Mai yasa Baki fad'a min ba". tai shiru tana rufe idanuwan ta.
yace." bari na shiga kitchen na had'o mike tea saiki Sha na kaiki hospitals koh?". ya fad'a Yana sauka daga kan gadon.

Ruky ta girgiza masa kai kafin tace.

"Na k'oshi".

Yace ."Noo dole sai kinci Wani abun" daga haka ya fice daga d'akin.babu dad'ewa ya dawo da kofin tea sai turiri yake ya aje kan table d'in Dake gaban gadon ya hawo gadon ta jawota zuwa jikinsa Yana cewa tashi Kisha sai mu tafi kinji?".

Ruky ta yamutsa fuska kafin tace .

"Na k'oshi"Bai saurareta ba ya kawo kofin bakinta ta kau da kai tana Jin bama tasan kamshin Madarar Dake cikin shayin.cikin damuwa yace.

"Please fiance Kisha ko ya yake saimu tafi asibitin koh?".ya fad'a Yana kaiwa kofin bakinta tai sipping sau biyu tuni amai yazo mata tai saurin matsawa daga jikinsa tai link mik'ewa Dan tafiya toilet Amma ta kasa tuni ta fara kwara Rashi akan tiles d'in d'akin Nan fa hankalin AA Arab ya K'ara tashi ya jawota zuwa jikinsa har Saida ta gama Sannan ya k'arasa da ita cikin toilet d'in ya wanko mata bakinta da jikinta suka fito ya kwantar da ita ya gyara inda tai aman sannan yazo ya Taya ta ta shirya ya kamota suka fito d'akin...

Hospital

Doc Yana murmushi yace .

"congratulations sir".

AA Arab ya Maida masa da Martanin murmushin da yay Masa kafin yace cikin Rashin fahimta.

"for what?".

Doc yace .

"Madam na d'auke da juna biyu harna tsawan 4 weeks".ya fad'a Yana murmushi.nanfa farin ciki ya bayyana a kan fuskar AA Arab cikin mamaki yace.

"doc! Are you keeding me?".ya fad'a cikin mamakin abinda Bai tab'a tsamamani ba kwana kusa.


Doc Yay Mir ya Jin Jina masa kai .

AA Arab Bai gamsuba yace.

" talk to me doc!are you serious?". ya fad'a Yana k'asa b'oye farin cikin Data shiga lokaci D'aya.

Doc Yana murmushi ya gyad'a masa kai kafin yace.


" yes sir am serious".

AA Arab ya zura hannunsa a aljihunsa ya ciro kud'i da Bai San adadinsu ba ya ajiye gaban doc Yana murmushi har San yace

"For u" goron albishir thank you very hugely doc". ya fada mata Wani Irin murmushin farin ciki.

Doc Yana kallan kud'in da mamakin yawansu yace.

"Duk nawane wannan yallab'ai?".ya fada Yana mamakin yawan kud'in.

AA Arab yay murmushi yace.

"U deserve it more doc! wannan ba komai bane akan abinda ka sanarmun".

Doc ya rufe bakinsa yace .

"Thank you very much sir! Allah ya Raba lafiya".
AA Arab yace .

"Ameen doc! yanzu aiba admitting d'inta kukai ba koh?".

Doc yace.

"Yes ba admitting d'inta mukaiba yanzu ma zaku iya tafiya dama magun gunane muka rubuta mata sai ku siya" .

AA Arab ya mik'e yace .

"Thank you doc".daga haka suka fito daga office d'in har zuwa Wani d'aki ruky tana kwance kan Wani gado inda ta kwanta take hutawa ita batama San meke faruwa ba Kawai ganin mutum tai ya rungumeta Yana ta kai mata sunba ta ko Ina ajikinta tare da Saka mata albarka.ita dai ruky duk tabi ta rud'e kafin ya sake ta Dan kansa Yana kallan ta da murmushi a fuskarsa Yana k'asa b'oye farin cikin sa ,ganin Irin kallon da take masa na Rahin fahimta yace .

"Congratulations mum on born".ya fad'a Yana kashe mata ido D'aya.

Ruky tai shiru tana tunanin kalmar kafin ta fahimci Mai yake nufi ta rufe fuskarta ruf da tafukan Hannunta alamar kunya ya K'ara rungumeta yace .

"Kina d'auke da cikin Ahmad Aliyu Arab, Allah yay miki albarka Allah ya sauke ki lafiya fiancee.
!"ya fada Yana rasa inda zausa kansa saboda farin ciki.itadai ruky mamaki kawai take dama cikine da ita yau itace ke d'auke da cikin AA Arab ya Allah haka ta Ambata aranta tana Jin Wani Irin farin ciki da soyayyar AA Arab na mamaye ko Ina na jikinta da Jin k'aunar abinda ke cikin nata kamar yadda take k'aunar uban cikin.haka Ya dinga sa mata albarka kafin ya kamota su fito daga d'akin ahankali dan tafiya gida ...


Tunda daga wannan ranar lauyayi Kuma ya sako ruky a gaba nanfa kullum tana cikin amai ta rame Sosai tayi wani Irin haske kamar me.dan sai yar aiki ma aka d'auko mata jikar baba hasiya Dake k'auye take mata wasu ayyu kan gidan ga AA Arab ya hana ruky d'aukar ko cokali agidan nan Dan wajen aiki kanma ya d'aukar mata excuse Bata zuwa saidai taci ta Sha ta kwanta haka Nan dai suke rainan cikin su cikin so da k'aunar junansu,har mamaki AA Arab yake Bata yadda yake nunawa cikin nan so k'auna tun kafin ma yazo duniya,badan fita aikinsa ya zama dole ba da Babu inda zaije Dan da kullum suna tare da ita, Danda dashi za'ayi rainon cikin nan,yanzu ma ko Yana office ya dinga K'iran ta kenan Yana tambayar ta lafiyar ta da abinda ke cikin nata ,ita dai saidai tai murmushi tace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login