Showing 39001 words to 42000 words out of 278032 words

Chapter 14 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1023

yay tsaki yace Kuma shine xakimin wannan Kiran haukan, banason Irin haka,ta marai raice tace to sorry Beb,dama nace na gama ta fada tana qoqarin hade lips dinsu ya ture Hannun da fuskar ta, ya shige toilet ta bishi da kallo tana qara Jin sha'awarsa,,. Amma
Bata isa tace a qara ba matukar bashine ya bukaci Hakan ba....


Bai Dade da shiga toilet dinba ya fito shaf shaf ya shirya Dan so yake yaje ya fadawa Dady cewa Ruky fa tayi blocking dinsa shikawai a daura aurannan this week,bayan ya gama shiryawa yace da aneee ta fito ya sauke ta, haka ta bishi tana Mai wata kwar kwasa suka fita daga gidan ,Mai gadi ya rufe gate din bayan sunbar gidan Yana Mai girgixa kai da musu addu'ar shiriya,bayan lateef ya sauke aneee a inda ya daukota ya Bata kudin sallama Dami guda,itako ta karba tana Mai Jin Dadi aranta,ya daga mata hannu yace u can leave,ta dubishi tace Beb govema xaka dawo ya hade Rai yace bana Mai maici ,tace bangane yace kamar kayan sawatane idan nasa bana maimai tawa ,to haka nake yiwa mace ma, xatai magana cikin tsawa yace shut up, get out ,cikin mutuwar Jiki aneee ta fita,haka ya figi motarsa ya kama hanyar gidansu,...


Alhaji sunusi Yana xaune shida Hajiya SA'A, lateef ya shigo cikin falon babu ko sallama,ya nemi wuri ya xauna kusa da dadyn nasa, Alhaji sunusi ya dubeshi bayan ya aje cup din lemon daya
Kai bakinsa,yace son,meya faru naga ka shigo kamar ranka a bace,lateef Dake Wani hade Rai yace dad ruky ce mana, Alhaji sunusi ya hade Rai yace ruky Kuma to metai maka,bayan mungama magana ,nace ka kwantar da hankalinka , yarinyar nan ba garara xatai a aura maka itaba,ba komai ba to me Kuma ya faru, lateef ya nuna kansa yace dad wai harni yarinyar nan tayi blocking, Kona kirata Bata shiga, Alhaji sunusi yay tsaki yace to meye abin Kuma Damuwa Dan tayi blocking dinka saime, kaidama xa'a kawo Maka ita har gida matsayin mallakinka sai abinda Gaga dama kaso kai da ita, lateef yace but dad nan da 2 weeks aidayawa, ni so nake na dinga Jin muryar ta kafin a kawota gidan nawa, Alhaji sunusi ya kwantar da murya yace kai dadina da kai gaggawa kabi komai a sannu ai Basu isa su Hanani aura maka ita ba,idan lokaci yayi ba ko, to ai tayi ta Banxa,Kuma may be iya sim dinka Daya tai blocking ka kirata da Daya mana, shaf lateef ya manta sbd gabadaya ya rude Rashin Jin muryar ruky shiyasa ma baiyi tunanin Kiran nata ta daya sim din nasa ba,cikin sauri yace wlh dad shaf na Manta na rude bari na nai Hakan, na shiga damuwa ne shiyasa,Amma bari na fita yanxu na kirata, Alhaji sunusi yace to kaga shikenan jeka,karfa kasa wata damuwa aranka, lateef yace yes Dad, Hajiya SA'A dai tana gefe tana kallan iKon Allah awurin uba da da,Saida laleef xai fita yace Hy mum, Hajiya SA'A ta kalleshi tace na'am son,idan ka ya rufe koma lura dani bakaiva,.....


Lateef y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a shafa kansa yace wlh mum ruky ce ta rudani, Hajiya SA'A ta tabe Baki batai magana Dan inta fadi Wani Abu marar Dadi sai Alhaji sunusi yanxu ya hayyako mata, lateef ya fita daga falon Yana bouncing, Alhaji sunusi ya bishi da murmushi,bayan fitar lateef Alhaji sunusi ya dubi Hajiya SA'A har sannan murmushi ne shimfide a fuskarsa yace wlh hajiya Ina matukar kaunar lateef bana so ko kadan ransa ya Baci,akan Wani Abu Wanda Bai kai ya kawo ba, Kinga wannan AURAN idan Kinga ba'a yishiba to Wani ne ya mutu acikinsu, Hajiya SA'A ta sauke numfashi tace nikan wlh Alhaji da zakuji ta tawa da hkr kukai da wannan yarinyar a aura masa wata wlh dayafi ga mata nan kala kala a gari idanma basuyi masa ba Ina da yayan kawayena da suke Sansa wlh da can ma yaje ya zabi Daya,...


Alhaji sunusi da tunda Hajiya SA'A ta fara magana yake mata Wani kallo ,ya hade Rai yace to shi lateef babu wacce yakeso sai Rukayya sbd haka babu ruwanki acikin maganar nan idan har baxaki goya mana baya ba toki ja bakin ki kiyi shiru tunda naga ke duk Wani farin cikin lateef ba sanshi kike agidannan ba, Hajiya SA'A ganin ya fusata yasatace Allah ya huci xuciyarka Alhaji niba haka nake nufi ba, Alhaji sunusi yay tsaki ya cigava da Shan lemonsa,......




07066508376________
'?
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*


*NA*


*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*


*_____(MRS SARAKIES)____*


*QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA) =?1?*


*Bismillahirrahmanirrahim*


____season one ep 1?? 8??


_______?&

ASP anas har hayin rigasa division ya kaisu,bayan yay Parking ya fito da sauri ya budewa DCP muktar kofa cikin girmamawa bayan ya Sara masa, DCP ya fito haka ma ruky ta fito,haka suka nufi cikin division din duk inda suka gitta Sarawa DCP kawai ake ana musu barka da xuwa,ya tambayi DPO din wurin yana nan babu musu sukace yes sir Yana ciki,haka wasu daga cikin police din suka take masa baya har office din DPO Dake cikin division din,bayan sunkai su har bakin office din suka juya kowa ya koma bakin aikinsa, ASP anas yay knocking office din, DPO Dake rubuce rubuce cikin wasu ta kaddu ya Bada ixnin shigowa,babu Bata lokaci ASP anas ya bawa DCP hanya , shikuma saiya shiga yace Ruky ta biyo bayansa,haka ruky ta mara masa baya ASP anas Kuma ya tsaya a wajen Yana xagaye wurin,.....


Bayan sun shiga sun tadda DPO Bashir daya dago daga rubuce rubucen dayake Yana jiran shigowar me knocking din ,ganin DCP da kansa yasa shi saurin mikewa tareda qamewa a inda yake alamar girmamawa tareda Sara masa at the same time ,bayan DCP ya ansa yay Maza ya fito ya karaso wajensa ya Mika masa hannu sukai musabaha,haka suka gaisa cikin girmamawa sannan ya Basu wurin xama DCP ne kadai ya xauna,ruky kan Saida ta tabbatar sun gama gaisawa sannan ta juya ga DPO Bashir Dake tsaye har sannan ta gaida shi ya ansa yana murmushi,duk itama watanni ne ya rage mata ta iya kaiwa matsayin DPO,itama ta xauna nesa da DCP sannan DPO Bashir ya wuce fridge din office din ya kawo musu ruwa da lemo ya aje gabansu ya koma wurin xamansa ya xauna,ya kasa nutsuwa ganin DCP da kansa har office dinsa,da tunani fal ransa ,Kuma xuwa unexpected haka,duk da duk cikin aiki ne wannan ba komai bane Amma Kuma xuwan nasa yay mamaki kwarai da GSK,.


Bayan DPO ya xauna DCP muktar duk Yana lura da Irin rikicewar da yay amma ya basar yace DPO ya aiki , DPO Bashir yay murmushi yace Aiki alhamdulillah ranka ya Dade ,DCP yace Masha Allah, sai Kuma ya koma serious yace DPO kayi mamakin ganinmu koh a division dinka ,DPO cikin dauriya yace kwarai kuwa ranka ya Dade ,DCP yace aikine ya kawomu,wannan division din,DPO yace toh toh ranka ya Dade,DCP ,yace kwanaki can da dadewa xan iya cewa ZA'Ayi shekara Daya koma da watanni kadan ,wata mata ta kawo Wani case na fyade da akayiwa 'yarta, ta kawo qara ,har Kun karba kunfara bin case din saikuma daga baya ban San meya faruba ,aka banxantar da case din shin zaka iya tunowa,DPO yay jimm alamar tunani, DCP yace ok sorry ban tambayeka yaushe ka fara aiki a division din nan ba,DOP yace xanyi watanni goma Sha Daya,DCP yace ok bakanan lokacin, da akai case din kenan ,DPO Bashir ya jinjina kai,....


DCP muktar yace ok bani list dinku na DPO Wanda shine last na barin wannan division din, DPO Bashir cikin gaggawa ya dauko ya mikawa DCP ,DCP Yana karba ya duba cikin seconds ya dago yace sani bulama shine last Wanda ya tafi kai Kuma ka karba, DPO Bashir yace yes sir, DCP yace ai yayi retired gashi a rubuce, DPO Bashir yace yes sir,DCP muktar yace aje abincikomin file din shafa'atu sidi ,babu Bata lokaci DPO ya mike cikin girmamawa ya fita,yaje inda suke rubuta ko Wani case da aka kawo duk min kankantarsa sai an rubuta,yasa yaransa suka duba sunan shafa'atu sidi,Saida suka Dade kafin su Gani,gashi Kuma komai Yana nan da date ta month harma da year da time duk gashi a rubuce, DPO yace aje a duba file din ta,babu dadewa suka shiga Inda suke aje duk Wani report nasu,svd komai nasu a tsare yake,,....


DPO ya dauko daga soft coffy din har original ya kawowa DCP, DCP ya karva yaduba ,bayan ya duba yace a Maida original din,ga sunan shafa nan Dana babarta da police din da aka Dan Kawa case din da komai, DCP ya Kalli DPO yace Ina cofur saleh da sajen lurwanu,suna division din nan,DPO Bashir yace sir Kofur saleh ya rasu kusan wata bakwai kenan shi Kuma sajen lurwanu Yana kan kanta, DCP ya jinjina kai yace Allah ya masa Rahma,suka ansa da Ameen yace Akira min sajen lurwanu,babu dadewa DPO ya fita ya kirashi,sajen lurwanu ya shigo jikinsa na kyarma Jin DCP da kansa na kiransa ,kardai ace laifi yay, shiko meya aikata haka,...


Suna shigowa DPO cikin girmamawa yace sir ga sajen lurwanu, DCP ya jinjina kai DPO yaje ya xauna,sajen lurwanu ya sake Sarawa DCP a karo na biyu , DCP ya ansa masa Yana Mai kallansa da kyau , ganin be xauna ba yasa DCP umartarsa Daya xauna ,cikin girmamawa ya ansa masa Yana xama kan Wani dan kushin, DCP yace sajen lurwanu xaka iya tuna wanna case din ya fada yana Mika masa soft coffy na case din shafa ,sajen lurwanu ya karva Jiki na rawa ,ya Bude ,ya fara karantawa xufa na keto masa ya fara sharewa , hannunsa da jikinsa sai rawa suke domin ya tuno wannan case shida Marigari cofur saleh,su suka tsaya a case din domin xuwan da babar shafa tai ,su kadai ta samu a akan kanta din Amma shi harga Allah Yama manta wlh da wannan case din ,ya dago Jin DCP yay magana,yace cikin inda inda eh eh ranka ya Dade na tuno,....


DCP yay murmushi yace katuno kenan tunda har ka tuna fine,meya faru kuka bar case din,bakubi diddigin case din ba, meyasa ma Baku bawa DPO case din ba, kodan kowani DPO saiyabi statement book din da ake rubuta ko wani case Koda ko baya nan,idan ya dawo ko kwana nawa yay dole saiya duba yaga cases din da suka faru wannan dokar aikice,to bansan meyasa ba ko shima DPO ya Gani Amma Bai dauki matakiba,case din ya tsaya iya hannunku kaida Marigari cofur saleh,sajen lurwanu yace wlh sir a lokacin munyi iya bakin kokarinmu Amma abin Yaci tura bamu Gano ko wayeba, DCP yace naji Baku San ko wayeba Amma ba haka yaka Mata kuyi ba,baka bani ansa ba,sajen lurwanu yace eh lokacin DPO bayanan ,Kuma Daya dawo bansaniba koya duba Kobe duba ba, DCP ya sauke numfashi yace,naji idan ma Bai duba ba meyasa daya dawo baku taka har office dinsa Kun bashiba ,kuga xaiyi Wani acting ko baxai ba,idan Bai karba ba shikenan,Kuma saiku kyale ,Amma kunsan baxa ku iyaba Kuka barshi a tsakanin ku, Kuma abin ta kaicin ma kuka wulakanta matar, Kuma kuka wulakantar da case din sbd ba yayanku akayiwa ba shiyasa Baku dauki case din da muhimmanci ba,bayan kunsan hukuncin duk Wanda ya aikata rape a kasarnan,,....

Sajen lurwanu ganin DCP babu Wasa a labarinsa yasa yace Dan Allah ranka ya Dade kayi hkr wlh duk bankawo wannan tunanin ba, DCP cikin hasala yace rufemin Baki ,gashi Abu har a gidan TV matar nan ta kai kukunta, Sannan Kun Bata mana suna matsayinmu na jami'an tsaro,ana mana kallan mungaxa ana mana kudin goro gabadaya alhalin wasune ke Bata sunan wasu yasa idan antashi ba'a banbancewa ake mana kudin goro, DCP ya dinga fada kamar ya Ari Baki,ita dai ruky duk abinda yake faruwa tana ji Kuma tana kallo,tana fatan yadda DCP ya dauki case dinnan da muhimmanci Allah yasa yacigaba da daukarsa da muhimmanci har su gano wannan axxalumin mutumin yadda xa'a hukuntashi,dai dai da yadda Shari'a ta tanadar, DPO ma Yana kallo Yana godewa Allah da ba'a lomacinsa bane abin ya faru,da shima yasan wlh sai kashinsa ya bushe,....


DCP yace dole sai an hukun taka, na ballagaxar da case din rape dakai ,wlh da ace hukuma ta qasa xata ji abinda ka aikata wlh da sai aikinma ka rasa shi,ya Kalli DPO yace akaishi , iyaka Kaduna da Abuja cikin wannan dajin dake can ciki inda Yan ta addar nan da suke takura wa al'umma da dauki dai dai Suna sace mutane shima ya Dandana fafatawa dasu,sajen lurwanu ba damar magana kansa a Kasa gabadaya ji yay kansa ya kunce yanxu wannan dajin xa'a kaishi, inda gabadaya kullum sai ansace mutane indai Sukabi ta hanyar yauma Saida aka sace mutane Kuma jami'an suma Saida aka kashe sbd xasu bawa mutanen da xa'a dauki ke din kariya,su hana Yan ta'addar daukarsu gashi Kuma gomnati har yau tana iya Bakin kokarin ta,Amma abin yaci tura ,dan suna tuninma kila akwai sa hannun wasu daga cikin manyan kasar nan ko Kuma jihar nan,yace innalillahi wainna ilaihi rajiun nashiga uku tunaninsa ya katsene lokacin da DCP yace I hope u getted,cikin girmamawa sajen lurwanu yace yes sir thank u, DCP ya Kalli Ruky yace let's go,sannan ya mike,itama ruky mikewa tai, DPO ganin tafiya xasuyi ya mike ya Sarawa DCP yace tnk u sir DCP yace u are welcome ,yace sir ko ruwa baku shafa ba,DCP yace don't worry ,we are full ,sannan suka fara shirin tafiya DPO ya Rakasu har bakin motar su ,duka police din wurin suka qaraso suka Mai a sauka lpy cikin girmamawa ya ansa musu da kalawa, DPO ne ya budewa DCP motar ya shiga itama ruky Wani sajen ne ya Bude mata ta shiga,ASP anas ya ta-da motar suka bar division din, direct office suka nufa,...


________?&

DCP ne xaune a office din CP,Bayan ya karanta Wani Sako da IG na qasa ya turo a state din guda biyu katsina da Kaduna,Wanda ya shafi Yan ta addar da suka takura wa State din wajen barnar da ake da salwantar da rayukan mutane wasu Kuma ayi garkuwa dasu wasu Kuma ai safarar su musanman ma mata, harma dasu kansu jami'an tsaron Basu tsira ba, kashe su suke Yi,gashi al'umma sai cecekuce ake a social media ana aibanta shuwaga banin,da jami'an tsaron suna ganin kamar sun kasa ne,....


DCP ya aje ipad din bayan ya karanta sakon ya gyara xama yace ranka ya Dade yanxu abin harya kai sai ankawo mana wasu jami'an daga wata qasa sunxo, su xasu mana maganin abin, CP yace gashi dai a rubuce Dan ance mu shirya tar barsu nan da ending month dinnan,zasu sauka a qasar , Kuma kasan harda makaman ya kinsu xa'a zasu xo mana dasu kasar , DCP yace meyasa ,CP yace suna ganin namu basuda qualities din da xasuyi aiki dasu, DCP yace turkashi lallai kasarnan,Amma Kuma ta Wani fannin nayi farin ciki da haka,sbd zasu mana maganinsu kasan suda kwarewa indai akan aiki ne yanxu xaka ga sun mana maganinYan ta addar nan gabadaya, sbd sun Raina jami'an mu na wannan kasar ,....

Gashi Kuma abin kullum qara ta axxara yake,CP yace hmmm,ni wlh nafi tunanin akwai masu daure musu qugu suke duk abinda suka ga dama,Amma ace har Sufimu makamai suna kashe mana jami'ai idan ba suna da daurin qugu ba, ayina suke samun makamai Irin Namu harma da Wanda sukafi namu,ai wlh jami'an mu da ake tura musu yaci ace muma muna samun nasara,Amma kwata kwata su suke kashemu, DCP ya jinjina kai yace lallai na yarda da zancenka tabbas akwai masu goya musu baya domin Nima Saida nai tunanin haka,...

CP yace hmmm,ai xamu Gani bari dai su qaraso, DCP yace but kamar mutum biyu na gani Ina nufin Kaduna mutum daya katsina ma haka, CP yace eh, DCP yace Amma mutum daya ai yay kadan ace shikadai xaiyi Maganin wasu yan ta'adda , CP yay murmushi yace ,hmm nima dai haka na gani Amma idan muka kula xakaga mu dasu ba Daya bane, Horan da suka samu mu bamu samu Irin Saba, zasuyi training namu ne akan yadda xamu bullowa Yan ta'addar ,Kuma su sun San sirrin kama duk Wani Mai laifi ,ko kuma su hada masa tarko batareda ,su sun San suna hada musu ba, kai fa turawannan sun riga da sun mana taxara nesa ba kusa ba,.....

DCP yace Amma shi IG meya manufarsa nayin Hakan, CP yace shi IG xalincin da Yan ta addar nan sukene ya isheshi shiyasa ya samu prisedent da maganar shikuma prisedent dayaje turkey yasamu president dinsu suka tattauna harya amince masa,ya vashi biyu daga cikin jami'an tsaron da suke ji dasu a qasar suka bashi, wlh wannan IG da GSK yake aiki xaiyi tukuru , kaga fa har president ya kaiwa maganar Kuma ya amince,DCP yace gsky ne, Allah dai yasa akawo qarshen mutanan,CP yace Ameen haka suka cigava da tattaunawa,....



_______?&

Ruky ce xaune a dakin ta Bayan ta gama shirin kwanciya,ta dauki wayarta ta kira Hanan Dan labarta Mata yadda sukai da DCP, har Inda sukaje yau,bayan Hanan tai picking ruky ta zayyane Mata komai ,bayan Hanan ta gama sauraran ta tace hmmm bana fada miki ba ,in Sha Allah DCP xaiyi iya bakin kokarinsa xai taimaka miki matuka,kedai abinda nakeso Dake shine Dan Allah ki daina wannan gidadancin da kike masa ,ruky ta hade Rai kamar Hanan ce agaban ta tace bangane ba, Hanan ta tashi xaune daga kwancen da take tace Ina nufin Dan Allah,kidinga Dan bashi time dinki indai ya bukata ,Ina nufin idan yace zai kiraki kuyi waya ko Kuma yace xaixo xance karki hanashi Dan Allah,Kinga Ruky wlh DCP kaunar ki yake kamar me,idan yaga kina bashi kula warnan wlh saiyafi Bada himma wurin qara tsananta buncikinsa,svd Yana samun kulawarki,.....


Ruky ta Bata Rai tace Kinga Hanan ,ni ba agreement mukai dashi ba,na saina Kulashi sannan xai bi case din ,Kuma ni kinganni nan bantaba Jin wai inasan DCP ba, shikadai kawai yake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login