Showing 84001 words to 87000 words out of 278032 words

Chapter 29 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1102

kika dauko kina gidana ZA'A karasa ta, ruky tai tsaki tace kai ka Isa na aureka lateef me xanyi da fasiki irinka, Kuma da kake cewa zakamin abinda zakamin,wlh baka isa kamin abinda Allah Bai rubuta zai faru Dani ba,daga haka tai masa kallan sama da qasa tareda da jan tsaki ta shige motar ta, Alhaji sunusi ya kamo hannun lateef ganin yadda ya xaburo kamar xai Danko Rukayya,yace rabu da ita,da kanta Saita jenye wannan qarar ko taki ko taso,daga haka ya kamo hannun lateef sukai hanyar gun mot??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????arsu, Wanda driver ke jiransu,Suma suka shiga driver yaja kowa da tunanin dayake fal ransa,......






07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD





*___JAMI'AR TSARO___*




*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*




*____(MRS SARAKIES)____*



*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA) =?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season one ep 3?? 6??



_________?&


Hajiya SA'A tayi mamaki matuka da taji labarin cewa Rukayya ita tai Karar su lateef har aka kawo musu sammaci, Bata taba tunanin xatai haka ba,ko a mafarki, Amma Kuma tasan halin danta saidai ta bawa Wani lvrin halinsa, dole Kuma akwai wata a qasa,bayan ta gama sauraran Alhaji sunusi,ta dubi lateef,cikin bacin Rai tace lateef ya juyo ya kalleta,tace inaso ka fadamin gsky shin da GSK Kaine kaiwa yarinyar fyade koba kaibane, Dan musan yadda xa'a bullowa lamarin, lateef ya Bata Rai yace haba mummy yanxu Dan Allah tayaya xan iya hada jikina da wannan kaxamar yarinyar yar talakawa,wlh ni banma Santa ba,ya fada yana ciccin magani....



Alhaji sunusi dayake yiwa Hajiya SA'A Wani kallo yace oh kema kinyarda kenan cewar lateef shi yay laifin kenan, Hajiya SA'A tai saurin cewa a'a Alhaji ba haka nake nufi ba, Amma kasan cewa lateef babu kalar ShaShan cin da bayayi,aidole na tambayeshi ya fadamin gsky, idan har yasan ya aikata ya fadamana karkaje kasha wahala gara idan yasan ya aikata ya fada sai abin yafi xuwa muku da sauki Dan akashe maganar batareda tayi nisa ba,, Alhaji sunusi yace Tayaya lateef zai iya hada jiki da yarinyar wai kin ganta ma kuwa wata yar mitsitsiya da ita, to mema zai samu ajikinta,da har zai mata fyade,inba sharri ba.....



Hajiya SA'A tace Alhaji ba haka nake nufi ba Ina nufin me xai hana mu zaunar da lateef Mu tursasashi ya fada mana gsky haka kawai kasan baxasu taba masa sharri ba, ruwa Baya tsami Banxa, Basu Sanshiba Basu taba ganinsa ba,haka kawai bazasu masa sharri ba gara idanma ya aikata ayiwa tufkar hanci tun wuri tunda kaga dai zabene yake xuwa, Alhaji sunusi yay caraf yace oh Ashe ma kinsan zabe ne ke xuwa,kinsan xa'a iya anfani da yarinyar Dan a Bata min siyasa ta , Kuma a min sharri,na fada miki kawai magauta ne sukeso suga sun batamin Siyasa ta, so kawai ake a cimin mutunci sbd anga zabe ya gabato,asa mutane karsu zaveni, kila ma abokanan hamayya tane kawai suka hada baki dasu akeso aga an kaini qasa, ke bakisan halin mutane bane kawai,ke Kalli mutum ke kyaleshi kawai,ko rantsuwa nai baxan Yi kaffaraba wadannan mutanan turosu akayi , itama Rukayya kudi suka Bata shiyasa ta shiga case din Tai dumu dumu aciki,.....


Hajiya SA'A ta dubi lateef tace lateef kafadamana gsky ka aikata ko baka aikata ba, lateef ya qara tsuke fuska yace haba mummy kema zarginnawa xakiyi,wai Dan Allah Taya Zanyiwa wannan yar mitsitsiyar yarinyar nan fyade, Alhaji sunusi yace SA'A ya isheki SA'A,wai ya ZA'Ayi ki tilastawa yaro abinda yasan Bai aikataba , kinga idan har baxa ki xuba ido kiyi shiru ba, to babu ruwanki cikin wannan case din,ni xanyi handling kayana,tunda bake akai qara ba nida lateef akayiwa,to kiyi shiru ki xuba mana ido kawai, Hajiya SA'A ta sauke numfashi tace aishikenan Alhaji tunda dai gsky ce kai bakaso afadawa lateef, Alhaji sunusi yace eh kiyi shiru ki rike gskyrki,daga haka ya haura sama lateef Shima ya fice daga falon,akabar Hajiya SA'A da tagumi,ta furta kasa kasa ko bakanan dole saina zaunar da lateef na tambayeshi, haka kawai ku bakwasan gsky.....



Bayan kwana biyu lauyan lateef yaxo ganawa,da lateef inda suka samu Wani ke bantaccen waje acikin gidan,su biyune zaune akan kujerun,na Shan iska, barrister Salman ne ke xaune cikin shigar kananan kaya,sai lateef Dake sanye da 3quater da shirt fara qal,ga sumar kansa Tasha aski Irin balatolin nan, barrister Salman ya dubi lateef Wanda ke kallansa babu yabo babu fallasa,ya Danyi murmushi yace malam lateef inaso ka fadamin gskyr magana shin mutanen nan da sukai Karar ku,da GSK ka aikata ko baka aikata abinda ake zargin ka dashiba, lateef yay Masa Wani kallo,...


Sai Kuma ya kauda kansa gefe, barrister Salman yace cikin kwantar da murya,lateef karkaji komai ,I am ur barrister karkaji shakkar fadamin duk Wani Abu Daka sani akan wannan maganar,kasan ni ba'a kadani a Sharia' idan baka saniba to mahaifinka ya sani, tunda ni nake masa aiki,sbd haka idan ka aikata ka fada min babu Wanda zan fadawa Koda ko mahaifin Kane, indai har bakaso ya sani baxai taba saniba,idan ma baka aikata ba,ka fadamin idan monkoma zaman kuto mu taje kotu da hujjoji masu karfi ,kotu ta wanke sannan su su biya tarar sharrin da suka Maka,ya qarasa fada yana kallan lateef Wanda ya xuba masa ido,jin abinda ya fada.....



Lateef ya furxar da huci Mai xafi daga bakinsa,Yana kallan barrister Salman har lokacin,cikin budaddiyar muryarsa yace idan na fada Maka gsky xaka wankeni daga zargin da akemin, barrister Salman yay murmushi tareda da jinjina kai yace Koda ko kai ka aikata ne, lateef yace xan fada Maka gsky ne bawai Dan kasa a kawo karshen case din bane, zan fada Maka gsky ne Dan kawai Rukayya Dan kawai na wanke kaina a idan Rukayya ta kuma yarda Dani cewa ni ban yiwa yarinyar fyade ba, sannan tasan cewa ni mutumin kirki ne Dan ta yarda Dani ta aureni, barrister Salman ido kawai ya xubawa lateef, Yana San Jin ya fada masa me yake ransa,.....



Lateef ya Kalli gefe daban yace tambas nasan yarinyar, barrister Salman ya zaro ido waje yace kasan ta, lateef yace kwarai kuwa bantaba dauka tana nan ba haryanxu,Dan wlh nama manta da ita, nai mamaki ma da harta iya ganeni,Kuma abinda yasa na tuna ta sbd yarinyar ta tsayamin arai tun bayan abinda ya faru, sbd itace yarinya mafi kankanta wacce na taba NEMA ta qarfin tsiya,ya bawa barrister Salman lvr tun daga farkon haduwarsu da shafa har xuwa rabuwarsu ,ya qarasa fada da cewa Kuma bawai danna aikata mata haka bane yasa ta tsaya min arai ba, kawai Dan na danji dadin mu'amala da itane a wannan lokacin kawai, abinda yasa na dage cewa banmasantaba, bantaba Ganin ta ba,sbd police din ne naga sunma rainani,da harna Yanke na fada musu gsky sbd Kona fada babu abinda suka isa sumin,saidai me , ganin Rukayya danai wacce itace akan case din a ranar da Daddy yaxo bellin Dina shiyasa na kasa fadar GSKY ,sbd indai na fada nasan xata qara tsanata ne akan wacce takemin da ,banaso Rukayya ta tsaneni akan wannan abin Daya faru ,sai Kuma ya juyo yace barrister kaji yadda abun yake, Kuma Ina patan babu Wanda zaka fadawa, wannan maganar kamar yadda ka fada,so ya kasance dagani sai kai, inaso Kuma ka cikamin ALKawarin dakai cewa,xaka dage cewa bani na aikata ba har muyi nasara akan case din Dan wlh banason na rasa Rukayya wlh Ina Santa , Rukayya itace rayuwa ta,.....


Barrister Salman ya sauke numfashi , sai Kuma ya dago ya dafa kafadar lateef yace shikenan lateef karkaji komai dama gsky nake San ji Kuma naji,danna san ta yadda zan bullowa Shari'ar Amma tunda ka fadamin komai karka damu babu Wanda xaisan maganar nan dagani sai kai,har mugama case din nan muyi nasara ,da yardar Allah, lateef ya sauke numfashi yace shikenan barrister, barrister Salman yace shikenan sai patan nasara Kuma, sannan sai mun hadu a kotu,daga haka suka mike , lateef yay cikin gida barrister Salman Kuma ya fita daga gidan Dan awaje yay parking motarsa,.....




__________?&


A bangaren su ruky kuwa sosai barrister su Suma yake nashi kokarin,wajen bincike ,duk kan Wani shaida da ake bukata sunyi iya bakin kokarinsu wajen tanadar ta, har unguwar su shafa sunje,har gidan da aka dauko lateef inda akaiwa shafa fyade sunje,duk inda ya kamata suje sunje,saidai shidar Gani da ido ce kawai basu Samu,Kuma barrister shamsu ya qara tursasawa shafa cewa, ta tabbata lateef dinne yay mata fyade ba Wani ba,ta tabbatar masa da cewa shine,.....



Duk Wani evidence Wanda xasu nuna a cotu su Rukayya sun dauka sun bawa barrister shamsu,duk Wani recording da sukayi daga farkon case din har kawo yanxu sun attarasu awaje Daya,Kuma Basu xauna ba,sun dukufa bincike babu dare babu Rana suna Kuma dagewa da addu'a , Allah yasa suyi nasara,a zaman da xa'ayi a gaba,....



Yanxuma haka zaune suke awani park wajen karfe uku na Rana, anan ne suke jiran barrister shamsu, ruky tana sipping lemo da aka kawo musu,Hanan Kuma tana latse latsen waya, sai Khalil shima Dake xaune Yana duba wata jarida,sai dai dai Kun mutane Dake shiga da fice awajen ,sai waitress Dake kaikawo,....


Babu dadewa barrister shamsu ya qaraso wurin,yay sallama duk suka ansa masa suna Mai gyara zamansu,bayan barrister shamsu ya xauna,bayan sun gaisa ya fuskacesu dakyau yace,naje unguwar har makocin gidan lateef naje nayi Sa'a na sameshi yaxo weekend, wannan satin,yace gsky ya riga lateef tarewa,Dan yace qarasa gidan lateef din da komai baifi one month ba, yace Amma shi baitaba, kawowa komai akan xuwan lateef ko Rashin xuwansa ba,sbd shi bama xama yake ba bare Kuma su hadu,yace hasalima Bai taba ganinsa ba, ni bannuna masa komai ba, nai Masa godiya na taho ,.....


San nan na danyi tambaya,a unguwar a dan siyasance Amma bansamu komai akai ba,iya kaci kowa cewa yake Bai Sanshiba,sbd motarsa ma tinted glasses ne,Kuma Bada mota daya yake xuwa ba,Kuma kunsan ba kowane ma zai san da xaman Wani ko Rashin Saba sbd kunsan unguwa ce sabuwa wacce babu ruwan kowa da kowa, ruky ta sauke numfashi tace shikenan barrister Babu komai in Sha Allah baxamu gushe ba xamu cigava da bincike tareda addu'a har Allah yasa adace, barrister shamsu ya ansa da Ameen, Khalil cikin murmushi yace mungode kwarai da GSK barrister Allah ya Saka da Alkhairi, barrister shamsu murmushin shima yayi yace Babu komai Mr journalist it's my pleasure, tareda mikawa Khalil hannu sukai musabaha, Hanan ma tace thanks barrister, barrister shamsu yace nevermind ASP,....



Ruky tace yanxu barrister, Sai me Kuma ake bukata, barrister shamsu yace Babu komai ASP yanxu kawai addu'a xamu dage da ita, ruky ta sauke numfashi tace to shikenan barrister in Sha Allah xamu cigava dayi, dukansu suka ce in Sha Allah,daga haka duk suka mike suka fita daga wajen,bayan Ruky ta biya Bill din,.....



___________?&


A bangaren AA Arab kuwa,yau kwanansa biyar da dawowa,yau kuma,duk su ukty da ukty Salma duk suka koma gidajensu, tareda da 'ya'yansu yanxu haka ma daga airport suke sunyi musu rakiya shida zuhrah da Ameerah, driver ne ke driving din,Ameerah ce a gaban motar kusa da driver sai zuhrah Dake baya kusa da AA Arab wacce ke masa surutu qasa qasa,suna tafiya ahanya bayan sun baro airport xuwa hanyar su ta xuwa gida,sun kusa xuwa wani park Dake gaban su zuhrah ta tabo AA Arab Dake latsa wayarsa tace yaya akhy dan Allah mu tsaya a park dinnan ka siya mana boga,AA Arab ya kalleta da idanuwan sa,cikin cool voice dinsa yace zuhrah boga Kuma ,tace eh yaya akhy wlh so nake naci,ta fada cikin shagwaba,Ameerah dake jinsu tai tsaki tace waike zuhrah meyasaki ke Saka aikine Dake,Yaya akhy karmu tsaya idan mun koma gida kyasa su safiyya su miki, ....



zuhrah ta turo Baki gaba tace ukty Ameerah badake nake ba,da Yaya akhy nake ,Kuma ni ta park din nake so ta fada tana juyawa Ameerah ido,AA Arab yay gyaran murya Jin conversation dinsu yace ya isa ,yace zuhrah muje na siya miki,yace driver idan munje dai dai park dinnan ka tsaya xamu sai Abu, cikin girmamawa driver yace Babu komai ranka ya Dade, zuhrah taiwa Ameerah gwalo wacce ke Harar ta, Ameerah tai kwafa cikin qasa da murya wacce iya zuhrah ce xata jita tace wlh xamuje gidane,babu dadewa suka karaso wurin,Saida sukaxo dai dai gate din wurin AA Arab yace yay parking a gefen titin,tunda ba'a shiga da mota wurin ,babu musu driver yay yadda aka umarceshi,AA Arab ya xura kafafuwansa ya sauka zuhrah ma haka, yace Ameerah ma ta sauko, babu musu ta sauko tana Dan hararar zuhrah,....


Sanye yake cikin shigar qananan kaya as usual,Wanda suka fito da kyansa sosai kamar ki sace sa ki gudu, sumar nan tasa Irin na larabawa agyare take tsaf kamar ko yaushe sai Wani tashin kanshi yake,Mai kashe jiki,ga iskan da akeyi kadan kadan tana Dan daga sumar tasa kadan kadan , Suma su zuhrah da Ameerah sanye suke cikin abayoyi , Ameerah black, zuhrah Kuma blue black,Yana rike da wayarsa a Daya hannun, Daya hannun Kuma yasa shi cikin aljihun Wandansa, Yana tafiya cikin nutsuwa, batareda kalle kalle ba ,gabansa kawai yake kallo,suna
gab da shiga wurin,....



Adai lokacin Kuma da su ruky suke fitowa, itama ruky sanye take cikin shigar uniform sai abayar data Dora akai itama black ,ita da Hanan wacce Tai mata matukar kyau, Khalil da barrister shamsu suna gabansu sai Hanan da ruky suna bayansu,wacce ke tai mata surutu, itadai ruky jinta kawai take, Khalil ne ya fara ganinsa cikin mamakin Ina ya taba ganinsa, Yana gab da xai wuce su, yasa Khalil yay saurin cewa barka dai yallabai, ya fada Yana murmushi tareda da Mika masa hannu alamar suyi musabaha,wannan maganar da Khalil yay wa AA Arab ita ta dawo da Hanan daga surutun da takewa ruky wacce jinta kawai take,Hanan ta Maida Kallan ta wajen Wanda Khalil kewa magana, itama cikin mamakin Ina ta tava ganinsa,take kallansa,Hakan yasa ta xuba masa ido har lokacin Bata tuna Ina ta Sansa ba,AA Arab yadan tsaya tareda juyowa jin anmai magana yasa yace cikin cool voice dinsa yauwa barka dai ya mikawa Khalil hannu Wanda tuni ya Mika masa suyi Musabaha,...


Ita ruky Kiran wayarta ma akai,Hakan yasa Bata Maida hankali kansa ba,tadan kalleshi saudaya adai dai lokacin da shima xai juya xaiyi gaba ,bayan sun gaisa da Khalil, Idansu ya sarke cikin na juna ruky tai saurin jenyewa nata Jin yadda kirjinta ya ansa, tareda yin gaba,har lokacin waya ce kare kunnanta,shima AA Arab janye nasa yay Jin Wani iri da tasirin kaifin Idanun nata sukai masa, cikin mamaki, Hanan itadai har lokacin kallan AA Arab kawai take Amma ta Kasa tuno a ina ta sanshi ,Kuma ta kasa furta komai,harya wuce kallansa kawai take tana kallansu su zuhrah Wanda Suke kama dashi bayama zuhrah,tuni ta juya ganin Ruky Bata gefenta, tai Maza ta cinmata Dan hartaje jikin motarta Kuma har lokacin waya take,....


Khalil ne ya karaso zai musu sallama Dan a motar barrister shamsu zasu tafi xai saukeshi a unguwar su,ya Kalli Hanan wacce har lokacin tunanin wannan mutumin data Gani kawai take Kuma ta kasa tuna Ina ta taba ganinsa, Khalil yace ASP kinsan waye wancan kuwa,Hanan tai saurin cewa a'a Khalil, Khalil Yana murmushi yace AA Arab ne fa,ai Hanan Batasan lokacin data fito da ido waje , tareda daka tsalleba tace AA Arab, Khalil na murmushi yace wlh shine,Hanan ta juya kamar wacce xata ganshi tace Khalil meyasa baka fadamin tun awurin ba,da wlh saina tsaya munyi magana ,kai wlh da har har hoto ma sai munyi, Khalil yace cikin murmushi ranki dade,wlh shine Nima sai Yanxu na tabbatar bayan munrabu Dan saida na dubo hotansa Dake wayata sannan na tabbatar,Hanan kamar me ,kamar xatai Kuka tace saina koma na ganshi ko Kuma na tsaya harya fito, Khalil yace ranki dade na tafi barrister na jirana sai kun taho,daga haka ya tafi, cikin sauri....


Hanan ta rasa Ina xatasa kanta Dan Dadi,yau itace gata ga AA Arab mutumin da take mafarkin inama su hadu, Amma yau gata gashi ko magana Bata samu sunyi ba,ta Kalli Ruky wacce ta gama waya yanxu,Dan batama San me suke cewa ba,tace Hanan mu wuce koh , ta fada tana kama handle din motar,Hanan tace Dallacan Ina Wanda ya wuce yanxu har suka gaisa da Khalil, Ruky ta yamutsa fuska tace waye kenan, Hanan ta harareta,tace bansani ba, Wanda ya wuce yanxu tareda wasu yan mata, ruky tace to ya akayi,Hanan cikin doki tace to AA Arab ne, ruky tai tsaki tace,wlh Hanan bakida hankali to Dan AA Arab ne saime shine kikabi kika rikice haka Dan kawai kin ganshi, Hanan tace wlh baxa ki Gane bane,ke kinganshi wlh yafi kyau a zahiri akan a hotoma ke Kinga kamar shi yay kansa,kai Allah yayi halitta ,ruky tai tsaki tace shigo mu tafi Dan Allah Hanan,kibar wannan Shirman,Hanan tace ke saina jira ya fito na qara ganin sa wlh , ruky ta tsaya take kallan hanan da mamaki , tana tunanin Anya ko Hanan Batada aljanu ,sai Kuma tsaki tace wlh tafiya xanyi, inyaso idan ya fito kika ganshi kin tafi daga baya, tunda waliyi ne,daga haka ta shiga motar ta,Hanan sai waigen gate din take taga ko xai fito , Amma shiru,harzata koma cikin park din, saita fasa ganin Ruky hartai reverse xata tafi yasata yin sauri ta shiga motar da xumar ai ance jibi xai fito aiki,tasan xata ganshi in Sha Allah......









07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD





*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE____*




*NA*




*_____NAJA'ATU UMAR FAROOQ _____*




*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1? QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA)=?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*




_______season one ep 3?? 7??



___________?&


*Bayan kwanan biyu*



Misalin karfe takwas da Rabi na safe AA Arab ne tsaye gaban dressing mirror Dake dakinsa Yana fesa turaruka masu bala'in kanshi ajikinsa,yayi shiga tsaf cikin uniform dinsa, domin yau take Monday ranar da zai fara fita aiki,akuma Headquarter office dinsa yake ,Wanda shine gava da CP awurin Ayanxu, ,daga shi sai CP yanxu a headquarter, domin shi mukamin sama ba'a state yake ba a federal yake, kawai dai Aiki ne ya kawoshi Kaduna ,dama can ma nukamin Daya rike dashi yafi na CP domin shi a federal yake,baifi rank uku bama ya xama AIG Kawai Dan wannan abin Daya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login