Showing 258001 words to 261000 words out of 278032 words

Chapter 87 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1070

Wani rawa da kakkarwa yake indai suke keb'e daga ita sai shi shiyasa garama tai Bak'i duk da bawai zaman gidan yake ba yana fita idan gari ya waye kamar k'arfe shabiyu na Rana haka, lokacin Bak'i sun fara zuwa to anan ne take samun ya Rabu da ita Amma indai daga ita sai shine Yana mak'ale da ita baya tab'a sassau ta mata.haka wunin yauma Tasha Bak'i sosai 'yan uwa da abokan arzik'i sukai ta zuwa,... washe gari da yamma ruky tana d'akinta tana zaune Bakin gado Bak'in da tai Basu Dad'e da tafiya ba shine ta shigo d'aki tana answering call , Babu dad'ewa AA Arab ya shigo d'akin bakinsa d'auke da sallama idonsa Yana kanta, take ruky ta juya jin anbud'e k'ofar tana kallon sa gabanta na fad'uwa Dan wallahi indai ta ganshi gabanta har Wani fad'uwa yake saboda Irin abunda yake mata koda yaushe,ya k'araso shigowa har cikin d'akin bayan ya rufe k'ofar ruky ta mik'e tana yin baya Ganin ya nufota tana Marai raice cewa yay murmushi kafin yay k'asa da murya yace .


"Why are you so scared fiancee!",ya fad'a Yana Yi mata Wani Irin narkekken kallo Yana k'ok'arin rik'o k'ugunta, ta Saka hannunta a k'irjinsa tana tokare shi Dan Hana kirjinta da nashi had'uwa ,tai narai narai da fuska tana kallan sa tace.

"Dan Allah kayi hak'uri ?"ta fad'a tana tura Baki gaba,yay murmushin ya kai bakinsa sai tin nata yayi kissing tai saurin juyar da kanta gefe tana tureshi tare da yin murmushi tana cewa.


"kai baka da aiki koda Yaushe saidai ka dinga damuna", ta fad'a cikin shagwab'a.


AA Arab yay murmushi Yana had'e ta da jikinsa kafin yay k'asa da murya yace cikin rad'a tare da sansanarta.


" to idan ban damu matata ba wa zan dama iye".ya fad'a Yana shafo fatar kirjinta da Hannunsa Yana kallan wajen.

Ruky ta rik'e hannunsa tana sakin murmushin tace .

Please yaya Dan Allah ka bari",

Ya d'auketa cak yay kan gadon da ita ai tana ganin haka ta sa Kuka tana k'ok'arin zillewa daga d'aukar ta da yay ,Amma Bai saurara mata ba Saida ya kaita har kan gadon ya kwantar da ita a hankali ta fara k'ok'arin d'agowa yay Saurin komar da ita yay mata rumfa da faffadan kirjinsa Yana K'ara duk'ar da kansa saitin fuskarta,ganin haka yasa ruky zaro ido waje tace.


"Dan Allah Dee!please karkayi wallahi mutuwa Zanyi idan ka K'ara ", ta fad'a tana matsar k'walla Dan wallahi ta tsorata da yanayinsa.ya D'ora hannunsa Saman lab'b'anta alamar tai shiru kafin yace cikin wata iriyar murya wacce ta fara sauyawa.

"Ki nutsu mana, muna da Bak'i a falon k'asa karsu jiki ,Babu abinda zan miki ok,dama zuwa nai na fad'a miki ki fito , Amma kika sa Zanyi abinda banyi niya ba". ya fad'a Yana kallan k'irjin ta Dake yin sama da k'asa Saboda tsoratan da Tai.jin abinda ya fad'a yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa .

"Ok! to d'aga Gani muje, suwaye Bak'in?,ta fad'a tana kallan sa.ya lumshe idonsa Yana bud'ewa lokaci D'aya kafin ya K'ara k'asa da murya yace .

ki bari mana na samu nutsuwa tukunna" ya fad'a Yana k'ok'arin k'wantowa kanta.ta zaro ido waje cikin tsorata kafin ta marai raice tace.

"Dee!kace fa Bak'i mukayi ka bari mana su tafi",.ta fad'a tana k'ok'arin yin kuka.


"Ya Sauke numfashi kafin yace .

"hmmm keda bama Kya Bari nayi cikin nutsuwa saidai idan nayi ta k'arfi, Kawai ki bari nai kissing D'inki",.

Tace" Dan Allah Dee! ka bari",

Yace only kiss fa",

Tace.

"Ka tabbatar iya shi zakayi?",

Ya d'aga mata kai kamar Wani k'aramin yaro Bai jira cewar taba ya kai bakinsa sai tin nata ya fara kissing gently ruky tai saurin rufe Idon ta ganin shi direct in to her eye yake Kallo ko kunya bayaji inji ta fad'a a zuciyar ta,tai shiru tana amsar sak'on ,GaninYana k'ok'arin wuje gona da iri yasa ta rik'e hannunsa tana marai raice tace.

"Only kiss fa kace",ya zuba mata Idan sa da suka fara sauya lokaci D'aya kafin ya iya cewa Dak'yar.

"Please fiancee I can't",ta zaro ido tace .

"You said! we have a visitors downstairs so why are you wants keep them waiting ai sai suyi tunanin Wani Abu muke". ta fad'a cikin rawar murya.


Yay Wani killer smile kafin yace.

"Ai ko yanzunma sun San Wani abun muke tunda sunjimu Shiru garama kawai kiyi hak'uri muyi in yaso sai suyi tunanin Hakan da hujja"ya fad'a Yana K'ara Maida bakinsa kan nata ,ruky ta tureshi da iya k'arfinta Amma ko gizau baiyiba illah zuba mata ido da yay Yana mata wani Irin murmushin mugunta . ruky tasa masa kuka tace.

"Please Dee!dan Allah ka bari muje naga suwaye visitors d'in", ya sauka daga saman kanta Yana gyara zaman hannun rigar jikinsa.ruky ta mik'e da sauri tana gyara wuyan rigarta kafin ta tura Baki gaba ta harareshi Yay murmushi yace .

"Oh!! ni kike harara ko?so kike nai Abinda banyi Niya ba kenan, tai saurin matsawa baya tana rok'arsa yay saurin rik'ota Yana had'a ta da Jikinsa kafin ya zuro da fuskarsa ta shoulder d'inta Yana mata magana yace.

"kinsan su waye suka zo?". ta girgiza masa kai yay murmushi ya rad'a mata a kunne,

take ruky tai saurin juyowa tana kallan sa da mamakin abinda ya fad'a murmushi shimfid'e a saman fuskarta tace.


"Wai baba lami da shafa ?".yay for Yana gyad'a mata kai .ai Batasan lokacin data d'ane jikinsa ba tana rungumeshi kafin ta d'ago ta kalleshi tace .


"Waya kawosu?".

yace .

"d'azu da safe bayan na fita baba ta K'irani da cewa zasu zo su gaishemu to Shine nasa driver ya dauk'o su ,ruky tai murmushi cikin farin ciki ta kai masa Sumba saman lab'b'ansa tana murmushi tace.

"Thanks alot Dee &I love u more"ta fad'a tana Wani kashe masa Ido d'aya .take ya K'ara rungumota Yana murmushi Shima yace .

"I love u too wifey",daga haka ya kamo hannunta yace .

"muje suna jiranmu a downstairs,Babu musu ta bishi suka fita daga d'akin Saida suka je stairs sannan ta k'wace hannun ta daga nasa ganin Bashi da niyyar sakin hannun nata ,


Bayan sun sauka k'asa suka zauna kan kujera 2 seater. da fara'a ruky ta tarb'i su baba lami tana gaidata Lokaci D'aya .Baba lami ta D'an zamo ta gaida Ruky .ruky tai saurin cewa.

" a'a baba tashi ki zauna ",cikin Jin kunya baba lami tace.

"A'a jami'a ban isa ba", ruky tai murmushi tace.

"Baba kin Isa Dan Allah ki tashi ki Zauna", Baba lami tace.

" to zan zauna ta juya ta gaida AA Arab.
AA Arab ya ansa mata da kulawa kafin yace shima ta koma ta zauna a kan kujerar babu musu ta koma ta zauna dama ita shafa tana Zaune k'asa akan carpet ta gaida AA Arab ya ansa mata da kulawa da tambayarta school tana murmushi tace masa Alhamdulillah.ya Jin jina kai yace."Allah ya taimaka",ta ansa da Ameen.sannan ta juya ta gaida ruky.ruky ta ansa mata tana cewa.

"Tashi ki zauna kan kujerar shafa ki daina zama a k'asa kinji?kinga fa doc sun hanaki zama a k'asa Ina dai fatan a gidan ma ba a k'asa kike zaman ba ko?".ta fad'a tana kallan ta.

Shafa ta gyad'a mata kai kafin tace "eh". Ruky ta Jin jina kai tace.


" to ya k'arfin jikin da fatan Babu wata matsala koh?".

Shafa ta gyad'a mata kai kafin tace.


"Babu komai Anty". ruky ta JinJina kai kafin tace.


" Allah ya K'ara lafiya suka ansa da Ameen, shidai AA Arab ya Maida kallansa kan wayar Hannunta , Amma Yana jinsu.daga haka ruky ta mik'e ta shiga kitchen Dan kawo musu ruwa, bayan ta fito ta ajiye musu ruwa da drink's da snacks kan table d'in Dake gabansu tace.


"Baba kusha ruwa". ta fad'a tana komawa wurin zaman ta,

Baba lami tai murmushi tace.

"To mungode jami'a",AA Arab ya mik'e tsaye Yana kallan Ruky yace .

"Let me answering the call out side",ta gyad'a masa kai daga haka ya fita daga falon.

Ganin baba lami sunki cin Komai data kawo musu yasa ruky cewa.


"Baba kusha ruwa mana",


Baba lami tace .

"To jami'a ", daga haka ta d'auki goran ruwan ta Bud'e shafa Kuma ta d'auki snacks d'in ta faraci.ruky ta haye sama Dan Basu waje suci abincin .... ruky ta kalli shafa tai k'asa da murya tace .

"Shafa kin tabbatar yanzu bakyajin Wani ciwo Wanda ya danginci ciwon da kikai a Baya?",.

Shafa tace .

"Eh anty! bana Jin komai Babu abinda ke damuna Inayin komai yadda ya kamata", ruky ta Jin jina kai kafin tace .


"Haka akeso ta Kalli baba lami tace"in Sha Allah baba shafa dai lafiya ta samu"baba lami tace.


"Wallahi jami'an ni kaina idan na zauna na Kalli shafa sai na dinga tuna Irin wahalar da shafa Tasha da Nima kaina kamar baza ta warke ba Amma sai gashi cikin hukuncin ubangiji da taimakon da Kuka Bada har tasamu lafiya nikan Babu abinda Zance daku sai dai nace Allah ubangiji ya Baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba Allah ya k'ara had'a kanku ashe haka Abun alkhairi ya k'ullu wallahi naji dad'i sosai,da yallab'ai yazo yake cemin ai ke zai aura naji dad'i sosai bakiji ba Saboda nasan baiyi zab'en tumun dare ba", ruky ta Bud'e ido da Baki Jin abinda Baba lami tace_tace .

"kai ba shiya fad'a miki?",baba lami tace wallahi Dan tun lokacin da muka tare a gidan Daya siya mana to Daya dawo yasa aka kai shafa makaranta To a ranar yake fad'a min wallahi naji dad'i sosai Allah ubangiji ya Baku zaman lafiya.

ruky tai murmushi tana ansawa da Ameen.sun Dad'e suna hira tana Kuma bawa shafa shawar wari da yadda zata dinga kulawa da kanta,har kusan k'arfe shida Saura na yamma sannan Suka ce zasu tafi . ruky ta k'ira AA Arab ya shigo ya samesu yace su fito ya sauke su sannan yace da Ruky ta d'auko mayafinta suje su sauke su tare.ruky taji Dad'i sosai Jin abinda ya fad'a haka na ta haura sama ta d'auko mayafinta suka fito daga falon bayan sun rufe ,AA Arab ya shiga D'aya daga cikin motacin sa Dake gidan suka duk suka shiga Sannan get man ya Bud'e musu gate suka fita ...Saida suka kai su baba lami har gida kafin su juyo baba lami tana tai musu godiya dasa musu albarka a AURAN su kamar zata Ari Baki, sukan suna ansawa sa Ameen,haka nan Baba lami suka shiga ciki su Kuma Suka bar unguwar. a Wani babban eatery menu suka Tsaya yay musu dinner sannan suka wuce gida....yau ma dai AA Arab Saida ya more a wannan dare ,Kuma har yau ruky ta kasa sabawa duk da kullum Saita shiga ruwan zafi safe da yamma Amma bata daina Jin zafi ba Dan kullum ji take kamar a Ranar farko abin ke faruwa Haka nan dai take rusa Mai kuka idan an gama kuma ya rungume abarsa Yana aikin lallashi.....



____________?&

A b'angaren Alhaji sunusi kuwa, azaba suke Sha ba kad'an ba ahannun wifer bayan wacce suke Sha ta gidan prison d'in aiki babu kalar Wanda baya Saka su shida babajo Ali tun Basu Saba ba gashi har sun dawo sun Saba,sun jeme sun rame sun kod'e kamar wad'an Basu tab'a rayuwar 'yanci ba,'yan cinma 'Yan siyasar da sukai lokaci Kuma ake ji dasu a wannan k'asar tamu, dama ita rayuwa haka take juyi juyi watarana idan Kaine a sama to watarana k'asa zaka dawo idan kuma Kaine a k'asan sai kiga ka dawo a sama matuk'ar Kabi Allah da manzonsa Allah yasa mudace >?2?.


Hajiya SA'A tazo gunsu shiga lateef har Sau biyu. na k'arshen da tazo ta data nunawa Alhaji sunusi pictures da videos na bikin su ruky da AA Arab saida yay kuka wai yaron dayake k'ok'arin ganin yaga bayan sa Amma yau shine yaci galaba akansu.take awajen nadama ta shige shi yanzu gashi 'ya'yan Dan uwansa Daya kashe Kuma ya wulak'anta rayuwar su yaci musu zarafi sune yanzu cikin wannan daular shi kuma gashi da yake ganin bazai tab'a fad'uwa k'asa ba sai gashi ya Fad'i wan war,ga babban mak'iyin sa AA Arab amma wai yau shine ya auri Rukayya Mai makon ta auri D'ansa lateef dayay ta fad'i tashi akan Ganin ya inganta rayuwarsa .ga su ya Tahir duk sunyi AURE take awajen ya hau kuka shab'e shab'e Hajiya SA'A na tayashi, Yana cewa idan taje gun lateef ta rok'ar masa yafiyar lateef agunsa, sannan taje har gidan mamah ta nemar masa yafiyarsa duka yaran da ita Kanta mamah.hajiya SA'A ta ansa masa tana kuka suna wannan halin akazo aka ce musu lokacin su yayi haka Hajiya SA'A ta mik'e tana barin wajen cikin Kuka da Dana Sani, itama kanta ta rame ta kode ta dawo siririyar k'arfi da yaji Dan Yanzu duk babu wannan jikin da take dashi,shima haka Alhaji sunusi ya bita da kallo Yana tunanin Inama ana Maida hannun agogo baya da Bai aikata abinda ya aikata ba haka ya koma d'akunan zamansu Yana rusar kuka kamar Wani k'aramin yaro.....


Da Hajiya SA'A taje gun lateef Saida ta zubar da hawaye saboda yadda lateef ya Koma,ya rame ya k'ek'ashe ya fita a hayyacinsa ya Tara wata uwar suma akansa ga wata k'asumba Daya ajiye,sai dai abin farin cikin Data tsinci Kanta aciki shine ganin yadda lateef ya nutsu lokaci D'aya, wannan abun data Gani tattare da lateef yasa zuciyar ta yin sanyi kad'an dama babban burin ta da addu'ar ta shine lateef ya nutsu kada ya mutu a wannan halin sannan Kuma kada yay halin ubansa, Yana k'arasowa ta rungume shi tana fashewa da Wani Irin kuka, abin mamaki Mai makon lateef shima yayi kukan sai gashi shine mai lallashinta take Hajiya SA'A ta d'ago tana Neman kallan sa kafin ta fara Neman yafiyarsa,yay Wani murmushin yak'e kafin yace cikin nutsuwar da samu acikin wannan prison d'in.


"na yafe miki mum,ni dama Babu abinda kikamin ke ai dama kina fad'a min gaskiya daddy ne dai baya fad'a min",ya fad'a da Wani rauni Dake cikin zuciyarsa.


Hajiya SA'A ta kalleshi da idanuwanta Wanda suka rine saboda Kuka tana kallan sa kafin tace .

Lateef ka yafewa mahaifin ka Yana Neman yafiyarka ",

Lateef yay shiru Yana kallan ta ,tace "kaji Dan Allah ka yafe masa ko zaiji sauk'i ta Wani b'angaren".

Lateef Ya numfasa kafin yace cikin bak'in cikin Daya kasa b'oyuwa har a fuskarsa saboda da Gaske yake baya san ko Jin maganar Alhaji sunusi bare Kuma yaji ammai zancen sa yace .



"Shikenan mum na yafe masa",

Hajiya SA'A ta k'ara rungumeshi shi tana kuka tana cewa.


" in Sha Allah lateef sai kafita daga wurin nan Batare da ka kai shekarun da aka yanke maka ba.shidai lateef jinta kawai yake.kafin yace


"Ni mum Abu D'aya nake so ki min, gashi har yau abin Yana damuna kulluma dashi nake kwana nake tashi Dan Allah ki nemi yarinyar nan ta yafemin"ya fad'a cikin damuwa.

Hajiya SA'A ta sauke numfashi kafin tace.

"in Sha Allah zan nemesu"ta kalleshi tace.

Lateef Rukayya fa tayi aure?"ta fad'a tana kallan reaction d'insa taji me zai ce.

yay Wani murmushi kafin yace.

"Dama nasan zatai AURE mum, Allah ya Basu zaman lafiya",ya fad'a Yana shaye hawayen sa.

Take Hajiya SA'A taji Wani Irin rauni ya mamaye mata zuciya ta D'ora kan lateef kan shoulder d'inta tana lallashinsa tana tunanin kozai je relief Dan tasan son Rukayya ajinin ajikinsa yake bazai tab'a iya cirewa lokaci D'aya ba Dole sai da kad'an kad'an, sun Dade ahaka tana kwantar masa da hankali kafin Azo ace mata lokacin ta ya k'are,haka Hajiya SA'A ta mik'e tana ji tana Gani tabar lateef cikin wannan mawiyacin halin tana kuka lateef yanayi haka nan ta tafi tabar shi.....



A b'angaren ZARI'A kuwa kamar yadda barrister shamsu ya fad'a sunyi waya da Ameenah a Ranar Daya koma Kaduna,bayan sun gama ya tambayeta ansar shi,inda tace masa sai tayi shawara tukunna,ai ko baiyi musu ba yace Babu komai saiya jita,aikuwa haka akayi ta samu ummah ta fad'a mata, ummah tace indai tana sanshi ai Babu komai Allah ya tabbatar musu da Alkhairi ,dama barrister shamsu yayi aure harda yayansa biyu mace da namiji kuma ya fad'awa Ameenah, Daya k'ira ta a daran Ranar ta fad'a masa cewar ta Amince Amma Kuma tana San zata cigaba da karatu yace wannan Babu komai shi da kansa ma zai NEMA mata ko Wacce school take so,to tun daga nan soyayya ta k'ara k'ulluwa a zuciyar Ameenah da barrister shamsu har Yana zuwa hira a sati sau D'aya yanzu hakama ya sama mata admissions anan ABU ZARI'A harta ta fara zuwa,Nana kuwa harta shiga aji na biyu a school of nursing ummah kuwa ita yanzu hankalinta ma ya Kwanta sai k'iba take abunta....



Baba asabe kuwa tana nan sai k'arewa take tana daga kwancen da take Dan wannan hawan jinin ya sakota a gaba ga Kuma hayaniyar ya'yan su mardiya ba dama tai musu magana sai iyayen su hayyayyak'o mata,ya zamto Kamar sune iyayen ita Kuma itace 'yar ,ga babban Bak'in cikinta shine Da har yau bata tabbatar da Wani shamsun ake magana ba Yana zuwa wajen Ameenah tana Jin dai yadda su mardiya suke ta hirar bazawarin Ameenah Mai mota ne Kuma gashi kyakkyawa Dan sun tab'a lek'awa sun ganshi lokacin daya zo,har suna fatan suma inama me motar Irin Sa suzo suce suna sansu ,itako Baba asabe Bak'in ciki kamar ya kashe ta,duk da ba'a sa ranar bikin ba, Amma kullum addu'ar ta Allah yasa ba shamsun da ya tab'a Neman Ameenah bane ba .ga babban Bak'in cikinta da damuwar ta zaman su Mardiya da lawisa a gidan amatsayin zaurawa har yau wannan Bak'in cikin Yana mak'ale aranta ,uwa uba zaliha dake d'auke da tsohon cikin shege sai girma yake Dan Yanzu yana wata na shida abin dai gabad'aya ya jagule mata kaf 'yan unguwar nan tasu Babu Wanda baisan zaliha tayi ciki ba sai Gori suke mata da habaici, wannan abun Yana D'aya daga cikin abinda ke K'ara sata a Damuwa,gashi Batada ishashshiyar lafiyar da zata fita , shiyasa kullum sai tayi kuka tana tuno da abubuwan Data aikata kardai ma ace sune suke bibiyar ta idan tai wanna tunanin sai tai saurin kawarwa Dan kadama ya dagula mata lissafi,ga uwa uba yadda malam Auwalu yay banza ya k'yaleta Dan ko magana baya mata bare


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login