Showing 51001 words to 54000 words out of 278032 words

Chapter 18 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1030

yan bakin ciki Saidai su mutu ,tunda nake aike kaga dai na Dade Ina wannan aikin Amma bantaba cin karo ko Ganin yaro qarami Mai halin manya irin AA Arab ba,DCP yace yanxu wannan yaran shine Wanda zaiyi maganin Yan ta addar, CP yace hmmm
Muktar kenan bakasan wanene Aliyu Ahmad Arab ba,yaran yasan kan duk Wani hatsabibin qasar nan ko Kuma marar gsky,kasan fa awaccen gwamnatinne suka sa lokaci Daya aka fitar dashi ,svd ya kusan yin baran barama shiyasa aka fitar dashi daga qasar ma gabadaya svd karya karyo musu lago kan aikinsu,sbd garin tone tonensa ya kusa tono garma,....


DCP ya gyara xama yace ranka ya Dade bani lvr kace kasan komai,CP yay murmushi yace nasan komai ,kawai alokacin ance ko xancensa akai duk Wanda aka kama a bakin aikinsa,har mutane akasa masu badda kama su shiga cikin al'umma majalisa majalisa ,wuri wuri indai aka kama ka ,kai xancen AA Arab saidai kaji ankwa a hannunka,daga nan Kuma sai firixun,idan aka kama Wani cikin ma'aikata yay xancen take xa'a kama mutum,koda ko xancensa kake sai an kamaka ,shiyasa lokacin kaji ko maganarma andaina,bare a dauko
Maganar Aliyu Ahmad Arab wato (AA Arab), shiyasa kaji yanxu Aliyu Ahmad Arab ya Bata bat,ko sunansa mutane kadanne suka sani,shima Kuma sai Wanda ya Dan Dade a harkar aiki Irin Namu, sannan ko ma'aikatanmu wadanda suka taso bayan tafiyarsa dede kune suka san Koda ko sunan sane bare Kuma labarinsa, ,wasu sun dauka ma ya mutu,Amma wannan gwamnatin dataga yan ta adda sun gagareta,da Kuma GSK suke sun shirya yin fito na fito da ita ai gashi xasu dawo dashi,DCP yace turkashi lallai akwai dawowar Maza kenan ,CP yay murmushi yace kasan waye ko Aliyu Ahmad Arab kuwa,....

Idan nace xan baka lvr saimu Wuni anan,mutum ne shi Mai SA'A arayuwa,Mai focusing duk abinda ya tunkaro shi ,ko Wani iri ne,wlh indai Aliyu Ahmad Arab ya dawo state dinnan wlh Yan ta'addar nan da suka addabemu sai sun Raina kansu,kai baba iya state dinnan ba Nigeria ma gabadaya , dagasu har masu goya musu baya,domin shi Hakan ba komai bane a wajensa ba,Dan ta kan wadanda suke sakasun kawai xai fara,sannan ya dawo kansu,shiyasa kaga shuwagabannin dayawansu basa San Aliyu Ahmad Arab a qasar nan,yawancinsu Sunyi murna da barinsa qasar nan,DCP yace kasan nasan lvrinsa lokacin da yay tashe a qasar nan,but bansan dalilinsa na barin sa qasar nan ba, saidai kawai barinsa kasar nan dayay lokaci Daya,CP yace hmmm muktar ka bari kawai akwai Dalilai bama daliiba,ka bari xakasha lvr saimun xauna tukunna, DCP yace Allah ya kaimu ranka ya Dade ,yanxu kenan Baki ya Bude kowa zai iya zancen AA Arab kenan tunda CP da kansa xai ban lvr ya fada Yana dariya , CP yay dariya yace ai yanxu mun Samu yancin xancen AA Arab tunda IG ma ya fada da president,DCP yay dariya harda kyakyatawa,sai Kuma yace Allah yasa mudace, CP ya ansa da Ameen,DCP yace xuwa yaushe kenan xai dawo qasar ko nace xa'a dawo dashi, CP yace ance Musa ran nan da few weeks, DCP yace Allah ya kaimu,CP ya ansa da Ameen kafin su cigaba da magana.....


________?&


Alhaji sunusi ne tsaye a folonsa Dake gidansa sai waya yake Yana saukewa,yanxunma waya yake da babajo Ali, gabadaya gumi yake kamar ba ac ce ta ko Ina afalon ba,ga fankar sama data qasa saiyi suke,Amma kamar ba aiki suke ba,ya jike sharkaf da xufa,yace babajo yanxu naga sanarwa wai Aliyu Ahmad Arab zai dawo kasar nan,daga Daya bangaren shima babajo Ali Dake tsayen kirjinsa na dukan uku uku Amma ya Dake svd karfin hali yace Nima na gani a internet, Alhaji sunusi yace innalillahi wainna ilaihi rajiun,yanxu shikenan komai namu tsai tsaya ne chak ,baxamu tava samun yadda Mukeso ba, indai tsinan nan yaron nan ya dawo kasar nan, kasar ma jihar Kaduna,munsamu dai su Marigayi yallabai taju sun kora mana shi amfitarshi daga qasar.....


Daga Daya bangaren babajo Ali yace,yo aidama su suke da ruwa da tsaki na sawa a koreshi daga qasar ganin Suma zai tona musu asiri,shine wato wannan jakar gomnatin zata dawo dashi ko sbd sunga yallabai taju ya mutu,ai wlh dama alokacin mun bari an kashe tsinan ne,wlh da haka Bata faruba ,da ai Babu Wanda zai musu aikin dashi zai musu, shiyasa xasu dawo dashi qasar din, Alhaji sunusi yace Allah dai ya tsinewa wannan gwamnatin da duk Wanda ya basu wannan shawaran,babajo yace honorable karka sare , Aliyu Ahmad Arab bazai tava Ganin bayanmuba ,saidai mu muga nasa, Alhaji sunusi yace wannan shugaban kasa ba akwai shugaban tsinannuba, Babajo Ali yace,ai ba tunanin president bane ba, wannan tunanin sa masa akai , Alhaji sunusi yace kamar ya Babajo, Babajo Ali yay murmushin takaici yace tunanin wannan tsinan nan Minister nanne da Kuma IG, Alhaji sunusi ya kasa zama haryanxu dai a tsaye yake yace kanaso kacemin su suka sa adawo dashi , babajo Ali yace kwarai kuwa,wai bakaga hoton meeting din da sukai a labarai ba, Alhaji sunusi yace ko kadan ban kula ba,...


Amma wadannan mutane ba akwai tsinan nuba,ni damuwa ta xa'a dakile wannan harkar da muke,Wanda sune gabadaya hanyar samun tattalin arxikinmu,wannan gwamnan wlh saiya gane da s MaiTama yake yake xancen ,saina koya masa hankali nasan shine ummul aba isin komai shiya dage sai ankawo tsaro da mafita a kaduna,to wlh mutanan kaduna yanxu suka fara shiga hannun mu, Basuga komai ba na tuggun da muka hada musu,babajo Ali yace hmm nidama nasan shine xai takura sai ankawo mafita,ka kyaleshi kwantan bauna xamu masa,karka nuna masa wani Abu ,da sannu zai afka Ramin da muke ta tona masa,idan ya shiga saimu rufeshi ta yadda babu Wanda ya isa ya gano inda yake, Alhaji sunusi yay dariyar baxata yace babajo kai shegene kasan takan mugunta,babajo Ali shima dariyar yay cike da mugunta yace karka damu honorable akwai mafita,ni nasan yadda xamu tafiyar da harkar mu cikin iya taku batareda da koshi ya Fargaba, Alhaji sunusi yace Tayaya babajo ,babajo Ali yay murmushi yace sai kace badani babajo kake tareba, rainon dattijon arxiki yallabai taju, Allah dai ya jikan musulmai,Amma karkai saurin sarewa mana mutumina, anyi dubu irinna su Aliyu Ahmad Arab,Kuma Basu gagari shugaban nin muba wato yallabai taju ,to Kuma waye Ahmad Arab,a wajen mu,ka kwantar da hankalinka babu Wani Abu da xamu fasa daga yadda muka faro kasuwancinmu, Alhaji sunusi yadan sauke ajiyar xuciyar salama,bawai Dan duka ya yarda da maganar da babajo Ali keyiba domin shi yasan waye Aliyu Ahmad Arab,bama shiba shi kansa babajo Ali ai yasan waye Aliyu Ahmad Arab, ai yasan yadda suka Sha fama dasu yallabai taju ,badan sunfi qarfinsaba lokacin sune da qasar su suke juya qasar yadda ransu yakeso, shiyasa sunayin magana aka fitar dashi daga qasar gabadaya shine Kuma Bai sake wai wayo kasar ba Koda wasa sai Yanxu ,da ake shirin dawo dashi qasar sa,kawai dai kila koya manta wasu daga cikin aiyukansa ne , babajo Ali yace Ina patan ka fahimta Alhaji sunusi ya gyada kai yace eh eh babajo ,babajo Ali yace nidai Dan Allah ka kwantar da hankalinka, Alhaji sunusi yace ai na yadda babajo kawai shikenan sai mun Hadu din daga haka suka Yi sallama, Alhaji sunusi ya kai zaune jagwab kan kujerar Dake saitinsa,ya fara lalumar abinda xai fifita kansa yaji sanyi,Dan wlh gabadaya jikinsa Wani Irin turirin xafi ne kawai ke fita Aliyu Ahmad Arab, AA Arab ai bala'ine duk Wani criminal Dake garin Kaduna waye Bai San Ahmad Arab ba ai saidai mutum bekai hatsabibin GSK keba,(tab >?? waini waye wannan Aliyu Ahmad Arab (AA Arab)dinne da Alhaji sunusi yake Neman sakin fitsari akansa tunma kafin yadawo kasar,eh lallai wannan mutumin xanso Nima ya dawo qasar kodan na gansa dagani har masu karatu),.....


________?&

Ruky ce xaune a falonsu da daddare tana latsa wayar ta ,hartagama chatting,har xata sauka sai Kuma ta shiga status ta fara viewing,ta tsaya akan na Shareef tana karanta abinda ya rubutua,*we are hopping u to arrived,our boss man ,AA Arab*


Kawai taga ya rubuta Bata Gane meyake nufi ba,Dan ta dauka Irin abin Daya sava yin posting ne na Yan ball,Dan yawancisune posting dinsa,kawai saita sauka Amma Kuma abin saitaji yadan kwanta mata ,Amma kawai saita basar, ta tashi ta haura sama bayan taiwa mamah Saida safe itada baba hasiya,bayan ta haura sama direct dakinta ta shiga,ta tube kayan jikinta daura towel ta shiga toilet dan tai wanka bayan ta fito, ta qarasa gaban mirror ta fara tsane jikinta da towel babu jimawa,taji wayanta Yana ringing Dake kan bedside drawer,ta dauka ta duba screen din taga Wani number ne ke kira ,saita xubawa number ido tana tunanin kamar tasan number,kamar an taba Kiranta da Irin number koma shine,har ta gama ringing batai picking ba kawai ta xubawa screen din wayar idone kamar wayar zata Bata ansar Mai Kiran, kamar baxatai picking , ganin ancigaba da kira,yasa kokarin dauka saida ta kusa tsinkewa tai picking ta kai kunne muryar Wanda ta daki dodon kunnan tane yasata, rintse idanta tana ambatan sunah Allah,a ranta....


Don ko kadan batai tunanin shine ba,babu sallama ko kadan bare kyawawan kalamai ,dama batai tunanin Hakan daga gareshi ba,Dan baya daya daga cikin dabi unsa indai ba ra'ayi yay ba,ahakan xai xama mijin AURE,to itako Taya ma xa'ayi taso lateef mutumin da bashida mana of speech,,daga Daya bangaren lateef yace shine kikai blocking Dina ko,waike atunaninki Hakan da kikai shine xaisa na Rabu Dake,wlh idan xaki nutsu gwara ki nutsu kinsan AURENAH Dake Nanda one week,kina gidana yanxu haka,daga ke har masu goya miki bayan kidinga min abinda kikemin din,wlh garama ki saduda kinsan dai Dady baya magana biyu koh,bawai kira nai muyi xanceva A'A kiranai kawai nai miki warning akan kashemin waya da kike,gashi yanxu har takai kiyi blocking Dina sbd samun waje,to wlh daga yanxu idan kika qara blocking Dina wlh saikinga abinda xanmiki na fada miki daga haka ya kashe wayarsa,....


Ruky tabi wayar da kallo bayan ta sauketa daga kunnanta,Wani malolon bakin ciki ne ya tsaya mata awuya,wai me lateef ya maidatane,daga shi har ubannasa me Suka maidasu , ita kenan Bata da Wani xabi sai abinda suka fada shida ubansa,wlh baxata tava auran lateef ba,saidai idan gawarta xa'a kai masa,zakuma ta nuna masa itama dai dai take dashi zata daina Jin tsoransa ta Dake itama,ta nuna juriya akan duk Wani barazana dayake mata,ahaka tai shirin bacci tai addu'a ta kwanta bawai Dan bacci ya dauketa ba, tunani ne kawai aranta.....




07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*_____JAMI'AR TSARO_____*



*____THE WOMEN POLICE____*



*NA*



*____NAJAATU UMAR FAROOQ____*



*_____(MRS SARAKIES)____*



*QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION(QUWA) =?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*


______season one ep 2?? 3??


________?&

Hajiya SA'A ce xaune akan Daya daga cikin kujerun falon ta, tana hada akwatuna set biyar Wanda ZA'A akai gidansu ruky na tambayarwa lateef auran ruky, Wanda Indai tambayace ai sunriga da sunyi ,kamar su yanxu aure ne suke jiran ranar daurashi nanda one week idan Allah ya kaimu , kayan tambayar ma dandai kawai al'adarsu ce shiyasa xasuyi,bayan ta gama rufe akwatunan ta dago ta kalli Alhaji sunusi Dake xaune akan sofar falonta ,tace Alhaji kadaiga kayan dama na kiraka ne ka Gani tunda kace ahada duk Wani Abu da akeyi akai din , Alhaji sunusi yace nifa duk bansan wadannan tsarabe tsaranenba Dan dai kawai kince ayine,Amma tunda har kinyi Kuma Kinga komai yayi aishikenan,tafara kokarin mikewa,tace a'a Alhaji yanxu yaushe kake ganin xa'a kai, Alhaji sunusi cikin kosawa yace duk ranar da kikaga yayi ,tace to su Hajiya mansura ne zasukai ko gobe ko jibi , Alhaji sunusi yace shikenan ni bari naje akwai inda xani Mai mahimmanci ana jirana, yace Ina lateef kwana biyu bana ganinsa Yana xuwa gida kuwa ,dafatan lpy yake, ....



Hajiya SA'A ta Dan tabe Baki tace Nima yau kwana na biyu banganshiba,saidai ya kirani awaya , Alhaji sunusi cikin Dan hasala yace nifa tunda xabennan namu ya gabato banaso lateef yadinga xuwa Wani gun Yana kwana,ko kuma gidajena na cikin garin Kaduna nan Yana xuwa Yana ShaShan cinsa aciki sbd gab ake da sa mana ido ko nace ana mana ma ,banaso ya janyo Wani abunda zai taba Siyasa ta musamman ni da nake da magauta Wanda kiris suke jira suji aibinka su samu na yadawa a social media, Hajiya SA'A tace ai Alhaji kaiya kamata ka fada masa Dan saiyafi Jin maganarka , Alhaji sunusi ya sauke numfashi yace xankirashi bari naje, Hajiya SA'A tace Allah ya kiyaye ya ansa da Ameen ya fita,.....


________?&

Sajen Jabir suna xaune shida cofur Audu ,sun danyi nesa da gidan yadda babu Wanda xai fahimci jami'an tsaro ne domin cikin shigar badda kama suke, idan ka Kallesu xaka dauka Irin masu gwangwan dinnan ne, masu tsince tsincen bole musamman ma a bololun masu hannu da shuni ,ko dedekun mutanan da suke unguwar Basu taba lura dasu ba sbd kowa harkar gabansa kawai yake,yanxu suna cikin Dan xaga wurin suna lura da komai ,kamar abinda almara wajen karfe 6:30pm, sukaga wata bakar mota kirar Benz,ta shigo layin sannu a hankali take tafiya,kamar me janta bayasan tuka ta,haka yake Jan motar,....


Tuni cofur Audu ya tava sajen jabir Dake daukar wata kwalba cikin wata bola Dake jikin wani gida Wanda yake farkon layin gidan da akai raping din shafa,shikuma gidan da akai raping din shafa a qarshen laying yake, Wanda shikadai ne bashida makota dukda shima wannan gidan din,masu gidan bawai xama suke ba,suna xuwa ne lokaci xuwa lokaci,bayan Jabir ya juyo cofur Audu yace sir ga Wani can yay parking kofar gidan, sajen jabir ya juyo ya Kalli Wanda ya fito daga cikin motar yay ,ya nufi gate din gidan, sannan ya xura key ya Bude gidan,ya Shiga ciki yay zooming din gate din , take gate din ya Bude,ya dawo ya shiga motar, ya shigar ta cikin gidan , Yana yin parking ya fito ya dawo ya qara clothing gate din,sannan ya nufi interance din shiga gidan ,....



kafin ya qaraso budurwar Dake gaban motar ta fito , cikin shigar wasu English Wears masu bala'in transperants,ga qaton glass a fuskarta, sai wani bala'in kanshi ne ke tashi a jikinta,ga attachments nan fal kanta ,ga farata Suma zako zako babu kyan Gani,haka ta nufi bayan Wanda yake kokarin bude kofar falon gidan,Dan tuni harya wuce ciki Dan baibi ta kanta ba, haka ta tako cikin yanga da lanqwasa harta tadda shi, bayan ya Bude suka shiga cikin falon,Wanda ya gaji da kayan more rayuwa iri daban daban, Dan babu abinda babu agidannan sai kace Wanda macece ke xaune agidan , basuyi wata wataba suka fada daki,.....



A bangaren su sajen jabir kuwa ,ido kawai suka xubawa Wanda yaxo gidan Batare da ya Farga dasu ba,Dan babu ta yadda ma zai kula dasu ballan tana yasan sunayi ,duk da baya ya Basu, Basuga fuskarsa sosai ba,iya gefen fuskarsa kawai suka iya Gani,bare Kuma ta cikin motar, dan tinted glasses ne gabadaya motar,harsuka shige gidan , suna kallansu, ganin ba fitowa xasuyi yanxuba tunda sun shiga da motar ciki yasa jabir dauko wayarsa, ya lalubo contact din DCP yay Kiransa,ya labar ta masa abinda suka Gani,.....



_________?&


Malam Auwalu ne ya shigo cikin gidan wajen karfe takwas da Rabi na dare ,bayan yay sallan isha'i ,ya Dan tsaya a majalisar su ta manya suka Dan taba hira,ya shigo gidan ransa a bala'in bace ,ganin abinda idansa ya Gane masa awaje,baba asabe cikin kissa akace sannu da xuwa malam,malam Auwalu Bai ansa ba saima Wani Banxan kallo Daya mata ya shige dakinsa,baba asabe ta tabe Baki Jin yadda malam Auwalu ya watsar da ita ya Kuma ci mata fuska gaban kishiyarta,bayan shigewar malam Auwalu daki da mintuna zaliha ta shigo gidan Hannunta dauke da bakaken ledoji,ta qasara shigowa gidan bakinta a washe kamar gonar auduga,ta nufi hanyar bangaren su,Jin muryar zaliha yasa Malam Auwalu fitowa daga dakinsa yace .....



Ke zaliha zonan waye wannan naga kin fito daga cikin motarsa, lokacin da xanshigo gidannan, gabadaya sai suka juya suna kallan malam Auwalu Wanda yay maganar ransa a bala'in bace,daga ummah har baba asabe, zaliha ta fara inda inda ya daka mata tsawa yace nace waye shidin, baba asabe tace a'a malam wai zaliha kake nufi ko Wacce, malam Auwalu cikin bacin Rai yace akwai wata zaliha ne agidan nan bayan ita,....


Baba asabe akace ,malam wacce Irin magana ce wannan kake jifan zaliha da ita, zaliha fa kace wai ta fito daga motar saurayi,zaliha da ta tafi dandali,sai dai ko atika yar gidan talatuwa kake nufi Amma zaliha babu motar Wanda take shiga nawa ma take,da har ZA'A 'ka'ka ba mata Irin wannan zargin ,malam Auwalu ya qara wurgawa baba asabe Banxan kallo yace,saidai uwar Dan dalilin ba dandali ba,nahaifi yar acikina Amma nakasa ganeta,ai ko sulu sainin dare naga zaliha wlh saina ganeta,ya juya ga zaliha datai sauri ta saki ledar hannun ta gefen barandarsu,yace wannan Dan iskanne zai batamin tarbiyar da nake muku,....


Ganin malam Auwalu ya juye ya dawo Wanda ta sani me xafi tace wlh baba ba Shiga motarsa naiba, tambayata yay wai inane gidansu atika shine na nuna masa,malam Auwalu ya dauko ice yay kan zaliha Data rafka aguje tai dakinsu ta sakato,tana ihun Irin sunan baba asabe,ta ceceta,yace wlh qarya kike Yi,ni abinda na gani aibe kama da tambaya yake Miki ba, fitiwo kikai daga cikin motar sa,waike har nawa kike da kikasan shiga motar saurayi,wlh zaliha idan na qara ganin kin shiga motar Wani wlh saina sauya miki kamanni,....


Baba asabe tace haba malam yanxu har tai Maka wannan baya nin Amma ka kasa yarda da ita, to mekake nufi Da kaga ta fito daga motar Wani,zaliha fa ba yarinya bace 'yar da ta Isa fita xance ce ,idanma tayi tunda ba Wani abun kaga sunayiba aida sauki,malam Auwalu ya jefar da iccen Hannunsa yace asabe, kina tunanin ni xanyiwa zaliha sharri ne,naga abinda da idona Amma ki karya tani,yartawa xanyiwa sharri,to bari Kiji tunda Abin Yaxo da haka aure xan mata da duk wanda naga Dama, da dai ajamin abin kunya,da mutunci na da komai baxa'a xubar min ba,Baba asabe tai tsalle ta dire tace wlh Nima babu Wanda ya isa yayiwa yata auren dole


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login