Showing 63001 words to 66000 words out of 278032 words

Chapter 22 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1088

ta matso kusa da Alhaji sunusi tana leken wayar ,tace Alhaji kiranka ake kai picking mana, ya qara kallan wayar yace bakuwar number ce,tace kai picking mana kaji ko waye,haka Alhaji sunusi yay picking call din,......



*Masusan a tallata musu hajarsu xasu iya Yin magana ta wannan number Dake qasa*





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD





*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)____*



*QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA) =?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*


_______season one ep 2?? 8??



___________?&

Ayau IG da minster tsaro xasu rako AA Arab xuwa jiharsa ta haihuwa wato Kaduna state, dama tun ajiyan sunje wajen Mai girma president inda ya Samu kar buwa ta musamman daga wajen president,da shaida masa cewa ,in Sha Allah ya dawo kasar sa kenan, babu Wani Abu da xai qara faruwa Irin Wanda ya faru ashekaru 6 da suka wuce , shidai AA Arab babu abinda yace sai godiya kawai da yay wa president,bayan sun gama suka Mike inda aka dauke su hotuna ,Wani akai daga shi sai president Wani Kuma sukai su hudu ,dashi da president da IG da Kuma Minister tsaro kafin kace me hotunan har sun xagaye kafofin sada xumunta,.....


Bayan sun baro Villa direct Airport aka wuce dasu inda xasubi jirgin karfe Daya da Rabi xuwa jihar Kaduna,bisa ga rakiyar wasu daga cikin jami'an tsaro domin Basu kariya daga sharrin masu sharri, jami'an tsaron daga kan police, army's, DSS,da sauran wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar tsaro,domin jirginsinsu iya su ya sune xasu tafi acikinsa cewar president, ,Wanda Hakan umarnine daga president,ya ilaihi xo kuga tsaro iya tsaro ni Mrs sarakies,>??ni kaina Saida na aje alkalamina kan littafina na tsaya ina kallan capacity iya capacity awurin nan, Ina ganinsu har suka shiga jirgi,saika dauka president ne,Wanda Bada su ZA'A ba da suka musu rakiya Saida suka tabbbar da tashin jirgin sannan suka koma,....



Anan kuduna kuwa,har sun Sami labarin xuwan AA Arab da su IG da minister tsaro da kuma Wanda xasu musu rakiya daga cikin masu ruwa da tsaki a har kar tsaro da Kuma jami'an tsaron kansu,Dan tundaga hotanan da sukai da president har da xuwansa airport, babu inda hotanan basu kareda ko Ina a kafar sada xumuntaba wato social media dama kasa Baki daya,ayau na tabbatar da farin jinin AA Arab inda ya Samo ASALI,Dan karkuso kuga yadda ake ta posting a social media, Dan duk inda ka shiga hotunan sane kawai suke yawo, status kuwa duk na Wanda ka Bude da pictures dinsa zakai fara cin karo,...



Wanda Hakan yasa duk Wanda baisan Shiba to a wannan Rana sai yaSan AA Arab,Kuma hakan ya xamto duk inda ka gitta a majalisa ma ta samari harma dama wasu majalisar ta manyan zancen AA Arab kawai suke Hakan yasa duk wanda baisan Shiba to awannan rana xaisan AA Arab sbd yadda hotunan sa suka karade ko Ina a padin kasar nan,gidan TV dama Dana radio gabadaya suna Airport suna jiran saukar jirgin nasu
Wanda gidajen tv har sun fara haskowa airport din ,da Kuma tattaunawa akan xuwan nasu,......


_________?&

A bangaren Alhaji sunusi kuwa,Bayan Alhaji sunusi ya daga wayar ,Yana jiran Jin Wanda xaiyi magana,yaji ance sallama alaikum dady Ina wuni ,Alhaji sunusi ya ansa, da yanayin muryarsa,cikin tashin hankali haydar yace Dady yanxu nakejin labarin wai ankama lateef, Alhaji sunusi Jin abinda haydar ya fada ya sashi Saka wayar a handsfree tareda mikewa tsaye,Dan Hajiya SA'A taji Dan ta matso da shine gab kamar xata fada cikin wayar taji Mai xa'ace awayar,...


Alhaji sunusi yace waye kai, haydar yace Nine haydar abokin lateef, Alhaji sunusi yace su waye suka kama lateef din, haydar yace wai jami'an tsaro ne, Alhaji sunusi yace Ina suka kaishi, haydar yace headquarter, Alhaji sunusi yace na gode daga haka ya kashe wayar, ya kai xaune kan kujera jagwab,Hajiya SA'A da duk ta rude Jin abinda haydar yace,tace Alhaji nashiga uku yanxu me lateef ya aikata da har Xa'a kaishi headquarter,.....

Alhaji sunusi ya furxar da zazzafan numfashi yace Babu Mai kai lateef headquarter saidai idan ko Wani babban Abu ya aukata,ya Mike yace bani key din mota ta gashi can a kan center table din can, dan baxan fita da motar da aka sanni ba, Hajiya SA'A ta miko masa key din jikinta na rawa ta mika masa ya karba tana masa adawo lpy,ya fita daga falon da babbar rigarsa sai tashin iska take,yay compound Yana Kiran driversa Wanda ya karaso da gudu Jin irin kiran da uban gidannasa yake masa Wanda dagani yasan ba lpy ba,ya xube a qasa yace yallabai Gani, Alhaji sunusi cikin hasala ya Mika masa key din batareda yace komai ba, driver ya karbi key din Daya ke Mika masa , Alhaji sunusi ya fada masa inda xai Kaishi,babu musu ya karba ya Bude masa gidan baya,suka nufi gate din bayan angwale musu gate din, direct headquarter suka nufa,.....

__________ ?&



Anan kuduna kuwa mamah ce xaune a falonsu ita da baba hasiya,suna kallan gidan TV na GADANGA TV & RADIO,Suma suna sauraran shirin nasu, wanda ya ta allakane akan xuwansu AA Arab,baba hasiya ta juyo ta kalli mamah tai tagumi Irin na alhini,tace unnn ni hasiya Hajiya kiga yadda ake ta zancen xuwan bawan Allah nan agari sai kace Wanda shugaban kasa ne zaixo ,dazu mafa Dana fita kasuwa da driver karkiga yadda ake ta zancen bawan Allah nan ,kamar me,mamah Dake xaune tana Shan fruits tai murmushi tareda Kallan baba hasiya,tace hasiya kenan,kinsan duk mutum me gsky da Amana arayuwa baya taba tabewa,Kuma ba'a cin nasara akansa ke anci nasarar akansa wata Rana sai gsky tayi halinta,da kinsan Irin gwagwar mayar da wannan mutumin yay a kaduna ke harma da qasa baki daya lallai kema zakice ya can canta ai masa wannan karramar akuma girmama shi sbd Irin sadaukarwar da yay,....


Ya Kuma Bada ransa fansa akan talakawa,kinsan ta addancin tun bayau aka farshiba,kinsan tun lokacin su Alhaji taju ,Wanda su sukai ruwa da tsakin barinsa wannan kasar ko nace aka koreshi,sbd sunga sune suke kan mulkin suke juya kasa yadda suke so ,sai abinda suka ce da formar president,shi xaiyi haka suka sa aka Kori bawan Allah nan daga kasar sa Wanda baijiba Bai ganiba, Kuma duk gudun karya tona musu asiri ne,yasa sukai Hakan,Nima duk wannan abin awurin Marigayi naji shi,shi yake fadamin ,kafin rasuwarsa, ta fada tana goge hawaye sbd tunowa datai da mijinta Kuma uban yayanta,Kuma tsohon dp IG,wato dp IG UMAR MAITAMA,baba hasiya jikinta yay sanyi ganin mamah na kuka tace Allah ya jikan uban mararuwa,yayi masa Rahma, Alhah yasa Yana Aljannah,...


Mamah ta goge hawayen ta tace Amin,a kullum idan xata tono da mijinta Kuma uban yayanta sai taji mutuwar ta dawo mata sabuwa,fil,har yau ta kasa manta yadda aka kawo gawarsa cikin jini,Wanda har aka kaishi kabarinsa jini Bai daina xuba daga jikinsa ba, tunanin ta ya katsene lokacin da gidan TV suka nuno da saukar jirginsinsu AA Arab ,ya sauka a airport din,ya ilaihi xo kuga jami'an tsaro awajen kamar Wanda president ne yaxo,....


Mutane koh karkiga yada suka cika wajen kamar wadanda aka gayyata, babu matsakar tsinke,kowa ya seta cameras sa Yana jiran fitowarsu, alokacin da suka fara saukowa ya ilaihi xo kuga yadda wurin ya rude da hayaniya jami'an tsaro sai surutu suke da bakinsu wajen Yi musu magana,suna Dan korarsu baya ganin kamar zasuje gaban jirgin,su tarosu,Wanda suka rakosu ne suka fara saukowa,da Kuma wasu jami'an tsaron da suka musu rakiya,sai Kuma IG da minster,Wanda gabansu da bayan su jami'an tsaro ne suna take musu baya ,sai shi uban gayyar,Wanda sannu a hankali yake saukowa, cikin shigarsa ta suits Amma wadannan bakakene ,da armless din fara tar, komai na jikinsa bakine,Wanda ya qara fitowa da ainahin kyansa na ruwa biyu da yake dashi,....

Ga sumar kansa sak ta larabawa data Sha gyara akoda yaushe itama bakakirin,sai sheki take da daukar ido,ga iska sai kadata take, kadan kadan gwanin ban sha'awa,yana maijin dadin Ganinsa a jiharsa, Wanda Rabon Daya tako xuwa cikinta yau shekara 6 kenan,wata nutsuwa ta musamman na saukar masa da ratsashi ta ko Ina ajikinsa,Yana shakar daddadar iskar garin,su IG da minster Saida suka saki Baki suna kallan iKon Allah,kawai ganin wadannan mutane masu bala'in yawa da sukaxo airport Kuma duk Sunsan sbd AA Arab sukaxo,Wanda sai kace Wani Dan siyasan da ake bala'in sone yaxo,bayan sun sakko tuni governor Kaduna shima ya taho tar barsu,Ashe shima Yaxo tundazu Yana cikin airport din ne, Yana jiran saukarsu....


AA Arab ya daga kai da mamaki ganin yadda ake kokawa da jami'an tsaron da mutanen asan sai sun karaso gareshi,Kiran sunansa kawai suke suna daga masa hannu,ga camera ta ko Ina sai haske take kawowa alamar hoto da vedios kawai ake dauka, awurin ,gabansa da bayansa police ne,kawai suke take masa baya,ga manya manyan guns a hannunsu sai xare ido suke,akaro na farko Daya Dan tsaya bayan saukowarsa yay murmushi, Wanda har fararen hakoransa farare tar tar dasu suka bayyana,suma ba dukansu ba,wayyo Allah nace Masha Allah lallai murmushi ba karamin kyau yake qarawa bawan Allah nan ,tareda daga musu hannu,ya furta thanks cikin cool voice dinsa sannan ya nufi wurin dasu IG suke da governor, gudun karya Bata musu lokaci , ya ilahi xo kuga ihu da sowa a wajen mutanan wurin yadda suka rude da kiran sunansa,AA Arab ya taddasu IG suna gaisawa da governor,Yana xuwa ya risina zai gaida governor, governor yay sauri ya dago shi ya rungume shi,yana patting bayansa yanaji tamkar Dansa na cikinsa,Yana Jin qaunarsa kawai tana ratsashi,ya dago shi suka gaisa,sannan suka nufi motaci Wanda akaxo dasu na musamman sbd xuwansu,bayan governor ya dagawa mutanen hannu alamar godiya,haka mutanan nan suka fara kokawar xuwa wajen motocin su da tuni aka tadasu , zasu fita daga airport din,Amma jami'an tsaron nan sun hanasu, qarasawa garesu.sai aukin Kiran sunan AA Arab kawai suke....


haka suka fita daga cikin airport din Wanda direct government house akai dasu ,Yan jarida suna San suji ta bakin AA Arab,suyi magana dashi ko yaya ,Amma babu dama haka suka gama dauke daukensu na hoto da daukar rahotansu na abinda suka Gani suka bar wajen , mamah tai murmushi tace gsky ne wato ubangiji baya taba barin Mai gsky tabewa a arayuwa ke kiga yadda ake taima mutumin kamar Wani shugaban kasa,baba hasiya da mamaki ya gama kasheta tace Hajiya yau naga Aya tab,ke kiga mutane sai kace tururuwa,mamah tai murmushi,Yaya hanaf ne ya shigo da sallama abakinsa ya xauna agefen mamah bayan ya gaidasu haka Shima yay ta mamaki suka fara maida xancen Dan shima ya Gani a tv Dake dakinsa,.....



_________?&

DCP ne xaune a office dinsa sai ruky Dake xaune itama Dan Bata Dade da xuwa ba,ya kirata awaya akan Yana San ganinta,ya kirata ne danya fada mata yadda suka kama suspect dinsu,,da yadda suka dauko shafa da yadda sukai da shafa,duk ya fada mata, Bayan ta gamaji Batasan lokacin data mike ba,ta xaro ido waje,tace sir lateef sunusi Mai Tama, DCP ya jinjina mata kai,yace Amma bansan Wani sunusi MaiTama bane ba,ko tsohon Dan siyasar nanne bansaniba,....

Ruky ta girgixa kai tace no sir Alhaji sunusi shine dai Mai sunan Dansa lateef, axuciyarta ta furta innalillahi wainna ilaihi rajiun,a fili Kuma tace sir muje na ganshi danna tabbbar, DCP yace please relax mubi komai a sannu ,tace sir inaso na ganshi ne sannan naje na samu shafa na qara nuna mata pictures dinsa,Wanda Ina dashi daga kan na shekaru baya can,tunma lokacin da abin ya faru inada pictures dinsa sosai Kuma shafa baxata taba masa sharri ba tunda ai yarinyar da wayanta lokacin da abin ya faru, Kuma ma ni nasan lateef Yana Neman mata,babu abinda bazai iya aikatawa ba,....


Daga haka ta fita daga office din, DCP ya bita abaya suka zagaya ta Bayan dakin da lateef yake ,ta window suka tsaya suna kallansa,suka tadda shi a tsaye ya kurawa bango ido Amma shi Bai gansu ba,ruky da tuni hawaye ya xubo idanta,ta share batareda DCP ya Gani ba, suka koma gefe ta kalli DCP tace Wani nasa yaxo, DCP ya girgixa kai, azuciyarta tace ni nasan babansa xaixo wurinnan ,Kuma wlh Babu Wanda ya isa fitarshi daga wurin nan,indai shafa ta tabbatar min da cewa shine ya wulakanta mata rayuwa haka,wlh Babu Wanda ya isa yay belin dinsa, a fili Kuma Kalli DCP Dake mata narkekken kallo, Amma Bata wannan take yanxu ba,tace sir thank u , thank for what u deed to , I appreciate with ur efforts ,nagode da goyon bayanka, akan case din nan,Allah ya Saka da Alkhairi bari naje ,daga haka suka varwajen, DCP yay hanyar office dinsa Dan shirin anjima su tafi airport Dan tarbar AA Arab,ita Kuma Ruky ta nufi mota tabar headquarter, Wanda direct tai hanyar asibitin, bayanta ta kira Khalil akan su hadu a asibitin,akwai update Mai mahimmanci,....


Bayan ta sauke wayar , gabadaya jitai kamar qara mata Wani courage ake akan yadda xata dage ta tsaya tsayin daka akan case din inhar ya tabbbar da lateef ne yay wanda yaywa shafa fyade,babu ruwanta da yadda suke dashi ,wlh ba cousin dinta ba,ba Kuma Wanda xata auraba,wlh ko mijinta ne sai inda karfinta ya qare,haka taita sakawa da kwacewa tareda goge hawayen da Batasan na meneba,har ta Isa asibitin,....



__________?&


A bangaren Alhaji sunusi kuwa,daga shi sai driver suka fita, direct headwater suka nufa,Dan yayi ta Kiran CP baya picking Kuma baya rasa dayan biyun suna tareda da governor sun tafi dauko wannan tsinan nan yaron AA Arab din,bayan haydar ya tabbatar masa da nanne inda aka kai lateef, Amma duk da haka saidai ya tambayi CP akace baya nan , yace inane office din DCP Shima akace masa bayanan,....


Ya tambayi wasu police da suka rage yace inane inda aka kai Dana, sukace waye shi danna shi,a fusace yace musu lateef sukace wlh su Basu San ma ankawo Wani nan ba,Nandai Alhaji sunusi ya tasa su agaba akan sai sun kaishi inda aka kawo lateef ai ance nan aka kawoshi ,suko suka dage akan su Basu ma San ankawo Wani nan ba, Alhaji sunusi ji yay kamar xai xauce Dan tashin hankali, Yana Kuma tunanin Irin Rashin mutuncin da xaiyiwa CP dama Wanda ya kama dannansa,....


Haka ya dinga xagaye headwater nan lungu da Sako ,Yana fama da babbar rigarsa da sai janshi take tana hardeshi kamar xata kadashi,Amma haka yake sabata a kafada,harya gama xuwa inda kafarsa xata iya kaishi Amma baiga inda aka kai lateef ba,Dan headwater akwaita da girma,Kuma duk da haka Bai gama zagayeta ba,ganin kansa na ciwo kamar zai rabe biyu yasashi komawa cikin motar yace da driver ya kaishi inda honorable babajo Ali ke jiransa dan tun daxu sai kiransa yake awaya Dan ya rasa Mai yasa, idan ya bari wurin babajo kuwa direct headquarter zai koma ai yasan kafin lokacin sundawo,wlh ayau sai sun sakar masa lateef Kuma ya wulakanta rayuwar su,xasusan dansa suka toxarta haka,ko laifi lateef yay, aiya kamata yay shi xasu Samu su fadawa bawai sudau doka ahannun suba,wlh lateef ko ciwon kai yay saiyasa sun Raina kansu,har lokacin Kiran number CP yake Amma har lokacin Baya picking kai daga karshema wayar akashe ya jita,haka ran Alhaji sunusi yay mummunan Baci,Jin wayar akashe wlh sai CP ya Raina kansa, haka ya cigaba da daukar alwashin yadda zai wulakanta duk Wanda yake dasa hannu a kama lateef,gefe Daya Kuma yana tunanin halinda lateef yake ciki,. Wanda baya rasa dayan biyun kila sai lateef ya kwanta jinya wannan xaman da yay a wulakantaccen wurinnan, tunda ba sabawa yay ba ,danshi aduniyar nan daka taba lateef gara ko waye ya rungumi transformer,,...
Kai Alhaji sunusi =?D?=?3?wlh mudai Banda mu, haka yay ta sakawa da kwacewa har suka isa wurin,





*Masu San a tallata musu hajarsu xasu xasu iya Yin magana ta wannan number Dake qasa*





07066508376_______
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*


*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*



*____(MRS SARAKIES)____*



*QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA)=?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*


______season one ep 2?? 9??



__________?&


Maman saude ta shirya tsaf domin xuwa ZARI'A, Ameenah ta Bata sakon wasika da ta kaiwa ummah,tasan Nana ce zata karanta mata, haka maman saude ta Saka wasikar nan cikin handbag dinta,ta adanata,ta nufi Tasha,wajen karfe uku ta sauka Dan dama karfe biyu da kusan Rabi ta tafi,ta sauka agidan yayarta maman suhail wacce ta cika da farin cikin xuwanta,ta rasa Ina xatasa kanta sbd Dadi,haka suka Wuni suna hirar yaushe gamo da Kuma hirar gidansu ,da yamma wajen karfe biyar da Rabi na yamma tace xataje su gaisa da babar wata makociyarta Dake nan layin transformer babu musu maman suhail tace shikenan saita dawo,.....


Haka maman saude ta shirya tsaf ta wuce layin gidansu Ameenah Dan xuwa gidansu Ameenah,batasha wahala ba ta Gane gidan svd Yana dab da wannan solar data fada mata,Kuma gidansu shine dai me blue din kofa, kamar yadda ta fada mata haka ta karaso har kofar gidan,da isarta ta fara knocking kofar gidan tareda da sallama , Amma shiru ba'a ansa ba saida ta qara tabiyu sannan aka ansa mata daga cikin gidan,....


Haka ta shiga gidan inda ta tarar da ummah abakin kofar falonta tana xaune,Wanda da alamar dai ita ta ansa mata sallamar, ummah ganin bukuwa yasa ta sakin murmushi tana sannu da xuwa karaso ta fada tana nuna mata gefen katuwar tabar mar data shimfida, babar saude itama murmushin ta Maidawa ummah, tareda qarasawa ta xauna atabar mar, ummah ta mike ta kawo mata ruwa a cup din stainless,tace ga ruwa Kisha babar saude tai mata godiya, ummah ta xauna sannan suka fara gaisawa,bayan sun gaisa babar saude wacce kallo Daya dataiwa ummah da tunshigowarta gidan tasan itace babar Ameenah sbd mugun kamar dataga sunayi sosai,...


Tace nasan Baki Gane niba koh,ta karasa fada tana murmushi, ummah da itama murmushin ta Maida mata tace eh wlh baiwar Allah,babar saude tace a Kaduna nake Amma a hayin rigasa unguwar mu Daya da Ameenah, ni makociyarta tace, ummah da tun lokacin da maman saude tace a hayin rigasa take,ta Kuma ce makociyar Ameenah ce,taji Wani sanyi aranta,tace to Ina patan dai Lpy,babar saude tana murmushi tace lpy lau wlh,dama xuwa nai xiyara gidan yayata Dake aure a nan,to shine Ameenah tace min ai a unguwar sune, shine ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login