Showing 69001 words to 72000 words out of 278032 words

Chapter 24 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1046

sun Rakasu airport haka suka dawo government house inda, police din da aka bawa AA Arab da security da zasu dinga kula da duk Wani motsinsa,sbd baxasuyi sakeba, tunda Sunsan Yan ta'addar da Kuma masu goya musu bayan baxasu taba zama haka ba,dole Suma xasuyi shiri na musamman,karsuje su kai masa hari,to shiyasa aka yanke hukuncin,bashi tsaro na musamman Dan saiya huta agida da iyayensa na tsawan sati Daya kafin ya fara fitowa aiki,.....



Haka Aka rakoshi da comboi xuwa gidansu Wanda yake a unguwar GRA,shima dai gidan akwai security ,sbd babansa shima tsohon ma aikacine gashi Kuma Yana kasuwanci ,da isarsu bakin gate din tuni security suka wangale musu gate din , motocin haka suka dinga shiga haraban gidan daya bayan Daya,Wanda motoci ne har biyar,sai kace Wani Dan majalisa,bayan anyi parking haka Wani police Dake gaban motar yay sauri ya fito ya Bude masa motar cikin girmamawa,haka ya fara zuro kafarsa guda Daya cikin nutsuwa kafin ya fito da dayar itama , bayan ya gama saukowa,ya Dan sauke ajiyar kadan ,yafara kalle kalle a harabar gidan dama Wanda ke dauke da manyan a permanent guda uku,ga parking lot guda biyu,Saida ya qare musu kallo sannan ya maida kallansa kan babban apartment din Wanda duka ya fisu girma,...



Bai fargaba saijin haniya yay,da yanda ake ambatar sunansa,ya qara xubawa a apartment ido , adai lokacin da wasu Yara farare tar tar kamar larabawa,suka nufoshi da gudu suna uncle ,u are welcome, axuciyarsa yace , wannan aikin ukty ne,taxo kenan dan rabonsa da yaran tun basufi two months ba,saidai idan Sunyi vedio call ta nuna Mai su,Kuma Suma har yau yaran Basu sanshi a xahiriba Amma sunshine a vedio call,dama tun ahanya suka addabeshi da Kiran wai ya taho, daga ji Yana waya da ummi shikenan suka karbe wayar suna Mai hayaniya,daga karshe ya daina picking call dinnasu sbd yasan sune,haka ya ware musu hannu suka fada jikinsa ya rungumesu,dan ba laifi AA Arab akwai shi da San yara,Yana murmushi har sannan,adai dai lokacin da Kuma gabadaya ahalin gidan nasu suka fito domin tarbarsa,daga Wanda suke nan har wadanda ba'a garin suke AUREBA sukaxo Dan xuwa yimai sannu da xuwa,....


Kafin yayi Wani motsin tuni sun qaraso wajen da yake rungume da abul da abla,inda ya saukesu Ganin,Yan uwannasa sun karaso,fuskokinsu dauke da madaukakin farin cikin ganin Dan uwannasu, kowanne burinsa yaje gareshi ,shima ganin suna murmushi yasashi kallansu Wanda har lokacin murmushi ne a fuskarsa,bayan sun qaraso ya Mika musu hannu ko Wacce sukai musabaha da ita daya bayan daya,suna Mai barka da xuwa Yana ansa musu Daya bayan Daya,ya daga kai ya hango ummi da Abba,da suke tsaye a bakin a apartment din,Wanda su kadai aka bari Basu qaraso ba,....


Ya kama hannun su abla suka nufi inda su ummi suke,Wanda Suma fuskarsu dauke take da murmushi da farin cikin ganin dawowar Dan nasu cikin koshin lpy,Wanda rabon sa da kasar 6 years kenan, danma suna Dan ziyartarsa lokaci bayan lokaci,bayan ya isa garesu ya sake hannun su abla ya karasa ga Abba Wanda ya ware masa hannu tuni ya qarasa ya rungumeshi,ya sauke ajiyar xuciya Yana Jin duk Wani kuncin rashinsu Daya dauki lokaci yana fama dashi ya kau atareda shi , Dan babu laifi yayi mutukar kewarsu, Abba ya patting bayansa yace sannu da xuwa Ahmad,sannu da hanya,ya dago yace sannu Abba,nasameku lpy, Abba yace lpy lau Alhamdulillah,Abba ya sakeshi ganin ummi na Mai hararar wasa,yace jeka xuwa ga fateema,naga tana hararata karta bugeni,su ukty suka sa dariya,AA Arab shima murmushin yayi,ya juya xuwa wajen ummi wacce ta ware masa hannu ta fara kokarin nufoshi tuni yay sauri ya tarota suka rungeme juna,....


Atare suka sauke numfashi tareda ajiyar xuciya,ummi tace sannu da xuwa baba nah,sai hawaye,shar Wanda suka sauka a gadan bayansa ya rintse ido tareda kankame ummi ,shima tuni xuciyarsa ta karye, abinda ya Dade da binnewa ashekaru 6 nan suna Neman dawo masa Amma saiyay sauri ya kau da tunanin,ya dago ya kalli fuskar ummi wacce tai sharkaf da hawaye ya fara share mata su Yana girgixa mata kai alamar ta daina, tareda murmushi,haka ummi ta kura masa ido Bata ko kiftawa,kamar Wanda take ganin xai koma inda ya fito,kamar mafarki take , yau Ahmad dinta ne ya dawo gareta, mafarkinta ya xama gsky tuni ta kama hannunsa tace muje ka huta banana, Abba yace mufa saidai hkr yau kan,dan fateema taga babanta babu xama, su ukty suka sa dariya,ummi tana jinsu Amma Bata tanka suba ta Kara danke hannun AA Arab kamar karta sakeshi,sukai cikin tangameman falonnasu Wanda ya gaji da huduwa, ukty ta kalli Abba Wanda ke murmushi ganin yadda ummi ta manta dashi ganin Ahmad,tace Abba muje muma ciki ka huta,sukasa dariya, Abba yay murmushi yace Allah yay muku albarka suka ansa da Ameen Sannan suka mara musu baya,....


Bayan sunshiga ummi ta zaunarshi kan kujera,itama ta zauna a gefensa,har lokacin murmushi ne kawai a fuskarsa, Yana karewa fuskar mahaifiyar tasa kallo Yana Jin qaunarta na qara mamaye masa xuciya,ganin yadda ta rude ta cika da farincikin ganinsa,SHikan sbd iyayensa kawai yasa ya dawo badan hakaba gsky dawowarsa saidai iKon Allah,ummi itama wacce ke murmushin tace sannu da xuwa baba nah,yace ummi ina wuni ,ummi tace lpy lau alhamdulillah, ya hanya yace lpy lau alhamdulillah ummi,ummi ta kamo hannunsa cikin damuwa tace ya naga kamar ka rame Ahmad,ya Dan waro ido yace ummi ramewa Kuma,ummi tace eh mana ,yay murmushi yace kawai stress ne,ummi ta sauke numfashi tace aishikenan, yanxu dai ka tashi kaje ka huta kafin lokacin sallah yayi, Abba Daya shigo yace Wani lokacin sallah Saidai na gobe Dan Yanzu haka gab ake da Kiran sallah yaje dai yay wanka saiya fito muje masallaci muyi sallah,ummi tace to Abba,tace Ahmad tashi muje na hada Maka ruwan wanka,ya kama hannunta yay kasa da murya yace ummi xan iya please ki huta,ya fada Yana langwabar da wuya,ummi tace ka tabbatar ya daga mata kai tace to ,kaje kadawo kaci Abinci yace to daga haka yay hanyar upstairs xuwa dakinsa Dake a apartment din, Yana shiga ya tadda komai need dakin sai tashin qamshi yake, Amma an sauya masa komai na ciki Dan ba na da bane,Dan wannan kallo Daya xaka musu kasan Sabine,azuciyarsa yace wannan aikin ummi ne, Allah ya Kara miki lpy da Nisan kwana,sai Kuma ya furxar da numfashi ya fara rage kayan jikinsa,bayan ya gama ya dauki rigar wanka wacce take itama subuwa Dake cikin press,haka yay sauri ya nufi toilet,Dan yin wanka tareda alwala,....



A falor kuwa su ukty ne kawai suke ta hirar , ganinsa da sukai a TV da yadda mutane suketa ta Dora shi a social media da Kuma yadda aka karrama yayan nasu kawai suke,suna Kuma farin cikin dawowarsa cikin kasarsa , kasar tasama jiharsa, addu'a kawai suke Allah ubangiji ya Dora shi akan makiyansa,ya kareshi da sharrin masu sharri, suna wannan xancen ne ya fito Dan xuwa masallaci adai dai lokacin da Abba shima ya fito Dan haka ya karasa ga Abba suka fita daga falon,ganin ana kiraye Kirayen sallah yasa ummi tace to iyayen surutu sai a tashi aje ai sallah koh,sukace wlh ummi kawai abunne ya burgemu cewar ameera,ummi tace naji idan kukai sallar koma miye kwa yishi daga baya ,zuhrah Dake itace auta ta matso kusa da ummi kama hannunta,ta tura Baki gaba tace ummi Kinga Yaya ko kallo na baiyiba ummi ta shafa kanta tace auta kiyi hkr kinsan agajiye yake idan ya huta na tabbata saikin gaji da kulawar da xai Baki , zuhrah tai murmushi tace to ummi,sai Kuma suka hada ido da Ameerah wacce ta Maka mata hararar, tace uwar complain ,komai complain,ummi ta kalli Ameerah wacce tai maganar tace Ina ruwanki ke Kuma Mai shiga abinda babu ruwanki,zuhrah ta mata gwalo ta haye sama da gudu ganin Ameerah ta biyota,ukty tace kai kudai Allah ya shirkeku , baza ku taba girma ba,ummi ta girgixa kai ta wuce daki ,sauran ma Suka tashi Dan suje su gabatar da tasu,



_________?&


Alhaji sunusi ne tsaye a office din CP shida babajo Ali Wanda yay Masa rakiya, Bayan ya samu wayar DCP wajen karfe 5:30 , CP yace yallabai daka zauna ai, Alhaji sunusi yace cikin hasala ni ba xamane ya kawoniba CP, so nake kawai ka fadamin waya kama Dana ya kawoshi headquarter da har aka kyaleshi tsawan kwana biyu ,Kuma kasan danna wane Amma kai shiru baka fadamin ba,...


CP cikin Rashin fahimta, yace yallabai Wani dannaka aka kama Kuma da har Xa'ace ankawoshi headquarter gsky bansaniba, Alhaji sunusi yace karka Raina min hankali mana CP dannawa lateef da aka kawoshi headquarter ne xakace baka saniba,kodai Wanda sukasa akamashin dinne suka rufe bakinku da kudi suka Hana,
kufadamin idan nazo ko Kuma ku hanani belinsa,CP yace wlh yallabai bansan ankawo danka ba, idanma nandin aka kawoshi gsky to Banda masaniya akai domin kwanana biyu kenan bana shigowa headquarter,...


Alhaji sunusi yace tonidai nan akace ankawoshi Kuma Wanda ya fadamin bazai qarya ba,CP yace bari na kira DCP naji koshi yasan xancen, Alhaji sunusi yace ka kira shi kaji shidin ko Yana headquarter aka kawo lateef din ,CP baice komai ba ya lalubo contact din DCP yay darling,bugu biyu DCP yay picking yace sir barka da yamma,CP ya ansa yace kana office ne, DCP yace yes sir, CP yace kana da lvrn kama Dan gidan Alhaji sunusi MaiTama da akayi aka kawo shi nan headquarter tamu,daga Daya bangaren DCP yace yes sir, CP yace ok gamunan xuwa office din naka,....


Bayan CP ya sauke wayar ya Kalli Alhaji sunusi Dake masa mugun kallo kamar xai dakeshi yace yallabai muje office din DCP muji yadda abun yake,haka suka dunguma xuwa din DCP, DCP Yana shirin barin office dinma suka shigo , DCP yace bismillahirrah, kuzauna sannu da xuwa yallabai ya fada Yana rusinawa Alhaji sunusi da Babajo Ali, ya ansa sama sama Yana watsawa DCP Kallan Banxa, yace ba xamane ya kawoniba,CP yace muktar yaushe aka kama shi lateef din,Kuma meya aikata,...


DCP yace sir shekaran jiya ne aka kawo shi nan,da laifin rape case ake zarginsa da yaywa wata yarinya, Alhaji sunusi yay tsaki yace rape case Kuma lateef din ne zaiyi raping wata yarinya, lateef da baya Neman mata ,to yar ubanwaye tukunna ma da xa'a masa wannan sharrin,Dan wlh sharri ne hada baki ZA'Ayi dasu Dan kawai anga Ina Neman takara, shiyasa akeso a Bata min siyasa ta,zargi mafa kace kuke bawai kamashi kukai dumu dumu ba, DCP ya Kalleshi cikin ido Yace yallabai muntabbatar da haka domin mun je har unguwar da yake xaune yake kawo mata munyi bincike sosai muntabbatar da haka, Alhaji sunusi yace aini tunda ba wai dumu dumu kuka kamashi ba, ai wannan Kuma bamu Mai yadda har sai Kun kawo shidai da xa'a tabbatar da haka,ko kotu akaje dole Saida shaidu tukunna ake zartar da hukunci...


Sbd haka ku sakemin Dana na tafi dashi Dan baxai qara kwanan wajennan ba, DCP yace yallabai ka gafarceni bawai musu nake da kaiba,Amma Dan Allah kabari Abi komai kamar yadda doka ta tanadar, Alhaji sunusi yace wai me kake nufi ne DCP,shi lateef din ya ansa laifinsane, yace ya aikata ko yaya,DCP yace Bai ansa ba Amma nasan da kansa Ma saiya ansa, Alhaji sunusi yace to Ashe shi lateef din Bai ansa ba,wai tukunna yarinyar yar ubanwaye ma da har xa'a tsaremin da akanta,kaga DCP Bai aikataba , idanma sharri xasu masa dansu samu kudi akansa to su fada ko nawane abiyasu, DCP yace yallabai baxancen kudi suke ba,Kuma yarinyar nan ba yar uban kowa bace a Kaduna su kawai burinsu a biwa yarinyar nan hakkintane kawai, Alhaji sunusi yace xancen Banxa zancen wofi, DCP kafitomin da Dana mutafi kana batamin lokaci Idan Kuma ba so kake kayi asarar aikin kaba to kafitomin da Dana, DCP yay murmushi kawai,....


Babajo Ali Daya rasa abin fada , ganin DCP xaiyi taurin kai, Kuma ba shakka sai sun biyomai ta qarqashin qasa yasa yaja CP waje can gefe ya rada masa Abu a kunne , CP ya gyada masa kai cikin sauri Hadi da girmamawa, sannan suka dawo office din,babajo Ali ya qaraso wajen Alhaji sunusi wanda ya lullube DCP da fada kamar xai kaimai duka Yana ikirarin saiya rasa aikinsa,yaja shi suka fita waje, ya radawa Alhaji sunusi abinda yasashi sakin numfashi, Alhaji sunusi Yace Taya xan bari saigobe xa'a saki lateef,BanSan halin dayake cikiba, babajo Ali yace CP yace ya tabbata Yana safe Yana waje me kyau , Alhaji sunusi yace Dan Allah babajo kabarni a saki lateef yau na koyawa wannan DCP hankali,babajo Ali ya girgixa kai yace komai a sannu akebi honorable,wanna CP baxai taurin kai ba,yace a bari xuwa goben xaisa DCP ya saki lateef din,....



Alhaji sunusi xaiyi mgn,babajo Ali yace Dan Allah honorable mu barwa goben duk dayane fa, idan har muka matsawa wannan DCP karka manta fa AA Arab yadawo jiharnan Kuma xai iya fitowa aiki Koda yaushe sbd haka mubi komai a sannu kada mu matsanta,Alhaji sunusi yace shikenan wlh dandai kawai kace hakane amma wlh da baxan taba yadda sai gobe ZA'A sakarmin lateef ba,daga haka suka koma ciki inda suka tadda CP yana tambayar DCP yadda akayi ya fada masa komai har Inda aka kai lateef batareda ya kawo komai aransa ba, Alhaji sunusi ya dinga Harar DCP ,babajo Ali yace to CP bari mu tafi sai goben , CP yace shikenan yallabai Allah ya kaimu daga haka suka fita CP y tafi danya musu rakiya,bayan fitarsu DCP , kawai ya tsaya yana mamakinsu a fili Kuma yace baxan tava yadda ko fitar da yarannan daga wurin nan ba,batareda wacce ta dankamin case din ta saniba, haba mutane sai San kansu kawai dan Basuga yadda aka lalatawa yarinyar rayuwarta bane shiyasa,da ace yayansu aida bama wannan xancen akeba,daga haka ya dauki key din motarsa ya rufe office din ya tafi parking lot Dan daukar motarsa ya tafi gida,...




*Masu San a tallata musu hajarsu xasu iya Yin magana ta wannan number Dake qasa*





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD





*____JAMI'AR TSARO____*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*



*___NAJAATU UMAR FAROOQ ___*



*____(MRS SARAKIES)____*



*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA)=?1?*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season one ep 3?? 1??



___________?&


Da malam Auwalu ya dawo da daddare, dayake baba asabe ce yau da girki,tuni tasameshi ta xugeshi tsaf, akan xuwan da Babar saude tayi,bayan ta kai masa abinci,suna cikin wannan halin ummah tai sallama, malam Auwalu ya ansa mata,ta shigo cikin dakin nasa, ganin baba asabe Saida gaban ummah ya fadi Danba shakka tasan asabe taxo ta xuga malam, tunda dama aita fada mata,daga yanayin kallan ma da baba asabe take mata tasan ta hada gulmar data sava hada mata awurin malam ta rasa ya xatayi da asabe,....


Haka dai ta qarasa cikin dakin jikinta a Sanyaye,Baba asabe Kuma ta tashi ta fara tattare kwanukan da malam Auwalu yaci abinci xata fitarsu daga dakin,bayan ta fita haka ta dinga bin ummah da Wani kallo, ummah dai Bata kula taba,Saida ummah ta tabbatar da fitar baba asabe daga dakin ,sannan ta dubi malam Auwalu Wanda ke kokarin kunna radio,kamarma baisan da xuwantaba, Amma haka ta daure,ummah tace malam magana naxo muyi, malam Auwalu ya kashe radio bayan ya kunnata, ya hade Rai ya dubi ummah yace Ina Sauraranki,.....


Ganin yadda ya hade Rai yasa ummah itama Dan hade nata ran sbd kwata kwata bataso yau baba asabe tai nasara akanta,ta tabbata kenan baba asabe ta xuga malam, ta kau da tunanin tace malam akan Ameenah ne,batajira cewar sa ba, ta cigaba da fadin,malam a GSKy na gaji da Irin rayuwar auren da Ameenah takeyi , na xalinci,na gaji da Irin axabtarwar da wannan yaran yakeyiwa Ameenah, yanxu yarinyar nan ko xuwa Tai ta fada Maka abinda yarannan yake mata na tabbatar karyatawa xakayi,yo inama taga fuskar tsayawa ka sauraretan,bansani ko kasan halinda take ciki shiyasa ma kwata kwata baka tsayawa kaji ta Bakinta oho, to yau dai Allah ya tona masa asiri,sbd haka gove idan Allah ya kaimu xanje na dauko Ameenah ta dawo gida araba auran kawai kowama ya huta,dan baxan zauna akashe min Yaba,ta qarasa fada tana huci...


Malam Auwalu dayake mata Wani kallo tunda ta fara xancen harta gama, yace maimuna kingama ummah tace eh na gama, ta fada tana kauda kai daga kallan da malam Auwalu yake mata,malam Auwalu yace to ita Ameenah ce ta tako tundaga gidan mijinnata ta fada miki Irin axabar da mijinta yake mata ko yaya ko ita ta fada miki cewa batajin dadin xaman gidan mijinnata, take cewa axabtar da ita yake,koyaya, ummah ta juyo da kallanta kan malam Auwalu tace haba malam, saita fada yau wata nawa rabon da Ameenah taxo gidannan,ai ka bincika kaji ko lpy, me yafaru Bata xuwa Kuma inba mantawa kayiba aida tana xuwa kusan duk bayan sati biyu, Amma kai naga alamar baka damuba sbd ba ita kadai ka haifa ba,Toni na gaji, idan kai baka damu da itaba ni na damu da ita,idan kai baka Santa ni Ina San 'yata,malam Auwalu ya Kalli ummah da mamaki yace maimuna,yau harni kike cewa bandamu da Ameenah ba,bana Santa,na haifi yar acikina Amma kice wai bandamu da itaba , ummah tace to kadamu da itan ne,yanzu duk jinyar da Xa'ace Ameenah tayi ka tava takawa da kafarka kace bari kaje ka dubata ,naga nan nan Nana taxo take fadamin halin da yarinyar nan take ciki,na sameka na fada Maka, dalilin haka har yayana ka kira kafada masa wai cewa xan kashewa Ameenah aure,Amma ko saudaya baka taba cewa ko ni ko Nana Wani yaje Yaga halin da take ciki ba,.....


Sbd ni Bansan ciwon haihuwa ba saina xauna
Harsai ya kashe min 'yata sannan xai kiraka yace a aika a dauko gawarta ko,to wlh nidai baxan tava yadda ba AURENe in Sha Allah Ameenah dai ta gama da wannan Dan iskan yaran ,malam Auwalu yace waini maimuna wayake xuwa yake xuga ki,yakeyiwa yarannan sharri ne akan Yana axabtar da Ameenah ko yanxunma Nana kika tura gidan Ameenah data Gano miki halin da take ciki,ummah tace ni ban tura Nana gidan Ameenah ba,Kuma Babu Wanda yake xugani Amma wlh nidai Ameenah daga yau ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login