Showing 216001 words to 219000 words out of 278032 words

Chapter 73 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1086

Allah ya kiyaye gaba"

AA Arab ya ce .

"Ameen "

sai Kuma ya ce "Oh na manta ma kince yau zaki bani ansa ta".


Ruky ta ce.

"Wani irin ansa Kuma?"ta fad'a da sigar tambaya.


AA Arab ya tsuke fuska kamar tana kallan sa kafin ya ce.


"aikinsani tunda ke kika fad'a,please ki fad'a min".ya fad'a da Wani Irin sauti .


Ruky ta rufe ido kafin tace .


" bazan iya fad'a ba sir".

AA Arab ya ce.

"Please fiancee ki fadamin ko zan daina jin abinda yake damuna"Dan Allah fiancee ji nake kamar zan yau bazan iya rayuwa ba indai Baki fad'a min ba"ya fad'a Yana Jan Wani Irin numfash???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i kamar Mai athma ...

Jin haka yasa Ruky ta riki ce tace " no please sir kayi hak'uri zan fad'a baza ka mutu ba"ta fad'a cikin muryar tashin hankali.

AA Arab ya gimtse dariyar sa da jinjina Rashin wayo Irin na ruky ya ce cikin k'asa da murya kamar Mai ciwon gaske

"ok Ina jinki".


Ruky tai kasa da muryarta kamar ta nutse haka take ji ta ce .

"Shikenan na amince". tana fad'ar haka ta kashe wayar tana sauke numfashi Dak'yar tana Kuma jin kamar Wani zunubin ta fad'a..


Ganin ta kashe wayar yasa AA Arab yay murmushi ya k'ara K'iran ta batai picking ba hakan ya Gane cewa kunyar sa take ji ,take ya lumshe ido Yana murmushi har lokacin komai na ruky burgeshi yake kafin ya kaiwa filon da yake kai Wani wawan runguma lokaci D'aya yana furta Alhamdulillah afili sannan ya shiga toilet ya d'auro alwala Dan ya Mik'a godiyarsa ga Allah...








07066508376_______
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*___JAMI'AR TSARO ___*



*___THE WOMEN POLICE ___*



*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*



*___(MRS SARAKIES =؋?)___*



*(' TAURARI WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season two ep 8?? 5??



_____________?&



Yau dai ruky k'in fita gurin aiki tai saboda kunya,Gani take baza tab'a iya had'a ido da AA Arab ba saboda abinda ya faru Daren jiya.ko da ya K'irata ma kin d'aga wayar tai , harta k'araci ringing d'inta ta gama batai picking ba,ji tai kunyar duniya ta rufa akan ta....


Yau wajen k'arfe biyar da mintuna 40 na yamma suna tare da Hanan , wacce ta biyo daga wajen aiki ta zo wajen ruky sakamakon K'iranta da ruky tai akan tana son ganin ta, suna zaune a tsakiyar kan gadon ruky,hanan ta ruk'o hannun ruky ta ce.


"Ni malama kin k'irani tun da safe kince min nazo akwai maganar da zamuyi kuma nazo kin min shiru kin k'i fad'a min, kin sani a gaba kina kallo na sai wani kame kame kike Dan Allah ki fad'amin mene ko zanji Dad'i".ta fad'a cikin k'aguwar taji wacce Irin magana ce ruky ta k'ira ta zasuyi..


Ruky ta sauke numfashi kafin ta k'ara rik'o Hannun Hanan akaro na babu adadi kamar zata saki Kuka tace..


"Hanan wai kinsan cewa yayi wai Yana Sona" ta fad'a tana Wani sunkuyar da kanta k'asa kamar Wanda ta aikata Wani babban zunubin.


Hanan ta D'an wato ido waje ta ce cikin Rashin fahimta.

"Waye yake son naki?".


Ruky tai k'asa da murya kamar Wani ne zai jita ta ce ."shi mana ".


Hanan ta ce "Ameer wai kike nufi? ".


Ruky ta harere ta sannan ta girgiza mata kai alamar a'a.

Hanan ta ce "to ni wallahi bansan waye Kuma yake son kiba bayan Ameer ko kinyi Wani saurayin ne bansani ba?",ta fad'a tana kallan Ruky.


Ruky ta kalleta sai Kuma ta kau da kanta gefe ta ce .

"yayanki mana"


Hanan ta ce "Wani yayan nawa Kuma ?"


Ruky ta ce.

"Yayanki mana na kalan dangi"?

Hanan ta d'anyi jimm alamar tunani sai Kuma can ta kalli Ruky da mamaki kafin ta ce.


"wai kina nufin kice min ya Ahmad kenen ko wa?".

Ruky ta jinjina mata kai alamar hakane .


Hanan ta waro ido waje ta washe Baki tare da wawuro Hannun ruky ta ce .


" Wai AA Arab kike nufi kowa? Kin sani a duhu ki fad'a min Dan Allah ".ta qara fad'a cikin mamaki tana Kuma jijjiga Hannun ruky....


Ruky ta ce "eh shi"

Hanan ta rasa inda zata sa kanta Dan farin ciki tana kallon ruky ta ce.

"Bani labari ya akayi ya ce Yana son ki? Kai wannan Abu yamin Dad'i sai kace a mafar?" Ta fad'a cikin k'aguwar ruky ta fad'a mata...


Ruky ta Wani kalleta kafin ta ce .


"Ni bansani ba ,na fad'a miki shine ,kuma me kike so ki sani bayan wannan".


Hanan ta rasa Ina zata sa kanta sai kace ita akace ana so d'in,sai Kuma tace .


"Ke wallahi abin ne da mamaki Ashe wannan zaman da kuke waje D'aya Ashe soyayya kuke shine kuka rufe ni a duhu" ta fad'a tana murmushi..


Ruky ta harareta kafin ta ce "sai dai abinda ya fi soyayya ba soyayya ba ko an fad'a miki ni haka nake".ta fad'a tana ture Hannun Hanan daga jikinta...


Hanan ta ce ke wallahi dole nai mamaki danni dai wannan zaman da kuke yi bamai tab'a yadda wai ya Ahmad zai ce Yana son ki ,kai Amma naji dad'i wallahi sosai.sai Kuma ta gyara zama kafin ta ce

"Ke fad'a min ya akayi Hakan ta faru?"ta fad'a tana murmushi...


Ruky ta Bud'e ido ta ce.

"kamar ya na fad'a miki ya akayi? wai ba gashi na fad'a miki ba".ta fad'a kamar zatai dariya saboda yadda Hanan ta Wani rikice lokaci D'aya...


Hanan ta ce.

"Ke ba haka nake nufi ba,Ina nufin Da yace Yana son naki ke Kuma me kika ce masa" ta fad'a tana jiran ansar da ruky zata Bata....


Ruky ta ce"me Kuwa nace masa, ni ban ce komai ba"

sai kuma ta rikyo hannun Hanan tace.


"jiya ne ma Daya ta kuramin da cewa na bashi ansa, shirya nace na amince Amma wallahi ni Hanan ban San ma na Fad'i haka ba ".ta karasa fad'a kamar zata saki Kuka..


Hanan ta harareta kafin ta ture Hannun ta data rik'e ta ce .



"Amma wlh bantab'a ganin sokuwa Irin kiba , yanzu a wannan zamanin wacce macace zata samu Irin AA Arab ya ce Yana son ta Amma tak'i amincewa lokaci D'aya idan ba keba,tab Amma wallahi kim bani mamaki ruky,naga keda bakin ki kike fad'a min cewa feenah taje har offiice d'in sa ranar ,Kuma kema kin tabbatar da abinda ya kaita ,to tunda ke bakyason shi Kinga ai kin huta, su feenah kuwa ita da doc Fatima sun samu miji Dan wallahi kina nan zaune zasu dinga zuwa office d'in nasa suna samunsa ,Kuma wallahi tun baya Basu attention har zai fara kulasu tunda ke bakyason shi" ta fad'a tana hararar ruky..

Ruky ta ce cikin damuwa"kai Hanan wanni irin fatane wannan ni wallahi kunya nake ji".ta fad'a tana tura Baki gaba...


Hanan ta Bud'e baki da mamaki ta ce .


"Kunya Kuma? Su Kunya manya" sai Kuma ta komai serious ta ce.


"kinga ruky wallahi idan ma zaki nutsu ki nutsu tun wuri kisan inda yake miki ciwoz dama ce Allah ya Baki saboda haka karki kuskura ki bar wanna damar taki ta kuf ce miki , wallahi ko ni na samu Mai Sona,yake Sona Nima nake son shi wallahi AURENAH Zanyi saboda haka wallahi ki rik'e AA Arab hannu bibbiyu Dan wannan mijin AURE ne kika samu"..


Ruky ta sauke ajiyar ta ce.

" Shikenan Zanyi trying in Sha Allah".


Hanan ta Bud'e ido tana kallan Ruky ta ce .

"Oh trying ma Zakiyi".


Ruky ta marai raice fuska kafin ta ce .

"To Zanyi duk abinda kika ce ".


Hanan ta harareta ta ce"karma kiyi nidai na fad'a miki".


Daga haka ta Mik'e Ganin 6:30pm ta gota ma tace.

"Ke tafiya Zanyi"


Ruky ta mik'e ta d'auki mayafin abayar ta, ta D'ora saman kanta , sannan tabi bayan Hanan wacce harta kai bakin k'ofar d'akin..

Suna sauka k'asa suka tarar da mamah ta fito daga kitchen Hanan ta D'an risina ta ce.


"Mamah na tafi",

Mamah tana murmushi ta ce "


"To Hanan mungode sosai Hanan ki gaida Hajiya Kareema".


Hanan ta ce "zataji In Sha Allah " daga haka suka fita daga falon gabad'aya...


Hanan tana zaune cikin motar tana kallan Ruky ta ce.


"Ina fatan dai kinji Mai na fad'a miki koh?,Saura Kuma idan ya k'ira karki tsaya kuyi hira ".ta fad'a in a serious note...


Ruky tana murmushi tace .


"To mamah Hanan Zanyi, Dan ke d'in saidai nace mamah sai kace wata 'yarki kike min wanna kashedin".


Hanan tai mata murmushi kafin ta ce.


"Allah serious k'awata, Dan Allah ki bashi dama ku more soyayyar ku gashi kuma Kun dace da juna,nima ki tayani da addu'a Allah ya kawo Min miji na gari soon muyi auranmu lokaci D'aya" ta k'arasa fad'a kamar zatai kuka.


Ruky sai da saki dariyar da bata shirya ba,ta daki kafad'ar Hanan kafin ta ce .


"Waike haka kike da son aure bansani ba".ta fad'a da sigar tsokana...


Hanan ta harareta kafin ta ce "dole kice min haka tunda ke kin samu mijin AURE,ruky karki manta fa shekara ta 25 fa ai dole naso AURE "..


Ruky ta rufo mata murfin motar tana cewa.

"Sannu wadda ta Isa AURE Allah ya kawo na garin".ta fad'a tana murmushi


Hanan tai murmushi ta tada motar tare da yin reverse ta bar k'ofar gidan,ruky itama cikin gidan ta nufa tana murmushi....



__________?&



Da daddare ruky tana kan gado akwance tai lamo da ita akan gadon,waya ce kare akunnanta wadda waya suke da AA Arab,da naji Yana cewa cikin deep voice d'insa.


"Uhmm my fiancee, meyasa yau baki shigo office ba ?"ya fad'a da wannan muryar tasa wacce take kashe wa ruky jiki..


Ruky ta rufe ido Kamar Yana gabanta ta ce cikin shagwab'a.

"Ni sir kunyar ka nake ji, Kuma ni bazan iya zuwa mu Hadu ba shiya yau banzo ba", ta fad'a tana Wani tura Baki gaba.


AA Arab ya lumshe idansa kafin ya Bud'e lokaci D'aya yace.


" Amma kinsan kinyi Laifi ko? Ai Bai kamata kik'i zuwa ba ,Dan dai Kinga a office d'ina kike shiyasa kikai zaman ki Baki zoba da ace a office d'in ku kike aida baza ma Kik'i zuwa ba"...


Ruky tai shiru tana sauraran sa..

AA Arab ya sauke numfashi kafin ya ce .


"Alright,let me ask u a question,to wai Mai yasa ma kike Jin kunya ta bayan ni bana Jin Taki?".


Ruky ta rufe ido Tak'i magana.



AA Arab ya ce " a kasa lance nifa banason wannan shirun naki please say something mana"..


Ruky tace cikin k'asa da murya"kai ai namiji ne,ni Kuma macece ".


AA Arab ya ce "oh really,su Kuma mazan aka fad'a miki Basu da kunya ne?",


Ruky ta ce ."to ai ba kamar mu mata ba".


AA Arab ya jinjina kai kafin ya ce "well,ni kenan bani da kunya da na fito nace ina sonki ko?".


Ruky ta ce.

"ni bance haka ba "


AA Arab ya ce .


"to miye idan ba haka ba".


Ruky ta ce "wlh sir ni dai kunyar ka nake ji".



AA Arab ya ce

"wait, nifa kidaina cemin sir d'in nan ".


Ruky ta ce a shagwab'e.


" to me zance "

AA Arab yay k'asa da murya kafin yace .

"Ni bakiji na Saura miki suna bane? kema saiki sauya min ".


Ruky tai murmushi ta ce.

"Ni bansan Wani suna zan fad'a Maka ba"...


AA Arab yace.


"Shikenan tunda ni bakya Sona".


Ruky tai shiru batai magana ba..

ya ce ."Hello, kinyi Shiru Hakan ya nuna min kenen bakyason nawa da Gaske koh? shikenan good night tunda bakyason Ahmad". Ya fad'a Yana wani narke mata...



Ruky tai saurin cewa.

"Noo please ni bance haka ba"..


AA Arab ya ce " eh mana gashi kin kasa canza min Suna, sannan kuma Baki ce kina Sona ba,ya fad'a da sigar tausayi.


Take jikin ruky yay sanyi ta ce .


"Noo please ni bance haka ba"..

AA Arab ya ce .


"Eh mana gashi kin fad'a"

Ruky tace "Noo please Kabar cewa haka "


AA Arab ya ce.

"Idan bakyason na dinga fad'a to kiyi abinda nace ".


Ruky tai shiru tana sauraran"

Ya ce" I'm waiting fiancee ".


Ta rufe Idon San ta ce cikin k'asa da murya kamar Mai rad'a.


"I love you"


AA Arab ya saki ajiyar zuciya sannan yay Wani murmushi yace

"I love you too my fiancee"..

Itadai ruky jitai kamar ta nutse awurin Dan kunya.


AA Arab ya ce.

"You know what?Bai jira cewar taba ya ce "yau gabad'aya da Bakizo office ba bakiga halin Dana shiga ba , Dan jinai kamar nai tsuntsu na zo gidannan na sameki".

Ita dai ruky tana rufe da idonta har lokacin...

AA Arab ya ce "please fiancee karki K'ara nesa Dani ,Dan bazan iya d'auka ba kinji?".


Ruky ta Jin jina kai kamar Yana kallan ta..

AA Arab ya kyira sunan ruky ya ce.


"Rukayya!"

Ruky tai shiru tana Jin kamar shi kad'ai ya iya fad'ar sunan ta.

ya ce. "Answer me please".


Ruky ta ce" uhmm"a k'asan mak'oshi...


AA Arab ya ce "

" Rukayya! Ina sonki ,kuma Ina k'aunarki,Ina rok'on Allah ya mallakamin ke amatsayin mata ta".

itadai ruky tai shiru tana sauraran AA tare da yin murmushi a hankali,Tana jin itakan tayi Sa'ar samun AA Arab a matsayin Mijin AURE,saboda yadda ya gama mamaye mata duka zuciya cikin k'an k'anin lokaci haka, Dan Bata tab'a tunanin zata bashi wuri na musamman ba acikin zuciyar ta...


ya cigaba ya ce "Yanzu kuma sai ki bani dama na turo gidan ku anemar min AURANKI ko?"ya fad'a in a serious note.


Ruky ta ce cikin dauriya.

"tun daga yanzu "


AA Arab ya ce "ko so kike na bari samarinki su rigani" ya fad'a da sigar tsokana.


Ruky ta B'ata rai Tare da turo Baki gaba tace.

"Nidai ka daina fad'a min haka, kuma su waye samarin nawa ?".


AA Arab Yay murya sannan ya ce .


"ba saina fad'a ba, nifa ko sunan su naji bana tunanin zan iya bacci a yanzu dai"


Ruky tai murmushi jin abinda yace tace.

"meyasa?".


Yace "saboda bazan iya had'a ki da Wani ba, saboda yadda nake kishin ki ,Dan bakisan idan naga kina waya da Wani ba yadda nake ji araina,bare Kuma na ganki tare da muktar aranar Kwana nake Ina Jin Bak'in cikin Hakan,idan nace zan Lissafo miki abubuwan da nake feeling akan ki sai mu kwana ba mu kai ko Rabi ba,sai Kuma ya ce"hmm Rukayya kenan Bakisan yadda nake k'aunar ki bane araina shiyasa,..

Sai Kuma ya cigaba ya ce .

"Let me told u something,tun a Ranar farko Dana fara D'ora idona akanki,to a ranar na fara kaunar ki,kuma naji duk duniya Babu wata mace Dana ke so Irin ki"..


Ruky tai murmushi tana sauraran sa tana Jin itama son shi na dad'a qaruwa aduka sassan jiknta.

Kafin yace "Bayan zu zan fayyace miki komai ba akwai lokaci,Wanda na ware shi na musamman arayuwa ta"

Ruky ta ce" meyasa baza ka fad'a min yanzu ba?".

AA Arab yay Murmushi ya ce kinaso ne na fad'a miki yanzu?".

Ruky ta ce ta gyada kai kafin tace"eh".

Yay murmushi yace.


"ki bari Bayan zuba akwai lokacin Dana tana dar mana na musamman"..

Ruky ta sauke numfashi ta ce "Allah ya kaimu ".

Yace "Ameen fiancee"..

Ita dai Ruky tai murmushi kawai.


Sun Dad'e suna hira Wanda Saida ya tabbatar da Ruky ta saki jikinta dashi tana kuma amsar duka sak'on dayake san isar mata Yana ratsa ta sannan ya k'yaleta ,bayan ya gama fad'ar abinda zai fad'a mata ya ce .


"oya kiss me fiancee" ya fad'a da wata murya.

ruky ta rufe Bakinta kafin ta Ankara taji ya sakar mata Wani hot kiss a kunnan ta Wanda Saida ta jaa numfashi sannan tai saurin kashe wayar tana murmushi ita kad'ai....


Bayan ruky ta sauke wayar haka kawai ta tsinci Kanta da shiga Wani Irin yanayi da addu'ar Allah ya barta da AA Arab kafin ta tashi shiga toilet ta fito sannu ta kwanta akan gadon tana addu'ar bacci......




_________?&


A takai dai Jama'a zaliha ta fara laulayi ,laulayi ma ko Irin Mai wahalar nan baba asabe Bata mata magana ko kad'an saidai hantara da zagi kala kala,Dan kullum saita tsinewa cikin zaliha ta uban cikin yafi a k'irga,tana nan dai tana shirin yadda zata Zubar da cikin nan, yanzu haka Bata nan ta fita unguwa Babu Wanda yasan inda ta tafi,Dan malam Auwalu Yana sa k'afa ya bar gidan ita tabi bayan sa,lawisa da mardiya suna tsakar gidan suna fama da yaransu , zaliha tana cikin d'akin baba asabe tun washe garin da akai wannan abin taso ta k'ira Alhaji tanko ta fad'a masa halin da take ciki to Bata samu dama ba sai yanzu,ganin ita kad'ai ce a d'akin yasa ta d'auko wayar ta lalumo number Alhaji tanko tai darling number Alhaji tanko Jin ta fara ringing yasa ta Sauke ajiyar zuciya tana addu'ar Allah yasa ya d'aga,babu dad'ewa kuwa taji yayi picking Yana cewa


"Baby ya ne?kwana biyu idan na k'ira wayarki bana samu fatan lafiya?" Ya fad'a cikin damuwa..

zaliha ta rufe bakin ta da hannu D'aya ta saki Kukan da take ta rik'ewa, Alhaji tanko ya ce cikin tashin hankali.


"lafiya baby meya faru?". Ya fad'a cikin damuwa,

sai da tai kukan ta Mai isarta sannan ta tsagaita tace .

Alhaji bani da lafiya, da aka kaini asibiti akace cikine Dani"ta k'arasa fad'a tana Mai rushewa da gunjin kuka,

Alhaji tanko ya ce "to! iKon Allah ciki Kuma?. To nawaye? Ya fad'a cikin Rashin damuwa.


Zaliha tace."na kane mana Alhaji ".

Alhaji tanko ya Zaro ido waje kafin ya ce "ke, ki Nemo Wanda yay miki cikin nan Amma ba niba saboda haka karki K'ara k'irana a waya", ya fad'a cikin GARGADI.


Zaliha ta zaro ido waje Jin abinda ya fad'a sai taji ciwan da take ji ma na neme shi ta rasa cikin fad'uwar gaba ta ce .


"Alhaji wannan Wani Irin magana ne ?kaima kasan wannan cikin ai nakane tunda Kaine ka fara sani na ba kowa ba,kuma kaima ai ka tab'a fad'a min haka,ko ka manta lokacin da kafadi haka".ta fad'a cikin fad'uwar gaba



Alhaji tanko ya had'e Rai yace.

"ke! karki Kuskura ki fad'amin maganar banza tun wuri ma Kije ki Nemo Wanda yay miki ciki amma bani ba saboda haka karki kuskura ki K'ara kirana daga haka ya kashe wayar sa yana Jan dogon tsaki..


Zaliha sandarewa tai a inda take zaune tafi mintuna biyar ahaka ta kasa Yadda da abinda Alhaji tanko ya fad'a mata ,kafin shock din ya sake ta ta fashe da Wani Irin kuka tana k'ok'arin shid'ewa...


A bangaren ummah kuwa Ameenah tayi wata D'aya da fara iddar ta ,ya kasance kenen Saura wata biyu da kwanaki ta gama iddar ta,idan Kuma ta gama tace zata koma makaranta, ummah dai Bata Hana tana, Nana ko tayi nisa a karatun ta Dan ta ci intro yanzu Kuma ta zama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login