Showing 156001 words to 159000 words out of 278032 words

Chapter 53 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1037

yasa Bai qarasa shigowa falon ba,ya dakata daga waje ya tsaya yana sauraran sa,Dan da karfi Alhaji sunusi yake yin Maganar da Wanda yakeyi din . kafafuwansa kusan kasa daukarsa sukayi sbd Jin irin magan ganun da suke fitowa daga bakin Dan uwansa, kasa gaskata abinda yaji yay, jiyake kamar a mafarki magan ganun ke xuwa masa, sunusi fa, sunusi Dan uwansa uwa daya uba daya fa,shine yake aikata Irin wannan miyagun abobuwan,Anya kuwa,Anya sunusi zai Yi haka kuwa.baisan tsawan lokacin Daya dauka ba,sai Jin muryar Alhaji sunusi yay akansa cikin firgicin kardai ace Yaya umar yaji abinda suka tattauna da yallabai taju, take wata mahaukaciyar xufa ta karyo masa,kafin ya Ankara AIG ya hankada shi cikin falon ya rufo kofar ya murxa mata key ,take Alhaji sunusi yay baya yay taga taga zai fadi Kuma saiya safe kujera.ya nuna Alhaji sunusi da yatsansa yace"GSK ne abinda kunnuwana suka juyo Muni ko Kuma karyane nace sunusi,? sunusi GSK ne ko karya ne?,ka fadamin sunusi,?ya qarasa fada yana Danko wuyan Alhaji sunusi Wanda yay tsilli tsilli da idanuwan sa, jikinsa na rawa Dan Bai taba ganun bacin ran yayan nasa ba irin yau.Alhaji sunusi kasa magana yay illah numfashi Daya dinga saki. AIG umar ya cikasa yace"wannan shurun da kai shiya tabbatar min da ansar tambayar da nake maka sunusi,kai conka sunusi,kayi asara wlh kayi asara, yanxu da iyayen mu suna raye sukaji Wannan abun kunyar daka ke aikatawa me kake tunanin xai faru,ya duniya zata Kallesu ,wlh da saika xama ajalinsu sunusi Dan nasan xuciyar su baxa ta iya daukar wannan abun kunyar da kake aikatawa ba....

Sai Kuma ya sassauta muryarsa yace "Allah sarkie su baba da baaba,Ashe Irin abunda suke hangowa kenan shiyasa suka dage Maka akan kada Kai siyasa,baxa kaiba,ba abun arxiki bace,Ashe su Sunsan abinda xai iya faruwa dakai Nan gaba, sunusi Ina kakai tarbiyar da iyayen mu suka bamu,yanxu karasa wacce Sana'a xakayi sai wannan ta musguna wa al'umma,me kake NEMA kaiko sunusi aduniyar nan daka zabi kayi wannan Sana'a,yace meye banyi Maka ba, idan Dan kudine yasa kake wannan Sana'ar,meye,zaisa baxa tambayeni ba,yace "ka bani ansa kayi shiru ....

Alhaji sunusi da har lokacin baiyi magana ba,ya dago da fuskar sa wacce ta sauya launi sbd bacin Rai yace "kawai ni ita tamin" AIG umar ya kwantar da murya yace "kamin ALKawari daga yau kabar wanna Sana'ar har abada sunusi,ni Kuma idan kamin haka nayi Maka ALKawarin xan baka Rabin dukiya ta Dana mallaka aduniya, sannan nasamo Maka Wani aikin".Alhaji sunusi ya girgixa kai yace "baxan taba iya daina Sana'a taba sbd da ita na Saba, AIG umar ya qara kwantar da murya yace "zaka iya sunusi Dan Allah kayi hkr kadaina wannan Sana'ar,naji idanma kudin Dana ambata makane yay Maka kadan xan baka dukiya ta gabadaya indai har xaka daina"ya karasa fada kamar xaiyi kuka.alhaji sunusi ya girgixa kai yace "wlh Yaya baxan iya ba, AIG umar yace "cikin fushi,wlh ni Kuma saina kama ku kaida duk masu aikata wannan aikin, sannan na tona Muku asiri a idan duniya ai kasan mune committee ko?, Alhaji sunusi yay murmushi yace "idan baka tona min asiri ba,to kai ba Dan halak bane Yaya daga haka yasa kansa ya fice daga falon,bayan ya murxa key din ya bude.AIG umar ya bi cikin sauri ya kiran shi, Amma sunusi Bai ko tsaya ba AIG umar kasa shiga cikin gidan yay Dan baya so ko kadan Wani Yasan Yana cikin damuwa.,ya dawo falon jikinsa sai rawa yake take ya hada wata uwar xufa ,ya xauna yana tunanin yadda zaiyi ya shawo kan sunusi ya bar aikata wannan Dan aikin....

__________?&

Gefe Daya Kuma Rukayya sun ku???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?sa fara xana SSCE,ga lateef ya fito mata a mutum yace Yana Santa, Rukayya tace ita Batasan shi ita karatu zatayi, shikuma ya ce zai jirata ko shekara nawa zatayi, Rukayya tace ita dai a'a, Dan ita amatsayin Dan uwa ta daukeshi ba'a saurayi ba,ganin Rukayya taki saurararsa yasa ya samu mamah da maganar, Mamah tai shiru Jin abinda ya girmeta,tai murmushi axuciyarta,can ta sauke numfashi cikin San Kwantarwa da lateef hankali Dan ita Gani take shi kansa lateef din, yaro ne,ba lallai ma Yasan mene ne sonba.tace "shikenan lateef ka kwantar da hankalinka kaga Rukayya yanxu Bata da wayo batama san abinda kake nufi ba, Amma idan ta girma tasan mene ne son, Kuma tace tana sanka in Sha Allah ni da kaina zan shige Maka gava gaba wajen ganin ka aureta".jin haka yasa lateef murna da Sakan kancewa shi xai AURI Rukayya, batareda tunanin ko ita Rukayya xataso shi Nan gaba kamar yadda mamah ta fada, Bai dauka cewa Rukayya zancen da tace Batasan shi daukarsa,ko Dan yarinya ce,kamar yadda mamah ta fada, daukarsa nan gaba idan ta girma zata so shi....

Tun daga wannan lokacin lateef ya makalawa ransa cewa shi zai auri Rukayya,Kuma son da yake yiwa Rukayya saiya qara lunkuwa azuciyarsa.yaje ya samu iyayensa da maganar su_ko basuyi masa musu Dan su duk abinda lateef yakeso to Suma shi sukeso..to tundaga wannan Rana AIG umar MaiTama yake cikin xullumi Amma Kuma Bai bari mamah tasan halin da yake ciki ba,Dan babu Wanda ya fadawa, Amma Kuma ya Saka aransa cewa saiya dauki mataki kan Alhaji sunusi.a bangaren Alhaji sunusi Kuma,shima kullum cikin xullumi yake da tunanin yadda yayansa xai tona masa asiri yake kamar yadda ya fada gefe Daya Kuma Yana tunanin ta yadda AIG umar MaiTama xai tona masa asiri....

Bayan sati biyu

awannan sati biyun da akayi, tsakanin Alhaji sunusi da AIG umar cikin xullumi sukayi shi,gefe Daya Kuma Alhaji sunusi Yana bibiyar yayansa batareda ya saniba,sai Wani tunani ya fado masa yadda zai samu mafita akan kada yayansa ya tona masa asiri kamar yadda ya fada, abinda Bai saniba shi AIG tsoratar dashi yay Dan ya daina wannan Sana'ar.shiko yallabai taju yadda zaiyi da AA Arab kawai yake, akuma lokacin AA Arab sunje Abuja shida commissioner wajen AIG umar MaiTama, duk Kuma akan wannan case din da suke na matsalar tsaro a kasa,Aiko Alhaji sunusi yaji shida yallabai taju cewa AA Arab da commissioner sun tafi Abuja duk daukarsu tona musu asiri zasuyi basusan su akwai abinda ya kaisu ba. tuni y'allabai taju yace " yasan matakin da xai dauka akan AA Arab, kafin ya kaiga tona musu asiri shi xaiyi maganinsa,wunin ranar acikin xullumi suka yita,har dare Kuma basuji wata magana akan suba.ganin ranar sunji shiru ba'a tona musu asiri ba. yasa washe gari Alhaji sunusi ya dauki hanyar Abuja ranar wata alhamis wacce taxama bakar Rana ga alahin AIG umar MaiTama,bayan Alhaji sunusi ya gama yanke Irin shawarar da yake tunanin ita kadaice mafitar da xai hana yayansa tona Masa asiri,ya shirya ya dauki motar sa shikadai ya tafi Abuja,Yana daf da shiga garin Abuja, ya xaro wayarsa yay darling number yayansa Yana Wani Hararar wayar kamar Yana gabansa.....

AIG umar MaiTama Yana office shi kadai Yana aiki a laptop dinshi, yaga Kiran Dan uwan nasa,sai yay mamakin ganin Kiran nasa Amma saiya kauda mamakin sa,Gani yake kila xaice masa ya daina Abinda yake Yi din.Yana yin picking baima gama yin sallamar da yay ba yaji muryar Dan uwansa Alhaji sunusi cikin tashin hankali da qaqari,Yana masa magana qasa qasa kamar Wanda yake cikin Wani mummunan yanayi.take AIG umar ya Mike daga xaunan da yake cikin firgici yace "meya faru sunusi?meya sakeka? kana Ina yimin bayani meya faru,? Alhaji sunusi ya qara makale murya ya kasa magana sai nishi kawai yake, take AIG umar ya rude Jin Dan uwansa kwaya Daya tal Daya rage masa aduniya Wanda shi kadai yake kallo yaji dadi Yana ambaton xai mutu,cikin dauriya AIG umar MaiTama ya qara tambayar Alhaji sunusi meya faru? yay Masa bayani.da kyar Alhaji sunusi yace cikin qaqari"na taho wurin ka Abuja ciwon cikina ya tashi, gashi na kasa komai Kuma ni kadai ne, kamar zan mutu haka nakeji Dan Allah kaxo ka taimakeni karna mutu Yaya umar,take AIG yace kaga " ka nutsu sunusi kana Ina yanxu?Alhaji sunusi yace"Ina daf da shigowa Abuja.cikin rudewa AIG yace gani nan xuwa ka nutsu kaji Allah ya sawake yanzu xanxo, Alhaji sunusi yace cikin Fargaba Dan ya tabbata kila kawoshi xa'a yi"Yaya kaidawa xaka taho ?AIG yace"ni kadai xanxo karka damu, Alhaji sunusi ya sauke ajiyar xuciyar salama, wacce da AIG a nutse yake da yaji .Alhaji sunusi Dan da harya firgita yayi tuna nin da comboi xai taho yace "to Yaya Dan Allah kayi sauri" AIG yace in Sha Allah daga haka ya fita daga office din, ya Tarar da yaransa kowa Yana position din sa.ganin ya fito a hargitse Yana cewa driver ya bashi key din motar, take police din Dake masa comboi suka taso suna tambayarsa da lpy Ina xashi yace" nan nan zance yanxu zan dawo, suka ce sir ka bari driver ya tuka ka"yace no karku damu basai an kaini ba ni xanyi driving da kaina",suka ce sir please kasan aikin mune Dan Allah ka bari to muyi Maka comboi kar muyi laifi,"ya Kallesu yace"karku damu basai Kun rakaniba I'm okay with that,ku kwantar da hankalinku,yanxu zan dawo daga haka ya karbi key din da driver ya Mika masa .bayan shiga yay wa motar key ya tafi amugun speed,ganin yanayin Daya figi motar take police din sukaji baxa su iya barinsa ya tafi shikadai ba, yadda yake arudan nan Dan haka xasubi bayansa anjima kadan idan yayi nisa Dan suga Ina xashi.....

07066508376________
'?

Follow the Mrs Sarakies =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1YFollow the Mrs Sarakies =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*___JAMI'AR TSARO ___*



*___THE WOMEN POLICE ___*



*NA*



*___NAJA'ATU UMAR FAROOQ ___*


*___(MRS SARAKIES =؋?)___=?1?



*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 6?? 5??



___________?&


AIG umar MaiTama tuki yake cikin tashin hankalin me xaije ya tadda ya samu d'an uwansa daya kirashi ya fada masa halin da yake ciki, Yana tuki ne Amma Yana masa fatan samun lpy kafin yaje acikin ransa.gefe Kuma Kiran Alhaji sunusi Danya kwatan ta masa Ina yake ya fada masa yaje ya sameshi.Alhaji sunusi cikin dauriya yake kwatanta masa inda yake din sai kace me ciwon GSK.haka Alhaji sunusi ya dinga jansa Yana fada masa inda yake,Saida ya kaishi can wata hanya wacce mutane Basu fiya biba, wacce ta kasance marar Rava.da ma take ya shirya yadda zai kashe Dan uwan nasa.AIG umar MaiTama cikin damuwa yake bin hanyar Yana mamakin meya biyo da sunusi ta wannan hanyar, wacce mutane Basu fiye biba.kwata kwata Bai kawo komai ba na Wani mugun nufi akan Dan uwansa aransa ba,Bai taba kawowa arance cewa Alhaji sunusi zai iya illa tashi ba .sanin Da yay Dan uwansa bazai taba cutar dashi ba,yasa ya kau da shakku akansa.Alhaji sunusi ya na zaune cikin motar sa ya hango motar Dan uwan nasa tun daga nesa na kawo wa kai titin da yake xaune cikin motar daga gefe titin,take ya dauki wayarsa yay darling wata number, Babu Bata lokaci akai picking Dan kamar dama jira ake,ana yin picking Alhaji sunusi yace "zaka iya tahowa"daga Daya bangaren aka ansa da angama yallabai....


AIG umar MaiTama Yana ta waige waige da hangen Ina xai hango motar Alhaji sunusi tunda yace masa Yana shigowa titin idan yay tafiya kadan xai hango shi.adai dai lokacin Daya hango motar Alhaji sunusi adai dai lokacin da wata babbar mota dake bin bayansa ta iyo kansa gadan gadan zata bi ta kansa, ganin haka yasa AIG umar MaiTama ya fara kokarin kauce mata saidai Ina Yana hango Alhaji sunusi ya fito acikin motar sa ya harde hannayensa a kirjinsa Yana kallansa,da murmushi a fuskarsa .ya dauke idansa daga kallan Alhaji sunusi da yake,ya Maida dubansa kan motar da take kokarin bi ta kansa ta mirror motar.yay saurin kaucewa motar Yana ambaton sunan Allah,sai dai motar gadan gadan kansa take iyowa,haka motar nan tabi ta kansa ta wuce Yana ji Yana Gani, Amma motar ba duka ta take Shiba,Rabin motar tabi ta kai tunda yay saurin matsawa gefe . Amma duk da haka taji masa rauni ba kadan ba.me motar ganin Kamar ya bi ta kan motar AIG umar MaiTama yasa ya tsallake motar ya gudu kamar yadda suka tsara da Alhaji sunusi idan ya gama ya gudu.babu ko d'ar Alhaji sunusi ya nufo gun da dan uwan nasa yake kwance cikin jini, ganin kamar ba gabadaya motar aka take ba ,Yana karaso WA yaga iya Daya gefen aka take Wanda ba inda AIG yake xaune ba,ganin motar batabi ta gun da AIG ke xaune ba, ma'ana driver seat ,yasa Alhaji sunusi qarasa site din da AIG ke ciki ya duba shi yaga Yana motsi ko bayayi,Yana xuwa ya leka shi ta site din da yake ya tadda shi Yana motsi ganin haka yasa Alhaji sunusi ya dago da kansa ya dubi AIG umar MaiTama ganin yadda fuskarsa ta jike da Jini. ya kura masa ido yace "nine nan nasa Mai motar can yabi ta kanka, Yaya umar ni zaka tonawa asiri koh?ina Dan uwan ka na jini Amma kace xaka tona min asiri akan Sana'ar da nake a idon duniya .to bari kaji kafin ka tona min asirin ni xan rabaka da ranka wannan plan din bana kowa bane nawane.shidai AIG kallan Alhaji sunusi kawai yake cikin mamakin Dan uwansa uwa daya uba daya shine yasa akashe shi.....



Alhaji sunusi yace "tunda baka mutu ba wlh baxan barka da rankaba yanxu zan qarasa ka".daga haka Alhaji sunusi ya bar wajen ya nufi motar sa, AIG ya bishi da ido daga kwancen da yake , bashi da iKon tashi bare ya gudu ,harya shiga motarsa yaga ya ta_da ta ya iyo kansa take ya rufe idonsa Yana Mai_mai ta kalmar shahada.Babu digon tausayi ko kadan Alhaji sunusi ya qara bi takan Dan uwansa,Saida ya tabbatar da baya motsi sannan yay wa motar sa key yay tafiyarsa.yabar Dan uwansa cikin wannan halin....



Yaran AIG sun biyo bayansa bayan da mintuna kadan saidai ya b'ace musu,Kuma ragon axancin da sukayi shine Basu biyo shi da wuri ba.sunyi kusan one hour suna Neman inda yabi Basu sameshi ba, kawai sai sukai deciding dasu koma office su jirashi kila bayasan su San inda zashi shiyasa, Kuma Suma suna tsoron su bishi yay musu fada yace ai yace kar Wanda ya bishi,haka nan suka koma office jikinsu a Sanyaye,sai dai har bayan awa biyu AIG Bai dawo ba, suka fara tunanin Ina yaje haka,wata awa biyun ma taxo ta wuce nan ma dai shiru Bai dawo ba take suka hadu suka ce driver sa ya kirashi awaya suji ko Yana lpy.Babu musu driver sa ya kirashi,sai dai tana ta ringing Bai picking ba,sai da suka sa driver ASP musa yay Masa Miss call yafi hamsin Amma baiyi picking ba, kai daga karshema wayar akashe,take suka fara tunanin Ina ya tafi da har zaice kar su bishi ya zabi tafiya shi kadai babu matakan tsaro babu komai, bayan yasan sune masu tsaran sa,masu masa comboi aduk inda zashi, Gashi yadda ake fama da wannan matsalar Rashin tsaron .yanxu idan Wani Abu ba fata ba ya faru dashi aka tambayesu me xasu ce, dole sune aruwa,tun da Alhakin kulawarsa tana wuyan su ,komai ya sameshi laifin su xa'a Gani.take suka ta-da hankalinsu gashi lokacin tashinsa daga office yayi, tunda karfe biyar da Rabi tayi.take hankalinsu ya tashi suka yanke shawarar tafiya nemansa, kawai Wani yace a'a Akira IG afada masa,Wani yace a'a gara a kira minster tsaro shine abokinsa Sosai,Wani Kuma yace a'a gara su fara Neman na sa tukunna.....



Suka tsaya amatsayar nemansa,suka rarrabu duk da Basu San ta Ina xasu fara Neman Saba Amma sun tabbatar baxai wuce cikin garin Abuja ba. suka bazu nemansa sune tun daga karfe shida har karfe takwas na dare Basu Samu inda yake ba,sallah ce kawai idan xasuyi suke tsayawa suyi.wasa wasa har qarfe Tara Saura Basu sameshi suka yanke shawarar suje gidan da yake sauka dayake idan yaxo Abuja agidan yake xama aciki, sai dai shima sunje ance be dawo ba,take xuba ta keto musu, meyasa ma basubi Shi ba tun farko ,suna wannan tunanin wayar driver sa tai ringing take ya xaro ganin Wani abokin aikin sane Wanda suke yin patrol da daddare a wajen garin Abuja yasa sukai kansa suna tambayarsa ko AIG ne ya kira?Musa ya girgixa kai jikinsa nayin sanyi, cikin sauri yay picking call din...



Daga Daya bangaren akace ASP Musa Kuna tare da AIG a gida ne?take gaban Musa ya fadi yace lpy meyasa kamin wannan tambayar ASP Yusuf? ASP Yusuf yace"wlh kaga muna cikin patrol ta wannan titin nan na mararraba muka ga wata mota ,kamar anyi accident ne,to shine muka karasa wurin muna xuwa mukaga kamar motar dasu IG da AIG suke hawace duk da motar da Kwan kwatse Amma mun leka ciki munga furkar Wanda ke cikin motar GSKY sai naga kamar fuskar AIG ce duk da ta B'aci da jini Amma ahaka na Gane kamar shine.take Musa ya saki wayar ya hau ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun da Kuma ya shiga uku,duk sukai kansa suna tambayarsa da lpy,Wani ne ya dauki wayar ya Kara akunnansa ya tambayi meke furuwa , ASP Yusuf ya Mai Mai ta masa, cikin rudewa yace "suna Ina? take suka fada musu,babu Bata lokaci suka shiga motocinsu suka nufi wurin,Saida suka girgixa ganin abinda yafi karfin ganin su, suka rasa ya zasuyi tabbas AIG ne, innalillahi wainna ilaihi rajiun meya faru dashi haka?waya kawo shi wurin nan yay Masa wannan kisan wulakancin innalillahi wainna ilaihi rajiun.sai ASP yusuf ne yay karfin halin Kiran Wani na kusa da IG Wanda agidan IG suke xama,ya fada masa akan ya fadawa IG halin da ake ciki, sannan ya qara Kiran Wani police Wanda ke gadin gidan minister tsaro akan ya fada masa .bayan ya sauke wayar ya koma suka tsai tsaya .suna nan wurin sama da mintuna talatin har sannan babu Wanda yaxo cikin muta nan da suka sa afadawa din,Dan Suma Basu ta'ba Shi ba zasu jira har sai an Basu umarni tukunna.



Wajen awa Daya saiga jiniyar motar jami'an tsaron ta karade hanyar,kafin kice me sun qaraso wajen,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login