Showing 168001 words to 171000 words out of 278032 words

Chapter 57 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1073

ta ansa musu a gadarance sannan ta kalli zaituna ta ce"ku girkawa SA'A abinci yanxu yanxu suka ansa mata da girmamawa sannan ta wuce sama ta koma dakin H???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ajiya SA'A, ta tarar Hajiya SA'A tana wanka har lokacin Bata fito ba.dan haka saita fito ta xauna falon Dake sama Dan jiran ta,ta dauko wayarta tana latsawa.......




07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y





*____JAMI'AR TSARO ____*



*___THE WOMEN POLICE ___*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES =؋?)=?1?*



*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



_______season two ep 6?? 9??



___________?&


AA Arab ne tsaye a department din da aka Saka 'yan ta'addar yaran goga harda shi kansa gogan gabadaya an Tara su cikin babban falon inda d'aku nan da aka tsare sun suke cikin sa,duk suna zazzau ne .Yana tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa Yana kallansu ,sanye yake cikin bakaken suits da suka amshi fatar jikinsa, sumar kansa Irin ta larabawa Tasha gyara sai sheki take, fuskar sa sanye yake da Wani bakin glass Wanda ya haska kyakkyawar fuskarsa, fuskar sa ba'a sake take ba sannan ba Kuma ahad'e take ba kawai dai xamu iya cewa tsaka tsakiya.gefensa hagu da dama CP ne da DCP da Suma suke tsaye cikin uniform dinsu yakasance sun sashi atsakiya, bayan ya gama kare musu kallo ya juya ya kalli ASP Shareef da ASP Anas Wanda suke daga bayansu atsaye,ganin kallan da AA Arab yay musu hakan yasa suka Gane me boss din nasu yake nufi .Shareef ne ya matso kusa ya tsaya gaban 'yan ta'addar nan sannan ya Bude Baki yace "idan akwai Wanda yake da mata acikin ku ya fada mana da Kuma address din gidan"ya fada Yana kallansu , sannan yay shuru Yana sauraran su......



Babu Wanda yay magana acikin su sai kallan junansu Kawai da suke suna sunne kai , Saida ya qara maimaita ta musu sannan few mutane daga cikinsu Wanda basu fi su uku ba suka daga hannu . Shareef ya dubi AA Arab, yaga AA Arab yay Masa alama da kai.sannan ya juya ya fuskancesu ya ce"ku taso"suka Mike daga xaunan da suke suka fito suka tsugunna daga gefe ya Kallesu ya ce "shikenan nan ku, suka ansa masa da "eh"wannan Karan ASP Anas ne ya matsa gurun sauran ya Kallesu fuska babu walwala ya ce " "Kowa ya wuce ya koma dakin da yake"babu musu suka mike kowa ya nufi inda yake,Saida ya tabbatar da sun shiga sannan yaje ya kukkulle duka dakunan kamar yadda suke ko da yaushe.Asp Shareef shiya karbi address din kowa ,Dan xuwa a taho da matan nasu kamar yadda his Excellency governor ya fada,sbd ya ce matan suna da hakkin su sani kafin ayanke musu hukunci.sai da AA Arab yaga komai yayi yadda yake bukata bayan sun Fadi address din, ASP Shareef ya mikawa AA Arab cikin girmamawa,AA Arab ya karba ya furta thanks a labbansa, sannan ya juya ya fita daga cikin department din CP da DCP suka mara masa baya har Kuma lokacin Bai nunawa CP yasan Komai na abinda ya aikata ba, kawai lokaci yake jira.ASP Shareef da ASP Anas su suka tusa 'yan ta'addar nan agaba suka shigar da kowanne inda yake sannan suka fito daga wurin suka bar police din da suke aiki awajen su Kuma suka koma office dinsu ....



AA Arab sun shigar da qarar kotu kamar yadda his Excellency governor ya fada ,ance nan da sati Daya mai xuwa ZA'A fara Shari'ar tasu harda case din su shafa ma .yanzu abu Daya yane xuwa biyu rage shine nafarko zaije gidansu ruky ko gobe ne wajen mamah da ita Kanta Rukayya akan maganar case din shafa dole Saida ita aciki domin ita tasan komai,Kuma duk Wani evidence dinsu ance Yana wurin ta da Kuma wurin barrister su wato barrister shamsu na na biyu Kuma zasuje suyi bincike aduka gidajan su Alhaji sunusi daga shi har babajo Ali Dan suyi bincike sosai akai .bayan azahar ya je asibitin da aka kwantar da shafa,yaje har office din doc Fatima tunda itace take kula da shafa ,file din ta komai ahannunta suke,police din da suke kula dasu shafa sune suka shiga har office din doc Fatima suka sanar da ita zuwan AA Arab ,cikin rawar jiki doc Fatima ta mike ta kalli police din ta ce "ASP meyasa baka ce ya shigo ba? please kace ya shigo ba damuwa,haka ya koma ya sanar wa da AA Arab cikin girmamawa.AA Arab ya jinjina kai ya qasara gaban office din ya tura kofar cikin nutsuwa ya shiga office din bakinsa dauke da sallama.doc Fatima ta mike daga xaunan da take ta sunkuyar da kai cikin girmamawa tana murmushi ta ce "welcome sir" AA Arab yace "thanks doc "ya fada Yana xaunawa kan kujerar Dake opposite din ta doc Fatima ya zauna itama ta zauna ,ta gaida shi ya ansa mata,kan ya ce cikin cool voice dinsa "doc yaushe kika cemin ma xa'a Yi aikin nan ?"doc Fatima fuskar ta da murmushi har lokacin ta ce "sir jibi ne in Sha Allah ZA'Ayi mata aikin "AA Arab ya jinjina kai kafin ya ce"Allah yasa adace" doc Fatima ta ansa da Ameen "AA Arab ya ce doc inason idan akwai Wani record da kukayi na wannan abinda Daya samu yarinyar nan,inaso ki bani duk report din arubuce sbd dashi zamu shiga kuto" doc Fatima ta ce "why not sir, babu komai bari na dubo Maka Allah yasa adace" AA Arab yace "Ameen "Asaman labbansa.....



Bayan Wani lokaci doc Fatima ta kawo masa report din ta ajiye masa agabansa cikin girmamawa ta ce "sir gashi" AA Arab ya dauka saida ya dudduba sannan ya kalleta yaga kallansa take ya dauke kansa yace "thanks alot doc "doc Fatima tace "never mind sir"ya mike ya ce bari na shiga dakin mu gaisa da maman ta"babu Wani Abu da kuke bukata koh? Doc Fatima ta ce "Babu komai an kunbiya komai sir "AA Arab ya jinjina kai kafin ya ce"ok" sai Kuma ya ce "bari naje doc" doc Fatima ta sunkuyar da kai cikin girmamawa ta ce "ok sir,Allah ya tsare " ya ansa mata da Ameen Asaman labbansa daga haka ya fita daga office din,doc Fatima ta bishi da kallo.bayan ya fito daga cikin office din,police din Dake tsaye bakin kofar suna monitoring dinsa suna ganin ya fito suka sunkuyar da kai qasa sannan suka take masa baya kowa da gun ahannunsa sai zare ido suke duk inda suka gitta daga nurses din har patients relatives din sai faman gaida AA Arab sukeyi,Yana ansa musu da kulawa da tambayar masu jiki.sun shiga dakin da aka kwantar da shafa ,bayan sun gaisa da babar shafa suka fito suka bar iya AA Arab aciki,ya Kalli baba lami Dake sunne kanta qasa ya ce "ya maijiki baaba?" baaba lami ta ce jiki da sauki ranka ya Dade " AA Arab ya jinjina kai ya ce"Allah ya sawake" yacigaba ya ce"ance jibi xa'a Yi aikin koh? Baba lami ta jinjina kai ta ce "eh haka suka fada yallabai" AA Arab ya ce "shikenan baba addu'a zaku dage da ita Allah yasa ayi aikin cikin nasara" baba lami ta ansa da Ameen thumma Ameen mungode sosai ranka ya Dade"AA Arab yace "Babu komai baba,"sannan ya ce "Babu dai abinda kuke bukata koh? baba lami ta ce "babu komai yallabai,wlh Babu abinda muka NEMA muka rasa komai ana mana mungode sosai Allah ya Saka da Alkhairi ya jikan iyaye idan Kuma suna raye Allah ya Kara musu lpy da Nisan kwana" AA Arab ya ansa da "Ameen baba" sai Kuma yace"bari muje Allah ya sawake"baba lami ta ce "Allah ya kiyaye yallabai mungode mungode,sai Kuma ta sunkuyar da kai qasa ta ce"yallabai "sai kuma tai shiru.AA Arab ya juyo ya ce "Kuna bukatar Wani abunne?baba lami tace "a'a naji ance ansamo su Hajiya Rukayya shine nakeso na ganta ko zanji Dadi"AA Arab yace "baba ki kwantar da hankalinki in Sha Allah zaki ganta" baba lami tai shiru sai Kuma tai saurin cewa "Amma tana lpy babu abinda ya sameta koh? AA Arab ya jinjina kai ya ce "eh Babu abinda ya sameta baba lpy lau take , Amma kinsan dole saita huta kafin ta fara fitowa aiki,nasan itama hankalinta Yana kanku,sbd haka karki damu xataxo nan Bada dadewa ba in Sha Allah" Baba lami ta ce"harnaji Dadi da Babu abinda ya sameta, Allah ya qara kiyayewa gaba " AA Arab ya ce "Ameen baba bari naje"daga haka ya nufi kofa,baba lami ta ce "mungode yallabai Allah ya kiyaye" ya ansa mata da Ameen sannan ya fita daga dakin.yana fita ya Tarar police din Suna daga bakin kofar suna jiransa,ya Kallesu yace"ku dinga kula sosai" "suka ansa masa cikin girmamawa,ya ce"bari naje"sukai saluting nasa sannan wasu suka rakashi har bakin motarsa suka Bude masa ya shiga sannan suka rufe sukai saluting nasa sannan suka tsaya ganin motar ta nufi gate din asibitin xata fita,saida sukaga tafiyar sa sannan suka koma ciki.....



___________?&


Washe gari da yamma wajen karfe biyar da mintuna, Hanan ce zaune bakin gadon Rukayya sai surutu take mata, Rukayya dai tana gaban mirror tana daure gashin ta da band Wanda ya Sha gyara sai sheki yake jelar gashin nan ta sauko qasa gashin sai reto yake agadon bayanta, Dan tun d'axu tai wankan xuwan Hanan ne yasa ta shiri rince ta tsaida ta take Tai mata xance, sanye take cikin riga da wando, rigar maidan budewa ce daga qasa sai Wandon jikinta Daya kasance jeans blue Wanda ya Dan kama ta kad'an ,tayi kyau sosai ba kad'an ba kamar wata yar turawa, ta dauki turarukan ta masu dadin kamshi ta feshe jikinta dasu .bayan ta gama ta dawo kusa da Hanan ta zauna wacce ke kallan ta Baki bude.ruky ta kad'a hannun ta a idon Hanan ta ce "rufe bakin" ta fada tana dariya, Hanan tai murmushi ta ce aidole in saki Baki da hanci Ina kallanki Kinga yadda kikai kyau kamar wata 'yar turawa ,wlh ruky komai naki me kyau ne sis Kinga yadda gashin nan yay Kyau" ta fada tana shafo gashin kafin tace"yaushe aka wanko wannan gashin kinsan Allah bandauka gashin nan naki xai dawo har haka ba duba da yadda yay bututu lokacin da aka dauko ki.ta fada tana kallan Ruky...



Rukayya ta tabe Baki tace" jiya anty mufeeda ta sani agaba Saida muka fita ta kaini saloon aka wanke shi"Hanan ta ce "anty mufeeda ta kyauta wlh,Kuma bakiga yadda gashin nan ya dawo hayyacin Saba kamar yadda kema kika fara dawowa hayyacinki ta fada tana dariya kasa kasa.ruky ta d'akawa Hanan *duka* acinyarta Hanan ta dafe wurin ta ce "och wlh saina rama" ta fada tana kawowa ruky hannu,ruky tai saurin matsawa baya ta ce "wlh Sadai ki rame" ta fada tana dariya ganin yadda Hanan tai da fuska kamar xata saki Kuka Dan harga Allah taji zafin dukan nan da ruky tai mata ba kad'an ba.Acan falor kuwa AA Arab ne ya shigo tun dazu duk suna falon gabadayansu harda su ya Tahir Wanda Bai tafi ba sai xuwa gobe ,bayan ya fadawa mamah ZA'A shiga kotu nan da sati Daya, sannan idan suna so Abi musu hakkinsu akan abinda Alhaji sunusi yayi musu to suyi magana.mamah ta sauke numfashi kan ta ce "Ahmad ,sunusi dan ta cuta ya cucemu Kuma Babu Wanda zai iya kwato mana hakkinmu sai Allah, nidai na barshi da Allah shine kadai xai iya Saka mana, aduk abubuwan da yay mana ,idan nace xamu bi hakkin mu baxamu taba hucewa ba tunda abinda da yay mana baxai taba goguwa azukatan mu ba, kaga idan muka barshi ma da iya hakkin mutane da yay ta xalinta wlh ya isheshi.da sauri ya hanaf ya Kalli mamah Jin abinda ta ce Dan Bai taba tunanin xata ce haka ba ya ce "wai mamah kina nufin mu kyaleshi kenan ya ci bulus duk wannan xalincin da yay mana ,ya tahir ya ce "ya isa hanaf hakan mamah ta kashe magana Kuma Hakan data fada shine dai dai kayi hkr tunda dai na tabbatar tunda gomnati ta shiga wannan case din kasan uncle sunusi saidai ya qarasa shekarun da suka rage masa agidan yari " ya hanaf ba haka yaso ba Amma yaja bakinsa yay shiru.shidai AA Arab Yana jinsu Amma yay shiru, mamah ta kalli AA Arab ta ce "Ahmad mudai munbarshi da Allah Dan shi ne kawai zai isar mana" AA Arab ya jinjina kai ya ce"shikenan mamah Babu komai, Kuma kamar yadda kika fada honorable sunusi shida mutanan da muka kama baxa su taba tsira ba dole sai doka tayi aiki akansu".mamah ta jinjina kai anty mufeeda tace"Allah yasa adace "suka ansa da Ameen.mamah ta dubi anty mufeeda tace"mufeeda kira su Rukayya suxo su gaisa da Ahmad" Babu musu anty mufeeda ta mike ta haura sama xuwa dakin Rukayya,ta tarar sai surutu suke itada da Hanan ,anty mufeeda ta Kallesu ta ce "ku taso ku gaisa da boss dinku"suka kalli juna alamar Mamaki Sai Kuma Hanan ta ce"to anty" anty mufeeda ta rufo musu kofar ta sauka qasa ....


Hanan ta dubi ruky ta ce "ke taso AA Arab ne yazo" Rukayya ta yamutsa fuska ta ce "Kuma shine sai ance muxo mu gaishe shi,"Hanan ta ce"lallai ma ruky wato kin samu kanki dole kice haka ,dama haryanxu kina nan da halinki a kan AA Arab?na dauka ai kindai na Jin haushin sa"ta fada tana kallan Ruky.Ruky ta harari Hanan tace sai dai abinda yafi Ina Jin haushin sa Ina ruwana dashi, miye had'ina dashi dazan ji haushin sa" Hanan tai dariya sai Kuma ta ce "yo Abu a duhu nidai ya Ahmad bansan Mai yay miki ba" ruky ta rike hab'a Jin kalan dangi agun Hanan wai ya Ahmad, ruky ta ce"oh harda su Yaya gsky hanan kin iya shish shigi" hanan ta ce "Babu Wani shish shigi ai ya can canci haka ne,kema Kuma kin sani sai dai kik'i Allah ai wlh kema ko Baki xo kin gaida shi Dan komai ba xaki gaida shi Dan kubutoki dayay daga Hannun uncle sunusi" ruky ta ce "oh Gori kike min kenan?" To shima Bai min Gori ballan tana wata ke" Hanan ta ce "babu Wani Gori sai gsky wlh ki taso tun kafin anty mufeeda ta dawo ta samemu" ruky ta mike ta xura hijab dinta dogo har qara blue bakaramin kyau yayi mata ba, Hanan ta dauki abayar ta ta xura sannan ta kamo hannun ruky tai qasa da murya cikin lallashi Hanan ta ce "Dan Allah idan mukaje kar kiyi wannan shirun naki,ki saki jiki ki gaishe sa wlh mutu_minnan he is very nice bashida wata matsala" Ruky ta harari Hanan ta ce "nifa ban iya Irin shish shigin kiba Hanan" Hanan ta harareta ta ce "sai dai abinda yafi shish shigi wlh Allah da GSK nake Dan Allah ruky ki saki jikinki ki gaishe sa karki bani kunya"ruky ta ce "sai Wani Fadi kike na saki jikina to dole saina saki jikina kamar Wani muharramina ke ni wlh duk abinda naga dama shi xanyi "Hanan ta Marai raice "tace Dan Allah ruky ko godiya to kiyi masa "ruky tace "duk godiyar dana masa a asibiti Bata isa ba saina qara wata ?Hanan ta ce "Amma ai ita godiya Bata yawa koh?ruky tace "ke Dan Allah kyaleni"Hanan ta jawo mata hijab tace"wlh zan fadawa ya Tahir na rantse da Allah idan Baki yiba"ruky tai murmushin da Bata shiryaba ta ce "toh naji Amma bawai Dan zaki fadawa ya Tahir ba ,sai Dan kawai ni nai ra'ayi" hanan ta ce "naji" ruky ta hankada ta ta ce "Yi gaba kanwar AA Arab" ta fada tana dariya,Hanan ta juyo ta ce wlh Allah kin Raina ni ruky Amma zan rama ne daga haka tai gaba ruky tabi bayanta tana murmushi har suka fita daga dakin....


Suna saukawa daga stairs, Hanan ce agaba ruky tana bayan ta Basu tarar da kowa a falon ba, AA Arab yaji qarar food step ana saukowa Amma bai dago da kansa ba,bayan sun sauka Hanan tai sallama da Dan karfi ruky ce tai qasa qasa,Hanan tana murmushi ta xauna kujerar Dake pessing din ta AA Arab Ruky akusa da ita har lokacin kanta Yana qasa, AA Arab ya dago da kansa daga latsa wayarsa da yake ya ansa musu Yana kallan hanan,wacce ke kallansa Bakin ta awashe,Hanan tace"Ina wuni sir" AA Arab ya Maida mata da Martanin murmushin data masa yace" lpy lau Hanan kina nan kenan?Hanan tace"eh Sir "kanta Yana qasa, ganin haka yasa ruky ta ce "Ina yini batareda ta kalleshi ba Kuma har lokacin kanta Yana qasa,Shima AA Arab ya ansa mata batareda ya kalleta ba,saiya Maida hankalinsa kan Hanan suna Dan taba hira sama sama ,bayan Wani lokaci ya Dan dubi Ruky wacce kanta ke qasa Bata Saka musu Baki ba tana wasa da yatsun hannun ta,ya ce "ASP" ruky tai shiru Bata dago ba Dan har ga Allah Batasan da ita yake ba,Hanan ta xungure ta Hakan yasa ta dago ta harari Hanan sai Kuma ta Kalli AA Arab Karo na farko da dara daran idanuwanta tana kallan sa, ya ce tambaya zan miki akan case da kika shiga har kika jefa kanki cikin matsala ya cigaba da fadin inaso duk Wani bayanai da hujjojin da kuke dasu ki hadasu waje Daya zan karba,xamu fara Shari'ar ne da xarar mungama tasu honorable ko Kuma kafin afara tasu nan da sati Daya in Sha Allah....


Ruky ta jinjina masa kai ta ce "ok wasu suna guna Wasu Kuma suna hannan barrister mu da muka dauka Amma zan sa Hanan tai masa magana tunda ni babu waya ahannu na" AA Arab ya jinjina kai yace"badamuwa nan da 2 to 3 days nake so komai ya xama ready idan kun hada sai a sanar dani Kuma inason ganin barrister naku" Hanan ta ce "in Sha Allah sir " Ruky sai hararar Hanan take qasa qasa yadda ta xaqe sai Wani shish shigema


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login