Showing 75001 words to 78000 words out of 278032 words

Chapter 26 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1053

duk abinda ke faruwa, Amma Kuma Bata ganta a online ba,gashi bataso ta kirata awaya agaban mamah dole sai dai idan ta Shiga daki ta kirata,


Baba hasiya Kuma tana dakinta, mamah ta dago daga kallan labaran da take a TV tace Rukayya, ruky ta aje wayar Hannunta ta dubi mamah tace na'am mamah,mamah tace tunda hasiya tana daki jeki dakin cikin store ki dubo min ko akwai sauran garin buhun semon Dan gobe tuwo nake San hasiya tai mana, ruky ta aje wayarta tace toh ta nufi hanyar kitchen hartaje bakin kofar shiga kitchen din sai mamah tai saurin tunawa da ashefa akwatunan da aka kawo nasa Ranar ta,da ita da lateef ta manta fa Ashe tasa akai mata dakin store din, Dan kwata kwata ta manta da ankawo gashi Kuma har lokacin ruky Batasan cewa ankawo kayan ba,Dan kokadan mamah Babu Wanda ta fadawa har anty mufeeda,Dan Bata dauki abin serious ba,dan wlh taiwa Alhaji sunusi uxuri, tace dawo na manta,bari hasiya ta fito saita dubo, ruky ta Dan Bata fuska tace mamah me yasa ki bari mana naje na dubamana,Mamah tace a'a dawo kawai na hutar Dake bari hasiya idan ta fito saita dubo ,kedin na hutar Dake, ruky ta dawo ta dauki wayarta taiwa mamah sallama ta haura sama, mamah ta ansa mata da Allah ya tashemu lpy,ta jadda da mata datai addu'a, ruky ta ansa to ta haye sama,...



Ruky ce a dakinta kwance wajen karfe 9:30 na dare,ta lullube jikinta daga cibiyarta xuwa kafafuwanta da duvet,tana waya da Hanan, gabadaya damuwa ta fito qarara a fuskarta ta,tana fadawa Hanan cewa lateef ne me laifin , harxuwa yadda suka kwashe da Alhaji sunusi,da Kuma lateef din kansa dasu CP, Hanan ta xaro ido waje bayanta gama Jin komai, kamar ruky tana gabanta tace innalillahi wainna ilaihi rajiun, Ruky yanxu Allah da GSK lateef ne,shiya aikatama wannan marainiyar Allah wannan danyan aikin ,tab dijan,ni wlh nama rasa abun fada,Kuma ke yanxu cigaba da case din xakiyi ko Kuma hkr xakiyi, tunda Kinga lateef Dan uwanki ne,.....



Ruky ta Kara gyra kwanciyar ta,tace a'a Dan ubana ba Dan uwanaba, sannan tace hmm Hanan kenan ke yanxu kina tunanin yadda na faro case din nan xan barshi ne,wlh dole dole sai an hukuntashi,Hanan tace cikin xolaya Amma ruky Ina lateef shi xaki Aura, ruky tace wlh xan dura miki ashar Hanan ,ke yanxu ko mazan duniya sunkare kina ganin xan auri lateef ne,Hanan tace Yi hkr mu dawo maganar serious, Amma ruky ai kinsan dai lateef Dan uwankine, Taya ZA'Ayi kice zaki dauki mataki akansa,Kuma kinsan halin ubansa sarai,bawai Baki saniba, sannan kinsan ko mamah wlh baxata taba yadda kice xaki shiga wannan case dinba kijawa kanki matsala ba,nidai yanxu shawarar da xan Baki itace, ki hkr da case din nan,ki Basu hkr ki fada musu illar abinda xaki jawa kanki idan har Kika xurfafa da yawa,wlh ko yanxu kika tsaya a wannan case din wlh kinyi musu qoqari,tunda har kikkai wannan matakin ,kawai gara kice su barwa Allah shi xai saka musu tunda yanxu wata sakayyar ma tun a duniya akeyinta,.....


Ruky ta gallawa wayar Harar kamar wacce Hanan dince a gabanta, tareda jan dogon tsaki,tace Hanan nifa bawai kiranki nai na fada miki wannan maganar bawai danki bani shawara na hkr da case dinba a'a na kiraki ne na fada miki dan kece kikace akaiwa DCP case din Kuma gashi yadda Abu ya kasance,Kuma da kike cewa na hakr na Basu hkr,a hkr da case din ashema,ni ba JAMI'AR TSARAN bace, Ashema ni rantsuwar danai ta Banxa ce,wlh Hanan idan har Kinga na bar case din nan,to wlh saidai mutuwa,nai Amma wlh nidai Ina raye sai inda karfina ya qare,akan case din nan, Kuma da kike cewa idan Mamah ta sani baxata barni ba saidai idan kece zaki fada mata,ko Kuma shi uncle sunusi, shiyasa tun farko ban bari tasan xancen ba,Kuma in Sha Allah harna gama case din nan baxata sani ba, saidai idan shi uncle sunusin ne xai fada mata,....



Sbd haka Hanan idan har baxa ki bani shawarar yadda xanyi ba, harna cika burina ba,to kiyi shiru ki xuba min ido kawai nai aikina,Hanan ko ganin Ruky ta dauki zafi yasa ta sauke numfashi tace to Yi hkr, me kikeso awajena,wacce shawarar kikeso na Baki, ruky ta sauko daga hawan da tai tace, Hanan so nake kawai nayi qarar su uncle sunusi,Hanan ta xaro ido waje tace what ruky qara Kuma,haba ruky ya xa'ayi kice xakiyi kararsu,karki manta fa akwai Alaka Mai qarfi atsakanin kufa,ruky tace wlh Babu ruwana da wata Alaka tunda har Nima suka manta da alakar Dake tsakaninmu suke Neman su tauye gsky to Nima haka xan manta da wata Alaka Dake tsakaninmu,nai aikina yadda ya kamata...



Sbd haka kawai ki xuvamun ido ki barni kawai nai aikina, Hanan tace Amma ruky, ruky ta katseta tace idan har ba toh zakice min ba to Dan Allah karki Kara cewa komai,Dan wlh Allah Hanan sainayi qararsu,Hanan tace Amma ruky dandai kawai kindage ne, Amma da hkr kikai wlh banga anfanin haka ba, Ruky tace Hanan wlh xan miki Rashin mutunci, Hanan tace nayi shiru basai anje ga haka ba, Amma ya kamata ki fadawa mamah, halin da ake ciki, Ruky tace Hanan baxan fadawa mamah ba,indai na fada mata wlh baxata taba yadda ba,Hanan kema Dan Allah karki fada mata,Kinga shiyasa tun farko ma,ban fadawa Shareef ba,sbd nasan halin surutunsa,da kaikayin bakinsa,tsaf xai kwashe ya fadawa mamah ita Kuma ta hanani,Niko wlh ban shirya Hakanba,Dan wlh sai sun san ni suka tabo ,so nake na nuna musu cewa ba kowa ake tabowa axauna lpy ba,Kuma su tabbatar da alwashin Dana dauka akansu,....



Hanan ta sauke numfashi tace bakya Jin mgn Ruky, ruky tace eh din baxan jiba,Hanan tace ga shawara , ruky ta yamutsa fuska tace wace Irin shawara,Hanan tace,da kinjira AA Arab idan ya fara fitowa aiki dan Nanda next week xai fara fitowa aiki,saimu kai masa, report din kawai ,wlh na tabbatar shi idan yaji xai dauki abin da muhimmanci musamman ma idan yaje Yaga yarinyar, ruky ta ya Mutsa fuska tace ke,rufamin asiri ,ban iya wannan shishshigin da gangancin Irin nakiba,haka kawai bansan mutum ba,bansan halinsa ba,kawai daga ji ana fada a gari cewa mutum kirkine kuma kawai saina dauki case na kai masa,wlh baxan yiba,....


Hanan tace oh hakama zakice wato ke baki yarda mutumin nan mutumin kirki bane kenan,wai baki Kalli vedios dinsa na dawowarsa kasar nan bane ba, Baki ga yadda ya dinga tranding bane a garinnan ba ko nace kasar ma Baki daya, bakiga yadda ake ta posting pictures dinsa a social media ba, status kuwa wlh duk na Wanda kika Buda dashi xaki fada cin karo,.....



Da ace ba mutumin kirki bane, Ina xakiga Irin dunbin mutanan da sukaje tarbarsa airport ba,wlh daba mutumin kirki bane,wlh Babu Wanda xai damu dashi Kuma kema nasan kingani kawai ,Rashin mutunci ne Irin naki, narasa Mai yasa AA Arab Bai mikiba kwata kwata arayuwa ba, Ruky tace a fusace,Dan Allah ya isa eh Bai min ba Kuma bazai taba yimin ba,waini Dan Allah wannan AA Arab din,Dan uwankine da Abu kadan komai saikin sashi a xancen ki,daga Jin labarinsa shikenan kibi kidaurawa kanki Damuwa,to tunda ke ya miki aini ba lallai saiyamin ba,ba AA Arab ba,idanma BB Arab ne ke kikajiyo,na rokeki daga yau karki qara kawomin xancen sa,idan muna magana Dan Allah,.....


Hanan tai murmushi tace,wlh duk ranar Daya sanni wlh saina fada masa yadda kika bi kika tsaneshi,ai wlh dole ma,na dage kodan AA Arab ya San ni ,Kuma kinsan idan ya sanni kema kinsan dole saiya sanki,wlh ki kuka da kanki duk ranar Daya San bakya qaunarsa, Ruky tai murmushin da Bata shiryaba tace au Allah Hanan uwar shishshigi, baxanyi mamaki ba,idan ya sanki domin kedin akwai shishshigi Dan tun bayauba na sanki da shishshigi ba, Dan saidai na bawa wasu lvr,Hanan tai murmushi tace wlh kijira, ruky tace ke sai anjima, kanwar AA Arab ,Dan saidai kanwar tasa yadda kike ji da mutumin nan, ke ke harma kinfi Kannan nasa ji dashi indai harYana dasu ,Allah yasa yasan kinayi, Hanan tace in Sha Allah wlh saiya sani, ruky tace ke sai anjima marar aikinyi daga haka ta kashe wayar ta,.a bangaren Hanan ko murmushin itama tai tana cin alwashin in Sha Allah sai AA Arab ya Santa saita bawa ruky mamaki....



A bangaren Ruky kuwa Bayan ta sauke wayar Khalil ta kira ta shaida masa duk Wani kudurin da take dashi akansu Alhaji sunusi,daga karshe tace Khalil kararsu xan kai kotu , Khalil yace ranki dade da kinyi hkr tunda Abin na gidane, Kinga Dan uwane kar ayi abinda xa'a Bata xumunci, ruky tace Khalil idan har kaima baxaka goyon bayaba,to ka kyaleni,ni xanyi handling kayana,idan har muna biyewa cewa Yan uwan mu suyi Laifi munsan su suka aikata din Kiri Kiri mu tauye gsky,Amma sbd San xuciya iran tamu ace baza'a mikasu ga inda ya dace su dauki hukuncin abinda suka aikataba, shikenan Dan akwai Alaka a tsakanin mu,sai muce baxamu, dauki mataki akaiva ko,....



Idan muna biyewa San xuciyarmu Taya xamuyi aiki tukuru,Taya xamu taimakawa wadanda aka xalinta,Taya aikin xalinci Irin wannan baxai ke yawaita a duniya ba,idan har muna duba Alaka,Taya xamuga albarka a cikin aiyukanmu,Taya xamu samu cigaba,arayuwarmu,Taya Allah xai barmu,bayan munyi rantsuwa da ALKawarin cewa,zamu aiki bisa gsky da Amana, aikinmu baxai taba yin kyau da cikaba ba har sai mundauki kowa equal ne,a wurin mu, ma'ana kowa daya muka daukeshi ,ko iyayen Kane sukai badai dai ba,idan hukunci ya biyo ta kansu,ai musu tunda ai ba'a wareba ance ga Wanda xa'a yiwa ba,idan ya aikata badai dai ba,ga Kuma Wanda baxa'a yiwaba,....


Amma idan ka dauka duk dayane,babu Dan masu kudi,babu Dan masu siyasa,babu dan masu sarauta, babu Dan masu Mulki,babu Dan talaka,kowa Idan ya aikata,barna Kuma hukunci ya biyo ta kansa, ayimasa dai dai da abinda ya aikata,idan muka dauka hakane to shine xamufi daukar aiyukanmu da muhimmanci,Idan mukai aka xalinci xai ragu acikin al'umma,Kuma Suma masu aikata laufukan su shiga hankalinsu,.....


Khalil ya sauke numfashi yace na yarda da duk kan Wani bayanin ki,ranki dade,wato ranki dade kinada Nisan tunani, wannan abinda kikai ya nusar Dani ya qara qaramin kwarin gwaiwar Nima ayi wannan taimakon Dani ,ranki dade babu komai Allah Yana tareda mu in Sha Allah Nima sai inda karfina ya qare,akan wannan case,din ,da ace haka shuwaga banin suke da Nisan tunanin Irin naki ,wlh da anxauna lpy a qasar nan, Allah yasa mudace, Ruky tai murmushi tace, Ameen Khalil nagode sosai da fahimta ta dakai,yace babu komai ranki dade,ya qara da cewa aduk lokacin da nake tareda ke ranki dade wlh Babu abinda yake sani nutsuwa sama da yadda nake qaruwa Dake,ga Kuma kyawawan halayanki,Ruky tai murmushi harda rufe Baki da Hannunta tace ba kai kadai ba Khalil Nima Ina qaruwa da kai, yace a'a ranki dade ni nafi karuwa sosai, ruky tace nidai bansan musu yanxu dare yayi bari na kwanta, Khalil yay qasa da murya yace Allah ya tashe mu lpy ranki dade,ki Kwanta cikin amincin ubangiji, ruky tace nagode sosai kaima haka,yace ranki dade yaushe xaki shigar da qarar tace in Sha Allah ko daga nan xuwa govene ko jibi,yace ok Allah ya kaimu,daga haka sukai sallama ruky ta kashe wayar ta tana lumshe ido tareda murmushi kafin daga bisani ta qara addu'ar bacci, sannan ta gyara kwanciyar ta,ta kwanta,.....



____________?&


Hajiya SA'A ce xaune tana kallan lateef Wanda ya mike tsaye, Alhaji sunusi Kuma Yana kan kujera,shima ya xubawa lateef din ido Yana kallonsa,ganin yadda ya hade Rai yana muxurai, Hajiya SA'A tace wato mu bamu isa mun fada Maka magana kijiba kenan,yanxu inbanda Rashin xuciya Irin taka lateef ,yarinyar tai Maka wannan,Rashin mutuncin ,ta wulakanta ka, a baynar Jama'a,Amma baka Gani ba kake ikirarin itace wacce zaka aura, lateef ya Kalli Hajiya SA'A wacce ta haderai bilhakki tana Mai fada,yace wlh nidai mom ita nake so Kuma wlh ita xan aura,ai auran nata da biyu xanyi so nake idan na Aureta na rama duk wannan Rashin mutuncin datai min ke atunaninki ,zan hkr ne da wannan wulakancin data min,da kaskantar Dani datai a idan Jama'a,.....


Hajiya SA'A tace aiba dole saita wannan hanyar madai zaka rama ba, Baga hanyoyi da yawaba,dole saita hanyar auranta xaka rama to wlh nidai baxan taba yadda ka auri wannan yarinyar marar mutunci ba,idan kai bakasan ciwon kankaba kaji xafin abinda tai Maka ba,to ni uwar data haifeka na sani,Kuma naji xafin abinda tai Maka,ta dubi Alhaji sunusi tace Alhaji bakace komai ba,....


Alhaji sunusi ya Kalli Hajiya SA'A,sai Kuma ya Kalli lateef Wanda ya qara tsuke fuska, yana hura hanci,yace lateef daka hkr da auran yarinyar nan,da ka barni nida kaina na dauki matakin abinda tai mana,Dan ba iya kai ta wulakanta ba,hardani,Dan wlh dakasan Irin hukuncin Dana yanke xan mata da bakace zaka auretava, Kuma wlh yanxuma ba hkr nai ba,wlh yarinyar nan saina wulakanta rayuwar ta, saitasan ni da kai take kokarin kunya tawa,sbd haka ka kyaleni da ita, ka bari mumynka ta zabo Maka matar AURE cikin yayan manya Wanda suka dace da kai Amma ba wannan yarinyar marar mutunci ba,Nima wlh dama ba San auran nan nakeba Dan dai kawai ka dagene,....


Hajiya SA'A ta karbe da cewa sosai ma, Alhaji ga yayan manya irin yayan kawayena dasuke son hada xuri'a damu,da wlh ko Ayanxu kakeso wlh xan samo Maka matar AURE,wacce ma tafi ita Rukayyan kyau,ni wlh banga abinda ka gani jikin yarinyar nan ba daka dage ita kakeso,Lateef ya katse ta yace mom ni wlh Rukayya nakeso,Kuma ita xan aura,svd haka karki qara kawomin xancen wasu yan mata,ya Kalli Alhaji sunusi yace Dady Dan Allah karka cutar da Ruky ka bari ni xan dauki mataki da kaina,idan na Aureta ai xance ya kare koh,sai yadda nai da ita,sbd haka Dady Dan Allah jibin ka AURAmin Ruky,dan Allah karka fasa,wlh idan baka AURAmin Ruky ba,wlh xan iya mutuwa, Alhaji sunusi yace cikin rarrashi shikenan kaje Allah ya kaimu jibin na yadda ka auretan,....


Lateef yace Dan Allah Dady karka mata komai Alhaji sunusi ya daga masa hannu yace naji, lateef ya fita daga falon cikin farin cikin xa'a aura masa Ruky,gefe Daya Kuma yana tana tunanin yadda xai rama abinda tai masa,bayan fitar lateef Hajiya SA'A ta dubi Alhaji sunusi cikin damuwa tace haba Alhaji Taya ZA'Ayi ka biyewa, lateef, Alhaji sunusi shima cikin bacin Rai yace kina ganin furucin da yay fa,wai xai kashe kansa Kuma kinsan xai aikata, Hajiya SA'A tace ba barazana yake ba,ai da hankalinsa,ba xai taba cutar da kansa ba,...


Alhaji sunusi yace sai kace bakisan halin Lateef ba, ko kin manta yadda yake masifar San yarinyar nan,idan Ban aura masa itaba,kina tunanin bazai kashe kannasa bane,to ni banshirya rasa Dana ba,farin cikin sa shine nawa,hakama bakin cikinsa shine nawa, idan ya aureta ma ai shine zaifi ma dadin rama abinda tai masan,daga haka ya shige dakinsa, Hajiya SA'A Kuma ta dafe kanta Dan wlh ba haka taso ba,.....





*Masu San a tallata musu hajarsu xasu iya Yin magana ta wannan number Dake qasa*





07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE ____*




*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1? QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA) =?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



_____season one ep 3?? 3??



__________ ?&


A bangaren su shafa kuwa a asibitin yau results dinta zai fito dan haka,tun karfe 11:00am Ruky ta baro office, Yanxu haka ma suna tareda Khalil,a department din,inda babu dadewa wata nurse ta fito daga office din Dake passing dinsu,na doc Fatima ta qaraso xuwa wajensu, ta ce ASP is u koh,ta fada tana murmushi danta Gane ruky, itama ruky murmushin ta sakar mata tace yeah,nurse din tace ok ,doc Fatima tana Kiran ki, ruky ta ansa mata da okay, nurse din ta bar wajen, ita Kuma Ruky ta shiga ciki,ta bar Khalil tsaye awurin Yana jiranta,....


Bayan Ruky ta shiga ciki,ta tadda doc Fatima tana xaune kan kujerarta me juyawa,inda tai Baya ta jingina jikin kujerar, bayan ruky ta shigo da sallama abakinta, doc Fatima ta dago daga kishingidan da take,tai murmushi tareda ansawa Ruky sallamar da dai,doc Fatima ta nunawa Ruky wurin xama babu Bata lokaci ruky ta zauna har lokacin murmushi ne a fuskarta,bayan sun gaisa cikin girmamawa da Dan sabon Daya shiga tsakaninsu,na wannan yawan xuwan asibitin da ruky take,doc Fatima ta gyara xaman glass din fuskar ta,ta dubi Ruky tace ASP ga results dai ya fito ta fada tana turawa ruky takardun,....



Ruky tai shiru tana kallan takardun gabanta,sai Kuma ta dago tana sauraran doc Fatima,doc Fatima ta cigaba da fadin,a gsky results din Baiyi kyau kamar yadda muke tunani ba, Dan dole sai an mata aiki nan da two months in Sha Allah,Dan har yanxu dole saidai mucigaba da dorata akan drugs din da muke Bata tun farko,saidai tunda ana samun Dan cigaba ,ba wata matsala bace in har an cigaba da Bata daga nan har lokacin aikin yayi,Dan aikinma ba'a nan xa'ayi ba,a Lagos Muke tunanin xa'ayi,idan Kuma munsamu yadda Mukeso kila doctors din da xasuyi aikin su iya xuwa Amma Bai xama lallai ba,so please ku kwantar da hankalinku in Sha Allah everything will be okay, ta qarasa fada tana kallan Ruky wacce ke kallan ta har lokacin,....


Ruky ta Sauke numfashi tace doc mungode, Allah ya Saka da Alkhairi da kokarin da kuke mana, Amma doc naji kina results din Bai Bada yadda ake soba,kamar ya bangane ba,doc Fatima tai murmushi tace kwantar da hankalinki ASP Ina nufin da ace results din ya nuna cleared da babu Wani xancen aiki,da xa'ayi mata ,Dan wlh wannan abun,da akaiwa yarinyar nan, yariga da yayi Muni da yawa,wata cutace aka Saka mata wacce tafi karfin kwayoyin hatittar da suke Bata kariya ajikinta,Wanda sunriga da sun mata illar da Saidai muce Allah yasa idan anyi aikinnan ta warke daga wannan cutar,domin cutar ba'a samunta ako Ina sai ajikin dabbobi, dabbobin ma, ajikin dogs akesamun su ,more especially Irin dogs din turawan nan ,na Nigeria ma ana samu Amma sunfi yawaita ana turawa,sune suke dauke da cutar,a wannan xamanin a yanxu daga Maza har mata suna amfani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login