Showing 18001 words to 21000 words out of 278032 words

Chapter 7 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1080

,baba hasiya tace to shikenan uwata saida safe,tace yauwa ,daga haka ta rufe kofar ta koma ,tana tunanin kila ya lateef ya shigone lokacin su mamah suna daki suna sallahn magrib,Kuma kila ya fitane lokacin sunshiga sallan isha'i a daki,ta kwanta ta lullaba ta duvet harkanta tai addu'ar bacci tana fatan bacci ya dauke ta ,gefe Daya Kuma tana tunanin yadda zata fara bincikenta kan case din shafa,...


*________ZARI'A_________*
Ummah tana dakin baba ta kawo masa abincin karyawa wajen karfe Goma da rabi, Nana Kuma ta tafi makaranta , zaliha Kuma tana bakin kofar dakinsu tana kwalliya, ,baba asabe Kuma tana yiwa zaliha abincin siyarwa,Dan tace ita Sana'a shine tushen arxikinta ,'ya'yanta data aurar ma duk babu wacce tai Boko,ko islamiya ma ba sosai suke xuwa ba, ita koh umma Ameenah itace yarta ta fari sai Kuma Nana Kuma gabadayansu suna xuwa makaranta, daga islamiya har Boko Dan Ameenah saida ta gama secondary ma har wani Mai Santa da aure ya fito mutumin kirki ga aikinsa da sana'ar sa ,har xa'a fara xancen Saka ranar auransu Amma baba asabe ta shiga ta fita ta hana malam Auwalu aurawa Ameenah shi sbd taga xataji Dadi tafiso kamar yadda yayanta suke shan wahala agidan AURANSU itama ummah kada yayan ta suji Dadi,bokonma Dan day kawai malam Auwalu Bai biye mata bane , Amma da Tasha xugashi ya hana su Ameenah xuwa duk da yanxu burin ta ya cika na ganin Ameenah agidan Kabiru da yadda yake gasata,wlh kullum idan ta tuna haka acikin farin ciki take,...


Dan shi malam Auwalu yace ra'ayin kowa ne baxai hanasuva itama idan tanaso tabar yayanta suna xuwa,tace ita Allah ya sawake Bai Bata kudi ba sannan ya hanata ta nema ita yayanta sune jarinta, yanxu ma ummah ce ta fito daga dakin malam Auwalu,Aiko saita fara habaicinnata na Sabo Wanda ita kan ummah harma ta Saba dashi,Dan Bata kula ta,sai Kuma ta fara wakar ta sana'a ,kai kufara Sana'a mata ,kai ku fara Sana'a mata,wacce Bata Sana'a aura ce oh lale lale mataba Dake xinaru,tanayi tana nuna ummah da Baki da hannu itako ummah saitai kamar Bata gantaba,Dan yanxu tayiwa baba asabe uxuri kawai, Dan kallan Sha Sha Sha take mata,haka ta shige dakin ta, zaliha ta kama dariya qasa qasa,tace Amma wlh baaba bakida dama, asabe ta tabe Baki tace yo inba Rashin xuciya ba, kana da 'ya'ya Amma ace wai baxakamoresuba,saidai kawai sudinga xuwa makarantar Bokon Banxa da wofi,

Zaliha tai shewa tace hmm baaba kenan,kedai bari yan wahala ba kuma ayi Bokon ma Amma babu abinda yake tsinana musu nidama shiyasa ma dana fara xuwa naji wahala,Kuma naga kema kince indai na xuwa yasa ni dainawa babu musu,muyi sana'ar mu ,muci musha mukoshi ta qarasa fada tana aje soson powder din cikin kayan kwalliya, tana mikewa tace baaba in kingama bari nazo na dauka kada afara ciki tashannan banjeba,aita jirana babu Dadi,baaba asabe tace ai na gama Mai kashin arxiki,daga haka ta mike dama ta gama hada komai, zakiya ta fito me napep din dayake kai kaita Tasha ya iso Yana waje,tai masa magana ya shigo ya dauka ya shigar napep su tafi ,Aiko haka akayi bayan ya gama shigarwa,haka zaliha ta fito cikin caba ado fuskar nan Tasha Jan Baki har wani shining take,ga giran nan Tasha bakar jagira,ga powder har tayi yawa fuskannan Tai fururu, irindai Yan tallan nan na qauye wadanda basa Boko bari arabi , haka taiwa baba asabe sallama tana taunar cingum,baba asabe ta daga murya yadda ummah xataji tace Allah ya kawo kasuwa Mai kashin arxiki, wacce Bata gaji tsiya ba,Bata Kuma gaji mutuwar xuciya ba,ummah tai murmushi tana girgixa kai Jin yadda baba asabe take wa yarta, wai duk Dan taji, ita yanxu ta Ameenah ma take wlh kawai jitai kamar Ameenah tana cikin Wani muwuyacin Hali Dan jiya har mafarkinta tai cikin mugun yanayi ,tana bukatar tai makonta gabadaya jitake kamar ta tafi gidan Ameenah haka takeji,...




07066508376________
'?
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*____JAMI'AR TSARO____*


*____THE WOMEN POLICE____*


_____THIS STORY IS TOUCHING HEART, I WAS SPEECHLESS TO EXPLAIN IT, BUT WE SHOULD SEE ON WHAT HAPPENED TO OUR LIFE KNOW, SO, BE WITH ME U LOVE IT MORE THAN U EXPECTED _______
'?


*NA*


*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*


*____(MRS SARAKIES)____*


*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA)* =?1?


*Bismillahirrahmanirrahim*


_____season one ep =??


_______
'?
'?


Yau talata yau direct asibiti ta shigo kafin ta wuce wajen aiki,Ruky ce zaune a cikin motarta inda Ibrahim Khalil yake gefenta,ta dubeshi tace malam Khalil, abinda yasa nace muxo nan , tattaunawa xamuyi akan yadda xamubi da case din shafa, lokaci yayi da zamu fara bincike akan wannan case din,sonake na fara bin cikena kafin shafa tasamu lpy, abinda yasa nace haka, nafiso idan aka kama duk Wanda yayi aika Aikan nan xamu fito dashi duniya ta sani da abinda ya aikata din ,yadda koma waye yaga yadda ya cutar da ita ,yaga yadda ya wulakanta rayuwar ta,idan al'umma sukaga yadda akayiwa shafa,zasufi daukar abinda da muhimmanci, Koda ko gomnati ce, shidai Khalil kallanta kawai yake babu ko kiftawa ganin yadda tai serious tana magana, tace nayi rantsuwa akan aikina,nai ALKawarin cewa zanyi aikina bisa gsky Kuma xan tsayu akanta Kuma zan kare mutuncin duk Wanda aka ciwa,xan hukunta duk Wanda yayi laifi ,Zanyi adalci akan ankina,Kuma zan tsayu akan Hakan Koda ko xan rasa Rainane ,kana ganin idan muka banxantar da rantsuwar da mukai Allah baxai kama muba akan Hakan,banaso naje wajen Allah a hukuntani akan aikina bayan nai rantsuwar cewa xan iya ,bayan Ina da damar yin Hakan to gwara nayi tunkafin lokaci ya kuremin ,sbd haka wlh ko Dan waye a kasar nan ,kodan kasuwa ,kodan siyasa ko Wani Mai Mulki kodan talaka ni Rukayya umar MaiTama in Sha Allah saina kamashi Kuma sainasa anhukanta tashi kamar yadda Shari'a ta tana dar,...


ibrahim Khalil ya sauke numfashi yace ranki dade ,Nima na Baki goyon baya indai akan ki tsayu kan gsky ne,naji duk abinda kika fada wannan shine aikin gsky, Amma ranki Dadi ba Raina kokarin ki nai ba mexai hana baxaki Sako Wani acikin jami'an tsaron ku ba ,Wanda kika yadda dashi cikin aikinnan ya xamto ku kubiyo ko kuma fin haka,ni Kinga Dan jarida ne ba duka aikinki xan iya shiga ba sai Wanda Bai Saba dokar aikin Kuba, ruky ta Sauke ajiyar xuciya tace karka damu idan da halin asa Wani sai asa din, ibrahim Khalil ya sauke numfashi yace yanxu ta Ina xa'a fara tace shafa xamu samu tunda kace yanxu tana magana Kuma akwai nutsuwa a tare da ita, anan xan samu wasu information din ,Dan itace tsaninmu wacce xata kaini duk inda nake bukata,yace shikenan ranki dade Allah yasa asamu nasara ta ansa da Ameen kafin su fita su nufi dakin shafa,, ruky ce xaune a kusa da shafa akan kujera,sai ibrahim Khalil Wanda yake gefenta ,baba lami Kuma tana wajen shafa tana Bata kunu Mai Rai da lpy Wanda ruky ce ta kawo musu Dan qarya taiwa mamah akan cewa xuwa xatai dashi office,

Ruky tace da shafa Ina jinki ta sauke kanta qasa tace , kangon da ya kaini a can saman unguwar yake Amma daga gefe, Ruky tace kince kangon Daya kaiki akwai gate awajen hakane,shafa tace hakane cikin sassanyan muryanta wacce jinya ta cinye,ta qara da cewa harma an rufin gidan ,Kuma anyi flasta, ruky tace zaki iya Gane wajen ,shafa ta sunkuyar da kai tareda da gyada mata kai ,ruky tace ok ,bari ashigo a dubaki in yaso saimu tafi,shafa tace toh a Sanyaye duk wannan abin da suke daukar Statement suke Ibrahim Khalil Yana recoding komai ,....

Ba'a dau lokacin ba Wani Dr da nurse ne suka shigo , ya duba shafa wacce yanxu dai ruwan baya xuba sosai Dan ba kamar lokacin da aka kawata taba,bayan ta dubata yace da ruky su biyo shi office dinsa, suna shiga office din,aka Basu wasu ta kaddu Wanda dashi xasuyi booking genie Dr din,bayan ruky ta karba tai cike ciken da akace tayi ,ta mika masa Dr ya bawa nurse wacce xata kai wani office Wanda anan ZA'A sakasu cikin file din shafa sannan ta nemi ixnin xasu tafi da shafa,Amma xasu dawo da ita dayake private hospital ne Kuma sunga ruky JAMI'AR TSARO CE Basu Hana ba ruky tai godiya ta fito, bayan ta fito ,ta samu ibrahim Khalil Wanda yana bakin office din yana jiranta,ta duba time taga 12 Saura ta dubi Khalil tace muje mutafi da shafa ta nuna mana inda mutumin ya kaita ,nan ne first suspect dinmu ,babu musu ibrahim Khalil yace ok, tace muyi mugama da wuri sbd naga time ya tafi sosai wlh munyi let ,ta dubi Khalil tace sorry malam Khalil ta hada hannayenta biyu guri Daya alamar Roko tana murmushi, Khalil yayi dariya yace haba ranki dade,saiki sa ana kallo na idan aka ga ace kina rokana,ya fada yana kallan mutanen Dake wajen ,Aiko kallan nasu ake,ruky tai gava tana murmushi tace ai ba laifi nai ba,shima murmushin yayi ya bita a baya suka qarasa dakin da shafa take ciki sukayuwa baba lami bayanin komai sukace in Sha Allah gove zasuga Dr,baba lami taji dadi sosai tadinga Yi ma ruky godiya kamar ta goyata, sannan sukace xasu tafi hadda ita sukeso ayi komai agaban ta,batai musuba ta shirya shafa wacce tana Dan takawa kadan kadan , haka suka shiga mota inda ruky ce ke driving,suna xuwa unguwar hayin rigasa daga hannun damansu can ,Tai musu kwatance wurin yana baki bakin titine ,saboda sabin Gini ake Wanda babu yawan gidaje awurin domin kamar Saban waje xa'a kafa,sbd duk yawancin wuraren wurin sabine Kuma kangwayene Dede kune aka rufa wasu Kuma Amma tare acikinsu,...

Haka Khalil ya sauko ya baya shafa ta front seat sbd ta duba gidajen da kyau,haka koh akayi,tadinga bin ko Ina da kallo sbd ginin ma tsilla tsilla ne xaka iya girgewa,haka suka dinga wuce gidajen da yanxuma akeyinsu,ruky tana nuna mata tace wannan ne tace a'a,ta Kara tambayar ta nan ma tace a'a, Ruky tace ki nutsu da kyau shafa,tace toh,harsai da suka kusa zagaye wurin sannan ta hango gidan ,Wanda baxata taba manta kalar gate dinba, coffee color ne,Wanda kyansa ma dayayin yadda gate din yake abin kallo ne,ruky ta daga kai ta dubeta Jin tace ga gidan can ruky tace Kin tabbata,shafa tace wlh shine anty,baxan taba mantawa ba,tunda ba saudaya ya tava kawoniba ta fada tana xubar da hawaye,ruky ta Sauke ajiyar xuciya ta dube Khalil shima ya duveta, tace muje mu duba, tace baba karku fito duba sawu kawai xamuyi muga ana xuwa gidan ko yaya,baba lami cikin rauni tace toh jami'a ,haka suka dinga bin layin Dan a nesa sukai parking Aiko sunga sawun mota sunabi sunabi har suka karaso inda yay parking motar gavan gidan ga sawun takalmi inda aka fito akai hanyar gate din gidan sawun takalmin har kofar get din gidan,Wanda yake nuni da cewa ko jiya ko yau anxo gidan ,domin gidan kadanne ya rage ba'a kammala ba,may be ma kila ko angama,kota wajenne ba'a kammala ba oho, ruky ta dubi Khalil tace mu wuce babu musu Khalil ya bita,babu Wanda yay magana acikinsu,kowa da abinda yake sakawa,har suka xo suka shiga mota,inda tace da baba lami,karkiji komai baba in Sha Allah,sai an bima shafa hakkinta,baba lami tace jami'a naga fa wannan gidan kamar na Wani hamshakin Mai kudi Kinaga fa harda bene, banaso kisa kanki a matsala nidai indai har shafa zata samu sauki ni wlh na bavarwa Allah komai kawai ki barshi hakanma kinyi kokari, Allah shine xai saka mata,. ..


Ruky tai murmushi tace baba karkiji komai in Sha Allah babu abinda xai faru,ita doka ai tana kan kowa ,babu Mai mulki ko sarauta ko siyasa,duk Wanda yayi badai daiba,ana hukuntashi ,Kuma Babu Wanda aiki vaya biyowa ta kansa,Kuma ki tayamu da addu'a kawai,ita muke bukata,baba lami tace shikenan Allah ya kareku a duk Inda kuke ,ya kareku da sharrin masu sharri,ya da tar daku akan abinda Kuka sa agaba,suka ansa da Ameen,sannan Ruky ta tada motar suka kama hanyar hospital, . ...


Bayan ruky ta Sauke su baba lami tai musu sallama Dan har dakin suka kaisu sannan sukaiwa baba lami sallama tana sa musu albarka kamar yadda ta sava,shafa ma tai musu sallama suka ansa mata da kulawa,sannan sukaje wajen Dr suka shaida musu cewa sundawo sannan suka tafi,inda ta kai Khalil har wurin aikinsa gidan , TV na GADANGA TV & RADIO,haka yay mata godiya bayan tace masa xasuyi waya,haka ta kama hanyar office bayan ta duba time ganin Daya Saura yasa gabanta mugun faduwa,ta duba wayarta Dan tama manta da ita Kuma a silent tasa,sbd kira aiko ta dauko ta duba miss call ne yafi ashirin,Kuma tasan akawai na Shareef aciki,haka ta Maida wayar ta ajiye ta Maida hankalinta kan tukinta,gefe Daya Kuma tana tunanin me xata fada a office idan aka tambayeta Ina ta tsaya,tana shiga ta xaro ido waje bayan tayi parking ganin motocin CP data Cikaro dasu wato yaxo headquarter kenan ,tunda ga police nan sun qaru, Batasan lokacin data fara anbaton sunan Allah ba,Dan CP Bashida mutunci indai akan aikine,danshi baya shiri da masu wasa da aikinsu,haka ta fara takawa jiki a Sanyaye,tana xuwa bakin office dinsu wani police Daya fito,ga ta kaddu a hannunsa , ya kalleta yace yanxu kikaxo ,kamar sokuwa da kyada masa kai ya rike haba yace tab,to CP Yashigo tun kusan 10:30, general meeting Yaxo, Kuma wlh yau ya kafa ya tsare ,duk Wanda ya makara karkiga yadda yake musu,cikin ruky ya kulle tace Dan Allah ,yace wlh ga attendance,tace gsky baxaniba,yace wlh gara kije Dan attendance dinnan shine kawai zaiceceki inma punishment dinne yaxo miki da sauki ,tace wlh tsoransa nake ji, police din yay dariya yace, Aiko haka xaki daure bari na qarasa Dan DCP Ne ya Aikoni,tace muje yay gava tana binsa a Baya tana Kuma kallan irin miss call din da tai missing kila Inaga ma shiyasa Shareef yay ta kiranta,har suka qarasa main hole din da ake meeting din,ganin ya shegi Bai tsayatava,yasa ta makale a bakin kofar ta kasa shiga ,Manya manya da kana nan police Dake headquarter nan kowa yaxo,CP ya juyo daga maganar dayake ganin shadow din mutum bakin kofa Kuma ba'a shigo ba,har ya basar ya cigaba da magana, ba'a shigo ba ya qara juwaya,yaga still dai shadow na mutum ne Kuma ba'a shigo ba,Dan haka cikin tsawa da yanayin muryar sa,yace who is standing here,come inside, Ruky da jikinta ke rawa ta shiga Dakyar kanta a qasa tanajin idanuwan mutanan wurin akanta jitai kamar ta nitse,ya kalleta yace who are you, from where are u, where are u coming let, are u out of ur sense, ruky sai hawaye, jikinta na karkarwa,...


*______ZARI'A_____*

Baba asabe ce xaune a a dakin malam Auwalu ta kawo masa abin karyawa, tana masa xancen data Saba ,na gulma akan ummah shidai kawai jinta yake,saiga ummah ta shigo,ta xauna bakin kofa tace malam xuwa nai ka barni naje na duba Ameenah,Dan wlh gabadaya hankalina Bai kwanta ba da komawar nan tata ba ,saina dinga Jin gabana yana faduwa,baba asabe ta saki Baki tana kallan ta ,tace haba maimuna wlh kece nan kike daurewa Ameenah kugu take kin xaman aurannan,Amma inba hakabaAmeenah aiba yarinya karama bace yarinyar da shekara goma Sha shida,Kuma kinsan dai tana cikin koshin lpy tunda Kabiru dai ai mutumin kirki ne

Kuma da zakice gabanki Yana faduwa wannan Rashin kudine kawai yake damunki kiyi Sana'a kinki kinsa yarinya a gava bakwa cas bare as kuwai sai Boko,to xamu Gani ai bokon ta Baku abinda xata vakun,malam Auwalu ne ya katse ta,yace ya isa asabe Bada ke takeba,ya dubi ummah wacce takewa asabe kallan badake nake ba,yace maimuna yanxu ya xa'ayi yarinya daga komawarta kice xakije gunta naga batafi kwana goma da komawa ba, gsky baxan bari kijeba nasan tana cikin koshin lpy,Dan da ace ba lpy take ba da tuni mijinta ya kirani ya fadamin, ummah tace malam kamin iyaka da asabe babu ruwanta Dani da 'Ya'ya na,ni 'ya'yana baxasuyi tallaba idan ke haka kika xabar wa naji 'ya'yan kije ga wajennan,ta nuna baba asabe tace wlh kika qara shiga min magana wlh saikin Raina kanki, asabe tace lallai maimuna wlh Baki isa ki hanani mgn ba ai gsky na fada ba karya nai ba,ai talaucinne ke damunki ba karya nai ba, ummah taiyo kanta, malam Auwalu ya mike ya daka musu tsawa, yace maimuna kije Nana saitaje ta duba Ameenah din , ummah ta fice tana huci,wlh da malam ya bari yau da saita koyawa asabe hankalinta tunda ita munafukace, malam Auwalu yace asabe ki Dena yiwa maimuna haka , kowa aida abin da yaga xai iya koh, asabe ta mike tace aidama baxaka taba daina nuna banbanci tsakanina da maimuna ba,daga haka ta mike fuuuu tai waje, malam Auwalu ya girgixa kai,





07066508376_______
'?

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*____JAMI'AR TSARO____*


*____THE WOMEN POLICE____*


https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD


*NA*


*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ____*


*____(MRS SARAKIES)____*


*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QUWA)* =?1?


*Bismillahirrahmanirrahim*


____season one ep 1?? 1??

_______
'?
'?

*Gidan AMEENAH*

Kabiru Dan Allah ka Kaini chemist ko Kuma kasiyo min magani wlh bani da lpy tun shekaran jiya,gashi babu abinda xanci Dan Allah Kabiru, ta fada tana xubar da hawaye Dan akwance take ko tashi Bata iya Yi, Kabiru Dake shiryawa xai tafi safgarsa yace ni bani da kudin kaiki chemist bare kudin magani, Kinganni nan sisina baxatai ciwon kaiba dan kina jinya kiyi addu'a kawai Allah ya Baki lpy,daga haka yasa kai yafice inda Ameenah ta dinga rokarsa tana masa magiya Amma koya kalleta,haka Ameenah ta dinga rusa kuka tanajin tausayin kanta ,ga gidansu ba'a gari yakeba , wlh da xata iya tafiya da gidansu kawai xata tafi inyaso baba ko kashe ta zaiyi wlh Saidai ya kasheta Amma auran Kabiru ta gamashi,...

Tana nan kwance taji ana sallama,Baxa ta iya ansawa ma bare tashi, ganin shiru saude na sallama ba'a ansa ba Kuma taga kofar dakin a Bude yasata afkawa dakin da sallama tana anty Ameenah, Ameenah Dake kwance tayi laushi ga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login