Showing 87001 words to 90000 words out of 278032 words

Chapter 30 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1051

farune yasa,.....



Ya fito daga dakin sa zai sauko kasa,da hularsa a hannunsa,ya sauko qasa kenan ya tarar da ummi tana hada dining table itada su safiyya masu aikin gidan, suke tayata jerawa ,adai lokacin da Ameerah da zuhrah Suma suke fitowa daga dakunansu cikin shirin fita school hannayensu dauke da jakan Kunan su,ya qarasa dining din ganin ummi tabar abinda take tana sakar masa murmushi, shima murmushin yayi bayan ya qarasa dining din yayiwa ummi side huge bayan su safiyya sunbar wurin, yace sabahul khair ya ummi, ummi tana murmushi tace,kaife halika ya habiby,yace Alhamdulillah ummi , ummi tace Masha Allah, tajawoshi ta zaunar shi kan kujera tana kallansa tace amfito xa'a fita aikin kenan,ya lumshe ido ya gyada mata kai,har lokacin murmushi ne a fuskarsa,ummi ta jinjina kai tace me xa'a xuba Maka ta fada tana bubbude warmers din,yace koma menene ummi na inaso, ummi tai murmushi ta xuba masa favorite food din dayake so,.....


Su Ameerah da zuhrah tuni Suma sun xauna ,suna kallan ummi da akhy din nasu,Saida suka ga ummi ta xuba masa abincin sannan suka gaidashi cikin girmamawa,ya juya Yana ansa musu da cewa school xasu tafi sukace eh ,ya jinjina kai yace Allah ya taimaka suka ansa da Ameen,ummi tace kunfito kenan Ameerah tace eh ummi ta fada tana kaiwa spoon bakinta, zuhrah kuwa saita turo Baki gaba tace ummi Nima ki xuba min mana ta fada tana kallan ummi,ummi tace haba Auta yanxu abincin ma saina xuba miki, Ameerah tace Yo ummi ai samu tai taga kina biye mata kome tace ne shiyasa, zuhrah tace ukty Ameerah badake nake ba,ummi tace Ameerah ki daina takurawa autata,ta kalle zuhrah tace bari na xuba miki, zuhrah taiwa Ameerah gwalo tana murmushi, ganin Ameerah nata Harararta,....




Ameerah tace wlh xan buge miki baki,AA Arab ya dago yay Musa wani kallo tuni kowacce ta nutsu ta Maida hankali kan cin abincin da suke,AA Arab ya rigasu tashi ,bayan ya mike ya Kalli tsadaddan agogon hannunsa Wanda yake na fata Baki , Wanda ya dace da tsintsiyar Hannunsa,sai Kuma ya fara takawa a hankali ya bar dining din,ya qarasa falor,dai dai ummi na fitowa daga bangaren Abba,yace ummi Abba na ciki ,ummi ta jinjina kai tace Yana nan,yace bari naje, ummi tace shikenan ta dafa kansa tace Allah ya karemin kai aduk inda kake
Son ya dawomin da kai lpy,ta Dan Masa nasiha dai haka,AA Arab ya kama hannunta ya sumbata yace Ameen ummi ,su zuhrah duk suka masa adawo lpy ya ansa musu da Ameen Yana nufar part din Abba ,bayan ya isa falon Abba,yay sallama daga bakin kofar, Abba ya ansa masa tareda bashi ixnin Shiga ciki, bayan ya shiga ya sameshi Yana yin breakfast nan ya xauna ya gaida Abba, Abba ya ansa masa cikin Kulawa yace xa'a fita Ahmad ,AA Arab ya dago da kansa yace eh in Sha Allah Abba, Abba yay murmushi yace Allah ya Bada SA'A ya kareka aduk inda kake ,ya baka nasara akan aikin Daya kawoka,AA Arab kansa a Kasa Yake ansawa da Ameen, kafin Abba yay Masa nasiha sosai,daga bisani yay masa sallama ya fita ganin lokaci nata tafiya,.....



Bayan ya fita ya tadda driver sa Wanda yake police shima harya xo da Kuma police guda hudu,moticine guda biyu, Daya itace Wanda xai shiga da Kuma police guda biyu Dayane xai driving din ,sai daya Kuma yana gaba,AA Arab Kuma xai xauna abaya,sai Daya motar police wacce xata kasance abayansu wacce yanxu taxo ta,suna ganin ya fito sukai saurin xuwa garesa sukai saluting nasa cikin girmamawa, shima cikin sakewa yake ansa musu,bayan sun gaisa suka shiga motarsu ganin shima an Bude masa motar ya shiga,babu Bata lokaci suka fita daga gidan bayan Mai gadi ya Bude musu gate, direct headquarter ya nufa domin akwai lacture da police suke duk qarshen wata Wanda duk wasu ASP Dake cikin garin dasu ake lacture din,,sai Kuma meeting din da zasuyi da some of police din Dake cikin headquarter,....


Bayan ya shiga cikin headquarter ,xo kiga police din da suke rige rigen xuwa taro motarsa,kowa so yake yaga shi ya Bude masa motar,Dan tuni dama sun San da xuwan sa,tunma kafin ayi parking motar tasa,bayan sunyi parking tuni CP ya qarasa wurin motar shida DCP muktar Wanda fuskokinsu dauke suke da murmushi, police din Dake gaban motar tuni ya sauko cikin sauri ya budewa AA Arab motar, Wanda sannu ahankali ya fara xuwa kyawawan kafafuwansa,Wanda suke cikin cover shoe masu bala'in tsada bakake dasu sai sheki suke,bayan ya sauko CP da DCP suka gaidashi cikin girmamawa,ya ansa musu shima da kulawa,.....


Duk police din Dake wajen kowa Saida ya gaidashi shima Yana ansa musu da kulawa,kafin daga nan CP ya jashi suka wuce cikin makeken holding taron,Wanda dama shi ake jira ,tuni ko Wani police ya hallara acikin hole din ,su uku ne kawai Basu shiga ba CP, DCP,sai AA Arab Wanda tare suka jero , suna tafiya Yana karewa wurin kallo Yana jinjina kai ,har suka isa bakin tafkeken hole din, Wanda suna shiga tuni wurin yay tsit kamar ba mutane awurin sbd yadda kowa ya nutsu ,daga Maza har mata Dake a wajen ,kallan AA Arab kawai suke wasu fuskarsu dauke da murmushi wasu Kuma Babu yabo babu fallasa,shidai fuskarsa a sake take haka ya qarasa Shiga cikin hole din,inda ya qarasa wurin xamansa Dake gaban hole din,shida CP da DCP,Wanda yasha decorations,kafin ya xauna suka mike sukai national anthem,kafin daga bisani su zauna, bayan anbude taro da addu'a,CP ya qara gabatar da xuwan AA Arab,da Kuma matsayinsa a wajensu,kafin daga bisani AA Arab ya fara jawabinsa,...


Babu Karar wata halitta a wurin sai sautin muryarsa Dake tashi, wacce ke tsuma Mai sauraro,cikin cool voice dinsa da harshensa , cikin turancinsa daya gauraye da larabci ,Wanda lacture din tasu Sundauki wajen awa Daya sunayi ,Kuma har lokacin ruky da Hanan Basu xoba , Shareef sai Kiran Rukayya yake Amma Bata picking ita Kuma Hanan ya kirata tace gasunan xuwa suna hanya, shima DCP sai Kiran Rukayya yake Amma baya samunta,idansa Yana kan kofa Yana dakon jiran shigowar sahibarsa=??,ga anyi attendance, kai har aka tashi daga lacture din nan su ruky Basu xoba, haka aka tashi daga lacture din, xa'a je ai break karfe Sha Daya Kuma a shiga meeting,....



__________?&


A lokacin da ake lacture nan, alokacin su ruky suna asibiti ita da Hanan wajen shafa wacce jikinta yadan tashi sosai,baba lami sai kuka take,su ruky suna bawa baba lami hkr,Dan abinda yasa ma Basu taho ba kenan daga xuwa dubiya suka tadda wannan abun, doc Fatima suke jira wacce ranar ba'a asibitin take ba, tana Wani asibitin,ita suke jira taxo ta in yaso saisu tafi,gashi Kuma har karfe Goma da kusan arba'in batazoba,sai Yanxu ne taxo,ita ruky ta bar wayarta a mota itakuma Hanan tana tare da tata,....


Gashi Hanan tasaka Rai da cewa yau xata ga AA Arab ,Dan ko lucture da tasan xa'a Yi da meeting din Bata damu dasu ba akan xuwan da AA Arab zaiyi ,ga ruky tazo ta Bata mata budget ,taso ace suna can AA Arab yaxo,ganin Shareef na Kiran ta yasata yin waje da sauri tai picking call din, bayan ta daga yace mata gashi nan AA Arab yaxo Kuma ankusa gama lacture ga Kuma anyi attendance,ai Hanan Batasan lokacin da cikin ta ya kada ba,Dan wlh indai kai missing Lacture da attendance sai kayi aikin dare na sati Daya,ai Batasan lokacin data kashe wayar ba bayan tacewa Shareef gasunan xuwa, .. ...



Cikin kidima ta koma cikin dakin wacce suka ci karo da ruky data fito dansu tafi, ruky tace meye haka Hanan, cikin damuwa Hanan tace Kinga gashi kinja mana aikin dare, ruky ta kalle ta da alamar tambaya tace da mukai me ,Hanan tai kwafa tace AA Arab yaxo Kuma shi yayi lacture ga anyi attendance,harfa antashi daga lacture yanxu meeting xa'a shiga Dan Allah mutafi ko iya meeting din musamu, ruky tai tsaki tace Dan yaxo kuma anyi lacture so what, ke dadina Dake tsoro wlh,Kuma wlh Babu Wanda ya isa yasa nayi aikin dare,ta qarasa fada tana juya ido, tace mutafi na gama kanwar AA Arab,Hanan tabita abaya ,tace aike dama vaxa ki damu ba, tunda kinada DCP babu Wanda ya isa yasa kiyi aikin dare Niko Wana ajiye a headquarter da xa'a ce baxanyi aikin dare ba,....



Ruky ta juya xata danko Hanan ,Hanan tai sauri tai gaba tana murmushi, ruky tai kwafa ta cilla mata key din motar tace sai kiyi driving dinmu Dan na gaji, Hanan ta cafe key din,ta harari ruky tace nifa svd banasan tuki yau, yasa na ki dauko mota ta,, ruky ta jingina jikin motar ta harde hannayenta tace to tunda baxa kiyi ba Nima baxan yiba,in yaso sai afasa tafiya,dama waya damu,ke kika damu Dan kije kiga yayanki ,Niko babu abinda yamin xafi,Dan wlh daga nan ma xan iya tafiya ta gida,ai babu shiri Hanan ta harareta,sai Kuma tace wlh xan rama ne wato kina sane dama yasa kika batamin lokaci Dan kawai bakyasan naga AA Arab sbd ke bakyasan sa,to wlh Baki isaba,daga haka Hanan ta Bude gaban motar ta shiga ruky tana dariya ta shiga gefenta,daga haka suka bar asibitin sukai headquarter,...


Basu suka Jeba,sai wajen 11:15:am lokacin har an shiga meeting dinma ,danma Hanan tai gudu sosai a hanyar su ta xuwa,ruky sai mita take mata ta tafi ahankali, Amma Hanan kota kalleta, saida sukaje headquarter ,suka tadda headquarter shiru kamar ba mutane acikinta,sai tsirarin police wadanda ke bakin gate da Kuma tsuraru masu Dan monitoring harabar headquarter din,bayan Hanan tai parking ta fito cikin sauri, itama ruky haka, sukai hanyar hole din police din sai kallansu suke da mamaki,ganin sai Yanxu suke xuwa,sai Kuma jikin Hanan yay sanyi wlh sai Yanxu ta fara tunanin ya zasuyi,ta Dan tsaya ta kalli ruky wacce ke gefenta tana duba wayarta alamar ma ita kamar ko a jikinta Bata damu ba,tace ruky ya xamuyi, ruky ta gintse dariyarta tace yako xamuyi keda kike xumudi xakiga yayanki ,sai kimana jagora ai,Hanan tai shiru sai Kuma ta fara tunkarar hole, din, ruky da itama karfin hali take tabi bayanta,....



Sunje dai dai kofar hole din sukaji wata daddadar murya na tashi cikin harshan turanci da nutsuwa, Basuyi magana ba, Amma wannan murya Sunsan Bata CP bace ko Kuma DCP, suka makale a bakin kofar sun kasa shiga cikin hole din sun kusa ten minutes ahaka Kuma ga inuwarsu ana Gani daga bakin kofar,CP ne ya kula dasu,Dan haka yace cikin daga murya who is standing there,sukai shiru ya qara maimaita wa,nan ma shiru yace are u debt ,Hanan taja hannun ruky suka shiga ciki wacce kanta ke qasa,suka Dan tsaya daga bakin kofar, Aiko idan mutane saiya dawo kansu yuuuu.abinda ruky ta tsana kenan ,.....


Shidai AA Arab jawabinsa kawai yake,Bai kallesuba, Amma yana jinsu,CP ya Kallesu da mamakin dama daxu Bai gansu dazu a lacture ba,yace from where are u, ante's, Hanan ce tai karfin halin cewa ,maganar ta a rarrabe,fr..from hospital, CP cikin mamaki yace to due what, ko kun manta cewa yau akwai xama na musamman ne,Dan Rashin mutunci ko lacture Baku xoba kenan,Hanan tace I'm sorry Sir,CP yace shut up, stupid, sorry for ur self,I said to due what,Hanan tace,I just to accompany my sister , cox she didn't feeling well, CP tsabar Rashin mutunci yace ita marar lpyr Bata magana ne,saike,....



Hanan ta Dan Bude ido tace sir she is the one fa, CP ya hade Rai yace who say so,ita Bata da Baki da bazatai magana ba saike,yace ke Hanan jeki xauna,ki kyaleta harsai tai magana tukunna ko ke kadai ce me baki,Hanan ta marai raice tace sir idan na saketa faduwa xatayi, CP yace nace ki sake ta ta fadin ,Dan wlh dama haushin Rukayya yake ji,tun ranar dayay mata magana a office din DCP tai Banxa ta kyaleshi ai yasan itace Kuma yasan karya take kalau take so kawai yake yaga karshen Rashin kunyarta , Hanan taki sakin Ruky saima qara damke Hannunta datai tana Dan xumburo Baki,. Dan ita Kanta tai mamakin tayama ta yanko wannan karyar da tai,...


Itako Ruky tana jinsa,yace ba magana nake miki ba Hanan ,I said leave her alone,sai asannan AA Arab ya dago ya Kallisu,yaga suwaye masu taurin Kannan,da har CP yana musu magana Amma basaji ,ganin wadannan yaran masu taurin kai,yasa ya qare musu kallo,idansa ya sauka akan ruky wacce ta sunkuyar da kai kamar marar lpyr gskn,gashi ta Wani turo Baki gaba,sai Kuma ya Kalli CP yadan ya Mutsa fuska yace cikin cool voice dinsa, they just disturbing us please,so allowed them to seat down i didn't want noise please, cikin girmamawa CP yace ok sir,ya dubi su Hanan yace go and seat down,ruky ta dago kai ta makawa CP Harara, xata Maida dubanta game maganar Aiko sai Idansu ya hadu dana AA Arab, gabanta ya fadi ganin AA Arab kila yaga Hararar da taiwa CP,Aiko saitai saurin dauke kanta , Hanan cikin Jin dadin AA Arab yayi serving dinsu ta qara sunkuyar da kai cikin girmamawa tace thank u sir ,AA Arab ya daga mata hannu , ruky tabi bayan Hanan wacce ke damke da Hannunta har lokacin suka bar wajen,suka nufi wajen xama,shiko AA Arab mamaki ta bashi ,wai tai laifi Dan ta samu yayi serving dinsu daga hannun CP Amma harta samu damar Rashin kunya,kawai saiya basar ya cigaba da bayanin sa dayake cikin nutsuwa,.Kuma har lokacin mamakin Irin karfin halinta kawai yake....








07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD




*____JAMI'AR TSARO____*


*_____THE WOMEN POLICE _____*




*NA*



*_____NAJA'ATU UMAR FAROOQ_____*




*____(MRS SARAKIES)____*




*=?1?QUEEN OF WRITERS ASSOCIATION (QOWA)=?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*



________season one ep 3?? 8??



___________?&


A bangaren gidansu Ameenah kuwa, ummah aranar batai baccin kirkiba , tunanin a wanni Hali Ameenah ke ciki kawai take, tariga da tasa aranta gobe da sassafe xata bar gidan ta tafi kaduna dauko Ameenah,Dan wlh babu wanda ya isa ya hanata dauko 'yarta ,da dai a kasheta saidai akawo mata gawarta gara ta daukota koda Hakan na nufin xata rayune batai AURE ba ya fiye mata,dadai akashe mata 'ya,....



Haka ta dinga sakawa da kwancewa har akai Kiran sallahn ASuba, sannan ta tashi ta dauro alwala,taje ta tashi Nana ma tayi,bayan ta idar da sallah ta nufi wardrobe dinta ta shirya tsaf cikin hijab dogo har qasa,ta fito daga dakinta,ta fito falor wajen karfe 6 na safe, Nana Dake kan sallaya ta mike ganin ummah cikin shirin fita unguwa tana linki sallayan hannunta tace ummah Ina xaki ,ta fada tana xuba mata ido, ummah tana kokarin Saka kudi cikin pos din hannunta tace Kaduna xani Nana xanje na dauko Ameenah ne,Dan baxan bari wannan jakin mijin nata ya kashe min ita ko Kuma ya nakas tata ba,gara indaukota ni Inasan 'yata idan shi malam 'ya'yan sun masa yawa,to nema NEMA nake.....



Nana ta sauke numfashi tace ummah gara kan kawai ki dauko Yaya Ameenah, Amma wlh abinda matar nan ta fada miki iyama wanda ta sani kenan,Ina Kuma ga Wanda Bata saniba,kinsan Yaya Ameenah da xurfin ciki,bakowa take fadawa damuwarta ba,kawai ummah kije Allah ya kiyaye, ummah ta ansa da Ameen tace idan xaki tafi makarantar ki kullomin ko Ina, kikai min key din gidan mmn sadeeq, idan na dawo xan biya ta can na karba,Nana tace to ummah saikin dawo daga haka ummah ta fita daga falon,tana ansawa Nana da ameen, ta fito tsakar gida taga zaliha tana dora ruwan zafi,ta dauke kanta,ta fito tai hanyar kofar gidan, tana xuwa tasa hannu xata zare sakatar ,saidai me babu Sakata ajiki,tai tai ta Bude kofar nan Amma taki buduwa sbd kwadan da aka sa ta waje,take gabanta ya Fadi kardai malam Auwalu ya rufe kofar da key , tunanin haka yasa ta koma cikin gidan a fusace tai dakin malam Auwalu,tana xuwa ta tura kofar dakin ta shiga,babu kowa a dakin,iya katifarsace kawai ,sai jakan Kunan sa,wato ta tabbata malam Auwalu shi yay mata haka kenan to wlh xata jirashi harya Dawo tunda ai ba dauwama zaiyi a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? wajen ba, Kuma xai dawo ya sameta, daga haka tai kwafa ta fita daga dakin ta koma bakin kofar gidan ta tsaya tana xaman jiran shigowar malam Auwalu,.....


A bangaren malam Auwalu kuwa duk Wani shiri da ummah take akan xuwa dauko Ameenah ya sani ,sbd tun furucin da tai jiya tace xata je ta dauko Ameenah yasan zata aikata din, shiyasa shikuma ya kwana cikin Shirin idan ya fita sallan ASuba,xai datse gidan da kwado, aiyasan duk min abinta dole saitai sallah xata tafi in yaso saiyaga ta Ina xata fita,ai dole ta koma,gidan ta zauna,da wannan tunanin yay anfani,ya Kuma kudurta aransa cewa ana idar da sallahn ASuba amasallacin da yake sallah Wanda ke a layinsu zai tafi gidan yayan ummah Dake tsallakensu yaje ya fada masa, abinda ummah take shirin aikatawa Dan shikadai ne xai taka mata burki akan abinda take shirin Yi din,.....


Bayan Yaya sabi'u yayan ummah ya gama sauraran malam Auwalu,ya numfasa yace ita maimunan ce tace haka,wai meyasa Batajin magana ne,yanxu Ina ita Ina xuwa gidan siriki,kai Rashin hankali,malam Auwalu da kansa ke qasa ,yace wlh Yaya nayi nayi infahimtar da ita illar yin Hakan Amma taki saurara ta,Yaya sabi'u ya sauke numfashi yace bari na fito saimu tafi gidan,Ina xuwa malam Auwalu sai hkr kasan mata ba hankali suka cika ba sai ana musu uxuri,cikin Doki malam Auwalu yace Babu komai yaya to sai ka fito,daga haka Yaya sabi'u ya shige cikin gidansa......


Babu dadewa Yaya sabi'u ya fito Yana gyara xaman hular kansa yace da malam Auwalu su tafi, Yana Kuma tunanin Irin matakin da xai dauka akan ummah,...



A bangaren baba asabe kuwa, wuyanta inbanda ciwo babu abinda yake mata,sbd shakar da ummah ta mata ba kadan bace ba,Dan inba karya taiba xata iya cewa tajiyo kanshin mutuwa,sbd azaba, Dakyar bacci ya dauketa, Washe gari da ASuba ta taso rike da wuya dayay mata nauyi da kyar ta iya cewa da zaliha ta Dora mata ruwan zafi ta kawo mata ta dumduma mata wuyanta, zaliha ta mike daga kwancen da take tana mutsuka ido Dan ko sallah batai ba,tace babarmu meyasa meki naga kina riqe da wuya,cikin axaba Baba asabe tace kije kiyi abinda na fada miki tukunna,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login