Showing 117001 words to 120000 words out of 278032 words

Chapter 40 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1044

taji baxa ta tava iya yafewa maimuna ba,dole saita sabauta rayuwar 'ya'yan maimuna,ta dorawa maimuna Kuma bakin cikin da ita da farin ciki har abada.haka rayuwa ta fara nisa musu,yaran baba asabe lawisa da bilki sun fara tasawa. Dan har makaranta suna xuwa,suna matakin primary,sai su Ameenah da aka sakasu a Rabin aji.Kuma har yau babu abinda ya sauya na Daya daga cikin halayen baba asabe saima Wasu sabbin data qaro.....



_Shi malam Auwalu mutum ne me kawaici, bawai Kuma kawaicin ma ita yake yiwa ba, a'a sbd baban asabe kawai yake yiwa asabe kawai cin,sbd mutumin kirki ne,kodan sbd shi Baxai saki asabe ba, sbd a hannunsa ya taso har kuma ya dauki 'yarsa ya bashi .Dan haka darajar mahaifin ta kawai take ci.tunda shi mutumin kirki ne,Amma wlh da badan hakaba da tuni ya Dade da sakinta ,Dan masifar da take takalar maimuna da ita ya ishe shi ,bugu da qari maimuna ma ,Dan tana hanashi ne, shiyasa kawai yake rabuwa da ita,shi wlh har mamakin Irin halin maimuna yake ,Dan macece mai hkr da kawai ci duk cin kashin da asabe take mata Bata taba daga ido ta kalleta ba bare ta rama,Kuma Hakan da take ba karamin qara kima ?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 da mutunci take a idansa ba,.Amma duk da haka baba asabe Bata fasa takalarta da masifa ba ,ga ko kadan Bata taba qaunar 'ya'yan maimuna, Kuma Bata bari 'ya'yanta suje wajen 'ya'yan maimuna, ballantana su hadu ko Kuma suyi xumunci,haka dai maimuna da malam Auwalu suke hkrin xama da ita...



"gefe guda kuma baba asabe tana ta kulafucin ta samu ciki ta haifi d'a namiji Amma shiru har su Nana da zaliha suka kai shekaru shida aduniya, Amma shiru kakeji .sai ummah ce kawai da Allah ya Bata cikin awannan lokacin,nan fa hankalin baba asabe ya qara tashi,tai tai ta saka ran samun cikin Amma shiru,tun tana boyewa har ya fito sarari kowa ya Gane Amma ita Hakan Bai Wani dameta ba .,ita kawai burinta ta samu ciki ta haifi d'a namiji kada ummah ta rigata haihuwar d'a namiji .ko Kuma axo ita Bata haifi d'a namiji ba,haka taita sa Rai da samun cikin Amma shiru.ita kan ummah Babu abinda ya dameta Amma fa duk tana hankalce da ita,baba asabe tai ta patan cikin ummah ya xube ko Kuma ta haihu ba Rai ,da Kuma addu'ar inma yaxo da Ran to mace ce,nan ta qara himma wajen addu'ar ta, cikin iKon Allah Kuma ummah ta haifi d'a namiji ,nan fa baba asabe ta kasa boye Damuwarta kamar tai hauka,haka taji, awannan lokacin Dan saida jininta ya hau sbd Fargaba da Kuma Damuwa, haka ta kwanta jinya.kums duk sun San akan me take jinyar,shi malam Auwalu mamaki ma ta bashi wlh, duk da Yana San haihuwar d'a namijin Amma wlh idan Allah bai bashi ba,zai gode masa ya Kuma rungumi Wanda ya bashi,Dan Wani Yana nan Yana nema baisamu ko Daya ba.to Kuma shi tunda Allah ya bashi ba saiya gode masa ba,nan gaba saiya qara masa Wani,sai dai yaron tunda aka haifeshi bashida cikakkiyar lpy,limonia ce dashi, haka suke ta yawan asibiti nemar masa lpy,harya dan samu sauki., Amma Wanda ya fisu san shi ya karbi abinsa,watansa biyu ya rasu,ai baba asabe kamar wacce aka yiwa bushara da gidan tsira, lokacin da yaron nan ya rasu Dan shima sunan Baban ummah yasa masa,kai Saida ta xuba ruwa akasa Tasha sbd farin ciki,tayi rawa tayi juyi,tofa daga nan ne Allah ya tsaida musu da haihuwar, daga ita har maimuna.Kuma duk da haka malam Auwalu bai damu ba,Dan Allah bai bashi d'a namiji ba,



Akwana a tashi babu wuya awurin Allah,haka dai kwanaki suke shudewa,satittika suna wucewa,watanni suna mikawa , shekaru suna kusantowa,har su lawisa suka fara girma,ita da bilki,suka xama 'Yan mata .baba asabe tafara kasa musu tallar abinci xuwa Tasha Dan sun daina xuwa makantar Boko data Arabi,tun ranar da aka musu dukan Rashin xuwa makaranta baba asabe ta hanasu xuwa tace ba jakai bane 'ya'yanta da xa'a dinga duka sbd wata Boko ,Bokon Banxa Bokon wofi,daba kudi Bokon take bayar waba, gara ta Dora musu talla ta mori 'ya'yanta.dalilin dukan nasu ma sbd sunyi fashi lokacin suna primary 6.,to tundaga nan baba asabe ta hana su lawisa xuwa Boko, Islamia ma suka daina xuwa shima Kuma akan dukan ne dai.akan basa Bada hadda kullum shiyasa suma suka musu duka nanma baba asabe ta hanasu xuwa, tace fa adinga daukar mata 'ya'yanta gara ta kasa musu abinci suna siyar mata koba komai ai xata samu kudi ta wannan hanyar,Dan babu laifi sun xama 'Yan mata.tunda zasu kai shekara goma Sha biyar haka,manema suka fara fito musu .to daga nan baba asabe tace xata Aurar dasu tunda sun isa aure, ga zaliha ai itama ta fara tasowa xata moreta..



"_Nan fa aka shiga shirye shiryen auran su lawisa,wata hudu aka sa.kwance tashi babu wuya awurin Allah,har dai lokacin biki yaxo , aka daura AURE aka kai ko Wacce gidan mijinta, lawisa aka kaita can jihar kano qauyan tofa,ita Kuma bilki anan qauyan ZARI'A yake Amma tabi mijin nata Lagos tunda acan yake neman neman kudinsa.bayan biki gida ya rage daga Ameenah sai mardiya sune masu tasowa,sai Kuma zaliha da Kuma Nana wacce itace qarama.bayan shekara biyu .su Ameenah da mardiya suna girma akuma lokacin ne kyan Ameenah da 'yar uwarta Nana yake qara fitowa. Dan babu laifi kaman nun ummah da kyanta duk suka dauko,ga samari sai fito mata suke, Amma ummah tace sai Ameenah tayi karatu,gasu samarin duk yayan masu Dan Hali ne,dan indai ta aurisu xataji Dadi agidan mijinta.acikin samarin nata, da akwai Wani shamsu Mai gidan motoci,Wanda nashi ne shida mahaifin sa, anan cikin ZARI'A yake,nan fa baba asabe ta tada Hankalinta ganin idan mardiya da Ameenah suka fita kafin abiyo mardiya ace ana San ta sau daya anbiyo Ameenah ance ana so Sau goma, Dan 'ya'yan sun kaman nin ta sukayo Dan baka kene,bakin ma Irin me shu nin nan.wannan Abu shiya qara kuntatawa baba asabe,duk da ummah ita bata barin Ameenah ta fita xance ,Amma baba asabe haka ta qudiri aniyar saita wulakanta rayuwar Ameenah, yadda babu Wanda zaice Yana Santa,...



Bayan shekara uku lokacin Ameenah ta gama junior ,ita dama mardiya ta daina xuwa tun suna primary. talla baba asabe take Dora Mata, ita ko ummah tace yayan karatu zasuyi Kuma malam Auwalu ya goya mata baya tunda haka ta zaba, itama baba asabe haka ta zaba, shiyasa ya kawo ido ya xuba mata, Tunda ya mata magana tace babu ruwansa ai 'ya'yan tane.alokacin ne Kuma wannan shamsu ya takura yace Yana San Ameenah, yanaso ya aureta kafin ta gama makaranta.inyaso agidansa saita cigava da karatun ahannunsa, ummah tace a'a da dai ya jira, idan ta gama secondary din, inyaso sai ayi auran.shamsu Bai gam suba Dan Yana mutuwar son Ameenah, baxai tsaya Sanya ba Wani yaxo ya rigashi tunda Yana ganin yadda samari suke gosulo a kofar gidansu .har iyayensa ya turo, babansa ya fara turowa wajen malam Auwalu,akan Yana so abashi ixni,malam Auwalu yace zaiyi shawara,ya samu ummah ya fada mata ummah tace da dai suyi hkr idan ta gama secondary din,da shamsu yaji haka ya ta-da hankalinsa akan Neman mafita yadda zasu yadda ya auri Ameenah a yanxu,ya yanke shawarar ya turo mamansa ko Allah zaisa adace,nanfa ya turo mamansa ta dinga sintirin xuwa,ganin yadda babarsa take sintirin xuwa gidan , ummah ganin idan kunya yasa ummah da kyar ta amince,Ganin haka yasa baba asabe kudurta aranta cewa wlh baza ta taba barin ayi aurannan ba,saidai ya auri mardiya,Dan idan yaxo gun Ameenah idan taki fita haka xakiga baba asabe tana tura mardiya taje ko zaice Yana son ta, Amma shumsu ko kallo Bata ishe Shiba,haka suka hkr, Amma Kuma "baxata fasa tura mardiya gun Saba,ta rasa ya xatayi, Neman mafita kawai take.ta rasa Gane Wani Irin farin jini yayan maimuna suke dashi . Dan ko kadan Batasan ace maimuna ta fita akomai,.kawai saita Yanke hukuncin samu wata aminiyata ta fada mata abinda ke damunta ,bayan aminyar tata ta ji me ke tafe da ita."ta rike haba tace dole ki mike tsaye,ai wlh ko nice baxan xauna ba,"tace akwai Wani malamin xaure ba boka bane ,tai mako kawai yake badawa itama tana xuwa inba damuwa xata Rakata,baba asabe "tace a'a bansan bin malaman nan fa. nifa karki kaini wajen boka,matar tace "wlh ba boka bane malam ne, addu'a kawai xai mata,da kyar baba asabe ta yarda,Dan Bata qaunar boka , tunda ubanta malami ne Dan dai kawai San biyan bukatar ta ne,to wannan shine mafari ,mafarin shigar Ameenah da ummah cikin wannan tashin hankalin da suke ciki.....




*Wanda suke so a tallata musu hajarsu xasu iya Yin magana ta wannan number Dake qasa*






07066508376________
'?Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DC2ekqRnajZAQQvErdaWfD?mode=ac_t







*____JAMI'AR TSARO ____*



*____THE WOMEN POLICE____*



*NA*



*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*




*____(MRS SARAKIES)____=?1?*




*Bismillahirrahmanirrahim*




______Season two ep 5?? 1??


_____________?&



"Baba asabe ta shirya tsaf Dan xuwa wajen malamin xaure bayan kawarta ta kwatanta mata inda yake.,acan cikin Wani qauyen ZARI'A yake .ta " tambayi malam Auwalu cewa xataje dubiya, wata 'yar gidan kawarta Bata da lpy,malam Auwalu be kawo komai aransa ba,ya amince mata,haka baba asabe ta shirya tsaf ta tafi, ko sallama bataiwa ummah ba.ta nufi Tasha direct ta hau motar da zata kaita wannan qauyen,bayan ta isa ta tarar da wasu matan aciki da alama Suma abinda ya kawo su kenan.Saida ya gama dasu sannan yace .ta shigo....



bayan baba asabe ta shiga," ya juyo ya kalleta,sai Kuma yace "ta fadi abinda ke tafe da ita,babu musu ta shiga kwara ro masa duk abinda ke faruwa da Kuma abinda take so ayi mata, malamin xaure yayi dube dubensa,ya dago ya kalli baba asabe yace "zamu iya rabashi da yarinyar, Amma bazai Yiwu ya auri yarki ba,domin taurarin yarki basu da haske ,baba asabe "tace babu komai ni indai baza ayi auran ba ai shikenan,malamin xaure yace Kije xaki ga aiki da cikawa,Nanda sati biyu,baba asabe ta qara gyara xama sannan tace "inaso arufemin Bakin malam, da Kuma ita uwar 'yar yadda babu abinda xasu iya Yi akai , sannan a mallakemin shi,sai abinda nace xa'a Yi, malamin xaure "yace shima angama,.....



Baba asabe tace"nawa ne kudin aikin, yace ki Bada duk yadda ya samu baba asabe Jiki na rawa ta kwance habar zanin ta, ta ciro duka kudin data taho Dasu ta xube agaban sa., iya na mota kawai ta bari, malamin xaure yace 'xata iya tafiya,baba asabe ta fito ranta fes ta wuce Tasha direct _ta shiga wata motar da xata kaita ZARI'A , tana shiga motar su biyu ne mata kawai aciki, dayar ma baye rabiya ce,itace bahau shiya kawai,duk sauran Kuma Maza ne,su mazan suna gabansu sune abaya sai mutum daya a gefensu,"....



"Biyun wadanda ke gaban su baba asabe,sune_suke magana wacce ta dauki hankalin baba asabe tunda suma hausawa ne,ta kashe kunne tana sauraran su,Daya ne,yake yiwa Daya magana da cewa" nifa wlh AURE nakeso nayi Amma har yau bansamu wacce tamin ba,_sai Daya Wanda ke sauraran Wanda ke magana ya kalleshi yay murmushi,sai Kuma yace"duk Yan matan garinmu da Dana gidanku Amma kace wai kana Neman matar AURE.? Wanda yay maganar yace" wlh duk babu wacce tamin har yanxu,.ga kawo ya takura min wai dole ashe karar nan _na Nemo matar AURE inba haka ya AURAmin 'yar kanwar sa,zakiya Niko ban taba San wannan kaular yarinyar ba, Wanda ke sauraran sa Mai suna dahiru yay dariya yace "au kwaila ma,? Wanda ke magana Mai suna Kabiru yace "eh mana",sai Kuma ya cigaba da fadin "Kuma kasan bawai Yan matan yimin ne basuyi ba ,kawai Ina da Wani dalili ne, nafison na samu wacce Bata sanni ba bansan taba,kai nifa bazan ma Yi auran soyayya ba.kawai auran cikar Wani burina nakeso nayi, dahiru Dake sauraransa,yace "Allah ya hadaka da wacce kake ra'ayin Kabiru",ya kare maganar Yana dariya.Wanda aka kira da Kabirun yay murmushi yace ko bansan taba indai aka bani ita zan karba,dahiru yace wai Wani Irin dalili ne haka.?Kabiru yay murmushin gefen Baki yace "sbd Sana'a ta kawai nakeso nai aure, bawai Dan Wani Abu ba,dahiru yace "Allah yasa toh, Kabiru ya ansa da Ameen a saman labbansa.,.....



Baba asabe tana Jin duk conversation dinsu,haka kawai taji Wani Abu ya darsu aranta xa Kuma ta gwada taga ko Allah xaisa adace.tana jinsu suna ta hirar xancen da suke , Allah, Allah kawai take taga sun sauka.bayan kamar mintuna goma Sha biyar , suka iso cikin ZARI'A,.su Kabiru da suke xance amotar suka ce su ahanya zasu sauka ,basai anshigar dasu Tasha ba. babu musu driver ya saukesu a bakin hanya,ganin haka yasa itama baba asabe tace "anan zata sauka " sbd karsu bace mata .Dan akwai maganar da take so suyi,...



Har sun juya sun fara tafiya sun dauki wata hanya.Suna cikin tafiya kawai sai ganin baba asabe sukai agabansu ,tana dan haki alamar sauri tai ta taro su ta washe musu Baki tana sannun ku dai 'Yan samari, dahiru ne ya ansa mata shima da murmushi.amma shi Kabiru juyar da kansa Ma yay,ta kalli Kabiru tace daxu naji kana maganar kanasan kayi aure koh? "Amma baka Samu wacce kake so din ba_,ta gyara tsayuwarta tace akwai 'ya ta zan baka auranta idan har kana Santa,sai alokacin Kabiru ya juyo ya kalleta Jin abinda ta fada,baba asabe itama kallan NASA kawai take,ai sai Yanxu ta qare masa kallo, wannan daga Gani bayaji,Bata tan tama Yana shaye shaye ko Kuma busa sigari,Dan kina kallan idansa da bakinsa xaki Gane Hakan,da alama faduwa taxo sai dai da xama xataso wannan wulakan taccen mutumin shi xai AURI Ameenah. Kabiru ya kauda kai ya jawo dahiru yace "mutafi cikin budaddiyar muryarsa wacce sigari ta gama Bude ta.yana kokarin barin wajen..



Baba asabe ta qara Shan gabansu tace"Dan Allah ku tsaya ku saurareni, Wlh da GSK nakeyi .ni taimakon ka kawai nake son Yi ,Kuma wlh idan ga ganta wlh xatai Maka Dan kyakkyawar GSK ce, dahiru ya kalli Kabiru yace "ka saurareta tunda faduwa ce taxo dai dai da xama, ba matar AURE kake NEMA ba,kila cikar burin naka ne yazo. Kabiru ya kalli baba asabe yace"Baki sanni ba Amma xaki dauki 'yarki ki bani,. kawai Dan kinji muna zance?.,baba asabe ta saki murmushi tace "ai d'a na kowa ne bawan Allah .Kuma kai bakowa bane face mutumin kirki na yarda da kai.kabiru ya kalli dahiru suka kalli juna,sai Kuma ya Maida dubansa kan baba asabe yace , "gsky kamar Baki karemin kallo bane,baba asabe tai murmushi tace "nidai burina kawai ka amince, babu ruwa na da wai ya kake ni abinda na gani shine kai mutumin kirki ne Wanda ko Wacce uwa xataso hada xuri'a da kai,cikin katse maganar ta ,Kabiru yace"Kuma ayina kuke baba, asabe tace,anan garin ZARI'A,yace" wacce unguwar,baba asabe ta fada masa cikin farin ciki.yace shikenan xanxo,baba asabe tace yaushe yace ko Nanda sati Daya ne, yanxu akwai abubuwan da xanyi,baba asabe tace "GSKy sati Daya yayi yawa kaxo ko gobe ne mana,. Kabiru yace "gsky bam miki ALKawari ba,baba saidai ko Nanda kwana uku,baba asabe ba haka taso ba tace "shikenan",sai Kuma tai saurin cewa "saidai bakasan gidanba,yace "Kuma fa hakane, yanxu ya xa'ayi,baba asabe tace" me xai hana yanxu mu shiga Dan SAHU daga nan sai muje kuga gidan ni na sauka ,ku Kuma saikuma wuce. dahiru yace "shikenan", .baba asabe ta shiga sauke numfashi ajajjere tana addu'ar Allah yasa maganin nan yayi aiki, Nan da sati biyun kamar yadda malamin xaure yace,haka suka tare Dan SAHU ya kaisu har kofar gidan su baba asabe,_baba asabe ta sauka ta nuna musu gidan tace "idan Kabiru yazo kawai yayi sallama yace wajen Ameenah yazo,in Sha Allah zata fito ,kuma xai ganta,kuma indai ya ganta saiya ji ta shiga ransa,Kabiru ya daga mata kai, dahiru ne yay mata sallama,bayan ta jadda da masa kar karya ALKawarin Dan Allah yaxo. daga haka Mai napep yaja suka tafi,baba asabe ta shige gida ranta fes, tana fatan, Allah yasa yaxo din....


Washe gari haka baba asabe taita farin ciki,Dan jiyama wlh batai bacci ba ,sbd farin ciki,idan ta Kalli ummah da Ameenah sai taji kamar anruga ma da an aurawa Kabiru ita ne, aranta sai dariya take musu.da yamma wajen karfe biyar da Rabi,baba asabe tana tsakar gida tana girkin dare Dan yau itace da kirki.ummah Kuma tana xaune bakin kofar dakin ta,tana yiwa Nana tsifa .Wani yaro ne ya shigo da sallama abakinsa , ummah ta ansa masa, yace "wai ana sallama da Ameenah,baba asabe ta dago ta dubi ummah taji me zatace,sai taji tace"waye "yaron yace wai yace sunan sa shamsu . ummah ta kalli Ameerah tace kisa hijab kije.Ameenah ta mike ta shige dakinsu Dan daukar hijab dinta.baba asabe ta wurgawa ummah Harara,sai Kuma tai murmushi axuciyarta tace" hmm an kusa a tafi gidan Kabiru yarinya,wlh wannan iyayin da kike maimuna, nake wai 'yarki me farin jini wlh saikin xubar da hawaye,muna nan Dake, tana wannan tunanin saiga Ameenah ta shigo da Leda riki riki.baba Asabe tai ta leken taga miye aciki Amma Bata Gani ba,ranta ya baci ta shige dakinta kamar xuciyar ta xata Faso kirjinta ta fito Haka takeji sbd bakin ciki, ace 'ya'yan maimuna kullum sune masu farin jini .'ya'yanta ko_ ko oho Ina wlh saita sabauta rayuwar 'ya'yan maimuna.Allah Allah kawai take gobe tayi Kabiru yazo,kuma aikin malamin xaure ya fara aiki"...



Da daddare ummah ta Aiko Nana ta kawo wa baba asabe kan kana da lemo dasu apple,da shamsu ya kawo wa Ameenah dazu,baba asabe ta kalli Nana da ledar hannun ta_tace "ta Maida basa so,haka Nana ta Maida , ummah batace komai ba tace ta ajiye, Tunda tariga da tasan halin Baba asabe ba tun yau ta fara ba.bayan tafiyar Nana Baba asabe ta fito tsakar gidan tai ta sakin tsaki a tsakar gidan nan tana habaice, habaice, Amma ummah Bata kula taba.alokacin ne Kuma Wani yaro ya shigo gidan da sallama yace "ana sallama da mardiya," Baba asabe tace "waye?, yaron yace ayuba ne, afusace baba asabe tace kaje kace Bata nan , haba yaro sai bakin talauci da naci,ita Kuma Mardiya tana sanshi ta dubi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login