Showing 165001 words to 168000 words out of 278032 words

Chapter 56 - JAMI'AR TSARO COMPLET by MRS SARAKIES.doc

23 Oct 2025

1072

ma cewa sukai idan Bata bar wajen ba sai sun harbeta,Jin haka yasa ta komawa gida ta rufe kanta a daki sai dirxar kuka take kamar ranta zai fita.ko bi ta kan wayarta Dake ta ringing Bata bi ba, acikin masu Kiran nata akwai wata yayarta wacce ta kalli abinda ke faruwa a social media shine itama tai ta Kiranta Dan ta tavvatar da abinda ta gani Amma Kuma Hajiya SA'A batai picking ba,haka yasa ta fara shiri domin taxo taga halin da take ciki dan dole SA'A ta damu, dole Kuma Saida Wani a kusa da ita .....


Hajiya SA'A tunda ta shiga dakinta wajen karfe biyu na rana ta rufo Bata Bude ba,har yayarta taxo gidan Bata Bude ba .su kansu masu aikin gidan sun tsorata da abinda Hajiya SA'A tai,babu Wanda yay gigin xuwa yace ta Bude svd sun San hilinta tsaf Saida zazzagesu.yayarta Samira ita taxo tai ta bugu tana fada mata itace ta Bude kofar, Amma Hajiya SA'A ta ki, Dakyar da magiya da Komai Hajiya SA'A ta Bude kofar tana ganjn yayar ta_ta ta fada kanta suka rungume juna , Hajiya SA'A tana ta kuka kamar ranta zai fita, yayarta Samira ta kamata suka shiga dakin ta rufo kofar suka zauna bakin gadon tana rarrashin Hajiya SA'A......



AA Arab ne xaune gaban his Excellency governor Kaduna,kansa aqasa Yana sauraran sa, governor ya qasara da fadin we are very appropriate of u Ahmad, tunda IG da minster sukaji labarin abinda kai bakaji Irin dadin da suka jiba,ga president shima bakaji Irin abinda yaji ba, Allah ya Kara dafa Maka ,ya dauka kaka,ya kareka aduk inda kake.AA Arab har lokacin kansa Yana qasa yana ansa masa da Ameen cikin girmamawa.excellency ya sauke numfashi yace "sai xancen kaiwa qara kotu ,xamu shigar da qararsu xuwa kotu cikin satinnan in Sha Allah,dukan su harda yaran nasa,ku tambayesu idan akwai wadanda suke da mata aje ataho da matan nasu, ana ya gobe xa'a shiga kotu,sbd idan Basu sani ba Dan Susan suwaye suke zaune dasu.AA Arab yace "yes ur Excellency". Excellency yace"sai Kuma yaran da kace shi sunusi ya dauke su har Yana kokarin rabasu da ransu ko ?sbd sun shiga case din wannan yarinyar,kace Dansa ne ma na cikin sa koh? AA Arab yace"yes ur Excellency, governor ya jinjina kai,sai Kuma ya ce" yaran da Kuka dauko su daga wajen 'yan ta'addar Suma xamu kira iyayensu suxo kafin ashiga kotun, duk dai abinda ya kamata in Sha Allah xamuyi, AA Arab yace"Allah yasa ur Excellency.sun Dade suna tattaunawa sannan AA Arab ya wuce gida lokacin karfe goma Saura na dare.....



Ya isa gida lokacin ummi ta sauko daga sama ,ya qaraso falon agajiye bakinsa dauke da sallama.ummi Tana qarasa saukowa downstairs ta ansa masa da murmushi a saman fuskarta,ya qarasa yay mata side huge Yana cewa sannu da Gida ummi na, ummi tai murmushi tace "sannu da qoqari namijin fama, Allah ya qara kiyaye ka aduk inda kake ya qara Dora ka akan makiyanka, Allah ya kulamin da kai aduk inda kake didat,AA Arab ya sumbaci hannun ta ya ce " Ameen first Love"kema Allah ya qara miki lpy da Nisan kwana keda Abba na".ummi tai murmushi tace "Ameen thumma Ameen didat dinmu" ya Dan ya Mutsa fuska ya ce "ummi tied" ummi ta shafa fuskar sa ta ce aidole ka gaji sbd abinda kai yau,ta cigaba ta ce "yau naga abinda ya faru,nayi mamaki na tausawa yaran da akace ansace su din, ita yarinyar ma Ashe qanin mahaifinta ne, Allah sarkie Allah kiyaye gava"AA Arab ya ansa da Ameen kansa akasa , ummi tace kaje kai wanka xan kawo Maka abincin ka Yanzu,saika kwanta ka huta gabadaya.baiyi musu ba ya ansa mata,ya haura sama xuwa dakinsa, ummi Kuma ta wuce dining room Dan hada masa abinda xai iya ci......





07066508376________
'?Follow the Mrs Sarakies=؋? =?1? HAUSA Novel Channel channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbBRj1D35fLuSHibdq1Y




*___JAMI'AR TSARO ___*



*____THE WOMEN POLICE ____*



*NA*




*____NAJA'ATU UMAR FAROOQ ____*



*___(MRS SARAKIES =؋?)=?1?___*



*TAURARI (' WRITER'S ASSOCIATION ('*



*TEAM 4 GOLDEN STAR (' WRITER'S*



*Bismillahirrahmanirrahim*



______season two ep 6?? 8??



___________?&


*ZARI'A*


Nana har sun gama zana jarabawar SSCE din su yanxu jiran results kawai suke nan da sati biyu masu xuwa suke Saka ran fitowar jarabawar tasu in Sha Allah.yau talata wajen karfe 12 Saura na Rana suna tsakar gida zaune, kowa yana yin abinda ke gabansa .ita baba asabe tana bakin murhu tana daba abincin siyarwa kamar yadda suka Saba,miya ce ma ta rage mata Bata qarasa ba Amma ta gama abincin babu dadewa .ummah Kuma tana Bakin kofarta kan baranda tana gyaran wake na girkin gida da zata Dora anjima kadan. sallamar da akai daga bakin kofar da muryar wacce tai sallama yasa su suka juya gabadayasu suna kallan Bakin kofar,wata 'yar matashiyar matar AURE ce ta qasara shigowa gidan da 'yayanta biyu D'aya macen itace Babba itace take rike da Hannunta sai namijin qara mine Wanda take goyo ,yar kace yar kace ta shigo gidan sai kace 'yar gudun hijiri,da Kodaddan zani da hijab Wanda ya cinye ta saman kanta,ga takalmin silifas ne ya si'de ya kode dun_duniyar kafarta gaba Daya tana waje, qafar nan tai butu tu kamar wacce aka kwato daga Bakin kura sbd datti,da Kun ganta kinsan tana cikin Yana yin rayuwa da tashin hankali ba kadan ba......


Baba asabe cikin Fargaba da tashin hankali ta taso daga bakin murhu tana gyara daurin xaninta jikinta na rawa ta karaso gaban ta tana kallan ta kamar Mai koyan magana ta ce"mardiya koba ita bace ba?"ta fada tana kare mata kallo atsora ce ganin kamar ba mardiya ba,kamar wacce tai shekaru tana jinya sbd yadda ta fita hayyacinta ta rame ta bushe kamar tsohuwa.cikin rawar Murya data kuka mardiya da idon ta Daya ciko da hawaye ta ce "nice Babar mu"sai Kuma ta fashe da Kuka.baba asabe jikinta yay sanyi ta riko hannun mardiya tai qasa da murya ta ce,"muje ciki Ina xuwa"mardiya ta gyada mata kai tana sheshshekar kukan da take ta rikewa,ta kamo hannun 'yarta suka shiga cikin falon baba asabe batareda ta yiwa ummah magana Dake xaune kofar falon ta tana kallan su ba.ummah tabi mardiya da kallo ganin yadda ta koma kamar wata Mai cutar AIDS.baba asabe kasa qarasa girkin nan tai sbd tashin hankali dan dama iya miyace takeso ta qarasa, ta wuce falon ta kamar xata kifa sbd sauri tana shiga ta tarar da mardiya ta kwanto D'an Dake bayanta yana mata kana nun kuka tana bashi mama 'yar macen Kuma tana xaune gefenta tana kalle kalle a cikin falon .baba asabe ta shigo cikin falon ta xauna kusa da ita tai qasa da murya tace "mardiya meya faru na ganki haka Rana tsaka kamar wacce aka Koro ko Kuma tai jinya ta shekaru? Ta qarasa fada tana kallan ta.mardiya ta fashe da Kukan da take ta rikewa tana matse hawaye da Hannunta ta ce " Babar mu ba gara idan jinya nai ba na san cewa jinya ce ta ramar Dani Hakan"ta cigaba da fadin jamilu ne Babar mu, tunda muka koma lagas waccen shekaran tundaga nan yake wulakanta ni,yake cin mutunci na da zagin iyayena,Kuma Bai tsaya nan ba kullum idan ya
Dawo daga kasuwa abuge yake dawo wa , sannan idan ya shiga gidan ya rufeni da duka kamar wata jaka , sannan ya dinga kawomin 'yan matansa karuwai Yana kwana dasu adakin da nake kwana agabana yake kwanciya da matan Banxa,idan nai magana haka zai hauni da duka kamar jaka ,yanxu da zaki Bude jikina duk tabon duka ne gashi Babu ci babu Babu Sha sai bakar wahala da axaba da yake gana min,nafi shekara Ina cikin wannan azabar, shekaran jiya yamin mugun duka sannan ya ce naje gida ya sakeni saki biyu , sannan ya Koro ni daga gidan yanxu ma da kyar na samu masu lodin kaya a babbar mota daga Lagos xuwa ZARI'A suka tai Maka min suka a doroni saman motarsu ta kaya na taho"ta qasara fada tana rushewa da Kuka.....



Baba asabe sakin Baki tai da hanci tana kallan mardiya gabanta na faduwa, Bata taba tunanin wannan ranar na xuwa ba, Bata taba tunanin jamilu xaiyiwa mardiya haka ba duba da yadda ya sota kafin ya aureta.amma Shine yau ya wulakanta mata 'yarta ya gana mata wannan axabar gashi ko ita da take uwar mardiya ta fita kyan Gani.da Kyar ta samu gathering courage wajen hada bakin ta tace cikin mamaki shi jamilun ne ya miki haka?mardiya tana sheshshekar kuka ta ce "eh babarmu" baba asabe tai qasa da murya ta ce "karki fadawa kowa wannan maganar Dan kada makiya suyi mana dariya,kiyi shiru da bakinki
,idan babanku yadawo zan fada masa asan yadda xa'ayi idanma ta kama akirawo jamilu a bashi hkr ki koma dakin ki sai ayi Hakan" da sauri mardiya Tasa kuka ta ce"wlh babarmu ni dai vaxan koma gidan jamilu ba so kike ya kashe ni ,Dan bakiga Irin azabar Daya dinga gana min da dukan da yake yimin bane shiyasa zakice na koma "baba asabe ta qara kasa da murya tace "shikenan naji, Amma ki daina daga murya ana jinki awaje kiyi shiru da bakinki bari na
Qarasa girkin Ina xuwa"baba asabe ta fada tana Mikewa ta fita daga dakin tai tsakar gidan.zaliha tana cikin uwar dakan baba asabe tana chab'a kwalliya ta fito cikin shirin fita Tasha inda take Saida abincin,ta caba kwalliya fuskar nan Tasha uban powder da Janbaki,turus ta tsaya ganin mardiya,ta rike haba tace "wa nake Gani da tsakar ranar nan kamar mardiya, mardiya ta kalli zaliha tace nice zaliha" zaliha ta qara rike hab'a tareda jinjina kai ta ce "kece kika koma haka mardiyakin ganki kuwa?"mardiya ta kalli kanta sannan ta kalli zaliha ta ce "zaliha ya baxa ki ganni haka ba dama kina ciki? zaliha ta jijjiga kai ta qaraso tsakiyar falon ta ce "wlh Ina ciki wanka nai zan fita Tasha da abinci" mardiya ta rausayar da kai ta ce "kinji Dadinki zaliha sai naji inama nice ke" mardiya tai murmushi xatai magana saiga baba asabe ta shigo da kwanan abinci a hannunta Wanda ta xubowa mardiya,ta Kalli zaliha ta ce "na Gama abincin an xuxxuba ga Mai napep din Yama xo,ta fada tana dire kwanan abincin gaban mardiya wacce 'yarta daga Gani harta matsa gaban kwanan tana murnar ganin abincin,baba asabe ta kalli mardiya ta ce "ki sauko kuci abincin mardiya" zaliha ta fito daga falon tai waje ta tarar har me napep din ma ya gama kwashe kulolin abincin,ta dawo falon tai wa baba asabe da mardiya sallama sannan ta fita kofar gidan......



Da daddare baba asabe ta samu malam Auwalu a dakinsa take fada masa abinda ya faru da mardiya,da yadda mardiya ta fada mata Irin azabar da jamilu ya rinqa gana mata.malam Auwalu kallan baba asabe kawai yake harta gama baya nin ta .bayan ya gama sauraran ta yay gyaran murya tareda gyara xaman sa ya kalli baba asabe Wacce take kallan sa taji me zaice taji ya ce" Allah ya kyauta" baba asabe ta kalleshi shekeke ta ce "ban Gane Allah ya kyau taba malam iya abinda xakace kenan? malam Auwalu shima shekeken ya kalleta yace "to me kike so nace asabe,ba sakinta yay ba,tunda sakinta yay idan ya nemi ta koma indai tana so saita koma , idan Kuma ta ce baxa ta koma ba sai a kyaleta har Allah ya sake fito mata da Wani mijin tai aure Amma haka kawai ya saketan sannan mu kirashi nace ta koma Ina kika taba Ganin anyi haka asabe dole sai idan shine ya nemi Hakan"baba asabe kasa magana tai gabanta na faduwa ko kadan bataso ace haka ta kasance da 'ya'yanta ba, tafiso ace yadda take yiwa maimuna gadarar 'ya'yan ta suna Jin dadin gidan miji Bataso ace mardiya ta dawo gida ba,kasa magana tai Hakan yasa ta mike ta fice daga dakin fuuu ,malam Auwalu ya bita da kallo Yana girgixa kai Dan wlh shi yanxu ya daina Saka Baki cikin sha'anin asabe da 'yayanta tunda haka ta zab'a Batasan laifin 'ya'yan ta zai xuba musu ido ne kawai...zaliha sai abinda yayi gaba tsaka ninta da Alhaji tanko,Dan yanxu ma daga gunsa take bayan ya gama biyan bukatar sa ya Bata kudi sannan ya mika mata ledar da ya yomata siyayyar kamar yadda ya saba, tun Bata Jin dadin abinda yake mata har yanxu ta kai Tama Saba tana Jin dadin abinda yake matan bama ta iya hanashi.haka ta shigo gidan bakinta a Washe Bata samu kowa tsakar gidan ba Dan ummah ma tana daki , direct kofarsu ta shige ta shiga falon ta tarar basa falon hakan yasa ta shige uwar d'akan nasu ta shiga ta tadda baba asabe da mardiya suna uwar dakin ta tana ta tambayarta abinda jamilu yake mata mardiya tana Bata ansa,ganin zaliha da ledoji riki riki a hannunta yasa baba asabe sakin murmushi tana sannu da xuwa kin dawo?zaliha ta gyada mata kai tana ya Mutsa fuska, tareda dire ledojin gaban baba asabe, itadai mardiya kallan baba asabe Kawai take har ta gama Bude ledojin gaban ta tana ganin kayan alatun Dake cikin ledar bakin ta kamar zai rabe biyu sbd murmushi yasa mardiya hadiyar yawu tana tunanin Ina ma itace zaliha,bayan zaliha ta xauna baba asabe ta kalleta tace "Niko ya salisu har yanxu Bai zo wurinki ba koh? , zaliha ta gyada mata kai tace "ni wlh babarmu Yama fita akaina na hkr dashi Dan bakiga Irin abinda wannan alhajin yakemin bane shiyasa wlh yafi salisu kudi Dan dai kawai tsaho ne" baba asabe ta harareta tace "ke Banxa ce zaliha ana ga gabas kina ga yamma mexaki da Wani tsoho Allah na tuba ga yaro sharkaf maijini ajika,ki kyaleni da salisu rabu dashi da alama Yana da tsari ne Amma ki bari xanyi maganin sa" zaliha ta kauda kai , baba asabe ta Bude ladar ta Kallesu tace kusa hannu muci, mardiya ta washe Baki tana Saka hannunta cikin ledar , tana tambayar baba asabe waya kawo wannan uban kayan ?baba asabe ta kalleta ta ce kedai kici kawai saurayin zaliha ne ya kawo "mardiya ta jinjina kai tana kaiwa jinyar kaza bakin ta ,daga haka baba asabe itama ta fara daga kwalbar lemo tana sauke wa.....



___________?&


Washe gari da safe ahalin gidan AIG umar MaiTama sun Hadu su dukansu a katon dining din gidan suna breakfast,har Hanan wacce tai shirin tafiya gidansu da sun gama breakfast din,can bayan sunyi nisa da cin abincin da sukeyi,ya Tahir ne ya fara mikewa follow by ya hanaf alamar sun koshi,can saiga ruky itama ta mike ,anty mufeeda ta kalli plate din gabanta sannan ta kalleta,ta ce "me kikayi haka Auta? ruky ta ya Mutsa fuska ta ce "koshi"mamah ta ce "me kikaci da har zakice kin koshi bayan abincin ma ba Wani na kirki kika ciba, so nake duk wannan ramar da bakin nan da kikayi duk su koma ki dawo Rukayya ta ainihi ba wannan ramammiyar ba"me zasuyi in ba dariya ba gabadaya dariya suka Saka harda ita Kanta Rukayya Saida ta dara, wannan shine karanta na farko da tai dariyar tun bayan data dawo gida.....



Ruky Ta ce "wlh mamah na koshi" mamah ta hade Rai tareda kauda kai gefe batai magana ba.dole haka nan babu yadda Ruky ta iya ta koma ta zauna tana tura Baki gaba tareda da hararar Hanan wacce ke tai mata dariya kasa kasa,sai Hanan ta mike itama alamar ta koshi.ganin haka yasa ruky tai saurin cewa "mamah itama aiga Hanan ta mike bakuce mata ta koma ta zauna ba"suka kalli plate din gaban Hanan ganin Babu komai yasa mamah ta ce "ita bakiga ita ta cinye ba kema ki cinye kiga xa'a ce ki koma ki qara" Hanan tai mata gwalo tareda hayewa sama xuwa dakin Rukayya Dan hado kayanta ta tafi gidan su, Ruky ta harareta ganin ta juyo tana qara mata gwalo, ruky tai mata alamar xamu gamu ne,haka nan babu yadda ta iya ta fara cusa abincin Wanda da kyar take turawa......



Rukayya ce tsaye gaban motar ya hanaf tana yiwa hanan magiya akan ta zauna,bayan tayi sallama dasu mamah wacce ta Bata atomfofi da tura ruka masu dadin kanshi Wanda da kyar ta karba,ya tahir shima kudi ya Bata,anty mufeeda ma ta Bata humra wacce ta siya awurin UK gidan kamshi collection Mai bala'in kanshi da kyau ga Kuma sauki.Hanan ta ce "lallai ma Dan bakisan kwanakin da nai bane shiyasa zakice haka" ruky ta harareta ta ce "nima Ashe kenan xan kasa kirga kwanakin danai ahannun uncle kenan, Hanan tai murmushi ta ce ai xamu hadu soon Kuma in Sha Allah xanxo ko jibi ne,da gobe ma xanxo to Dan dai kawai sbd gobe xanje government house ne shiyasa" ruky ta jinjina kai ta kamo hannun Hanan ta ce" nagode sosai sis da kokarin da kikai akaina dama ahalina gabaki daya,baxan taba iya biyanki ba saidai nace Allah ya biya miki bukarunki na alkhairi" Hanan ta rufe mata Baki tana girgixa mata kai ta ce "karki qara godemin tsakanin mu babu godiya sis komai nai miki ban fadi ba you deserve it more dear" ruky xatai magana ya hanaf Dake cikin motar ya danna musu horn tuni Hanan ta shige gaban motar tana dagawa Ruky hannu.ruky itama ta daga mata tana ki gaida (Amma) Babar Hanan kenan.daga haka ya hanaf yaja motar ya fice daga gidan bayan me gadi ya Bude masa gate, Rukayya Kuma ta koma ciki tana Mai Jin Wani Iri aranta.....



Hajiya SA'A, Dakyar Dakyar yayarta Samira ta lallasheta, sannan tai shiru, hartasa ta shiga wanka bayan ta hada mata ruwan wanka a toilet din dakin nata,ganin xata tube ta shiga toilet din yasa Samira fitowa daga dakin nata ta sauko kasa main falorn gidan Dan xuwa kitchen tasa masu aikin gidan su girkawa Hajiya SA'A abinci Mai Rai da lafiya, bayan ta shiga kitchen din bata samesu ba Dan haka ta leka dakinsu Dake can bayan kitchen din,ta kwala musu kira,zaituna ce ta fito ita da wata suna ansa mata tareda gaisheta cikin girmamawa, Samira


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login